Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA.....🐓*
( _Ko Ana Muzuru Ana Shaho Sai Yayi_)




Na
*Nuceeyluv😘*



*Alhamdulillah Allah ya sake dawo Dani a sabon littafi na me suna a sama👆🏻, Bayan dogon hutun zango da mukaje💃🏻 yaudai gamu tsundum mun dawo, Ina masoyan Dangin Na fulani😂 kun gane ai😉 @SIRRIN ZUCIYA😜 da fatan Baku manta ba🤣 toh yanzun ma Nuceeyluv batayi kasa a gwiwa ba Dan ta sake zuwar muku da Wanda yafi SIRRIN ZUCIYA😋 karki Bari a baki lbri 'yar uwa💃🏻 karki Yi sake a barki a baya💃🏻 masu iya mgn kance sawun giwa ya take na rakumi🏌️‍♂�? toh wollah haka abun yake dokin Wannan littafin ya take SIRRIN ZUCIYA nesa ba kusa ba😍 haba madarar dadin ma ai sai mun luntsuma cikin lbrin...*✍�?







1....



Tafe yake cikin takun sa na kasaita Yana me kokarin zare labcoat dinsa cikin wani irin salo me matukar birgewa, *DR. UMAR SALEES* kenan matashin Dr. Me jini a jika Yana da cikar sura irinta mazanta, Idan Yana tafiya sai kace basarake kazalika idan Yana mgn tamkar Jinin saura Kai kace Dan sarki ne, Jajir yake idanunsa dara-dara lumsassu Wanda suke yanayi da kamar yanajin bcci, kwayar idanun sa fara ce tass tamkar Madara Dan haske yyinda bakin dake tsakiya ya Kara kawatu, Yana da saje irin na isassun 'yan gayu da hancin sa Wanda ya dace da kyakkyawar fuskar sa, a takaice dai UMAR Yana da kyau da cikar sura shiyasa dayawa Mata ke kware masa, maza ke jin kishin sa, toh da Allah yasa shi bana matan bane sai ya kasance bema San sunayi ba Dan Abinda ke gabansa ya ishe shi, Wani abun mamakin shine Koda yaushe fuskar Umar a dinke take is hardly aga Yana dariya saita kure idan abin yakai dole yyi dariyar kaga yadan murmusa kadan, hakan ma sai idan tare yake da abokin sa Sadeeq,

Sadeeq shine kadai best frnd dinsa tun yarinta har kawo yanzu tare suke, Bayan shi baya yiwa kowa dariya fuskar San Nan a dinke take, shiyasa dayawa 'yan Mata saidai su kware masa daga nesa badai a kusa dashi ba Dan kowacce ganin sa take tamkar Namijin Zaki. Huh! Kada na cika ku da surutu domin idan nace Zan zayyano Sura da Kamala irinta Umar Zan rubuta littafi guda ban gama ba#lol😜.

Cikin sauri ya Isa cikin office dinsu direct inda ake rataye labcoat ya nufa Nan ya rataye tasa a wajen, a gurguje yyi sallama da Prof Sa'idu dake kan kujera Yana duba system, Prof Sa'idu ya dago Kai Yana duban Umar hade da kokarin zare glass dinsa yace,

"Saurin me kke haka Umar?"

Umar yadan Sosa keyar sa cikin girmamawa yace,

"I'm sorry an kirani a gida ne emergency before mu shiga theater room"

Prof ya girgiza Kai Dan yasan Umar Kai tsaye zai Gaya maka gsky komai dacin ta, shiyasa ya yadda dashi Dan yasan karya ba dabi'ar sa bace,

"Okay you can go, But u make sure ka dawo akan lkci kasan yanzu zaku koma school"

"Insha Allah I will try best"


Girgiza Kai Prof Sa'idu yyi, yyinda Dr. Umar ya juya da sauri yabar cikin office din, budewar kofar sa keda wuya daidai lkcn Dr. Sadeeq ya taho office din shima, Kadan ya rage basuyi Karo ba, Dr. Sadeeq ya dubi Omar da mmki yace,

"Kai lpy?"

Ya tmby Yana wara ido, dafa goshin sa Omar yyi Yana me dawo da hannun ya hade su waje daya👏🏻 yyima Sadeeq haka bece masa komai ba ya raba zai wuce, da sauri Sadeeq yasha gaban frnd din nasa yace,

"haba Omar wani lkcin fa wulakanci ne dakai wlhy, tmbyr ka fa nake Amma ka wani hade min hannu kamar wani ba'indiye"

yyi mgnr cikin tsokana Dan ya Saba fada masa hakan sbd kamar Al'adar sa ce mgn wahala take masa gara yyi maka nuni da hannu, Dan cije lips dinsa yyi Yana me shafa lumsassun gashin kansa cikin nutsuwa yace,

"sorry Sadeeq Ina sauri ne"

cikin kulawa Sadeeq yace,

"Ina zakaje haka kke sauri?"

Sake shafa sumar sa yyi yanaji kamar ya make Sadeeq din Amma ya Sansa da naci idan be Gaya masa ba yanzu zai Dame shi da tmby, cikin nutsuwa yace,

"Abba ne ya kirani before mu shiga theater room yanason gani na Dan yanada wani muhimmin zance dazai Gaya min, a lkcin naso na fasa shiga sbd yadda yake min mgn nasan serious issue ne, sai yace min tunda na riga na fda masa inda zamu shiga na Bari idan muka fito sai na same shi a gida tunda mukayi mgnr naji zuciyata ta kasa nutsuwa hankali na ya kasa kwanciya kaga kuwa Dole nayi sauri"

Sadeeq ya sa hannu a Aljihu Yana zaro keys sannan yace,

"ga Wannan key din sai kaja mota ka tafi Dan kafi sauri"

girgiza Kai Dr. Omar yyi Yana Dan dafa kafadar Dr. Sadeeq yace,

"Karka damu Aboki Zan Isa gida da wuri Insha Allah"

rage fara'ar fuskar sa Sadeeq yyi Yana me duban Omar daya juya ya fara tafiya cikin takunsa na kasaita, shidai ya rasa gane kan Omar besan wanne irin mutum ne shi ba me tsananin gudun abun hannun wani, to Amma by now ya kamata ace abotar su ta wuce hakan, da sauri yabi Bayan Omar din Dan harya fara taka harabar hsptl din, ba xato Omar sai ganin Sadeeq yyi a gaban sa hakan yasa yaja baya da sauri, Sadeeq cikin bacin Rai yace,

"A tunanina Omar kayana naka ne haka zalika kayan ka nawa ne, karka manta mun wuce a kiramu abokai saidai 'yan uwa to meyasa kke da tsanani ne Omar? Kodai har yanzu baka daukeni kamar yadda na dauke ka bane? Karka manta yadda Abba yake mahaifi a gareka Nima haka na dauke shi tamkar uba kazalika iyayena sun dauke ka tamkar dansu meyasa har yau ka kasa sakin jiki da mu ne?"

Hmmm....! Sadeeq Yaja ajiyar zuciya Yana cusa masa keys din Aljihun gaban rigar sa yace,

"ko badan ni ba kahau motar kaje domin Amsa Kiran Abba cikin gaggawa"

ya fada Yana me bar masa wajen da sauri danma karya dawo masa da key din. Girgiza Kai Dr. Omar yyi Yana Dan cija lips dinsa badan yaso ba haka ya canja akalar tafiyar tasa zuwa parking space cikin Jerin motocin da akayi parking ya zaro wata zazzafar BMW me tsananin daukar ido da haske ya Buda cikin Nutsuwa ya shiga ciki, wohoho kaiii..! Gsky Omar karshe ne kamar Dan shi akayi motar tayi matukar dacewa dashi, kafin wani lkci harya bar cikin hospital din.



*****
....gwalalo ido tayi tana me sake Mirza idonta dgske shine kwance cikin jini male-male

"Na shiga uku ni Saratu"

Ta fada tana rufe bakinta kar makota suji, babban tashin hankalin ta kada ace mlm Sale ya mutu Nan take cikinta ya duri ruwa tunowa da tayi dazu fa da tayi masa laben taji Yana waya da MARU idan Bata manta ba taji yace yazo, Tabbas zaizo ta fada tana Kara Tabbatar wa da kanta hakan, a sukwane ta shige dakinta ta debo kudin napep cikin hanzari ta saka hijab dinta a karkace kafin wani lkci ta zari jakar ta kamar ta wanzamai ta jawo kofar ta rufe Fadi take,

"bansan wanne tsautsayi ne ya dawo Dani gidan Nan ba a Wannan lkcin"

da sauri ta zura takalmin ta wari da wari ta sidado tabar gidan Dama unguwar baki daya Allah ya sota ta faki idon mutane Babu Wanda ya lura da ficewar ta.


Barinta unguwar keda wuya Dr. Omar ya sanyo hancin motar sa cikin unguwar, daga bangaren gidansu yyi parking sbd yasan motar bazata karasa jikin kofar gidansu ba dalilin Kwata data biyo ta wajen, cikin sassafar ya bude kofar tasu Yana me yin sallama cikin nutsuwa.

Shiru gidan ba kowa be wani damu ba Dan ya Saba da hakan shi da mahaifin sa mafi akasari sune suke jire gidan Yana takaicin Wannan Aikatau din da mahaifiyar su takeyi babban Abinda ke jefashi cikin kunci da damuwa kenan uwa uba idan ya tuna yadda ta tsane shi kamar Arne da kafiri sai yaji gaba daya duniyar tayi masa zafi, idan ya hango yadda ta maida mahaifin su tamkar wani sakarai duk ta shanye shi sai yaji kamar beyi sa'ar zuwa duniya ba gefe guda kanwar sa Data maida ta tamkar wata jari abin na ci masa tuwo a kwarya, Ya rasa inda xaisa ransa yaji Sanyi damuwa da tunani sunyi masa yawa ainun ya rasa Kama asalin bakin zaren.....

Tunda yaji shiru yasan da alama ko Abba Yana lazimi ne gyangyadi ya dauke shi tunda 11am yanzu da alama ya shiga yin walaha ne, a nutse ya yaye labulen Yana me sawo kansa cikin dakin Abban nasu,

kyammm..... Dr. Omar ya kame bakin kofa bakinsa a hangame sallamar dayayi niyyar Yi ta makale a makoshin sa, jikinsa ne ya fara kyarma labban sa na motsi saidai ya kasa furta komai, dakyar da sidin goshi ya samu hada kalmomin da zasu bada sauti cikin rudani ya furta A...a...a..b..bbb..A...bba...! Dr. Omar ya furta hankalin sa a matukar tashe ya Isa gaban Abban nasa dake kwance cikin jini male-male.
*ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA....🐓*
( _ko Ana Muzuru Ana Shaho Sai yayi_)




Na
*Nuceeyluv😘*



2...


Acan bangaren Saratu kuwa koda tabar unguwar direct wani lungu ta fada Bayan wata bishiya jikinta na kyarma ta zaro wayarta Tecno tana me latsa Kira, bugu daya aka dauka cikin sauri Saratu tace,

"mun shiga uku Nas(Nurse)"

daga dayan bangaren akace

"nifa dadina dake Sara kin cika rudu Wlh ni ki gayamin meye? Dama dazu muna waya naji kin kashe ba sallama na Kira wayarki daga baya a kashe"

"Hmmm..."

Saratu ta ja numfashi me nauyi hankalin ta a mugun tashe tace,

"Nas muna cikin tashin hankali Wlh Asirin mu da muka binne shekaru masu yawa Yana dab da tonuwa"

A Razane Nas ta Mike daga kishingiden da take tace,

"Me kike nufi Saratu?"

Wata wawiyar ajiyar zuciya Saratu ta sake saki tana me Dan waiwayawa Bayan ta Dan kar taje akwai me jinta a hankali tace,

"Wayar da mukayi dazu dake Ashe mlm sale Yana tsaye a bayana yaji dukkan Abinda muka tattauna musamman ma dake wayar a bolum(volume) take"

"Bantan uban nan kayyasa...."

Nas ta furta bakinta na Bari tace,

"Wlh duk inda kike kizo ki sameni Dan baki Isa ki ballo min ruwa Ina zaman zamana ba Wannan mgnr Sam Bata waya bace"

Saratu jikinta na rawa tace,

"yanzu haka ma gidanki na nufo"

"da yafi miki"

Nas ta furta tana datse wayar cikin tsantsan takaici. Gumi ne sharkaf ya jiqe Saratu dukda sanyi2 da akeyi a garin sbd Albarkar Ruwa da aka samu a ranar, Nan taci gaba da tafiya tana me kokarin tare Dan napep Bayan ta gama fitowa daga lungunan unguwar su kadan ya rage Bata afka Kwata ba sbd sauri, cikin sa'a kuwa ta samu Wanda ya tsaya cike da azama tahau direct ya wuce da ita inda tayi masa kwatance hade da kashe wayarta gaba1 sbd tsaro.



~~~~
A bangaren Dr. Omar kuwa batare da tunanin komai ba ya kinkimo Abban nasa Yana jijjiga shi hankalin sa a mugun tashe, ganin yadda jini ke malala yasa shi Dan janye Abba gefe guda, cikin azama ya fito daga dakin tunowa da yyi da 'yar karamar First Aid box dinsa daya ajiye a daki, time to time Dama Yana siyan mgni ya ajiye sbd halin Babu kada rashin lpy ya Kama mutum azo a rasa kudin mgni Abinda befi a kashe 200 ba shiyasa daya samu kudi yake aje Abinda yafi zama emergency a gida,

Cikin sassarfa ya jawo box din sannan ya juyo zuwa dakin Abba, batare da Bata lkci ba ya shiga hada kayan aiki Dan tsaida jinin da yake zuba Dan idan yace zai Kai Abba a haka zaiyi asarar jini sosai kafin su Isa hsptl din musamman Matsalar goslow da ake fama dashi a garin, Kafin wani lkci harya gyara masa inda yake zubar jinin Nan Bayan keyar sa, jikinsa ne yahau tsuma dayaga mugun ciwon dake keyar Abba, kallon inda ya jawo shi yyi Yana nazarin wajen Tabbas Babu ko tantama Abba zamewa yyi a nasa tunanin kenan.


Da sauri ya fito kofar gida ko zaiga Makocin su mlm Shamsu ya taimaka masa su fito da Abba daga gidan, cikin sa'a kuwa Yana fitowa mlm Shamsu na kokarin Sanya mashin dinsa cikin gidansa da alama dawowar sa kenan, saurinsa ya Kara yacin masa Yana me Mika masa hannu, Mlm Shamsu da fara'a yace,

"Umara kaine Ina Abban naku?"

Omar ya shafa sumar kansa data zame masa tamkar Al'ada Kai tsaye yace,

"Dan Allah taimaka min zakayi na fito da Abba"

"Yah Subhanallahi!"

Mlm Shamsu ya furta Yana jirkice mashin din nasa gefe guda yace,

"meya samu mlm din?"

Yyi mgnr Yana bin Bayan Omar daya kusa shigewa gida, a haka suka karasa cikin dakin mlm Shamsu nata sallallami, Shidai Omar bece komai ba har suka fito anan wasu tsirarai dake unguwar suka fara taruwa da Al'ajabin Abinda ya samu mlm Sale, Shidai Omar bece komai ba tunda a takaice ya fadawa mlm Shamsu zamewa yyi ya bugi kansa da karfe shine sanadin suman sa, hakan yasa shi mlm shamsun shike Basu bayanin Abinda ya faru,

a gurguje yazo ya kulle kofar gidan nasu sannan ya shige motar cikin azama, wani irin juyi da yyi da kan motar Kai kace wasan tseran mota zaije, kafin wani lkci harya bacewa mutanen unguwar da suka taru yanzu fiye da dazu sai maida zance ake Ana jajantawa hade da Allah wadai da matar mlm Sale wacce neman kudinta shine tafi darajawa fiye da auren ta.


Yana hanya Sadeeq ya Kira shi, da sauri kuwa ya dauka Dan Yana bukatar hakan,

"yauwa pls a shirya gadon daukar marasa lpy kafin na iso pleaseeee.."

Ya katse hanzarin Sadeeq din tamkar shine yyi Kiran, hankali a matukar tashe Sadeeq yace,

"Waye baida lpy?"

"Abba ne."

Omar ya fada a takaice kafin ya datse Kiran Yana me aje wayar gefe, Sadeeq dake daya bangaren be takura masa ba shima ya shiga matukar damuwa da sauri ya tashi Dan samun Wanda zasu riko gadon.


*
Cikin Rahamar ubangiji sai gasu a hsptl din, kamar yadda yace hakan ce ta faru Dan Already har an fito da gadon ma shi ake jira, cikin sassarfa aka fito da Abba daga motar zuwa kan gadon marasa lpy, a gurguje kuwa aka wuce dashi emergency room, tuni Dr. Sadeeq ya fito musu da labcoat da kayan aikin da xa'a bukata kafin wani lkci sun dukufa kan Abba Dama sauran wasu Doctors din Ana bashi taimakon gaggawa sbd dogon suman daya tafi.



***
Kadan ya rage tayi tuntube Allah ya kiyaye Nan ta afka dakin Nas da tun dazu take safa da marwa hankalin ta yaki kwanciya, ba xato kuwa taji fadowar mutum dakinta, A Razane ta juyo ganin Saratu ce yasa tadan saki ajiyar zuciya tana me zama kan kujerar ta, Cikin masifa tace,

"Saratu a wanne shirmen ne yasa kika sa Asirin mu ke dab da tonuwa?"

Saratu tace,

"kinji na rantse miki da Allah Nas bansan Yana bayana ba sai juyowa nayi kawai Naga Yana shararar hawaye tamkar an balle famfo Fuskar sa babu Annuri kamar Wanda aka Aiko masa da sakon mutuwa, shiyasa na katse layin da sauri."

"Toh Amma me yace miki?"

"Hmm..!"

Saratu tadan ja majina tace,

"budar bakinsa sai cewa yyi Allah ya Isa ban yafe miki ba Saratu, kin cutar damu, bazamu taba yafe miki ba, Ashe zaluncin naki yakai har haka? Ko a mafarki ban taba tunanin zakiyi makamancin Wannan ba, Kuma Wlh ki sani *ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA KO ANA MUZURU ANA SHAHO SAI YAYI* bazanyi kasa a gwiwa ba dole na sanar dashi dukkan tuggun da kika kulla keda shadaniyar da kuke waya shekaru sama da talatin. Yana gama fadar haka ya juya cikin fushi ya nufi dakinsa Dan daukar wayar sa, ke na takaice Miki lbri Nas tunda ya fara mgnr hankali na yake a mugun tashe ji nake duniyar tana hautsina min, babban takaicina shine har yanzu ban fara cin moriyar Abinda na binne shekaru talatin baya ba, Kai ni yau Naga ta Kaina ni Saratu"

ta karasa mgnr tana dafa kanta, Nas tace,

"kina nufin haka kika fito batare dakin hanashi yin wayar ba?"

Tayi mgnr tana zaro ido cikin kidima, Girgiza Kai Saratu tayi tace,

"yaushe Naga ta zama? Binsa nayi Ina bashi hakuri kamar Wanda nake zuga shi, haka ya dauko wayar Ina labe Ina jinsa a lkcn duk wani dabarata ta kwance Tabbas da Allah yasa yyi mgn a lkcin Babu Abinda zai Hana Asirin mu tonuwa, toh haka na sake shiga dakin cikin bacin Rai nace yanzu bazaka hakura ba sai kace mutanen farko sbd taurin Kai? Kallo na ya tsaya Yi Yana girgiza Kai yace tsakanin ni da ke waya kamata a fadawa hakan? Wato kinga ban dauki mataki ba Koh? Jira nake sakon Nan ya Isa ga inda ya dace kafin na dauki mummunan mataki a kanki, jin hakan ya sake jefani cikin rudani da tashin hankali, kinsan Dama Yana Dan dogara sanda sbd kafarsa karshe zuciya ce ta debeni na warce sandar tare da rima Mai ita a tsakiyar ka, dake abin yazo masa a bazata tuni ya dafe kansa sbd tsananin xafin daya shige shi sannan kafar da tadan lankwashe sai gashi ya Fadi a daidai karfen gefen gado kafin nayi aune sai gani nayi jini ya fara malala ta kasan keyar sa, shiyasa banyi wata-wata na baro gidan da sauri sbd nasan yaron Nan Maru Yana hanya tunda yace yazo."

"Kin kashe mu, kin kashe mu Saratu"

Nas ta furta tana dafe kanta,


"Tsautsayi, Tsautsayi ne Wlh."

Saratu ta fada itama,
Wani mugun tsaki Nas taja me cike dajin haushi tace,

"Toh Wlh bazata Sabu ba Dole mijin Nan naki mu nakasar dashi"

Tayi mgnr cikin bacin Rai, Saratu tace,

"nakasar dashi shi zai Hana ya fada? Kinsan taurin Rai irin nasa kuwa?"

Nas tace,

"ke dallah bakya gane Abu Sam wani lkcin, zuwa zamuyi wajen bokan daya Saba Mana aiki boka na tsamiya domin ya rufe masa baki ya daina mgn kwata-kwata a Rayuwar sa haka zai dinga bin mutane da ido ba halin mgn"

Shiru Saratu tayi batace komai ba can Nas ta katse Mata tunanin da fadin,

"Ko bazaki iya bane?"

Saratu ta girgiza Kai tace,

"nazari nake"

"kutt... Toh tsaya kallon ruwa kwado ya Miki kafa kin sani Sarai idan Asirin Nan ya tonu sai kinfi kowa cutuwa Danni nawa kadan ne ehe"

Hankalin Saratu ne ya sake tashi ta Mike zumbur Fadi take,

"shirya, Maza shirya mu tafi Dan Allah Wlh bakiji yadda na sake fadawa tashin hankali ba matukar ya farka bazai fasa qudurin sa ba."

Nas tace,

"haba ko ke fa"

tayi mgnr tana wucewa uwar dakin ta, kafin wani lkci itama harta shirya sannan ta sankamo Tata jakar kamar ta wanzamai suka fito a gidan da gaggawa.



~~~~
A bangaren Dr. Omar Kam cikin Ikon Allah suka samu nasarar Gyara ciwon mlm sale, komai sun gyara masa tsaf an shirya shi tsaf gwanin ban tausayi, Saida aka gama Batare da shawarar Dr. Omar ba Dr. Sadeeq yasa aka maida mlm Sale special room sbd samun nutsuwa, Dr. Omar kamar zai masa mgn ya fasa Dan kar frnd din nasa yaga kamar Yana Raina masa taimakon sa musamman idan ya tuna da dazu akan shiga mota badan Allah yasa yaje da motar ba Tabbas da zasu wahala wajen neman abun Hawa hakan daya tuna sai yaji Dadi kwarai Dan ba karamin taimako ya masa ba.

Ba kowa a dakin daga shi sai mlm sale gashi suna Shirin komawa skul dama after zuhur prayer zasu koma, wayarsa ya Ciro cikin fargaba da Rashin sanin wacce irin Amsa za'a bashi ya lalumo number Ummansu, Dakyar dai ya iya danna Kiran sbd fargaba, rintse ido yyi kawai Yana sauraron Kiran ya shiga, Shiru number ta fara searching can yaji tace is switch off,

"Hmmm...!"

Wani marayan ajiyar zuciya ya saki Yana me maida wayar sa Aljihun sa hade da shafa sumar kansa Yana nazari, Shigowar Dr. Sadeeq yasa ya dago Kai bece komai ba, Dr. Sadeeq yace,

"kasan muna d lecture 2 to 4 ya kamata kazo muje Sallah sai mu fara Shirin tafiya kafin Nan ka Kira Umma saita tsaya a wajen"

Dr. Omar ya danyi shiru kamar bazai magantu ba can yace,

"Bata gida"

yyi mgnr a takaice, Dr. Sadeeq be zurfafa da tmby ba yace,

"Okay Bari nazo"

Nan yaje ya sako wata Nurse Rukayya matar tanada mutunci Dan tadan manyanta ma yazo da ita wajen, Dr. Omar sai ganin su yyi, kafin yace komai DR. Sadeeq yace,

"yauwa Aunty Ruky Zaki kula Mana da Abban mu kafin mu dawo munada wani uzurin ne me karfi"

Nurse Rukayya tace,

"Babu damuwa Sadeeq Zan kula da wajen sai kun dawo"

"yauwa mun gode"

Dr. Sadeeq ya fada Yana jawo hannun Dr. Omar subar dakin, Hade fuskar sa Dr. Omar yyi be jawu ba saima daskarewa da yyi a wajen, ganin haka yasa Nurse tace,

"Bari na jira ku a waje ku Gama saina shigo"

"Okay"

Dr. Sadeeq ya furta, Tana fita kuwa Dr. Omar yace,

"Ce maka akai bazan tsaya a wajen ba?"

Yyi mgnr a zuciye, Dan karamin tsaki Dr. Sadeeq Yaja yace,

"Da ace bamu da lecture me muhimmancin bazan ma fara neman wata ta taimaka Mana ba, ka sani Sarai ranar Nan mun Dade muna jiran tazo yanzu idan ta subuce Mana yaushe kke tunanin zamu sake samun wata damar? Kasan ba kamar sauran lectures bane da muka Saba Attending karka manta a kowanne lkci anaso mutum ya dinga amfani da damar daya samu kafin ta kufce masa"

Dan lumshe ido Dr. Omar yyi Yana me shafa lallausan gashin kansa dayan hannun a qugun sa, yadan cije lips dinsa kadan a takaice yace,

"Alright!"

Girgiza Kai Dr. Sadeeq yyi Yana yowa gaba, haka shima Dr. Omar din ya biyo

Please Login or Register in order to submit comment