Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Deeda ba tasan kana son ta ba, ba ta
yarda ma sonta kake' ba, to’ ba. ka da
(right) akan‘ Deeda. Baka da Wata dama'akan ta
da har za 'ka 'zo-ka‘daga mana‘hankali,’ baka
da damar 'dagawa kowa hankali akan
(failure) :dinka._
Wannan‘ rashin nasarar naka ne don haka ka
dagawa kanka hankali ba Daddy ko ni; k0 Sister
ba. Idan ka ci gaba da haka ka zama mai son
kai, kuma mai son kai ba zai taBa nasara» ba a
duk inda yake. ‘ _.
Sabeer, ka_ fadi a matsayin 'ka- na namiji, da
'kuma matsayin ka na- miji- (you failed as a
man; you failed as a husband); don .haka
baka' .da damar dagawa k0wa hankali".
.Sabeer ransa yar yi masa zaf1, wani bakin iciki
yaji ya ‘tokare masa kirji akan Wanda da ya‘ke
Cikin zafin 'zuciya yace Unclle Ib, Kazafin da za
‘ka 'min kenan? Me kalamanka suke nufl?"
Ibrahim ‘yace, "Ba 'kalamai na bane,’ ina fassara
maka abin'da ke cikin wasikar Deeda
menene, wanda kai karantawa kawai ka yi, ba ka
fahimci wasikar karba". " Sabeer ya nuna shi da
yatsa, ya ce.’ "Ya ishe ka Uncle Ib, ‘Wannan
Kaskanci da wulakancin da ka min yanzu ba
zan“ .iya jura ba, in ka sake “zan, manta
dangantakar da ke tsakaninmu. Abinda nake ji
game da. Deeda a 'cikin 'zuciya ta, Kwakwalwa
ta da dukkan ilahirin jikina, idan ba. so bane,
to.wani_abu ne wanda ya‘ girmi ’so, ya kuma
fishi matsayi. Abinda nake ji game da Deeda wani
abu ne da kai k0. wani mahaluki bai taBa jin
irinsa game da wani' ko wata a duniyar nan ba,
don haka’ kar ka‘ Kara Karyata min (feelings)
dina, soyayyata ta gaskiya ce, kar ka sake
KoKarin (convincing) dina akan cewa soyayyata
.ba gaskiya bace". ' . Ibrahim ya yi murmushi‘, ya
ce. ‘ "Sabeer kenan, ni da kai mu ka San haka,
.muka'san cewa 'soyayyar ka ,gaskiya ce. Sai dai
wacce ka ke yiwa ba ta san kanayiba ba,
ah shared a profile .
birnin. gayu
chapter16
saboda bata taBa daukan ka (serious) ba, duk
‘wani abinda za ka 'yi ta dauke shi a matsayin
yarinta, tana ganin ka yaro, ba ka san ciwon kan
ka ba, balle ka san me kake so.
Sabeer, gaskiya daci gare ta, amma ya zama dole
in fada maka. Duk da ka girma, amma sam kaki
ka girma din. A tunani na yanzu matsayin ka ya
wuce a nema maka abu k0 ai maka abu ka ci. Ka
wuce lokacin da Daddy, ni k0 Sister za mu maka
abu, lokaci ne da 'za kai wa kan ka abu, mu dai
sai dai mu ba ka- shawara, in .kuma kayi ba dai
dai ba mu gyara maka. '
Amma har yaushe Sabeer za mu dinga maka
komai? K0 kana tunanin za , mu tabbata da kai?
Rayuwar nan ba ta da tabbas, komai na iya
faruwa.
Ka godewa Allah kana da gata, iyaye, 'yan uwa,
wanda suke tare da kai, za su sa ka a hanya in
ka karkace. Akwai dubbai irin ka a duniya da ba
su kai ka shekaru ba, amma sun dauki nauyin
iyayensu da' kannen, su.
Sabeer, lokaci yayi da za ka'“san ciwon kanka in
har" kana ,so ka Samu 'yadda kake 'so a rayuwa,
in ba ka _so.abinda ya faru
da kai ya sake faruwa da kai me ka ke
tsammani? Ba Deeda kadai ba, akwai-macen 'da
'ta san ciwon kanta,. ta San me take, ta‘
. yarda da'zama da kai?
. ' Ka taf1 gun Daddy,» in kana son abu'ba’: ka
iya samawa kan .ka, ‘in .mats'ala k0 Wata
’damuwa ta ta‘so maka ba ,ka iya magance' ta,‘
ba kasan 'me’za ka‘ yiba, ,ba .ka da wata'
dabara, ba tunani?‘
‘."Sabeer,-namijin musamman a gidansa'
Shugaba ne, haka kowacce mace za .tai fatan
danta ya gaji ubansa, ya yi' hali irin na
mahaifinsa; ya ,zama gwani (rolemodel) na
'ya'yansa. Ka gaya min Sabeer wani ‘halaye ne
daga cikin halayen ka; matar ka za ta so tayi
(Alfahari da shi,. 'har ta‘ soka zama uban
yayanta?
. Sabeer, ya zama ,dole mu dinga yiwa kanmu -
‘tambaya, muta fadawa. kanmu
gaskiya"- ‘ ’ Tuni jikin Sabeer ya yi sanyi, kansa
sunkuye sai hawaye yake . Tabbas bai taBa jin
kasaWar sa ba tunda yake a rayuwa sai yau.
Ibrahim ya tausaya masa matuka, haka nan ya ji
dadin nasarar da yayi akan Sabeer.
- Ya matso' gabansa, ya. tallafi fuskar sa suka
hada ido, sai ya fashe da kuka, ya fada jikinsa.
"(Uncle Ib, I am sorry) a 'shirye nake da na dau
duk wani . gyara, ba zan sake fitinar Daddy k0 ”
Sister ba, ba zan sake dagawa kowa hankali ba.
Ka fada min Uncle Ib ya zanyi? Ina son zama irin
mijin da Deeda ke so, ina son zama irin'ka,
saboda Deeda na sonka. inason son zama irin
mijin da Deeda za tai, alfahari da shi, haka ina'
son 2ama (rolemodel) na 'ya'yana. ‘
Uncle lb, ka yafe min, na fitine ku da yawa, yanzu
ka fadamin ya zan yi? Duk abinda kace zan yi".
Ibrahim ya yi murmushi, yace
"Na‘ji dadi da ka fahimce ni, zan baka shawara, in
sa ka a hanya, amma sauran aikin naka'ne. '
- Kagana farko ya zama dole .ka kare mutuncin
Deeda a matsayin ta na matarka. sannan
mutuncin ta naka ne. A yanzukar ma ka bari
Daddy ko Sister su ji ta gudu balle mutuncinta da
kimar ta ya ragu a idonsu balle~har_ ‘su dora
mata wani‘ 'wahala‘ da damuWa Ka san~ Daddy
’zai~iya komai akan ka, wanda a garin haka zai
Batawa Deeda,’ ita kuma za ta dora lafin akan
ka. Kaga‘hakan zai sa ta' Kara'tsanarka, tare da
niSanta' kanta da kai.Maimakon haka, kayi
abinda zai kawo kusanci tsakanin ku".
.Lokacin Sabeer yadago kai ya kalleahi
Me zan'yi Uncle Ib?" ' - .Ibrahim din ya gyara
zama, ya- kalleshi', ,yace' "Deeda matar ka ce,'
don haka ka' bita inda ta ce duniyarta‘ce 'ka je
ka nuna mata
ba wani bambanci tsakanin duniyar ta da' naka,
ka nuna mata duniyar ku daya, rayuwar ku daya,
ka kuma tabbatar mata da cewa son deeda ba
rigima ba ce k0 fitinar Sabeer. Son ta so ne na
hakika, so‘ na gaskiya, wanda za ka‘ iya yin
'komai kuma za 'ka jure komai muddin bai
saBawa shari'a ba. Duk Wahala, duk Kunci, duk
Bacin rai, KiShi, da yinwa ruwa da iska, zafl da'
sanyi duk za ka jure. Ina fatan kana gane Hausa
a dundule da nake maka?"
Sabeer ya girgiza kai, ya ce. - '
"Ina fahimta, kuma ina hango abinda ka ke hango
min". ’
Ibrahim—ya shafa kansa, ya ce
"(Good my smart brother)". Yana murmushi.
Ya ce, "Na san za ka iya, za ka yi abinda ya f1
haka. Ni" kawai na nuna ‘maka abinda za 'ka yi
ne, sauran dabara ya rage naka. ‘
Sannan abu na karshe Sabeer. kar ka
taba roKon so_(nevcr beg for love). Idan ka
tabbatar mata da soyayyar ka sai ka sa mata na
ka soyayyar (make her fall for you); ka kasance
ka karanci tunaninta yanayin ta da yadda take
komai, zai zo maka da sauKi
‘ Sannan hakuri, juriya. Idan ka yi Wannan nasara
tana tare da‘ kai da yardar Allah. Sauran ka yi
addu'a ka barwa Allah".
"Nagode Uncle 1b, zan shiga ciki in cewa Daddy
zamu yi taflya; ba zan -nuna-_ masa Deeda ta
gudu 'ba, sai in xo in shirya‘in tafi
‘ Zan tafi neman Dceda, zan tafi Kauyen su, k0 a
kango take zama zan bi ta mu zauna tare". ,
_ Yana gama fadi ya mike, Ibrahim ya bude masa
kofa ya fita, ya bi shi da kallon tausayi. _
("Allah-Sarki Sabeer. dama, ta ya zaka iya
rayuwa‘a Kauyen su Deeda? Yaron da zaman
Nigeria kanta'. ke masa wahala yana cikin
babban gida 'na ' jin dadin 'rayuwasa
amma ya'na mitar zafi da wahala, ina ga , zaman
kauye? Allah ba da sa'a Sabeer, zan yi ta maka
addu'a". -
Ya mike kan doguwar kujera; tunanin Deedan da
tsananin sonta ya dinga bijiro mishi. Sassanyar
muryar ta da fuskar ta mai cike da kwarjini da
annuri', tare da murmushin ta mai tafiya da
dukkan wani damuwar sa, sannan da Sanyin hali
irin nata.
."Deeda, ya zama dole ki manta Ibrahim, saboda
kina da masoyi wanda ya f1 Ibrahim son ki, haka
Ibrahim ba shi da filin da zai iya ba ki a gidan sa
da rayuwar sa. Filin da zan iya baki a zuciya ta
ne, sai dai zuciya ta kadai bai isa ba, zuciya ta
kadai (is not enough)"
Haka ya kwanta a wurin, idon sa rufe, tunani kala
—kala aransa. '
A ' Kai tsaye Sabeer ya wuce Bangaren su, gaba
daya jikin sa a mace, haka zuciyar
sa cike da kuncin rashin Deeda‘. Haka- nan ya
tsinci kansa cikin kadaici da tsananin kewa.
‘ A tsakiyar falon ya zauna ya ’hada kai. da
gwiWa, duniyar tai masa - zafi, maganganun
Ibrahim ke yawo“a kunnen sa.. Hakan ya sa ya-
ji yana son yin kuka, sai dai bai bari hawayen
sunzubo ba ya ‘yi kokarin” tsai 'dasu, ya mike 'ya
nufi bayi don-yin wanka, ya sakarwa kan sa
shawa.’ A lokacin' ya‘ samu damar sakin
hawayen sa,'ya fashe‘ da wani irin kukan takaici
da Karfinsa. Ya yi kukan samai isar sa,.Sannan
ya fito’ya hau shirya kayan sa cikin wani dan
madaidaicin jaka'; . '
Duk inda ya'motsa 'Deeda yake ji ‘a ransa a '
zUciyar sa da Kwakwalwar sa,’ tunaninn ta‘ya
hana shi sakat,_ ita kawai yake jida gani, haka
nan'ita yake? son gani, da ita 'kadai yake son ya
kasance Hakan ya bashi Karfin gwiwar
taf1ya’nem0 ta duk inda ta ishiga, haka nan
inbazata' ta iya biyo shi BIRNIN .GA'YU ba._. shi
zai bita duk inda
take ya zauna da ita ya rayu da ita a k0wane irin
hali,
’Da- .wannan tunani» ya 'gama shirya ‘kayan 'sa,
ya. .dauki duk Wani abu da-yasan zaii masa;
amfani, ya nufi motar ya‘ zubasu, ya dawo ya
shirya tsab, sannan‘ ya nufl Bangaren mahaifinsa.
Kai tsaye ya wuce' dakin bacin sa, nan kuwa ya
same‘shi yana bacci. Nan ya ‘tsaya yana kallon
sa, ya' rasa .abin yi, Shin ya tashe 'shi k0 a'a?
Anya'zai iya .tafia‘ bai yiwa mahaifin sa ‘sallama
ba .ya yi dai dai kuwa? Ba zai, iya' taflya bai
masa sallama ba, hakaba zai iya 'tashin saba, ya
nemi kujera' ya ’zauna‘ yana jiran tashin sa.
Zaman ida 'yayi‘ shiru yana tunanin Deéda da
kewar ta na shigar' sa, nan da nan. idanun
sa' .suka .ciko duk-lokacin da yake tunanin ta
sonta » na matsa masa, sai ya ji' yana .sOn yin
kuka. Nan. ya mike da sauri dOn ba ya Son yin-
kuka’ a gaban mahaifinsa
Her ya juya zai tafl',"sai .kuma ya sake
jUYOWa yayi ya tsaya yana kallon sa.A lokacin
Daddy ya bude ido, ganin Sabeer .a tsayge ” ya
bashi mamaki, amma sai ya y1 dariya Ya taShi
gami da ‘sa glass dinsa, ya zauna tare da jingina
a jikin gadon, ya ce
"Sabeer, kaine da safen nan?"
Ya fada yana ‘murmushi, fuskar‘ sa cike da
faraa'a tare da jin dadin ganin dan nasa. .
Nan Sabeer din ya matsa gabansa ya zauna,
haka kawai ya ji yana jin nauyin mahaifin nasa.
Ya dan sunkuyar da kai tare da fadin.
"Daddy, ina kwana?"
' Daddyn. ya jawo hannun sa yana murmushi, ya
ce
"Laflya Sabeer...". Tare da fad‘m.
"Lallai na yarda aure mai gyara mutum, mai
kuma mai da yaro babba. Yau
na ga Sabecr dina ya girma, yau na ga wani
nutsuwa da girma a tare da kai. ALHAMDU
LILLAH da samun abokiyar rayuwa irin
Deeda.Sabeer ,kayi dace kwarai, ka rike. yarinyar
nan amana,'kuma hannu‘bibbiyu‘. kullum' 'ina‘
maka‘fata da addu'ar samun kyakkyawar rayuwar
aure, ba .na fatan -_rayuwar ka ta Zama irin
nawa, me. cik’ da ‘keWa, rudani da rashin ‘
nutsuwa da kwanciyar hankali.‘ Ina maka ‘_
addu'an rayuwar 'aurenka ta cika da farin ciki, '
ka rayu da iyalin ka cikin farin ciki da kaunar
juna. Yau na ga alamar cikar burina a safiyar
auren ka; yau Sabéer dina ya riga Daddyn sa
tashi,‘ya.shirya‘tsab, ga wani sabon nutsuwa. a
tare da kai. YarOna ya Zama (serious) ya girma,
ba - sauran yarinta, ba fitina, ba rigima. .Zan ci
‘gaba da muku addu'a Allah ya barku- ,tare da
Deeda har iya qarshen rayuwarku " Ina ga lokaci
Yayi 'da-'2an bar“ ‘maka‘ komai 'kai da‘yan
uWanka, inada‘ tabbacin kai da Ibrahim kun isa".
Tunda'. Daddyn 'ya‘ soma magana kan Sabeer'
na sunkuye', Wani' irin rudani, da
baqon yanayi ya dinga ji a'jikinsa'da- zuciyar sa,
haka wani irin tsoro ya jii'Yana shigarsa. ‘ _Ya’
dinga jin wasu‘ 'irin bakin abUbuwa a jikin sa da
zuciyar sa wanda bai taBa jin irin su ba. .Haka
kawai‘ya ji‘ wani irin Kaunar mahaifin sa da
tausayin sa tare da fargaban kar‘ mahaifin sa ya
gane Deedan guduwa' tayi.' Nan ya yi qarfin hali
ya dago kai, ya yi murmushi ya ce "Daddy na
gode da addu'o'in ka,~ da kaunar ka gare ni,
Allah Ya saka maka da gidan, Aljannah. Kafin
yanzu ban taba gane muhimmancin ,ka da irin
Kaunar da kake 'min ba ‘sai yanzu. Daddy,-
(please) ka yafe min duk abinda na maka a
rayuwa na Bacin rai, da fatan ‘za ka sa min
albarka a rayuwa ta,‘ ba zan sake duk abinda ba
ka so ba ina bukatar addu'ar ka fiye da komai".”
‘ ‘ Ya, kwanta a~jikin mahaifin nasa gami da
fadin. _. - . " "Daddy ka yafe min".
Daddyn ya yi dariyar jin dadi ya ce
"Sabeer na yafe maka, kuma zan ci gaba da
maka addu'a Allah ya baka sa'a da nasara a
dukkan abinda ka sa a gaba, Allah Ya sa maka
hakuri da juriyan mu'amala da mutane a duk inda
ka ke
Sabeer ya dago kai ya yi dariya, ya ce.
"Na gode Daddy, dama ina so- in roKi. alfarma ne
Kafi in koma aiki office ina so mu yi wata tafiya-
ni da Deeda na dan tsawOn wani lokaci, in mun
dawo In-sha Allah zan koma aiki, haka nan ba za
ka samu matsala da mi ba. Kafin in dawo aiki sai
Uncle Ib da Sister su cigaba da aiki kafin mu
dawo". ,
Daddy ya yi dariya ya ce, "Na fahimta, lokacin ka
ne yanzu, ba mai. hana ka taflya. Ka dau Deeda
ku zaga duk inda za ku zaga a duniyar nan
na‘tsawon lokacin da ku ka ga dama, ku ka
gama hutawar ku, sai ku dawo. Offlce da‘ aiki zai
'jira, amma wannan lokacin na ku ba zai jira ba,
wucewa
zai yi. . Saidai duk inda kuke ka dinga waya
muna jin labarin ku, ka kulada kan ka da Deeda;
.ka tabbatar kuma ka, dauki .(Debit card) .dinka,
duk’ inda ka. keza ka ,iya,cire
kudi yace To Daddy, na gode, ba'zan manta ba;
Allah Ya kaara lafiya, A‘llah Ya kara girma
da daukaka'
'Ameen Sabeer'
Nan suka yi 'Sallama cikin farin ciki da son
juna,mahaif1n sa na godewa Allah. ‘ ’ Yayin da
Sabeer ya fice, ya nufi jikin motar sa ya jingina,
tunani kala kala a ransa. ;Yana godewa Allah da
Ya. Sa Ibrahim ya tsai da shi bai je ya’ fadawa‘
mahaifinsaba. "Tabbas da ya‘je‘ da bai 'ga
'Wannan farin ciki da nutSuwa a ‘ tare da
mahaifin. sa ba, Wanda ya'samu ta dalilin, sa. '
‘ .- ' " ya wuce wurin yayarsa, a nan ya tarar da
ita tare da Ibrahim. Kansa a sunkuye ya gaiShe
ta, ta amsa tana' murmushin Karfin
hali, tana tausaya masa, saboda ta gama jin
komai wurin Ibrahim. ". ' Sabeer yace, "Sister zan
wuce". , "To Sabéer,.Allah ba ‘da sa'a allah ya
kiyaye hanya"; .' ‘ Ta fada cikin muryar rauni, ya
amsa
.. ."Ameen in. Sannan ya kalli Ibrahim, ya Ce.
‘ ' "Uncle Ib, (Please za' ka kaini ‘tasha
inda zan samu motar Kauyen su Dedda?"
’ Farida ta kalle’. shi, "Haba Sabeer, ka
tafi da .motar ka mana, ba sai ka shiga
motar kasuwa ba". . '
. " Ya girgiza mata’ kai, "A'a-Sister,
zan fuskanci Wata sabuwar rayuwa ne. Ina
so ‘in ga iyakar'iyawa .ta, ‘da juriya ta; Kafin
in tabbatairwa da kowa ina Son tabbatarWa
kaina, me zan iya? Meye ba zan iya.ba? _ Sister,
kar'ki damu, na san rayuwar da
zan fuskanta ba‘mai‘ sauki ba ce, "amma zan
iya insha Allah". " '
' ‘ Yakalli Ibrahim, yace"Uncle Ib, zan jira'ka a
mota". Nan ya juya ya fita, Farida ta'.bishi‘ tana
Kwala _ masa ‘kira hankalin ta a “tashe, Ibrahim
yajawo ta. ' ' " ‘"Kar ki tsai dai shi Farida, in ki ka
hana shi tafiya yau‘ zaki yi dana sani a gaba, ki
Kyale shi. Lokaci na farko kenan Sabeer zai. yi
'abinda yake dai dai, ya soma fuskantar gaskiya a
rayuwa, ya soma gane' yadda ya dauki rayuwa ba
haka take ba"; Farida ta fashedakuka,tace' '
,"Haba Ibrahim, Sabeer ne fa? Ya 2a ka barshi ya
tafi wani wurin da ba zai iya k0 da kai kansa ba
balle har- ya iya gane wurin? Ya za a yi ya tafi
shi daya,-yaron da bai taBa fita k0 nan nan shi
daya ba? Yaron da. 'zaman Nigeria da Kano ma
ke masa wahala, shi me‘ za ka tura shi wani
Kauye? Ya zai ‘rayU, a w‘urin?‘Me. ,zaici? Me
zaisha? A inazai kwanta?
‘- ’Ta fashe da kuka. "Gaskia Ibrahim
ba zan yarda da’wannan tsarin ba, Daddy ~ma in
yaji_ ba zai ‘ yarda ba. Wai' ka manta Sabeer'da‘
Yanayin sa,‘ne.?" ~(Please) F arida". Ya'katse'
ta. _ "Ki. Kyale‘shi, Sabeer mutum ne, kuma;
namiji ne. Sannan kar ki manta matae 'sa
zaibi,matar,sa'2ai nemo, yana da dukkan- dama,
" (right) dinsa-ne ya je ya nemo matar sa, ya
dawo da ita, ba wanda zai yi'masa wannan. Ya
zama ' dole ya. dauki \dukkan wani
(responsIbility). nasa,-ya dauki 'dukkan wani
nauyi da ke kansa'; Shi zai wa kanSa_ wannan ba
wani ne zaimasa ba " . “ ' . " ' ~ Kar ki manta.
magana ne da bani na mutuncin sa; da kimar sa,
da a. idon matar sa. Ya zama dole ya tsira': :da
~ mutuncin,'da‘darajar sa a idon matarsa Kar
kimanta, a ‘halin yanzu Deéda‘ ita ce rayuwa da
duniyar Sabeer gaba daya ya‘ zama doleta gane-
haka, Ya zama "dole'ta fahimci' ceWa yadda
take‘tunanin. Sabeer‘ ba
haka yake ba, .ya zama dole tasan Sabcer abin
'sone, abin ,alfahari ‘né ,ga ‘ kowacce- mace.,
Haka’ nan duk_ duniya ba zata .samu miji irin
Sabeer ba, ba za ta samu mai son‘ta ' _ irin'
Sabeer'ba; ,Ko ba za ta" so shi‘ ba, ya‘ zama
dole ta San kimar sa da darajar“ sa, da
muhimmancin sa.~ Kiyi Koqarin fahimta Farida ba
abinda zai samu Sabeer". ‘
Nan ta zaUna ta fashe-da kuka, tace1 _ "Ibrahim,
ina tausaya masa ne, shin Deeda‘ta cancanci- ya
sha wannannan wahalar
saboda ita?" ‘Yayi murmushi, ya ce, "Yayata,
wannan lokaCi ne zai iyé nuna ta cancanta k0
a,a?
Nan ya juya, "'Ni na tafi kaishi‘ tasha, sai na
dawo". . Nan- ya fice ya barta tana kUka tare da’
tausayawa Kaninta.
Tunda suka fara'tafiya ba. wanta ya' cewa kowa
komai, har. Suka iso‘ tashar. (Bus)
da‘ zai je .Dawakin, ‘Tofa, daga nan in ‘ya sauka
zai samu motar da zai kaishi qauyen su Deeda,
'hayin HAGO‘. —. ‘ ‘
Nan Ibrahim ya biya kudin motar tare ‘da‘yima'
direban motar bayanin cewa in sun sauka a taSha
ya néma masa motar‘da za ’ta kauyen Hayin
hago ya sa ‘shi. Direban yace in. sun isa. Zai
samumota, amma Sai .akori kura, don ba
kowacce 'irin mota ke shiga ba, sai manyan
manya irinsu ‘ akori kura-din ‘ Ibrahim '-yayi -
dariya don ya san_ da,
wannan, sai dai ya. tambaya a gaban‘ Sabeer ne
"saboda yaji da kunnen sa
Ibrahim ya- kalle' shi, yace
. "'Ka ji,'ko za ka iya?"~ -. .
Jikinsa a sanyaye ‘ ya girgiza. kai al'amar eh‘ zai
iya. Sai dai da alama- tunda 'Sabeer ya zo tasha
yaga ‘yadda yanayin’ yake hankalin sa' ya soma:
taShi. '
~' Ibrahim ya ja hannunsa ya shigar. da shihar
cikin‘ (bus) Ganin yanayin cikin' (bus) din, da irin
kalar‘ mutanen “da‘ ke ‘ciki
ya shiga zuciyar sa ta dinga‘ harbawa, tsoro
karara ya bayyana a fuskar sa.
Ibrahim ya kalle shi, ya ce
"Kar ka damu, ka kau da kai ga komai a nan, ba
wani abin tashin hankali. Ba wani abu a nan, duk
komai da kowa‘ a, nan (normal) mutane ne.
Kayan ka na ‘bayan- (bus) din, inkun sauka ka
kula,_ ka dauka kar ka manta".
Ya mika masa' Karamar wayar sa, ya ce
"Za tai maka amfani,‘ haka nan'a duk lokacin da
ka ji Wani baKon yanayi ko tsoro', ko wani
shakka, akwai' (application‘) na addu'o'i, ka bude
ka karanta. ' 'Akwai Alqur'ani a ciki, shi ma ka
dinga karantawa (you will be fine). Na sa
maka’sauran waSu tarkacen cikin ‘jakar kar,
wanda qila zasu yi maka amfani. Ni zan tafi,
Allah Ya kiyaye hanya".
. Bai yarda ya kalle Shi ba, saboda bai son ya
karaya, don haka ya juya zai tafi
Hakan ya sa Sabeer ya mike da sauriya kira shi,
ya Kankame ’shi, zuciyarsa'na harbawa, tsoro
Karara a fuskar sa. ’ - Ya rungumeshi, ya ce. ~
'.'Un‘cle Ib, inajin tsoro (I am seared) kar ka tafi
ka barni, kazo mu tafi tare, (I am scared of being
alone)". ' Ibrahim ya, tausaya masa sosai, ya ji "
tamkar‘ ya hana shi tafiya, ya ji kamar ya ja . shi
su koma. Sai dai hakan ba‘zai yiwu ba, inya
tafi'da shi Wurin,Deeda shirinsu zai warware. ' .
Ibrahim ya dago shi 'daga jikin sa, ya masa
murmushi cikin karfin hali, don ba shi Karfin
gwiwa, yace. _ ‘ ' "Sabeer, wannan yaKin naka ne
(and you must-do it alone). Kark‘a' ji ,tsoro, ba
komai, ba abinda zai faru da kai. Matar' kaza ka
je ka' dauko, ka tuna'Deedan ka, Wacce _ta ke
rayuwar. ka da farin‘ cikin ka a yanzu tana can,
bai kamata ka ji dar ba, ba kai“ kadai bane; Allah
.na tare ~da kai, saboda
niyyar ka mai kyau ce, haka nan da lokaci kadan
za ~ka kasance tare da Deed, kar ka damu. '
. Kar ka manta duk abinda ya shige ma duhu ka
yi tambaya cikin kwantar da kai, in manya ne 'ka
musu cikin ladabi, in. yara ne ko sa'annin ka kai
musu cikin tausasa lafazi.. Ka zauna lafiyada
kowa ka ji?"‘ .,
.Sabir din'ya girgiza masa kai alamar ya ji.
Ibrahim: din ya~ zaunar da ‘shi, sannan ya‘ flta.
Sabeer ya-bi shi da kallo yana jin tamkar ya‘ bi
shi, 'har ya shiga mota yana kallon sa ta
window. Haka Ibrahim" din ya dinga kallon sa
shima hankalin sa a tashe,.ya rasa 'me .ke masa
dadi? Har motar ta tashi yana zaune a mota ya
kasa tuKin, kewa da rashin Sabeer ya shige shi., .
Tunda aka haifi Sabeer ba su‘ taba rabuwa ba,
duk inda zasu je suna tare, kafar sa Kafar Sabeer,
k0 Farida ba ta‘ kai shi kusanci'da .Sabecr ba.
Haka Sabeer shi ne mutumin da ya fi kusanci da
shi a dUnia
duniya fiye da kowa; kullum suna tare, .su yi fada
su ‘shirya. Ya zama tamkar uwa kuma uba ga
Sabeer; haka Sabeer ya‘ zama tamkar dansa,
abokinsa, kanin sa.
‘ Ya tuna Sabeer ba ya iya yiwa kansa 'komai a
'rayuwa, kula da kansa ma bai iyashi. balle kula
da kayayyakin sa. Zuciyar sa. tai; masa Kunci, ya
runtse ido‘ yana .addu'a a ransa, tare da yiwa
Sabeer addu'ar samun nasara, da fatan Allah
_.Ya kare shi. Ya jima a wurin kaifin'ya tafi ' ‘
Hakan ce ta kasance ga Sabeer, shi ma tunda
suka‘ ‘fara tafiya a (bus) din hankalin sa a tashe
yake, kallo daya in an masa za a ga'rudani da
tsananin tsoro da firgita Karara a fuskar sa. '
Rufe idonsa ya yi' gam ya Ki budewa tare: da
rungume jakar sa ta hannu Karama da ya goya a
baya ya ciro ya jefa wayar a ciki, ya rungume‘ta
tare da' damke idanun sa ‘yana addu'a; yana
kuma tunanin Deeda, ya‘ hango fuskar ta. .Wani
lokaci‘ yakan yi murmushi.
in ya tino zai je; ya ganta, zai ‘kasance tare da
ita., ,Da wadannan tunanen ya mance damuWar
sa,. har suka .iso karamar hukumar Dawakin
Tofa. A. nan‘ ya ga mutane na ‘ta sauka, shi dai
'ya rasa abinyi, ya tsaya yana kallon su har'
suka sauka duka. Ya lura kowa na ta harkar
gabansa. ~- Direban ne ya shigo ya ce, "Malam,
‘ba‘ za ka sauka ba' ne? Ba kaine mai taflya
Kauyen Hayin Hago ba?" Sabcer 'ya girgiza masa
kai ' tare da cewa."Eh zan je, motar ka ba 2a ta
iya kani ba?" Ya fad‘a‘kamar zai yi kuka, - '
Direbah' ya Ce, "Wa'? Ai mota- ta ba zata iya
shiga wannan Kauyen."ba, musamman yan ’zu'a.
damina; Akori kura ce ko babbar mota'masu
manyan tayu za su' iya ga wata can” akori kura'
kayi sa'a sun yi lodi za’su tafi kai" nono, sai ka
je' ka biya .su ku tafi. Amma' fa ba za ka samu
gaba‘ ba, don ka yi. latti ya cika, kayi' sa'a ma
ba za kayi
jira ba, tun safe suke'lodi". ‘ ' ‘
: Nan (Sabir ya taso ,ya fito yana bin mutumin.
yadda~ zai 'biya‘ kudin motar ma bai. iya' ba,
sai da direban ya taimaka masa ya ciro kudi a
aljihun sa, k0 Kirgawa bai yi baya miqa musu.
Nan ,suka tsaya suna kallon sa, Naira dari biyar.
zai ba su, amma ya Ciro kudi‘da yawa.
.. ' Nan mummin ya ja shi gefe ya' ce ’
' "Kai malam, shatar motar‘za ka yi ne
duka?""A'a kudin motar nake biya".
"Naira dari biyar ne ai‘ na fada maka". ' Nan ya
miKa masa dubu daya ya je ya biya masa,.da‘ya
kawo masa canji ya ce ya bar masa, nan ya
washe baki'yana ta godiy‘a.' Yanunawa Sabeer
bayan akori kurar ya ce, ya hau.‘ Nan. ya ‘ tsaya
yana zare ‘ido, buhunhuna ne a cike da
kayayyaki,’ sai wasu. Fulani guda biyu, bai san
ma a ina zai zauna ba-.- '
Ya juya ya kalli mutumin kamar zai. yi
kuka,_yace’A inaza‘n'zauna?" Mutumin‘ yayi
dariya, albarkacin alkhairin da kamin "Bari
in‘nema maka Wuri". - ' Nan ya~ matsar da
wasu kaya, 'ya gyra wani lungu inda zai iya
zama. “Sabeer' ya. .kalli mutumin, ya kalli
~Wurin,_yace. ‘ ' "A'nan zan zauna?Kwarai
kuwa";DA a Ina kake tunaninzaka zaunan
Hmmm
jama,a shin wai ita wannan Son DA ake magana
batasan ya kamata bane ya za,ai ta dau dan
babban mutum Mai naira kaman saber ta kaishi
wannan kauyen? ‘ ‘ lol
c y'll
hared a profile .
birnin gayu
chapter17
_ Ya ce, "Ai na maka gata ma, da sai dai ka
zauna a saman buhunhunannan' Ba yadda ya‘
iya, ‘hakaya yi ta Kokari‘n' haWa, da- kyar.
direban' ya taimaka masa’ ya‘ hau, bayan ya sha
kasa sau, biyu, a ukun ya dace ya samu‘ ya
shige, ya makure~-guri guda’ yana 'runtse ido
yana ji bayan sa na" amsawae.
; Direban ya tsaya yana kallon ‘sa, yana
mamak’i, don . ya lura , kamar " haWaye . ke
shirin f1ta masa Nan"ya"'shiga

6 Comments On BIRNIN GAYU
avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

??

avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

Perfect

avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

Good

avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

A

avatar
sadiya-umar

1 year ago

Reply

Good and interested

avatar
sadiya-umar

1 year ago

Reply

Good and interested

Please Login or Register in order to submit comment