Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tabbas Masoyine Bata
Shakkar Cewa Inbata Fara Shakuwa Da Sakonninsa Ba
Sannan Inta Ci Gaba Da Nesanta Kanta Da Sakonninsa
Dole Taikewa Kamar Yadda Ita Da Zuciyarta Suka Yarda
Sunyi Kewa A Kwanakin Da Suka Gabata Tazauna Tajanyo
Wasikar Datakarbo Daga Gidan Waya Adireshin ANNUR
MIKYWAY CAFE DAGA ABUJA?
CAFE DIN DAKE ABUJA INDA KUMA TASAI WAYOYIN
HANNUNTA BIYU TASAI MODERN DINTA INDA TA
SAI KYAMARARTA INDA TASAI......... KAI BAZATA IYA
KIRGAWA BA.
Inhar Taje Hankalinta Baya Kwanciya Tanaji Ajikinta
Kamar Tana Da Nasaba Da Gurin, Tanata Tunani Ta Bude
Wasikar Ko Kuma Kawai Ta Share Taikarfin Hali Ta Bude
Taga An Rubuta ""RAYUWATA ZAN BAYYANA MIKI KAINA,
NAKI MAHAUKACIN MASOYI"" TARE DA SA HANNUNSA,ta
Ce Wato Mahaukacin Masoyi Daga Annur Mikyway
Yake,ya Abinyake?
Innalillahi Wa Inna Ilaihirajiun
Tanamamakin Yaya Haka Tafaru,,dago Kan Nan Dazatayi
Saitaga Alamun Mutum A Inuwar Labule Ta
Taga ,yanaganin Ta Dago Da Sauri Ya Bar Wajen,takori
Dukan Da Zuciyarta Take Cikin Zafin Nama Ta Isa Tagar Ta
Yaye Labulen Tahau Leke Leke Amma Bataga Komai Ba
Sai Motocinsu Dake Gurin Kwanyarta Tafara Dawo Mata
Da Abindata Karanta A Takardar Mahaukacin Masoyi
Zanbayyana Miki Kaina Shine Wato Yanzu Ya Bayyana A
Labule Taja Baya Tana Raya Abubuwa Masu Wahalar
Fassara Wanda Tagama Hakikancewa Mahaukacin Masoyi
Ba Aljanibane Amma Abinda Mahaukacin Masoyi Keyi
Yawuce
Azaceshi Cikin Mutane,to Waye?
Ta Fizgo Hijabi Ta Zira Ta Ce Zan Binciko Waye
Kai,abindayakama Naikenan A Farko, kasha Zamanka Zan
Nemoka,
a Falo Ba Yushau Ba Hajiya Sai Sumoli Tafice Itakuma
Sumoli Ta Tsargu Don Haka Ta Mike Ta Hau Lekenta Ta
Taga Ruma Nafita Ta Hango Yushau Yafito Ta Tsakanin
Motoci Kaitsaye Ya Nufota Take Ta Tsargu Da Ganinsa
Kuma Ta Alakanta Hakan Da Mahaukacin Masoyi Fuskarta
Daure Ta Tsaya Ina
Zaki Haka?

Ta daga Takardar Tsakaninka Da Allah Yaya Yushau
Bakada Masaniya Akan Wannan Takardar?
Yanamata Kallan Rashin Fahimta Ya Karba Yana Nazarinta
Cikin Yamutsa Fuska Kirjinsa Na Dukan Uku Uku Basaikin
Hadani Da Allah Ba Ruma Wallahi Bansan Komai Akanta
Mene yafaru?
Ta Amsa Takardar Tana Nazarinta Yanzu Ina Daki Naga
Inuwar Mutum Naleke Nata Labule Ko Kaganshi
Tunda Tanan Ka Bullo, Kallon Juna Sukai Ido Cikin Ido
Wanda Yushau Yake Da Yakinin Hakan Baitaba
Faruwa Tsakaninsa Hakanyasanya Masa Muguwar Kasala
Kirjinsa Nata Bugawa Da Sauri Taja Baya Ayanzu Kam
Tasan Yushau Ya Wanke Hannu Nezai Danna Maballin
Kunno Mata Danjar Bakin ciki Wahala Da Kunan Zuciya,
Tsoronta Daya Kada
Hakan Yafaru Gaban Abbah Dan Zata Iya Keta Idan Alhji
Ta Ce Batasansa Tajuya Zata Bar Gurin Ga Mamakinta
Saitaji Yushau Ya Ruko Hannunta Yaja Ta Baya Dasauri
Suka Shiga Tskanin Motoci Tsoro Da Shakku Tuni
Sungama Mamaye Ta
Yaya Yushau Menene Haka?
Sai Ga Hawaye Daga Idansa So Nake Na Baki Kalmar Da
Ban Taba Baki Ba Duk Tazo Kunnenki A Makare Saidai
Niyanzu Take Shan Sharafinta A Kirjina Alhalin Ina Cike
Da Jin Haushin Ciwan Rashin Zuwanta INASONKI
RUMAISAU WALLAHI INASONKI
Dasauri Ruma Ta Ce Kadaina Rantsewa Meyasa?
Indaza A Laluba Zuciyarka Da Kyau Sai Antarar Da Kaffara
Takamaka
Bajinsona Kake Ba Illah,,,
yatareta Ruma Duk Abinan Danakeji A Kirjina Game Dake
Kicemin Baso Bane?
Taja Baya Hawaye Suka Fara Zuba Daidai Lokacin Idanta
Yakai Kan Sumoli Ta Ce SO DAYANE TAK TUNI NA
SADAUKAR DA NAWA GA WANDA YA CANCANCESHI DUK
DA UBANGIJI BAI NUFA ZAMUCI GAJIYAR SA NIDA
WANDA NASO DINBA,ILLA JIN KUMAJIN RADADIN
DANAKE JI YAZAMA
KAFFARA,AMMA NAKA SON KAGA INDA KA SARAYAR
DASHI,TA NUNA MASA SUMOLI
Yakalli Sumoli Baiji Zuciyar Sa Ta Sauya Ba......
Yaitsaki Yamaida Kallansa Ga Ruma, Ruma Ta Ce "Nikuma
TAWA RAYUWAR BA A KIRKIRETA DAN TAZAMA FANSAR
FARINCIKINKA BA YAYA YUSHAU MURUFE WANNAN
CAFTAR AUREN JUNA DA MUKAI A
BAYA KUSKURENE DA CIN AMANAR ZUCIYOYINMU
WADANDA DUK BA HAKA SUKESO BA HAKA ZALIKA
IYALAN DAMUKA SAMAR BA HAKAMUKASO BA NI NAI
DANASANIN HAIHUWAR SU DOMIN TAUSAYIN
RAYUWARSU KAI KANA BAKINCIKIN HAIHUWARSU
DOMIN TAUSAYIN RAYUWAR SU KAIKANA BAKINCIKIN
HAIHUWAR SU SABODA BASU FITO DAGA MACEN DATA

CANCANCI HAIHUWAR 'YA'YANKA BA,
KI Bar Maganar Nan Dan Allah Tafara Tafiya
Ya Ce Zansa Karfi Da Lallashi Kidawo Rayuwata Zanbaki
Abinda Ban Baki A Baya Ba Wato So Da Kulawa,
Takada Kai Ta Ce ToGA HANYA NAN AMMA KAMAR AKWAI
WANDA YAFIKA KARFI DA IYA LALLASHI AKAN HANYA
WATO DAN AUNTY.
.
To en gidan nan ku zama shaida Ruma ni take so , kunji
dai da bakinta..lol.
.
Sai jibi ma dora.
.
Dan Aunty
GORAN DUMA (p 52)
.
.
Takada Kai TaCe To GA HANYA NAN AMMA KAMAR AKWAI
WANDA YAFIKA KARFI DA IYA LALLASHI AKAN HANYA
WATO MAHAUKACIN MASOYI IN ALAMUN KARFI YANAGA
MAI KIBA SAI INGA KAMAR ZAI IYA KAYARDAKAI
Tunda tai maganar Tai Taga Yanayin Sa Ya Sau Dan taga
Ko suna Da Alaka Da Mahaukacin Masoyi,ransa A Bace Ya
Ce wanene Mahaukacin Masoyi?
Wannan kuwa Ba cin Fuska Bane?Zakijerani Dawani
waima Mahaukaci Asan Dan kinga Nafada Sonki Ruma?
Saitasami Kanta Dayimasa Murmushin Mamaki Sannan
Takauda Kai Batare Data Amsamasa Ba Tawuce Cikingida
Ta
Barshi Agurin Motocin Sumoli Naleke Ta
Window,gabadaya Zuciyar Ruma Ta Zaku Da Sanin
Mahaukacin Masoyi,tanazama Adaki Sai Ga Sakonsa Ta
Waya Wanda Ke Nuna Shaidar Yagama Kallon Diramarta
Da Yushau HANKALINA SOYAKE YA KWANTA ASHE BANI
NAKE YAUDARAR ZUCIYATA
BA?
TAJIMA TANA RADAMIN ZAKI SOMU, Cikin Karkarwar
Hannu Tasami Kanta Da tafa Gajeren Sako Taimasa Amsa
A Karo Na Farko,WAYE KAI?
INA SON IN SANKA,
Taitajiran Amsa Har Karfe Goma Na Dare Tadinga Kiran
Wasu Layiyyinkansa Bata samuba Taji Afuwar Son Tasan
Mahaukacin
Masoyi A Yau Tamkar Dandayaso Fitowa Cikin Mahaifiyar
Sa Dan Haka Tanemi Abinda Yake Mata
Dadi A Duniya Tarasa,sai Ta Hau Social Network Ta Tura
masa KALAMANKA NA NUNA JARUMTA A
SOYAYYA DA RAYUWA,AMMA AYYUKANKA SUN KASA
TABBATAR DA HAKAN,YAKIN BOYE DAGA MUTUM
BOYAYYE?
LALLAI BUYA YAYIN CIMMA BURI ALAMACE TA
RAGONTAKA,IDAN BA A CIKIN RAGWAYE KAKE BA

INASON INSANKA,
Tafi Awa Biyu Sannan Tasami Gajeriyar Amsa Ta Inbox
Dinta A Facebook,LOl!
BANSAN NI RAGONE KO JARUMI BA,ABINDA KAWAI
NASANI NI MAHAUKACINE A SOYAYYARKI
MAHAUKACINDA IN BAI SHIGA SAHUN DAKARU A
KWANJI BA DA ADALCI ZA AKIRA SHI BARDE A
SOYAYYA,KINA SON GANINA?
NAZACI KINCI ALWASHIN GANONI DA KANKI,
TANAKARANTA Wanna Sakon Nasa Tamike Zumbur Kawai
Saitasami Kanta Da Kwankwasa
Kofar Dakin Baccin Hajiya Tsawon Mintuna Biyar,sai Ga
Hajiya Tafito Daga Sashen Alhji Cikin Magagin
Bacci Fuska Cike Da Tsoro Tana Duban Agogo Wanda
Yanuna Sha Biyu Da Rabi Lfya Jikin Ne Ruma?
Arikice Take Idanta Fal Da Kwalla Takama Hannun Hajiya
Inason Zuwa Abuja Gobe Indawo Jibi,kinemarmin
Wannan Damar Wajen Alhji Dan Allah Meyafaru?
Wani Abu Kike Da Bukata Kikejin Mu Bazamu Iya Yimiki
Ba Sai A Abuja?
Kina Girgiza Kai Kina Kuka?
Amsarki Na Nufin E,h Da A,a Kenan,ba Abin Kuka Bane
Hajiya,raunina Ne Kawai Yakawo Kukan,a Barni Inje
Abuja Nai Alkawarin Da Nadawo Zansanar Dake Komai
kuma Na Rantse miki Da Allah Sai Kaddarar Ubangiji
Inzan Dara Jib
Ruma Na Sauka A Tashar Utako Maimakon Ta Dauki
Shatar Mota Zuwa Gidantake Wuse,kawai Saita
Umarci Dan Tasi Dayakaita Milkway Cafe Bata Da Yakinin
Zatajima A Ciki Ko Bazata Jimaba Dan Haka Tasallami Dan
Tasi Tataka Cikin Barin Jiki Dana Zuciya Ta Shiga
Kantin,babu Abinda Ke Yawo Aranta Irin Sakon
Mahaukacin Masoyi Na Safiyar Yau INAJI A JIKINA A YAU
ZANGA MASOYIYATA,
Kamar Kullum A Milkway Na Baya BaBu Abinda Ya Ragu A
Kallon Mayatar Da Ma,aikatan Gurin Kemata Saima
Karuwa Datake Tsammanin Yi,itama Ta Dake Ta Janyo
Daddatan Magani Ta Ci Kuma Tadinga Tafiyar Kasaita Har
Taisa Bangaren Datafi Wayo Wato
Yanar Gizo,ina Son Ganin Manajan Gidannan Malam
Bayan Sallamar Ko Gaisuwa Bataimasa Ba To Madam Kira
Shi Za Ayi Ko Kuma Kai Ki Gurinsa Za Ayi Akaini, Kaitsaye
Tafada Cikin Cin Magani Tamike Tana Rataya Jaka,zo
Muje,bayan Yagama Jimaminsa,har Ofishin Manaja Tai
Arba Dashi Gajeren Mutumin Nane Wanda Ya Ce Kallanta
Yafi Kallon Talabijin,suna shiGa Taga Fuskar Rashin
Gaskiya Atare Dashi Lfya Garba?
Yatambaya Arikice Bayan Tafiyar Garba Office Din Yai
Shuru Shiyasakata A Kwandan Shara Yanata Tafa Sako A
Wayar Sa Itakuma Tanata Nazarin Ofishin To Hajiya
Inajinki, Nazo Ne Inji Dalilinda Yasa In Nazo Gidan Nan
Nake Zama Muku Magiji In Ban Manta Ba Kaida Kanka Ka

Taba Fadamin Nafi Majigin Dadin Kallo
Mudin?
Kalmar Dayafada Cikin Alamar Shakansa Ma Baiyarda Da
Kansa Ba, Kudinfa Ta Amsa Rai A Bace,yai Kasake
Hankalinsa Nakan Waya, Shikenan Abinda Kikeson Sani?
A Amsa Min Wannan Tambayar Mana Sai Aji Idan Akwai
Wata, Karon Farko Dayai Murmushi, Kin Tsargu Ne Kawai
Amma Ni Ban San Munakallanki Kamar Majigi Ba,nidai
Kawai Nasan Bama Iya Ganinki Bamu ShiGa Rudani Ba
Amma Har Yau Bamu Gano Dalili Ba,duk Da Haka Kiyi
Hakuri,
ruma Taji Kamar Ta Kwarfa Masa Mari Saboda Haushi
Amma Ta Hadiye Ta Balle Jaka Ta Fito Da Takardar
Mahaukacin Masoyi Wadda Ya Aiko Ta Gidan Waya Kuma
Daidai Wannan Lokacin Sakon Mahaukacin Masoyin
Yashigo Wayarta,
ASHE DA GASKE KINA SON GANINA DAN ALLAH MEYA KAI
HAKA DADI A DUNIYATA TA YANZU?
TA Hada Da Wayar Da Wasikar Duba Wasikar Nan Waya
Rubuta
Ta Agidannan Kuma Sa Hannun Watake Dauke Dashi Duk
Taimasa Tambayoyine Cikin Hanzari Da Hadiye Rikitarta
Manaja Yafi Minti Biyar Yana Juya Waya Da Wasika
Sannan Yadago Muryar Sa Na
Rawa Ya Ce,lambar Da Sanya Hannu Duk Na NAZIFI
MUHAMMAD NE
Nazifi Muhammad?
NAZIFI MUHAMMAD?
Tasake Maimaitawa A Rude Ganin Yakasa Amsa Mata
Kuma Yana Bintada Wani Rudadden Kallo,amma Bakinsa
Yakasa Furta Kalma Ko Guda,taja Kujera Datun Tuni Take
Tsaye Rike Da Majin gininta Ta Zauna Inatambaya Kayi
Shuru?
Madam Tambaya Kikayi Kenan?Nazaci Maimaita Sunan
kike Domin Yanamiki Dadin Fada?
Ta Hadiye Doki Da Mamakinsa Kuma Datakara Saitajanye
Dukkan Rudanin Da Fuskarta Ke Nunawa Ta Barwa
Zuciyarta Tanaji Dasu,to Ba Bu Laifi Inason Ganinsa,baya
Gari Takara Zuramasa Ido Kuri Tsawon Lokaci Ta Ce
Menene Matsayinsa A Gidan Nan?
Shine Mamallakin Wajen,da Sauri Tajuyo Amma Naji
Kakira Sunanshi Kaitsaye?
Yadan Fara Dariya Aikamawa Take A Daure Mai
Daurewa,hakane Ina Son In Sani Mutum Ne Ko Aljan?
Mamaki Ya Bayyana Karara A Fuskar Sa Bakinsa Na Rawa
Ya Ce Wanne Irin Aljani Kuma?
Dama Aljannu Abokan Huldarmu Ne Dahaar Zan Shaida
miki Shi A Mamallakin Gidan Nan,
tatareshi Cikin Ci Da Zuci Kukusani Ni Ba Matsayinsa Nazo
A Sanar Dani Ba,shinakeso In Sani Dan Haka Karmu Ja
Maganar Kasanar Dani Ranar Dazai Dawo,
To Kahadani Dashi A Waya Cikin Jimami Ya Ce To Bara

Nanemi Izini Agurinsa Yatafa Sako Yaturamasa
Sannan Ya Tsaya Dako,can Sai Ga Amsar Amincewa
Sannan Ubangida Nasa Yakirashi A Waya,kaitsaye
Shikuma Bai Daga Ba Saiyamika Wa Ruma Tare Da
Mikewa Yabar Falon Tadaga Wayar Dajin Karfin
Gwiwar Juya Harshe Yadda Taso,amma Daga Sallamar Sa
Ya Warware Mata Duk Notikan Laka Da
Karfin Hali Baki Yahau Karkarwa Jiki Yadauki Bari,duk Da
Haka Bata Iya Amsa Sallamar Ba,ranki Yadade Ance Kina
Son Magana Dani,?Tattausar Muryar Tasa Takara Dukan
Dukan Kunnenta Da Zuciyarta Kawai Saitaji Wani Irin
Rauni Ya Mamayeta Dan Haka Batun Tai Maganarma Bata
Tasoba
Rumaisau Kinajina Kuwa?
Cikin Mamaki Tadanyi Wani Nishi, Waye Wa,,,,wa Takasa
Direwa Kawai Saita Hakura Rumaisau Yaya Jikin?
Kawai Saitasami Kanta Da Sheshekar Kuka Itakanta Takasa
Tantance Abinda Yasata Kuka baitankamata Ba Tsawon
Lokacin dataji Kamar Bawa Kanta Hakuri
Amma Kafin Tafadi Abindata Sak'a Fada Ya Rigata Cikin
Wata Irin Murya Mai Rauni, "kin Dauki Hakki. .
.
Dan Aunty
GORAN DUMA (P 53)
.
.
Kin Nemi Tarwatsa Zuciyata Mai Sauraronki Kina
Kuka,,dakin San Hakane Da Ba Kice A Hadaki Daniba Gara
Yin Umarnin Duk Inda Nake Nazo Nasameki Zanyi
Biyayya Nazo Kuma Ina Da Yakinin Inkinga Kaunarki Dake
Kwance A Kwayar Idona Zaki Tabbatar Inkinyi Kuka
Agabana Zaki Cutar Dani,maganganunsa Sunkara Rudata
Ainun,data Lalubi Ilahirinta Sai Ta Tarar Ita Kanta Neman
Manta Kanta Take,bare Ta Tuna Maganar Dazata Fadawa
Wannan Majanunin Magana Wadda Ta Shafi Jiya Dayau
Dinta Shida Ba A Toshe Masa Basirar Ba Saiyaja Sunanta A
Hankali Tamkar Yaimata Allura
Saigata A Farke,bakinta Yagaji Da Bari Ya Furta Abinda
Kwakwalwartata Ta Kera Watakila Ina Kuka Ne Saboda
Bansan Da Irin Mutumin Danake Tare Ba,,ina Kuka Bisa
Yadda Kake Wahalar Da Zuciyata Tare Da Gangar Jikina
Yakatse Ta Cikin Muryar Lallashi Kinga Yi Hakuri Ki Koma
Gida Zanzo
Nasameki Har Gidan Ya Katse Wayar, Ruma Tai Tsuru Da
Wayar A Kunne Batare Data Iya Saukewa
Zuciyarta Na Bugawa Fat Fat Hajijiya Na Dibanta Saidai
Takasa Motsawa Nanda Can Sai A Manaja Ya Ya Ce Mata
Kano Kika Nufa Ko Wuse?
Ta Juyo Tana Binsa Da Kallo Da Alamar Tai Mamakin Jin
Kanonta A Bakinsa Da Wuse Wannan Ya Tabbatar Mata
Duk Shakiyancin Da Ake Mata Yana Da Masaniya Saitaji
Ranta Yai Mugun Baci Ta Ajiye Masa Wayar Sa Takarasa

Goge Hawayenta Kunnuwanta Kuma Na Sauraronsa Yace
Yayi Umarnin Duk Inda Kika Nufa Idan Kina Da Bukata A
Bayar Da Mota Akaiki Bata Tsinka Ba Kallan Dataimasa
Yana Tattare Da Amsar Banida Bukata Ta Wuce Kai Tsaye
Batare Data masa Sallama Ba Ta Bar Office Din, Shikuma
Baidamu Da Basarwarta Ba Yatake Mata Baya Ya Rakota
Har Bakin Titi Ya Tayata Jiran Tasi,bai Mata Magana Ba
Itama Hakan Bayan Sun Tsayar Da Motar Shiya
Sallami Mai Tasi Yaimata Bankwana Ita Ko Tankasa
Bataiba, Tana Mota Tanata Lissafe Lissafen Yadda Nazifi
Yake Da Yadda Har Ya Wuce Makadi Da Rawa A
Sha'anoninta Har Dana Tsakaninta Da Zuciyarta Wadanda
Suka Yi Kama Da 'ya'yan Cikin GORAN DUMA Wanda Sai
Anfasa Za A Iya Lissafawa Tai Shige Da Fice A Duk
Lungunan Zuciyarta Dakuma Magabatan Alamuranta
Musamman Cikin Rayuwarta A Abuja Dakuma Milkway
Danta Gano Ko Ta Taba Cin Karo Da Wannan Mai Kiran
Kansa Mahaukacin Masoyi,amma A Sunan Manajansa Ya
Shata Masa Wai Nazifi?
Ta Shafa Sosai Ba Ta Tuna Shi Dinba Sai Can Ta Dan So Ta
Tunano Shi Bayanta Tariyo Sha Biyar Ga Watan
Nuwamba Na Shekarar Dubu Biyu Da Sha Biyu A
Kwakwalwarta Shugaban Milkway Ya Fado Mata,amma
Acikin Basaja Yadda Yanzu Zata Kasance Cikin
Shakkunshine Nazifi Kokuma Wani Daban 15 Nov 2012
Sunyi Da Nusaiba Kanwar Mijin Yayarta Balaraba Zatazo
Raka Ta Milkyway Dan Ta Siyo Ipad Satika Kadan Da Fara
Rubutunta A Jaridar Aminiya Don Saukaka Mata Aiki,sai
Nusaiba Taimata Waya Cewa Suhadu A Milkyway Ta
Tsayar Da Motar Innarta Honda A Harabar Milkyway
Tanemi Kiran Nusaiba A Waya Amma Saita Tarar Wayarta
Ba Bu Ko Kobo Haka Tajima Zaune Cikin Motar Tana
Waige Waigen Shigowar Nusaiba Dazama Yafara
Gundurarta Saita Fito Ta Rumgume Hannu Ta Jingina Da
Motar Tana Ta Faman Baza Idon Kan Motoci Da Mutanen
Dake Shige Da Fice A Wajen,cikin Haka Wata Shudiyar
Jeep Ta Shigo Harabar Milkyway Hade Da Tagumi Ta Tsura
Mata Ido Har Tazo Ta Gifta Ta Kadan Tatsaya Kafin Kuma
Ta Gifta Ta Din Ne Suka Hada Ido Da Matukin Motar,wani
Matashi Baki Mai Dogon Hanci Da Fararen Idanuwa Yana
Sanye da Bakin Wando Da Shudiyar Tshirt Da tambarin
Mikyway Cafe Ta Kawar Da Kai Saidai Jikinta Ya Ci Gaba Da
Batashi Baidauke Idanuwansa
Daga Kanta Ba Harya Wuceta Kamar Mintuna Goma Bai
Bude Motar Sa Yafito Ba Tana Tsaye Tana Ci Gaba Da
Waige Waigenta Har Idonta Yazo Zagaye Kan Motar Sa
Adaidai Lokacin da taGa Yana Gyaran Madubi Da Alama
Ita Yake Karewa Kallo,ranta Yai Mugun Baci Har Ta Zabga
Masa Harara A Duhu Tayi Tsaki Tare Da Duban Agogo
Cikin Takaicin Nusaiba Asannanne Tasami Azancin Shiga
Ciki Tasanya Kati A Wayarta Dan Kiran Nusaiba Ta Rufe
Motarta Tanufi Ciki Agurguje Ya Rufe Mota Ya Biyo

Bayanta Don Haka Takara Daga Kafa Dab Da Isarta Ta
Waiga Saitaga Manaja Nadan Rusunawa Matashin Nan
Yana Masa Barka Da Zuwa Tasake Hada Ido Da Shi Tadan
Motsa Baki Alamar Bataji Dadi Ba
Ka Share Yallaban Nan Yau Malam Kakira Ni Da
Muhammd Kawai Domin Acikin Tarko Nake Neman
Maitayani Yakin Kubuta Nake Batare Da Daddawar Da Na
Kamo Ta Subuce Ba,bata Damu Da Zantikanta Da Suka
Biyo Baya A Tsakanin Matashin Da Manaja Ba Domin
Zaurance Suke Harma Da Sauya Harshe Zuwa French
Wanda Gaisuwa Kawai Ta Iya Dashi A
Cikin Zafin Nama Kuma Sai Gasu Gaban Kantar Lokacin
da take Mika Dubu Dayan Katin Sun Dauke Hankalin Mai
Bata Katin Dayimasa Zance Shima Cikin Harshen Da Bata
Lakanta Ba Dan Haka Yakasa Dauko Mata Katin,ranki
Yadade Barka Da Yau,inji Matashin Nan Wanda Yadamu
Da Kallonta Bayan Yazo Dab Da Ita Ya Tsaya,,yauwa Barka
Dai Kamar Nasan Fuskar Nanfa Afuwa Cankowa Nakeson
Nayi
Yasa Nadamu Da Kallanki, Ta Gyara Tsayuwa Da Kyar Ta
Ce Hmm,,kamar Munyi Karatu Da Kyar Ta
Ce,,hmm,,kamar Munyi Karatu Tare?Bata Tankamasa
Ba,hm,,,bani Katin Mana,,,
yadan Yi Turus Cikin Kallanta Sannan Ya Ce Ranki Yadade
Kozaki Miko Min Wayar Na Kwashe Miki Lambobin
Ansami Matsala A Katin munan Idan Ba Ai Taka
Tsantsanba Batai nazarin Komai Ba Tamika Masa Wayar
Karaf Manaja Ya Amshe Wai Shizai Samata Da Alama Na
Takuramiki Ko?
Ba Haka Bane Wai A Ina Mukai Karatun Tare?
Alamar An Kureshi Ya Ce A Bayero Univer Sity Mun
Karanci Aikin Jarida Wannan Yasa Tadan Sauko Harda
Murmushi Hakane Yaya Bayan Rabu Sai Alkhairi Tuna Min
Suna Ta Ce Cikin Kwanciyar Hankali Rumaisau Aliyu
Ahmad Haka Kuwa Na Tuna Takara Dubansa Da Kyau Da
Alama
Tanada Shakku Saidai Yadda Yayi Fuska Saitaji BaBu
Bukatar Ta Tambaye Shi Kokuma Tayi Ja Inja
Dashi To Hausawa Sunce Bata Karya Wuya To Kuwa Ta
Yafo Ta Harzuwa Lokacinda Za A RaBu Saura
Dame?
Sai In An Kuma Haduwa Haka,nikuma Sunana Nazifi
Muhammad To Madallah Ta Tattara Dukan Hankalinta Ga
Abokinsa Gajere Wanda Take Tsammanin Abinda Yake Da
Wayarta Ya Wuce Loda
Kati Ta Tsuke Fuska Ta Ce Masa Malam Yayadai?
Kar Ka Wuce Gona Da Irifa!Yaki Dagowa Ya Dubeta Yana
Bata Amsa Habadai Aimu Bamu Da Irin Ma Shimuke
Nema Madam Yana Rufe Baki Yamika Mata Wayar Ta
Karba Tana Tura Baki Bata Tanka Wa Kowa Ba Ta Bar
Gurin Kwaji Dashi Tafada A Fili Ta Fice Daga Farfajiyar
Tana Neman Nusaiba ,nusaiba Takaraso Suka Shiga Sayen

Wayar Inda Batasamu Siyen Ipad Din Datai
Niyya Bama Sakamakon Garabasar Waya Mai Tsada Da
Suka Yi A Kananun Kudi Abinda Ta Iya Tunowa
Kenan A 15 Nov 2013
Amma Tayi Ta Tuno Fuskar Sa Takasa Ballantana Ta Iya
Tuno Ko Ta Kalli Kafarsta Taga Kofato Shiyasa Data Tuno
Hakan Baiwani Sanyaya Mata Raiba Yadda Ranta Ke Jagule
Saitaji Inama Ace Ta Wuce Kano Yau?
Duk Tsiya A Yanzu Kano Tafi Abuja Kwanciyar Hankali
Domin Basajar Kano Ta Waya Da Social Network Kawai
Ake Mata Amma Ta Abuja Bayan Rainin Hankali Tattare
Dake Databa Rai, Ta Karkare Ta Hadiye Damuwarta Bayan
Ta Tarad Da Gudan Jininta Hamida Ba Bu Lfya
Wani Kurji Ya Fito Mata A Kirji Tanata Faman Jinya Saita
Fake Da Tausayin Hamida Ta Hada Kukan
Tausayin Da Basajar Mahaukacin Masoyi Ta Ci Kuka Ta
Koshi A Zuwan Ciwon Hamida Ki Gode Allah Kawai Da Ba
Kauye Kika Bayar Da !Yar Riko
Ba,munyi Tunanin Huda Mata Kirjin Nana A Gida Amma
Muka Nufi Asibiti ashe Damunyi Hakan Da Danyen
Hukunci Muka Yanke,inji Momin Ruma Ruma Ta Tsayar
Da Kuka Tazaro Ido Cikin Mugun Kaduwa Lallai Allah Ya
Tseratar Da Hamida Domin Da Anyi Hakan Akwai Matsala
Saita Biyewa Momi Wajen Hamdala Ga Allah Har
Washegarin Momi Najiran Jin Wani Abu Daga Ruma Akan
Zuwanta Abuja Domin Hajiya Tasanar
Mata Komai Amma Ruma Taki Tankawa Duk Da Cewa Ko
Gabadaya Aka Duba A Jikinta Tana Nuna Damuwa Da
Kasala Amma Iyakarta Haka Cikinta Mai Hadama Ya
Hadiye Shi Kadai ya Hana Bakinta Furtawa Sai Ga Tama
Tana Shirin Komawa Kano Momi Takasa Daurewa Saita
Tareta Da Zancen
Tunjiya Nake Kawaici Inajiran Jin Kin Furta Abinda Ke
Damun Zuciyarki Da Rayuwarki Amma Ga Alama Kina
Son Na Karya Billena Na Tambaya,
Ruma Tayi Walai Da Ido Tana Murmushin Yake Lah!
Mekika Gani Momi?
.
.
Dan Aunty.
GORAN DUMA (P 54)
.
.
Ni Ba Bu Abindayake Damuna,kinganki Kuwa?
Komai Naki Yana Nuna Damuwa Inana Ture Wayar
Damukai Da Hajiya Kenan,ruma Tayi Kasake Bata Da Ta
Cewa Tunda Hajiya Ta Burma Mata Ciki,momi Ma tadan
Ja Fasali Fadamin Ruma Meke Faruwa?
Naso Ace Saida Kikazo Gidan Nan Sannankika Nufi Sabgar
Taka Kawoki Abuja Nayi Niyyar Sanyawa
Abiki A Boye Aga Abinda zakiyi,amma Saikika Shammaci
Niyyata Har Yanzu Ruma Bata Da Niyyar

Tankawa So Ma Take Ta Fashe Da Kuka Saboda Tunano
Yadda Tayi Kwanar Jinya Da Zuciyarta Kowa A
Kuntace,kame Kamen Tashoshin Ainihin Mahaukacin
Masoyi Ya Cunkushe Wa Kwakwalwar Amma Har Cajinta
Yakare Bata Canko Wadda Zata famata Shi Tar Tar Ba
Anya Wannan Rayuwar Zata Dore Ciki?
Ta Ina Zata Bi Ta Kubuta?
Kawai Sai ta sami Kanta Cikin Hawayen Momi Kam
Tausayin Da Rauninta Akan Ruma Tana Hadiyewa Har Taci
Nasarar Data Bata Kwarin Gwiwar Yimata Nasiha
Zanyi Murna Idan Ba Tarkon Soyayya Kika Fada Ba Ruma
Dan Banasan Kifada Tarkon Son Mutumin Da Bai
Cancanta Ba Dan Baisan Muhimman cin ki Ba
Haryaja Ragamar Rayuwarki Cikin Son Zuciyar Sa
Kawai,mace Irinki Datafi Sauran Mata Rauni Tana
Bukatar Taka Tsantsan Acikin Soyayya Kinfi Kowa
Sani,aranta Ta Ce Kamar Momi Nasan Cinka Abinda
Ke Wakana A Tsakaninta Da Mahaukacin Masoyi Saidai
Kurkuren Lis Cewa Ita Tafada Tarkon So Ba Wata Hallitar
Ce Tafada Tarkon Son Nata Ba Kila Momi Bata Taba
Hasaso Ko Tarkon Sonka Aka Fada Kana Iya Shiga
Hadariba Ta shiGa Goge Hawayenta Batare Data Kammala
Tunaninba Inafatan Dazara Kinkoma Zaki
Cikawa Hajiya Alkawarin da kika Daukar mata?
Da Sauri Ruma Tadago Tayi Ma Momi Duban Rashin
Fahimta Momi Tamike Tana Shirin Barin Wajen Tana
Amsa Mata Tafadamin Kin Mata Alkawarin Kina Komawa
Zaki Sanar Da Ita Dukkan Abinda Ke
Akwai Ruma Tashi Ga Gyada Kai Batare Da Hayyaci Ba To
To,,,,dama Bazan Karya Alkawari Ba,
************
tana Isa Kano Daidai Lokacindatake Shiga Harabar
Gidansu Sakon Mahaukacin Masoyi Nafado Kasancewar
Wayar Na Hannuta Cikin Dukan Zuciya Ta Kashe Ido Ta
Hau Dubawa BARKA DA ISOWA RANKI YADADE,IDANKIN
HUTA KILA ANJIMA NA SHIGO MUGA JUNA
MAHAUKACIN MASOYI
Bataji Bakinciki Kofargaba Game Da Sakonsa Ba Tadai
Samikanta Cikin Saurin Shigewa Cikingida Wanda
Batafara Mamakin Neman Dalilinsa Ba Sai Gata Tashiga
Gidan
Mutangida Nata Hidimar Murnar Yimata Maraba Rashinki
Ko Na Awa Dayane Agidan Nan Kufai yake
Mayaimin Da Gidan,inji Mubarak Koyai Dariya Amma
Ruma Murmushin Yake
Hajiya Tun Daga Shigowar Ruma Tadora Mata Ido Ta
Cemasa Idan Tai Aure sai Muga Yadda Zakai Mubarak
Zaiyi Magana Tatare Shi
Kajira Nai Sallar Magariba Bar Tadin Ka Wuce Alwala
Yawuce Yana Dariya Aima Zan Barta Ta Huta Sai Gobe
Zamu Fanshe Hirar Kiyi Sallah Kici Abinci Muzauna Ko?
Fuskarta Ba Bu Alamar Wasa Kilatayi Hakan Ne Dan Kar

Ruma Takawo Mata Wargi Hakanyasa Ruma Tadinga
Komai Cikin Fargaba
Tana Saka Yadda Zata Sanar Da Hajiya Murdadden
Labarinta Da Mahaukacin Masoyi A Kar She Tatarar Da
Bata Da Zabi Illai Tasanar Mata Komai Tinda Tai Alkawari
Da Wayarta Akai Tattaunawar Tadinga Nunawa Hajiya
Komai Na Sakonninsa Duk Da Hajiya Takidime Amma Bai
Hanata Magana Anutse Ba Meyasakika Ci Gaba Da Rike
Wannan Abin A Zuciyarki Kekadai?
Kuma Mekikaje Yi Abuja?
Hajiya Taimata Karin Bayani Ikon Allah HajiYa Tafadi Cikin
Jinjinawa Tare Da Nanata Kalmar Duk sunyi Shuru
Zuciyar Kowanne Tai Nisa A Saka Wani Aikinda
Zuciyartata Ta Hada Cikin Lissafin Shine,fargabar Allah
Yasa Anjima Din Nasa Karta
Zamo Tsakar Dare Dan Karya Bayyanar Mata Abinda Tafi
Zatonsa,wato Aljani Ko Kadan Batason Ya Bayyana A Haka
Batare Da Dalilin Tsoronsa A Aljani Ba Saitare Da Dalilin In
Aljanin Ne Sun Rabu
Kenan,inkin Amince In Sanar da Alhji Wanna Katon
Labari In Ganin Dole Maza Su Shigo Ciki Hajiya Ta
Katsewa Ruma Tunani Duk Da Ita Ma Bata Hattama Nata
Tunanin Ba,amma Tasanya Masa Karfi,mujira Yau Da
Gobe Da Jibi Dan Ganin Abinda Zai Biyo Baya,karmu Tashi
Hankalin Kowa Hajiya Kila
Lamarin Baikai Natashin Hankali Ba,yaya Zanyi Da
Mominki Mai Jiran Nakai Mata Kanun Matsalarki?
Hankalin Momi Atashe,,,rumaisau Rumaisau Tamike Cikin
Alamun Son Ficewa Daga Falon Fuskarta Na Nuna Gajiyar
Jiki Data Zuciya Ki Kyale Ta Kawai Hajiya Yadda Momi
Take Damuwa Cikin Matsalolina
Inason Duk Abinda Zataji Akaina Indai Zan Iya To Taji Mai
Dadi,,shikenan hajiya Ta Fada Badan Taso
Ba Ta Bi Ruma Da Kallo Har Ta Kule Tanadan Dingisa
Kafarta Wadda Kem Bayan Kwanar Fargaba Tare Da
Tsammanin Bango Zai tsage Mahaukacin Masoyi Ya Bullo
Ruma
Batasami Bacci Ba Saikarfe Hudu Saura Hakan Ya Janyo
Da Kyar Ta Iya Katse Bacci Ta Gabatar Da
Sallar Asuba Akan Lokaci Sannan Ta Koma Ta Ci Gaba Da
Ramuwar Bacci,karfe Tara Daidai Wayarta Ta Farkar Da
Ita Da Shigowar Kira Saidata Koshi Da Kallon Agogo Har
Kiranya Katse Sannan Tasami
Taba Wayar Daidai Lokacin Wani Kiran Yasake Shigowa Ta
Daure Ta Hadiye Kasalarta Ta Daga Tare
Da Sallama Yushau Ya Amsa Cikin Kuzari Nayi Ta Baza Ido
Inganki Gidan Atika Jiya Har Dare Bangankiba Kuma Naji
Atika Ma Na Mitar Baki Zo Dubata Ba,ta Basar Ta Ce Yau
Zanje,yushau Yadan Jinkirta Sannan Ya Ce Karfe Nawa?
Ina Son Mu Hadu Ne Akwai Muhimmiyar Maganar
Danake Son Mu Tattauna,bansan Lokacin Dazan Shiga Ba
Tafada A Raunane,amma Ta Raunana Muryar Tatane Dan

Ta Basar Da Zuciyarta Wadda Ta Dauki Zafi Inta Bar
Muryarta Dazafi Kila Ya Rage Mata Kima Shikuma Saiya
Marairaice Kidaure Ki Tsara Lokaci Shigar Taki Ko Saboda
Ni,
Ba Lokaci Zanzo In Batamiki Ba Ruma Ragowar
Rayuwarmu Nakeson Muyi Wa Garambawul,
tayi Iyakar Bakin Kokarinta Tai Magana Amma Takasa Don
Kar Ta Cika Rashin Mutunci Da Kyar Ta Ce Ok
Yushau Baidamuba Yasake Zagewa Da Rarrashi Ko Wuni
Zakiyi?
E,h Wuni Zanyi Toki Saka Idan Ganina Bayan Laasar Yayi
Kyau Ta Amsa Masa Ta Kashe Wayar
*******
A Gaggauce Yushau Yahau Shirin Fita Alhali Ya Shaidawa
Sumoli Yaukansa Ciwo Yake Kodake Da Biyu Ya Ce Haka
Dankartadameshi
Yasamu Damar Yin Tunani Hanyar Dazasu Samo Masa
Ruma Na Biyu Kuma Mugun Haushinta Yakeji,jiya Ya
Dauketa Yakaita Gidan Atika Da
Kwadayin Haduwa Da Ruma Yadinga Zarya A Gidan
Tsammanin Ganinta Amma Har Dare Ba Bu Labarinta Ta
Ce Masa Kaikuwa Dan Allah Ko Bazaka Sauya Motar Nan
Ka Daure Kakai Ta Gareji Adan
Kwaskware Injinta Ayimata Sabon Fenti Fisabilillahi Kai
Ko Kunya Bakaji Kowa A Danginka Shar Shar Da Motocin
Nunawa Sa,a Amma Kaikana Fama Da Karfen Shekaru
Aru Aru Haka Zuciyar Yushau Ke Tafarfasa Daidai Yadda
Sumoli Take Masa Magana Tunda Uban Wani Bai Sayi
Shar Ya Baniba Sai A
Kalleni Da Wanda Allah Ya Bani Sai Dai Idan Anga Ban
Cancanci Zama A Irin Wannan Duniyar Da Wannan Motar
Ba To A Iya Kokarin Rufe Ido A Bude Kar Aganni,
ai Bakafadi Ba Yushau Idan Ka Saka Wa Ubana Da Zagi Da
Cin Fuska Tunda Yadauki Aure Yabaka Da Wuya Ba Bu
Dadi Ina Zaune Ina
Rufa Maka Asiri Yakada Kai Cikin Fushi Sumoli Takara Da
Cewa In Ma Sake Zagina Zakai Yushau Zageni Mana,,,,
insauran Gashin Kumarka Bai sanyani Kuka Zaginka Ai
Bazai saniba Karamin Misali Auranmu Kusan Shekaru Uku
Banta Ba Batan Wata Ba Amma Dan Masifar Mammako
Sha Katafi Kakasa Kai Ni A Nemo Dalilin Rashin
Haihuwata,,.,,ta Dawo Cikin Kwalliya Malam Inakake
Shirin Zuwa Bayan Kace Bakajin Dadi Ya Cemata Yasamu
Kiran Gaggawa Daga Office Ta Ce Bara Nadauko Mayafi
Mufita Tare Inba Gidanku Zakaje Ba,gidan Dakana Rabe
Rabe Kana Komai Amma Baka Kasa Motsa Kwanjin Son
Zawarci Ba,yafice Bai Tanka Ba
Tadawo Da Mayafi Ya Ce Wai Malama Ina Zakibine?
Muje Kasaukeni Gidan Atika mana Kashiga Ka Biya Kudin
Lesunan Ankon Suna....
,
dan kari, ni ma dole naje gidan Atikar nan nasha kallon

yadda zata kaya,
ko da akwai pasinja anan gidan??
.
Dan Aunty.
GORAN DUMA (P .55)
.
.
Dubu Nawa?
Dubu Arbain Da Takwas Mana Ta
Amsa Masa Kai Tsaye Tana Taunar Cingam Kas Kas,cikin
Tsawa Ya Ce Daga Dubu Goma Bazan Karamiki Ko Ficika
Ba In Baki Da Kudi Ki Mayar Musu Kayansu Ba Bu Jimawa
Sai Gata Tadawo Dauke Da Lesunan Ta Zube Masa Kan
Gado Cikin Fusata
Gasunan Katafi Dasu Ka Mayar Bani Dubu Goman Zanbi
Wata Hanyar In Samo,ai In Na Ce Dakai Zan Dogara Har
Abada Araba Danni Zan

2 Comments On GORAN DUMA
avatar
jannat

1 year ago

Reply

08062236094

avatar
jannat

1 year ago

Reply

08062236094

Please Login or Register in order to submit comment