Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuka
ya dinga fizgirta, amma ita ma ta dinga hadiye shi, a
karshe cikin rawar murya ta ce.
"Yaya Yusha'u me nake yi na zafi haka?"....
Dan Aunty.
GORAN DUMA (P 32)
.
.
Ya tsare ta da ido, ya ce. "Tsakaninki da Allah idan Auwal
ne za ki zauna da cikinsa tsawon wata biyu ba ki sanar da
shi ya yi
farin ciki ba?"
Takaici da rauni ya cikata, dan haka ta saka masa ido ta
kasa tanka masa.
Ya ce. "Ki amsa min mana!"
Ta girgiza kai tana dubansa kai tsaye da alama ya fara

'kure ta.
Ta ce masa.
"Idan na amsa wata'kila kai tsaye ka yiwa amsar tawa
kallon wautacciya, in daga zuciyata kai tsaye amsa zata
fito."
Cikin gadara ya ce.
"Idan ma a haukace zata fito ina jiranta. Na kuma
tabbatar ba zata sauya daga yadda na zace ta ba".
Hawayen idonta ya fara gangarowa, tana kallonsa kai
tsaye ta ce.
"In da Auwal ne ba zan kai tsawon wata biyu da ciki ba
tare da ya binciko da kansa da kansa ba,
cikin wata biyun nan wanne irin amai ne bana yi, wanne
irin zazza6i ne ba na yi, wacce irin kasala ce bana yi?
Yaya Yusha'u duk sanda zan gabatar maka da wadannan
matsaloli 'kar'kari ka ce min ok Sannu, Allah Ya sauwa'ke
sai ka ga na galaibata ne kake kawo min maganin
shawara, ko kuma
tarkacen magunguna daga kyamis...
Saboda haka ne sam ba ni da 'karfin gwiwar sanar maka
da wani abu da ya dangance ni..." Rumaisa'u bata kula ba
ne, tuni Yusha'u ya zo wuya taf! Tana direwa kuma ya fara
zubar da bala'in da ya 'kunshe.
"Ka ji ba! Rumasa'u ni kike fadawa wannan maganganun
saboda rashin ladabi ko?
Saboda tsabar ke butulu ce wacce irin kulawa ce bana yi
miki?
Duk namiji ne zai jure wannan jarabar laulayin naki
amma ina iyakacin kokarina kina nuna min na gaza,
kuma saboda tsabar raini ki keta idona ki nuna Auwal ya
fi ni matsayi a gurinki?...
Dadin abin ya gama yi miki nisa, duk yadda kike jin fitsara
dai ba zaki dauko gawarsa ki gina mata daki a cikin gidan
nan ki ce kishiya ne shi ba...."
Bai ko saurareta ba fuuu! Ya fice ya bar dakin sai ya bar ta
da binsa da kallo, lokaci guda kuma hawayenta ya dauke
saboda maimaita kalmar
KISHIYATA da Yusha'u ya ambata tare da tuno yadda
Auwal yake ambaton kalmar da KISHIYI.
Kusan sati guda Yusha'u na gaba da Rumaisa'u, ba gabar
magana ba har da na dauke hannu a shigo
mata da abubuwan masarufi dangin ciye-ciyen kayan
gina jiki, kaza, balangu, kifi da kayan itaciya, ''Inko hakane
gwara ya daina fita. Don ni ban ga amfanin dukiyar da
iyalina ba zasu
amfaneta ba'' wadanda su kadai ne ba ta rasa ba a abin
da ya kamata kada sickler ya rasa su, saboda haka 'kanjikinta ya 'karu, ga nata na asali ga na raunin ciki sannan
ga na 6acin rai.
Suka sake share wasu sati biyun a haka, bayan muguwar
rama yanzu ta fara d'ashewa alamun jini ya yi mata
'karanci, babu ciwo dai sosai, sai yawan kwanciya da bin

sanyi wanda shi ma alamu ne na
'karancin jini a jikin sickler.
A karo na hudu da Innarta ta kirata dan ta ji batun
zuwansu asibiti, sai ta fada mata gaskiya don 'karya ta kan
fada mata cewa 'mun je', yau cikin kuka sai ta fada mata.
"Wallahi Momi ko soron 'kofar gida ban taka da sunan
asibiti ba, a halin yanzu kuma ina cikin wani
hali dan ina ganin alamomin rashin jini... Amma don
Allah Momi mu nemi wata shawarar kar ki yiwa Yaya
Yusha'u magana, tuhumata yake da kai 'kararsa."
Momi ta rasa abin da zata ce saboda mugun takaici,
kawai sai ta ja numfashi ta ce.
"Shikenan, ba ni awa daya na yi tunani zan kira ki".
Ba ta ko jira cewar Rumasa'u ba ta kashe wayar, kai tsaye
kuma ta kira Yusha'u cikin tsananin fushi, ko
gaisuwarsa ba ta amsa ba, ta ce.
"Yusha'u ka tuna na ta6a fada maka cewa, ina da juriya
akan komai amma ban da akan Rumasa'u?
Zan iya yi maka kawaici akan komai amma ban da na
wasa da ranta, mun shiga sati na uku a maganar da na yi
maka ba ku nemi hanyar asibiti ba, yanzu da na
tuntubeta ta tabbatar min tana tare da alamomin
'karancin jini. Wallahi Yusha'u ba zan iya zuba ido ka yi
min sanadin Rumasa'u ba..."
Muryarsa a tausashe, amma maganarsa zazzafa dan cewa
ya yi. "Ai babu mai iya kashe wani sai Allah!"
A fusace Momi ta ce masa.
"Au haka ka ce?
Shikenan Allah Ya kaimu gobe ni kuma zan zo in nuna
iyawata akan hanawa ka zama silar Rumaisa'u, in ma ka
6oye manufar shirya
kasheta ne saboda an aura maka ita bisa tilas ni zan yi
maka gatan rabaka da aurenta..."
Ba ta ko jira cewarsa ba ta kashe wayar, nan take ya hada
gumi kashir6an dan ya san Momi ba wa'ka take ba,
zazzafar mace ce shigen mahaifinsa. Tsab zata zo kuma ta
dauke Rumaisa'u dole kuma maganar ta je kunnen
mahaifinsa, wanda zai iya mummunar sa6a masa.
Bai yi dogon nazari ba ya hau kiran Momi tana 'kin amsa
kiran nasa, shi kuma ya nace cikin tsabar dakan zuciya,
amma yana mita. "Mahaifin Rumasa'u ya zama hoto,
dama yawancin masu d'amarar nan matansu ke juya su,
haba me za a yi da auren 'yar mace?"
Ire-iren mitar da ya dinga yi ke nan yana nacin kiran
wayar Momi, kusan sau ashirin sannan ta
daure ta daga. A ladabce ya ce.
"Don Allah Momi ki yi hakuri, wallahi za a yi yau din nan
ba zamu kwanta ba sai an je asibiti, na rantse miki".
Ta sauke hucin 6acin rai, sannan cikin lumana ta ce.
"Yusha'u ka yi tunani da kyau, bai kamata sai an yi
yun'kurin gwada maka 'karfi zaka tausaya wa 'yar
uwarka ka yi mata abin da ya kamata ba, ko babu igiyar

aurenka akan Rumaisa'u ai abar ka tausaya mata ce,
yanzu ta ce min jininta ya yi 'kasa sosai,
idan aka sake nan da kwana biyu, sai dai ka ji batun yi
mata 'karin jini".
Cikin 'kas'kantar da murya ya ce.
"In Allah Ya so ba za akai wannan matakin ba Momi, ki yi
hakuri". Cikin sakewar Murya ta ce."To na yi, Allah Ya yi
muku albarka".
Da ya koma gida da yamma,
Rumasa'u ta kawo masa abinci a dakinsa sai ya dinga
satar kallonta. Ta yi mugun ramewa, sannan
ta yi wani irin fari, idanunta kuma sun yi wani 6ulu-6ulu
sun kukkunbura. Ta zauna jim amma kafin ya 'karasa cin
abincin sai ta tashi ta koma dakinta ta kwanta, yanzu
babu abin da yake mata
dad'i sai kwanciya, hatta dan karance-karancen jaridu da
mujallun da ta ke samun yi a da yanzu gagararta yake,
duk da ma dai Mubarak me daukar nauyin kawo mata
jaridun jarabawa ta 6oye shi. A haka ta jiyo motsin
shigowar Yusha'u, haka kawai sai ta ji gabanta na faduwa
dan ta
ha'ki'kance da kyar idan ba gadar mata da wani takaicin
ya kawo shi ba.
Sai dai ya shigo dakin cikin sakin fuska ya nemi stool ya
zauna idonsa a kanta, ta dan dube shi da kyau sannan ta
lumshe ido.
Ya yanke shirunsa da cewa.
"Kwanciyarki ta yi yawa, ko yaushe ke kenan a akwance".
Ta bude ido ta dube shi, amma ta kasa cewa da shi
komai. Ya sauke numfashi ya ce. "Jaridancinki dai a gidan
aurenki da mijin aurenki
kike sauke shi. A zamanmu dad'i da wahalarmu gaba
daya babu na sirri kunnen iyayenmu da 'kawaye kaiconki
Rumaisa'u, wallahi ba ki morre hali ba..."
.
Dan Aunty.GORAN DUMA (P 33)
,
,
Ta kokarta ta tashi zaune ba tare da ta shirya ba ta ji kuka
ya kwace mata babu kakkautawa, yana kallonta zuru yana
dokin ta yi shiru har kukan nata ya fara ta6a ransa,
babu shiri ya cimmata ya fara rarrashi. "Ki yi hakuri ni
ban fada dan cin fuskarki ba, na fada ne dan ki ankara da
laifi da cutarwar da ki ke min fisabilillahi ina mutunci a ce
duk sirrin gidanmu a kunnen Hajiya, Momi da sauran
dangi da 'kawaye..."
Ta dakatar da shi cikin kuka. "Ba gudun cin fuska ya ba ni
kuka ba Yaya Yusha'u, illa mummunar shaidar da ka yi
min a matsayinka na mijina har kana tir da halina....
rayuwar nan ba ta da garanti musamman ta mutum
irina... Idan Allah Ya kar6i raina yanzu wannan shaidar
'kila ta yi tasiri a kaina... Dole in yi kuka dan ban san

yadda zan gyara ka yarda da ni ba".
Ya 'kara tausasa murya ya ce. "Ki daina kai 'karata gurin
Momi ko Hajiya, ki dinga 6oye sirrin gidanmu ba fa jahila
ba ce ke Rumasa'u, kin sani yana daga nagatar mace 6oye
sirrin mijinta..."
Ta jima tana kallonsa cikin hawaye, sannan ta kwace
kafadarta ta koma ta kwanta alamar ta ma rasa abin da
zata ce.
Ya yi saurin dagota ya ce. "Babu abin da zaki ce?"
Yana rufe baki ta amsa.
"Idan in ce dan in kare kaina ne ba zan ce din ba,
dan kar mu ci gaba da 6atawa juna lokaci, amma zan iya
cewar da zata iya zame maka wani nauyi a
ayyukanka biyu na duniya da lahira cewar tawa ita ce,
duk matsananin halin da zan shiga kuma duk yadda
Momi zata kwakkwafe ni ta ji matsalata ba zan kuma fada
mata ba, in ka kula da ni kanka Yaya Yusha'u, in ka yi
sakacin da na rasa raina sai ka shirya amsa tambaya
wajen Ubangiji fa'kat!"
Yusha'u ya yi wuri-wuri ya rasa abin da zai ce mata, sai da
kyar ya lalubo shi.
"Abin da kika fadawa Momi ke nan ina sakaci da ranki?
Amma sam ba ki yi min adalci ba Rumaisa'u".
Ta goge hawayenta duk da wasu sun kuma kunnonwa, ta
dube shi ta ce.
"Kana dai so sai na kare kaina ko? To ka san dai mutum
ba zai rayu ba sai da jini?
Dube ni".
Ta shiga gwale idonta fatar ba'kinta tare da nuna masa
tafukan hannayenta, sannan ta dora.
"Jinina ya yi 'kasa sosai, da ko ba ni da ciki dab nake da
shiga mawuyacin halin da zai kai ni matsayin 'karin jini.
An yi maka batun fa'idar zuwana asibiti tun sayi biyu da
suka wuce ba ka dauki batun da muhimmanci ba, ban yi
tsammanin zai zama laifi ba dan Momi ta binciki halin da
nake
ciki na sanar mata ina da matsalar rashin jini, ko babu
komai ya fi sama ta ka a ce musu ga ni kwance ana 'kara
min jini... ko su zo su bayar da jini a 'kara min".
Da ya rasa bakin magana sai ya fanshe akan kalamanta na
'karshe.
"Lokacin da ba ki karkashin ikona ma na ba ki jini
Rumasa'u bare ki yi min gori... in leda goma ne zan
iya baki ba leda daya ko biyu ba". Yana rufe baki ta amsa
masa.
"Rigafi ai ya fi magani".
Ya ce, "Me kike nufi?"
Ta amsa masa, "Ka yi tattalina kar na rasa jini ya fi
burgewa akan ka bar ni na rasa ka bayar da leda
goma a 'kara min".
Yanzu ya rasa abin da zai ce mata bilha'k'ki, sai ya 6uge
da duban agogo lokacin da aka rera kiran sallar magriba,

ya wuce kai tsaye batare da ya kare kansa ba.
Abin mamaki ba ya 'karewa a duniya, karfe tara na dare
Yusha'u ya shigo mata da Dan'Isiya mai kyamis a nan
unguwarsu dauke da akwatin magunguna da allurai.
Dan Isiya ya tsare ta da lacca da hudubobi bayan ya gama
karade ta da tambayoyin da ake wa sababbin zuwa awon
haihuwa, mata masu lafiya ba sicklers ba. Kallonsa kawai
ta ke kamar wani duron ya'kin
neman za6e, wani lokacin kuma ta sauke ganinta akan
Yusha'u wanda ya hakimce shi a dole ya yi abin arzi'ki.
A karshe Dan Isiya ya ce, tun da cikin bai kai ko wata uku
ba ba sai an yi awo ba, yanzu zai dauki jininta ya tafi da
shi lab. gobe zai kuma yi mata allura yanzu sannan ya
bata magunguna musamman na 'karin jini.
Duk Rumaisa'u na kallonsa bambarakwai har ya fito da
sirinji ya zu'ki jininta, sai da ya zu'ko allurar da zai mata
ne sannan ta magantu. "Tun safe ban ci abinci ba bai
kamata a yi min allura ba, zai fi kyau a bari sai gobe".
Dan Isiya ya mayar da ruwan allura cikin kwalba yana
cewa.
"Eh gaskiya ne, in Allah Ya kaimu goben sai na zo na yi
miki".
Yusha'u kuma ya ce.
Amma kina kallonsa ya zu'ko?
To ya zauna ya jira kici abincin mana ya yi miki..."
Ta girgiza kai ba tare da ta dube shi ba, ta ce. "Nidai sai
gobe".
Dole ya kyale ta, ya mayar da hankali ga Dan Isiya da ke
zube masa magunguna yana masa bayaninsu.
Yusha'u ya ce.
Ina fatan akwai na 'karin jini?"
"Akwai".
Yusha'u ya ce masa.
"Yauwa, ka hada mata da maganin kasala da na 'karfin jiki
ba ta da aiki sai kwanciya".
Nan ma Dan Isiya ya ce.
"Duk akwai".
Ya dure musu magunguna tuli a leda ya mi'kawa Yusha'u,
shi kuma ya mikawa Rumasa'u ya wuce
raka Dan Isiya. Ya dawo mata da gasasshen nama da
nonon roba
mai sanyi. Da kansa ya nemi faranti a kicin ya zuba
naman ya kawo ruwa da lemo ya zube, sannan ya ce
mata.
"Ki zo ki ci ki samu ki sha magani".
Tun da ta ga 6arin jikin da ya ke ta san ba na Allah da
Annabi ba ne, tattalin raya darensa kawai yake,
dan haka ta zage ta yiwa naman cin 'koshi cikin 6oye
6acin zuciya, dan ta san idan ma ba ta taimaki
kanta ta ci ba babu abin da Yusha'u zai raga mata,
gara ma ta kori yunwa ko ta rage wa kanta wahala.
Har ta gama cin naman da fargabar abubuwa biyu, wato

yadda zata ji jiki a shimfidarsu da kuma yadda zata
gujewa shan wadannan magungunan da wata
'kila in ta sha su yi ajalinta.
Bayan ta gama ya dauke farantan da tarkacen kayan da ta
sha lemo da yagot, sannan ya dawo ya janyo ruwa ya
janyo ruwa ya tsiyaya mata a tambulan kana ya janyo
ledar magunguna ya fara 6alla. Kijrinta sai dakan uku-uku
ya ke ta dube shi ta ce.
"Yaya Yusha'u har na gaji da gaya maka ba na shan
maganin da duk ba likita ne ya rubuta min ba".
Ya tsayar da 6allo maganin sororo yana kallonta, cikin
hadiye bacin rai ya ce.
"Da yake nan ya ba ki wadannan magungunan?
Dauko miki shi da na yi har gida bai zama garkuwar da
zaki zarge ni da shi ba musan abin da muke ba?"
Ta girgiza kai a raunane, tace. "Likita daban mai kyamis
daban Yaya Yusha'u, in ya san abin da yake yi na tabbatar
ba lallai ya san yadda ya kamata tafiyar da sickler ba...."
Ya tare ta da alamar rarrashi, Rumaisa'u bata zargi karya
ba, ya yi kewarta yana kuma son ya fanshe a yau, dan
haka ya 'ki su yi fada, ya ce mata. "Tun da kin iya karatu
kin kuma san kan magungunan me yasa ba zaki dube su
ki gani idan ya yi miki ganganci ba?"
Tun da an ce Mutum ba ya 'kin ta mutane, ta mika hannu
ta kar6i magungunan na farko da ta dago
sai ta tarar capsil ne na 'karin jini. Ta daga maganin tana
duban Yusha'u fuskarta cike da takaici ta ce.
"Daga inda ya dauki maganin karin jini ya ba ni na san bai
san aikinsa ba..."
Yusha'u ya tareta cikin tsabar mamaki.
"Amma dai ke kika ce kina da 'karancin jini ko?"
Ta amsa masa cikin sabawa da takaici.
.
Abbas Abdulkadir Hada Hada ( Dan Aunty.)
GORAN DUMA (P 34)
.
.
Ta amsa masa cikin sabawa da takaici.
"Ba zan iya 'kirga sau nawa na yi 'karancin jini daga
haihuwata zuwa yau ba, amma ko sau daya likita bai ta6a
ba ni maganin 'karin jini ba, sickler ba ya bu'katar
maganin 'karin jini, domin cikin kowanne irin maganin
yana dauke da sinadarin Iron, su kuma sicklers suka sha
maganin 'karin jini to
jininsu zai daskare kamar gasara, abin da zai faru da su
kuma Allah ne kadai zai iya faru da su kuma Allah ne
kadai zai iya iyakance shi".
Yusha'u ya yi shiru kawai yana kallonta, ba wai bai yarda
a ita ba, amma in ya bi ta kamar ya fadi, sai
dai dole faduwar zai yi, dan a yanzu rashin dabara ne ya
jagula mata rai, sai ya daure kamar wani soko
ya ce. "Shikenan sai ki duba sauran".

Ta mayar da maganin 'karin jini cikin ledar, tana cewa.
"Ka yi hakuri Yaya Yusha'u, babu maganin da zan iya sha
a ciki, in na sha na jefa rayuwata cikin hatsari".
Yanzu Yusha'u ya kasa hadiye 6acin ransa, dan har ga
Allah yana ganin Rumasa'u amfani ta ke da zurfin iliminta
tana nuna masa iyakarsa, komai ya yi bai iya ba dan
tsabar rainin hankali ita da ta karanci
jarida wai ita ce zata kushe wanda ya karanci lafiya.
Ta kushe wannan ta kushe wancan komai cikin gadara
kamar wata uwar mutane.
Ya yi kokari ya rage zafin 6acin ransa a muryarsa, ya ce
mata.
"Amma dai idan kin yi min haka ba ki yi min adalci ba,
kawai dan ki nunawa duniya kina iko dani,
kina kallo in kawo mutumin duk ba ki musa ba sai bayan
tafiyarsa ki ce ba kya son aikin in mayar masa da
magungunansa?
Wannan ai ya yi kama da wulakanci..."
Ta katse shi a sanyaye.
"Yaya Yusha'u idan na katse hanzarinka a gabansa shi ne
wulakanci, gara in bari ya tafi muyi komai mu biyu... wai
ma don Allah Yaya Yusha'u har sau nawa zan fada maka
ba na shan magani kai tsaye?
Tsawon zama a gidanku ka ta6a ganina a kyamis...?"
Shi ma ya tare da tsawa.
"Ban sani ba! Ni dai kin wulakanta ni, abin da nake ta
gudu ke nan, duk mai zurfin karatu ta 'kalubalanci
mijinta, ta yi jayayya da shi, ko ta raina masa azanci
sunnarta ce, kamar ni ma ban ta6a allin nan ba.... Haba!
Ban da kaddara me zai kai ni?
Ba gara ma mutum ya tafi kauye ya auro ba".
In dai da sabo ya kamata Rumaisa'u ta saba da wannan
gori da cin fuskar, duk kuma 6igiren son
zuciya da rashin gaskiya.
Tun kafin abin ya yi tsawo ai ta mi'ke ta bar masa falon ba
tare da ta ce ci-kanka ba, ta shiga bandaki
ta wanke baki, sannan ta bi lafiyar gado tana addu'ar
Allah Ya sa ma ya yi zuciya ya tafi dakinsa ta huta.
Sai dai addu'ar tata ba ta kar6u ba, dan ko mintuna
ashirin ba ta yi da kwanciya ba ya shigo ya sauya
kayan kwanciya, ya zauna bakin gado ya ce mata.
"Yanzu ya ya kike so a yi?"
Ta dan zura masa ido sannan ta ce.
"Da me?"
Ya ce, "Da maganar 'karancin jinin bana son a kai ga
maganar sai an 'kara miki jini".
Ta yi murmushin gajiya da abu daya, ta ce.
"Idan ba zan yi laifi ba kuma ba zai zama umarni na ba ka
ba, asibiti ya kamata na je gobe".
Ya janye mata abin rufa ya fara murza tafin kafarta yana
cewa.
"To ya ya zan yi?

Ai kawai na zama mijin ta ce sam-sam ba na yi miki
kwarjini. In Allah Ya kaimu gobe sai mu je asibitin."
Ta janye kafarta tana 'karamar dariya.
"Allah Ya kai mu goben. Yanzu sai ka tashi ka tafi
dakinka..."
Ya tare ta lokacin da ya fara nade su cikin bargon.
"Haba yarinya kin ma isa, ai rashin kwanjin nawa bai kai
nan ba".
Da sapiyar ranar sai ya nemi hanzarin cewa na manta yau
akwai ni da zuwa rogo, satin da ya wuce Alh yayi min
maganar kaddamar da wata rijiya da yake a waya ne bai
min cikakken bayani ba, sai naje naji, ki bari idan na
dawo da yamma sai muje asibitin,
ta kada kai da sauri cikin bugun zuciya , rijiyar Awwal ce
ta kuma tabbatar idan Yushau ya jiyo gaskiyar maganar
Allah ne kadai ya san yadda zai tashi hankalinsu.
Saboda haka ta wuni cikin zullumi da tashin hankali gami
da pargaba,
lallai kuwa' yushau ya shigo gida karpe goma na dare
puskar nan tasa kamar an saukar masa sakon mutuwa ko
hutawa baiyi ba ya para surparta da bala'i irin wanda bai
taba yi mata kamar sa ba, tun tana kokarin kare kanta har
ta zubo masa ido tana kallo cike da tsabar bakin ciki a
tsukun wannan lokacin da za a kawo mata tayin mutuwa
babu abin da zai hana ta amsa,
sai sha daya da kusan rabi ya hakura ya tapi dakin sa yana
ta mita, wai don me tana auren sa tana auren soyayyar
wani har da irin wadannan sadaukarwar da ya rantse
kuma ko kwatar abin da tayiwa Awwal shi bazata iya yi
masa ba,
lokacin da yake bala'in idon Rumaisau a kekeshe yake
babu alamun kuka saboda masipar bacin rai, sai bayan
pitarsa ta samu kukan ya goce mata,
ta dinga yi babu kakkautawa dan ta hakkake duk rashinsa
ya jepata cikin wadannan masipun auren Yushau ke wa
sila. Da akwai Awwal kila da yanzu tana daga cikin matan
da za a lissapa su a sahun parko na jin dadi da sa'ar miji,
amma yanzu ratuwarta da lapiyarta na wani hali na tsaka
mai wuya,
wajen karpe biyun dare ta nupi dakin kwana saboda jin
numpashinta na shakewa, da zummar tilasta kanta bacci
dan ta manta wadannan bacin ran ko dan kai lapiyarta ta
sami nakasu.
Sai dai da alama ta makara dan numpashinta yaci gaba
da shakewa lokaci daya kuma cikinta yayi wani irin
juyawa tape da ciwo sai ga damshi-damshi ta sami kanta
a ciki,
nan da nan ta para ambaton Innalillahi wa inna ilaihi rajiun . Ta san lallai tana cikin tsaka mai wiya, bari zatayi, zata
bubar da jini alhali dama bai ishe ta ba,
ta barke da kuka ta isa bandaki kamar dama ana jiran ta
shiga bandalin ne jini ya balle , tun tana tararradin rasa

gudan jininta (wato danta) har ta dawo pargabar tsira da
ran ta,
saboda yadda xiwon ciki ya addabe ta ,jini kuma yaki
tsayawa har numpashinta na neman daukewa.
Da rarrape ta sawo dakinta ta janyo waya sai ta rasa ma
wanda zata buga ta sanarwa , ko yushau bai gargade ta
sanar da iyayen su halin da take ciki ba, ita kuma tai
alkawarin ko zata mutu ba zata kuma sanar da su din ba.
To idan ta kira wani a yanzu ta pada masa wannan
mummunan labarin sai sun tuhumi ina yushauu ?
Ko wacce irin laya za a yi musu sai sun parke.
Numpaninta na kokarin kubucewa ta dinga kiran yushau
yana kallon kiran yana sharewa, kusan sau goma sai da
kyar ya daga cikin tsaki sai dai a wannan lokacin ta para
pita hayyacinta sai ta kasa magana illa wata irin
sheshsheka,,,, nan da nan yushau ya dawo cikin azancinsa
da gudu ya watsar da wayar ya doshi dakinta ya same ta
kwance gaban gado cikin jini a sume.
Halin da ya same ta shi kansa ba dan yana jar zuciya ba
kila ya sume cikin tsabar rikita da barin jiki ya dago ta
yana padin na shiga uku zan kashe yar mutane,babu bata
lokaci ya janyo durowa ya dauki ID card dinta na shaidar
kasancewarta sikila da gudu ya pice ya pita da mota,
sannan ya dawo ya dauke ta ya nupi asibitin nasarawa,
da yake akwai group din jininta a jikin Id card dinta ba a
tsaya jiran diban na yushau ba aka makala mata wani.
Har azahar na washegarin ranar Rumasa'u tana cikin
wani hali na kasa gane kai, Yusha'u ya yi
nadamar abin da ya yi matu'ka, musamman da ya sami
tabbacin cikin Rumasa'u ya zube, hannun
agogonsa ya koma baya a matsayinsa na mai dokin ganin
dan kai. Tun sha biyun rana Mummy ta sauka cike da
tashin hankali wanda ta yiwa Yusha'u kallon tsana a
fakaice ba, babu wanda ya san tana yi idan ka dauke shi
Yusha'u.
Da azahar da suka sami damar shiga dakin kowa cikin
jimami, Hajiya da iyalanta kaf in ka dauke Mubarak da
tilas ya je makaranta, ga Alhaji ga Mummyn Rumasa'u
tare da Balaraba.
Ko zama Mummy ta kasa yi tana tsaye rungume da
hannnu ta 'kurawa ledar jinin da ake 'karawa Rumasa
ido, idon Mummy ya fara fitar da kwalla saboda tsabar
tausayin 'yarta. Ta ji a ranta akwai sakaci cikin hatsarin da
ya faru da 'yarta, sakacin da ta
tabbata ba 'karshensa ke nan ba, za a kuma wani dan
Yusha'u mutum ne mai taurin kai da wasa da al'amura
cikinsu har da rai.
An dai gaya mata silar hatsarin daga bakin Hajia iya ma
kamar yadda Yusha'u ya fada mata cewa. "Ana dan zafi,
ita kuma kin san ba a kunna mata fanka, sai na ce ta tafi
dakinta ni ina son kunna
fanka. Ina bacci kwatsam ta kira ni a waya na ji muryarta

cikin wani hali kafin na 'karasa dakin na tarar da ita a
sume."
Sam Momi ta kasa gamsuwa da wannan fatawar. Ranta
kuma ya yi mugun 6acin da ta ke jin lallai sai
ta bude kwanji a kan 'yarta in ba haka ba Yusha'u zai yi
mata sanadinta ko da yake cuta ba mutuwa ba ce, amma
zai iya yiwuwa ta 'kare rayuwarta cikin
wahala saboda rashin kulawa.
Idonta cike da kwalla ta sauke ganinta a kan Yusha'u da
ke zaune kan kujerar da ke gaban gadon Rumaisa'u, ta ce
masa.
"Yusha'u me ya faru ne wannan tsausayin ya afku?"
Yusha'u ya kasa hada ido da ita, ya kwaso in'ina. "Wallahi
Mummy... Muna kwance ta tashi ta.... shiga bandaki kawai
ta fara kwala min kira kafin na farga ta fadi a nan
wajen..."
Hajiya da su Atika suka ware ido suna kallonsa, tun daga
nan jikin Hajiya ya yi sanyi ta tabbatar akwai
wani abu da Yusha'u ke 6oye wa tunda har ya yi baki biyu
haka, Alhaji ma ya dan kalli Hajiya ya basar cikinsu babu
wanda ya tanka.
Mummy ta 'kara tayar da ganinta sosai akan Yusha'u, ta
ce.
"Shin kun je asibiti kuwa kamar yadda na ro'ki
alfarmarka a waya?"
Nan ya shiga kame-kame cike da borin kunya. "Ranar ban
koma gida akan kari ba. Jiya kuma mun je bikin bude
rijiyar nan... Damadai yau na ke shirin ta je asibitin..."
Alhaji da takaici da fargaba ya fara kaiwa bango ya tare
shi ta hanyar shiga maganar ya cewa Mummy.
"Wai me yake faruwa da kika sanshi kina Abuja mu ba
mu sani ba?"
Kai tsaye cikin raunin murya ta fada masa.
"Lokacin da cikinta ya yi wata biyu ta kira ni ta fafa min,
amma da sigar neman shawarar yadda

2 Comments On GORAN DUMA
avatar
jannat

1 year ago

Reply

08062236094

avatar
jannat

1 year ago

Reply

08062236094

Please Login or Register in order to submit comment