Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta
zo ta rungume shi da gudu tana ' tsalle tana
murna tare da-wani irin ,dariyar da bai taBa ganin
irinsa a fuskar ta ba. ‘
Kan Inna takoma suna murna, yayin da ya' harde
hannu', ya kwantar’ da kai'yana kallon ta. Wani
sUkuni ya ji ganinta a' haka. .Bai _taba ganin
farin .cikia fuskar. ta kamar na yau ba.
Fitila ya dauko ‘yana' haska fuskar ta, ya ga ta
masa Wani irin kyau,
"Haka dariyar yake ina fuskar ki .Deeda? Me‘
ya'sa' ba‘. kya dariya, kullum ,fuska a dame? (I
will make sure) inga: kin fara dariya irin na yau, (I
will‘ Always giv you 'a reason to smile)". ' '
Haka suka kasance‘ cikin -tsananin farin ‘ ciki a
Wannan daren, musamman ma da ya Kara da Ce
mata su- Daddy ya bawa kwangilar. Ya kuma
tabbatar mata cewa Daddy ba ya fushi da ‘ita,
zuciyar sa 'tayi' sanyi. -
Deeda takalleshi ta dan‘ canja fuska, ta . ce
"Duk da haka Sabeer ya kamata ka koma Daddy,
don yana buKatar ka". ',' "Haka ne Deeda, , zan yi
koka‘rin ‘ komaWa inmun gama wannan aiki.
Kafin nan' ’ nima zanyi'kokari inga na gama
nawa' aikin na samun fili a zuciyar Deeda.inason
a sani ba zan taBa miki dole ba, dOn haka zan
Kara kokari, zanyi dukkan Kokari na ba tare da na
cutar da keba, haka ba tare da na sake
Batawa Daddy rai . ’ba Deeda; ba zan iya‘ zama
a inda bake ba, saboda Deeda in ba ke a .wuri 'ba
na iya komai, kwaKwalWata da zuciya ta‘ ba sa
iyo komai sai tunaninki damaganar ki,‘ . ,‘Deeda;
(I cant do without you by my side)": '- Nan ya
kwanta a kancinyar "ta kamar kullum, ya
dukunkuné kamar baby, tana "shafa kansa,
zuciyar ta ‘tayi mata‘ nauyi da tsantsar son. sa
Ya Zama dole yau ta sauke .- Wannan nauyi ko'
za ta ji sanyi a‘Zuciyar ta. "Sabeer". _ - ‘ ‘ Ta
kira sunan sa cikin murya mai cike daso
dakauna,tace. - ‘ . "Ya kakeji game ‘da ni? Kana
tsammanin har zuwa- yanzu Deeda ba ta fara ..
'son kaba? Kana ganin in har‘Zuwa 'yanzu‘
Deeda ba ta fara son ka ba sai yaushe?’ Ba ka -
taba ji k0 .sau daya a zuciyar ka cewa Deeda ta
fara sonka‘ba?”
Shiru ya yi yana 'kallonta
sa ido cikin ido, daga karshe ta kasa jure kallon
da yake mata, ta kau da kai.
Ya yi murmushi ya ce, "Ran dana soma jin k0
fahimtar Deeda na tana sona zan sanar da ke.
Ranar zan dauki Deeda na'mu bar garin nan tare
da Inna. Ina da tabbacin ranar tana tafe
kwanakusa". '
Nan ya juya ya kara gyara kwanciyar sa, yana
rungume da hannun ta har bacci ya dauke shi.
Nan ya barta tana tunani da zafin zuciya. Ita
kadai ta San irin tsananin da Zuciyar ta ke ciki
saboda rashin furtawa Sabeer abinda take ji a
zuciyar ta game da shi. Kullum tana son nunawa
Sabeer irin son da take masa, amma sai ta kasa.

a Washe gari Sabeer ya tara manyan kauyen da
sauran jama'ar kauyen ya fada musu abin arzikin
da ya same su, wanda ya ce musu wani Bawan
Allah ne mai kudi ya dauki nauyi. Ya fada musu
cewa mai BIRNIN GAYU; sai dai bai nuna musu
mahaifinsa bane, sai dai ya ce musu
_mahaif1n sane ya musu hanya da ya '20
Kauyen. Saboda Shi bai son. nuna musu wani -
matsayin' sa‘ nadan me' kudi, ya fiso su dauke_
shi _ a ; matsayinsa. .na,,talaka dan
.uwanSu. " ~ Nan fa gari ya karade da murna‘‘,
suna godiya ga Allah. ' . “ _ Ibrahim bai samu
.dawowa ba harsai bayan sati ' guda, kafin su
sami izini ya dan; dau lokaci, dukda k0 Kokarin"
Daddyn.’ Sai dai, daga Karshe sun yi naSara. _ ' ‘
Lokacin ‘da Ibrahim ‘zai taho tare'da: ,Farida ya
20, saboda ta ce tana son zuwa ta zauna' da
‘Sabeer‘ ko na kwanaki‘kadan ne‘ '
' kafinsu dawo. kowanne dare 'Deeda ta' kwanta
-‘barci ".ba' ya zuwa, soyayyar Sabeer da
tunanin, yadda Kauyensu zai ,dawo bayan. -‘
gama mUsu _gini,_‘da shi take~ kwana take
tashi~. -Yayin da Sabeer kullum" yake nasarar
'kara Karfin soyayyar Sa a zuciyar Deeda. ‘
Wata safiya cé wani‘ mummunan ‘al'amari ya
faru da ‘ Deeda, “wanda ya haddasa tsananin
bakin 'ciki"’da tashin ' hankali a rayuwar ta. ,
Kamar yadda “suka saba kullum,
Sabeer‘ya shiga da safe don ya-shirya su fita
. ; su duba gurin aiki. Lokacin Deeda.ta lura ya
ya"
manta rigar wankan sa‘ da‘yake daurawa.
' Nan ta yi saurin dauka ta kai masa, ba ta
shiga ba ta sa hannu da niyyar ajiye masa a
saman garu, kasancewar ginin bai da tsayi sosai.
A dai dai‘ lokacin Sabeer ya' dauki towel dinsa
yana daurawa, kamar da wasa ya dago kansa, a~
lokacin idon sa ya hango masa hannun Deeda,
wanda hakan ya mugun tsorata shi tare da firgita
mai tsanani, ya gigice saboda ganin yadda
halittar fatar hannun nata ya koma. Ya yamutse,
ya feso da wani abu mara kyan gani.
Ita kanta bata san fatarta ya kai haka yamutséwa
ba, ta san dai dama ya ‘fara yi
kadan-kadan, bai kai haka ba.
Kara Sabeer din ya yi mai firgitarwa tare da kiran
sunan Deeda, ya‘ fito a rude suka ci karo,
hankalin ta a tashe.
"Sabeer lafiya?"
Gaba daya ya kidime, ya ‘ kasa magana. Ya yi
cikin daki da sauri, ta bishi. Ta lura a tsorace
yake sosai, ya kankame ta tare da Boye fuskar sa
a jikinta‘, zuciyar sa na bugawa da Karfl, hankalin
sa a tashe. ,
"Deeda ‘ki Boye ni, bana son sake ganin wannan
abun. Wani abu na gani marasa kyan gani, ya
ban tsoro.
Deeda, abin ba kyan gani. Wani irin halitta da ban
taBa ganin jikinsa haka ba Deeda zai biyoni".
Ras! Rass!! Gabanta yai mummunan faduwa da
ta fahimci me ya faru. Tuni abinda ya taBa
faruwa da Sabeer ya fado mata, lokacin da ya' ga
Kadangare a dakinsa.
Hakan ya sa ta' mai da kallon ta kan hannunta.
"Inna lillahi wa inna ilaihi ,raji'un!". .
Shi ne abinda take maimaitawa a bakinta. Ita
kanta hannunta ya firgita ta balle Sabeer.
Ta fashe da wani irin kuka, ta tsinci kanta cikin
tsananin tashin hankali da kidima; ta rasa ma ya
zata yi?
Ta mike da 'sauri tare da bamBare Sabeer a
jikinta, ta yi 'saurin dauko hijabi ta sa fa rufe
jikinta'tare da Boye hannunta, ta_ nemo kaya ta
taimaka masa ya sa. Bakinta na bari, ta na kuka
tana lallashin Sabeer tare da bashi baki cewa ba
komai, ba wani abu a wurin ‘
Ta lura da wani irin zufa da ke. fito masa .tamkar
ruwa. ‘ Ta share- masa tana lallashi tare da tofa
masa addu'a, duk da itama hankalin ta ba ya
jikinta, tana cikin tashin hankali, tana neman
taimakon wanda za ta kokawa matsalar ta ya
bata baki. Amma ba ta da wanda za ta fadawa
matsalar ta ko da ~ kuwa Inna ce, saboda
tsohuwa ba za ta jure .
wannan sabon tashin hankalin ba. Ba ta da
sauran karfin- daukan wannan tashin hankali a
wannan shekarun nata.
"Deeda, ki kori abin nan, zai biyo ni,gashi nan ina
ganinsa a idona yana bina".
' Ya Kara damke ta,"Deeda...".- ‘
Surutun sa ya katse matta tunani, ta tallafe shi
gami da kwantar da shi a jikinta tamkar wani
yaro Karami.
Ganin yadda yake numfashi sama- sama ya
dada‘ firgita ta', ta rasa inda za tasa ranta,
addu'ar 'ma ta kasa, sai ta fara wannan ta' saki
ta kamo wannan, 'ta rasa abin yi. Kawa sai ta
fashe da kuka, Sabecr kam a take ya shide ya
"suma,tasa wata irin Kara, Kirjinta' kamar zai
Balle tsabar tsoro da bugawa da yake. ‘ ‘ '
"Sabeer, me ya same ka?"
Ta fito da sauri' ta debi ruwa tana watsamasa,
amma' abin,ya gagara.‘ Ta fita waje kamar
mahaukaciya tana ihu. '
jama,a "Ku taimake ni!!!!!!".
hared a profile .
birnin. gayu
k
chapter. 22
A nan ta yi sa'a ta ci karo da Ibrahim tare da
Farida da Inna suna shigowa. Ganinta a gigice
tana tana kiran' sunan Sabeer ya firgita su ‘duka,
suka nufi cikin _dakin da sauri dukkan su, yayin
da ta tsaya a Kofar dakin ta kasa shiga. .
' Kallo daya Ibrahim yai masa ya gane (Attack)
din da ya samu, tabbas wannan ciwon firgita da
tsoro da ’Sabeer ke da shi ba shi da magani sai
addu'a,‘ sai kuma wasu dabaru da shawarwari
daga masana wannan abin.. _ ' . ’ . ' Farida
rudewa tayi ta kasa yin komai,~ duk da ta san
matsalar Sabeer, amma ba ta taBa ganinsa cikin
mummunan firgita haka ba.
' "Sabeer".
Ta dinga kiran ,sunansa tana girgiza shi,‘
hankalin ta a tashe. .
Ibrahim din ne ya ci gaba ‘da "Yan" dabarun sa
wanda ya saba’ masa, tare da addu'a yana tofa
masa, yana shafe masa
fuska da ruwa. ' “ ‘-
Inna dai sai zama 'yar kallo,tayi don ba ta taBa
ganin Sabeer din haka ba, kuma tasan"
makamancin haka bai taBa faruwa da shi : ba
tunda yazo kauyen. Haka‘nan fitar su. da - safen
sun bar su lafiya a gida za su same su” 'a can,-
Inna kuwa ita tayi musu jagora don zagaye cikin
Kauyen‘. Deeda ko na bakin kofar dakin ta'_kasa
komawa ciki, hankalinta a. tashe, zuciyar ta -
cike’ da kunci da baKin .ciki; - ' . ' ‘ Sabeer din'
ta ji ya farfado, nan .ta dan daga labulen kadan
ta leka .shi don ganin halin da yake.
; Kankame .yayarsa‘ ’yayi- sosai, har
yanzu' da alamar tsoratar a tare da shi, sai dai
da sauki akan dazu.. . ‘ . ' . .Ya‘ ce, "SiSter, ki
daukeni 'a nan, kimaida ni gida inda ba zan sake
ganin wannan_ mummunan abun‘ mara kyan gani
ba. ‘ ‘ _ Zuciyar ta taji ta buga, .tsoro da
fargaban rasa Sabeer ya shige ta, ta ji gumi; na
tsiyayomata. Ba ta san tana Yiwa Sabecr wannan
Kaunar ba sai da ta ji 'za ta rasa shi.
Nan ta tsuguna tana kuka, "Wayyo ni Deeda ya
zan yi da raina in Sabeer ya taf1 ya " barni bayan
Soyayyar sa ta gama min illah, _. yanzu nake jin
sabon sonsa da. kaunar- sa a
raina?" ' ' Ibrahim ne yadinga shafakansa yana
fadin ."Kwantar da hankalin‘ ka 'Sabeer; ba ',
abinda za ka sake gani, kaf Kauyen nan ba su da
wani abu mai muni k0 abin Ki' da zai maka‘illa,
ka cire tunani a' ranka, ka ‘mai ‘da hankalin ka
akan _-abinda ya' kawo ka da kuma kyakkyawar
niyyar ka na "son kyautatawa kauyen‘ nan Har *
ka manta ' Deedan ka? Ka marinta da naka?" ‘
- ' ' Lokacin ya dago kai tare da: zurawa
Ibrahim ido, ya ce. ‘ ' * ‘ "Deeda na, ina take?
Zan zauna da ita
duk rintsi ba zan tafi ba Uncle Ib, zan zauna‘ in
karasa abinda na fara, kar ka cdwa Deeda na ce
zan tafi
Ya kalli Farida, ya ce ."Sistcr, zan zauna, ina son
zama da Desda, Deeda na ce ni‘ daya". ' .
Ya. fadi yana lumshe ido, yana maganar a hankali
har bacci ya dauke shi.
Farida ta gyara mai kwanciya tana hawaye Inna
na bata baki, yayin da Ibrahim ya fice gun deeda.
' Farida ta' dago kai tana kallon dakin sama da
Kasa, yanayin' sa da abinda ke ciki. ' A ranta ,ta
ce
'Sabccr dina da ya' saba da_ rayuwar duk wani
jin dadi rayuwar hutu, sam bashi da abinda ya
hada shi‘da wahala, haka ba ya" jurewa ‘wahala
ko kadan, shi ne ya 20 yana rayuwa a irin
wannan kauyen a wannan ' dakin? .
Tabbas Deeda na jinjinawa -son da Sabeer yake
miki yana miki so mai girma,
mAi karko, mai karfi kauna' ta asali. Dubi yadda
ya rame, ya. yi baki. Allah Ya sa‘ kin ‘ , fahimci
zuciyar kani na, zan yi koKarin bincike da kula da
takun ki, kina Son Sabeer k0 har yanZu? In dai
ba ki son kanina ina da tabbacin' babu zuciya a
Kirjin ki". . ._a waje~ Ibrahim ya kalli Deeda da
ke tsugune tana kuka, ya kira sunanta. . "Deeda?"
' ‘ ‘ ‘ , Ta dago kai ta kalle shi, suka hada“ ido, ta
sunkuyar'da kai. Hakan bai sa ya fasa. mata
tambayar da ya yi niyya ba, ya ce’. ' ’ " "Akwai
wani‘abu da Sabeer ya gani ya ‘ ’ forgita .
shi?" ,Zuciyarta ta harba, tambayar da take tsoro
. ' ‘ kenan, Amma sai tadaure, ta ce; . - ' "Nima
ban sani ba". Murya kasa—Kasa 'Amma ‘ai ‘kuna
tare,’ ya kamata ki,,,‘ Tayi saurin mikewa ta kalle
shi“a ’fusace,’ ta ce"Nace maka nima ban sani
ba, nima ’ ‘ban sani ba,_ ka kyale‘ni". '
, Tana gama fadi ta ‘fita da sauri, gindin gadar
nan- ta nufa, duk kuwa da ‘sanyin da ake tana ta
zabga kuka, ta rasa meke mata dadi. Shi- kenan
jikinta ya raba ta da Sabeer’. Ya zama'dole su
rabu k0 tana so ko'bata so. .» ,'Wayyo ni Deeda,
ya zan yi in soma rayuwa ba'Sabeer?“ ' ‘
.TsaWon aWa guda‘Sabecr na bacci, yayin-da
Farida da Ibrahim ke kaiwa da ‘ kawoWa, suna
'tunanin mene ne.'matsalar hakan? Duk tsawon
wancan lokacin Deedan na can tana, ta kuka,
yayin da aka bar Inna da ‘tunanin me ke“ faruwa?
Sabeer’ din 'kuwa na tashi' Deedan ya soma -
nema, da- bai ganta ba a gidan to ya san inda; -
zai je ya samo ta, bai Bata lokaci ba ya nifi
gindin KarKashin gadar. Ganin tana ta zabga kuka
ya daga hankalin sa.
"'Deeda me ya same ki? Me' akai’ miki?"
. 'Jin' muryar ‘sa a bazata ya firgita ta, ta ~
mike da Sauri ta Kara lullube jikinta
Bate lokaci ba kuwa ya rungume ta yana lallashi
tare da fadin
"(Sorry) Deeda, kar ki yi kuka, ko mene ne ya
same ki k0 ya Bata miki rai kar ki damu da shi,
saboda Sabeer yana son ki, yana kuma tare da ke
har abada. Sannan ba zan hana ki kukan ba (just
that) kar ki Boye min hawayen ki, ki 20 ki kwanta
a kirjina kiyi kukan ki, ni kuma in lallashe ki".
.Hakan ya sa‘ta Kara kwantar da kai a
' jikinsa, hawaye na tsere a fuskar ta, yayin da‘
'take jin wani irin ciwon son sa mai radadin
gaske yana ratsa ta.
"Wayyo Sabeer,‘ ta yaya zan fada maka wannan
mummunan halittar da kake tsoro wanda
.hannuna kawai ka gani ya tsananin firgita ka, ta
yaya zan soma fada' maka haka dukkan jikina ya
koma lokaci daya? In har ba za ka iya jure ganin
na hannuna ba ta yaya za ka soma jure ganin na
dukkan jikina? Ta
yaya zan fara fada maka cewa ina kukan ciwon
sonka, ina kukan rabuwa da kai? Ina
kukan rashin miji mai tsananin' so na? Ina'
kukan kasancewa da kai ayau. na karshé? Ta
yaya zan soma fada maka matsalar da ba ka da
.maganin ta? Ta yaya zan soma fada maka duk
wahala da' kokari da kayi don ka‘ ‘ rayu da
Deeda ba za ka taba‘ Sanin Deeda ka rayu da ita
ba? Saboda'Deeda ciwo ce, cutace a tare da kai,
wacce bashi'da magani sai rabuwar mu. Abu mai
ciwo da wahala a rayuwa ta yanzu shi ‘ne yadda
zan danne sonka’, ; Boye shi, in binne shi a
Karkashin zuciya ta,~ in' kuma, nuna maka ba na
Kaunar ka, kuma .ba Zan taBa kaunar ka ba, don
kayi’ gaggawar barin rayuwata kafin nai
maka‘illah". ’ Wasu sabbin hawaye 'Suka gangaro
' mata, ‘ta qara kankame Sabeer' kamar za ta.
koma . jikinsa su harsu zama- abu guda, 'yayin
da shima/ yayi ,mata kyakkyawar " :riqo "yadda
za ta' ji dadin kwanciya a. "jikinsa‘." _Sun jima
ahaka sannan .ta zare jikinta
a hankali ta juya ta nufi gida, ya bita yana kiranta
tare" da mata surutai da tambayoyi,” ' amma ba
ta kula shi ba. Sai dai bai damu ba, dama ya San
halin ta,‘miskilar gaske ce, ta saba masa-hakan;
~ '
* -* *
Tun lokacin da abin ya faru Deeda’ ta‘ . daukewa
Sabeer wuta‘ gaba daya, ba ta kula ' shi, ta
.janye jiki‘daga shi al'amuran sa gaba daya, duk '
da 'ba abinda ta rasA ‘a rayuwar ta kamar ‘ ganin
,Sabeer k0 jin muryar sa,'- yayin da ganinsa.
cikin tashin hankali yaf1 komai. KunCi a‘_
rayuwar. ta.- a'Haka nan abu mafi kunci a
rayuwar. ‘Sabeer shi ne‘rashin Deeda.wannan
al'amari ya mugun daga masa’ hankali,‘ sabon
canjin dayA ‘yagani a‘ tare. da Deeda’ ya jefa shi
cikin kunci da~ tsanani, Wanda a .tunaninsa'
ganin Ibrahim yasa ta" daina ,kula shi, 'ya soma
tunanin har yanzu ' Deeda Ibrahim‘takeso ba shi
ba. '
Haka Farida da Ibrahim din duk sun lura ‘ da
takun Deeda, wanda suka kasa fahimtar ina ta sa
gaba. ;'
Duk da ana ci gaba da aiki ~a kauyen; komai na'
tafiya dai- dai, kullum suna tare a wajen, amma
Deeda ba ta taBa 2ama kusa da ' Sabeer, daga
ya matso kusa da ita sai_ ta tashi, k0 a gida k0 a
gun aiki. Bata kula shi, kullum fuska a dame ma
take gaida shi, yayin da duk wata hidima da
takemasa da ta
daina, sai Inna ke masa. Innan kanta abin ya
dame ta, ya kuma
daga mata hankali, don da ba haka ta san Deeda
da Sabeer ‘suke ba.Ta yi fada, ta yi nasiha,
amma Deedan ta kafe.
Lokacin Sabeer ya Kara ramewa, ya
fara fita hayyacin sa. Tunani ya, yiwa zuciyar sa
da Kwakwalwar sa yawa, sam ba ya iya bacci sai
dai ya sace shi. '
. Dukkan su suna tunanin Deeda Sabeer ne ba ta
so, kuma ba za ta taBa sonsa ba, musamman da
ta ga Ibrahim a kusa da ita a
yanzu. Sai dai 'shi Ibrahim"ya 'san Deeda'
Kwarai, ya karanCeta,_ dole~ akWai abinda take
Boyewa,_musamman ma- da ya lura in ta ga
Sabeer'ta fiye shige masa, wanda‘hakan . yake~
haukata zuciyar Sabeer tana‘ daisa,
mummunan kishi a zuciyarsa., Lokaci guda Deeda
ta' juyawa Sabeér baya, Wanda wannan ya sa'
ya rasa nUtsuwa ‘ da kwanciyér hankali, gashi
kuma ’bashi- da _ ikon" mata dole, Duk ,dabarun
sa, duk ‘ kokarin sa ba abinda ya canja.‘
~ Wannan ya hana' F arida komawa, 'saboda ta
tabbata in ta tafi za'a' yi ba dadi‘tsakanin Sabeer
da Ibrahim, saboda yanzu, ma k0 gai‘suwar ba ta
hada. su. Haka. nan ta,” yanke: shawarar 'samun
Deeda" suyi' magan‘ don kawo qarshen matsalar.
'A‘ kwana a tashi a hakan aiki’ ke tafiya-» ‘
SOSai, ‘lokaci guda‘ Kauyen ya dau haske," ‘ginin
ya fito da sosai, gini mai ~ Karko. Nan da nan
aka soma'-’shiryd—shiryen . bikin bude'asibiti
da' .‘makarantar ‘da aka'
gina, primary da secondry. Haka nan tuni an
dauki ma'aikata Wanda har da gidaje aka musu,
tare da tanadar musu duk wani abun more
rayuwa, kamar tonar bohol-bohol ‘a kauyen, tare
=da jan wutar lantarki, har (da solar) Daddy ya sa
aka sa musu.., . .
‘ Gaskiya Dr. Sulaiman yayi koKari kwarai, don
kuwa ya zuba dukiyar sasosai a Kauyen, ba don
komai , ba sai don komai ba " sai don taimakon
al’ummar yankin, ;don inganta _rayuwar, ;su da
kuma nema’ musu abin yi, tun ‘daga kan sana’a
har karatu.
Tabbas ya samu 'ladan Al'ummar yankin ya
kuma .sha ~Addu'a‘ sosai da - Albarka a
wurinsu. Hakanan ya ba da misali . Wa
takwarorin sa masu kudi dan kuwa‘ nan da nan
masu kudi suka fara rige-rigen koyi dashi’
musamman masu son shiga siyasa, a . tunaninsu
siyasa yake. Saidai shi Dr Sulaiman bai » taBa
tunan-in k0 sha'awar' siyasaba. _
Ana .Washe gari . za'ayi. bikin bude
makaranta da Asibitin Farida ta samu'deeda dan
suyi magana.
A harabar Asibitin ta same su ita da Ibrahim suna
duba yadda ginin ya tsaru, suna tattaunawa.
Farida ta isa garesu, ta yi musu sallama suka
amsa a - tare. Ta kalli Deeda, ta ce.
"Na yi mamakin samun ki tare da mijina
maimakon mijin ki".
Deeda ta sunkuyar da kai cikin jin nauyin Farida,
ta ce
"Na 20 sake duba ginin ne, shi ma"
Ibrahim ‘ya 20, sai muka hadu, amma ba wai tare
muka 20 ba...". ’
"Ba sai kin min dogon bayani ba". ‘ Farida ta
katse ta.
' "Ba wannan nake bukata ba, magana nake son
yi da ke na mintuna kadan in be za ki damu ba".

Ibrahim na jin su bai ce musu komai ba, saboda
bai son wani sabani k0 rashin fahimta ya shiga
tsakanin su. Harya juya zai
' " tafi saya tsaya; Yadawo wurin Fafida, ya kalle
ta—yace‘. Yayata, ina- fata kin yarda da ni?" ~
_Ta yi murmu Shin yaKe,‘ ta girgi kai. _, Shima
murmushin yayi mata, ya kalli 'Deeda, ’sannan ya
Wuce; " ' , .. Farida ta. mai ‘da hankalin ta'- kan_
Deeda, ta zura -;mata ido, . Deedan- kanta_
sunkuye,tace.“ ., ,' ‘ . ‘ "Deeda‘, tambayoyi uku ke
damun ' kwakwalwata da _zuciya ta, yau ,nake
zaton k0 zan dace‘da samun amsar‘su. .. r . Na
fi' k0wa mamakin," shin‘me'Sabeer 'da Ibrahim-
Suka gani a’ jikin ki? Me suka gani ;a tare da ke
da babu ’shi a sajin 'yan’ _matan duniya? Na
rasa dalilin naCe miki da suka yi; Tunda’ "rashin.
da' Sabcer suka hadu da ke koWacce‘ rana son
kaunar 'ki, ‘ zumudin ki kadai nake. gani a tare
da su, da , ke suke kwana .Suke tashi. Shin ,wai
meye'
‘ ' sirrinné?”
Deeda ta dago kai ta kalle ta, ta ce "Bani" da
wani; sirri, Allah Ne ‘shaida ta, wannan ikon Sa
ne". ' ' Farida ta yi murmushi, ta ce. '
"Na ji wannan. Na biyu shi ne, ba kya jin kunya‘
kina matar aure kina‘ keBewa da mijin da ba
.naki' ba? Kina» auren Kanina, amma zuciyarki,na
son mijina, ta wani wurin yayan mijinki, ta wani
wurin- mijin yayar mijin ki?’ Ba ki da hankali ne?
In; ’ilimin ki da addinin naki yake? Ina tarin
kunyar ki? Kin. Kira kan ki Hausa Fulani, amma
ayyukan ki ko Kabila ba zaiYi haka ba
Ta shake wuyan Deeda,‘ ta ce
"Akwai zuciya a-jikinki kuwa? Ba kya ganin' halin
da. Sabcer ya shiga saboda ke?'ba kya ganin
kokarin da Sabecr yake yi akanki guji ran da_
haKKin. sa zai kamaki kina matarsa amma sam
zuciyar ba tausayi? Inba ki so Sabeer don son"
da yake mikiba‘ baki ,so shi don abinda, .yayi
miki da ke da Kauyennan
ba kiso shi don wannan ba ki so shi saboda '
wayewar sa, in ba ki soshi don wannan ba ki so
shi don dukiyar sa, saboda ilimin sa, saboda
wayewar sa. In ba ki so shi don wannan ba, ya
kamata ki so shi don Allah. Saboda. Sabeer
yanzu ya koma namiji na gari, halayyar sa,
ayyukan sa’ba na banza. Shin Deeda me kike so?
Ya kashe kansa saboda ke?"
' Ta fada cikin zare ido da fushi, yayin . da‘
Deedan ke fidda numfashi sama-sama, saboda
shaKar da ta mata. Sannan ta sake ta, ta ce. ‘ ‘
"Ki bani amsa, me kike so a 'duniyar nan Sabeer
ya miki? Ko ransa ki keson dauka kamar yadda ki
ka fada?"
Nan ta yi kasa da murya, "'Deeda, ba laifinsa
bane, laifin munes. (Please) ki rangwanta masa.
In ganin Ibrahim ne yasa ki yi masa haka za mu
fita daga rayuwar ku, na yi alkawari
Cikin- karfin hali da 'kunar zuciya
Deeda-tace - Ba wannan_ nake so-ba'Sister, Saki
'- nake so daga Sabeer, ya fita daga‘rayuwa ta;
Bana' bukatar Sabeer', haka bana buKatar
Ibrahim,’ ba na buqatar duk ’Wani (member).
na'BIRNIN GAYU";
- .Baki isa .ba, . kinyi kadan, dole ki kasance
aBIRNIN GAYU Karki manta har- yanzu
mahaifinki yana cin arziKin BIRNIN’ GAYU, in har
mu ba zamu iya juya ki ba shi_ . " zai iya juya >
ki, kamar yadda ya aura miki' "Sabeer da farko
Na‘fada miki k0 ta tsiya ko'
ta arziqi' sai kin kasance da Sabeer“
.. Tuni Deeda ta ji hankalinta' ya'tashi; tabbas
.idan Suka- sako mahaifin‘ ta. cikin‘ lamarin
shirinta zai wargaje, Zai sa ta zama. , da .Sabeer
.dole,'-wanda duk yawan .so da . kaunar da take
masa'zai zamo da shi’ ne abu mafi' tashin
hankali a tare da'ita. -‘ '‘ Cikin' tashin hankali ta
kalli Farida tace. - Sister, please kar ki min
'haka', kar ki
sako mahaifina ‘ciki. Sister, kar ki zama mai -
son kai'. Ba na Son. Sabeer, ya za'a ki sani
zama da shi dole? Zama da mutumin da ba ka .
so gara kayi rashin wanda baka so". ' "Me yasa
Deeda?" ‘ . “ Farida ta fada ‘kamar za ta yi kuka.
"Me Sabeer yayi haka“ da ki kemasa Wanann
Kiyay‘yar? Laifin sa kawai don yana miki wani rin
mahaukacin so da ba shi - da iyaka? Deeda,
lokaci ya yi da 2a ki karBi Sabeer‘, ki yarda da
shi a matsayin Kaddarar ki, .Yau zan gaya miki
sirrin da ba ki bani ba, bayan mahaifiyar Sabee‘r
da Daddy, ‘ Sabeer ba shi da wanda suka ‘fimu
ni'da ' Ibrahim, mu ne rayuwarsa. _ ‘ ' A lokacin
da na auri Ibrahim mun yi rigima da yan 'uwana
da kuma Daddy, cewa '- dukiyar mahaifina ya
gani shi yasa yake son aure na, zai auri macen
da ta girme masa‘ don kwadayin abin duniya, Ba
irin tashin ‘ hankalin da ba mu fuskanta ba, har
suna
cewa daga ya samu kudi zai rabu Dani ya samu
Karama dai dai shi, Wanda hakan yasa ya yiwa
Daddy alkawarin cewa ba shi ba kara aure sai
wani ikon Allah, sai kaddara. Akan wannan
sharadin mukai aure da Ibrahim wanda zan iya
cewa ya cece ni ne daga hannun mayaudaran
maza, wanda ba sa so na don Allah sai don
dukiyar mahaifina. Bayan munyi aure akwai
girmamawa da shaquwa a tsakanin mu, .wanda
har ya haifar da soyayya a tsakanin mu. Akwai
yarda da 'fahimta sosai tsakanina da shi, haka
nan bai taBa tunanin wata 'ya mace ba.‘ Daga
shi har Sabeer ba su da wacce ta fini. Rana tsaka
.na fara rashin lafiya sosai,~ wanda daga baya ni
da Ibrahim da sauran likitoci muka fahimci ina da
(Levkemia Imyeloma). Hankali na ya tashi
Kwarai, saboda rai dai Kwaya daya ne, in aka
rasashi shi kenan. Wani lokaci ba mu fahimtar
kima da daraja rayuwar mu, da irin kyautar da
Allah Ya mana. sai mun 2a mutuwa kusa.
A lokacin da na fahimci ina da wannan mummuna
ciwon, a lokacin na ji ina son rayuwa ta sosai, na
ji ina son rayuwa da mijina da kuma kanina. Don
haka na dage da addu'a da (treatment) ba wasa.
Sai dai a hankali na fahimci rayuwata na karewa
ba- tare da na cimma manufofona da yawa ba,
don haka na fara da Sabeer. Kokarin gyara shi da
sauran su, na kuma dinga addu'ar . Allah Ya
kawo wata mace rayuwa: Ibrahim, haka Sabeer’,
Allah Ya bashi macen da za ta iya kula da shi, ta
kuma zauna da shi tsakani da Allah,

6 Comments On BIRNIN GAYU
avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

??

avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

Perfect

avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

Good

avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

A

avatar
sadiya-umar

1 year ago

Reply

Good and interested

avatar
sadiya-umar

1 year ago

Reply

Good and interested

Please Login or Register in order to submit comment