Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take zagayawa a cikin ta,
duk kuma da girman nan nata sai ta zama bata isa abin
iya kallo ba cikin abin da Ubangiji ya halitta amma sai ya
kebance ita kankanuwar duniyar d niimomi masu tarin
yawa, Ya karrama dan Adam a cikin ta sannan Ya bashi
zabin makomarsa a hannun sa, a cikin ta aljanna ko wuta,
wanda yabi Allah cikin ta yayi kunci a gare shi to
muminancinsa ya bayya na, wanna ya ki yarda da
AllantakarSa ko ya zama pandararren bawa to tayi masa
yalwa rabonsa kenan.

A yanzu hawaye ne ke diga a puskarta ba kuma wannan
karatun kadai ya sanyata hawaye ba har da tuna yadda
duniyar nan ta shude mata da mutun muhimmi a cikin
ta, kamar yadda ta tabbatar ita ma wata raba zata shude.
Rauninta kuma ke raya mata ba zata taba samun wanda
zai maye mata gurbinsa ba, wannan tunanin ne ya pado
mata da na sakon mahaukacin masoyi, a rikice ta zauna
dandamalin dutse ta dauko wayarta a jaka cike da doki
hannunta na karkarwa ta danna muryar...
Rumaisau kin taba nazari akan zucia?
Harumin gaske ne ke rike akalarta ya ja sabanin ta jashi,
tawa zuciyar kamar ni take ja. Ma'ana ban cika jaurimi
amma na kasa yarda ni rago ne dan na rike hujjar
zuciyata na ja ne ga alkhairi ne wato ke.
Zuciyar tawa na da karpin hali ko?
Bana ganin bakinta ni kuma dan ta gamsu kin hada
dukkan alkhairan da idan anyi paputuka a kanki ba a
sarayar da lokutar a wopi ba, dan ma duniar nada abun
tsoro ko?
Gangancin shigar haske cikin duhu da shigar duhu cikin
haske ya isa kada zuciyar mai imanin mutuwa wadda
bata bukatar imani cikin sharudanta, ga wanda ya yarda
da ita da wanda bai ma yarda da ita bam duk ba wanda
take ragewa
duk sanda na yi tsaye cikin lambu ina kallon sararin
samania sai na cika da shakkar anya kuwa ozone layer da
akce yana kekkecewa ne yake kara gudun dunia ba
waccan mutuwar ke kusatoni ba?
Duk sanda na tuna haka sai nayi kwalla ina ganin kamar
zanyi mutuwar da babu gata, wato wadda na ke so bata
yarda ina son ta ba.
Mukwana lapia.
Bata gama tantance matsayin da zuciyarta da azancin ta
suka karbi sakon mahaukacin masoyi na yanzu ba ta
hanga yushau ya nupo ta kai tsaye yana ta sauri kamar
mai shirin tashi sama..
Ambaton MUTUWA wadda take da kishiyar rayuwa
asakon mahaukacin masoyi ya sata kallon Yushau na
tahowa garau!
Saboda tunaninta da yake son tino rayuwar ta ta baya.
Yau da gobe a rayuwarta.
Mutuwa a cikin rayuwarta.
Kaddarori marasa dadi na rayuwarta.
ASALIN RUMAISA'U.
Mahaipin ta...
.
in shaa Allahu gobe zamu ci gaba daga inda muka tsaya..
.
Dan AuntyGORAN DUMA 5
.
.
ASALIN RUMAISAU

Mahaipinta Aliyu Ahmad dan karamar hukumar Rogo ne
a kano. Mahaipiyarta Khadija inyamura ce mutumiyar
Enugu wadda ta musulunta a hannun mahaipinta sukayi
aure da zama a garuruwa daban-daban kasancewarsa
dan sanda.
Mahaipinta dan dangi ne sosai a kauyen Rogo da cikin
garin Kano duk da cewa su biyu ne kacal a gurin nasu
mahaipan wato shi da kuma yayansa Usman mahaipi ga
Yusha'u da kannensa mata hudu sai Mubarak auta,
mahaipinta da mahaipiyar ta akwai zama na soyayya da
pahimtar juna mai kwari a tsakanin su, Allah bai wadata
su da iyali masu yawa ba daga yayarta Balaraba (Aisha)
sai ita auta har a halin yanzu wajen uwa da uba.
Bayan rauni na kasanxewarta a jinsin mata masu rauni
sai wata jarrabar Ubangiji Yayi mata na kasancewarta
daga masu pama da larurar nan ta sankarar jini (sickle
cell ) cutar da gatan da iyayenta ke nuna mata bai hanata
tasowa cikin wata irin mawuyaciyar rayuwa ba , alal
alakka sun karbi kaddarar haihuwarta da Ubangiji Ya
nupe su dayi suna godia a gare Shi tare da rashin gazawa
ko kosawa cikin tarin dawainiya gare ta yadda ya kamata,
duk wani sikila ya samu.
Iyayenta naji da ita suna tausaya mata suna tattalinta
ninkin yadda suke tattalin yayarta Balaraba sun jure duk
wani alayi na ciwonta, kai karewa saboda ita innarta ta
koma karatu bangaren lapia bayan tayi digirinta na parko
akan Na'uwa mai kwakwalwa (computer engr.) kapin
aure, bayan sun haipeta da shekara daya ta karkade
zaninta ta koma makaranta inda ta karanto wanda ya
kara taimaka mahaipiyar kwarai wajen yadda take kula
da rayuwar ta.
Tayi karatu a tape kuma cikin gata kamar yadda ya
kamata har matsayin kammala babbar sakandire ta pito
da sakamako mai kyau, saboda haka ta sa ran shiga
Jami'ar Bayero ta kano dan karanta aikin jarida.
A daidai wannan lokacin mahaipanta zaune a enugu
saboda haka ta debo zaman karatunta ba dan son ran
iyayen ba ta dawo wajen yayan mahaipin nata Alh Usman
wanda ke zaune a kano kuma shahararren dan kasuwa a
kasuwan kantin kwari.
Daidai wannan lokacin Balaraba yayarta ta auri Mukhtar
ma'aikaci a garin Abuja , shima Alh Usman Ya aurar da
yayansa mata uku, Atika, asiya, maimuna sai Hapsat kadai
wadda take tsararta sannan Mubarak sai ko babban
yayan su Yusha'u da ya tasamma zama tuzuru babu aure.
Yushau ba a gaban iyayensa ya girma ba tun daga yaye
kakarsu ke rike dashi a Rogo har bayan rasuwarta ma sai
yaci gaba da zama inda yapi wayo , can yayi firamare da
sakandire yazo gidan su kano yayi NCE a FCE kano bayan
kammalawan sa saboda sabo da rogo sai ya kuma
komawa can ya kama aikin koyarwa amma idon kudi da
ya gani lokacin zaman karatunsa a kano yake zuwa

kasuwa gun mahaipin sai ya hana shi mayar da hankali ga
koyarwar inda bai hada shakaru biyu cikinta ba ya ajiye
ya dawo kano yaci gaba da harkokin kasuwanci.
Duk sauran kannensa ma sunyi karatu daidai gwargwado
na iyakar sakandire suka yi aure, Asiya da Atika da suka
auri yan boko sun sami damar ci gaba har sun para aiki,
amma Maimuna na zaune a gida da kasuwancinta,
albarkacin Rumaisau yabawa hapsat damar dorawa daga
sakandiri bayan nacin ta sami B.U.K ta gaza sai ta bige da
sa'adatu Rimi collage.
Hankali da nutsuwar Rumaisau tare da rashin kuzarinta
wani abu ne da sam baya dada yushau da kasa, yana
mata kallon wata muguwar shagwababbiya kuma mai
shegen raki, wadda yake ganin ba a kanta aka para ciwo
ba amma akwai alamar tapi kowa kururuta shi, kullun ita
ke nan cikin ciwo da neman uzuri ayadda ta baro gidan
su suke kirkirar mata shagwaba da mayar da kai baya
haka anan gidan nasu babu wanda ta rage, alh da Hajia ,
hapsat da Mubarak kuma suka pi kowa taya bera bari a
wajen su komai na Rumaisau na musamman ne kai
saboda Rumaisau sun hakura da yawa daga jin dadin
rayuwar su,
saboda Rumaisau Alhi ya cire duk wani A.C a cikin gidan,
panka idan Rumaisau na guri cikin su hudun nan babu
mai shan iskarta, in kuwa shi ya guntse ido zai kunna duk
zasu taso kansa da korapi.
Duk wani aikin gida na mata babu ruwan Rumaisau da shi
ko ta sa kanta zatai hajia kan hana, abincinta na
musamman ruwan wankanta na musammam, duk inda
zata pita kuma sai anyi dawainiyar da ba zata yi tapiar
kasa ba,
ba ta da aikin da ya wuce taci ta sha ta pita yawon
makaranta, anjima kuma ta ishe su da rakin ciwo.
Ba wannan ne kadai abin da ke damun Yushau akan
rumaisau ba, har da matsayin karatunta wanda sam baya
kaunar wata mace ta taka matsayinsa, in kuma har ta
taka din to yana mata kallon wata gagara kundila a duk
wani nau'in halin tsiya.
Wadannan dalilan ne suka hana shi iya boye kin da yake
wa rumaisau wanda ya hada da hapsat saboda tattalinta
ga rumaisau da kuma kama turbar rumaisau na zurpapa
ilimin boko.
Hakurin Rumaisau da zaton alkhairinta yasa bata taba
hasashen yushau ya tsaneta ba, pahimtar da tayi masa
kawai shine shi daban ne a cikin gidan mai wani
murdadden hali da kake kasa passarawa, yana da pushi
yana kuma da halin sauye-sauye, saboda haka ta koyi
zama dashi, bata cika nuna shigarta wani hali a gaban sa
ba dan gudun yaki bata muhummanci taji haushi, bata
daguwar hira dashi , bata neman taimakonsa ko wanne
iri, kuma idan hajia ko Alh sunyi masa umurnin kaita
makaranta ko asibiti yana paman kumburi ta kan bashi

hakuri tare da karawa kanta nustuwa dan kai yaga
giggiwarta, amma duk da haka bata tsira ba,
akwai wani lokaci da Alh ya sanya shi kai ta taronsu na
masu ciwon sikila ya jirata har aka tashi taron, a hanya
sun taho yana paman cika da batsewa har ya pashe da
cewa '' inda zaka san ciwon nan shipcin gizo ne har da
wata kungiyam wai dan tsabar lalacewar zamani ciwon
ake wa kungida ko ya san ba ciwon ne ya dame ku ba
wata hanyar neman kudi kawai kuka mayar da ciwon.
Rumaisau tayi murmushi tana kallon tagar motar kapin
da kyar ta samo abin cewa '' yaya yushau kamar yin
kungiyar zai pi rashin ta ampani, ni dai tana kara min
imani da godia ga Allah wanda ya halicce mu yadda Ya so
ba dan kiyayya ba, sai dan Ya zamo jarrabawa a gare mu
kawai dai kayi mana patan ya zama mana kappara.
Yushau yayi wani tsaki sannan ya tsule bakin sa.
Shekararta ta karshe a BUK hapsat ta kammala NCE har ta
para aiki, mahaipanta sun dawo Abuja da zama a wannan
shekarar ne ta hadu da gwarzon masoyin da take jin har
dunia ta nade baza tayi irin sa ba.
Ba wai tana rasa masoya ba ne, sai soyayyar bata wani
nisa saboda rashin goyon bayanta, ko kuma in sun san
matsalarta su kauce.
Sun hadu a wata laraba ne tana tsaye a bus stop cikin
BUK new site tana jiran motar da zata kai ta old site ita
kadai ce tsaye a wajen sai pama take da rikon tapkekiyar
lema a hannu, saboda hadarin daya para daurewa, zai iya
zubar da ruwa bagatatan, saukar ruwa a jikinta kuwa
wani tushen tashin hankalli ne da zai iya motsa ciwonta.
Daidai wanan lokacin Auwal Yazo giptawa ta gabanta da
motarsa.
Tabi motar da kallo cikin tunanin yadda suka kwashe da
Mominta a hutun daya gabata.
''Rumaisau da zaki iya tuki a kano sai na sai miki mota,
saboda yau da gobe duk sapiyar Allah da yammaci sai na
tuno yadda zaki pita ko zakii dawo gidam sai na dinga jin
kamar zanyi tsuntsuwa nazo na dauke ki m na san
wahalar da dalibai suke sha''
ta dubi mahaipiyarta cike da so da kauna tace momi ai
kina min addua in Allah Ya so ba zan tabe ba.
Momi ma ta zura mata ido tana murmushi tace duk da
haka zan iya siyen motar?
Ta kada kai tace in hankalinki zaipi kwanicia ki siya
mana...
Momin ta tareta da padin to wacce iri kike so pada min
idan kudina basu kai ba in nemi taimajon dadinki.
Rumaisau tayi daria tace ta daidai kudinki nake so.
Momi ma ta sake yin daria tace shikenan zan baki
mamaki.
Auwal ya kula da kallon da Rumaisau tabi motarsa dashi
ta madubi. Kasancewar shi ma ya sa mata ido kawai sai
ya taka birki , sannan yayo baya ya risketa, ganin haka

yasa ta dauke puskarta zuwa kallon wani gurin daban,
tama ajiye lema ta bude jaka ta ciro gilas ta kwama.
Auwal data kara jan hankalinsa sai ya bude mota ya puto
ya zagayo wajen tana share puska ya dubeta sama da
kasa yace '' Mace! mace akwai waskiya, yadda kikayi
puskar nan badan naga sanda kika zubo min ido ba in na
kwana dubu ina rantsewa babu wanda zai yarda idan
nace kin kyasa.''
da sauri ta dago ido ta dube shi sannan ta dubi motar a
takaice tace ba kai nake kallo ba...''
ya tare ta da sauri wa kike kallo?
Ta nuna masa motar tana cewa gata ai tapi ka kyau.
Ya danja da baya baki bude na alamar shan mamaki ya
kallo motar tasa sannan ya dubi kansa yana gyara kwalar
riga tare da gilashin idon sa cikin daria sosai ya dapa
motarsa yace yanzu wannan tapi ni kyau don Allah?
Dube ni pa ki gani son kowa kin wadda ta rasa , ni ba
dogo ba, ni ba gajere ba, ni ba pari ba ni ba baki can ba,
ga idom ga dogon hanci, shape din ba irin na maza ,
komai yaji pa kar ki bari kiyi asara yarinya.
Mota ki kayleta in kina raye sai ki ga kinyi wadda tapi ta...
Nipa na ma tsaneta daga yau... Dan kishi ne dani...
Yanzu ta daga kai suna duban juna ita dashi kai tsaye
bada zummar komai cikin ranta game da shi ba sai game
da maganganunsa kasancewarta mai sanyin hali tana son
mutun mai barkwanci, ba ta sami abin cewa ba ya rigata
da padin yaya naji zaki danyi manejin tapiyar dani?
Karon parko tayi murmushi ta girgiza kai kayi hakuri a
patar bakina kawai kalmar ta tsaya, bani motarka da kallo
amma zahiri ba ita din nake nazari ba, wata duniyar
tunanin na tapi daban kasan ana haka ko?
Ya kada kai yana murmushi ma sani amma dai kinji nace
bana son kisiya?
Ta sunkuya tana murmushi ta dauki lemarta ta mike tana
padin kodai kishiyi?
Sukayi daria su duka ya karbi lemar hanun ta. Zo mu tapi
kinga ruwa na shirin sauka kai ya daki puskarki yayi mata
lilla.
Ta girgizakai tana murmushi nagode kawai amma bana
hawa lift.
Da sauri ya tareta waya pada miki lift zaki hau?
Ke da motarki.. Na rantse zaki iya shape komai a duniata
saboda haka kece alparmar tawa ba ni zan zama
alparmarki ba.
Ta kara dubansa da kyar a sanyaye tace wannan dokin
pa?
Daga ganin sarkin pawa sai miya tayi...''
ya sake tareta da padin watalila na kalla naji wata
kwakkwarar zumunta ta sarkape zucia ta, da na karaso na
kalli puskarki sai kawai naji mun zama JINI DA TSOKA
daya.
Ta sake duban sa da kyau tana daria abin da take ji a

ranta game dashi, shine ya iya dadin baki, da bata
dandani shekaru da yawa a dunia ba , parat daya zai
wapce imaninta.
Ta lumshe ido kai tsaye tace bana son bata maka lokaci
ko juyar da karramammun kalamanta, gashi ciki dole na
zabi daya.
Kai tsaye shima ya amsa kin zabi bata min lokacin indai
ba kishia ne dani ba, karramammun kalamaina karki
wani kalli karancin su, yadda ya kamata su pito a kunnen
ki ne, wallahi ban tsara su dan in burge ki ba, zo mu tapi
don Allah.
Bai jira cewarta ba ya bude mata kopa. Ta danyi jim sai ta
kasa tankwabewa ta shiga moyar.
Ya rupe sannan yazagaya ya shiga yana mika mata
lemarta ya tashi motar,.har suka zo bakin gate kalma
daya ta hada su, menene sunan ki?
Kai tsaye ta amsa masa Rumaisau Aliyu Ahmad.
Yace sunan ki mai dadi, ni sunana Auwal Ibrahin Hadi.
Bata tanka ba shima baii kuma tankawa ba har suka zo
bakin gate wata iska mai karpin gaske ta taso da alamun
yanzu ruwa zai sauke, kirjin Rumaisau ya para dukan
uku-uku cikin matsananciyar pargaba ta dubi maza da
matan dake tsaitsaye cikin tashin hankali , ta tabbatar duk
yadda hankalin su zai tashi bai pice pargabar zasuyi mura
ba, ita kuwa in ruwan ya daketa zai wahala batayi ciwon
da ya kusantarta da ita da kabari ba.
Rage gudun da Auwal yayi yasa pargabar ta karuwa,
saboda zaton sauketa zaiyi amma sai taga ya nupi titi zai
haura, ta sauke ajiyar zucia muryarta na sarkewa ta dube
shi tace da ka taimaka ka dauki matan can nasan baza a
rasa wadabda zasuyi hanyar da zakayi ba, za ka sami lada
idan ka taimake su.
Ya dan ja pasali yana duban titi ba tare da ya dubeta ba
yace.
allah ya kawo mai taimakon su ni bana daukar mata a
motata.
Ta dan juma tana duban sa duba na rashin pahimta
sannan tace ni ba ka gane nawa jinsin bane?
Yayi murmushi ba tare da ya dubeta ba. Kakkarpar alakar
da zuciya ta ta kulla dake ya koro wancan kudurin nawa
daga naki jinsin, kin zama yar gida a zuciata da duk wani
abu da na mallaka.
Ta gaji da kallon sa ta kawar dakai . Ruwa ya para sauka
da karpuli cikin sauri ta balle jakarta ta puto da rigar
sanyi ta saka tana kumbiya-kumbiya.
Bai tanka mata ba amma dai hankalinsa na kanta duk da
idonsa na titi, tana bayyana alamun jin sanyi amma
kawaicinta ya hana ta zuge gilashin bangarenta, kuma da
hakan yasa yayi mata aikin da ta kasa yana cewa na lura
kunama ce ke, kawaicinki kuma na son hanaki abinda
kike so...
Tayi yar daria ta amsa nida na zo ci rani har ga Allah bai

kamata in zake ba.
Ya watsar da wannan batun nata yace ina zan kai ki?
Tayi dira-dira alamar canki-canki sai ta kasa zabar gurin
zuwa tayi shiru kawai sanyi na kadata.
Hankalinta yayi gida amma ta inda zata bi taje?
Ina zata pake ta sami motar?
Ya juyo yayi dan nazarinta cike da mamaki yace ina zaki
je?
Muryarta na rawa tace ai na kasa zaba ne, bana son sanyi,
ruwa in ya dake ni illa yake min, da makaranta zanje
amma na pasa saboda sanyi, yanxu inka sauke ni kapin
na samu motar ma ruwan yayi min abinda yaga dama.
Yaci gaba da kallon ta cikin nazari bai pahimci abin da
yake son pahimta ba ya kada kai yace nima ba zan iya
ajiyeki ruwan ya dake ki ba, ina da ganawa karpe uku sai
dai ayi min uzurinta, inane unguwar ku.
Muryarta taci gaba da rawa saboda laipin da takejin zata
yiwa kanta da gidansu, a ganta saurayi ya sauketa kamar
zubar da mutunci ne, amma kamar wannan zabin zaipi
dukan ruwan.
Na gode Allah Ya saka maka da alkhairi, a Gandun Albasa
nake.
Yace hanyarmu daya kenan ni a Na'ibawa nake, ziyara na
kawowa wani malamina shekaru na biyu da barin
makarantar nayi digirina na para aiki a karkashin
gwammanti,
ya kamata na ajiye iyali Allah bai kawo ba sai yai Allah
Yayi min katarin daura damba,
Rumaisau tayi dip kamar ruwa ya cinyeta tausayin kanta
ne ya hanata nazarin amsar da zata bashi taji kaunarsa a
ranta, sai dai taki yarda irin kaunar da take dorewa da
aure ce, kauna ce kawai irin wadda dan Adam ke wa
wanda yake zaton mutumin kirki ne ko kuma wanda yayi
ma alkhairi?
Tayi sararo tana kallonsa kawai yana jin kallon da take
masa a jikin sa, amma ya hadiye ya juya ya kalle ta.
Ta juya a hankali tabi tagar da kallo tare da sauke ajiyar
zucia ba tace komai ba.
Bakida abin cewa akan abin da na pada?
Ta girgiza kai a nuste tace kar ka batawa kanka lokaci
nasan ban cancanta zama iyali ba.
Yayi saurin yi mata duban rashin pahimta amma ya
takaita azarbabi wajen ce mata Ai ina tsammanin ba ayin
komai babu hujja ko?
Ki pada min dalili dan duba na gani.
Ta muskuta tace dashi don Allah kayi hakuri.
Yayi kasake yana kallonta sannan yace indai ba laipi
zanwa Allah ba to bazan iya hakura ba...
Ta tare shi da padin ina patan nan gaba ba zaka zarge ni
da rupa-rupa ko yaudara ba?
Ya ki daukar maganarta da muhimmanci ba tare da nuna
damuwa ba yace ina saka rai alkhairi ya biyo baya, idan

kuma akasinsa ya samu zan dogara ga Allah, amma ki
sani idan akwai laipinki ciki Allah ne baZai barki ba.
Musamman da yake a rupe kike ba ni uzurinki.
Tayi shiri kawai shi kuma ya share maganar ya shiga
tambayarta karatu, da wani abubuwa da yake jin suna da
muhimmanci a cikin alakar da yake son kullawa da ita,
cikin ikon Allah suna wuce Gadon kaya babu ruwan babu
iska ko hadarin ma babu saboda haka taji ranta ya apu da
son ta sauka ta hau motar haya ta karasa, amma ta kasa
yi masa magana har sai da aka kira shi a waya ana
nemansa wajen taro ya bayar da uzurin sa yana sauke
wayar tace kawai ka sauke ni anan na shiga mota na
karasa, sai ka wuce sabgoginka,
da yake tun parko ke ika kirkiramin sabogogin ba, karki yi
mamaki inna ki bin umarninki. Dole tayi daria ta share
zancen , ya tsayar da motar a harabar gidan su yana dan
zuba mata ido saboda yadda yaga kamar ta kadu da
ganin wani da ya tsaya da motarsa kusan lokaci daya
dasu.
Da sauri ya kallo motar dan ganin tana rawar jikin
picewa, ta juya ta dube shi da duban rashin pahimta ya
nuna Yushau yana padin wanene wancan?
Ta dubi Yushayu sanan ta dube shi atakaice tace Yayana
ne.
Yayi zuru yana kallon yushau haka kawai yaji hannkalinsa
baikwanta da shi ba sam ya kada kai bisa dole ya bude
kopar suka puta lokaci gidam da sauri ya nupi yushau
dake kokarin rupe mota yayi masa sallama tare da mika
masa hannu. A wulakance yushau ya amsa idon sa na kan
rumaisau sannan yace Yaya kuke da wannan?
Auwal yayi zuru yana kallon Yushau da rumaisau yadda
yushau yayi magana puskarsa babu walwala ne yabawa
Auwal damar nustuwa ya karance shi.
Akwai alanar nutsuwa a rumaisau sai dai a rikice ta debo
masa amsa dan Ajin mune.. Ya taimake ni ne saboda
ruwan da ya tare ni..hanyarsa kenan shi yasa ban nemi
sauka ba da muka wuce inda ake ruwan.
A gadarance yushau yace kina pada min hanyarsa ce dan
kun shirya kullun ya dinga dauko ki yana kawo ki ko?
Ban san iyakar tsawon lokacin da zan dinga pada miki
nan arewa ba kamar can kudu bane, babbar kazantace
aga mace ta dauki namiji aboki..
Ganin yana neman tsinkata ta tare shi da cewa larura ce
yaya yushau nayi gudun dukan ruwa ne .
Yushau yayi tsaki tare da yin gaba yana cewa duk illar da
dukan ruwa yake dashi ai bai kai na sayar da mutumci ba,
koda yake wayewarku ta halatta muku haramci.
Rumaisau tayi suguri ranta yayi mugun baci, ta san
yushau bai iya magana ba sam, haka yake yinta kamar
kashi, amma a yau ta para shakkar dan tazo cin arziki
gidan sune,
a sanyaye ta dubi Auwal da yayi shiru rungume da hannu

yana kallon kasa tace na pa gode zan shiga ciki, ya dago
da alamun tunani ya dubeta me yasa kika ki pada masa
gaskiyar matsayin da na zaba mana?
Sai kika alakanta mu da jabun dangantaka?
Ta dan ja nunpashi sannan ta amsa har yanzu kai kake
kidi da rawarka, da zaka bi ta tawa zamuyi sallama ne mu
rabu har abada, karatu ya kawo ni garin nan yakamata
naji dashi shi kadai. Mts! Ni bana son hargitse-hargitse
wallahi.
Ya pahimci cikin bacin rai take saboda haka sai da ya
shirya kalaman da zai mata sannan yace kina da wanda
kika tsayar?
Ta girgiza kai , puskarta a dauke, ya numpasa yace idan
haka ne na tabbatar kinzo kano ne dan mu hadu mu auri
juna ba tare da nayi gibi a karatunki ba, ki daina
gaggawar yanke hukunci akan lamarin rayuwa da hakan
gara ki zama mai dabar tsara al'amuranki, ina neman
alparmar kar ki koreni.kuma ban matsa miki ki so ni ba,
amma ki bani dama mu pahimci ko zqmu iya tapia tare.
Yanzu idonta cike yake da kwalla saboda takaicin kalaman
yushau gidan su kawai take tunawo da yadda take da
kima da mutunci a cikin sa.
Auwal na ganin kallarta ya dan shiga damuwa amma a
nutse ya tausasa murya yace mata idan akwai matsala
dan Allah ki pada min kuka na nupin damuwa. A
kalamaina banga abin da na pada da zai bata rai ba.
Ta kirkiro murmushin karpin hali dole tace masa babu
komai Allah Yayi mana jagora.
Tun daga wannan ranar Auwal ya zame mata wani barin
rayuwa ya kware da samar da mahallan parin ciki a
zuciyarta da kirkinsa da kuma yadda yake kula da ita da
damuwa a cikin abin daya dame ta.
Kullun sai yazo gidan su tare da cewa yana bata mata da
yawan lokutai a waya, haka kuma takanas yake binta
makaranta ya daukota, babban zunubinsu da ya tsayewa
yushau a rai kenan saboda imanin da yayi na cewa duk
yarinyar da ta je jami'a sai ta lalace, ya rasa yadda zai
pahimtar da hajia da Alh a matsayinsu na wadanda
kamar su ke waliyantar da Rumaisau saboda kyan hali.
Rumaisau ta para nisa cikin abind a bata zaba tsarabarsa
a rayuwar ta ba wato SO, tana ji a ranta ita nakasasshiya
ce duk yadda so zai zo mata in ta amince masa wata rana
zai zame mata madaciya, amma a yanzu Auwal ya ture
wannan tsarin a ranta sai ya barta da zullumin yadda
rayuwa zata kasance musu a gaba. Zai rabu da ita ne idan
ya san ita sikila ce ko kuwa zaiyi shahadar auren ta?
Zabi na karshe ne patanta, sai dai zuciyarta na wuyatantar
da yiyuwar sa.
A yanzu sun pice watanni uku tare duk wani laulayi da
alayin cututtukanta babu wanda auwal bai gani ba, yau
kapa ciwo gobe cikim jibi zazzabi, gata mura... Kai shibai
taba ganin mutun mai laulayi kamarta ba, amma wannan

bai gutsuri komai cikin soyayyarta ba sai ma kari saboda
tsabar tausayin da take bashi, kuma laulaye-laulayenta ne
ya koya masa tarin hanyoyin da zai nuna mata kulawa,
dan haka ya zama dan gida dan gaske a zuciyarta da
zuciyar kowa ma a gidan in aka yi gepe daya da
murdadden Yushau.
Asai dai duk wannan shakuwar tasu ya rasa dalilin da yasa
rumaisau taki amince masa manya su shigo maganar, ya
bata lokaci ya kara mata amma har yanzu ta kasa gabatar
masa da uzuri, sai dai hakan yaki ya dame shi dan yana
da yakinin ya kai matsayin da yapi karpin yaudara a
zuciyar rymaisau sai kawai ya zuba mata idon ganin
gudun ruwa, musamman da yake karatun nata yazo
karshe..
.
Dan Aunty.
July 31 at 8:26 PM ยท PublicGORAN DUMA 6
.
Ya bata lokaci ya 'kara
mata, amma har yanzu ta kasa gabatar masa da
uziri, sai dai hakan ya 'ki ya dame shi dan yana
da ya'kinin ya kai matsayin da ya fi 'karfin
yaudara a zuciyar Rumasa'u, sai kawai ya zuba
mata idon ganin gudun ruwa, musamman da yake
karatun nata ya zo 'karshe.
Wata rana sun fice goma na dare suna hira a
zahiri daurewa kawai ta ke saboda cikinta da ke
ta faman murd'awa. Ta daure din har suka yi
sallama ta shiga gidan a birkice, zta wuce ciki
Hajiya ta yi kiranta.
"Zo nan Rumaisa'u, me yake faruwa na ga kina
yamutse fuska?"
Ta 'karaso ta zauna a gajiye.
"Wallahi cikina ke min ciwo".
Hajiya ta dubeta cikin tausayawa, ta ce.
"Sannu, sai ki yi 'kokari

2 Comments On GORAN DUMA
avatar
jannat

1 year ago

Reply

08062236094

avatar
jannat

1 year ago

Reply

08062236094

Please Login or Register in order to submit comment