Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daya hangota da sumoli fara tas kuma
ko aljana ta shafa mata lfya wajen caba
kwalliya NASA wasane baidau kallon Ruma kadai buga
masa zuciya ba komai daya shafeta ma buga masa
zucuyar yake ba said a kunnensa ya kwaso masa muryar
Hassana NA cewa rumaisau amma dai baki da kirki tun
safe kin kulle a daki har mijin naki yazo ya tafi ai kamata
yai Ku kafa tarihin kwasar
hotuna a ranarnan,,,,
acikin rudu YUSHAU yake amma kunnuwansa sunjiyo
amsar ruma tace fadar miji a baki baya muku wuya babu
Wanda ya danka min sadaki amma Ku daga ganin sarkin
fawa sai miya tai zaki hassana tabar gurin tana amsamata
nasan yayi nasara ya gama din mai irin fuskarsa da
zuciyarsa sun cika saurin nasara,
fiye da awa daga YUSHAU na jinyar zuciyarsa da Neman
mafita har SUMOLI tagama sallamarta tasameshi a mota
babu magana kawai yatashi motar ya fice sumoli TAGaji
da shan kamshi Dan haka ita ta tankashi tana taunar
cingam ranka ya Dade lfya kuwa ?
lfya mekika gani?
saida ta jero kwa say uku cikin gwaninta tace naganka a
firgice ne sannan yinin yau kadai naga kakara
ramewa,badon kaidin kai bane aidanakaika asibiti ko
ruwa adan samu daura maka Leda guda inka yarda
nakaika gurin kawata
FAUZIYA D SULEMAN takara mka nasan kyauta zataimaka
in kudin kakeji
yushau Yasan Iskancin tane Ya Motsa Amma Tunda Bai
Shirya Masa Ba Sai Ya So Basar Da Maganar Da Cewa
Inatare Da Hayaniyarki Aina Bar Kiba Sumayya Ke Ai
Gashi Nan Kina Shirga Kiba, Wallahh Tallahi Ba Bu
Ruwana Tsabar Ma makon kane Yake
Ramar Da Kai Ni Din Ma Kibar Godiyar Allah Ce Ba Dan
Haka Ba Nasan Sai An Kirga Kashi A Kirjina Inya Ci Gaba

Da Takaici Yasan Sai Ya Haifar Masa Da Ciwan Zuciya
Sumoli Bata Damu Ba Dan Haka Yaja Bakinsa Yai Shuru
Daganan Ta Ci Gaba Da Zuba Har Ta Cemasa Yau Kusan
Sati Biyu Kenan Bata Ga
Aladarta Kuma Tana Jin Kasala Da Tashe Tashen Zuciya
Kila Cikine Tare Da Cin Alwashi Na Rantse Da Allah Nima
Ina Haihu Saina Yi Wadannan Bidioin Andaina Barina A
Baya Tayi Jiran Amsa Harta Kule
Ta Cemasa Haba Malam Kokana Da Yakinin Cikinannan In
Natashi Kwado Zan Haifa Aikataya Ni Murna Ko Na Ganin
Idoce Maimakon Haka Sai Cin Magani Kake Yayi
Murmushi Ya Ce Kece Da Wauta Wallah Tun Kafinki
Tabbatar Da Cikin Harkin Fara Lissafin,,
tatareshi Tana Dariya To Meza A Fasa?
Ya Ce To Allah Ya Inganta Amma Dai Kidaure Ki Haifo
Nimiji Mai Kama dani....
.
Dan Aunty
GORAN DUMA (P. 59)
.
.
summaya Tazaci Yabo ne Cikin Tuntsira Dariya Ta
Ce,insha Allah Namiji Zan Haifo Lafiyayye Ammame
Kama Dani Don Nafika Kyau Ya Kada Kai Kawah Da Alama
Hankalin Nacan Ga Ruma Sumoli Ta Ce To Waimeyasa Ka
kE son Namiji?Bawai Namijin Nafiso Ba A A Kece Kawai
Har Abada Banaso Ki Haifo Mace Dan Me?
Cikin Doki Da Tashin Hankali Ya Ce Dan Banason Ki Haifi
Mace Ta Gado Halinki Na Zamo Kullum Cikin Kiran
Mubarak Ya Daura Mata Aure In
Kuma Ba A Yi Sa'ar Maikai Zuciya Nesa Dazai Saketa Cikin
Sauki Ba Saiya Nadamata Na Jaki Kafin Ya
Sakota Kai Dan Giya Ne Ma Nasan Saita Janyo Abinda
Kullum Zai Sa Ya Yanke Tada Muka,...
sumayya Tai Mugun Zuwa Wuya Danhaka Takasa Maida
Martani Har Saida Tagansu A Tsakiyar Gidansu To Allah
Yasa Namijin Kar Ya Biyo Halinka Wallahi Har Nafara
Tausayama Matan Dazasu Aure Shi A Waje Acan Amma
Dasun Shigo Ko Gizago Da Mammako Ya Ishesu Oho Dai
Yafada Cikin Dariya Sannan Yajuya Yafice Daga Gidan A
Guje Yana Dariya Yanufi Masallaci....
Yushau Kaitsaye Bayan Dawowar Sa Daga Sallar Ishai
Kaitsaye Yakoma Gidan Suna,ba Bu Yadda Atika Batai Da
Ruma Ta Zauna Ta Kwana Ba Amma Taki Yarda Haba
Aunty Atika Menene Bambamcina
Da Hafsat Ita Bakice Ta Zauna Ta Kwana Ba?
Cikin Raha Ta Cema Atika Kowa Na Dariya Atika Ta Kada
Kai Babu Bambamci Sadakine Kawai Ba Miko Waliyyai
Sun Daura Auren Ba,wato Yadda Take Da Kifinta A Gora
Haka Kike Danaki,
oho Kuma!Ruma Tafada Cikin Dariya Ana Haka Sai Ga
Mubarak Ya

Shigo Yana Wata Dariya Wadda Tasha Bambam Da
tasu,ruma Ta Nuna Masa Kofa Karka Zauna Muje
Ka Kaini Gida Naga Aunty Atika Ta Dage Sai Ta Mayar Dani
Arha,,,
mubarak Yatareta Yana Dariya Ya Ce Ai Bata Kai Yaya
Yushau Ba,shi Da Duk Ma Yakeson Siyenki Baki Ga
Fa,kamar Zai Rushemin Da Kuka Yake Rokona Na Rokeki
Da Girman Allah Kifito Ki Saurareshi,ruma Na Takaici Su
Asiya Na Shewa Asiya Ta Ce GORAN Ruma Fa Manyan
Kamu Ya Yo Guda Biyu Dazu Ya Kamo TIGER SHARK
YANZU KUMA YA KAMO KAWARA Dakin Yafara Gaurayewa
Da Dariya Hafsat Ta Ci Magani Dazu Harda Kwanciya
Akasa Amma Dai Aunty Asiya Kin Iya Yanka Lasa Nawa
Tiger Shark Zai Wa Kawara?Yaya Yushau Ne Ya Zama Haka
A Wajenki?
Suna Ta Dariya Kamar Abin Arziki Maimuna Tarike Hannu
Ruma Kamar Abin Kirki Tanajan Ta Zuwa Kofar Daki Allah
Sarki Wallahi
Kawaran Can Ya Fara Bani Tausayi Jeki Ganshi Ko Na 'yan
Mintunane, Itakanta Ruma Sai Suka Bata
Dariya Ta Yafito Mubarak Tana Cewa Zo Mu Wuce Daga
Nan Mubarak Mubarak Yai Dariya Ya Ce A,a Ki Daije Anti
Kawararnan Mu Karfasa Ta Ke Zame Mana Ba Muya Ta
Bude Kayar Baya,ruma Ta Fice Ta Bar Su Cikin Rashin
Kwarin Guiwa Dajin Takaicin Shi Ga Hanci Da Kudundune
Da Yushau Kemata Tasameshi Tsaye Jikin Motar Sa
Mubarak Yasanar Dani Kana Nemana Baiji Dadin Yadda
Ta Daure Fuska Ba Dan Haka Yajima Baice Komai Ba
Yanumfasa Ya Ce Yaya Gajiyar Taro?
Alhmdlah Ta Amsa Masa Cikin Kokarin Tilastawa Kai
Dazun Har Natafi Bamu Gaisa Ba Duk Da Cewa Takanas
Domin Na Ganki Nazo,ta Dauki Maganar Nasa Rainin
Hankali Amma Cikakken Nata Hankalin Ya Shanye Nuna
Bacin Rai Saita Ce Hakane Tokasan Komai Sai Allah
Tabbas Yafada Yana Kokarin Dorawa Amma Saita Rigasa
Zarcewa Yanzu Kuma Dare Yayi Sai Wani Jikon Kenan?
Muzamu Wuce Gida Kedawa?
Cikin Rashin Jindadi Nida Mubarak ne,in Ba Bu Damuwa
Me Zai Hanaki Zona Kaiki Gidan?
Akwai Wasu Muhimman Batutuwa Danakeso Mu Tattauna
Dake A Hanya Tadanjima Alamar Ranta Baisoba,kome
Kika Gani?
Kaje Kawai Ma Hadu Wani Jikon Har Waya Nayi Wa
Mubarak Yazo Daukana Bazaiji Dadi Ba Idan Na Bar Shi
Yakoma Shi Kadai Indan Shine Barina Nemi Afuwa Kafinta
Tare Shi Har Yafara Magana Da Mubarak A Waya Afuwa
Mubarak Zan Wuce Da Ruma Zuwa Gida Kataho Kai Kadai
Ya Budemata Kofa Ya Zagaya Bata Da Zabi Dole Ta Shi Ga
Motar Zuciyarta A Kuntace Yushau Yaita Kalatarta Da Hira
Dazata Budemasa Damar Gabatarmata Da Kudurinsa A
Saukake,amma Ruma Tai Fuska Kalmominta Tamkar Sai
Ya Siya Kamar Yadda Dariya Da Murmushinta Sukenuna

Karara Sunfi Karfinsa Saida Yaga Haza Sannan Yai Wa
Shirin Nasa Kutse
Ruma Ina Muka Kwana?
Dame Fa?
Yajima Yana Tunani Wajen Kirkirar Kalamai Masu Dadi
Wanda Baima San Ya Iyasu Ba Bansan Komai Ba A Yanzu
Sai Sonki RUMA KOMAI NAWA RARRAUNA NE SABODA SO
KARFIN GUIWATA KADAN NE SHINE GANIN ALLAH YA
JINKIRTA MIKI AURE DOMIN NA DAWO MIKI A MATSAYIN
MASOYI
MAI SHAFE KOWANNE IRIN AIBU NAKI,
ya Tsagaita Amma Shiru Kakeji Saidai Kawaicintane Kawai
Ya Boye Mugun Takaicin Da maganganunsa Suka Kunsa
Mata,musamman Daya Tuno Wani Kurarin Zawarci
Dayaimata A Can Baya Kafin Ya Saketa Wanda Ya Tabbatar
mata In An Sake Bazata Auru Ba Sai Shi Daya Saba yimata
Alfarma Yadawo Zai Sake Yimata Wani Alfarma Ta Kada
Kai ta Sake Amma Ta
Hadiye Komai Saidai Ta Bar Hawaye Nashan Sharafinsa A
Fuskarta Dayake Fitilar Motar Bata Cika Haske Ba Kuma
Wani Kaso Na Hankalinsa Nakan Tuki Bai Lurada
Hawayenta Shurunta Kuma Yakara
Masa Karfin Guiwa Ci Gaba Da Magana Dan Ki Tabbatar
Da Cewa Da Gaske Nake Duk Surukutar Dake Tsakanina
Da Alhji Kwanakin Uku Da Suka Gabata Na Nade Kunyata
Najemasa Da Maganar Yayi Farin Ciki Kwarai Saidai Ya
Bani Damar Na Nemi Hadin Kanki A Ganinsa Wannan Ne
Horo Gareni Bisa Kurarkuren Dasu ka faru, Mu Dauko
Hamida Mu Rike Abarmu Zan Sake Rantse miki Da Allah
Na Shiryawa Dukkan Lalurarki Ke In Takaita Miki Ma Har
Na Fara Nemar Miki Magani,
tun Lokacin Daya Ambaci Zuwansa Wajen Alhji Ta Watsar
Da Kallon Windon Motar Ta Koma Kansa Cikin Dauke
Numfashi Bata Kuma Kara Fahimtar Maganganunsa Ba
Tun Bayanda Ya Fadi Sharadin Alhji,tayi Shakkun
Sharadin Wanda Ke Cike Da Danne Hakki,wanda Tana
Kara Jaddada Shakkar In Zai Fito Daga Alhji,a Hankali Ta
Dauke Kai Daga Kallonsa Ta Cemasa Nayi Farinciki Tunda
Alhji Ya Bayarda Damar Yarda Tana Hannuna Dan Haka
Ina Mai Baka Hakuri Tare Da Tunatar Dakai Ni Da
Ayyukana Bamu Sauya Ba Ciki Har Da Zuciyata Mai Bijiro
Da Kudirori Ta Sanya Gangar Jiki Aiwatarwa Lallai Kafin In
Aureka Na Zaci Banida Zabinko Mawazan Aura Tunda Na
Rasa Wanda Zuciyata Keso Amma A Yanzu Na Fahimci
Aure Ba Hakkin Kaina Ni Kadai Bane,lallai Ko Na Sarayar
Da So A Cikinsa Dole In Nemo Wa 'ya'yana Da Zan Haifa
Lafya Da Farinciki
Bangane Abinda Kike Nufiba?
Tawa Rayuwar Baata Da Sauran
Tanada Na Zuci Ko Na Gangar Jiki Amma Dolene Inyi Aiki
Tukuru Dan 'ya'yan Dazan Haifa Su Zamo
Masu Lfya Ba Irina Ba Cikin Matakin Kuwa Harda Hakura

Da Aure Idan Ban Sami Mai Nau'in Jinin Dazan Haifi Masu
Lfya Ba,
sun Isa Harabar Gida Yajanyo Wata Leda Dama An
Fadamin Kune Kuke Daurewa Aljanu Gindi Ta Hanyar
Manta Kaidinsu Kuyi Tamika Wuya Ga Asibiti, Cike Da
Mamaki Wato
Mai Hali Duk Inda Ya Juya Baya Sauya Halinsa Ko Ta Ina
Yushau Ya Bullo Saiya Nuna Shi A Baude Yake,fitsarin
Rakumi Ne Ance Maganin Sikilane Karafiyan Idankin
Gama Shansa Zanzo Muje Amiki Rukiya Ba Gaggawa Nake
Ba Ruma Inkin So Saikin Warke Garau Zaki Koma Dakinki
Koda An Daura Auren
Tuni Ruma Taiwa Kwalbar Rikon Tsantsani Shidai Kallan
Mahaukaci Karafiyan Takemasa Kamar Magani Karfiyan
Din Daya Kawo Mata
Kinyi Shuru?
To Nagode Da Kokari Allah Ya Bar Zumunci,tatashi
Zatafice Daga Motar Ya Ce Baki Ce Komai Ba Ai?
A Lalace Ta Ce Da Me?
Game Da Hujjojin Dana Kawowa
Hanzarinki Na Nema Wa 'ya'yanmu Makoma Mai Kyau
Takarasa Ficewa Mujinkirta Tattaunawar Har Saina Gama
Maganin Munga Abinda Haliyai,to Ba Bu Laifi Yafada Cikin
Karsashi Dajin Farincikin Ruma
Tadawo Rayuwar Sa Tagama Indai Wuyar Ciwo Shine
Kasa Gano Maganinsa Sukai Sallama Yafice
Tashi Ge Gida Kulallen Kanta Dauke Da Yushau Tsohon
Miji,tare Da Mahaukacin Masoyi Sabon Miji,
Daidai Lokacine Alhji Ya Saki Labulen Falonsa Shima Nasa
Kan A Rude,shine Yake Kishin Ruma Da
Rayuwarta Ita Bata Kishin Kanta Harda Bazata Iya Gane
Yushau Dan Ta Adda Bane A Rayuwarta,
bayan Share Dare Cikin Raba Daidai Tsakanin Bacci Da
Ido Biyu Bayan Sallar Asuba Tasamu Ta Runtsa Karfe
Takwas Da Rabi Mairo Ta Farkar Da Ita Da Zummar Ta
Amsa Kiran Alhji..
.
Hhhh.. Wai dan ta adda?
Lallai kuwa Yushau dan ta adda ne Naziri kuma dan
Kidnapin.
Dan Aunty kuma Masoyin Ruma...
.
Dan Aunty.
GORAN DUMA (P 60)
.
.
Tun Data karasa Farkowa Ta Shiga Rudani Da Fargaba Dan
Tana Da Yakinin Banza Batakai Zomo Kasuwa A Gurguje
Takarasa Shiryawa Ta Iske Shi Afalonsa Yadda taga Fuskar
Alhji Kuma Ya Kara Bata Tabbacin Da Sauki Lfya Suna
Gaisawa Bai Tsaya Bata Lokaci Ba Yace Jiya Naga Yushau
Yakawo Ki meke Tsakaninku?

Kayan Cikinta Suka Kada Ba Komai Alhji Ko Dai Bakyaso
In sani?
Rauninta Yasanya Alhji Ya Rage Gizagon Fuskar
Sa,kwanaki Yazo Yasameni Da Maganar Yanaso Ya
Mayar Da Aurenki Atakaice Bamu Rabu Ta Dadi Da Shiba
Sai kuma Abin Mamaki Da Takaich Jiya Sai Na
Ganku Tare Kila Kin Karbi Tayinsa Kenan Gaskiyar Magana
Abin Baiyin Dadi Ba Sam!
Ruma Taji Wani Irin Tausayin Alhji Ya Rufeta Ashe Sharri
Yushau Ke masa Daya Ce Wai Ya Amince Ta Natsu Kafin ta
Amsa Dan Bata Manta Tsakanin Da Da Mahaifi Sai Allah
Duk Abinda Za Ai Lallai Baikamata Ta Wuce Gona Da Iriba
Muna Shirin Tahowa Gida Da Mubarak Ajiya Yazo Yanemi
Alfarmar Dan Allah Inzo Yakaini
To A Hanya Dai Ya Nuna Min Manufar Sa Kamar Yadda Ya
Sanar Dakai Amma Ban Amsa masa Da
Komai Ba Cike Da Doki Alhji Ya Ce Yauwa Kinyi Kyan Kai
Dan Ni A Wajen Batun Komawa Auren Yushau Ma Sam
Bata Tasoba Wanda Hakan Yasa Har Nadanyi Miki
Karambani Ban Sani Ba Ko Dadi
Zaiyi miki Kokuma Daci Ta Dago Cikin Muguwar Fargaba
Meta Zata?
Wani Yaro Mai Hankali Da Mutunci Kuma Dan Babban
Gida Shekaran Jiya Nan Yazo Min Da Kokon Barar Aurenki
Ni Kuma Nai Masa, Har Yanzu Ta Kasa Dauke Ido Alamar
Dukkan Furucinsa Suna Sauka Inda Yakama A
Kwanyarta,anyi Masa Amanna An Bashi Auranta
Kenan,wanene Wannan Ya Dace Da Ita Zallarta Mai Amsa
Sunar Ruma Kuma Mai Dogon Numfashi A Matsayinta Na
Sikila?
Tambayoyinda Sukemata Yawo A Makogoranta Kenan
Amma Ta Tabbatar Bata Da Muhallin Furtasu Nayi Masa
Amanna Ai Ba Sadakinsa Na Karba Nakira Shaidu Ba
Ruma Kamar Yadda Na Fada Miki Hankalinsa Na Yaba
Dakuma Gidan Da Yafito Saikuma Tarihin Son da Yake
Miki Wanda Naji A Bakin Sani,,
Waye Shine?
Kaitsaye Ya Ce NAZIFI MUHAMMAD Aiya Cemin Kinsan Shi
Kamar Ta Girgiza Kai Cikin Rudewar Kwakwalwa Amma
Saita Cije Rudunta Yasha Sharafi A Kwanyarta Kadai
Muryarta Na Rawa Ta Ce, Nasanshi Daga Nesa,
shima Hakan Ya Cemin Inji Alhji Yafito Daga Hadeja Ta
Jihar Jigawa Daga Shahararren Dan Kasuwar Nan Alhji
Muhammad Hadi Da Mahaifiyar Sa Hassana Haifaffiyar
Kano Da Rano,yayi Digirinsa Na Daya Sanin Halayyar Dan
Adam Na Biyu Ya Karanci Kasuwanci Amma Daya
Bangaren Yanada Nasibi Sosai A Bangaren Na,ura Mai
Kwakwalwa Saiya Hada Taura Biyu A Baki Ya Ke Taunawa
Ji Da Harkokin Kasuwancin Mahaifinsa Da Kuma Nasa
Harkokin Na Aiki Karkashin Kamfanin Layin Waya A,T,S
Dakuma Shagunan Sayar Da Kayayyakin Da Suka
Danganci Sadarwa Daya Daga Ciki Shine Milky Way Cafe

Dake Abuja Ya Samarmin Ma Anan Ya Ganki Bayan
Wannan Yana Da Kamfanin Ginin Website Tare Da
Ma,aikata Shekarunsa Talatin Da Biyar Yataba Neman
Aure Sau Biyu Allah Bai Nufa Ba Dan Haka Ya Jingine
Maganar Auren Wadda Bata Tashiba Sai Akanki
Atakaice
Ta Ture Duk Wani Shi Ga Ukun Data Shi Ga Farinsani A
TariHi Amma Baimasa A Shige Da Fice Ba Wanda
Yake Bashi Damar Kama Da Aljanu A Ayyuka,kila Dukkan
Aiyukansa Ko Na Neman Aurensa Kawai Kila Matahaka
Matan Kan Kubuce Ciki Har Da Ita
Alhji Ya Ce Nayiwa Mahaifinsa Farin sani Haka Dai Yaita
Bata Tarihin Nazifi Ciki Harda Wahalar Da Mahaifiyar Sa
Ta Sha Wajen Haihuwar Sa Inda Dole Likitoci Sukaiwa
Mahaifiyar Sa Tiyata Aka Ciro Nazifi Wanda Daganan Aka
Ciremata Mahaifa Saboda Haka Nazifi Shine Danta Na Fari
Kuma Autanta Saida Mahaifinsa Yataya Ta Karajin
Alkunyar In Ya Kara Aure Zatai Tsammanin Haihuwa Yake
nema Har Zuwa Yau Bai Zubar Da Makaman Karar Nan
Tasa Ba
Ruma Wannan Halaccin Nasa Ma Yana Daya Daga Cikin
Abinda Nake Fata Nazifi Ya Gada Kisami Danshi Ruma,
ruma Tayi Nisa Zuciyarta Na Rage
Nauyi Tana Kara Mata Damun Fuskokin Nazifi Da Kallo Ba
A Mai Suddabaru A Waya Da Sakonnin Test Ba,a Fuskar
Da Alhji Kawai Yasanshi Dakuma Cuda Jiyanta Da Yau Mai
Auwal Da Yushau Sannan Goben Ta Wadda Nazifi Keson
Shiga.
Kije Kiyi Nazari Zaizo Yau Ku Tattauna Kuma Ba Bu Dole A
Ciki In Baimiki Ba Ko Ke Banason Ki Cuci Kanki Ki Karbe
Shi Bare Ni Nayi Miki Kuka,
TaCe masa Yasan Ni Sikila Ce?
Yasan Ni Bazawara Ce?
Yasanki Ciki Da Bai Kafin Yazo Neman Aurenki Alhji A
Yanzu Nasan Ba Kyan Hali Ko Na Asali Kawai Nake Nema
A Miji Ba Ina Neman
Nagartar Lafyata Ko Ta 'ya'yan Dazan Haifa,,tuni Na
Sakawa Raina Zuwan Mijin Da Zan Haifa 'ya'ya Masu Lfya
Ko Da Kuwa Cikin Jiran Mutuwata Zata Riskeni,
ban Fahimcekiba Tajima Cikin Girgiza Kai Da Rausayawa
Idonta Cike Da Hawaye Ta Ce Ina Nufin Ka Bani Sati Biyu
Na Tattauna Da Nazifi Tattaunawa Dangane Da Ciwona
Sannan Muje Asibiti Nasan
Matsayinsa In An Sami Akasin Da Lfyar 'ya'yan Dazamu
Haifa Zata Shiga Gararin Jihadi Ne Mucetosu
Ta Hanyar Hakura Da Auren juna In Kuma An Dace Nayi
maka Alkawari Sakeyi Maka Biyayya Akaro Na Biyu
Alhji Ma Yaji Hawaye Naneman Kwacemasa Na Gamsu
Insha Allah Ba Za Akara Samun Akasin Da Aka Samu A
Baya Ba,tamike Ta Bar Falon Daidai Lokacinda Wayar
Hannunta Ta Kad'a, Hello Akayi Shuru Da Alama Anajinta
Saita Sake Maimaitawa Rumaisau Nazifi Yakira Sunanta

Cikin Yanayin
Nutsuwa Da Kuma Damuwar Yadda Yaji Muryarta Tai
maza Tajanyo Natsuwa Na Am Barka Da Safiya
Barkanki Dai Yaya Naji Muryarki Kamar Kina Cikin
Damuwa Yadan Gitse Murya Ko?
Zuwa Yanzu Nasan Kinsan Waye Mahaukacin Masoyi
Kuma Waye Nazifi Muhammad To Don Allah Mu Ajiye
Game A Gefe Guda Muyi Abin daya Kamatarmu Ina Cikn
Rudun so Ruma Ba Bu Abinda Zai Warware Ni Sai Shiga
Zuciyar Wadda Nakeso Nasamo Aminci Kuma Naji
Matasayi Na Ina Sonki Ruma Karkiya Wasa Da Alamarina
Bokanci Ko Aljananci Datake Zata Masa Ya Dawo Sabo Ta
Ina Yasan Alhji Yasanar Da Ita Kansa?
Wannan Yasa Ta Tare Shi San Dataji Zaizarce Da Maganar
Abinda Ya Riga Yafara Samun Gurbi A Yuciyarta Wato
Sonsa Gyara zancenka Dai Nasan Nazifi Muhammad
Amma Har Yanzu Bansan Mahaukacin Masoyi Ba Yai
Karamar Dariya Ai Bakiso Ki Gani Bane,,to Ina So Insanni
Yaushe?
Duk Lokacin Daka Shirya,
Nasanar Dake Yau Kawai Nake Da Ita A Kano Kin Lashi
Lokatai Da Yawa A Hutu Cikin Rashin Kulawa Ta Ce Ba Bu
Matsala Muna Iya Daga Sanin Har Zuwa Lokacin Dazaka
Samu Lokaci Kai Tsaye Ya Amsa Ko?To Dama Nakira Kine
Inji Karfe Nawa Kika Shirya Zuwana?
Dazaka Zo Din Kakemin Lissafin Na Lashi Lokuta Saboda
Haka Zaka Buga Sammako Gobe E,h Ai Maganar Aurena
Zata Kawo Ni Ba Maganar Mahaukacin Masoyi Ba Ruma
Tadan Rausaya Kai Na Gajiya Da Yawo Da Hankali Inkaji
Wani Abu A Bakina Dangane Da Aurenka Malam Ai Ka
Kaddara Kawai Ba Daga Zuciyata Yataso Ba Ta Yaya Zan
Auri Mutumin Da Ban sani ba?
Au Yanzu Baki San Nazifi Muhammad Ba Alhalin Nasan
Alhji Bazaimiki Kwange A Tarihina Ba Ta Cemasa Nida
Mahaukacin Masoyi Nake Magana Yanzu Shine Kuma
Bansaniba,yaCe mata Shikenan
Kishare Mahaukacin Masoyi Ki Saurari Nazifi Muhammad
Kawai Ki Sanar Da Ni Lokacin Da Zanzo Don Allah
Karo Nafarko Datayi 'yar Dariya Shikenan Kazo Bayan
La,asar Ka Saurari Maganganun Fatar Bakina Wadanda
Suka Sha Bambam Dana Zuciyata Zaka Fara Sanin
Gaskiyar Zuciyatane Daga Ranar Dana Sanka A Hakikanin
Sunayenka Biyu Nazifi
Muhamma Da na Mahaukacin Masoyi
Nidai Bukata A Saurareni Yafada Yana Ci Gaba Da Dariya
Har Ta Kashe Waya Bai Ankara ba,
.
Pls. Amin uzuri rashin jina kwana biyu. Kauyen namu ne
wutar ta baci, babu caji...
.
Dan Aunty.
GORAN DUMA (P 61)

.
.
Katin Zamowarta Sikila Tagani A Hannunsa Wanda Da
Alama Tayi Murna Da Ganin Haka Ya Zauna A Kujerar
Kusa Da Ita Ya Ce Kinama Gamsuwa Da Sanin Dakika Yiwa
Nazifi Ko Kina Bukatar Kari?
Ruma Tadubi Shi A Takaice Cikin Yanayin Kasala Da
Sanyin Jiki Amma Rudu Ya Hanata Tankawa Dole Ta
Kawar Dakai Tana Dan Kebe Baki Na Rashin Madafa
Nazipi Ya Mike Ina Zuwa Ya Ajiye Card Din Itakuma Tana
Tunanin Miyaja Raayinsa Haka Bata Canki Adadin Lokaci
Ba Yadawo Falon Hannunsa Dauke Da Wasu Takardu Kai
Tsaye Ya Karaso Gareta Yamika Mata,hannunta Na
Karkarwa Ta Karbi Takardun Tafara Kirgasu Da Ido Guda
Uku,sannan Cikin Sa Wa Azarbabi Karfi Ta Fara Nazarin Ta
Farkon A Natse Dukkan Takardun Sunfito Daga Asibitin
Koyarwa Na Aminu Kano Takardar Farko
Ta Sakamakon Gwajin H,I,V NE Kanjamau Wanda Yanuna
Ba Bu Cutar, Batasan Abinda Ya Rudata Ba Da Sauri Cikin
Bugun Zuciya Tajanyo Takarda Ta Biyu Itakuma
Sakamakon Gwajin Ajin Jini Ce Blood Group Wanda
Sakamakon Yanuna Rukunin Jinin Nazifi B Ne Ganin
Hakan Yakara Mata Dokin Na
Ukun Wanda Takesa Ran Nan Makomar Aurenta Yake A
Takarda Na Ukun Indai Dagaske Nazifi Yasan Ita Sikila Ce
Da Gaske Ita Ce!Taji Gabanta Yasake Tarwatsewa Cike Da
Tsoro Tabi Takardar Da Nazari
Sakamakon Gwajin Gynotype Ne Kamar Yadda Tazata
Tako Yi Dokin Ta Tarar Duk Wani Nauin Da Ake Wa Duba
Da Nazari Tayiwa Takardar Nan Tayi Na Fargaba Tayi Na
Doki Tayina Shakka Tayi Na
Tabbatarwa Tayi Na Murna Sakamakon Gwajin Nazifi
Yanuna 'ya'yan Jininsa AA NE Akar She Ta Daga Ta Dube
Shi Cikin Zubar Da Hawaye,zuciyarta Da Kwakwalwarta
Basu Tattauna Bataji Sun Aiki Bakinta Na Yanke Hukunci
Mekake Nufi?
Tafada Cikin Rauni Wanda Hawaye Ya Taimakawa Nuna
Kai Nazifi Ya Zube Gabanta Cikin Kuzari Ya Dafa Hannun
Kujerar Datake Zaune Maimakon Hannayenta Da Inda
Halacci Su Suka Kamata Yadafa Shima Idansa Suncika Da
Kwalla Amma Ya Kyalesu Ya Bayyana Daga Makyankyasar
Soyayya Suka Taso Bana Rauni Ko Farin ciki Irin Nata Ba
Yazura Idonsa Cikin Nata Ya Ce Ina Nufin Nazifi Ya
Cancanta,,,na
Cancanta Ruma Kizo Mu Rayu Tare Tayi Baya Cikin
Tarairayarmu A Matsayin Ma Aurata Taimakon
Junane Ruma Ko Wannan Yakamata Kituna Inasonki
Ruma Idan Kin Aureni Kin Yi Taimako Kuma Kin Ceto Dan
In Ba Haka Ba Kila Son Naki Ya Iya Kisa In Narasa In Na
Aureki Na Taimakeki Dan
Rauninki Na Bukatar Mai Sonki Irina Lfyarki Tana Bukatar
Mai Sadaukar miki Da Komai Irina Ya'yanki Suna Bukatar

Sirkin Jinina Wanda Zai Cetosu Daga Zama Gundarin Sikila
Taji Tana Neman Barkewa Da Kuka Sai Rausaya Kaikawai
Take Ta Ce To Idan Hakane Kaine Kawai Zaka Iya Taimako
Bandani Domin So A Aure Yakamata Ne Ba Wajibi Ba
Zaman
Lfya Da Kwanciyar Hankali Kan Riskar Da Kyakyawar
Manufa Kammaluwar Iyali Masu Koshin Lfya Da
Kyakyawar Zuciya Sune Manufar Iyali So Ne Zai Jagoranci
Haka Ko Hakuri Da Sadaukarwa
Yanzu Hankalin Nazifi Yafara Kwanciya Yanzu Zuciyar Sa
Ta Canja Bugu Daga Fargabar Yada Manufa Saboda Ta
Shinshino Nasara Yanzu Bugunta Na Cin Nasarane
Dakuma Wanzuwarta A Fagen Da Masoya Ke Taka Rawa
Sabanin Da Can Ba Da Take A Matsayin Masoyiya Ita Kadai
Kuma Take Taka Rawarta, Yamike Tsaye Yana Nazari Ya Ce
Sam
Bazan Yarda Da Raayinki Ba Abubuwa Da Dama Nacin
Albarkacin So Ni Shaidane Zuciyata Babban Masaki Takai
Aka Cika Mata Da Sonki Ba Shine Dalilin Dazan Iya
Sadaukarmiki Da Komai Ba?
Tun Da Dadewa Nasan Type Din Jinina B Ne Amma Banta
Ba Daukar Sa Wata Tsiya Ko Ya Sanya Ni Murna Ba Saida
Na Tarar Danaki Type Din AB Wanda Da Aceni
AB Ke B Kila In Dauwama Cikin Rauni Da Kukan Bazan Iya
Biyan Hakkin Soyayya Ba Alokacin Dakike Bukatar jini
Tanadin Zaman Lfya Da
Kammaluwar Iyali Ne Ko Kuma Tanadin Sadaukarwa So?
Ruma Kamrauninta Yasa Ta Sheshekar Kuka
Kwakwalwarta Ta Gaza Nazifi Ya Durkushe A Gabanta Ni
Inkin Danganta Son danake
Miki A Tanadin Aure Kawai Kin Yiwa Son Kwange Ina
Sonki Da Kyau Zan Iya Sadaukar Da Komai Dominki,in
Ban Aureki Ba Ma Ba Fasa Sonki
Zanyiba,dan Haka Nasan Sonki Ba Shiga Zuciyata Dan
Bukatar Aure Kawai Ba Yadda Nake Jin Sonki
Ba Haka Na Saba Ganin Maza Nason Matayensu Ba,takasa
Magana A Cikin Tunaninta Abu Uku Kacal Ne Aranta
Amma Masu Fadi A Tarihinta, "Auwal Yadawo,tafada
Acikin Ranta Yayinda Kamar Nazifi
Yasan Tunaninta Ya Ce Nafi Auwal Sonki Ruma
Ina kasan Auwal?
Kai Tsaye Nazifi Ya Amsa Komai
Ake Nasani Ruma Wannan Zai Baki Shaidar Ban Fara
Sonki Da Wasa Ba Ta Cemasa Duk Lokacinda Ka Shirya
Nasan Sirrin Mahaukacin Masoyi
Saikadawo Ka Karbi Amsata
Cikin Dariya Ya Mike Tunda Kince Duk Abinda Zanji Daga
Gareki Yau Na Fatar Bakine Na Yarda Da Maganarki Ta
Yanzu A Fatar Baki Acan Cikin Zuciyarki Nasan Kin Binne
Amincewa Dani Duk Ranar Dakika San Mahaukacin
Masoyi Saikin Baniko?
Nayarda Zantafi A Hakan Wato Da Gaske Har Yanzu Zakaci

Gaba Da Wasa Da Hankalina!Haka!Bazaka Tausayaminba?
Da Gaske Ruma Bansan Mahaukacin Masoyin Dakikeson
Saniba Baya Gani Da Nake Tsaye Gabanki Ba,har
Yanzu Nakasa Gano Abinda Ya Baki Mamaki Ko Yake
Rudaki A Mahaukacin Masoyi Ko Sunan Ne?
Wato Mahaukacin Masoyi?
In Shine Abokina Mas!Ud Ya Rada Min Tun Bayan Ganin
Haukan Son
Danakemiki Daga Gani Daya Kacal Sannan A Lokacin
banda Sunanki Da Lambar Wayarki Daya Ban San Komai
Akan kiba, Kaine Bakasan Ni Ba Anya?
Ta Ina Ka Bi To Kasanni Da Har Kake Iya Sani Nani Da
Abinda Zuciyata Take Rayawa Taina Kake Kallon Halinda
Nake Ciki Har Kayi Tsokaci Akai?
Ban Manta Ba Kayimin Ganin Farko Ne Ranar 15th Nov
Kuma Ina Tsammanin Tun Wajen 18th Nov Nafara
Samun Sakonninka Wadanda Suke Nuni Kana Ganin Duk
Motsina Da Gaske?
Cikin Bayyana Mamaki Kinsan Da Haka Kika Kasa Sanar
Dani Saida Lokaci Ya Kure?
Kinga Yanzu Za Akira Sallar Magariba To Naji Kwantar Da
Hankalinki Kibani Sati Biyu Inje
Gida In Rago Ayyukan Gabana Indawo Takanar Inzo
Muwuni Kina Nuna Kwarewar Aikinki Akaina Wato
Jaridanci Na Ci Alwashin Ba Bu Amsar Da Ba Zan Bayar
Bisa Zahirin Gaskiya Ba,,,,
kayi Alkawari?
Nakusa Ta Ce Ba Bu Laifi Allah Yakaimu Ina Rokon
Alfarmar Kafin Satin Biyun Kibani Damar Turo Manya Su
Share Fagen Neman Aurena,,na Karanceki,,kuma Bakinki
Ma Bai Furta Sharadin Aurena Jigine Yake Da Sanin
Mahaukacin Masoyi Ba,,
to Yanzu Na Furta Tafada A Hanzarce Da Alamun Matsawa
Kanta Da Dakewa Shikenan Ma Na Samo Amsar, Ita Ce Ba
Haka Bane Tundakin Tabbatarmin Furucin Bakinki
Dabanda Kudurin Zuciya Dole Tasami Kanta Cikin Dariya
Tana Kada Kai Kawai Shima Yana Tayata Sai Sannan
Hankalinta Yadawo Kan Abincin Saukar Babban Bakon Da
Aka Jeremasa Bakaci Komai Ba?
Wayafada Miki?
Tarakashi Har Wajen Motar Sa Dan Tafiya Suka Tsaya
Suna Dan Hira Yana Bugun Cikinta Danjin Kalmar
Amincewa Daga Fatar Bakinta Kamar Daga Sama Yushau
Ya Jefo Tambaya Daga Bayanta Rumaisau Wanene
Wannan?
Ta Shanye Cikin Firgici Sannan Tajuya Ta Dubi Nazifi
Wanda Ke wasa Da Makullin Mota Yana Cillawa Sama
Yana Cabewa Yanayinsa Yana Nuna Banza Ya Baiwa Ajiyar
Yushau Tun Datana Dayakinin A Sanin Da Yaimata Bazai
Kasa Sanin Yushau Cikin Rayuwarta Ba Sau Uku Tana
Kallon Mutanen Biyu Dake Gabanta Daya
Bayan Daya Tamkar Mai Canki Cankin Wanda Zata Fifita

Ko Wanda Zata Kaskantar Yushau Yazo Wuya
Kamar Sunaso Su Yarfashine,kai Bakasan An Mata Miji
Bane?
Ruma A Firgice Tajuya Tare Da Dora Hannu Aka Kuma Da
Shirin Kurma Ihu Musamman Data Ga Nazifi Na Dunkula
Hannu Murya A Tausashe
Nazifi Ya Amsa Aini Ne Mijin Ranka Yadade Sannan
Yashiga Motar Sa Yanadaga Ma Ruma Hannu Zamuyi
Magana A Waya Daga Yushau Har Ruma Sunyi Mutuwar
Tsaye Kowa Danasa Dalilin Mutuwar,nazifi Na Bacewa
Yushau Ya Farko Ta Hanyar WaiGowa A Fusace Ga Ruma
Dan Ya Sauke Mata Fishinda Ya Tattara Amma Yana
Waigowa Yagawayam Tuni Ta Bace Cikin Rashin Hayyaci
Shima Ya Ruga Tasa Motar Ya Figa A Guje..
.
Dan Aunty
GORAN DUMA P( 62)
.
.
Masud Na Kwance Rigingine Kan Gado Da Laptop
Gabansa Yana Shawagi A Shafin Zumunci Na Facebook
Nazifi Nata Faman Kai Komo A Tsakiyar Falo YazaBuro A
Fusace Ya Fusge Laptop Kamar Zai Bugata Kasa Saikuma
Yafasa Ya Dangwarar Da Ita Kan Sofa Yajuya Cikin
Hargagi, Wallahi Zan Kashe
Kada Mari Malam Nazo Da Matsaloli Amma Ka Hana
Kwakwalwarka Ta Tayani Neman Waraka Da Wannan
Latsetsen Takaici Ya Ishi Masud Yayi Zugui Yana Kallon
Nazifi Sai Can Ya Basar Cikin Ko Inkula Ya Ce Aume Ma Ka
Ce Menene Matsalar Ya Ce Da Alama Tarkona Yagama
Kama Ruma Harma Nayi Azarbabin Sanar Da Ita Kafin
Sati Biyu Zanturo.
Munfito Zataimin Rakiya Muka Ci Karo Da Wannan
Banzan Mutumin Yushau Alamunsa Sun Nuna Lallai
Yanzu Tauraron Ruma Haske Yake A Idonsa,,ina Tsoron
'yan Ubanci Da 'yan Uwanci Masud Za A Iya Yankan
Bayana Bayana Idan Nayi Wasa,,kasamo Wata Dabarar?
Da Sauran Aiki Masud In Nayi Nasarar Samun

2 Comments On GORAN DUMA
avatar
jannat

1 year ago

Reply

08062236094

avatar
jannat

1 year ago

Reply

08062236094

Please Login or Register in order to submit comment