Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zai iya kusantar da shi dan rahamarsa a
gare mu da ni'imarsa. Zai iya tankwa6ar da shi
dan isarSa a kanmu da zartar da abin da ba mu
ba mu san da shi ba, dan haka duk abin da ka ji
na fada kar ka danganta shi da kanka Auwal,
danganta shi ga son yiwa ubangiji biyayya da
faranta ran Abba, a wani hannun kuma da 'kin
biye zuciya sakokinta... Ina sonka Auwal".
Ya kai 'koluluwan rauni da tausayin Rumaisa'u
wanda ya 'kara masa miliyoyin 'kaunarta,
ma'kogwaron ya cunkushe da su, shi yasa duk
yadda ya yi 'kokarin ya ce wani abu ya kasa,
kawai sai ya dauki takardarsa ya nemi hanyar
fita.
Ba ta takura kanta da binsa ko kiransa ba, kawai
sai ta raka shi da mafi sau'ki cikin abin da zata
yi, wato binsa da kallo har ya fice, sannan ta
durkushe ta fara kuka mai dalilin.
Kwana biyu babu labarin Auwal, babu wayoyinsa.
Ta yi 'kokarin kira duk a kashe. Ta yi tunani ta yi
issafin duk ta kasa cankar dalilin 6uyansa ko
kuma abin da ya 6oye shi, duk canki-cankin da ta
ji yana neman tafiya da numfashinta.
Auwal ya janye neman aurenta, hasashen da ke

kusan tafiya da numfashinta. Auwal ba shi da
lafiya, zargin da yake tilasta mata son lallai ta
san halin da yake ciki.
Kwana na uku ya kama alhamis, ba ta yi shawara
da kowa ba ta wanke 'kafa da yammaci ta dauki
Hafsat suka tafi Na'ibawa gidan su Auwalu.
Tun a hanya Hafsat ke tambayarta abin da ke
faruwa, musamman ganin yadda hankalinta ya yi
matu'kar tashi ba kamar a lokuta baya ba, inda
ko ya shafe kwanaki bai zo ba bata damuwa.
Rumasa'u ba ta 6oye mata komai ba ta zayyana
mata yadda suka yi.
Hafsat ta ce, "Ina ganin gara mu fadawa Inna
gaskiyar lamari idan muka je".
Rumasa'u ta dafe 'kirji ta ce, "Wai rufa min asiri,
kada a ga za'kewata da wawancina."
"Ba wawanci ba ne, Rumasa'u, yarda ce da nuna
bu'katuwar al'amarin nan."
Kallo daya Innar Auwal ta yiwa Rumaisa'u ta
gane ta, duk da ba su ta6a haduwa ba. Amma ta
yi mata farin sani a hotuna dan haka ta sauke su
da rawar jiki kamar zata goya su. Kasala da
kunyar da Rumasa'u ke bayyanawa ya sa Innar
Auwal jin wani irin tausayinta ya ishe ta.
Ta zauna suka gaisa cikin girmama juna.
"Duk manyan naku lafiya ko?"
Inji Innar Auwal, Hafsat ta amsa
"Lafiya kalau".
Rumaisa'u kai na 'kasa. Suka dauki shiru kowa
da abin da zuciyarsa ke sa'kawa, Rumasa'u na
jin tsanar kanta da kankambar zuwa gidan
surukai, surukan ma wanda auren d'an nasu da
damuwa da 'kila wa'kala, amma 'kaunar dan nasu
da sanin halin da yake ciki ya kore nadamarta
mai taurin kan da ta 'ki 'karuwa, sai ta tsaya
suke ta damun zuciyarta tare. Yanzu abin da ta
fi d'ko shi ne, ta ina labarin Auwal zai 6ullo
mata?
Can Inna ta nisa ta ce.
"Ku sha lemon don Allah, Nuraddin nake jira ya
shigo ya dubo shi ko ya farka, yanzu da
abokansa suka zo duba shi suka ce yana barci".
Wani irin tashin hankali ya bayyana a fuskar
Rumasa'u. Ta dago ido ta dubi Inna, amma ta
kasa cewa komai sai bakinta ne ya ke rawa.
Hafsat ce ta yi mata abin da ta ke son yi cikin
jimami da sanyin murya, ta ce.
"Ayya ba shi da lafiya?"
Inna ta jinjina kai, ta ce.
"Ba shi da lafiya, na yi tsammanin ma dubiyarsa
kuka zo, kwana biyu ke nan yana fama da wani
matsanancin ciwon kai".

Rumaa'u a rikice ta ke amma ba ta fasa
tambayar Inna ba
"Inna dama yana yin irinsa?"
Cikin nuna jimami Inna ta ce.
"Dama yana da yawan ciwon kai, tun yana
'karami ya yi san'karau shikenan yawan ciwon
kai ke bibiyarsa, sai dai bai taha tsananta masa
irin wannan lokacin ba, amma yau da sau'ki ba
kamar jiya ba. Yau har ya ci abinci an yi hira da
shi, ftowar mu ke nan bacci ya dauke shi".
Rumaisa'u ta sauke numfashi cike da dukan
zuciya, duniyar gaba daya ta yi mata 'kunci ba ta
san lokacin da kukan zucinta ya fito fili ba, had'e
da hawaye har da shessheka. Hafsat da Inna
suka bar yiwa juna jajen rashin lafiyar suka koma
rarrashinta.
Jikin Inna na 6ari ta mi'ke ta fita tana cewa.
"Bari na sanar masa da kaina, ki je ki ganshi, jiki
fa ya yi kyau".
Bayan Inna ta fita Hafsat ta ci gaba da tausar
Rumasa'u, yayin da Rumaisa ta d'ago da
hawayen ta ce.
"Hafsat ni kadai na san yadda na ke jin Auwal a
kirjina, duk wani abu na illah ko mai nuna
salwantarwa a Auwal ba na iya jure masa, ina
son Auwal, kawai shi ne abin da na sani".
Hafsat tsakaninta da Allah ta ce.
"Yadda na ke addu'ar Allah ya bar ni da Sani,
haka na ke addu'ar Ya barki da Auwal ko ma
fiye, don na tabbatar kun yi dacewar da abokan
burmi irinku su ke wahala".
Shigowar Inna ya tsayar da maganar Hafsat, ta
ce.
"Yauwa ku 'karasa, ya farka na same shi yana sa
wayarsa caji".
Rumasa'u ta riga tashi suka fita cikin jagorancin
Inna, har dakin Auwal, sannan ta yo baya....
.
Dan AuntyGORAN DUMA 17
.
.
"Na yi zaton kin manta da ni".
Da kalmar da Auwal ya tare ta ke nan duk da ya
ga hankalinta a hargitse, sai kallon sa ta ke
kamar in ta dauke ido daga kansa zai 6ace mata
ne, saboda haka har ta zauna ba ta cikin
hayyacinta, ta dai sami kanta da amsa masa.
"Dan na yi maka wanne laifi kake ganin zan
manta da kai Auwal?"
Dole ya basar da zancen kasancewar da Hafsat a
wajen ba ya son su dire zancen da matsalarsu
zata bayyana kanta.

"Hafsat yau ku ne a gidanmu?"
Abin da ya ce ke nan, Hafsat ta nisa idonta a kan
Rumasa'u ta ce.
"Ai dole ce mai sa wa a kwana a ido Auwal,
kamar Rumaisa'u ta san ba ka da lafiya kwana
biyun nan in na ce maka ba ta cikin hayyacinta
kar ka musa".
Ya yi zuru yana kallon Rumasa'u da idanuwansa
masu aika mata wasu sa'konni masu dad'i da
marasa dad'i, da ta kasa jurewa kallon sai kawai
ta yi kasa da ido 'kwallah ta cika ido taf!
Ya ri'ke kai saboda taruwar hawaye, take ya ji
ciwon kansa ya dawo sabo dal, ya fara kokawar
ri'ko juriya tana silalewa har ya yi nasarar
dam'karta, cikin son nuna jarumta ya ce.
"Yi ha'kuri Rumasa'u...."
Ta tare shi a raunane.
"Ya ya jikin?"
Jikinsa a sanyaye ya amsa.
"Na ji sau'ki ai... sai godiyar Ubangiji, kin san rai
da jini".
Ta kada kai tare da nisawa dukkanin hankalinta
na kansa.
"Anya Auwal ba damuwa ka sa wa ranka ba har
ta janyo maka ciwon kai? Inna ta tabbatar min
ba ka ta6a ciwon kai kamar haka ba, ka ga kuwa
yadda ka rame Auwal?"
Ya koma kujera ya yi rigingine ya dafe kai da
hannun hagu sannan ya dafe 'kirjinsa da hannun
dama saboda yadda ya ji shi ma ya dauki ciwon
nan take fuskarsa na 'kokarin 6oye ciwonsa ya
ce mata.
"Sai da dalili Ubangiji zai jarrabi abin halitta
Rumasa'u? Ki taya ni mu yi fatan zama kaffara
kawai dole ya yi 'kokarin tashi zaune ya dubeta
murya a sanyaye ya ce.
"Rumasa'u idan ba ki dalafiya haka nake sanya
ki gaba mu yi ta kuka, ko ciwona ne ya fi na
kowa?"
Ta yi saurin girgiza kai.
"Ina jin abubuwa da yawa marasa dad'i a raina
Auwal duk suna nuna min yadda ba zasu iya jure
rashinka ba".
Ya yi mata inkiya da Hafsat a wajen abin da ya
fahimta matsalarsu ce a maganarta, saboda haka
ya goce ta da cewa..
"Da ciwo ya san in da rai ya ke Rumasa'u ai da
tuni kin tsufa a can, rayuwa da mutuwa duk Allah
ne, kuma da yawan abubuwa na faruwa ne ba
yadda mutum ya zace su ba, ni yanzu so nake ki
kwantar da hankalinki mu yi hirarmu mu fanshe
kwana biyun da muka rasa, kinga sai ta zame

mana ta tarihi ko? Ina jin tunda muka had'u ba
mu ta6a kwana uku ba mu ga juna ba".
Ya 'kare maganarsa ne da dariya sai Hafsat ce
ta taya shi, ta kalli Rumaisa'u taga fuskata a
cunkushe. Tunanin halin da take ciki na rashin
lafiyarsa da 'kila wa 'kalan aurensu, ba ta ga
wani abu da zai ba ta dariya ba.
Fahimtar hakan da Auwal ya yi yasa ya dinga
daurewa yana ta tsaokano ta da hira, har saida
ya ga abin ya faskara sannan ya dubi Hafsat ya
ce.
"Hafsat don Allah ki ba mu minti biyar akwai
wata wuta d ana hura nake son kashe ta".
Hafsat ta mi'ke tana dariya ta ce.
"Ni ma na yi niyyar hakan cikin raina, ina da
bukatar Rumasa'u ta sami nutsuwa."
Ta wuce Auwal bin ta ya yi da cewa.
"Yauwa Gimbiyar Sani, Allah Ya barku tare".
Hafsat na fita ya baro kujerar da yake ya zo
gabanta ya zauna cikin raunin murya ya ce.
"Fad'a min abin da ya fi damunki yanzu na
wanke miki shi Rumasa'u, idan dai ciwona ne
aikin ga na ji sauki ko?"
Ta goge hawayenta sannan ta sauko daga
kujerar duk suka zauna a kafet suna fuskantar
juna, tana ta faman goge hawaye, sannan da
kyar ta 'ko'karta ta ce.
Me yasa ka kashe wayarka?"
Ya 'kura mata ido kawai ya kasa cewa komai har
ta kuma dorawa ba tare da ta dube shi ba.
"Ya ya kuka yi da Abba?"
Kai tsaye cikin dakewa ya amsa mata.
"Wannan rashin lafiyar tawa ta sa ba mu zauna
mun tattauna ba, amma dai na nuna masa
sakamakon gwajin".
"Me ka fahimta a tare da shi?"
Kai tsaye ya amsa mata "Fuskarsa ba zata iya
bayyyana abin d ke fake ba, duk yada zai nuna
'karfi ko hangen nesansa ba zai sauya ba ko ya
yi abin da Ubangiji bai nufa ba, zai sauya ba ko
ya yi abin da Ubangiji bai nufa ba, na ba shi
sakamako na kuma fad'a masaain da ke raina, ke
ce farin cikina dan kin haifi 'ya'ya irinki na shirya
zan tanada su a ha'kuiri na da juriyata da kuma
yin tattalin aljihu iyakar iyawata ina da wannan
burin a raina, na niyyace shi duk wani abu
sa6anin haka idan haka idan ya faru haka
Ubangiji Ya 'kaddara mana, ke ma ki yi min
uzirinsa".
Rumaisa'u ta yi sakato tana kallonsa, saboda har
yanzu ba ta tsinci abin da ya kamata ya faranta
mata rai cikin maganarsa ba, idan al'kawuran

sonta d akyautata mata ita da 'ya'yanta ne tun
ta saba jinsu a bakinsa, tana kuma da ya'kinin
daga zuciyarsa suke tasowa saboda haka yanzu
abin da ya dame ta shi ne ya ya za su yi su kai
ga cimma burin kasancewa tare bare har ta jefa
wad'ancan al'kawaran nasa cikin abubuwan da ta
ke jiran kasancewarsu a rayuwa?
"Zan tafi".
Abin da ta iya ce masa ke nan cikin hawaye. Ya
d'an runtse ido cikin girgiza kai ya ce.
"Yanzu sai ki tafi ki bar ni Rumaisa?"
Ta mi'ke tana ci gaba da goge hawayenta ta ce.
"Wata'kila gobe in dawo idan ba ka murmure ba,
sai dai ka ba wa Inna ha'kuri wata 'kila ta ga
rashin kunya ta da za'kewa ta, ni ma haka na
tsinci kaina, in dai abu ba haramun ba ne, don
sakaf nake ganinsa a fuskarka".
Shi ma ya mi'ke yana dariya ya ce.
"Inna za ta fahimce ki Rumaisa, kin ta6a zuwa
gidanta ban da yau? In Allah Ya so ma goben ni
zan zo ba ke za ki zo ba, ai idanuna sun ganki
sun yi kwari".
Ita ma ta yi dariya ta yi ajiyar zuciya.
"Hum...!" Alamar har yanzu ba ta ware ba, suka
jima suna kallon juna, sannan ta kad'a kai cikin
hawaye ta wuce, jirin da yake ji ya hana shi yi
mata ko taku daya da sunan rakiya, daga nan
tsayen har ta je bakin 'kofa sannan da murya
'kasa-'kasa ya ce.
"Rumaisa'u... Ina sonki, kar ki manta da
wannan".
Ta tsaya tare da juyowa suka yiwa juna
murmushi, sannan ta fice, shi kuma ya haye
kujera a gajiye yana lumshe ido, yana son
Rumaisa'u tana sonsa, har yau bai ta6a yanke
'kaunar za su gaza kai wa ga burinsu ba.
Ta sami Hafsat da Inna suna ta hira ko a fuska
babu wanda ya nuna mata wani abu. Ta zauna a
sanyaye cikin hawaye, wannan ya sa kowa ya yi
dif a dakin tsawon kusan mintuna biyu, sai can
Hafsat tayi ajiyar zuciya ta nisa ta ce.
"Inna ashe tun tuni Auwal bai sanar da ku cewa
Rumaisa'u sickler ba ce ko? Tuni kuma ta
shawarce shi ya sanar da ku, amma bai yi hakan
ba har sai da kuka ji a gari. Tabbas ba mu
kyauta har da ni, amma don Allah Inna ku yi
mana uziri, sun fiye son kansu ne shi yasa su ke
juyawa matsaloli fuska...
Auwal da Rumaisa'u sun fara son juna da radin
kansu amma yanzu ga shi sun ya gaza rabuwa.
Inna don Allah ki fahimtar da Abba kar ya raba
su..

Zaku iya neman wata mafitar ta samarwa Auwal
wasu 'ya'ya ba nata ba...
Na tabbata za su iya lamuntar haka, raba sun ne
kawai muke jinsa wani abu da na ha'ki'kance
numfashinsu ya gaza dauka..."
.
.
Dan Aunty.GORAN DUMA 18
.
.
Rumaisa ta yi sororo hawaye na kwarara daga
idanunta. Wadannan kalamai ne a bunne cikin
ruhinta, amma baki ya gaza furta su. Inna ta dubi
Rumaisa'u da ke shesshekar kuka. Inna ta yi dif
damuwar duniyar nan ta bayyana a fuskarsta, duk
da tuni ta san da sha'kuwa a tsakaninsu raba su
abu ne mai wahala wanda ko ita ba ta mafarkin
haka duk da dangar da ta ke hangowa iyalansu a
gaba, a yau sun ba ta tausayi su duka har ta fara
jin sallamawa cikin ranta. Cikin 'karfin gwiwarta
ta ce.
"Ku manta wannan maganar, iyakacin Abba
fad'ar da kuma nuna yun'kurin da zai iya ba dan
nuna 'kiyayya ba, sai don gujewa wahalhalu a
gaba.
Amma komai ai sai Allah Ya kasantar 'yar nan,
ko shi kansa na san yana shakkar ta inda zai
kwaso ya hana ko ku aure, auren da ya rage
kwanan wata guda da 'yan lamarinmu ga Allah,
Allah Ya tabbatar mana da alkhairansa kin ji? Ni
ban so ma ya sanar da ke ba wallahi".
Yanzu hankalin Rumaisa'u ya kwanta ta kuma
sami nutsuwa a cikin ranta, har ta saki wani
raunannan murmushi. Suka yi shiru ba wanda ya
iya furta wani. A 'karshe sai sallama suka yi da
Inna suka nufi gida.
Mahaifin Auwal na tare da Innar Auwal bayan
dawowarsa da dare yana cin abinci ya ce mata.
"Ya ya jikin danki?"
Ta yi dariya ta ce.
"Wai yaya jikin danki, to ya sami sauki har ya je
masallaci sallar isha'i".
Ya ce, "Ko kuma ya tafi zance ba".
Ta yi saurin girgiza kai.
"Ba na tsammanin hakan,dan juria kawai na
hanga a idonsa, ciwon kan nan yana matsaya
masa, ka je wajen likitan da ka ce zaka je neman
'karin bayani a kan auren nasa?"
Cikin fuskar jimami ya ce.
"Na je, labarin babu dad'i Asma'u. Likita ya
tabbatar min mafi rinjiyaen 'ya'yan da zasu iya
haifa da kashei 70% za su zamo sikila ne, sai dai

wani hukuncin Ubangiji. Amma duk da haka dan
sabar son kai ya ke shawartata kar a hana su
aure. Yanzu tsakani da Allah hana su aure ba
jihadi ba ne? Su a wahale 'ya'yan da za su haifa
a wahale? Mene ne aibun dan ya auri mai lafiya
ita ma ta nemo wand aba zasu haifi 'ya'ya masu
cuta ba?"
Inna ta sauke numfashi cikin alhini ta ce.
"Ka bar su kawai Alhaji, yaran nan sun fara ba ni
tausayi, ai dazu ta zo duba shi, in ka ga
yanayinta sai ka tausaya mata, na tabbatar
yadda ya damu da ita haka ta damu da shi. Nan
gurin ta zaune min tana neman in ro'ka ka kar ka
raba su, har tana bayar da 'kofar yana iya auren
wata da zata haifar masa lafiyayyun 'ya'ya...
Yarinyar ta ba ni tausayi wallahi sannan ina
tsoron makomar da za su fad'a idan aka raba su,
dan ni ina shakar babu taimakon wannan
jumurd'ar cikin tsanantar ciwon kansa, ka san
yawan tunani cikin damuwa babu abin da ba ya
haifarwa".
Abban ya jima cikin jan numfashi, sannan ya
hadiye abin da ya tara, ya cigaba da cin
abincinsa, har ya kammala can ya ji motsin
shigowar Auwal, saboda haka ya kira shi a waya.
Ya shigo idonsa zuru-zuru saboda rama, a yanzu
haka ma da 'kyar yake sauke numfashi saboda
azabar ciwon kai. Ya nemi guri ya zauna cikin
sanyin murya ya gaishe su.
Mahaifin nasa ya zura masa ido tsawon wani
lokaci yana kallonsa cikin tausayawa a zuci,
sannan ya yi gyran murya ya ce.
"Auwal tuni na yi maka shaidar tawakkali, me
yake son sauya ka har ka dami kanka cikin abin
da ban isa in sa ba bare in hana?"
Auwal ya yi masa shiru yana masa kallon rashin
fahimta, saboda haka mahaifin nasa ya dora.
"Fadata fadar Allah ce dan na kawo ra'ayina
akan aurenka zaka dinga neman kashe kanka
Auwal?"
A sanyaye ya ce masa.
"Me na yi Abba?"
Abban ya nuna Innar Auwal din ya ce.
"Ga ta nan, yanzu nan ta gama zargin shigata
lamarin aurenka ke jaza maka ciwon kai. Ni ma
na gaskgatata, ai duk yadda kake ciwon kai ba
ka ta6a fita hayyacinka irin haka ba".
Auwal ya 'kokarta ya yi murmushi, ya ce.
"Wallahi ba haka ba ne Abba, hankalina a kwance
yake da ina da ya'kinin in dai ni mijin Rumaisa'u
ne, babu abin da zai hana ni aurenta, ko ina da
damuwa ba zata wuce na tausayinta saboda

rauninta na mace da kuma lalurarta ba, wanda
wannan zai raunana zuciyarta ya iya yi mata illa.
Ina kuma cike da tausayinta idan ban zamo
mijinta ba yadda na ga ana gudun aurenta, ina
tsoron mata auren wanda zai kasa kyautata mata
da kyautata rayuwarta... Gaba daya damuwata
akan yadda Rumaisa'u zata samu rayuwarta
ne.... Na san kuma wannan bai isa dalilin jaza
min lalurar da Allah bai gadar min ba, saboda
haka ku kyautata zato a gare ni, ku cika ni da
addu'arku ta fatan alkhairi, har kullum ina
alfahari da kasancewar iyayena. Ni addu'arku
kawai nake bu'kata da cire zarge-zarge a cikin
jarrabawar da Ubangijina ke min".
Su duka jikinsu ya yi sanyi, kaunar Auwal ta 'kara
mamaye zu'katansu, Auwal dan halak ne wanda
akwai wahala ka ji sharri ya fito bakinsa, duk
yadda kake jin abu mummuna ne in ya gifta shi
ba zaka ji raknsa ba, kuma ba zai sauya masa
manufa ta son zuciya ba, mutum ne shi mai
jarumtar mayar da lamari ga Ubangiji.
"Allah Ya yi maka albarka, Ya rabaka da duniya
lafiya ka ki".
Innarsa ta riga mahaifinsa magana, tana direwa
shi ma mahaifin nasa ya dora da cewa.
"Allah Ya kyautata rayuwarka duniya da lahira
Auwal, Ya rabaka da 'kuncin duniya da lahira, Ya
'kara fadada 'kirjinka da halayen kwarai, da son
Allah da ManzonSa. Ta shi ka je, Allah Ya ba ka
lafiya Ya hore maka dukkan alkhairan da kake
ha'ko".
Ya dan dakata yana musu godiya, sannan ya
tashi ya fita cike da dokin kiran Rumasa'u a
waya ya ba ta albishir, dan ma kansa na mats
amasa da ciwo saboda haka ya fara shan
magani, sannan ya kishingid'a na wasu mintuna
wai ko kan nasa zai dan sassauta ciwo, amma da
hakan ba ta samu ba, sai ya kira wayarta a haka,
sai dai kash! Wayarta a kashe ta ke, amma da
yake ya 'kagu da jin muryarta haka ya yi ta
gwadawa har bai san adadi ba.
***
Washegari da hantsi 'karfe goma da minti hamsin
Rumaisa'u da Hafsat da Hajiya suna tare a
falonta suna hira, Rumasa'u dai ta kasa
hankalinta fiye da dari ma idan ana kasawa, a
hirarsu a tunanin lafiyar Auwal, aurensu,
'ya'yansu, da kuma wayarta da duk bayan minti
biyar sai ta kira wayar Auwal din, ta yi ta faman
rurinta bai daga ba.
Tun asuba ta ke nemansa a waya bayan ta
kunna wayarta ta tarar da 6oice mail na ya kirata

kusan ashirin, tun sannan ta ke gwada kiran
wayarsa har kawo wannan lokacin da 'kila in ya
zo zai tarar da 100 missed calls. Babu itin
tunanin da ba ta yi ba, ya saka wayar a silent, ko
kuma jikinsa ne ya matsa masa, sai dai wata
zuciyar tata na kore wadannan hasashen da
wasu hujjojin, su ne.
Idan jikinsa ne ya matsa masa, ina wadanda ke
tare da shi da ba za su daga wayarta ba?
Da wadannan dalilai ta dogara ta kasa cira 'kafa
dan nemo wani hasashen, kuma gabanta ya
dinga 'kuntata zuciyarta.
Haka ta ke zaune cikinsu tana yake da faman
kiran wayar Auwal, har ma lokacin da Hajiya ta
dubi agogo ta sauke numfashi ta ce.
"Oh ni 'yan nan kawaici ne fa ya fara 'karewa,
Alhaji tun fita sallar asuba bai shigo ba, Yayanku
ma bai shigo cin abinci ba, Murabak kuma da
shirme na tambaye shi ya tsaya min shirme, wai
abokinsa ya bi suka fita".
Rumasa'u da Hafsat suka yi saurin duban agogo,
Hafsat ta riga magana da cewa.
"Kin kira shi a waya kuma?"
Hajiya ta ce, "Yo ai a gida ya bar wayoyin na
fada miki tun sallar asuba".
Cikin alhini Rumasa'u ta ce.
"Wani lokacin wayar ma ai hoto, kun ga tun safe
nake neman wayar Auwal tana shiga amma ba
amsa..."
.
Jama'a ku bani shawara, Ina shirin shiga neman auren
Ruma tunda naga da Auwal kamar da wuya kuma gashi
jini na A.A ne, daman na jima da jin son ta har cikin xucia
ta, gudun kada na raba kauna da Auwal ne na danne
xuciar, amma yanxu abun ya xo min har wuya .
Ko ya kuka gani?
Lol.
.
Dan AuntyGORAN DUMA 19
.
.
Kafin ta rufe baki sai ga Alhaji ya yi sallama ya
shigo fuskarsa na kokawar 6oye sa'konnin tashin
hankali iri-iri, komai nasa a birkice ya ke, sai dai
akwai alamun yana tilasta kansa gayyato
nutsuwa.
Duk suka yi masa barka da zuwa, Hajiya ta dora
da tambayarsa cikin kulawa.
"Alhaji lafiya kuwa?"
Ya wuce zuwa ciki yana cewa.
"Lafiya mana, me kika gani?"
Ta bishi cikin sauri suka shige falonsa a tare.

Ya nemi kujera ya zauna cikin dafe kai hannu
biyu. Nan take jikin Hajiya ya dauki 6ari ita ma ta
silale kujera ta zauna tana sakin numfashi cikin
sauri ba ta katsi hanzarin shirinsa ba, saboda
haka ta raka shi suka yi tare".
Tsawon wasu mintuna, sannan ya mi'ke ya je ya
murzawa 'kofa mukulli sannan ya dawo cikin
kasala, ya zauna ya dubi Hajiya ya ce.
"Allah ne Ya yiwa yaron nan Auwalu rasuwa!"
Tsawon wasu mintuna, sannan ya mi'ke ya je ya
murzawa 'kofa mukulli sannan ya dawo cikin
kasala, ya zauna ya dubi Hajiya ya ce.
"Allah ne Ya yiwa yaron nan Auwalu rasuwa!".
Hajiya ta dauke numfashi tana dubansa.
"Alhaji wanne Auwalun?"
Ya amsa mata yana kallonta.
"Auwalun Rumaisa'u".
Sai ga Hajiya a tsaye cikin wani matsanancin
firgici, sai dai ta had'a shi da fadin.
"Innalilahi wa'inna ilaihi raji'un, Alhaji hatsari ya
yi, dama ba shi da lafiya?"
Alhaji ya yi zuru yana kallonta tsawon fiye da
minti daya, ita kuma tana ta faman kai wa da
komowa tana ambaton innalilli wa inna ilaihi
raji'un har sai da ya fahimci ta kai adadjin da ya
kamata ta nemi wani abin, sannan ya tare ta.
"Zauna mana, wannan muryar da kike son ki
daga mana zata 6allo mana ruwa".
Ta koma ta zauna amma kuka mai keta zuciya
ya bijiro mata, sai dai ta hana shi fitowa ya sake.
"Alhaji ba shi da lafiya ne?"
A sanyaye Alhaji Ya amsa mata.
"Wai Hajiya sai mutum ya yi cuta Allah ke kar6ar
ransa? Ji nake lokacin mutum na cika yake
komawa ga Ubangijinsa? Irin wannan tambayoyin
ba su da wani hurumi tunda ba za su ta6a dawo
da wanda ya tafi ba tare da cuta ba".
Hajiya ta ci gaba da kuka cikin jero kalmomin
yabo tare da kururuta halayen Auwal na kwarai,
tana had'awa da nemo masa rahamar ubanhiji.
Tsawon wani lokaci Alhaji ya yi dif cikin tsabar
alhini, har sai da ya sami ga6ar abin cewa da ta
fara sambatun halin da Rumasa'u zata shiga.
Alhaji ya sauke numfashi ya ce.
"A halin yanz abin da ya fi zafafa zuciyata ke
nan, ko bayan dawowarmu ma'kabarta duk san
da mahaifinsa ya dube ni cikin kuka ya ke
maimaita min.
Rumaisa'u ta yi rashin masoyi... duk wanda zai yi
kukan rashinsa bayanta zai bi... maganata ta
'karshe da shi a kanta ne, inda yake ce
min...idan ina tare da damuwa ba zata wuce na

tausayinta saboda rauninta na mace, da kuma
lalurarta ba. Wanda wannan zai iya raunana
zuciyarta ya iyayi mata illa, ina kuma cike da
tausayinta idan ban zamo mijinta ba yadda na ga
ana gudun aurenta... Ina tsoron mata auren
wanda zai kasa kyautata mata ya kyautatawa
rayuwarta... Gaba dayan damuwata akan yadda
Rumasa'u zata sami rayuwarta ne..."
Hajiya ta 'kara fashewa da kuka ta ce.
"Yanzu zancen da nake maka tun safe ta ke
neman wayarsa, in ka ga yadda hankalinta yake
tashe sai ka rantse ta sami labarin rasuwar tasa
ne..."
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un".
Alhaji ya fad'a cikin dafe kai, sannan ya dago ya
dubi Hajiya ya ce.
"Yanzu yaya za mu yi?"
Hajiya ta ware hannu cikin kuka.
"Ban sani ba Alhaji".
Falon ya 'kara daukar shiru, ya mi'ke ya shige
wanka, har ya fito Hajiya na zaune gurin tana
faman sharar hawaye, shi kansa ya rasa da
kalmar da zai ce ta yi hakuri har ya kintsa ya zo
ya kuma zauna wa.
Falon ya 'kara daukar shiru, ya mi'ke ya shige
wanka, har ya fito Hajiya na zaune gurin tana
faman sharar hawaye, shi kana ya rsa da kalmar
da zai ce ta yi hakuri har ya kintsa ya zo ya
kuma zauna.
"Ki bar kukan nan haka, mu taru mu samo wa
yarinyar nan mafita, ta ina za a shero mata
wannan mummunan labarin? Ina tsoron shide
mana wallahi, ga ta dama ba mai isasshiyar
lafiya ba".
Hajiya ta dago ta dube shi idanunta jawur ta ce.
"Mu 6oye zuwa gobe, ko jibi kafin sannan mun
samo abin cewa".
Alhaji ya yi kasa'ke, sannan ya ce.
"A yi waya a sanar wa mahaifinta, inda hali su zo
nan mu taru mu san ta inda za mu 6ullo mata".
Hajiya ta yi saurin gyada kai cikin amincewa.
Hafsat da Hajiya sun wuni suna kuka a 6oye,
yayin da Rumaisa'u ta wuni cikin muguwar
kasala da hasashe iri-iri akan Auwal, wanda
wayar da ta ke masa ma ta daina shiga, ma'ana
an kasheta ko da kashe kanta.
Ko kwayar abinci ba ta kai bakinta ba, hana
rantsuwa ta wuni tana makar ruwa sai rake ga6a
hhudu da ta sha. Su kansu saboda lalurarta ta
damu da shan su bisa dole.
Bayan sallar la'asar dai hakurinta ya 'kare, tana
sanye da hijabin da ta yi sallar ta za'kulo Hafsat

a can dakin baccinsu tana kudundune akan
sallaya ta

2 Comments On GORAN DUMA
avatar
jannat

1 year ago

Reply

08062236094

avatar
jannat

1 year ago

Reply

08062236094

Please Login or Register in order to submit comment