Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

soke kai cikin 'kafafu. Rumasa'u ta
zauna bakin gado tana ce mata.
"Hafsat yau ma fa sai kin agaza min kin raka ni
duba Auwalu. Na rantse yau idan na kwanta ban
san halin da yake ciki ba, sai zuciyata ta buga".
Wani malalacin kuka ya bijirowa Hafsat, amma ta
yi jarumtar danne shi a ma'koshi, ba tare da ta
dago ba ta ce.
"Ni ma ba ni da lafiya Rumasa'u".
Cikin jimami Rumasa'u ta ce.
"Ayya! Sannu, me ke damunki?"
Hafsat ta hada da sautin kukan da ke yun'kurin
fitowa ta ambata.
"Zazzabi..."
Rumasa'u ta yi saurin mikewa tana cewa.
"Kuma sai ki zauna ki ta kuka Hafsat, bari na
kawo miki magani ki sha sai ki kwanta ki huta, ni
zan ira Mubarak ya dawo mu je mu dubo Auwal,
jikina yana ba ni Auwal yana cikin wani hali
wallahi".
Wannan maganar tata ta sa Hafsat 'kara kecewa
da kuka.
Ta fita ta dawo mata da ruwa da panadol ta bata
ta sha, tana kuma mata sannu, Hafsat ta kwanta
ita kuma ta zauna bakin gado tana faman kiran
wayar Auwal cikin tsananin damuwa.
Rashin samun nasa ya sa ta shiga hasashen
wanda zata kira ta ji halin da Auwal ke ciki. Da
yake ya bata lambar wayar Innarsa, kai tsaye ta
kira amma ita ma a kashe.
.
Allah sarki, hasashe dai sun nuna Ruma ta dan Aunty ne
.
.
Dan Aunty.GORAN DUMA 20
.
.
Rashin samun nasa yasa ta shiga hasashen wanda zata
kira taji halin da yake ciki, da yake ya bata lambar wayar
innar sa kai tsaye ta kira, amma ita ma a kashe, a karshe
sai ta kira abokinsa Sulaiman cike da karsashi, '' sulaiman
yaya gida, ya iyalin???
Abinda tace masa kenan lokacin da ya daga wayar da
sallamarsa, murya kuma a dashe , a rude ya amsa mata
lapia Ruma, yaya jikinki ?
Cikin sauri ta amsa Alhamdulillahi sulaiman, don Allah
idan baka da zazzapan azuri ka leka ka dubo min Awwal,
tun sape nake kiran wayar sa a kashe, jiya mun rabu
bashi da lapia duk hankalina a tashe ya kasa kwancia, ka
jeka dubo min shi don Allah,
mubarak nake jira ya dawo ya raka ni na dubo shi.

Sulaiman ya dinga jan numpashi cikin matsanan cin jin
tausayin Rumaisau sai ya da dauke kwalla a idon sa
sannan ya kwaso in'ina yi mata karya '' lah bana gari
Rumaisau, ina kaduna a halin yanzu....
Cikin tsananin damuwa tace Hasbunallahu wa ni'imal
wakil.. To Allah Ya dawo dakai lapia, ina ganin kawai zan
tapi ni kadai.
Yayi saurin tare ta da padin, a'a ki zauna bari na yiwa
wani makocinsu waya.
Bai jira cewrta ba ya kashe wayar, ta tashi ta koma palo
tana paman jiran kisan sa shiru har piye da mintuna
ashirin, da ta kuma binsa sai ta tarar ya kashe wayarsa ,
kawai sai ta mike ta nupi kicin inda hajia ke tsaye cikin
shirin pita sanye da hijabi tana kuka da mai aikinta Talatu
tana goge kular da aka shakare da abinci.
Rumaisau ta jingina jikin durowa saboda kasala a
raunance tace hajia na raka ki gidan gaisuwar mana, sai
mu biya mu duba Auwal, ina tsammanin jikin sa ne yayi
zaapi shi yasa bai bi ta kan wayar sa ba.
Hajia tayi dira-dira sannan ta samo abin padi cikin in'ina
sai dai ban sanarwa Alh ba, kila yayi pada, jiya ma da na
sanar masa zuwanku sai da yayi ... Kiyi hkuri zuwa dare in
bai kira ba sai in tura Mubatak ko yayanku,
rumaisau ta jima tsaye ba tare da ta tanka ba kawai sai ta
juya a hankali ta pice daga kicin din, hajia da Talatu suka
kawar da kai daga kallon ta suna dauke kwalla,
har kwana biyu ana paman kwana-kwana da ita, saboda
tsabar damuwa itama sai da ta kai ga....
.
Kuyi hakuri da jina shiru jiya en wasu uzuri ne suka rike
ni, yanzu ma rubutun ba yawa ,
.
Dan Aunty na Ruma..
August 10 at 8:25 PM ยท PublicGORON DUMA (P 20**2)
.
.
Har kwana biyu ana faman kwana kwana da ita, saboda
tsabar damuwa ita ma sai da ta kai ga kwanciya.
Akwana na biyu da rasuwar, Innarta da babanta suka zo
gaisuwa, mahaifinta ya koma ya bar Innarta da aka fake
mata da cewa zata zauna ne saboda 'yan shirye-shirye.
Akwana uku da rasuwar tana kwance cikin zazzafan
zazza6i, Innarta da Hajiya da Hafsat da Mubarak duk suna
zaune ana 'yar hira. Can hajiya ta ce. "Hafsat debo
magungunan Rumaisa'u ki ba taa".
Sai da Hafsat ta zo da maganin sannan Rumasa'u ta daga
kai ta kalle su cikin kwalla ta ce.
"Hajiya wai me yasa kuke son ku damu da yi min abin da
ba zai amfane ni ba?
Na yi kawaici amma kamar ba ku san ina yi ba, amma da
kuka ganni a gefen kabari me yasa ba za a gayyato min
Auwal mu yi sallama ba?......

Na ga idan an yi hakan kamar za a sami lada, ba a bar ni
na mutu da zafi da radad'in son ganinsa ba".
Cikin daraba Hafsat ta silale ta bar falon gudun kecewa da
kuka a gaban Rumaisa'u. Hajiya da Innarta an sara mai
amsa mata, sai Mubarak ne ya 'ko'karta ya ce.
"Mutuwa ai lokaci ne Anti, an fada miki Auwla yana
kwance asibiti, amma ana rad'e-rad'in yau za a
sallamo shi, idan Allah Ya kaimu gobe ba sai mu je ki
duba shi ba".
Ta yi zuru tana kallon Mubarak, sannan ta amsa. "Wato
da na ce ka je ka dubo shi ba ka je ba kake min maganar
rade-radi?"
Ya yi saurin cafewa da fadin. "A can fa na ji".
Sai ta kawar da kai ba ta ce ce komai ba.
TA FARU TA 'KARE!
Sai da Auwal ya sami kwana biyar da rasuwa Rumaisa'u ta
sani, ta hanyar wata 'kawarta. Tun safiyar ranar ta
tilastawa 'karfin zuciya da na jiki domin ta samu ko
sulalewa ne ta yi zuwa dubo Auwal, saboda haka ta wuni
babu kwanciya.
Da yamma bayan sallar la'asar ta yi shirin fita, tana tsaye
falo gaban madubi ta ji 'karar shigowar sa'ko
a wayarta.
Da sauri ta ciro wayar cike da doki da fatan Allah ya sa
Auwal ne. Ta fada a sarari sai dai kash! Sai ta tarar da
shaidar da ke tabbatar mata da Auwal ya bar dniyar turo
sa'ko.
Ga abin da ta tarar: Salam
Lallai duk wani mai rai matafiyi ne, wanda ba shi da
garanti na lokacin da tsawon tafiyarsa zai 'kare,
bukatarsa kawai tanadin guzuri mai kyau domin samun
masauki mai kyau lokacin da ya cimma zangi.
Ina tayaki alhinin rashin Auwal, Rumaisa'u Ubangiji ya
haskka kabarinsa ya sanya mutuwarsa hutu ce mu kuma
in tamu ta zo ta riske mu da imani.
Nan take numfashinta ya nemi daukewa zuciyarta ta fara
bugawa da 'karfi, kuma nan take hankali da zancinta suka
tsaida aiki. Saboda haka ganin kanta ta yi kawai a falon
Hajiya, wadda ke tare da Innarta da Yusha'u.
Cikin muryar rashin hayyaci ta ke nuna su da wayar.
"Umma, Hajiya yanzu kun san cewa babu Auwal a doron
duniyar nan kuka bar ni nake 6ata lokacina a cikinta....
Kaico! Ban ga wani da ya ta6a zabga asara irin tawa ba, na
rantse da Sarkin da Ya yi ni..."
Hajiya da Umma suka taso a lokaci daya suka nufota,
amma kafin su 'karaso tuni aikin gama ya
gama, dan nan take ta sulale 'kasa ta fad'a kan girkakken
teburin gilas din da ke tsakiyar falon, ta datse goshi nan
take jini ya fara gudu a wajen, ita kuma tuni ta suma.
*** *** ***
Ba Hajiya da Umma wadanda dama Rumasa'u ke kwance
a zuciyarsu ba, hatta Yusha'u da yake hangenta sama-

sama sai da ya shiga matsanancin tashin hankali da abin
da ya faru da ita kamar
kiftawar ido, shi da ya ke zaune sai ga shi ya riga su isa
gare ta ya dago ta yana ambaton.
"Innalillahi wa inna ilaihiri raji'un".
Hajiya da Umma duk suka gigice, sun ma rasa kalmar da
za su fada duk wadda suka kamo sai ta guntule, Yusha'u
kuma kawai sai ya sureta ya yi waje da ita, Hajiya babu ko
mayafi ta bi shi cikin
salati, Umma kuma sai ta shiga cikin hankalinta inda ta yi
sauri ta kira mijinta ta ce.
"Daddy Ruma don Allah ko me kake yanzu ka sake shi ka
biyo jirgin 'karfe biyar ka taho Kano,Ruma ta gamu da
wani had'ari na tabbatar za a nemi jinin 'kara mata, ka zo
ka ba ta jini".
"Subhan Allahi, garin ya ya?"
Sai a sannan ta fara shesshekar kuka, ta amsa masa. "Ta
sami labarin rasuwar nan a waya, shi ne ta fada kan
gilasgi... Ba ta iya 'karasawa ba ta kece da kuka mai buga
zuciya.
Ta bazama waje jikinta na rawa, tana zuwa motar Yusha'u
na ficewa daga harabar gidan. Sai a ka
barta da Talatu da Hafsat suka koma cikin gida suna
faman kuka, musamman da Hafsat din cikin kuka ta
labarta musu hirarsu ta 'karshe ranar da su ka je gidansu
duba shi inda ya ce mata.
"Rumaisa'u idan baki da lafiya haka nake sa ki gaba nayi
ta kuka?
Ko ciwona ne ya fi na kowa?"
Ita kuma ta amsa da cewa. "Ina jin abubuwa masu yawa
marasa dadi a raina Auwal. Duk suna kwatanta min yadda
ba zan iya jure rashin ka ba".
Shi ma ya kuma amsawa da cewa......
Ya kamata ace yanzu kuna commnts da likes, masuyi
muna godia, wanda basayi nake magana,
bawai babu masu karantawa bane, idan mutun bazai iya
commnts ba ko da like yayi mana, mutuwar gidan nake
dubawa, ada da bamu kai haka yawa ba ana samun
commtns kusa da 100 zuwa saman sa yanzu kuma pa?
Idan da za'a na commnts da like rubutun ma zan kara shi
saboda a samu a gama shi da wuri, amma ina bata sama
da awa daya zuwa biyu ina typing dan kawai commnt din
da bazai wuce minti daya ba sai ya gagara?
Idan kun lura a parkon littapin napi yin sa da yawa amma
rashin commnts din ku ya kashe min gwuiwa na rage
hanu dan nima nake hutawa.
.
Dan Aunty.
GORAN DUMA (P 21)
.
.
"Da ciwo ya san ind arai yake Rumasa'u da tuni kin dade

a can, rayuwa da mutuwa duk na Allah ne,
kuma da yawan abubuwa na faruwa ne ba yadda mutum
ya zace su ba. Ni yanzu so nake ki kwantar da hankalinki
mu yi hirarmu mu fashe ta kwana biyun d amuka rasa,
kinga sai ta zame mana ta tarihi ko?
Ina jin tunda muka hadu bamu ta6a
kwanaki uku ba mu ga juna ba".
Haka dai suka yi ta tuntuni suna ba wa kansu yajin da ke
saka su kuka,
Innar Rumasa'u daga 'karshe ma sai ta fara furta kalaman
da ke nuna ta cire rai da gudan jinin tata.
Sai da awa daya ta haura sannan Yusha'u ya kirasu a waya
ya sanar da su suna asibirin Narassarawa,
sannan suka shirya suka rungud'a suka tafi asibitin.
Rumaisa'u dai tana cikin wani mawuyacin halin da ko
ma'kiyinta ya ganta sai ya tausaya mata kuma lalura ta
'karu a kan ta da, wato buguwar da ta yi a ka ya sabbaba
mata katsewar wayoyin turo sa'konni daga kwakwalwa
zuwa wani sashe a fuskarta inda suka daina aiki sam! Ga
kuma bukatar jini a jikinta, saboda haka kafin ma
mahaifinta ya zo wanda rukunin jininta ne,
yawancin lokuta ma idan bu'katar 'karin jini ta taso mata
shi yake ba ta. A wannan karon kafin ya 'karaso har
Yusha'u ya bata leda daya.
Wannan dangi dai haka suka kwana cikin tashin hankali,
suka tashi da shi yayin da mahaifan Auwal suka zo asibitin
ake yi da su.
Mahaifin Auwal ya fi kowa shan kuka dan yana ji a ransa
kamar shi ya yi sanadiyyar rasuwar Auwal
wanda Allah Ya nuna masa ishara, ya dauke shi mai
'koshin lafiyar da ya ke tun'kaho da shi, ya bar Rumasa'u
da yake kallon gawa-ta'ki-rami, duk da ita ma gata nan rai
'kwa'kwai, mutu 'kwa'kwai.
Shi yasa duk lokacin da ya yi arba da ita sai kuka ya
su6uce masa, ya kuma dinga ba ta hakuri tare da addu'ar
Allah ya tashi kafadunta duk da ba ta san yana yi ba. Haka
ma Innar Auwal wadda kusan son
da ta ke wa Auwal ya dawo kan Rumasa'u,
musamman idan ta tuno da ro'kon da Hafsat tayi mata
lokacin da suka je har gidan. "Auwal da Rumaisa'u sun
fara son juna da rad'in kansu amma yanzu ga shi sun
gaza rabuwa . Inna don Allah ki fahimtar da Abba kar ya
raba su... Za ku iya neman wata mafitar ta samarwa
Auwal wasu 'ya'ya ba nata ba... Na tabbata za su iya
lamuntar haka, raba sun ce kawai muke jinsa wani abu
da na ha'ki'kance numfashinsu ya gaza dauka..."
Ashe dukkan su da gaske suke, Auwal ya bar duniyar
Rumaisa'u ta nad'e k'afar wando zata bi shi.
.
BAYAN SATI UKU
Allah mai yalwata zu'katan bayi da farin ciki ra raba su da
'kuncin zuciya, Shi ya kyautata zuciyar Rumaisa'i, bayan

farfadowarta ba ta da aiki da ya fice kuka da kiran
mutuwa, kuka kuwa mai 'kona
zuciya da kusan hadiye ta, duniyar da duk alatun da ke
cikinta suka zame mata wani ba'kin duhu mai
cike da rashin aminci, duk mutumin da ta kalla sai ta
dinga yi masa kallon wanda bai san komai ba a
ba'kin cikin duniya kuma bai rasa komai ba a cikin
arzi'kin duniya, sa6anin ita da ta zama wata ganga
babu rufi.
Lokacin da ta fahimci 6arin fuskarta ba ya aiki ko daya
abin bai d'ad'ata da 'kasa ba, kusan ma shi ne abin da a
halin yanzu ke faranta mata rai, dan shi yake nuna mata
sauran 6angarori a jikin nata ma
suna dab da tafiya su bar wannan duniyar maimduhun
tsiya, duniyar da duk babu Auwal to labudda ita hoto ce a
wajenta.
Amma da yake ba ita ke tasifirin kanta ba, sati biyu ba ta
rufe ba sai da kaso hamsin cikin dari na zafin zuciyarta da
ta ke ji ya ragu, sai burbudin kashi hamsin na kewa da
tausayin kai saboda yanke 'kaunar ta yi asarar da ba zata
ta6a mayar da ita ba,
wannan ya sa ko daya ba ta damu da yadda tafiya ta yi
mata 'karanci ba, ta ke ganin ma kamar ba ta 'kawar da ta
fice cutar tunda ita ke kusantar da ita ga 'kaura a duniyar.
Sati uku, hud'u, sau'ki ya fara samuwa a 6angaren fuskar
tata da ya dauki hutu, ta fara motsawa kad'an-kad'an
bayan likitoci sun tabbatar da ba ta cikin wani had'ari a
lafiyar jikinta da ta wadatar jini a jikinta, sai suka
sallameta da tarin sharud'ai na
kwantar da hankali da 'karanta tunani domin kwakwalwa
ta samu hutu ta mayar da abin da ta
rasa.
Komawarsu gida ne ma ya famo mata ciwo, dan akwai
abubuwa da yawa a gidan da ke tuna mata Auwal wajen
Innarsu a haraba inda yake ajiye mota, a falo inda suke
hira, wayoyin hannunta guda biyu wadanda duk shi ya sai
mata su,
turarenta da kuma da yawa a cikin kayan kwalliyarta da
tufafin sawarta, kai ko magani ta zo sha sai ta tuno shi,
duk san da ya zo cikin gaisuwarsu sai ya binciki ta sha
magani, duk da cewa takanas yake yo mata waya ya ce
mata idan
ba ta sha maganinta ba ta dauka ta sha.
Wannan dalilin da ya sa ta ji gaba daya Kanon ma ta
gundureta, a cikinta ta hadu da Auwal, kuma a
cikinta suka rabu.
Kwana biyu da komawar mahaifiyarta gida ta cimma
Hajiya a daki bayan ta ji a ranta lallai ba zata iya ci gaba
da rayuwa a Kano ba. Cikin in'ina ta debo maganar.
"Hajiya jibi nake son komawa gida".
Hajiya ta dan yi sororo tana kallonta, a kallon nata ne
kuma ta fahimci da gaske ta ke. A sanyaye Hajiya ta ce

mata.
"Gida kuma Rumaisa'i?"
Ta kada kai kanta na kallon 'kasa, Hajiyan da Hafsat suka
'kara kallon juna, Hajiya ta riga magana.
"Na yi tsammanin za ki jira bikin su Hafsat Rumasa'u?
Ki daure ki samawa zuciyarki filin ajiye farin ciki, duk abin
da Ubangiji ya tsarawa mutum dacewarsa shi ne ya
rungume ya yi gadiya cikin tsoron Allah".
Rumasa'u ta daddage ta yi murmushin ya'ke, amma ta
kasa cewa komai, sai Hafsat ce ta katsa kame kunnenta da
cewa.
"Haba Rumasa'u ko ba a garin nan kike ba ai duk inda
kike kin taho tun yanzu dan mu yi shirye-shiryenmu tare,
bare kina garin me za ki koma gidan ki yi sati biyu ki
dawo?
Haba Rumasa'u me ya yi zafi?"..
.
.
Allah sarki masoyiya, ba dan jikin nata ba ai da nayi
magana an hada bikin mu da ita.lol.
Dan Aunty na Ruma..GORAN DUMA (P 22)
.
.
Nan da nan idonta ya cika da kwalla, ta kawar da kai tana
nad'ewa.
"Ni garin ne kawai ya yi zafi, na tabbatar idan na yi nisa
da shi zan sami sau'kin 'kunan zuciya...
Don Allah Hajiya ki bar ni in tafi, lokacin auren na
dawo..."
Hajiya ta tari numfashinta dan ta ga tana shirin rikicewa.
"Shikenan za mu tattauna maganar da Alhaji zan sanar da
ke zuwa dare, sai ki fara shiri ko?"
Ta kad'a kai, fuskarta ba ta bayyana abin da zuciyarta ta ji
da maganar Hajiya ba; dad'i ko ba yabo ba fallasa?
Alhaji ya 'kurawa Hajiya ido cikin rashin hayyacin batun
da ta gama zantar da shi, akwai alamun ya kasa
hankalinsa fiye da yadda ya kamata ya kasa shi, can ya
nisa ya ce.
"Kin san abin da raina ke raya min game da yarinyar
nan?"
Hajiya ta girgiza kai kawai tana kallonsa, ya 'kara jan
numfashi sannan ya sauke ajiyar zuciya ya ce. "Da kamar
ace ka isa da d'an yau, sai in saka Yusha'u ya maye gurbin
Auwal a yi auren nan kamar yadda aka tsara. Ina cike da
tausayin yarinyar nan ko daya ba na 'kara kaunar ta shiga
hannun da zata wahala, ko hannun da bai san
darajarta ba, samun irin marigayi Auwal wani abu ne mai
gajiyar da numfashi shi yasa na cika da tsoron hannun da
zata fad'a".
Hajiya ta jima kafin kwanyarta ta fanso kanta daga
firgicikin da ta shiga, Yusha'u nata ne, amma ta tabbatar
hada shi aure da Rumasa'u wani ganganci ne,

musamman idan ba da amincewarsu ba, har ga Allah ba
ta shakkar Rumasa'u saboda sau'kin hali da taushin
zuciyarta, mace ce da duk yadda ka kai da ba'kin hali da
wuya ka gundurar da ita, har ka
gani a fuskarta, amma Yusha'u wani irin mutum ne mai
juyayyen hali da kin fahimtar mutane da jujja
ko da gangan. Saboda haka kullum ra'ayinsa yake tfy,
kowa bai iya ba, ita kanta ta san ba don Yushau yy sa'ar
tsayayyen uba ba, da su kansu iyayensa sai sun yi kuka da
shi. Amma da yake babu 'yar musu tsakaninta da mijinta
sai ta binne wannan zargin ta kawo wani da
ta ke jin zai musu ma'ana, wato ta sanar da Alhaji labarin
Hafsat ta baya na yun'kurin hana Auwal
auren Rumasa'u da mahaifinsa ya yi. Ta 'kare da cewa.
"Yanzu babu abin da ya fi tsaye min a rai irin
wannan, auren Rumasa'u nan kusa zai taimaka wajen
mantar da ita Auwalu, ta ya ya hakan zata kasance idan
ana gudun auren sickler?"
Kai tsaye Alhaji ya tare ta da fadin.
"Ni ma daya ne cikin dalilaina na son Yusha'u ya aureta,
'yar uwarsa ce ya san darajarta kuma ya san matsalarta.
Ina ji a raina duk wani da zai yi tattalinta bayansa zai bi,
dalilina na biyu shi ne, kawo 'karshen zaman wannan
tuzurancin nasa ba tare da dalili da 'kosai-kosai da shi. Shi
ba dan zuhdu ba, ba komai ba ballatana a kalli abin a
matsayin ya hana shi aure, kullum maganarsa daya ke
nan bai ga wadda ta yi masa ba. To ga 'yar kirki nan ya zo
ya aura na san duk 'kawar da yake a mace ba zai zarce
hangen irin Rumaisa'u ba... ke ni Allah Ya had'a kansu,
rasuwar Auwal din wata aya ce a cikin fatara".
Hajiya dai sai sauke ajiyar zuciya ta yi ta ce. "Allah Ya
tabbatar da abin da ya fi alkhairi".
Ya amsa da, "Amin". Lokacin da ya ke laluben lambar
Yusha'u a wayarsa, sannan ya ce. "Ki rarrashe ta ta bani
sati daya, zan tattauna da wadanda suka kamata akan
maganar Yusha'u, in akwai yiwuwar hakan ina ganin ba
sai ta koma gida ba ko?"
Hajiya ta yi dariya ta ce.
"To ai ni ban ma san abin da zan ce mata ta kwantar da
hankalinta ba, yadda ta ke nunawa zamanta anan zai ci
gaba da tuna mata Auwalu".
Ya kara wayar a kunne yana amsa mata.
"Ki fada mata na ce sai nan da sati daya, zata fahimce ki".
Da dare Alhaji ya ji muryar Yusha'u a palon Hajiya, ya
tabbatar kuma Rumasa'u na falon tare da Hafsat da
Mubarak, kawai sai ya nufi falon kai tsaye da niyyar sanya
ido ya ga yadda suke mu'amalar juna wata'kila ya san ta
inda zai fara tunkararsu.
Kowa na zaune ana hira cikin sakewa, amma Rumaisa'u
na kwance kan doguwar kujera ta yi dif kukan zuci ta ke,
domin tana hana hawaye zuba a idonta. Duk lokacin da
idonta ya kai kan agogo ta ga karfe tara zuwa goma har

sha daya na dare, sai ta ji wadannan lokutan ne ta tarar
da missed calls din Auwal, daren da zai mutu, kaiconta
shi ne ina ma ta daga ta ji abin da zai fada mata, wanda ta
ke jin ya matsu ya fada mata tunda ya dinga jero mata
kira sama da ashirin duk abin da yake son fada mata ta
tabbatar da ya sameta ya fada matam da
yanzu ya zame mata wani rubutu da zata dinga
karantawa yana rage mata d'imi.
Idanun Alhaji a kanta, ta muskuta ta dan goge kwallar da
ta fi 'karfin zuciyarta ta fito ba tare da ta lura Alhaji na
kallonta ba, ta janyo wayarta ta fara dubo sa'konnin
Auwal a wayar tana goge hawaye
a sace.
Alhaji ya yi gyaran murya ya ce. "Rumaisa'u yaya dai na
ga kina 'yan 'kananan hawaye?"
Ta yi saurin basarwa ta juyo ta dube shi, amma ta rasa
abin cewa, har sai da Hafsat ta dube ta a nutse ta ce.
"Tunani ko?"
Ta yi saurin girgiza kai ta kama ciki, ta ce.
"Cikina ke ciwo". Alhaji ya yi saurin duban Yusha'u wanda
ko juyowa bai ba, yana ta faman ji da kayan marmari,
sannan ya juya ya dubi Rumasa'u cikin tausayawa,
ya ce.
"Ayya kin sha maganinki kuwa?"
Ta kada kai ba tare da ta samu damar maganar ba.
Alhaji ya kuma juyawa ya dubi Yusha'u ya ce.
"To ko asibiti zaku tafi, Yusha'u tashi ka kaita asibiti".
Yusha'u ya ji wani irin takaici ya tokare masa ma'koshi,
da kyar ya sami wani dan sarari bayan ya
hada takaicin da lemo ya hadiye, ya kokarta yana duban
Rumasa'u ya ce.
"Toh, tashi mu tafi".....
.
Ni yau rai na ma ya baci, ya za'a hada Ruma da
mudadden namiji bayan tace ni take so?
Sai bayan sati biyu ma kawai.lol.
Dan Aunty.
.
.
Ta yi saurin girgiza kai tana duban Alhaji.
"Ai bai yi tsanani ba Alhaji, akwai maganin da zan sha".
Hajiya ta shiga maganar.
"Tafarnuwar za a jajjaga miki?"
Dole ta kada kai cikin ajiyar zuciya, Hafsat da ta san aikin
ta ne sai ta mike tana cewa.
"To bari na kawo miki, Mubarak zo mu je ka taya ni
6arewa".
Alhaji ya yi saurin tarewa.
A'a! Debo tafarnuwar ki kawowa Yusha'u ya yi aikin".
Rumaisa'u ta dubi Yusha'u da sauri, amma ba ta iya
karanta komai a fuskarsa ba, amma dai fuskar tasa
ce ta 6oye, domin ya shiga rudanin cewar akwai wata a

'kaasan zuciyar Ahaji saboda haka dagewa
ya yi murmushin karfin hali ya ce.
"Alhaji ai ba na son warin tafarnuwa".
Alhaji ya tsare shi da ido ya, ya ce.
"To ai haka zaka koya ka saba, misali idan ka haifi sickler
zare hannunka zaka yi ka bar matar da dawainiya?"
Da yake Yusha'u ba yaro ba ne, nan take ya kamo tashar,
gumin goshi ya fara masa sallama, dan sanin waye
mahaifinsa akan a'kida, sai ya yi 'kasa da kai kawai yana
hirji a zuci.
hafsat takawo masa tafarnuwa da ruwa da kofi ta zauna
zata tayashi alhji yace tashi ki bar shi.
Haka yagama komai ya ce mata to taso ki amsa taje ta
amsa ta kafa kai ta shanye.yauwa haka ake idan
wani nakusa dakai bashi da lfya taimaka masa zakai..alhji
ya ko ma nashi yushau ya jima yakasa
tashi yaje kiran mahaifin nasa saboda kiran mahaifin
nasa yasan auran ruma ake son likamasa dukda yasan
imma hakan ta tabbata baisa ya bijiremasa ba..ya isa
dakinsa alhji ya ce wani dan sharar fagge naimaka dazo
akan
danwani aiki danake son baka wanda na tabbata zakaji
dadi. dan ALLAH kai wani tunani akan Ruma kasama mata
wata makoma dazata iya zama da zata iya
zama mata masalaha dangane da halinda ta tsinci
kanta..naimaka hakan ne danganin kaine babba
dagani har abbar ruma in muka mutu dawainiyar ya yan
mu zai iya hawakanka..nandai alhi yaitamasa bayanin
yanda zai fahimce shi
amma daga kar she sai yushau ya ce inaga alhji komawar
ruma gidansu yafi mata kwanciyar hankali..
daga kar she dai alhji ya ce kai nakeso ka maye gurbin
auwal.. A dukkan maganar Alhajin babu ga6ar da Yusha'u
zai karya ya shigar da nasa 'korafin saboda haka
ya hau rawar baki.
"An ji, ita an ji daga gare ta ne?"
Kai tsaye Alhaji ya amsa masa.
"Ba na jin yarinyar nan. Ai Rumaisa'u ta haifu". Gugar
zana kawai Yusha'u ya dauki maganar
Alhaji, don haka ya yi 'kunar bakin waken fitowa ya fadi
abin da ke ransa.
"Dan Allah a yi min afuwa Alhaji, wallahi ni Rumaisa'u ba
ta daga cikin irin matar d anake son aure.... akwai na'kasu
da yawa a Rumasa'u da ba zan iya jurewa ba".
Alhaji ya 'kura masa ido fuskarsa ba ta nuna yadda ya
kar6i maganar Yusha'u ba, ya ce.
"Uhum! Lissafo min abin da ta rasa ko wanda ya yi mata
yawa a matar da kake so"..
kodaya bana da ra ayin auran macen da iliminta yadara
na sec. sannan ALLAH yasa banasan shagwababben
mutum.kuma aganina duk kokarin mutum zataga ya
gaza.

cikin tsananin ba cin rai alhji ya ce duk wadan nan
hujojjun naka ba bu wanda yaikama dana addini.alhji
ruma fa tafini zurfin karatu duk yarinyar dataje jamia
idonta a bude yake.ganin mazansu suke kaidaya dasu
basu isa dasuba.kila
kuma kawai ta wafto rigimar kunbi kun shagwabata
ciwon nan nata kamar wani kayan alfarma ya
zamemata.alhji ni ga badayama banasan auran dangi
alhj ya ce yanzu ne na fahimci bada zahiri kake amfani ba
son zuciyakawai.alhji ya ce da zuciya
daya na za barmaka ruma a matsayin iyali

2 Comments On GORAN DUMA
avatar
jannat

1 year ago

Reply

08062236094

avatar
jannat

1 year ago

Reply

08062236094

Please Login or Register in order to submit comment