Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akwai masu pada da gasken
kuma suyi a aikace amma daga matar har mijin basu kula
da hatsarin da suke ciki na gaza sauke hakkokin juna
lokacin da suka ki daukar mataki akan kalmar ba da yake
tapi ganin laipin matar , ta tashi nata sharhin sai tace.
' mata pa akwai kwakwazon korapi, tare da gaza hakuri in
an kwatanta musu irin sa na tabbatar duk matar da
mijinta yace mata don 'yayana nake zaune dake.
Mawuyacin abu ne wannan auren nasu ya dore saboda
yadda zata tattara kauna ta yanke masa.
Ta pito ta cigaba da bun ragowar labarun da marubuta

suka aiko, tayi tsokaci (comment) a wanda take muradi
tayi jinjina (like) a wadanda suka burgeta.
Ranta ya para haske kirjinta ya dan samu sarari dama zan
kapin mahaukacin masori ba karamin kaye da sanda
nishadi duniar marubuta ke bata ba.
Ta bar nan ta tapi dandalin masorya jaridar Aminiya,
zababbiyar jaridarta kenan tun kapin ta zama
marubuyarsu saboda haka ita ma wata ginshikice a
padada mata zucia,
jakar sakonninta (inbox) ya rika kuka ta duba akwai
wulgawar sakonni kusan goma a ciki.
Kamar zata share su ba tare data duba ko daya ba
kasanwewarta marubucia bugu da kari kuma mace wada
bata tsallake neman maganar maza marasa mapadi a fb,
amma da ta tuna kila akwai wadanda zasu iya
dangantarta a masu sakon yan uwa ko abokan aiki da
kawaye sai ta tapi inboz din kamar yadda tayi tsammani
ta tarar sakon yayarta Balaraba, wadda ke paman yi mata
mitar taje Abuja taki zuwa gidan ta kuma ta tsiri wata
muguwar dabi'a ta kashe wayoyi , ta amsa mata da ban
hakuri da alkwararin share mata hawaye,
tana barin Balaraba taci karo da sabon sakon Mahaukacin
masoyi Username dinsa kenan Mahaukacin masoyi.
Zuciyarta ta para bugawa pat-pat amma da karpin hali ko
karanta sakon batayi ba ta tapi bincike bangonsa (wall)
abun da ta tarar bazai mata ampanin komai ba sabon
acct ne haihuwar shekaran jiya, babu komai a cikinsa na
dorarwa, adireshin ma banda suna babu komai bude,
bata tsawaita wani tunani ba ta toshe shi yadda bazai sake
sa ido a kanta a fb ba cikin jin karpin gwuiwar abun da
tayi taci gaba da harkokinta tsawan awa daya.
Tana shirin sauka saboda lokacin baccinta yayi ta koma
inbox saboda tunanin kar ta bar sakon da suka kamata
sai kuwa taci karo da sabon mahaukacin masoyi mai
karin I a karshe,
wato mahaukacin masoyii shaidar ya harbo jirginta ya
kuma dana mata wani tarkon,
na para mamakin yadda kike son bude kwanji ki guje min
duk da ban bude nawa na para sonki da yanke kaunar
rabuwa dake ta dalilin wani abu ne mai sauki na.
Idona a kanki yake Rumaisau ki daina wahalar da kanki
da tsammanin zaki iya kubce min, wannan wani irin
zalunci ne don Allah?
Kin kashe wayoyi saboda ni, na share wannan takaicin kin
shigo dandalin sada zumunta na cika da doki na biyo ki
amma kawai dan rashin adalci sai ki kulle tsakanina dake?
Ki daina tsammanin zan yarda da wannan..
Bata ko karasa karanta sakon ba tayi baya a guje ta pice
daga fb din sannan ta kashe na'urar gaba daya ta bige da
rapka tagumi.
Ta tabbatar da kanta in ta kai karshen sakon kila
mahaukacin masoyi ya pada mata kalar kayan da ke

jikinta da irin yanayin zaman ta nan rudanin a yanzu ne
ta para ji a ranta ya kamata ta san waye mahaukacin
masoyi.
31/1/2013
tana zaune a gida dab da azahar mubarak autan hajia ya
kirata a waya '' anti kin pita binciken da kika ce zaki?
A tausashe tace A,a mubarak, wani abu ya paru ne?
Ya amsa a ladabce yana daria . Babu abun da ya paru
dama neman alparma zanyi ki karaso nan B.U.K ki dauke
ni na bada aron mashin dina kin san kuma hana goyon
nan ya janyo karancin abin hawa.
Tayi yar daria tace ban pita ba amma bari nazo na dauke
ka yace godia nake anti amma dai a dan gyara laipin aron
babur din da na bayar.
Tace masa karka damu.
Cikin sauri ta debi wayoyinta da tun hantsi ta kunna take
jiran sakon mahaukacin masoyi wanda tayiwa tanade
tanade marasa lissapi bai kira din ba, har ta sallaci azahar
ta dawo da tsakkamin zata tarar da sakon sa nan ma
shiru, har zuwa lokacin da mubarak ya nemi agajinta.
Hajia taimaka ki ara min mota in dauko mubarak.
Ta samu hajia a palonta ta pada mata haka tana yar daria
hajia tayi mata kallon tsab ta ce a.a kiyi daria da kyau.
Kina pama da kanki zaki je wani dauko mubarak?
Ina babur din sa?
Kai tsaye ta amsa yayi paci yace min ya rasa mai liki
saboda matsalar masu gyaran sannan ga kwarancin abun
hawa a gari,
shine sai ke zaki dauko shi?
Ta wuce kan talabijin ta dauko makullun motar tana
cewa to yaya za ayi hajia?
Nima ina son ganin wulgawarsa a gidan tun sape bakina
ke tsami ba abokin hira.
Hajia tayi daria tace Allah ya bada sa'a Allah ya kiyaye
hanya.
Tana picewa ta amsa Aamiin
hajia ta sauke kai tana girgizawa xuciyarta cike da
tausayin Rumaisau tattausar mace mai kirkin gaske
amma Allah Ya kaddaro rayuwarta cikin jarrabawarSa.
Bata taba jin wanda ya zauna da Rumaisau ya padi rashin
kirkinta ba duk kuwa wanda yace batada kirki da zarar ka
dube shi zaka ga rashin kirki a puskar sa.
Tun kapin ta shiga makarantar tayi kiransa a waya
Mubarak karpa na shigo ka cika min mota da abokanka
inba haka na karka kuma taso ni zuwa daukar ka.
Yana daria ya amsa na san da haka shi yasa ma na ware
gepe.
Tace dashi cikin daria aha! Ka shirya na shigo.
Yace amma akwai yan uwan ki mata nasan...
Yaki karasawa yana daria ita ma tayi dariyar tace babu
matsala.
Tana shiga ta ciko mota da Mubarak da abokan karatunsa

mata, sai wani nataccen abokinsa shau'aibu da ya matsa
sai an dauke shi har yana cewa Rumaisau, anti in ma ba
zaki dauke ni ba sai na daura dankwali kona yapa gyale,
sai in ara cikin yan matan nan bazaki rasa mai spare a
jaka ba.
Dole Rumaisau ta yi daria tace mai yayi zapi?
Shigo mu tapi.
Ta hada su a gaba shi da Mubarak ta tashi motar yayinda
wasu tunanuwa masu nauyi suka wulga a zuciyarta,
tunanin da ke pawar sa ta kukan jini inda anayi duk da ta
san akan su tana kukan da yapi jini ciwo.
Haka ta tashi motar ta pice a guje tana satar kallon
wurare a makarantar, wadda ta kasa hadiye wa sai da ta
para zubar da hawaye, sannan ne mubarak ya tuno katon
kuren da ya tapka, yayi saurin dora hannu aka ya kame
baki yana satar kallon titi cike da nadama.
Ba yau ya para gayyato rumaisau tazo daukarsa ba amma
yana sane da yadda matsayar dalibai jiran shigowa bus a
nan makarantar ke zama wani katon abun pami a raunin
Rumaisau, dan haka sai ya kan yi gaba su hadu a hanya ta
dauke shi su pice ko zatayi hawaye kadan ne.
Saboda haka ne ita da Mubarak suka yi dip a motar,
matan baya keta hiranrsu ,
shu'aibu da ya rasa abokin hira yake saka musu baki,
Mubarakk ya rasa bakin bawa Rumaisau hakuri ita kuma
ta kasa daina zubar da hawaye har suka pito makarantar
suka hau babban titi.
Mubarak dubo min gilas dina a jaka.
Rumaisau ta pada dan tsananin kaunar ta manta abin
dake sata hawaye da kunan zucia.
Cikin doki mubarak ya dauko jakarta yana cewa inaga dai
anti gayyatar karshe na miki ta zuwa ki dauke ni indai
ranmu zai dinga baci haka
ta karbi gilas din tana dariar yake tace ko baka gayyato ni
ba mubarak inna surantawa kaina makarantar nan inayin
abun daya pi haka, gara ma ka dinga gayyato min ina
zuwa kila na saba da kallonta gwauruwar ta...
Ta kasa ci gaba da magana saboda kukan da ya toshe
mata makogwaro ta bige da bude gilas kawai ta saka
sannan ta hadiye kukan.
Motar tayi tsit har suka kawo mahadar tituna na
kabugam yanzu ta hakura da kukan duk da karpin hatsi
tasa masa amma dai yabi umarninta ne da taimakon
hango wasu mata biyu datayi suna bara a tsakanin
motoci.
Matan ba wai tsoppin almajirai da ido ya saba gani ba, a'a
matasan mata yan shekaru ashirin da biyar zuwa talatin
kuma abun da yapi shayar da takaici shine da yanayi irin
na mazan da sukayi kaurin suna wajen hawa gajimare
( shaye-shaye)
bata magana cika jakar mamaki da alhininta ba sai ga su
gabanta dayar zuro hannu ta rike sitiyari tana layi, Hajia

ki taimake ni kamar yadda Ubangiji Ya miki sutura ki bani
na siye abinci da dan hayaki...
Dayar kuma ta cape da cewa bata wulga ta kantaba... Kina
hada mutum da Allah baya nupin an rasa yadda za ayi in
motar nan cancakar naso sacewa na rantse yanzu zan
muku rupa ido in dauke shi.. Ko ba haka ba?
Suka dubi juna ita sa su Mubarak zai yi magana ta hana
shi dayi masa inkiyar ya bude mata jaka amma sai ya
kankame jakar ya juya keya ta pahimci manuparsa
saboda jaka tayi yar daria ta dube su da kyau tace aini ma
da na ganku murna nayi da Allah ko yar naira shirin ce ku
bani goro zanci.
Nan da nan kamar walkiya suka bace daga gare ta, duk
motar kowa ya rude da daria lokacin da suka sami hannu
suka wuce.
Shu'aibu yace anti yaya akayi kika san mashayan nan ba
sa son a roke su kudi?
Tana daria tace ko daya, na san wanzami baya son jarpa,
amma dai nayi mamaki in labari aka bani shayeshayen
mata ya kai matakin pito da su kwararo da dabi'u irin na
yan daba, Wallahi karyatawa zanyi.. Amma sai idona yaga
zahiri..
Shu'aibu ya tareta da padin anti ai gara wadannan da
ganinsu kin san dama sun gagari iyayen su ne akwai wata
budurwa a anguwar mu bazan iya kirga sau nawa na
ganta a make ba, na sha kamata na kai ta gidan yayata a
tsare ta yapi a kirga, ina mata gudun batagari su cimma
wata mummunar manuparsu akanta.
'' Innalillahi wa innan ilaihi raji'un.
Rumaisau ta pada cikin kololuwan bayyana takaici da
alhininta sannan ta dubu mubarak tace mubarak ko akan
shaye shayen mata zanyi batuna a wannan watan ne.?
Good!
Wannan zai kayatar kuma zai padakar.
Zaka taimakeni da bincike kenan?
Ya amsa mata da karpapawa,
babu matsala yau zuwa gobe ina cikin yanci.
Ko baka cikin yanci ma naga ai kana dagawa kayi aikina.
Ta pada ba tare da ta dube shiba da yayi dan nazarinta sai
yayi daria yace Allah ya sa ban kauce hanya nayi kuskure
a magana ta ba.
Tayi daria kawai, shuaibu yace ka kawota gidanmu taga
yarinyar danayi maka maganarta idan tana da bukata.
Cikin sauri Rumaisau tace mai zai hana?
Idan babu damuwa muje gida kuci abinci sai mu pito
tare.
Ok babu matsala inji shuaibu, mubarak ya dora da cewa
sai kuma ina?
Tace da sape ka raka ni freedom nayi cigiyar hajia
Maryam (Maryam Babban suna, ina gaida duk mai suwa
Maryam , (Dan Aunty) )
1/2/2013

ta wayi garin ranar yau da kumajin datajima bata
tabadarwa kanta shi ba har ga Allah tanaji a ranta sunyi
hannun riga da Mahaukacin masoryi tunda dai gashi
kwana 2 kenan babu sakonsa a waya saboda shi ma ta
kara lokutan hawa fb amma ya bacewa ganinta wannan
ba karamin dadi ya yiwa ranta ba ta shirya karasa watsar
da shi da tunanin yadda zata gungura rogowar tsumman
rayuwarta data ke wa take gawa taki rami .
Ba kamar yadda ta so ba wato zuwa freedom tare da
mubarak sai Alhj ya bashi wani aiki na wakiltarsa daurin
aure garin katsina, a ranar juma'ar da jiran bikin nadin
sarauta a washegari asabar, wannan yasa ita kadai taje
freedom bayan an sauko masallaci.
Bata sami ganin hajia Maryam ba kan abin da yakai ta, sai
dai ta samu garantin ranar samunta, bata dawo haka ba
sai da ta shiga sashin labarai neman ji daga wanda ya
kawo wani rahoto game da yadda wata yar maye ta
dabawa wani matsashi wuka.
A ranar yau Rumaisau ta kara godewa Ubangiji da Ya
jukuntota a mai son bincike dayin rubutu game da
abubuwan da zasu ampani al'umma, saboda yadda take
haduwa da ayoyinsa iri iri masu kara mata tsoron Allah
da goge maSa, da kuma masu sanyata gudun yi maSa
butulci da daukar sabonSa ba a bakin komai ba.
Tana freedom radio akayi sallar la'asar dan haka kapin ta
pita sai da tayi alwala ta shiga masallacin mata tayi sallah.
Bayan ta idar ta bude jaka ta hau goge gogen puska da
gyara daurin kallabi ta gama tana mayar da kayan jaka
taken shigowar sako ya kasa a wayarta,.da karpin hali irin
na dan daudun daya kamo kadangare ta capko wayar ta
para duba sakon.
''Rumaisau ban kasance ma'abocin sauraron wakoki ba
amma abun mamaki wata waka ce yanzu take gilmawa
kunnena wadda ta motsa min dubun taki kaunar a
makoshi na, kin san wakar?
Itace wakar YAR MAYE. Wakar ta shige ni! Ta sani
tsausayin kaina piye da tausayin matan dake je pa kansu
a haln shaye-shaye, saboda na san giyar kaunarki ta make
ni piye da yadda ko wanne irin kayan maye ke make
ma'abotansa.
Idan kin taba nazari akan yan maye ki zace ni da kalar
tsausayi piye da yadda kika san su,
mahaukacin masoyi.
Tayi iyakar kokarinta wajen hadiye rudaninta saboda
wasu mata biyu dake salla gepenta kuma wannan
dakewar tata xe ta bata samar yin wani tunani na zaton
duk yadda akayi mahaukacin masoyi akwai kapar da yake
samun labaran halin da take ciki ya turo sakonsa a kansa
in dai shi ba junnu bane.
Bata tsawaita tunani ba bare ta samo abun da zai kore
mata wanda ya gaskata ta para latsa wayarta ta kira
Mubarak.

Mubarak wa ka sanarwa cewa zanyi rubutu akan masu
shayeshaye kuma waka sanarwa zuwa na freedom?
Mubatar ya jima yana jan numpashi kapin ya amsa mata
anya nayi maganar da wani?
Kusan mapa Wallahi na manta maganar tun jiya da muka
je unguwar su Shuaibu.
Tayi ajiyar zucia ita ma ta jima tana jan numpashi sannan
tace Ina shuaibu?
Yace munyi waya dashi yau da sape yake cemin yana
kwance a gida saboda ya gamu da masassara (zazzabi),
wani abu ne ya paru?
Muryar Rumaisau na rawa tayi saurin girgiza kai kamar
yana gabanta a'a babu komai kanajin babu wanda zai iya
sanina wajen shuaibu har ya bashi batun ina bincike akan
mashayan mata?
Nan ma Mubarak ya ja pasali sannan ya amsa anya ina
tantama wai me ya paru ne?
Tayi dariyar karpin hali tace ok babu komai yaya
katsinan?
Ina patan kana shirin ganin gari?
Mubarak ba dan ransa ya so ba ya yarda da wannan
ninkuwa bai bai din da tayi masa ya amsa a sake sukayi
sallama suka ajiye wayoyi.
Tana daukar mota ta pigeta sai Dawaki road gidan Hafsat
yayar Mubarak, wadda take tsararta kuma tare ma sukayi
yammatancin su .
Hafsat da tsohon cikinta ta karbeta cike da mamaki .
Rumaisau bata irin wannan ziyarar ta bazata to yaushe
ma ta ke son zuwa gidanta duk irin shakuwar da sukayi?
Suka zauna apalo Hafsat ta sa aka cikata da kayan sanyi
amma ko kallon inda suke Rumaisau taki yi.
Tayi nazarin agogo sannan ta sauke ganinta akan Hafsat
tana padin Hapsat wata almara ke paruwa dani, shine na
daukota na kawo miki mu tattauna akanta, a gaggauce
saboda kin san babu lokaci.
Hapsar ta gyara zama idonta akan Rumaisau sai dai bata
tanka ba.
Ta budo sakonnin mahaukacin masoyi tun daga parko
tana mata bayani tare da yanayin da sakonnin ke samun
ta, har Rumaisau ta dire wa hapsar ta dauki abin, dan
daria kawai ta ke tuntsira mata sai da ta ga ranta ya baci
ne ma sannan ta dawo ta saurare ta .
To wai ke me kike zato?
Rumaisau ta dan harare ta.
Idan na zata mai zai kawo ni gidan ki?
Da ba sai nayi zamana nayi hukunci da zatona ba?
Hapsat na kunshe baki tace Allah Ya baki hakuri amma ni
nayi zargin ko a makaranta shapinki na jarida ne wani ya
boye yake wasa da hankalinki haka?
Rumaisa tayi saurin girgiza kai tace kuma a lambobin
wayata wadda bana hulda da kowa sai dangina
salonninsa na parko pa a layina dan alkawari yayi su layin

dako layika na cin amana shi dai bai kamata yaci ba,
hapsat ma bata son tsawaita wannan maganar akan layi
dan ta san makoma abin. Saboda haka tayi saurin tare
Rumaisau da cewa anya kuwa ba Yusha'u bane?
sai kawai Rumaisau tayi zuru tana kallon haprsat kamar
wadda hankalinta baya jikinta tace ko a tatsunia bai
kamata kiyi zaton yaya Yushau ba, me ya ani da yaya
Yushau zai bata lokacinsa a kaina?
Ko kin manta ne ?
Ai ko a layin mutane nake zaton mai turo min sako bai
kamata ki kawo yaya yshau ba.
Hapasar ta rausaya kai cikin sallamawa tace haka ne wai
dama da ake zargin mai wayar a cikin dangi..
A dan kupule Rumaisau tace ko mun rage mu biyu daga
ni sai shi ya kamata in pita waje neman mai turo min
sako.
Hapsat tayi shiru saboda rashin abun cewa,
kamar amsa ga abin da sukayiwa tagumi suna tantama
sai ga taken shigowar sakon mahaukacin masoyi..
Rumaisau na dubawa ta gashi ne, sai ta mikawa hapsat
wayar ba tare data karanta ba. Ta mike da hannu dunkule
tana dukan hannun hagu tare da pareti a palon.
''Rumaisau akace mutun mutun gida ne da rabin mutun
da wanda ba komai ba, wanda yake mutun shine mai yin
shawara da al'amuransa, kuma mai ra ayin madaidaici
wanda yake rabin mutun shine mai shawara amma bashi
da madaidaicin raayi ko kuma yana da madaidaicin raayi
amma ba shawara, wanda yake ba komai ba shine mara
shawara, kuma mara raayi.
Wani babban sahabi yace mana ''kuyi shawara da
mutanen kirki na gama yi miki sanin raayi madaidaici
wato tuni na san cikar rabautarki ashe ke guda ce naji a
raina kina son kiyi shawara akan harkar soyayyata haka
ne?
Ina sauraron abunda hukunci zai yanke min,
mahaukacin masoyi.
A pili Hapsat ta karanto sakon, zuciyarta na harbawa ,
hannunta sai karkarwa yake ...
.
GORAN DUMA 4.
.
.
a pili Hafasar ta karanto sakon zuciyarta na harbawa,
hannunta sai karkarwa yake idon ta cikin na Rumaisau
bakin ta na rawa tace da wa kikayi zancen zaki zo neman
shawara a gurina?
Babu tsoro a puskar Rumaisau ta kebe baki tace da
harshena dai ban pitar da sautin zan nemi shawarar wani
ba dazun nan a freedom na zanta da zucia ta ina pitowa
kuma kai tsaye na nupo gidan ki.
Mun shiga uku, hapsat ta pada tare da wurgar da wayar a
dan tsorace cikin jikinta yasa da sauri Rumaisau ta isa

gareta ta ruko kapadarta tana daria matsalata dake tsoro
Wallahi, baki san babu abin da zai iya samun dan Adam
ba sai abin da Ubangiji Ya kaddaro maka ba?
Bana tsammanin wani katon Al'amari cikin sakonnin
mahaukacin masoyi, kawai dai na gajia da bacin lokataina
da tunanina ne wajen wassapa shi yada sakonninsa.
Hapsat tayi kasake sai nan take ta dawo hakalinta ta mika
hannu ta dauki wayar ta sake duba lambar, nan take ta
dannan maballin kira, ta gama bincike dab da zata shiga
sai ta katse, kusan sau goma tana gwadawa hakan na
paruwa a karshe ta kwape lambar a wayarta ta jira nan
ma hakance ta paru suka dubi juna kowacce puskarta da
jarumta tace ina horonmu da addua da mayar da lamari
ga Allah Rumaisau karmu raya wani mugun abu a cikin
sakonnin nan mu kwantar da hankali mu kuma dauke su
ba komai ba ki bani kwanaki biyu nayi wani dan bincike
idan kin amince zan sanar da sani.
Rumaisau tayi saurin girgiza kai ban amince sani yaji ba
kin san sanida surutu maganar tana iya zuwa kunnen su
hajia ba tare da mun shirya mata ba,
cikin saduda hapsat tace hakane amma dai surutun sani
mai maana ce ki daina suppanta shi da wani aku...
Ta kare da zolaya duk kuma suka yi daria suna pitowa
harabar gidan suka ci karo da sani mai gai ya wangale
masa kopa ya shigo.
Suka tsaya jikin motar da Rumaisau tazo da ita suna jiran
karasowar sani . rumaisau ta rungume hannu a kirji tayi
puska ma'ana ta shiryawa shegantakar da sani mijin
hapsat zai zo yayi mata, tunda ya saba,
lallai kuwa idon masu hidima da ke karakaimar yi masa
maraba da xuwa bai tsure shi ya kasa girgije su ya nupi su
kai tsaye ba.
Hapsat na dan boye puska tana satar daria tayi masa
sannu da zuwa hankalinsa na kan rumaisau yana mata
kallon sama da kasa a karshe yace a'a yau mutanen
zuhdu ne suka tuno da mu?
Ta tuno da ita dai Allah Ya sani ba dan kai nazo ba.
Ta tare shi tana nuna masa hanyar wucewa ya tuntsire da
daria yace matsalata dake kenan sai ki dinga dagewa sai
kinyi pada kuma da yake ba dabiarki bane sai ba yayi miki
kyau har tapia ke nan.
Bazaki zauna mu gaisa ba gashi naga puskarki da abin
karatu...
Wannan kalaman nasa suka sata daria kawai ta bude
kopar mota ta shige suna dan barkwanci har ta pice...
Ta tattara duk wata sabga da zata iya dugunzuma mata
hankali a ratuwarta ta watsar, in sako ya shigo wayarta ta
daina budo shi inta hau fb ta share inboz sai komai nata
ya dawo dadai.
Sati daya a tsakani sai mahaukacin masoyi ya dawo
kwado mata kira a waya da parko share kiran ta dingayi
amma daga bisani sai ta yanke shawarar ta daga wayar

suyi ta ta kare ita da mai kiran, amma idan ta daga sai
iska shuuuu...
Babu motsin murya sunyi haka ya zarce sau goma a
karshe kawai sai tayi blockin din layin sa gaba daya a
wayoyin ta ba tare da jin cewa zata yi nadama ko kaico
ba.
Sati na biyu akayi rasuwa a kauyen su Rogo hajia nada
ganawa da liyitanta a Egypt daidai wannan lokacin bisa
larurar ciwon sugar da take pama dashi, alh kuma tare
dasu tapi saboda haka ta wakilta Rumaisau taje gaisuwar.
16/02/2013
tana zaune cikin yan uwa a gidan gaisuwar har bayan
sallar azahar sannan ta tapi gidan Goggonta karpe uku
take jira ta karasa ta dauko hanyar dawowa gida saboda
haka ta kimtsa komai tana zaune kawai.
Goggonta ta shigo tana mata wani irin kallo sannan tace
Yushau bai san ke hajia ta turo ba sai yanzun nan nake
pada masa.
Rumaisau ta daidaita maganae goggo a memory dinta
amma ta rasa gane ta inda maganar ko wani abu a cikin
ta zai ampaneta, saboda haka ta hadiye a sanyaye tace
ashe yazo?
Goggon ta amsa mata eh tun sape yana nan ai ina
tsammamin ma ya riga ki zuwa.
A dai ci gana da hakuri Ubangiji Yana son bayinSa masu
hakuri, rayuwar dai kina ganin yadda take hutsirewa kana
tsaka da kara mata burika, wadanda kake kokaawar
imma a sannu ko wadanda kake son sawa karpi rauwar
Garbati nan ta isa mutun aya Ruma, shekaru goma sha
shidda bai leko gidan ba yana can kudu da kyar akayi
masa kiranye ya dawo gida anata parin ciki da murna har
anyi masa matar aure kinga duka duka bai hada sati 2 da
dawowarba Allah Ya karbi abinSa , ai wannan gudun
dunia wajibi ga mai son cikawa da imani
rumaisau jinta kawai take ta san waazi take mata abin da
take waazi a kansa ma ta kasa tantancewa musamman da
yake akwai batun yushau da aka yi shimpidar waazin a
kasan ta kasa gane me goggo take son nusassheta akan
hakuri da yushau, wanne tawaye take da bukatar ta yi
hakri akan sa?
Amma dai da yake baya da jayayya sai ta rausaya kai tace
Allah Ya samu cika da imani.
Goggo na amsawa hakan yayi dadai da shigowar Yushau
cikin daikin puskar Rumaisau babu yabo ko pallasa ta
taishe shi sannan ta mayar da hankali akan wayarta, tana
dube dube goggo ta sa musu ido a pakaice yushau na
satar kallon rumaisau yace nansan bada mota kika zo ba
ko?
Ta dago sarato tana kallon sa amma yanayin puskar
hakurinta ta hana a gane yadda ta karbi batun muryarta
na rawa tace hakane motar haya na hawo.
Yadanyi dariar da yake tunanin zata sami matsuginni a

zuciyarta yace aina sanki da tsoron tukin daguwar hanya.
Ta share daria da batun nasa hanyar muyar da hankali a
wayar ta tana nazarin sakonnin makaranta rubutun ta a
jaridar Aminiya,
karpe nawa zaki tapi?
Ya pada kamar bai damu da yadda ta share shi ba ta dago
agogon hannunta ta duba ba tare da ta bude shi ba tace
ina jiran karpe uku ta karasa ne sai na komai shima ya
duba agogon yana padin nima ita nake jira sai mu koma
tare ta danyi kasake bukatar tasa na mata kururuwa a
kwakwalwa sai pamar kwakwalwar cetayi aikin da
zuciayar nata ta kasa, wato ta girgiza kai tace nayi
alkawari da dan mashin zai zo ya kaini tasha,
kai tsaye ya amsa mata sai na biki na dauke ki.
Bai jira cwarta ba ya pice abinsa. Sararo ta hada binsa da
kallo da sauraron wayarta mai take shigowar sakon
murya, sai da ya pice ta sauke idon akan wayarta cike da
rudani da mamaki shakarunta nawa da yankewar samun
sakon murya a waya.? A lokacin da take samun sakon
wayar ma daga wani muhimmin mutun ne a duniyarta.
Wasa! Tana budewa sai ga lambar mahaukacin masoyi
kawia sai ta mike ba tare data shawarci kanta ba , goggo
ta dan bita da kallo ita kuma ta tsawaita muryarta tace
goggo yau na manta banje hawa dutse ba, mintina
ashirin bari naje na dawo.
Goggo da yake ta san rumaisau da maganar son hawa
dutse bata zargi komai a ranta bam ta santa duk sanda
tazo ta kan ware lokaci ta shiga daji ta hau dutde shi yasa
yanzu ta amsa mata da cewa ai da yake ba zuwan
nustuwa yau kikayi ba kiyi sauri to ki dawo kije gidan
gausuwar kizo ku tapi kar ya gaji da tsumayinki ya tapi.
Ga yamma ga wahalar mota kinga babu dadi.
Rumaisau na kokarin picewa tace idan ya gaji da tsumayi
kawai yayi tapiyarsa dama ina da ajandar kwana idan hali
yayi.
Goggo bata samu amsa mata ba ta kule.
Ba zata iya tantance yadda akayi ba ta isa wajen dutsen
ba, ta sulale a sanyaye ta haye samansa sannan kamar
yadda ta saba ta siga juyawa a hankali tana hango
karshen gari (harizone )
wannan aladar muhimmiyar gaske ce a rayuwarta dan ta
kan kara mata imani da tsoron Allah wanda Ya halincci
wannan makekiyar duniyar da

2 Comments On GORAN DUMA
avatar
jannat

1 year ago

Reply

08062236094

avatar
jannat

1 year ago

Reply

08062236094

Please Login or Register in order to submit comment