Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka yi abin da
ransu ba zai ji dad'insa ba...q
Ya tare ta kamar a 'kufule
"Rumaisa'u sickle cell ne yakai girman da ba
za a auri mai shi ba? Haba! Wannan
maganar banza ki ke..."
GORAN DUMA *****13
Ita ma ta tare shi a tausashe "Auwal babu
yadda za a yi ni da kaina in 'kir'kiro
abubuwan da zai nesanta mu da juna,
amma duk abin da yake matsala ina guje
mana shi kasancewara sickler na san da
yawanmu irin matsalolin da suke fuskanta a
rayuwa, ciki har da tsangamar da dangin

miji ke masu matsaloli (sicklers) da za yi ta
faman dawainiya da nauyi akan mijinsu ko
kuma haihuwar dawainiya da su. Auwal
wani lokacin ma mazajen ke tsangwamar
matan akan sun zame musu nauyi... Kai wata
ba sikilar ba ce idan suka taru ita da dangin
mijin suka haifi sikila sai ya tattara laifin ya
dora mata, wata mahaifiyar sikila da na sani
ta ta6a bani labarin yadda mijinta ya fito kai
tsaye yake 'kalubantarta akan cewa matansa
hudu, amma ita kadai ta ishe da haihuwar
sickler duk da cewa tare da mijin suka
haifeta. Amma ka fahimta ba gudu nake a
tsangwame ni ba ko ko kuma a 'kalubalance
ni, na rantse maka babu wata wuya da ba
zan iya jurewa ba, kawai dai bana sn ka yi
abin da magabatanka za su yi kuka da kai.
Idan aure zai shiga tsakaninmu ya kamata
mu kori duk wani abu da muka san
'kalubale ne a rayuwarmu ta gaba dan a
gaban ba mu da lokacinsa abin da ke
gabanmu ma ya ishe mu".
A sanyaye ya nisa, ya ce.
"Na fahimce ki, in Allah Ya so zan yi abin da
kika ce, amma dai dole mu hanzarta zuwa
gwajin, ina son yin tanadin dukkanin wata
juriya a kanki".
Ta yi murmushin karfin hali cikin saduda ta
ce.
"To shikenan, Allah Ya za6a mana abin da fi
alkhairi Auwal".
Ya amsa cike da farin ciki.
"Amin Rumaisa'u, Allah Ya sa mutuwa ce
zata raba mu".
Ta yi dariya ta ce.
"Kuma ya zama ni zan rigaka mutuwa, na
tabbatar rayuwa zata yi min 'kunci idan
babu kai".
Shima ya yi dariyar, ya ce.
"To kin ga gara ni na riga ki mutuwar,
saboda ni ba zan iya jure rayuwar da babu
ke din ba".
Da dad'i ya cikata kawai sai ta amsa masa da
cewa.
"Ina sonka Auwal!"
Ya nisa cikin wani irin shauki ya ce.
"Ni na san ina yi miki abin da ya fi So
Rumaisa'u".
Babu abin da ya motsa dan jua baya akan
soyayyar da Auwal ke mata, sai ma wani
'karin tattali da tausayi da yake mata. Ya
daura d'amarar sanin duk wani abu da ake

gudunsa ga sickler, nisali ko a ina yake idan
iska ta taso a wajen sai ya nemi Rumasa'u a
waya, idan ta shiga motarsa sai ya zuge
gilasai tsab, sannan duk wata sabga ta aljihu
da zai mata ya juyar su kaf akan abubuwan
da zai taimaki lafiyarta, dangin kayan sawa
masu kauri da rufe jiki, dogayen riguna,
hijabai, ni'kab har da safar 'kafa da hannu.
Haka nan 6angaren abinci mawuyacin abu
ne ya je mata ba tare da wani abinci da zai
amfaneta ba, ko da mafi 'kan'katarsu ne
wato rake.
Tun daga nan hankalin Rumaisa da na
iyayenta ya kwanta, suke ganin lallai ta sami
mijin marainiya, Auwal ya zama dan gida a
nan Kano, Rogo har ma da Abuja kowa a
dangin Rumaisa'u.
A nasa dangin ma Rumaisa'u, saboda haka
na'am da girman gidan su Rumasa'u,
saboda haka har sun amince da aurensu.
Auwal ya kasa tarar mahaifansa ya sanar da
su Rumasa'u sickler ce, saboda ta tsorata shi
da yadda iyaye ke kar6ar lamarin dansu ya
auri sickler, sai ya ke shakkar goyan baya
daga nasa iyayen, musamman da yake shi
kadai suka haifa, yadda suke zumudin
aurensa ya fahimci yadda suka dora masa
burin tara 'ya'ya saboda haka ya yi kirmisisi
ya 'ki sanar da su, haka ma zuwa gwajin ya
share shi saboda fargabar da ta cika ransa,
alhalin ko me ma suka samo ba zai iya karya
masa gwiwar auren Rumaisa'u ba.
A haka manyansa suka je nemar masa auren
Ruma aka yi duk yan hidimomi bisa
al'adunsu aka sanya musu rana, in ta
kammala karatu za'ayi.
*BAYAN SHEKARU BIYU*
Wata biyu ya rage aurensu, wanda za a
had'a da na Hafsat da angonta Sani. Zancen
duniya da ba ya 6uya, sai ga batun cewa,
Rumaisa'u sikila ce a kunnen mahaifan
Auwal.
Kwatsam wani dare ya bar wajenta ya koma
gida, ya shiga wajen Innarsa neman ruwan
zafi, mahaifinsa ya yi kiransa fuska babu
walwala a fuskarsa ko kad'an.
Ya nemi guri ya zauna cikin sanyin jiki,
mahaifin nasa ya ce.
"Daga ina haka?"
Sai ya ji tambayar ba wai, saboda babu irinta
tsakaninsa da mahaifin nasa ko da can ma
da ba shi da gurin zuwa ba a fiye tambayar

ina ya je da dare ba ko dan yanayin aikinsa.
Amma yau shi ne ake tuhumarsa inda ya je.
Kawai sai ya yi 'kasa da kai, dan bai san abin
fad'a ba, yana ji a cikin ransa nan da wata
biyu Baban nasa ba zai ganshi a wannan
lokacin ba ma bare ya tambate shi.
Mahaifiyarsa ta shigo da fulas har da
farantin kayan shayi ta dire a gabansa, zata
fara hada masa ya yi sauri ya kar6e ta yana
godiya. Ta nemi guri ta zauna, shi kuma jiki
a sanyaye ya fara bude gwangwani yana
sauraron mahaifinsa da ya dora.
"Yaya me jikin?"
Ya dago da sauri ya dubi mahaifinsa
hankalinsa a tashe, amma fuskarsa ta kasa
nunawa. Ya tattare 'kululun da ya taso masa
a ma'kogwaro ya kora shi ta hanyar
hamud'ar madarar ya hadiye sannan ya ce
wa mahaifin nasa.
"Abbba ina ka san ba ta da lafiya?"
"Zancen duniya ai ba ya 6uya".
Abban ya fada cikin rashin kulawa tun daga
nan Auwal ya sha jinin jikinsa, kawai sai ya
ci gaba da hidimar gabansa. Abban ya gyara
zama ya ce.
"Wato Auwal ka san yarinyar nan sikila ce ba
ka sanar da mu ba, dan kawai ka na son
abin da zaka sanya mu 'karanta?"
Auwal ya dago cikin bugun zuciya ya dubi
mahaifinsa bakinsa na rawa ya ce.
"Abba... Mene ne 'karantar a auren sickler?"
Cikin 6acin rai Abba ya ce.
"Auren sickler ba 'karanta ba ne, kantafi ne
kawai da rayuwar 'ya'ya da ta aljihu... In da
'karantar ta fito shi ne zuwan da zamu yi mu
ce mun janye..."
Tuni har hawaye ya fara zuba a idon Auwal,
wanda ke kallon mahaifinsa garau da
alamun rashin kwanciyar hankali bare
kimtsa maganar da zuciyarsa ya kamata ta
haifa, bakinsa kuma ya furta hakan ne kuma
ya sa Innarsa ta sami sararin shiga maganar.
"Wannan d'an ka yi wauta in dai ka san
cewa yarinyar nan sickler ce, amma ka juya
wa matsalolinta baya zaka aure ta... Muna
zaune 'kalau ka kawo mana sickler dangi..."
A yanzu ya sami ga6ar abin cewa wanda
ra'ayin kansa da na zuciyarsa suka yi tarayya
yana 'kokarin tsayar da hawayen ya tare
mahaifiyarsa.
'Idan dai zan iya haihuwar da Rumasa'u, to
lallai zan iya haihuwar sickler da wata mai

lafiya wadda ba sickler ba ce..."
Shi ma mahaifinsa da yake zazzafan mutum
ne sai ya tare shi.
"Idan Allah Ya hukunto hakan na tabbatar
idan za ka haifi sickler goma da Rumaisa'u
idan wata ce sai Allah Ya ta'kaita ka haifi
hud'u..."
Auwal kawai sai ya yi shiru ya ci gaba da
shan shayin da ya fi kama da shan magani,
'kwalwarsa ta tsaya cak! Da 'kirkirar mafita
ko ta 'kofofin da duk ransa ya raya masa har
ya gama kushe masa aure da Rumasa'u tsab
ya 'karkashe batunda da haramta aurem.
Auwal dai bai tanka ba, har mahaifin nasa ya
diga aya sannan cikin rashin hayyaci ya tashi
ya fice daga falon.
GORAN DUMA
BY M.I.S.B
*****14
Tsawon daren nan ba zai iya dorar da wani
abin kirki da ya yi ko lissafinsa ya yi ba
dangane da yadda zai 6ullowa al'amarin, ya
san dai ya gurji kukan da tsananin 'kauna
da tausayin Rumasa'u ya haifa, kuma su
suka hana shi hasala komai bayan ya 'koshi
da ji a ransa duk tsanani ba zai iya rabuwa
da Rumaisa'u ba.
Sai 'karshen dare ya sami runtsawa saboda
haka bai sami sallatar asubahi ba, 'karfe
shidda dai-dai wayar Rumasa'u ta farkar da
shi.
Yana ganin sunanta kan wayar sai da
'kwalla ta taru a idonsa, ya daga yana
kokarin gyara muryarsa saboda daskarewar
bacci da kuma ta ma'ka'kin tausayinta da ya
ma'kale maasa a ma'kogwaro.
"Rumaisa'u" Muryarta tar ta ce "Duk
wadannan gaibu ne Abba, babu wanda ya
san abin da gaba zata haifa, kamar yadda ba
mu isa za6ar abin da muke so mu 'kyale
wanda tanmu yake hasashen hadari cikinsa
ba. Da dan Adam na da iko akan za6in abin
da yake so na matar da ta zarce Rumaisa
saboda abin da nake mata ya fi so, shi yasa
ban san ko wacce irin matsala ba a kanta,
amma da yake na san ba dukkan abin da
mutum ke so yake samu ba, tun bayan
umarninka na jiya na kwana ina gwajin
yadda zan iya rayuwar da babu Rumaisa'u.
Na yi ta cin karo da gazawa, har ta fara
barazanar keta min zuciya. Ban fitar da rai
zan iya din ko kuma zan kasa ba, na san a

biyu daya ce zata faru, ko in iya d'in in
wanzu bisa tsarin da ka za6a min, ko kuma
in gaza ta dalilin in bijire maka ba, wanda
babu irin haka a tarbiyyar da ka ba ni... Abba
kar ka damu da yadda ka ganni har in mutu
in Allah Ya so ba zaka had'u da abin kuka ta
silata ba..."
Yanzu hawaye ya fara cin 'karfinsa, kuma shi
ne ya tilasta shi diga aya ba don ya rasa abin
cewa ba.
Duk jikin mahaifinsa ya yi sanyi, sai kallon
Auwal yake shi ma kamar ya yi hawayen,
amma wata zuciyar na tuna masa siyasar
Auwal ta dadin baki da sadaukarwa har ka
yi masa abu ba tare da kana da niyyarsa ba,
wannnan ne yasa ya daure ya ce.
"Abin har ya yi zafi haka Auwal? Ba zaka iya
fitar da yarinyar nan a ranka cikin ruwan
sanyi da dalilin matsalarta a rayuwarka da ta
'ya'yanka ba?"
Auwal ya muskuta da murmushin ya'ke
alamar akwai magana fal a cikinsa, sai dai
yadda zai furta ya yi girma, don haka ya
hadiye ta kawai ya bi mahaifinsa da shiru,
har mahaifin nasa ya gaji da jiran cewarsa
ya nemi guri ya zauna idonsa akan Auwal.
"Tun farko ka san Rumasa'u sickler ce?"
Auwal ya kad'a kai, mahaifin nasa ya dora
wata tambayar.
"Wanne mataki ka dauka akan yadda za ku
rayu tare, ko kaucewa yadda za ku haifi
'ya'yan sicklers?"
Auwal ya jima kafin ya tattaro abin cewa.
"Ta yi 'kokarin hana ni aurenta tun ranar da
muka had'u na dage. Duk matsalolin da ka
lissafo min da bakinta ta lissafo min su,
amma ba su gigita ni yadda suke gigita ku
ba... Da ta ga haka sai ta shawarce ni yin
gwaji dan sanin makomar 'ya'yanmu, na
amince a sannan amma sai na ga gwajin
6atawa kai lokaci ne da tanadar wa kai
fargaba, don na ji a raina ko wane irin
sakamako gwajin zai haifar ba zan iya
barinta ba, saboda haka na ce ta bar
maganar gwaji".
Mahaifinsa ya jima cikin shiru yana jiya
maganganunsa, kafin ya yanke hukuncin d
ayake jin shi ne na 'karshe.
"Gaskiya ta yi hange mai kyau saboda haka
shawararta ita ce abin bi. Ka je ka yi gwaji
idan akwai matserar 'ya'yanku sai ku yi
aure, idan kuma babu, to ku dubi girman

Allah ku ceci 'ya'yanku ta hanyar ha'kura da
juna".
Duk da Auwal ya ji maganar mahaifinsa da
kamar maimaici kawai, ma'ana babu wani
sassauci haka ya cije a ladabce ya gyad'a kai.
"To na gode Abba".
Ya m'ke kuma salin-alin ya fice ya shiga
'kwan'kwasa falon Innarsa.
Auwal bai 6oyewa Rumaisa'u komai ba
dangane da yadda suka yi da mahaifinsa da
hujjarsa ta sanin kukanta nasa ne, kukansa
ma nata ne. Tuni suka yiwa juna wannan
al'kawarin na tarayya akan matsalolinsu dan
nemo hanyar araka.
Rumasa'u ta jima ba ta yi magana ba, ba dan
rashin abin cewa ba sai dan saisaita
maganar don gudun kada tayi muni a
kunnen Auwal ko kuma ya zama wani
mataki na karyar masa da gwiwa.
"Kin 'ki cewa komai Rumasa?"
Ya fada bayan ya gaji da jiran cewar tata.
Ta gyara tsaiwarta ta 'kara jingina sosai da
motarsa saboda tana jin jiri. Ta yi
murmushin 'karfin hali ta ce.
"Abin da Abba ya yi shi ne ya kamata Auwal,
so ne tun farko ya ke runtse mana ido
alhalin wani dad'in gushi ne kawai a cikin
rayuwar aure, wanda ake 'kulla si domin
kammaluwar iyali. Ya wajaba ne mu
samarwa iyalanmu makoma ta gari, ba ya
kamata ba Auwal".
Shi ma ya yi murmushin 'karfin hali bayan ya
ji a ransa kawai 'karfafa masa gwiwa ta ke
so ta yi ba ainihin abin da ke cikin ranta ke
nan ba, ya ce.
"Kamar ke da Abba kuna mantawa ba a yiwa
Allah wayo, ke kanki aya ce Rumasa'u,
Innarki da Abbanki babu sickler ciki, amma
suka haife ki..."
Ta tare shi da dariya.
"Ba 'kokarin yin wayo ba ne, 'ko'karin
amfani da hankali ne, wanda Ubangiji Ya
hore mu da shi dan za6ar abin da zai
amfane mu da gujewa abin da zai cutar da
mu, abin da ya faru da mu cikin akasi mun
yarda daga Ubangijinmu ne ba tare da
sakacinmu ba, sai mu yi fatan zamowarsa
kaffa".
Auwal ya yi zuru kawai yana kallonta sannan
ya nisa ya ce.
"Ban sna me yasa duk cikin lissafinku ba
kwa duba uban yaran da samun su yake

'kila wa 'kala ba, sa ku kuka himmata
sarayar da shi alhalin shi ne a hannunku. To
zan fada miki abin d ana fada Abba jiya na
kwana da 'kokarin lissafa yadda zan yi
rayuwar da babu ke, na ji kamar
numfashina zai yanke daga lissafin kawai ba
tare da fitar da sakamako ba, amma dai ban
cire rai daga rahamar Ubangiji ba, duk za6in
da ya yi min ina fatan rahma da jin 'kanSa a
ciki".
Ta zuba masa ido, dauriyarta na kokarin
'karewa. Kasa gajiya da kalonsa da ta yi ne
ya sa ita ma ta tabbatarwa kanta wa'ka
kawai ta ke, amma tursasa kanta za6ar
tsaka-tsakin al'amura, sai dai kuma ta kasa
hana zuciyarta rauni da son nuna gazawa
da ta tsaya kawai ga bayyanawa ta hanyar
'kura masa ido cikin hawaye.
Haka suka tsaya ita kuka, shi hawaye, har
daga 'karshe ya zagaya mota ya shige yana
cewa.
"Zo mu je asibitin".
Ta yi saurin duba agogon hannnunta da ya
nuna 'karfe sha daya da mintoci sha hud'u.
Ta bude motar ta sunkuya a tausashe ta ce
masa.
"Bari na sanar da Hajiya".
Ya yi saurin tare da fadin.
"Rumaisa'u kar ki sanar da kowa
matsalarmu fa, umarni ne da kuma kokarin
kwantar da hankalinku ke da Abba zai kai ni
gwaji, ba dan na yarda da iya raba ni da ke
ko ya yi wani abu a cikin sonki ba. Ya
kamata ki ri'ke wannan kada ki yi 'kokarin
raba ni da kanki, son da nake miki mutuwa
ce kawai zata iya raba ni da shi".
Ta sororo cikin sanyin jiki tana kallonsa. Ta
hadiye kwallarta ta ce masa.
"Auwal wai me yasa ka damu da kira mana
mutwa? Ai ba sai ka kirata zaka bayyana min
kana sona ba,.."
Ya tareta cikin kyalkuala dariya.
"Me yasa ba kya so na kirata? In akiranta ne
dan na sna ita ce mai YANKE 'KAUNA, duk
yun'kurin raba mu da kuke ni dai na
tabbatar ita kadai ce zata iya raba ni da son
da nake miki. Amma na san ba ni da karfi ko
dabara a cikin aurenki yadda Ubangiji Ya so
haka zai yi".
Ta murza yatsu tana dariya, ita ma ce.
"Shikenan. In Allah Ya so ni da kai mutu ka
raba".

Ba ta jira cewarsa ba ta wuce. Ya bi ta da
kira, ta tsaya ba tare da ta juyo ba, ya dan
daga murya.
"Na fa gaya miki kar ki fad'a".
Sai kawai ta kad'a kai ta wuce tana dariya.GORAN DUMA 15
.
.
Dr. Hadiza ta gyara zama ta janyo wani fayil
cikin murmushi ba tare da dubansa ba ta ce.
"Soyayyar da kake mata da amincewarka na
aurenta a matsayinta na mai sikila shine matakin
farko na magance matsaloli ko yi musu kallon
'kanana a cikin aurenku, idan duk kun yarda da
wannan to kamata ce ku zo min tare, duk abin da
zan fad'a tare zai amfane ku, idan ma 'karfafa
gwiwa ne tare zai 'karfafa muku".
Auwalu ya jima bai tanka ba, sannan ya ja
numfashi cikin kasa hankula barkatai ya amsa.
"Haka Allah ya tsara na riga na taho ni kadai d'in,
amma na daura damarar zantar da ita komai
kamar yadda kika zantar da ni, hikimia ko ta aro
ce zan aro in yi 'kokarin fahimtar da ita".
Ofis din ya dauki shiru sai 'karar takardun da
likitan ke bud'awa da kuma bugun zuciyarsa da
ya cika masa kunne da rud'u.
Likita ta dago kai ta dube shi da wata takarda a
hannunta tana juyawa.
"Sakamakon gwajinka ya nuna cewa, kai AS ne,
ma'ana zaku iya haihuwar mai AS za kuma ku
iya haihuwar mai SS, wato ranar da ka bayar da
A ta bayar da S dinta za ku samar da d'a irinka
(AS). ranar kuma da ka bayar da S din ka dama
ita abin da zata bayar ke nan, to za ku samar da
d'a SS (sickler) irinta.
Abin da zan 'karfafa muku gwiwa da shi a nan shi
ne, ku shiga cikin hankalinku ku kyautata zaton
alkhairi ga rayuwar 'ya'yan da zaku samu a gaba,
wanda Ubangiji ne kadai Ya san yadda za su
kasance. Idan Allah Ya ga dama sai ya azurta ku
da 'ya'ya goma babu sickler ko daya a ciki,
ikonSa ne Ya umarce ka ka yi ta bayar da A
dinka har ku gama haihuwarku, idan kuma Ya si
zai iya jarabtarku da haihuwar sickler, Allah babu
yadda bai iya ba. Kai kanka zaka iya haifar
sickler ba tare da ka auri Rumaisa'u sickler ba.
Idan wadda ka aura din AS ce kamai ai za ku iya
tarayya wajen bayar da S zalla ku samar da
sickler. Abin da ya ke a rubuce dai babu wanda
ya isa kankare shi, dukkanmu ba dan ba
damarmu muke, Ubangijin da Ya yi ka AS shi ya
yi A. Ba don ya fi sonsa da kai ba. Kuma shi ya
yi S.S ba dan Ya yi masa laifi ba, sai dan haka

Ya so, haka Ya ga dama. Dan haka babu wani
dalili da zamu dogara da shi wajen hana aurenku
ina fatan ka fahimce ni?
A 'karshe ina shawartarka da kwantar da hankali
da mayar da lamari ga Allah, na tabbatar zai
saka maka da dubun alkhairi idan ka dogara da
shi ka auri wannan baiwar Allah ba tare da ka
guje ta ka gadar mata da takaici a zuci ba, kai
kuma ka saka 'karfi da dabara a cikin taka
rayuwar ba, yadda kake nuna wa ina fahimceka
da cewa ka dauki ciwonta naka, wannan ko
wanne sickler ke bu'kata. A yarda da rauninsa, a
tausa masa idan ciwonsa ya taso, a yi masa uziri
a taimake shi ta wadannan hanyoyin kula da
maganinsa, kaucewa abin da zai motsa ciwonsa,
hana shi aikin wahala tare da 'karfafa masa
gwiwar cutar da yake bautar Ubangiji ce. Idan ya
yi tawakkali ladansa ba zai lissafu ba. A yarda in
an haifi d'a sickler da shi ba shi kadai ya haifa
ba, da sauransu.
Duk wadannan dabi'un taimakon na zace su a kai
malam Auwalu dan Allah ka yi 'ko'kari kar ka ba
ni kunya".
Tunda ta ke magana hankalinsa ya kasu uku,
daya a kanta, daya akan batun mahaifinsa (ka je
ka yi gwajin idan akwai matserar 'ya'yanku sai
ku yi aure, idan babu to ku dubi girman Allah ku
ceci 'ya'yanku ta hanyar ha'kura da juna), daya
kuma wanda ya ke da kawo mafi tsoka akan
'kauna da tausayin Rumaisa'u, wanda a yanzu shi
ya sa shi fitar da 'kwalla bayan Dr. Hadiza ta
dire, zuciyarsa ta dame shi da son ya fad'a mata
'dama can ba ni ne matsala ba, mahaifina ne'.
Sai kuma ya ga fada matan wani rage karsashi
ne a dogon lokacinta da ta 6ata tana ba shi
shawarar rayuwa da Rumasa'u, wanda ko ba a
shawarce shi ba, abin da burika da ra'ayoyinsa
ke zartarwa ke nan.
Ya hadiye duk wata damuwarsa ya yi mata
godiya sosai, tare da nuna 'karfin imanin babu
abin da zai raba shi da Rumasa'u, suka yi
sallama dukkansu suna yiwa juna godiya.
Bayan ya fito asibitin ya yi mazantakar wucewa
ofis dan gwada 'karfin hali da na zuciyarsa da
koyawa kai jarumta cikin lamarin d ake fin 'karfin
iyawa, mahaifinsa ne abin jinsa, wanda alamu ke
nuna yana son saka 'karfinsa wajen taruwar
iyalai da babu tahalikin yadda za su samu.
Rayuwarsu zata kai ga haihuwar ko zata gaza, za
su haifa din ko ba'kararru ne su? Duk wadannan
gaibu ne babu wanda ya san shi sai Allah, idan
ya sa wa kansa damuwar rana guda a kansu ya

had'a wautar da zata kamanta shi da rashin
hankali.
Suna zaune a falon da suke hira, idan sun so
jimawa suna hirar ke nan, idan ba za su jima ba
dama a motarsa suke jingina su yi tad'insu.
Rumaisa'u ri'ke da takardar sakamon gwajinsu
tana juyawa, idan akwai abin da ya fi 'kunci da
d'aci to ranta shi ya yi. Abin da ke shirin faruwa
da ita zuciyarta ta 'ki yarda zata iya daukarsa
duk yadda ta yi 'ko'karin gwadawar.
Auwal ma ko da gwaji ya kasa ce mata wani
abu. Tunda ya ba ta takardar har sai da ta gaji ta
tsinka, cikin yi masa kallon kai tsaye.
"Auwal ban ta6a jin kaico da nadamar
kasancewa ta sickler ba sai a yau. Na tsani kaina
da duk wata tawaya da ta ke son raba ni da kai
Auwalu..."
Ya tare ta cikin dakewar 'karfin hali.
"Kar ki yi sa6o Rumasa'u, wannan wacce irin
wauta ce? Ki shiga cikin hankalinki, duk yadda za
ki so ni bayan Ubangijin da ya halicce ki ya
wajabta in bi. Tsanar kanki da tsanar
kasancewarki yadda Ubangiji Ya tsaro ki tawaye
ne da butulci gare Shi..."
Ta dam'ke bakin da ya yi mata amfani biyu, hana
sautin kukanta fitowa da nuna nadamar abin da
bakin ya fad'a, cikin raunanniyar muryar kuka ta
ce.
"Astagfirullah, Allahumma gafirni war hamni..."
Ta zare da shesshekar kukanta.
Shi ma duk yadda ya so ya daure sai dauriyar ta
fi 'karfinsa ya fara hawaye, ba dan yana zatar
musu rabuwa ba, sai dan shaukin yadda suke son
juna da tausayin Rumasa'u wadda ake son raba
su ta dalilin aibun da ba ita ta 'kaga wa kanta
ba. Mace mai sanyin halin da ta kasa fitowa kai
tsaye ta ga laifin mahaifinsa da ke son raba su,
'karfinta da yaji ta ke juyawa aibata mahaifinsa
baya.
Sun jima suna 'yan koke-kokensu kafin ita da ta
fi shi sharafin damuwa ta kuma soko wata
kato6arar.
"Da za a ba ni za6in rayuwar da babu kai ko
mutuwa, Auwal da gudu zan za6i mutuwar, har
yau ni ban san ta inda zan fara rayuwar ba, shi
yasa ka ji na kasa 'karfafarka bin umarnin Abba
don Allah ka yi min wannan uzirin... Ina sonka
ban san babu a kanka ba Auwal, wannan ciwon
ya fi sickle cell ciwo a raina..."
Ya tare ta cikin kasa tattara kalaman da za su
fidda ma'ana sosai, saboda rud'ani.
"Ba zamu rabu ba Rumasa'u ki daina ambato

mana rabuwar... Ni duk maganar nan ma ta
gundure ni wallahi".
Ta dago ta bi shi da kallo cikin hawaye.
"Haka ne burina Auwal, amma ba zan yaudari
kaina na dorar da shi da fatar baki ko ture abin
da ya kamata na duba ba".
Suka kuma daukar shiru sannan ta goge
hawayeta 2a fuskance shi
"Ka sanarwa Abba?"
Ya yi saurin girgiza kai yana kallonta sararo. Ta
'kokarta ta ce.
"Sai ka yi gaggawar sanar da shi, ya yanke mana
hukuncin da Ubangiji Ya za6a mana, fara shirin
zama tare ko kuma shiga makarantar koyon
juriya da rashin juna, ko wanne Ubangiji Ya za6a
mana muna fatan ya zama alkhairi a gare
mu".Ba ta jira cewarsa ba ta mi'ke zata bar
falon....
.
Dan Aunty
August 4 at 9:12 PM ยท PublicGORAN DUMA 16
.
.
Ya yi saurin dakatar da ita da cewa" Duk kurin da
na gama yi na cewa babu abin da zai sauya a
cikin soyayyarmu da auren kin fayalar da shi
kenan, dama kin tura ni gwaji ne dan ki rabu da
ni Rumasa'u?"
Ta yi saurin dawowa gabansa ta dur'kushe tana
girgiza kai cikin hawaye. Ta kasa magana sai
kallonsa da hawayen, shi ma ya motsa baki, ya yi
maganar amma ya kasa, har sai da ta gama nata
alayin ta riga shi samo abin cewa.
"Ina sonka Auwal... aurenka shi ne babban burin
da da ace ina da iko zan kusantar da shi tunda
ba ni da ikon na yi imani aurenko rashinsa da ni
kaina da kai duk muna shawagi ne cikin hukuncin
Ubangiji, zai iya kusantar da shi dan rahamarsa a
gare mu da ni'imarsa. Zai iya tankwa6ar da shi
dan isarSa a kanmu da zartar da abin da mu ba
mu san da shi ba, dan haka duk abin da ka ji na
fad'a kar ka yiwa ubangiji biyayya da faranta ran
Abba, a wani hannun kuma da 'kin biyewa zuciya
sakokinta... Ina sonka Auwal"....
Ya kai 'kololuwan rauni da tausayin Rumaisa'u
wanda ya 'kara masa miliyoyin kaunarta,
ma'kogwaron ya cunkushe da shu, shi yasa duk
yadda ya yi 'kokarin ya ce wani abu ya kasa,
kawai sai ya dauki takarda ya nemi hanyar fita.
"Ba zamu rabu ba Rumaisa'u ki daina ambato
mana rabuwar... Ni duk maganar nan ma ta
gunudure ni wallahi".

Ta dago ta bi shi da kallo cikin hawaye.
"Haka ne burina Auwal, amma ba zan yaudari
kaina na d'orar da shi da fatar baki ko ture abin
da ya kamata na duba ba".
Suka kuma daukar shiru sannan ta goge
hawayenta ta fuskance shi.
"Ka sanarwa Abba?"
Ka yi saurin gaggawar sanar da shi, ya yanke
mana hukuncin da Ubangiji Ya za6a mana, fara
shirin zama tare ko kuma shiga makarantar
koyon rashin juriya da rashin juna, ko wanne
Ubangiji Ya za6a mana muna fatan ya zama
alkhairi a gare mu".
Ba ta jira cewarsa ba ta mi'ke zata bar falon.
Ya yi saurin dakatar a ita da cewa.
"Duk kurin dakatar da na gama yi na cewa babu
abin da zai sauya a cikin soyayyarmu da auren
kin fatalar da shikenan, dama kin tura ni gwaji ne
dan ki rabu da ni Rumaisa'u?"
Ta yi saurin dawowa gabansa ta dur'kushe tana
girgiza kai cikin hawaye. Ta kasa magana sai
kallonsa da hawayen, shi ma ya motsa baki, ya yi
maganar amma ya kasa, har sai da ta gama nata
alayin ta riga shi samo abin cewa.
"Ina sonka Auwal... aurenka shi ne babban burin
da da ace ina da iko zan kusantar da shi tunda
ba ni d aiko na yi imarin aurenko rashinsa da ni
kaina da kai duk muna shawagi ne cikin hukuncin
Ubangiji,

2 Comments On GORAN DUMA
avatar
jannat

1 year ago

Reply

08062236094

avatar
jannat

1 year ago

Reply

08062236094

Please Login or Register in order to submit comment