Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce,
aljanna ba ta samuwa da wayo ko dabara sai da aiki".
Nan ma cikin rawar murya ya ce.
"Zan je gobe da sanyin safiya cikin yardar Allah.
watakila anan motar ya zubda shawarar data basu.dan
tunda sukai haka da ummanta baikara bi
takanta ba har aka shi ga hidimar biki sosai.ruma duk
wani farincikinta da ita da ummanta da balaraba duk
yake suke kawai. aka daura auren ranar lahadi
akakai hafsat gidanta dawaki road aka kai ruma nata
gidan sallari kowa ya watse aka bar su da halinsu.
kamar kowa ce amarya abokan ango sunkawo ango
sunkuma danyi barkwanci sukai sallama da
amarya suka tafi.ruma takasayin komai illa data tuna
auwal amma a
a wannan karan taki zubda hawaye musamman
data tuna cewa ummanta taimata batun sayarda abunda
ta ce ayi wannan kadai ya wuni yana faranta ran ruma
agundure ya cemata ALLAH ya sauwaka kuma
maganar gwaji ma aita wuce kamar yadda nafada,indai
zuwa gwajin bazah. tankwabe alhji hana shi daura
aurenba....
nibandauki ciwon ruma wata matsala ba a cikin auren.a
da ita..
momi tajima kafin ta iya magana
yushau bakasan auren nan alhajine ya matsamaka
ko?
cikin murmushin yake ya ce aa
niba matsamin akaiba,kawai a inda muka sha banban ku
abinda kuka daukeshi damuwa ko matsala ni awurina ba
matsala bane.
Momi fuskarta cike da damuma ta cemasa dan ALLAH
yusha u meyasa baka bijirewa auren ruma ba tunda
akwai matsa a cikin auren?
abinda baka fahimta ba shine,kai baka kallon ciwon ruma
matsala,nikuma a duniyar nam banida matsalar datafi shi
girma,ko tattalin ciwon ruma nake,to na tabbatar ina
yimasa tattalinda yake wa rayuwarta amfani dan ina
kokarin kore dukkan abinda zai motsamata ciwon saboda
inajin hakannyanadagamin hankali nandai yushau yagane
yayi katobara kuma idan hakan yaje kunnen alhji da
matsala danhaka ya
gyara zancensa "Haba Momi ba ki fahimce ni ba ne, ko
Rumasa'u ba

ta aure ni ba, ai ni mai zage kwanji in kare mata abin cuta
ne, balle ni in zame mata cutar, don Allah ki kwantar da
hankalinki ki bi mu da addu'a... Ni fa babu wanda ya
matsamin aurenta".
Momi ta yi shiru kawai da alama zuciyarta ta fara sanyi,
sai can jimawa ta ce.
"To maganar zuwa asibiti?"
Tana direwa ya amsa cikin kwantar da kai da murmushi.
"A kyale maganar gwajin kawai, ko ya ya zata haifar min
'ya'ya ina son su haka zan kuma tanade su".
ta ce koya zaku haifadai angaya muku mutum daya dai
baya haifar sikila. hm..ya ce ko yaya zamu haifa momi kui
mana adduar ALLAH ya bamu ikon kula dasu.. (kaji gulma
kamar dagaske) ta ce amen amma tilasne kaje ga
mashawartan sikila da jin irin dawai niyar dake gabanka.
ya cemata zanje gobe da sanyin safiya insha ALLAH....
.
To ai banda Yushau ko da mace lapiyar ta kalau ba sickler
bace tana bukatar tattali da kulawa piye da yadda
sarauniyar ingila take bukata,
pls take note my guys.
.
Dan Aunty.
GORAN DUMA (P 28)
.
.
.
watakila anan motar ya zubda shawarar data basu.dan
tunda sukai haka da ummanta baikara bi
takanta ba har aka shi ga hidimar biki sosai.ruma duk
wani farincikinta da ita da ummanta da
balaraba duk yake suke kawai. aka daura auren ranar
lahadi akakai hafsat gidanta dawaki road aka
kai ruma nata gidan sallari kowa ya watse aka bar suda
halinsu.
kamar kowa ce amarya abokan ango sunkawo ango
sunkuma danyi barkwanci sukai sallama da
amarya suka tafi. ruma takasayin komai illa data tuna
auwal amma a
a wannan karan taki zubda hawaye musamman data tuna
cewa ummanta taimata batun sayarda abunda ta ce ayi
wannan kadai ya wuni yana faranta ran ruma Ango da
amarya wato ruma da yushau,shi kallon tv ita kallom
yatsun hannunta fiye da minti sha
biyar .rumaisau dai bata da abin cewa amatsayinta na
mace da akasani da karancin azarbabi da
yawaita kunya yushau ne mai abin cewa inyayi kuma yai
masa kyau
amma girman kai da tattalin shugabanci yahana shi motsi
a kar she saikawai ya mike yana nuna
mata leda ya ce ganaman nan samo faranti kibani nawa.
ta yunkura jiki a sanyaye ta je kitchen ta samo faranti

biyu .yan
shila ne guda shidda,ta zuba masa uku muryar sa narawa
ya ce biyu ya isheni.
ya wuce yana cewa to saida safe
ALLAH Yatashemu lfya amsar data bashi kenan bayan
fitar sa,
kaitsaye bazata ce taji ciwon abinda yaimata ba.in ma
hartaji ciwon to bazai wuce na bar mata sarari mai katon
fadi ba wanda zataita sukuwar tunanin auwal da lissafin
DAMA ACE (SUNAN WANI LITTAFI.) haka tawuce kitchen
ta aje naman a frige dan tarasa abin ci ta garkame
kofarta...
tayi kuka iya yinta inda daga baya ta tuna da hudubar
mahaifiyarta ayaudin kafin akawo ta gidan miji.
babbar ALFARMAN DAZAKIMIN RUMA ITA CE MANTAWA
DA AUWAL A FURUCI DA HAWAYENKI GABAN MIJINKI,KO
BAYAN IDONSA,KIBAR GANIN BABU RAN AUWAL DAN
HAKA BAI ISA A YI KISHI DA SHI BA,INA TABBATAR MIKI
KO BAYAN KO BA TA BA AUWAL BA BAKINKINE YA
KIRKIRE SHI YUSHAU ZAIYI IYA KISHI DA SHI ,MATAKIN
DAZAI DAUKAKUMA WANI SANADI NE NA KORE ZAMAN
LFYA A TSAKANINKU WANDA HAKAN KEME
ZAI DAMI DUNIYARKI..DON ALLAH RUMA KARKI BANI
KUNYA BANTA BA ZATON DUK WANI ABIN TIR A CIKIN
SHAANINKIBA.DON ALLAH KICI GABA DA KORESHI A
ZAMANKI DA YUSHAU KITOSHE DUK WATA BARAKA
DAZAIKUKA DAKE MUSAMMAN TA KORAFIN KIN
MALLAKAWA AUWAL ZUCIYARKI KINBAR MASA GANGAR
JIKINKI..
SHIDAI AUWAL TASA TAKARE MUNA SAKA MASA RAN DA
CE DA RAHAMAR ALLAH
wannan nasihohin sune sukafi tsayamata a rai tsawon
kwanaki bakwai abinda ke faruwa kenan tsaka.
Tsawan wadannan kwanakin hajiya ke tada mubarak ya
kaimusu abinci safe rana da dare.saboda haka ruma
batakowani irin aikin wuya inbanda wanke wanke da
shara saiko tafasawa yushau ruwan shayi a duk sanda yai
umarni hajia nada azancin na dauke musu nauyin
abinci,hikimar hajiya shine,daga cikin babban abinda
yake motsawa sikila ciwonsu shine aikin wahala
ko yin aiki mai yawa a lokaci guda.a wasu lokuta wasu
dayawa ba asanin sikilane sai sunyi aure.dalili
.anan shine.aure yasa dawainiya ta hau kansu na kula da
gida da hidimar maigida.sannan basu saba kwanciya da
namiji ba,kwatsam sai su wayi gari cikinta.musamman
idan suka hadu da namiji mai yawan bukata.sai abin yafi
karfin yanda zasu iya dauka..
a azancin hajiya babu da cewar akai ruma da mai aiki a
halin yanzu
ga amarci gakuma rashin fahimta dake tsakaninsu duk
wadannan uzurorine dake bukatar kadaici saboda haka
hajiya tadau nauyin basu abinci har na sati biyu sannan

tai maganar yar aiki kuma duk
lokacinda mubarak zaije takan masa kashedin idan yaje
yaimata share share kuma yana kwatantawa to saidai
abinda hajiya takewa hidimar shi kamar baima kama
hanyar faruwar hakan tsakaninsuba danta koina kofofin
alama a damke suke.shiyana
takama da girmankai da tattalin shugabanci.
hakadai suka cigaba da zama.ALLAH cikin ikonsa kuma
saiya kwantarmata da ciwonta saudaya
mukamukinta ya tayarmata da ciwo,kuma data shafa
CONFO bai dauki lokaci ba ya saki.
lokacin data dauki kwana shadaya a washegarin ranar
waadin komawar ta asibiti game da ciwonta ya cika duk
da barunta tarasa hikimar dazata fadamasa fita saboda
taji aranta idan babu kofar dazasui nishadin jima'i to
batun zuwa asibiti zai iya bada kofar dazasu kara tsanar
junansu
ita bazata iya hakura da batun ba haka bazata iya tsaga
idonsa ta tambaye ba kawai saitakira hajiya suka gaisa
taimata jajen jiki
takuma sanya mata albarka.a ladabce ruma ta ce hajiya
gobene nake ganin likita ko inyaya yushau
yazo zaki tunamasa hajiya taji wani irin jiri na
dibarta.lallai daliline kuma mara dadi zaisa mace ta biyo
ta wata hanyar dan
sanar da mijinta wani batu,alhalin tare dashi take kwana
take tashi.bakin hajiya na rawa ta ce meyasa bazaki sanar
masa ba?
ruma tai dariya wanda hajiya taji kamar ta kunya ta ce
wallahi hajiya narasa da hikimar da zanfada masane ba
zan iya ba dan ALLAH kifadamasa.
hajiya ta cemata to harma yazo yatafi amma zan masa
waya waiko satinda wuce kinje ganin likita da gashin
fuskarki kuwa?
a sanyaye ta amsa a.a
to meyasa?
tafada adan fada ce.ruma tai shuru
kintambaye shine ya hana?
ta ce a.a bantambayeshi ba amma zandi ga tambayar sa.
hajiya tai shuru tana tunani tajima da sanin ruma akan
kawaicinta bata yinsa cikin abinda ya zama dole sai idan
anfi karfinta saitaimata nasiha akan cewa tafi kowa
kusanci da mijin ta.
ta ce zankiyaye hajiya kitaimin addua cikin tausayamata
hajiya ta ce ALLAH yaimiki albarka.
da yamma yushau yadawo gida kamar yadda ya saba ya
kulle dakinsa yadan huta yai wanka yana
shirin fita hidar abinci wajen ruma sai ga hajiya takira shi
a waya
kana lissafe da cewa gobe ruma zata ganin likita ko?
oh fuskarta ko?
da wannan tunanin na shi go gida yanzu mts!ina ganin

ma zamu sauya asibiti...kada ka cemin bakwa zuwa
gashin fuskar
ni akan sikilarta nake magana yaji wani bakin ciki da
takaici ya rufeshi.
.
Dan Aunty.
GORAN DUMA (P 29)
.
.
kai tsaye dakin ruma ya nufa yana kwankwansawa ta
bude a ladabce tai masa sannuda zuwa tanakokarin ta
fito,amma sai ya tureta kadan ya wuce falon nata, ta bisa
da kallo,har saida ya zauna.jiki a sanyaye..takara gaidashi
haka yake ta kallonta bako kyafta ido itakuma saita buge
da wasa da yatsun hannunta tsoro duk ya
cikamata zuciya saida yagaji da kallonta zuciyar sa kuma
tadan sassauta kunan laifin dayake ganin tamai.
kawo min abinci.asanyaye ta mike tare da mamaki
aranta.tamike harta wuce baidorar da abinda zuciyar sa
take rayawa game da ita ba ammadai abine yasani shine
sanyin jikinta, ya dauki hankalinsa yadade da sanin ruma
kasaitacciyace ta nunawa gaban sarki,.amma baita ba
kula da sanyin
jikinta ba,in ma matantakarta takeson nunawa tabbas
taci wasan dankuwa ta nunu.
Ya ce mata abinda kikemin na tabbata baki taba ganinsa
gurin alhji ko hajiya bako?
ta ce menaimaka?
ya ce tunda kikazo gidan nan na taba fita kin min .adawo
lfya?
ko indawo kimim sannu da zuwa?
abincima saina roka balle insaka ran zaki zubamin ko ki
zauna gabana inacin abinci ina kallanki.
tagama cika damamaki da wannan tsabar karfin hali
natake laifinkai.da abokin mayar da maganarta ne sai
itama ta tambaye shi KATABAGANIN ALHJI KO DADY YA
FITA BA TARE DA SANIN MATAR SABA?
IDAN YADAWO BATA KUSA SAI YA NEMO TA WATAKILA
SHIYASA TAKE ZAMA A GABANSA YA CI ABINCI,KO BA
.HAKA BA.
todake bazata iya fadi infada dashi ba saitaja bakinta ta
kulle ta ce to ni menake dashi daza a kallah.?
yajima yana kallanta tare da murmushi a fuskar
sa..meyasa kika
watsar da korafina na farko kika za bi amsa ta karshe
kikaimasa sharhi?
ba watsarwa naiba,abinda nadauka kawai shine rashin
sabo ne.murmushi kamar a mafarki ya tausasa murya ya
ce kuma bakyaso
musaba ko?
Nayimamaki ace waike dakanki bazaki iya min maganar
zuwa asibiti ba saikin sanarma hajiya,kuma kisan da wuya

,
na fahimcima ke gabadaya wannan fuskartaki bata
damunki.niko bakiji yadda nake tausayinki akanta ba, tai
shuru..danko maganar tausayin ce ruma bazata
daUKeta ba. yana tausayintane zata kwana go ma sha a
gidansa amma baita ba yimata ko sannu akan ciwan ba.
badan ransa yasoba washegari yakaita asibiti tagama
yadawo da ita ya tafi Sabgoginsa.
haka dai suka ciga ba da zama .duk dare adakinta ya ke
cin abinci.haka zaita takalo hira ita kam amsawar atakai
ce dukkansu sai suke wa kansu kallan girman kai
shiyanaganin dan bai isa bane tanashare shi.itakuma
tanaganinsa a mai daukar dala ba
gammo na kwanciya yasami soyayyar mace da mulkinsa
daya saba shikenan sai suka zarce a
cinaka in ci nawa ,
watansu guda ta fara shi ga matsalolinta na yau fari gobe
baki.amma baisan tanayiba saboda rashin kulawa.agida
idan tawayi gari da ciwo kamar yadda ka'ida yake,zata
garzaya asibiti amma agidan yushau babu wannan
dantawayi gari taga idanta yazama dorawa daya daga
cikin alamar tashin ciwanta kenan.haka tai shirin zuwa
asibiti da zumar zuwa tanajin motsinsa taje suka gaisa
tafadi matsalarta amma sai yaki daukar hakan da
mahimmanci.saiya ce ba wani abubane shawara ce
zantaho miki magani baiko saurareta ba yai gaba saida tai
kuka musamman ma data tunada auwal tun ma kafin
yasan ita sikila ce.
akwai lokacin dayazo ya taradda idanta yai hakan cikin
tsananin kulawa ya ce ya kyautu kije asibiti wannan
sauyawar idan naki ya wuce a ce shawara ce tadanyi
murmushi batare da ta tankaba.ya ce inbabu damuwa
muje inkaiki asibiti.tacemasa babu matsala gobe zanje
asibiti akwai magungunan danake sha.watakila kafin
goben makaga idon ya washe kaitsaye ya cemata mekika
sha ta ce ina zuba glucose a cikin ruwan
dazansha,inyawaita shan ruwa,da rake..ALLAH ya
sauwake.
dan bawan ALLAH washegarin dazai dawo sai gashi da
gwangwanin glocuse,biyar da yankakkun rake Auwal
ALLAH YAJIKANKA..
tare da kokarin yanke tunaninta.dan tana tuna asarar
data tafka na rashin auwal.
haka ta hakura ta zauna ta tilasta wa kanta shan ruwa
bako glucose din a ciki. dan wanda tazo dashidin yakare
da dare sai gashi da tulin magunguna shawara iri iri.dan
takaici tana karba tai kitchen ta watsa su friege tadawo
hannunta nadukan cinya taizaune tana karatun jaridar
aminiya. yana gamawawda abincinsa ya cemata
da anayiwa na miji kishiya da sai ince ko kukan ina da
kishiyoyi jaridun nan ko kunya bakyaji kullum
ni ina zaune ke kina karatun jaridun nan

Yushau ya ce ina magungunan naga kin aje ko ciwan be
dameki bane?
ransa yai mugun baci,itama ta hadiye duk wani bacin rai
ta ce masa irin wadannan magungunan da matsala a
jinina na gazawa wajen tace abinci shine dalilin taruwar
abinda kagani a idona.innasha illah zaimin.
ya cemata amma kinsan hakane kika barni na siyo?
batare data dubeshi ba ta amsa baka bani damar
naimaka bayani ba kana yanke hukunci kai
tafiyarka.hakane ammadai bayan natafi kya kirani ki
gayamin.taimurmushi kawai ya ce mata ruma kinki sakin
jikinki dani ko?bansan yadda kike kallan hukuncin ALLAH
a tsakaninmu ba.
a zuciyarta ta ce yakasa gane matakin datake dauka haka
ta kasa gane abinda yake nufi a yanzu.a farin sanin
dataimasa ba bu dadin baki ko agidansu a tsakaninsu
dalilin kirkirar su a yanzu kuma takasa gano danya
amfanetane.hawayen ta ne yai dalilin baro nasa
mazaunin zuwa inda take idan wani laifi nake miki sai ki
gayamin wata irin rudewa da kidima yau ya bayyana
atare
da ita yau ita ce a jikin wani namiji wanin ma yushau?
sai tarasa inda zata tsoma ranta,a kidime ta ce ba bu wani
laifi in ma akwai nayafe
yushau baidamu da kidimewarta ba saiya kamo
hannunta yana murzawa
Da yawan lokuta ciwanta na tashi.amma idan yushau
yakai kololuwar nuna kulawar sa kawai ya ce mata ruma
daurewa zakiyi dayawan mutane inzasu samii gado da
likita kwanciya zasui,nikaina nan bakiji yadda nake fama
da abu kaza ba.....
.
Ina yiwa en uwa barka da shan ruwa,
Allah Ya amsa ibadun mu da addu'oin mu na khairi baki
daya.
Allah Ya sa muna daga cikin bayin da aka enta su xuwa
Aljannah,
Aamiin.
Dan Aunty
GORAN DUMA (P 30)
.
.
nikaina nan bakiji yadda nake fama da abu kaza ba.....
hakan shine kadai furucinsa.
watansu biyu da aure hajiya takawo musu ziyara ganin
yadda ruma tai muguwar rama kuma takara kasalancewa
saboda gigitar ayyuka ba yan ta ko ma gida da yushau ya
zo taimasa magana kan
yanema wa ruma yar aiki, ransa yai mugun ba ci saiya
tattaro korafinsa yayo gida da niyyar karewa akan ruma
Tunda haushin ruma yakeji ko kallan dakinta baiyi
ba itakam aranar ta wuni zazzabi.ammadake tasan uzurin

ciwo agurin yushau ba uzuribane haka ta
daddage tai abinci jalof din taliya da lemon kwakwa ta ri
ga ta aje abincin adakinta dataji shuru saita
kaddara ya hadiyotane saboda haka ta kokarta ta kwashi
kayan abincin ta bishi dashi.
ya fito wanka ta gaidashi ya amsa fuska ba ya bo ba
fallasa suna zaune shuru har yayi rabin plate
sannan yadaga kai ya dubeta yanzu dan ALLAH ruma
mene ne abin wahala a irin wannan girkin sai 'yan wanke
kwanuka da aka ci.?
tai shuru tana kallansa kirjinta na bugawa ta ce masa
meyafaru?
cikin gatsali ya cemata kinfini sani.kuma niba wannan
yadameni ba.wai duk lokacindakike son wani abu saikin
hadani da hajiya?
kodake kinsan ba bu gaskiya a batun in samo miki 'yar
aiki ina kudan yake balle romonsa?
dan ALLAH ina aikin yake a gidan nan bare a nemo wata
mai hidima
mamaki da takaici ya ishe ruma amma dake jaruma ce
sam fuskarta bata nuna ba.kamar cikin jimami ta ce
dashi kaga kuma bani naimata maganarba.rannan
datazo ta tarar banida lafiya ina aikin gida a wahalce
watakila wannan ya sanyata hasashen
samo mai aikin amma bani nasa ta ba yaya yushau.
kunya taso takamashi amma dake sarkin ki fadine.sai ya
maza yai fuska. Ya ce mata babu wata mai aiki da za
asamo kodan saboda dalilai biyu,kisami damar mike
kafa,shawara takara samun gurin zama a jikinki,ko kuma
kici gaba da mike kafa kina abinda na tsana.wato karatun
jarida
ta hadiye ciwan maganar sa cikin sanyin murya tace to
naji abar maganar.
haka ta kwashe kwanukan taje ta kwanta gashi jikinta da
zazzabi,ga sanyin iskar fankar dake kadata gashi ba dama
taRAGE DAN Yushau mutum ne mai matukar jin zafi
shiyasa yake kallon nata gudun iskar a matsayin wata
tsirfa yana shan lemon kwakwa ya dubeta
meyasa baki yi lemun shinkafar nan ba yafi wannan
dadi.?
murmushin yake kawai tai aranta ta ce yushau komai kai
baka burgeshi ranar datai na shinkafar ma cewa yai
wannan menene
marabansa da kunun zaki.?
ya cemata akwai nama dana shi go dashi kiyima farfesu.
tai shuru tana tausayawa kanta yushau baisan yakamata
da kawaici ba. yaya yushau wallahi inafama da zazzabi,
kadan min uzuri zuwa gobe.
baiko dubeta ba ya wuce yana cewa aidaurewa zakiyi,
bari nakawo miki PANADOL karfi da yaji kin mayar da
kanki 'yar kwaya..yakawo mata tare da ruwa tasha tanufi
kitchen tafara aikin.dan yanzu ruma talura indai tana son

lallai sai yushau ya damu da lalurartane to ranta yadunga
baci kenan....
gab da sallar magarib ta kammala yushau yashigo kichen
din da shirin zuwa masallaci.
Har kingama ya shigo yafara dauraye kwanunka yana
kifewa..yana cewa laulayinki idan aka biyemasa sam baza
a morekiba..tai shuru bata tanka ba tana ta numfarfashi
har tagama wanke wanken dayaga shurunta yayi yawa
yasa yakai hannu wuyanta yaji zafin zazzabin cikin jimami
ya ce zazzabin yakaru ruma sannu.kawai saitaji kwalla na
zuwamata
amma haka ta daure tahana kwallar fitowa can sai gashi
ya shigo da maganin boska ya mikamata yana cewa maza
balla biyu kisha yanzu zakiji zazzabin ya sauka.ta amsa ta
aje gefe ta cemasa na cemaka banashan magani kaitsaye
batare da umarnin likita ba sai kilu tajawo min bau idan
nai ganganci.
ALLAH yasauwake ya ce sannan
ya koma kan abincinsa itakuma tashi ge dakinta yana cin
nama tunaninsa nakanta kullum mace babu lfya da
aurensa amma yana hada kafada da gwauro duk yadda
yake da bukata sai dai bukatun
subi ruwa sai lokacin barci ya shiga dakin ya tadda tai
barci yataba wuyanta yaji haryanzu da dumi ya dinga
shafa kanta har saida tafarka...
duk abinda zai saukar da zazzabin kin koreshi, kiyi wanka
da ruwan sanyi kinki,kisha boska kinki,yanzu dankinsha
sau daya sai wani abu
yafaru?
itakam takasa magana sai yarike mata hannu yana
matsamata zuwa kafada .tasan dukkan manufar sa
saboda haka takawad da kai cikin bata fuska.
haka yadafa ruwa ya tilasta mata wanka dashi.
data fito wanka zazzabin yadan sauka.hakan kuma ya
bama yushau damar ji da ita.iyakar yadda yaso
wanda ko mai cikakkiyar lfya ce zataji a jikinta.yahau
barcinsa ya barta da mayar da numfashi adaidai.
hakadai suka ci gaba da zama wanda yushau saiyana da
bukata yake lallabarta tare da tattalinta.har kullum ruma
kukanta bai wuce
naganin zata kare rayuwarta cikin Rashin 'yanci dasafe
ruma tatashi. da matsanancin ciwan baya hartakai saidai
yushau yaimusu karin kummalo amma ya bar na ruma a
kichen.
yasame ta adaki kidaure kitashi ga abincinki can akitchen
kidanci kisha magani ninatafi kasuwa
haka ruma tadaure duk wani bacin rai tace masa adawo
lfya. kogama ficewa gidan baiyi ba tarushe da kuka..tunda
ta auri yushau ko saudaya bata taba zuwa taronsu na
sikila ba kwatsam tawayi gari da zaton tana da ciki saboda
rashinganin aladarta.
.

Eh uwa barkan ku da sallah, da fatan ana shan shagali da
hidiman sallah lafiya,
Allah Ya amshi ibadun mu Ya maimaita mana,
Aamiin
sannan barka da sallah na, ban daukewa kowa ba ina jira
ehe..
Dan Aunty.
GORAN DUMA (P 31)
.
.
Ruma tai kuka hartagaji kamar ranta zaifita.dan ta
tabbatar a yadda yushau ke tafiyar da ita,lallai
rayuwarta na cikin hatsari domin mace in sikila ce a duk
lokacinda tasami ciki tun cikin na na wata biyu zata
kasance karkashin kulawar likita duk bayan sati biyu
har zuwa watannin sannan tako ma antenatal.
wajibine ba bu ita ba bu aikace-aikacen masu nauyi da
yawa kuma wajibine ta haihu gaban likita saboda
matsaloli barkatai musamman game da jini Duk
wad'annan dokokin suna nufin gata, ita kuwa ta san bata
dashi, Yusha'u ba mutum ne mai fahimta
ba duk yadda ake fahimtar da shi ba a sauya masa ra'ayi
da fassara.
Har cikin ya yi wata biyu tana cikin halin kuka da damuwa
ta kasa sanar da kowa, mafita a wajenta ita ce ta sanar da
Hajiya, amma idan ta tuna jan idon da Yusha'u ya ke idan
Hajiya ta yi masa wani Umarni bisa tunaninta a kanta, ya
kan zo ya yi ta zabga mata gori da goruba, to ina ga yanzu
ta sanar da ita.
Da ta rasa mafita kawai sai ta yiwa Innarta waya cikin
kuka ta sanar da ita tare da neman shawararta.
Hankalin Mahaifiyarta ya yi mugun tashi duk da dama a
tashen yake kasancewar duk 'karshen wata sai ta ziyarci
Rumaisa'u, kuma ganin da ta ke mata tana tabbatarwa
Rumasau ba ta cikin kwanciyar hankali da 'koshin lafiya.
Cike da 6acin rai Mummy ta ce.
"Ni dama na san sai auren Yushe'u ya cutar da mu,
Yusha'u mutum ne mai mugun girman kai, babu wanda
ya iya sai shi".
Rumasa'u ta kasa cewa komai sai shesshekar kuka, dan ta
san gaskiya Innarta ta fada.
Momi ta yi dogon tunani, sannan ta ce.
"Ki kwantar da hankalinki, zan same shi a waya".
Rumasa'u ta tsayar da shesshekar kukanta tare da fadin.
"A'a Momi ki ba ni shawarar yadda zan fahimtar da shi,
ba na son ya yi ta tuhumata da maganar ina kai
'kararsa...."
Ita ma Momin ta tare da fadin.
"Dole hakuri zaki yi ki bar ni na yi masa magana,
Yusha'u na da raina mutane ko ni din ma ba lallai in yi
nasarar ya ji maganata ba amma dai na san duk tsiya zan
fi ki, tunda zan iya bibiyarsa idan na nemi ba'asi idan ya

'ki abin da na ce".
Rumasa'u na cikin fargaba, amma dai dole haka ta yarda
da batun Momi suka yi sallama kowa rai babu dad'i.
Yusha'u na kasuwa wajen azahar Momi ta yi masa waya,
cikin zaton faruwar wani abu ya daga wayar dan sanin da
ya yi Momi ba ta kiransa a irin wannan lokacin.
Ta fi kiransa da daddare ko da safe lokutan da ta tabbatar
yana gida.
Ya gaishe ta cikin ladabi da ci-da-zuci, ita kuma ba ta ja
masa rai ba ta fadi abin da ke tafe da ita.
"Cikin Rumasa'u ya cika watannni biyu ko?
Ya wajaba lallai ku je asibiti ka san sickler mai ciki
preterm labor ce, watau kullum tamkar cikin na'kuda
take. Dole sai da kulawar likita zata raini cikin dan ceto
ranta da na abin da ke cikinta".
Ya ji maganar banbarakwai wai namiji da suna Hajara,
dan shi dai bai ma san Rumasa'u na da ciki ba, kuma bai
iya boyewa ba ya ce wa Momin.
"Ni walllahi ban ma san tana da ciki ba".
Ba tare da ba wa maganarsa muhimmanci ba Momi ta ce.
"Allah Sarki, ka san Rumasa'u da kunya, ni kaina ba dan
akwai wannan dalilin ba na tabbatar ba zata sanar da ni
ba. To don Allah ina rokon arziki kar ka yi wasa da
lafiyarrta ku je asibiti a shirya mata fayil, kuma abi
dokokin likita".
A sanyaye ya ce mata. "Babu komai, in Allah Ya so za a yi,
Allah Ya inganta, Ya sauke ta lafiya".
Momi ta amsa, "Amin". Sannan suka yi sallama.
Ya wuni da abubuwa biyu, tsabar murnar cikin Rumasa'u
saboda dokin samun magaji, da kuma
takaicin yadda Rumasa'u ke yawan hada shi da iyayensu.
Da ya dawo gida da yamma ya jima a dakinsa Rumaisa'u
ba ta shigo ba, saboda haka ya sameta a
dakinta, sai ya tarar da ita a bandaki tana kwara amai,
dole ya sassauta 6acin ransa ya yi tsaye a
bakin kofa yana mata sannu, har ta gama aman, ta gyara
wajen ta wanke baki sannan ta wuce firji ta
ciko tambulan da ruwa ta zuba glucose ta shanye sannan
ta dawo ta zauna yana bin ta da kallon da
ya sanya ta tsarguwa shi yasa ta kasa hada ido da shi, shi
kuma ya 'ki tanka mata.
Can ta mi'ke ta kawo masa lemo da fura sannan ta koro
masa bayani.
"Don Allah ka yi hakuri yaya Yusha'u, wallahi na sha
ciwon 'kafa dazu shi yasa ban sami sararin yin
abincin ba".
Ya jima cikkin shiru sannan ta tsinka bayan ya tsiyayi
leman ya sha. "Ya ya zan yi Rumasa'u, tururuwa ta yi
jidon banza ma ballantana ranar garar 'yarta".
Tana 'kila wa 'kalan fahimtar inda maganarsa ta dosa duk
da ko ta fahimta din ba ta da kalmar amsa
masa dan haka ta kyale kanta da damuwa da sai ta

fahimta. Sai da ya gama shan furar sannan ya dubeta da
kyau, ya ce.
"Yanzu tsakani da Allah Rumaisa'u kina dauke da cikina in
rasa arzikin ki sanar da ni?
Duk lamurana ba kya daukarsau da muhimmanci idan ba
wandanda ba ki 'kudurta kai ni 'kara wajen mahaifanmu
ba".
Ta yi shiru 'kirjinta sai bugawa yake saboda tsoro, bakinta
sai rawa yake ta kasa samo hanyar kare kai saboda haka
shi kuma ya sami sararin fitar da dukkan zargin da
zuciyarsa ta sa'ka masa.
"Tun kafin auren nan fargabar a ta dame ni ke nan, ni na
san zurfin iliminki ba zai barki daukata wata tsiya ba bare
ki kimanta ni, duk wani abu na ha'k'kina ko naki kina
ganin na yi tsororo ki cika min shi ko ki gabatar min.
Babu wani abin arziki da nake tsinta a wajenki sai na
'korafi da kaiwa iyayenmu magana... Takardar jarida ko
mujallarki ta fi ni kima da daraja..."
Yanzu kwallar da ta taru a idonta ta fara saukowa,
cikinta kuma ta dago ta dubi Yusha'u murya a raunane ta
tare shi.
"Wallahi Yaya Yusha'u ban ta6a kai 'korafinka ko 'kararka
ba, wannan kuma da na fadawa Momi ba 6ata ka nake
nufin yi ba, kawai dai na yi tunanin ita zata fi iya fahimtar
da kai matakin da za a iya dauka a kaina. Yadda aurenmu
ya zo bagatatan ne duk ya janyo wannan matsalar, tun
kafin mu yi aure ya kamata ka san yadda rainon cikina zai
kasance..."
Ya tare ta a zafafe. "Karki sauya min magana ko ki yi min
gori Rumasa'u, yadda aurenmu ya zo ni ban ta6a
daukarsa wani daban da yadda ya kamata aurena ya
kasance ba, Allah ne Ya za6a min ke ban kuma yi butulci
ba na kar6a, na ri'ke ki da iyakar adalcin da zan iya. Duk
wani abu daban sai dai in a wajenki ya ke, ba kuma a
baibi kike ba ni yadda na kabari ya fi ni daraja a wajenki
ba..."
Sai ta bude baki cikin tashin hankali tana dubansa,

2 Comments On GORAN DUMA
avatar
jannat

1 year ago

Reply

08062236094

avatar
jannat

1 year ago

Reply

08062236094

Please Login or Register in order to submit comment