Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ni asibitin albarka zan sa masa".
Ta yi murmushi kawai ta yi masa sallama ta fice duk da

kuwa dari da hamsin ne a jakarta, ko cikakken
kudin a daidaita sahu ba ta da su daga Sallari zuwa
asibitin Nasarawa, ga shi safiya ce bare ta je banki ta fitar
da kudi. Amma dai da yake gidan zafi yake mata sai ta
jefa katin ATM dinta a jaka ta fito daga gidan ta kama
tafiya a 'kafa zuwa titi ta sami adaidaita sahun da zai kai ta
asibiti a kudin jakarta.
Akwai tazara tsakaninta da titi saboda haka hutunta hudu
a hanya, tana na hudun ne kan wata kwalbati kamar daga
sama Hafsat ta tsayar da motarta kusa da ita tana matsa
mata hon.
Cikin farin ciki da goge gumi ta mi'ke ta nufi motar Hafsat
ta bude mata cike da mamaki tana tambayarta.
"Daga ina zuwa ina?"
Bayan Rumaisa ta shiga motar ta daure cikin murmushin
ya'ke tana cewa.
"Daga gida zuwa asibiti, ke kuma daga ina kika fado mana
da sassafe haka, ko ba gidana za ki ba?"
Hafsat ta juya motar rabin hankalinta na kan Rumaisa ta
ce. "Daga gida nake, jiya Mubarak ya sanar da ni ba ki ji
dadi ba, da ke na kwana a raina shi yasa na doko
miki wannan sammakon".
Rumaisa ta yi murmushin jin dadi ta ce.
"Kin kyauta wallahi, kin ceci rai, ina Sani da ya bari kika
fito da safe haka?"
Hafsat ta amsa mata tana dariya.
"Ya fita shi ma, da dai ya kwaso min mita sai kuma ya
mayar da ita gori, wai gara na dinga zuwa ina
ganinki ko na yi zuciya in taya 'kokarinsa in karb'i baby".
Rumaisa ta tayata da dariya ta ce. "Sani ba dai ba'a da
zare-zaren magana ba".
Hafsat ta murgina kai, ta ce. "Ai fa.....
Hafsat ta murgina kai, ta ce. "Ai fa, me kike zaune kan
waccan kwalbatin?"
Cikin son a basar da maganar Rumaisa ta ce.
"Hutawa nake, wai 'karfe nawa?" Hafsat ta dan kalleta da
kyau sannan ta mayar da kallonta ga titi ta ce mata.
"Tambayar da na so in miki kenan, da sanyin safiyar nan
kika fito a yanayin jikinki kuma har da
tafiyar 'kafa, ina Yaya Yusha'u?"
Cikin hadiye 6acin rai Rumaisa tta ce. "Yana gida, kansa
ne yake ciwo..."
Da sauri hafsat ta tare ta.
"Yadda har ba zai iya tu'ki ba kuma ba zai iya fitowa ya
nemar miki adaidaita sahu ba?"
Sai Rumaisa'u ta kasa amsawa, wannan ya sabbaba shiru
a tsakaninsu, saboda kowa da abin da zuciyarsa ke
sa'kawa.
"Mu 6ulla ta zoo road ko zan samu fitar da kudi a Sahad".
In ji Rumausa'u cikin rashin nutsuwa dan ta san fada
kawai ta yi dan kar kai tsaye ta roki Hafsat
kud'i, amma ta san yanzu ba zata iya fitar da kudi ba.

Hafsat ta dan harareta ta ce.
"Da wannan safiyar?"
Rumasa'u ta yi shiru kawai, ita kuma Hafsat ta dora cikin
zafin rai da 'kufula.
"Mubarak ya fada min hannunki ke ciwo har ya fara
kumbura, mu gani".
Rumaisa'u ta janye hijabi cikin d'ar-dar ta nuna mata
yadda hannun ya kumbura kamar yana dab da jan ruwa.
Hawaye ya cika idon Hafsat ta janye ido tana cewa.
"Yaya Yusha'u ya san haka hannunki ya yi?"
Ita ma Rumaisa sai da ta goge kwalla saboda tuno yadda
suka yi jiya akan girkin abinci da damun
fura, sannan ta amsawa Hafsat.
"Ya sani, na fada miki kansa ke ciwo".
Hafsata ta sauke fushinta akan Rumaisa'u cikin zafin rai ta
ce. "Wai Rumasa'u me yasa kike damuwa da kare
azzalumi irin Yaya Yusha'u ne?
Kina son wawantar da mutane game da yadda yake
danne hakkinki. Ni kuma ban ga ribar da kike samu a kan
haka ba...
har gara ki bayar da 'kofar a kwato miki 'yanci idan ba
haka ba yana dab da kai ki kabari..."
Kuka ya su6ucewa Rumaisa'u cikin shessheka ta ce.
"Ni wallahi da zan mutu ma sai ya fiye min, ni ban ga
zaman duniyar nan ya kar6e ni ba..."
Sai su duka suka kama kuka. Haka suka je asibiti jugumjugum, sun 6atar da kimanin awa biyu a asibitin, Hafsat
kuma ta 6atar da kudi masu yawa,
sannan ta dawo da ita gidanta da zummar zata dawo da
yamma su tattauna wata magana.
Ba ta sami Yusha'u a gida ba, saboda haka ta dan sami
kwanciyar hankali, a 'kalla ba ita babu 'kyara da
tsangwama da kuma sa aikin rashin tausayi. Wajen 'karfe
biyar ta fito da darduma a baranda ta shimfida dan ta sha
iska, dakin akwai dan zafi,
kuma tana tsoron kunna fanka ko kadan din ce dan kar
garin neman 'kiba ta samo rama.
Ta daga waya ta kira Hafsat, sai ta ce mata tana hanya.
Tana sauke wayar ta ji tsayuwar motar Yusha'u, sai
gabanta ya yi wani mummunan faduwa da ba ta
ta6a jin irinta ba, kawai sai ta kama ambaton Allah a zuci.
A haka Yusha'u ya fado gidan cikin mayen 6acin rai
saboda haka nan take jikinta ya dauki 6ari, ta sami kanta
da tashi zaune tana ture farantin rake da ke gabanta.
"Rumaisa'u wanne karanbani ke sanya ki yi min bincike a
waya, kina gane min sirri kuma ba'kin
cikinki ya sanya ki wargaza kyakkyawar dangantakar da
ke tsakanina da su?"
Ta hadiye dukkan fargaba da takaicinta ta dube shi da
sanyaiyiyar murya ta ce.
"Ban gane na gane maka sirri ba Yaya Yusha'u,
bayan cewa ni ce sirrin naka, kuma barrgonka malullu6ar

asirinka".
.
Sai gobe idan Allah Ya kaimu.
Dan Aunty na Ruma.GORAN DUMA (P 39)
.
.
Ya fara kumfar baki.
"Allah Ya kiyaye, a ina kika zama sirrin nawa bayan cewa
zuciyarki ma6oyar sirri ba ni ne a cikinta ba,
amma dan 6ata baki ki ce ke ce..."
Ta tare shi da 'karfin halin kyautata murya har ma da
d'an murmushi ta ce.
"Duk yadda ka dauke ni mara amfani a rayuwarka ba zai
hana na zama sirrinka ba, misali jiya 'karfe nawa ita
Sumolin ta turo sa'ko kuma ta kira wayarka?
Karfe daya da 'yan mintuna ta kira wayar shaidar ni ce
sirrinka tare ta same mu, ita tana can tana faman juyi da
filo tana mafarkin ido biyu. To bari ka ji, ni ba kishi nake
da ita ba dan ba aikin banza na zo yi a duniyar ba bare na
tsaya 6ata
lokacina wajen wula'kanta kaina da jera kafad'a da wata
mara mafad'i ba".
Ya tsattsare ta da ido fuskarsa a jagule.
"Ke wace ce mara mafadin?"
Yana rufe baki ta amsa masa kai tsaye. "Ita Sumolin
mana! Matar kirki ce zata kira namijin aure karfe dayan
dare har tana wasu maganganu na rashin tarbiyya..."
Kawai sai Yusha'u ya wanketa da wasu zafafan tagwayen
mari a cikin sakanni kadan abubuwa biyu suka faru,
hancin Rumasa'u da ya 6arke da jini da kuma shigowar
Hafsat gidan, ta samu Yusha'u tsaye yana surfa masifar
borin kunya dan shi kansa ganin jinin ya yi mugun kad'a
shi.
Hafsar ta tsaya cak cikin tashin hankali tana kallon
Rumaisa'u da ta durkushe ta tara hannayenta jini na zuba
cikin kuka tana ambaton innalillahi wa inna ilaihi raji'un.
A bayyane yake yanzu ba ta zafin marin ta ke ba, ta jinin
da ta ke asara ta ke wanda ta tabbatar 'kila rashinsa ya
janyo mata wata matsalar.
"Haba Yaya Yusha'u, don Allah ina abin duka a jikin
Rumaisa'u?"
Hafsat ta fada cikin 'kumewar takaici tana duban Yusha'u
cikin tsana, shi kuma ya tare ta da nade
tabarmar kunya da hauka. "Fita! Fice min daga gida, 'yan
iska dama ku ne masu zuwa har gidan mutane kuna
kashe musu aure... Fita!. Kar na 'kara ganin 'kafarki a
gidan nan".
Ta zabga masa hararar da ta ku6uce mata, ta ce.
"Amma dai ai ka bari na taimake ta ko?"
Ya yi kanta kamar zai rufe ta da duka.
"An 'ki ki taimake ta, tun wuri ma ki fita idan ba jiran naki
dukan kike ba...."

Ta yi baya ta fice tana 'kun'kuni.
"Allah Ya kiyaye, ai ni mai dukana sai ruwan sama, ita ma
Allah Ya isa." Hafsat ta tsaya cikin mota ta kira Alhaji cikin
kuka ta ke fada masa.
"Alhaji ka taimaka ka shigo lamarin Rumaisa'u Yaya
Yusha'u zai yanke maka danyen hukuncin, ya kashe
Rumasa'u ya janyo maka masifa..."
Alhaji ya katse ta cikin dukan zuciya da si'kewa. "Ke bana
son jaye-jayen bala'i, me ya faru?"
"Na zo gidan na tarar ya yi mata tsinannen duka, yanzu
haka ina 'kofar gidan dan ya hana ni shiga,
ita kuma tana cikin gidan ba ka ga yadda jini ke fita ta
hancinta ba".
Cikin firgici Alhaji ya ce. "Subhanallah, lallai zai yanke min
danyen hukunci, ki jira ni ina nan Ibrahin Taiwo Road,
amma gani
nan zuwa gidan yanzu"
Da farko Yusha'u shigewa daki ya yi saboda tsabar 'ki
fad'i, ya san lallai ya 6allo ruwa, amma bai san ta ina zai
tare shi ba, saboda girman kai shi dai ba zai ba ta hakuri
ba, to ai babu ma sararin ba ta hakurin dan ya fahimci
Rumaisa ta dauki lamarin da girma, yadda ta ke ambaton
innalillahi ririta jinin nan
kamar zata mayar da shi jikinta ya san ta zuzuta abin, ko
da yake dama ita da lamarin jini babu
dama. Ya sauya riga ya dauki mukullin mota tare da
niyyar yin 'kunar ba'kin waken zuwa ya kai ta asibiti,
amma kamar a mafarki sai ya ji muryar mahaifinsa a
cikin gidan cike da tsananin 6acin rai.
"Basirar Yusha'u ta toshe da yake tunanin sai ta hanyar
mutuwa kawai zai iya rabuwa da Rumaisa'u, idan ya
saketa wanene zai matsa masa sai ya zauna da ita.....?
Babu komai Hafsat shiga ki hado min kayanta. Cikin
sanda da tashin mukulli yana ta zabga da na sani.
Ko cikakken minti talatinba a yi ba ya ji sun fice, sai tashin
moticinsu ya ji.
Hafsat ta wuce Gandu da kayan Rumasa'u, Alhaji kuma ya
doshi asibiti da Rumaisa'i, dan tana ganin
abin da ta fara ce masa shi ne.
"Alhaji a kai ni asibiti, ha6o yana daya daga cikin abin da
ake gudarwa sickler".
Da muryar tausayi ya amsa mata.
"Na sani Rumaisa'u, yanzu za mu je asibiti, ki yi hakuri
don Allah, duk ni na janyo miki. Amma Allah
Ya sani na yi tsammanin na isa da Yusha'u, ashe shi bai
dauke ni mahaifi ba,
Ba karamin zafi lamarin nan ya yiwa Alhaji da Hajiya ba,
musamman kuma da suka sami zugar Hafsat wadda ke
kwance musu duk wani abu da ta sani
na muzgunawa da Yusha'u yake wa Rumasa'u har da
'karin gishiri.
Kwana biyu, uku Alhaji na zura idon zuwan Yusha'u

amma ya 'ki zuwa. Da farkon shi Alhaji ke 6oye hanyar da
za su hadu a kasuwa, amma da ya ga Yusha'u ma share
kunne kullum in ya kalli Rumaasa'u a gida sai ya ji takaici
ya sha'ke shi,
wannan ya sa ya bude hanyoyin da zasu hadu, amma
shiru har sati biyu.
Alhaji ya koma neman Yusha'u a waya, amma sai dai
wayar ta 'karaci burarinta Yusha'u bai daga ba.
Daga nan ne kuma Alhaji ya tabbatar Yusha'u ya shirya
nuna masa iyakarsa.
Wannan neman da Alhaji ke masa ne kuma 'kara 'kular
da shi.
Mugun son kansu yake gani, sun aura masa 'yar dangi
sun ce auren zobe ne babu shi babu wani auren , ko da
son wata zai kashe shi sannan wadda suka aura masa ba
ta cika macen da za a so ba,
mace kullum tana gado sai shegen kaifin harshe. A ta6ata
kuma cibi ya zamo 'kari, 'kila ma da gangan
ta fito da wannan jinin dan dai ya san shi dukan da ya yi
mata ba wani taka kara ya yi bare ya karya ba.
Yau ya je gidan su Sumoli ya dawo da 6acin ran takurar
ya fito, wadda Innarta ta ke masa. Ya dawo Alhaji ya ishe
da kira a waya, da haushi ya ci gaba da 'kume shi kawai
sai ya shirya fanshewa a kan Rumaisa'u. Karfe sha dayan
dare ya kira ta a waya. A tsorace ta dau wayar cikin
karkarwar murya ta gaishe shi. Ya amsa a gundure,
sannan ya 'kara 6ata murya ya ce.
"Wai ke zaman me kike a gida?"
Ta shiga numfarfashi ta kasa cewa da shi komai. Ya kara
nisawa cikin gadara ya ce. "Ya kamata ki san abin da zaki
fada musu su dawo
da ke dakinki, ni dai wallahi ba zan zo bikonki ba, malama
ba dan ke kadai aka halicce ni ba da zan
zauna bakin cikinki ya kashe ni ba. Kafin a sami namijin
da zai jure wannan jarabar laulayinki sai an
tara dubu, ni na jure dan me za a hana ni auro wadda
zata share min hawaye?
To kina jin dai abin da na ce, ba zan zo ba, in kin yi
dabarar da suka dawo da ke dakinki kanki za ki
taimaka, kina ganin dai yadda zawarcin zamanin nan ya
ke, bazawarar da ta shekara biyu ko uku a gida ta sami
miji sai an ba ta makin distinction balle ke mai dagawa
kabari hannu, mutum na ta abinci yana ta maganinki...."
Tun da ya faro cin zarafinsa ta ke hawaye, sai da ta ga
abin babu 'yan uwantaka ko sanayyya da arzi'ki sannan ta
tare shi tana kuka.
"Yaya Yusha'u da kana shaye-shaye sai in ce wadannan
maganganun a cikin maye kake min su,
ka manta ne idan na tashi daga matsayin matarka ni 'yar
uwanka ce, jininka?
Bari yi min barazana da saki da zawarci duk abin da
Ubangiji ya rubuto min sai ya same ni.

Da can na ta6a za6arwa kaina aurenka ne?
Na san ni nakasasasshiya ce. Duk wanda ya aure ni
alfarma kawai ya yi min, saboda haka na gode da
alfarmar d aka yi min a baya Yaya
Yusha'u, kuma a yanzu duk abin da yake ranka a kaina ka
zartar da shi kar ka damu da abin da zan
za6a ni amfane ni ko zai cutar da ni, ni duk abin da Allah
Ya za6a min zan yi biyayya a gare shi in gode. ..
.
Kuka ya hanani karisawa, ganin masoyi cikin wani hali
babu dadi...
Idan kuna so a kara yawan rubutu sai an kara yawan
comments da likes.
Dan Aunty.
GORAN DUMA (P 40)
.
.
A karshe ina son yi maka nasiha, ka daina ta'kama da
ciwona wanda ka la6e a bayansa kana cin mutuncina. Ka
san ina dauke da cikinka, gwaje- gwaje sun nuna mace
ce, Yaya Yusha'u babu tabbacin lafiyayya ce ko sickler,
Allah babu yadda bai iya ba, Yaya Yusha'u idan ta kasance
sickler wanne tanadi zaka yiwa aurenta?
Ka mayar da hankalinka ya kamara ka karrama dan wani
dan ko bayan ranka a karrama naka".
Ta sauke wayar cikin kuka, kuma ta kasheta gaba daya.
Kamar Alhaji ya san da faruwar haka a tsakaninsu, da
sanyin safiya ya aikawa Yusha'u sa'kon kar ta kwana
kamar haka.
""Ba alfarmar da na saba nema a wajenka zan nema ba,
lallai ina son ganinka yanzu kafin ka fita, na shirya kawo
'karshen matsalarka da Rumaisa'u a yau, in ka 'ki zuwa
zan iya yanke hukuncin da na za6awa kaina ko da kuwa
na kai ka kotu ne.""
Ba 'karamin kada Yusha'u wannan sakon ya yi ba, daga
ganin kalaman sa'kon ya san Alhaji ya yi fushi, fushi mai
tsanani dan haka sam bai yi tunanin gocewa ba.
Jikinsa babu nauyi ko wanka bai yi ba ya kintsa ya fice.
Tun daga gurin Hajiya ya fara ganin dauke wuta, kar6ar
da ta yi masa ko karen makota bai ta6a ganin ta yi masa
ita ba.
Ya riski Alhaji a falonsa yana lissafe-lissaffe da raskwana
yana shigarwa. Ya amsa sallamarsa fuska babu yabo babu
fallasa, suka gaisa a haka.
Yusha'u ya tattakure yana lalubo kalam ban hakuri, bai
gama kammala su ba ya fara shirin rero su, kafin sannan
ma har Alhaji ya 'kosa ya dago ya dube shi ya ce.
"To ranka ya dade ina jinka".
Ya muskuta zai rero abinda ya sa'ka da rawar murya.
"Alhaji don Allah.... a yi hakuri... wallahi..."
Alhaji ya yi saurin tattare fuska ya daga masa hannu.
"Ji nan Yusha'u, ba abin da na kiraka k yi ba ke nan, kar ka

dauke ni wani masoyin zuciya mana!
Haka kawai zan gayyatoka ka zo ka ba ni hakuri ni din
banza?"
Jikin Yusha'u ya 'kara daukar 6ari, zai yi magana Alhaji ya
tare shi.
"Yusha'u ban gayyyatoka dan mu yi tanki-in-tanka ba, ka
saurara min kar ka cika ni na sharara maka
mari ka zage kwanji ka rama, dan na san ba kyalewa zaka
yi ba, tunda babu Rumasa'u a gida wadda zaka koma ka
rama a kanta kamar yadda ka yi rannan".
Galala Yusha'u ya 'kame baki, ya san halin Alhaji tabbas
idan ya yi magana zai iya tafka masa marin,
idan ya yi kuma ya tabbatar da laifin da aka li'ka masa na
rama mari akan Rumaisa'u.
Kamar daga sama Alhaji ya ambata dalilin kiran.
"Za6i zan ba ka, sabon aurenka ko kuma zama da
Rumasa'u bana son dogon surutu, maza ka za6i daya ka
tashi ka ba ni guri".
Yusha'u ya ji maganar kamar a mafarki, zuciyarsa ta
dinga bugawa numfashinsa na kamar zai 'kwace, da
rawar murya ya ce.
"Duk ina sonsu Alhaji laifin Rumaisa'u ne... Na ce mata ta
daina ba ni abu da hannun hagu.... Na yi magana kuma ta
nemi zagina... ban san lokacin da na mareta ba wallahi....
Marinta kawai na yi...."
Takaici ya yi mugun 'kume Alhaji, ya tare shi cikin fushi.
"Kai Yusha'u duk ri'karka ka san na fi cikin za6in da na ba
ka mu kashe wannan maganar".
Yusha'u ya dinga juya takarda tsawon mintuna goma,
duk sa'kar da ya kamata ya yi ya kwatanta
masa zama da Rumaisa'u wanda ba ya tare da komai sai
kasawa da wulak'anci, sannan yana ganin ko ita din ya
za6a wasu wahalhalun dokokin za a kafa masa, har gara
in ya rabu da ita ko su Alhaji sun yi fushi za su sauko su
huce.
Ya daddage ya yi ta cizawa, amma ko sau daya bai hura
ba, ya dage ya rangadawa Rumaisau saki a takarda ya
ninke ya mi'kawa Alhaji.
Sai da kwalla ta cika idon Alhaji bayan ya ware ya tarar
da.
"Na yanke igiyar aurena daya da Rumaisa'u, idan ta haihu
ta sami miji ta yi aure".
Sai da Alhaji ya yi 'kokarin mayar da kwallarsa, sannan ya
dago ya dubi Yusha'u.
"Da ko 'yar taka tana haifa maka shi ta mi'ke maka
amaryarka zata shayar da shi?"
Yusha'u ya yi dira-dira ya ce.
"A'a Alhaji, ta shayar da shi sai mu yi jinga kamar yadda
musulunci ya tsara".
Alhaji ya kada kai ya ce.
"To da kyau, sai ka fara da jingar renon ciki kafin a kai ga
ta shayarwa, wannan zai fara ne daga yau,

ya kama daga abincinta zuwa maganinta. Ina fatan ka
fahimta?"
Yusha'u ya yi sororo dan ganin tsabacewar ta yi yawa, sai
ka ce wanda ba a san daga inda ya fito ba?
Bai gama shanye wannan mamakin ba Alhaji ya watso
masa wani.
"Ka je ka fara shirin aurenka, komai da ya kamata a kai ka
kawo za mu jagorance ka mu kai, abin da na san za mu
iya ke nan ni dai sisi ba zan iya taimakonka da shi ba,
wanda na yi maka na baya ma idan ba ka gode ba kana
iya dawo min da kayana.
Tashi ka bar min gida".
Zabu-zabu Yusha'u ya fito ko sallama bai yi wa Hajiya ba,
ya fice ya bar gidan.
Wuni Alhaji na nu'ku-nu'ku da sakin da Yusha'u ya yiwa
Rumaisa'u, ko Hajiya ya kasa sanarwa bare Rumasa'u illa
dai ya kira dan uwansa. Mahaifin Rumaisa'u ya sanar da
shi cikin kuka da nadama,
sai mahaifin Rumasa'u ne ya dinga ba shi hakuri yana
tuna masa ai kowanne bawa ba ya kaucewa kaddararsa, a
'karshe ya nemi a bar Rumaisa'u ta taho Abuja, ama
Alhaji ya nuna karaya da cewa.
"Kun ga na gaza ko?
Ku yafe min ba laifina ba ne wallahi...."
Ya 'kare maganarsa cikin hawaye.
Babu shirin mahaifin Rumaisa'u ya janye maganarsa.
"Sam ba haka nake nufii ba Yaya, amma dan hankalinka
ya kwanta na janye maganata, na bar maka Rumasa'u ka
yi duk abin da ka so a kanta, ai 'yarka ce ba tawa ba
Yaya".
Daga haka ya kashe wayar. Sai dare Alhaji ya sami
Rumasa'u da Hajiya da zancen, bayan doguwar nasiha
wadda ke nuna nadama da kwane-kwanen son fadae laifi
a karshe dai dole ya fada amma cikin neman afuwa.
"Ki gafarce ni Rumasa'u, na zaci alkhairi a aurenki da
Yusha'u, ban ta6a kawo sharri ba amma tawa na yi Allah
Ya yi tasa, na cutar da ke don Allah ki yafe min...
Yau Yusha'u ya nuna min iyakata ya rubuta miki saki daya
ya ba ni.... Ina rokon alfarmar kar ki yi nadamar
kasancewata uba gare ki..."
Numfashin Rumaisa'u ya so ya dauke saboda gigitar zafin
sakin da Yusha'u ya yi mata. Ba ta jin dadin auren
Yusha'u, amma ba ta6a hararowa kanta zai saketa ba,
sakin ya yi mata ciwo kusan
ta kwantana shi da mutuwa, sai dai wannan akwai
nutsuwa da son cusawa kai tawakalli, musamman
ta dalilin sanyayan kalaman Alhaji masu katse hanzari.
Ta isa gabansa cikin rauni da hawaye.
"Ka daina fadar haka Alhaji, babu bawan da ke iya
kaucewa 'kaddararsa, na dogara ga Allah, sakin da Yaya
Yusha'u ya yi min bai ta6a komai cikin darajoji
da kimarka ba Alhaji, sai ma 'kara su da ya yi.

Sannan ya 'kara min nutsuwa da yak'inin gata da
tsantsenin mutum ba ya katange shi daga 'kaddararsa...."
Ta mi'ke 'kafafunta na harhard'ewa ta bar falon zuciyarta
na wani irin zafi... Ina ma ta san inda mutuwa ta ke!
Tabbas da ta bi ta ta yafitota ta nuna mata kanta.
(Tashin Hankali!.... Masoyan Rumaisa'u na murnar
mutuwar aurenta. Ita kuma na cigiyar Mutuwa saboda
radadi da zafin sakin.....)
.
YA HADU DA SUMOLI
Lokacin da yake Ganin Bekin Iyayansa Da Kullamasa
Auran Ruma Dayake Ganin Gangancine Auren Mai Zurfin
Ilimi Yana Shago A Kantin Kwari Kyakkyawa Sumoli Fara
Tas Mai Tsawo Da Kiba Sunzo Sayen Kaya
ZANBAKU TARIHIN HADUWAR SU DA YUSHAU IN BRIEFLY
DANKU FAHIMTA*******
Suna Ta Hira Da Kawarta Indashikuma Yushau Yaketa
Aikinsa Kuma Yanasauraron Hirarsu Sumoli Tadubi
Kyallen Shaddar Dasuka Zo Siya Ajakarta Tafito Dawasu
Kananun Litattafi Waisu Text Message Guda Uku Wasu
Litattafaine Wadanda Matasa Masujin Sharafin Soyayya
Kan Zauna Su Rubuta Sakonnin Soyayya Daga Masoyi
Zuwa Masoyiya Kawarta Hadiza Naganin Littafin Tai
Kuwwa Ta Ce Kai Sumayya Wadannan Littafan Fa? Sumoli
Ta Saci Idon Yushau Tare Da Kallon Kudin Hannunsa
Sanna Ta Kifta Mata Ido Tana Mayarda Littafin A Jakarta
Wallahi Na Adduoine Najido Zanfara Allah Yakawo Miji
Nagari Yanzu Auren
Yazama Abin Tsoro Dole Ne mu dage Mukaiwa Ubangiji
Kuka Tai Hakan Dan Yushau Ne Kuma Hakika Har Ta
Shako Wuyansa Yadansaci Kallanta Kawarta Tace Oh
Hakane,yanzu Dan Kinaso Ki Gayamin Daga J,s 3 Kingama
Karatu?
Nasan Yayan Gidankufa Basawuce Aji Uku A Sakandiri
Wallahi Kuwa Yayyena Uku Duk A Haka Aka Aurar Dasu
Yayata Umma Ce Kawai Tasamu Miji Mai Shaawar Karatu
Ya Barta Ta Zarce A Gidanta Amma Babanmu Duk
Kwakwarki Ason Karatu Ba Zai Lamunta Ba Haka Sukaita
Basajar Zancensu Mahaifinki Ya Burgeni Sosai Nandai
Suka Kulla Soyayya Tsakaninsu,dukan Kayandasu Sumoli
Suka Dauka A Aljihun Yushau Tundaga Wannan Ranar
Yushau Yadaura Dambar Neman Sumoli,
Sumoli Su Biyar Ne Adakinsu Duka Mata Ne An Aurar Da
Sauran Saura Itakadai Mahaifinta Yafizuwa Kudu Daga
Arewa Kayan Gwari Yake Siyarwa Lokacinda Girma
Yakamashi Gashi Fitinar Matar Sa
Tatasa Shi Danhaka Ya Tattara Komatsansa Yakoma Kudu
Watan Yushau Biyu Suna Soyayya Da Sumoli Iyayata Suka
Matsamasa Ya Turo Hardai Yasaketa Adaren Ranar Duk
Yadda Ruma Taso Ta Basar Damaganar Sakinda Yaimata
Takasa Darar Ranar Saiyazamemata Tamkar Daren
Samun Labarin Rasuwar Auwal Indatake Tunani Lallai Da

Kyar Idan Rayuwa Zata Kara Budemata Shaf
Idan Rayuwa Zatakara Budemata Shafi Mai Haske Koda
Kuwa Za A Dan Gutsiro Kyallinsa Ne Daga
Shafi Irin Na Auwal Kilamashafi Masu Duhu Za A Yi Ta
Bude Mata Kukanta Na Abincikintane Waddata
Hakikance Irintane Wato Sikila Tunda Yai Sanadiyar Barin
Rabinda A Baya Wanda Shine Kila Zaizo A,S
Tausayin Abincikinta Wasa Wasa Ranar Nan Da Sanyin
Asuba Saida Alhji Ya Kwashi Ruma Zuwa
Asibiti Suna Zuwa Aka Basu Gado Wannan Yadawo Da
Ciwan Abinda Yushau Yai Danye A Zuciyar Mahaifansa Da
Surukansa Musamman Innar Ruma Wadda Karamcin
Mahaifin Yushau Kadai ke taka Mata Birkin Kiran Yushau A
Waya Taimasa Allah Ya Isanta
Malyria Tafara Cinkarfinta Ga Jininta Yafara Hawa,ciwan
Mukamiki Ya Motsa,nandanan Sai Ga Ruma A Hanyar
Lahira,wai Gidan Sauro Ma Kunrasa Arzikinsa Ruma?
Kwananta Uku A Asibiti Yushau Ya Cika Aljihu Da Kudi
Yadoshi Gidan Nasu,gidan Cike Da Kannensa Mata
Dukkansu Tare Da Hajiya Suna
Shiri Da Alama Shirin Fita Wani Guri Suke,yai murnar
Rashin Ganin Ruma Haryaji Haushi Indai Samun
Mijin dazai kula Da Ita Kamar Shi Abi
Ta Wajen Alhji Yafara Zuwa Wanda Yaimasa Irin Saukar
Dakewa Maroki Ga Mutumin dasam Baiyi
Niyyar Kyau Ta Ba,meyafaru?
Alhji Yatambayeshi Cikin Fuskar Shanu,yafito Da Kudi
Yamikawa Alhji Tare Da Koro Bayani Gasu Alhji Sai A Ciri
Wanda Za A Kai Kudin Aure,,a Ware Sadaki,akaimusu
Harnadanyi Wani Karanbani Nasanardasu Kunanantafe
Ranar Sati,.
tundakaika Haifemu Ko?
Kawai Tunkudar Keyarmu Zakai Ka Ce 'ya'yan Nan Zoku
Kai Kudinnan,
ayi Hakuri Alhji Dama Dan Sun Matsane Alhji Ya Kalleshi A
Kule,ammadai Yashanye Bacin Ransa Ya Ajiye A Gefe
Yadau Wayar Sa Kan
Tebur Yana Latsawa To A Fita A Siyo Min Kati Zansa A
Waya Akira Yanuwa Masu Kai Kudin Auren Suzo
Sukai,mamaki Da Mugun Takaici Suka Gallabi Zuciyar
Yushau Yaje Mota Yadauko Katin Dari Hudu
Yakawo Ma Alhji Fuskar Alhji Ba Walwala Za A Raba Kudin
Akai Rabi Hakane?
Daga Baya Kuma Akai Sadaki Ko?Alhji Baijira Cewar Sa Ba
Ya Ce To Ranar Asabar Din Zakazo Kakaisu Ko Kuma
Kudin Ma Zaka Bayar Na Ara Mota A Zuba?
Rannan Naimaka Maganar Daukan Nauyin Rainon Cikin
Ruma Alhji Ya Ce Rannan Naimaka Maganar Jinyar Cikin
Ruma Kasameta Kunyi Maganar?
Ban Ganta Ba Ranar Har Na Bar Gidannan Amma Yau
Zansameta To Alhji Yafada Cikin Halin Ko In Kula Ya Ce
Tadanyi Jinya Sosai Cikin Kwana Biyun Nan Wanda

Nauyin
Cikim Bakin Cikinka Dakuma Guggubin Wahalardata Taho
Da Ita Daga Gidanka Suka Hadu Suka Jazamata
Talasarmin Kudi Sosai Dan Saidatasha Ledar Jini Biyu
Saboda Malyria Takamata Da Zafin Kasansu Sickle Malyria
Ba Karamin Hatsari Ba Ce Atare Dasu Ince Ko Arzikin Ne
Ko Na Maganin
Sauro Batasamu A Gidanka Ba Yushau Yakasa Magana
Zuciyar Sa Kamar Ta Fashe Saboda Takaici
Ta Ci Kudi Sama Da Dubu Hamsin Don Mundanje Asibiti
Mai Kyau Ne Idankafita Ka Karbi Rasidai Gurin Hajiya
Kaduba Dan Allah Inasan Kudina Gobe Alhji Nasane
Kallan Mamaki Yushau Yakemai Danhaka Yafice Yana
Cewa Kakokarta Kuyi Jinyar Nan Saura Kuma Kasanya
Zalunci Ciki In Hakan Ta Faru Tozan Fitar Da Ita A
Alamarin Ni In Shiga A
Fusace Ya Fice Yana Kunkuni A Zuciyar Sa Allah Bazai
Hanani Yadda Zanyiba Yakarade Gidan Bai Ga Ruma
Danhaka Saiyadawo Falo Ya Taddasu Suna Shirinfita
Ransa A Baceyake Harma Yanafakan
Idan Hajiya Yana Hararar Hafsat Wanda Ita Ma Take
Murguda Masa Baki To Malam Fitafa Zamui
Hajiyatafadama Cikin

2 Comments On GORAN DUMA
avatar
jannat

1 year ago

Reply

08062236094

avatar
jannat

1 year ago

Reply

08062236094

Please Login or Register in order to submit comment