Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bayan na cika
zuciyata dafatan zaku zamewa juna alkhairi kuma idan
ina da hakki akanka abinda na zabarmaka kenan amma
idan kaki sai inSaka maka ido
shikenan alhji ALLAH ya tabbatar mana da mafi alkhairi
badan ransa yaso ba..
awashegarin ranar ne kiran alhji ya risketa hankalinta
kwance dan a tunaninta zaimata nasi hane kamar yanda
yasa ba kila kuma ta bankwana.amma bayansun gaisa sai
yana ta tattalinta tare da kutsamata maganar yusha u
cikin
da bara irin tasa ta manya.
Abba ya ce mata rumaisau yushau ne yazo mana da wata
magana yanaso ya maye gurbin auwal.ayadda ya cemin
ya jima yanasanki ganin kinkarbi auwal yasa ya
hakura.nima kuma dama inada muradin hakan kimanta
da wata ibtila i dakika sami kanki aciki.
rumaisau kizama mai godiya ga ubangiji.ki amince ayi
auran nan kamar yadda aka sanya da mari
gayi.idan rumaisau karkaf abushe take kallon alhji to
mizataima kuka ko tashin hankali.duk wata damuwa ko
abinsanya kuka dazata ci karo dashi a duniyarta mutuwar
auwal ya isa akira shi matakin kar she.idan kuwa wannan
bakincikin
baikasheta ba yakamata kowani tashin hankali ya zamar
mata gada
ta ce masa alhji badan ka bayar da goyo n bayanka a
maganar nan ba alhji dana nemi hanzari.ya ce ina
jinki ruma ta ce masa alhji da baka goyi bayansa ba
harshensa ne yaimazuciyar sa karya takowani bangare
nasan yaya yushau baida tsarin auran irina.baikamata
mutum lafiyayye kamar sa yakare a auran nakasasshiya
irina ba nanda ruma ta bi duk wata hanya tagama aibanta
abinda aka
gani ake son hada auranta da yushau..
alhji ya ce mata duk wata lalurarki ta sikila idan har bata
hanaki auran auwal to bazata hanaki auran yushau
ba.yadade yanai mata nuni
da abubuwa dasuka sanya yakesan ayi auranta da yushau
yanzu kam Ruma tana tunanin KARA,KAWAICI,
SADAUKARWA, yakamatne tsakaninta d.a alhji da hajiya
wadanda suke karramata daidai da mahaifanta..ko

sudasu zata iya dogara ta dubi yushau matsayin mijin
aure
Shirye shiryen biki ya kankama innar ruma ta iso ana
sauran kwana biyu amma kafinhakan tunda alhji
yajizatazo ya tura su yushau rogo saboda bayaso umman
ruma ta fahimcin rashin jituwar dake tsakaninsuhaka
yushau yayarda sukatafi badan yaso ba ahanyarsu ta
tafiya rogo bawanda yaimagana acikinsu.saidai ruma ta
karbi sakonninda take ta suka sata hawaye idan ta shiga
motar auwal sai ya zuge glassai tsab ya rufe, yakuma
kashe A.C sannan a motar sa baya rabo da CAR HEATER
saboda ita,ga tuki cikin
natsuwa,ko da a hanyar da bata da kyau ne saboda kar
tajigata,bugu da kari yakan umarcetatada fito da
hijab a jakarta tasa idan da mayafi ta shiga motar....
.
Dan Aunty.
GORAN DUMA (P 24)
.
.
duk wadannan gatancin sun kufcemata ko kallo bata ishi
yushau ba bare ayi maganar tattali
danhaka taiyi ma kanta gatadakanta ta rufe gilasan.shiko
sai zuba gudu yake a hanya ya cika mata kune da wakar
ala wanda idan ta rantse saurare kawai yake amma baya
duba maanar wakar.
sunkusa karaye aka bugo mata waya wannam karan ya
rage karar wakar ta daga wayar ta sada zumuncine da
gaisuwa daga TAHIR wani member ne a kungiyar su ta
masu sickle cell. yaimata gaisuwar auwal tare da
jajantawa yushau ya ce mata wanene kukai waya da shi?
tajima kafin ta ce sunansa TAHIR TAFIDA MUHAMMAD
tana rufe baki ya watso mata wata tambayar yakuke
dashi?
memberne a kungiyarmu ta sickle
cell acan muka san juna muke zumunci.
ammadai kina da kudurin idan munyi aure zaki bar
kungiyar?
dayake na kwana sanin aurena ba zai rabani da sikila
ba,sai ban ta ba tunanin zan bar kungiyar ba.
amma nasan kin san duk lalacewa
kinsan cewa mijinki yana da ikon hanaki duk wata
muamala da yake da shakkunta ko?
duk yadda kike jin wayewa nasan kinsan mijinki yana da
karfi akanki.
ruma tajima kwarai maganganunsa nayi mata ihu
aka.saidai tayi jarumtaR boye kaico da hawaye,saboda
haka ta shirya magana ma sai ta kori rauni a zuciyarta
wata sha afa da mukai kenan nida kai da iyayen mu a
kaida duk wanda zai auri mai sickle cel ya kamata a zauna
a tattauna dashi bayan gwaji yaji matsalolinsu yaga abin
juriya akai in zai jure din,

yushau ya ce dan na ce ki bar kungiya idan kinyi aure?
ko ruhin ciwon naki makale yake da kungiyar da idan an
hanaki ya tsinke Ranki
duk dai taji zafin maganar amma a sanyaye ta girgiza kai
shikuma ya sami damar dorawa cikin zafin rai
kiyi kokari ki fahimceni karki dinga sauya min magana
kina hada min ita da ciwo.yanzu dai naji kina waya da
wani wanda ba muharraminki bane...
a raunane ta amsa da cewa ban dauki fadan hakan laifi
bane sannan ban shirya karya ta shi ga tsakanina dakai ba
Idan hakane sai ki yanke hulda da abinda kikasan
banaso,dankar kifada min gaskiya inki fahimtarki kiji
ciwo.inkuma karyar kike yimin ALLAH ne shaidata,kamar
yanzu dakika cemin dan kungiyarkune ai bansan
gaibuba,in bayan dangatakarku ta kungiyancin akwai
wata dangatakar yaya zansani kaitsaye ta amsa tana
duban titi.
kobaka sanidinba rashin sanin ba zai cutar dakai ba,ko da
cutarwar ta fargaba ce tunda kasan ciwon
sikila ba kanjamau bane da ake bukatar mai shi ya auri
dan uwansa mai shi shi sikila so ake ya nemo lafiyayye ya
aura dan
dorewar haihuwar yayansu masu lafiya.saboda haka
karkadamu kanka da dangantakata da wani
sickler ko kuma ka saka mana zargin dangantakar
soyayya
afusa ce ya juyo ya dubeta idan na fahimceki umarni kike
minko?kawai saitasami kanta da tuntsi
rewa da dariya tana kare masa kallo kaitsaye ta ce.
"Haba dai, yaushe zan maka umarni?
Na ga dai kamar bai kamata mu dore a gizago da
biyayyar babu ji babu gani ba. Ya wajaba mu tattauna
matsalar ciwona da kai a yanzu kafin nan gaba ka ce an
baka a rufe".
Karkacewar da bakinta ya yi wajen dariyar da take, yasa
tausayinta ya danne takaicin dariya da ma'anar maganar
da ta yi masa. Ya kawar da kai ya bi titi da kallo, sannan
murya 'kasa-'asa ya ce. "Tunda ba fasa auren za a yi ba
idan na ji abin da bai yi min ba cikin abin da za mu
tattauna din ai barin tattaunawar ya fi..."
Ta tari numfashinsa da fadin.
"Me yasa za a kasa fasawa in kuma ka ga ba ka muradi?
Duk sickler ya san a saka aurensa a fasa ba wani ba'kon
abu ba ne, saboda haka babu abin da zai fari dan ka fasa".
Ya jima kwarai yana sa'ka maganar da zata fito bakinsa
kafin ya barta ta fito.
"Da zaki ajiye bokonki waje guda, in sami
kawwamammen matsayi a wajenki irin wanda
nagartattun iyayenmu mata ke ba wa mzajensu, to ina jin
zan zama mai hakuri da tuntuninki ga Auwal.
Dan haka ba kya bukatar 6ata lokacinki wajen yi min
umarnin in aure ki ko in fasa tare da sanin

fasawar tawa ba zata rage ki ba, ko ta amfane ki, tunda
wani za ki aure ba Auwalu ba".
Ta yi shiru kawai tana juyawa maganganunsa, kaasa
fahimtarsu sosai ya sa martaninta ya bi ruwa.
Shi da ya damu da jin ta bakinta sai ya tuna mata yana
mai kallonta.
"Ba zaki ce komai ba?"
A sanyaye ta amsa masa. "Ga6o6in maganganun naka ne
da yawa, yadda kowace na karya za tashi guda in kuma
jata ta yi tsawo, saboda haka kar ka zaci muhimmin abin
da kake son jin bakina a kansa."
Kai tsaye ya amsa mata.
"Kar ki dauki kanki wata tsiyar saboda kin yi zurfin karatu,
ki zauna da ni zaman bauta kwatankwacin yadda kika ga
iyayenmu na yi. In kika yi hakan
shine kika ba ni karramammen matsayi wanda zai wanke
min dukkan tsatsa a raina na auren mai
zurfin ilimi da ban ta6a shiryawa rayuwata ba".
Ta dinga jan numfashi kafin ta amsa masa cikin dakewa.
"Ina jin da taka karramawar zaka sai wancan matsayin da
kake ambatawa, in kuma ka cire zacezace da zarge-zarge ka kuma cire garaje cikin mallakar
matsayin da 'karanta rainuw da kuma
sau'kaka fahimta, wannan shi ne".
Ya yi dif kamar ruwa ya cinye shi da harshensa ya yi
niyyar fada mata abin da zuciyarsa ta fahimta a
maganarsa. To abin da zai gaya mata shi ne bokon da
yake gudu ta yi masa.
Bashi da za6i, dole ya yi shiru ya kyale ta, ai a kan
sharafinta take tunda tana da Alhaji me tsaya mata. Har
suka shiga cikin garin Rogo babu wanda ya tanka wani,
suka sauka a gidan kakaninnsu, duk
da tuni kakannin sun 'kar, sai 'ya'ya da jikoki. Haka kowa
ya dinga sanya musu albarka, Yusha'u na
shan albarkar yarda da ya yi ya auri Rumaisa'u da
nakasarta, Rumasa'u na shan albarkar ajiye jimamin
rasuwar Auwal da ta yi a gefe ta yarda ta kar6i dan
uwanta.
Sun wuni a nan gidan, sai dab da la'asar suka nufi gidan
Goggo. A gidanta Yusha'u ya yi mafi rinjayen
zamansa saboda sha'kuwarsa da 'kaunar da 'yan uwa da
Allah Ya zuba mata. 'ya'yan wa da 'kani da mahaifinsu.
Son danginta neyasa duk sa'adda ta kwashi Auwal suka je
Rogo, to a gidan Goggo zata sauke shi, su yi
hira su yi barkanci tare da Goggo.
Wannan dalilin yasa suna shiga gidan yanzu gaba daya
jikinta ya yi la'asar, musamman da Goggo ta baza musu
tabarma wajen da ta saba shimfida musu in ta zo da
Auwal, sai ta kasa zaman kan
tabarma ta koma kan 'karamar kujera ta zauna tana
kokarin hadiye kwallarta.
A haka suka gaisa duk tana rikice, a karshe dauriyarta ta

kai 'karshe lokacin da wasu rukunin zabbi suka gifta, ta
tuno lokacin da suka zo da
Auwal an kyankyaso jariran zabbi fiye da ashirin reras
abin sha'awa, ya daga kai ya dubeta ya ce.
"Don Allah zabbin nan ba su burge ki ba Rumaisa'u?"
Ta bi zabbin da kallo tana murmushi, sannan ta ce......
.
Dan Aunty.
GORAN DUMA (P 25)
.
.
"Ba na jin sun burge nikamar yadda suka burgke ka,
tun dazu fa na ankara kana ta faman satar kallonsu..." Ya
tare ta cikin dariya yana kallon Gaggo.
"Satar kallo kuma?
In zan kalli zabbi sai na saci kallonsu kamar ke zan kalla a
gaban Goggo?"
Shi ma Goggon ta tare shi da fadin.
"Dan ma ita din ba satar kallon nata kake a gaban nawa
ba, 'karfi da yaji kun mayar da ni kakarku". Suka tuntsire
da dariya su duka.
Auwal ya ce. "Kar ki sami damuwa Goggo, ko barewa a
daji da danta ta ke wasa. Ina son zabbin ya ya zaki yi da
ni?"
Goggo ta yi murmushi ta ce masa.
"Ka zo garin nan ka siya a yi maka kiwo. Ya kuma bin
zabbin da kallo, sannan ya juyo ya dubi Rumaisa'u.
"Har yanzu ba su fara burge ki ba Rumasa'u?
Anya kuwa zabbin nan ni ma sun burge ni?
Duk abin da ya burge ni fa ya kamata ya burge ki".
Ta bi zabbin da kallo suka zuba musu ido tare, sai can ta
juyo ta dube shi cikin murmushi ta ce.
"Wallahi sun fara burge ni".
Da tausasshiyar murya ya ce mata.
"Haba ko mu fa".
Sai suka bar Goggo da sallalami suna yi mata dariya.
Yanzu da Rumaisa'u ta 'kurawa Zabbin ido cikin kwalla
nan take ita ma Goggo ta tuno tunowar da ita ma ta
tilasta mata kwallar, sai suka bar Yusha'u galala yana
kallonsu da kwanon ruwa a hannu.
A karshe kukan zucin Rumaisa'u ya ki 6oyuwa sai da ya ta
fashe da kukan bayan ta sunkuya kamar zata shid'e.
Da sauri Goggo ta 'karaso wajenta ita ma nata kukan ya
'ki 6oyuwa ta ru'kota duk suka rafke da kuka cikin kuka
Goggo ta ke cewa.
"Manta Auwalu a zuci wani abu ne da ba zai ta6a yiwuwa
ba, dan cikin rayuwarsa ya guji abin tir,
babu yadda zamu yi haka zamu ci gaba da daurewa
muna yi masa gatan da ya fi bu'kata yanzu, wato addu'a".
Ga mamakin Yusha'u sai ya ji wani matsanancin kishi ya
turnu'ke masa 'kirji, ya sababba masa fusatar da ya ajiye
ruwa ya tashi a fusace ya fice daga gidan. Hakan ya basu

dama cin karensu babu babbaka,
suka ci kukansu, Rumaisa'u na maimaita.
"Kin ga yadda Allah Ya yi da ni ko Goggo, na rantse da
mafarki ne abin da ke faruwa da ni idan na farka bacci ba
zan 'kara bacci har abada".
Sun jima cikin wannan damuwar, da koke-koken har sai
da mutam gidan suka fara zagayowa kewayen Goggo dan
gaishe da ba'ki, Goggo ta ari juriya ta hau yiwa Rumaisa'u
ga yiwa Auwal addu'a da sadaka su ne gatan da zai iya
samu daga gare ki a halin yanzu."
Rumaisa'u ta yi namijin 'kokarin gyada kai da sauri cikin
gintse kuka lokaci daya zuciyarta na halarto da aikatawa
Auwal dukkan Wani gata da kwanjinta zai iya in dai zai
taimaka wajen sada shi da rahamar Ubangiji amma ta ji a
ranta mantawa da Auwal ne har abada ba zata iya ba.
Ta tuna da auwal dake firar dasuke ya ta hallakane akan
matsalar ruwa inda tatuna wani zuwansu
rogo yake cemata abu nafarko dazansaka agaba bayan
hidimar bikin mu ita ce
insamu yan kudi inzo garinnan in gina rijiya ko bayan
raina sai ladar ya amfaneni farad daya tafara tunanin
hanyar dazata bi ta
cikamasa burinsa duk zuwan dazasui da auwal indai
akwai lokaci sai sunje kan dutse.saboda haka ta shirya
tama gwoggo sallamar fita zuwa kan dutse duk da tasan
zuwannata sai gadar mata da kunan zuciya ahaka
takasance har rana tagama yinja tafara sauka a hankali
tayi kuka hartakasa gajiya duk wanda yaganta a wannan
halin sai ya
tausayamata.bata hango yushau na zuwa ba motsinsa
kawai taji tajuyo taga fuskar sa ba annuri
wai anan zaki kwanane?
aranta ta ce abune mai matukar wuya ta taRe da giRman
ciwo a ce tarasa mai tattali da fara a kamar gonar auduga
ace ta bige da auran mai kyaliya da gizago kamar zaki. ta
tashe ta bi bayansa tana mai share hawayenta..har suka
iso kano tara saura babu wanda ya tanka acikinsu Suna
faka mota tafara kicikicin bude motar amma a
kulle danhaka saitai shuru dan bazata iya dubansa ba
balle ta nemi dalilin yin hakan.yajima yana huci san nan
ya sauke cikin gyaran murya Sannan ya ce bawai gudun
laifinake ba illa gudun daukaR bakuna,in ma laifine
yakamata a tuhumeni da wanda nake da ruwa da
tsakinsa,ba lallai agida su
san haka ba,kiyi kokarin gyara wannan hawayen wofin
dakike zubdawa dan karki janyo a dora min alhakinsa
bata tankamasa ba tagoge hawayenta tsab ta rabka
tagumi.ki kwance jaka ki shafa hoda ta cemasa dazan fito
ma ban shafa hoda ba ta muskuta cikin tsananin kuncin
zuciya ta cemasa shafa hoda tana nufin farinciki ko jin
zakin rayuwa,nikuwa duk nayi bankwana dasu.a fusa ce
ya fice daga motar yana cewa au na shafa cewa a cikin

takaba kike wanda baikamata na manta hakanba
itama ta fito ta wuce dan tuna cewa yaufa mominta
zatazo
tana isa ta ga innarta ga kuma
balaraba yayarta harda kari ma wato da innar auwal.
Maimakon ruma taiwajen innarta saita nufi innar auwal
tafada cinyarta tafara rera wani irin kuka mai tsuma
zuciya.inna data gama wani kukan sai ga zuwan
ruma.inna nanata kukan ruma na nata
kukan mai keta zuciya ke akaima rasuwa ruma kekikai
rashin auwal.Allah ya baki hakuri da dangana Allah
yajikansa kekuma ya baki wanda ya fishi.wadan nan
kalaman nata ne suka kara kular da yushau.da ya shigo
yanzu,yakada kai yai waje baitsaya.ba balle
ya gaida bakin a can falon alhji wani takai cin
yatararmmahaifin auwaldin yatarar tare da alhji suna
hira.hirar kuma ta auwal da ruma game da yan
matsalalolinda suka taso gab da auren.akar she
hirar ya rufe da cewa dake shi ALLAH babu ruwansa sai
ya saukar da ayar sa gareni.ya karbi auwal mai lfyar
alhalin shikadai na haifa.yayanke min hanzarin 'ya'yan
dana tara burika akansu.nake kuma tafaman hura hanci
akansu.alhali bani da sani akan Samuwar su ko rashin
samuwar su.
hakadai har yushau yadaure yagaida su tare da
alhji.danhaka alhji yanuna yushau ga mahaifin auwal tare
da cewa ga wanda ze maye gurbin auwal.
ya ce masha ALLAH karike ta da kyau yarinyar tsakani da
ALLAH yaimasa nasiha kwarai....
.
Daga uhum sai uhum baki na dai har yau a kulle yake..
Dan AuntyGORAN DUMA (P 26)
.
.
RUMAISAU DA MOMINTA CIKIN DARE.
har sha biyun dare ruma,hafsat tare da balaraba da
momin ruma da barci ya ciyo idan hafsat,kuma taga
alamun nuna tausayinta ga ruma kuma kamar tanasan
kebewa da yartata.saboda haka taimusu
sallama ko minti biyar bataida fita ba momi tadubi
Ruma da kyau ta ce.inafata ba matsa ma kanki da
zuciyarki kikai ba kika aminta da auran yushau.?
ruma tajinjina kai tare da murmushin yake ta ce
bazan iya zabar mijiba momi dantagama zancenta yaya
yushau zai shi go rayuwartane dan rashin
zabina bai zama karewar numfashina ba baikuma
kankare aure daga cikin ayyukan da aka rubuto a
allon abinda zanyi a duniya ba,rashin auwal ne
matsala a rayuwata ba auran waninsaba.momi ta ce
to ALLAH yajikansa yasa aljanna ce makomar sa.kekuma
ki rage yawan damuwa kinsan yanayin
ciwonki.balarab kawai kallonsu take yi saboda

tsabar tausayi takasa cewa komai.ruma ta shaRe
hawayenta ta ce ina tilastawa kaina musamman
danganin bakincikin rashin auwal ya isa ya karar
da nawa numfashin.amma gani a raye ALLAH Ne kadai
yasan abinda yake boye yaSa ya barni araye
bataRe da auwal ba saidai ina neman wata alfarma
wadda nake ganin zata taimaka min narage tuna
auwal
cikin kunan zuciya,illah in na tuno shi nai farinciki
umma da balara ba cikin doki tare da hada baki wa ce
alfarma?momi kiyimim alfarma na sayar
dawasu hannun jarinda kika saimin da kudin
motar da alhji ya hanaki siyamin.kikuma banidama
na sayar da sarkokina
ahadamine kudin da dangin auwal suka barmin ko
a siyar dawasu da wasu daga cikin kayan lefan... Cikin
kaguwa momi ta ce aime da kudin?
Ruma ta shaida musu yadda sukai da auwal
dakuma bukatar cikamasa burinsa.asanyaye
balaraba ta ce amma dai zaki iya dorewa dayimasa
addua samun rahamar ubangiji ruma ba saikin
salwantar da dukiya mai yawa ba..momi tai saurin
dakatar da ita ta ce
a a balaraba ba salwantar wa ba ce,ya kamata
tunanindatai auwal yafi karfin komai agurinta,ba
komaikarki samu damuwa za ayi zanfadawa
dadynki idan kudin basu cika bama zancikamiki.
cike da farinciki ruma t.ai godiya momi taji farinciki ya
cikata dan tada de bataga farincikin ruma kamar
na yanzu ba tun kafin rasuwar auwal
sunata hira har suka fado kan yush.u
anan ne ruma tafadi wata alfarma momin su alhji
sundauki yaya yushau dan gida a ciwona suna
ganin kamar babu wani bukatar a tattauna matsalar
ciwona dashi dan haka ba a tattauna
dinba.bana son a share wannan batun
kirjin momi yaf.ara lugude dan haka tai zuru tana
kallon ruma ta tabbatarw kanta akwai
dalilindayasa ruma wannan maganar
kasancewarta mace mai zurfinciki da karanta korafi.ta ce
fadamin gaskiya saboda ALLAH mekika
hanga kikawo wannan maganar?
A sanyaye ruma ta shaida ma ummanta yadda
sukai da yushau bayanta amsa wayar tahir tafida
muhammad takare da cewa
bazan iya dorar da yadda yaya yushau ke karbar
alamurana ba,amma ko ma menene baya karbar
.alamura da sassauka fahimta
yazuwa yanzu momi ta rafka tagumi sannan
damuwa tattare da fuskarta
momi ta ce kunya da nauyin alhjh. nake ji ruma da
badan haka ba bazan bawa yushau aurenki ba cike da

tawakkali ta dubeta
badam nadaga miki hankali kodan in sanyawa
ranki rashin natsuwa cikin aurena da yaya yushau
ba.nandai suka ci gaba da tattaunawa daga karshe
ruma ta ce ki kyau tata zato a aurena da yaya
yushau,.. washegarin ranar alhamis kenan ya shigo gaida
umman ruma..nan ya taddasu harda ummansa
haryatashi zaifita umman ruma.ta ce masa idan
babu damuwa kadawo kamar karfe sha biyu don
ALLAH inason kakaini yankaba wajen aunty fati
. Yusha'u ya hadiyi wani irin yawu wanda ya taimaka
masa hadiye 'kuntata masa ran da yake jin an yi, ya
dubi agogo ya ce.
"Babu damuwa Momi, zan yi 'kokari in dawo din
duk da akwai tarin ayyuka a gabana kasancewar
jiya ban sami sararin zuwa kasuwar ba, amma dai komai
runtsi zan yi 'kokarin dawowa zuwa
azahar... Ko kuma na yiwa direban Alhaji maganar
ya zo ya kai ki...?"
Ta yi saurin tare shi da girgiza kai.
"Kai nake so ka kai ni..."
Hajiya ma ta yo kansa ta fada. "To wai umar me kake a
kasuwar me shegen nauyi
haka?"
Nan da nan ya karya murya ya ce.
"Babu matsala zan dawo, ku shirya zuwa sha
biyun".
Hajiya ta juya kai, Momi kuma ta yi saurin cewa. "To Allah
Ya dawo da kai lafiya na gode".
Ya amsa, "Amin." Sannan ya fice ransa na yi masa
wani irin 'kuna, takurar da yake fuskanta daga
mahaifansa akan wannan auren bai san dalilinta
ba. Sai ka ce shi ya dau ran Auwal?
Dole kafin sha biyun ta cika ma ya dawo gidan ya dauki
Momi, kasancewarsa mutum mai saurin
fahimtar abin da mutane ke yi, ko shirin yi yasa shi
zargin akwai abin da Momi ke nufi da ya kai ta
'Yankaba tunda ya ga ita kadai ta fito. Saboda haka
da suka dauki hanya bai dauki furucinta a ba-zato
ba lokacin da Suna tafiya daga cikin harabar gidan t. a
cemasa
yushau waikuwa kunje sickle cell counselling
centre kaida ruma?
yushau mutum ne da bai iya karya ba danhaka
kaitsaye ya ce a.a bamuje ba,jiyannan dai ruma
taimin magana.nikuma inagai idandai zuwa neman
shawaran bazai sauya komai na yuwuwar auren
mu ko rashin yuwuwar hakanba.inaganin babu
bukatar batawakai lokaci momi ta ce masa neman
shawara zai iya rushe aurenku.amma idan
kunso..yushau yakurawa titi fuskar sa ba ya bo ba
fallassa ya ce OK. hakan yasa takauda kai ta ci gaba da

bayanani
tundaga
matakin farko har iya idan take ganin zai fahimci
komai.tadade tana masa bayani daga kar she
tadaka ko zaice wani abu kafin ta dora da....
Gwajin ba ya daukar wani dogon lokaci, za a dauki jininka
ne a sirijni sai shigar cikin na'ura ta
musamman domin wannan aikin. Gwajin zazzabin
maleriya ma ya fi gwajin sikila jimawa.
Sannan komawa asibitin ko sickle cell couseling
center ga me shirin auren sickler a karo na biyu, shi
ma wani gingimen muhimmi ne cikin dukkan matsayin
da gwaji ya nuna mutum, AS ne ko AA, in
AS ne zai je neman shawara tudu biyu ne, wato
matarsa da kuma 'ya'yansa ko 'ya'yanta da zata
haifa ko zai haifa.
Cikin shawarwarin likitoci nunawa abokin zama
yadda ciwon sickle cell yake kamar yadda na fara yi maka
bayani a baya alamomin tashin ciwon,
kulawar da ya kamara ciwon ya samu a gida idan
ya tashi da kuma abubuwan da ya kamata a kiyaye
dan kar ciwon ya tashi, da kuma abin da za a yi a
gida in ciwon ya suman a garzaya asibiti, juriyar
zuwa asibiti duk wata, sannan da tanadin kudi saboda
ciwonsu, ko mutum AA ne ya kamata ya
kwana da wannan Sani.....
.
Dan Aunty.
GORAN DUMA (P 27)
.
.
.
In kuwa AS ne zai 'kara da tanadin kudi dan hidimar
ciwon sauran sickler duk da zai haifa,
tunda ciwon sickler ba ciwo ne da ake warkewa ba, yadda
Ubangiji ya halicci mutum ke nan haka Ya so da ganinsa
ba dan yana 'kinsa ba, illa iyaka dai ya kamata mace ko
miji su sani ba mutum daya ke gadar da sickle cell ba,
ma'ana ba dan mace sickler ba ce kawai ta ke haihuwar
sickler ko ba dan miji sickler ba ne aka haifar masa
sickler ba, a'a duk su biyun mata da miji ke karo-karo su
haifi sickler..."
Momi ta dan dakata ko Yusha'u zai ce wani abu kafin ta
dora da zayyana masa yadda sicklers ke jin
ciwo a jikinsu da kuma matakan da ake bi wajen
taimakon gaggawa, ciwon ya sauka amma sai jikinta ya yi
sanyi, domin ko kadan fuskar Yusha'u ba ta sauya da
tausayi ko mamaki ba, kusan ma kamar a gundure ya ce.
"Allah Ya sawa'ke, kuma maganar gwaji ma ai ta wuce
kamar yadda na fada, in dai zuwa gwajin ba
zai tankwa6e Alhaji hana shi daura auren ba... Ni ban ma
dauki ciwon Rumaisa'u wata martsala a cikin aurena da

ita ba..."
Momi ta jima tana kallon tagar mota cike da matukar
takaici, sannan ta daure ta ce.
"Yusha'u ba ka son auren nan, Alhaji ya matsa maka ko?"
Ya yi girgiza kai cikin murmushin ya'ke ya ce. "Ni ba
matsa min ya yi ba wallahi, bamban muka sha da ku
kawai, abin da kuke kallon shi ne
matsala ni a gurina ba shi ne matsalar ba".
Har yanzu Momi sha'ke ta ke da takaici, sai dai wayewarta
ta hadidiye takaicin, ta nisa ttace.
"Yusha'u me yasa ba ka yi tunanin mun fi ka gaskiya ba
tunda mun rinjaye ka".
Ya jima cikin shiru kafin ya tanka.
"Momi ai duk ba wasu abubuwa ne masu zafi da za yi ta
tashin hankalu a kansu ba...."
Fuskar Momi cike da damuwa ta girgiza kai ta tareshi.
"Don Allah Yusha'u me yasa ba ka bijirewa auren
Rumasa'u ba tunda akwai matsala a cikinsa abin da ba ka
fahimta ba shi ne, kai ba ka kallon ciwon Rumasa'u
matsala, ni kuma a duniyar nan ba ni da matsalar da ta fi
shi girma, ko tattalin ciwon
Rumasa'u nake, to na tabbatar ina yi masa tattalin da
yake wa rayuwarta amfani dan ina kokarin kore dukkan
abin da zai motsa mata ciwo saboda ina jin ciwon cikin
matsalolin da ke daga hankalina. To kai ba ka dauki ciwon
matsala ba ta ya ya zaka iya kare
shi?
Abin da kake dauka shine matsala wata'kila ni da
Rumasa'u mu 'ki kula da shi, dole ne wadannan
bambance-bamncen fahimtar su gadar mana da
matsaloli a gaba akan wannan Yusha'u na so ace
ka 'ki auren nan... Ina da juriya akan komai amma Allah
Ya sani ba ni da ita akan Rumaisa'u, ina fada
maka gaskiya ne dan ba zan iya fitowa in hana ka aurenta
ta dalilin bambancin al'kibla ba".
Nan da nan Yusha'u ya gane kato6arar da ya yi, wadda ya
ke tsoron zuwanta kunnen Alhaji, dan
haka ya yi sauri ya gyara muryarsa da ladabinsa.
"Haba Momi ba ki fahimce ni ba ne, ko Rumasa'u ba ta
aure ni ba, ai ni mai zage kwanji in kare mata
abin cuta ne, balle ni in zame mata cutar, don Allah ki
kwantar da hankalinki ki bi mu da addu'a... Ni fa
babu wanda ya matsa min aurenta".
Momi ta yi shiru kawai da alama zuciyarta ta fara sanyi,
sai can jimawa ta ce.
"To maganar zuwa asibiti?"
Tana direwa ya amsa cikin kwantar da kai da murmushi.
"A kyale maganar gwajin kawai, ko ya ya zata haifar min
'ya'ya ina son su haka zan kuma tanade su".
Momi ta dan juyar da fuska ta ce.
"Ko 'ya'ya zaku haifa dai ai na fada maka mutum daya ba
ya haihuwar sickler".

Cikin irin karya wuyan nan na to da hausawa suka ce ba
ta karya wuya ya ce.
"Ko 'ya'ya zamu haifa Momi, ku yi mana addu'ar Allah Ya
ba mu ikon kula da su".
Yanzu ta fara saukowa sosai, ta ce masa. "Amin. Amma
tilas ne ka je ga mashawartan sickler dan jin irin
dawairniyar dake gabanka da kuma
abin da zaka yi hakuri a kai. Adddu'a ma ibada ce, amma
akwai ayyuka tu'kuru kamar yadda aka

2 Comments On GORAN DUMA
avatar
jannat

1 year ago

Reply

08062236094

avatar
jannat

1 year ago

Reply

08062236094

Please Login or Register in order to submit comment