Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da nake so * komai wuya komai
dadi".
“'Na ji".
Nan ya mike ya fice. Momi murna ya lullubeta,
tace lallai na yarda tabbas Deeda alheri ce a tare
da ita dalilinta yau ta sa ta samu kamfani gaba'
daya
, "Wow! Amina'kudi kan kudi bari' ta_ Shigo in
san ‘daba'run da zan yi in turata ta fara zuwa
masa aiki. " yau‘.
,*.*j .*9*, *9* .
Deeda ta ga fitar Sabeer, .don haka ta tashi ta
koma cikin Falo ta samu ‘ Momi. Har za ta‘wuce
ta kirata; "20 mana Deeda, magana‘zamuyi". "To
Momi". . . Ta fada lokacin da take kokarin
zaunawa., Momin ta ce, "Deeda magana zamu yi,
don Allah ina so in rokeki wata alfarmane, wani
aiki na ke so in qara miki, amma in zai miki yawa
zan iya rage miki wasu daga cikin ayyukan da ki
ke min”. ‘ "To ina jinki Momi".
_"Wani aiki ne"?
"Allah Yasa‘dai baif1 karfina ba".
Momi ta gyara zama ta. ce, "Daman ina son ki
dinga zuwa Bangaren dana kina kularmasa dashi,
ne kina gyara masa‘ kamar yadda kike gyara min.
, .
" Deeda ta kalleta cikin ware ido da alamar zai
yiwu? Ta‘ce; "Hajiya namiji nefa, kuma- bai da
mata "Karkidamu, in ya fita da’ Safe sai ki gyara
ki dawo‘ ba-zama za ki yi acan ba. kamar: girki
'in kin dafa kawai ki shirya a Table ki dawo‘ —
Dana ne bashi da matsala ba zai miki «bin da ki
ke tunani ba, ki yarda' da ni ba zan kaiki inda 2a
a cutar da ke ba, kuma ba zan bada dama ya
cutar'da ke ba, yaran gidan nan suna da tarbiyya
~suna: da halin girma. Please Deeda taimakona
za kiyi".
Haka Momi ta marairaice .tana' rokon Deeda, duk
da ta .san‘ wani tsiyar Sabeer ya shirya mata
DOn dole Deeda ta amince da buqatar Momi
sannan sabo da Ibrahim, amma ba don ta so
hakan ba. -
Ta ce, ke nan Hajiya na ji zan dinga zuwa
namasa in dawo, amma fa in ya némi ya keta min
mutunci ba Zan kyale ba,~ zan dau mataki.
Sannan zan yi magana da Inna mai Fura in ta
amince shi ke nan".
'~‘To' kar ki damu ba sai kin je ba ma zan sa a
daukomin; ita zan nema mata Wurin zama a
BiRNIN GAYU. ta dawo kusa da ke, inaga zaki fi
Sakewa in kuna zuwa aikin tare da ita
Deeda tayi wani lallausan.murmushin jin dadi. ' ‘
-
Ta ce, na gode, za ki dawo da kaka kusa da ni
"Kwarai Déeda. wannan qaramin aikine ne da zan
iya yi sabo da abin da ki ke min :na. kyautatawa
kuma wannan aiki da kika karba yau.
Komai zan'iya sabo da farincikinki, don. Haka zan
dauko Kakarki in dauki nauyinku, ,zan ba ku gurin
zama da dukkan wani abu .na jin dadin rayuwa
da zaisa ki farinciki".
"Na gode Momi, Allah
ya saka DA alkhairi
"Ameen. Sai dai Deeda ina son ki fara aikin daga
yau, sannan please ki bishi ahankali yana da
saurin fishi’da'zuciya, yananda fada, amma ba
shi da matsala, kar ki damu
Deeda ta ce, "To hajiya na ji".
A ranta kuma ‘té cr "Ni kuwa nasan fadansa da
halinsa, kuma nasan ya yi hakanne donya kuntata
min shi ya sa ya bullo ta nan, sai dai zan jure
wulakancinsa".
Nan ta mike ta yi ciki, ta canja shiga sannan ta
dauki 'Waya~za ta bugawa Ibrahim. Kafin ta kai
ga kiransa Wayarsa ta shigo.
Ta yi. saurin .dauka tare da yin 'sallama "Daman
ina shirin kiranka". ne yanxu
ya sauke ajiyar zuciya tare da fadin ’, yanzu aka
yi Waya aka fada min abin da‘ ya daure min kai,
ina tsammanin Sabeer ya samu Waya a wurin
wani a gidan nan. Ya kira Legal Adviser dinmu da
kuma MD. na Kamfaninmu da ke Lagos ya ce
yana so'ya barwa Momi Kamfaninsa Ya za
akayi Sabeer ya dauki Step din-nan ba tare da
sanin Daddy ba,kuma na rasa dalilinsa, na son
yin“haka, yana so a hada Takardu a kawo masa
Deeda ta yi ajiyar 'zuciya ta Ce, "Sai yanzu na
fahimci abin da ya sa Momi ta ke lallaBani. Wai
Sabecr ya dauki wannan abin da tsananin da zai
iya yin komai don kawai ya dau 'fansa ya
nunamin matsayina." ' ne
' "Me ya faru?" Ibrahim ya tambaya.
Nan ta labarta masa yadda akayi. Ya yi shieu na
dan gajeren lokaci ya Ce, "Sabeer ne fa, "kadan
daga aikinsa ke nan (He Will just do anything
Crazy) don kawai ya cimma manufarsa. Sabeer
fltinanne ne akan abin da ya sa gaba ko yayi
niyya.
Deeda ina gudun kar Sabeer ya cutar da_ ke, ban
zaxa zai Bullo mikita‘wannan hanyar ba
(He will to run you) za ki‘iYa kuwa?"
"Zan iya Ibrahim in dai wahala ce ai ba ta kisa,
wuya kuwa a cikinta aka haifeni a 'cikinta na
tashi na girma".
"Duk da haka Deeda in kin‘ga ba za ki iya yiba‘
to kibari kina ji?" -
"Na ji".
"Na gode". '
"Kar ka damu, ai Kudi Momi -za ta biyani' aiki na
ne". .
Dariya ya yi gami da girgiza'kai ya ajiye Wayar. '
'
"Deeda ke nan, wani lokaci halinta kama yake
min da na Sabeer".
Nan ya shiga tunanin. yadda zai tsai da_ deal din
da sabiecr .ya_ yi_ da Momi
Deeda kuwa Mayafinta ta dauko ta fito Momo da
kanta ta rakata bangaren Sabeer. din Sun yi
tafiya mai dan tsaWo tamkar ba a gida daya suke
ba, akwai tazara tsakanin bangaren Momi da na
su Sabeer.
Sun sami Sabcer zaune falo ya dora kafa daya
akan daya yana kadata yana jiran isowarsu. '
Tun daga falon Hajiya ta fahimci halin da gidan
yake, gaba daya akwai
Ta ce, "Sabecr ga Deeda, 'sai dai aiki za ta yi
maka ta tafi. Kuma don Allah a kiyaye",
. Kansa ya dage‘bai kulata ba, 'hakan ya sa ta
wayance, ta ja Deeda tana ‘nuna mata cikin gidan
kafin ya ma ta rashin kunya, ya kunyatala a
gaban Deeda. ‘ cikin da kewayen gidan ta nuna
ma ta, sannan ta juya ta tafi
Ya zaune a Wurin' Dccda ba ta kula Shi ba ta
hau yin abin da Ya ‘kawota. '
,. Gyaran Kicin ta ta fara’ wanda 'ba wani datti 'a
cikinsa sai sabo da ba girki ake a ciki ba, har'ta
fita falon ta share ta goge,,ta gyara duk
Barnar'da ya yi. "
Yana ganin tana Moping‘ya qi tashi a wurin,
kuma yaqi matsar da qafarsa, ita kuma ta Ki
kulashi ta wuce. .
‘ "Ke mai aiki!" Ya fada cikin tsawa.
"A gidanku haka aka koya miki? Kina ganin
mutum ba‘ za ki gaishe shi' ba?
Daman ''yan kauye Tala‘kawa ba hankaline da ku
ba
Ba ta ce masa komai ba, ta'dawo gami da
rusunawa ta‘ ce. "Ina yini?"
Kan da kai ya yi bai kulata ba, hakan ya sa ta
wucewa. Ya sake kiranta.
"Aikin nan bai- fita ba, sai kin sake, sannan idan
kin gama akwai wani aikin a daki.
Kuma kar ki zata-zan fita in barki ki yi yadda kika
’ga damane, ina nan idona akanki.
. Nan ma'bata' musa masa ba, ta koma ta fara
sake' goge-gogen ta sake sharan da moping din,
hakan ya qular da shi, don'ko a fuskarta bai ga
alamar ta ji haushi ba. .
Nan ta20 wucewa ta gabansa yai ma ta wani
mugun kallo. ke tsaya! " ’ Cak! Ta tsaya ba tare
da ta Waigo ta kalleshi ba. ' "Ina fata kin soma
ganin isata da power na, tun a nan kafin zuwa
gaba‘ zan nuna' miki ke matsiyaciya ce,
matsayinki a karkashin takalmina yake' Bai ‘Bata
lokaci ba ya sa kafa ya doke robar da take.
moping'din ruwan gaba daya. ya zube a wurin.
yasa hannu ya hankadeta, suuu!
kuwa ta tafi ta zame ta daku a kasan tayils din“
dakin. ’ ’
"Wayyo Allah na Ta fada kamar za tayi. kuka. ‘ ‘
' Ya kyalkyale da darin mugunta ya ce,* "Sai na
illa,ki na karya miki baya kin zo. baki da sauran
amfani. Su Miss. Manager an zama Mss. House
Girl. "
"Mugu kawai, Allah Ya saka min abin da ka yi
min, iyakar abin da zaka iya yi ke nan",
"A'a ba iyakarsa ba ke nan," yanzu muka fara, mu
je zuwa, oya! Ma za tashi ki goge ruWan da ya
zube
Nan ta mike da kyar ta nufl Kicin ta dauko wani
mopan ta hau gogewa.
Ranar dai har Kujeru sai da Sabccr yasa ta daga
ta share but bango sai da ta' gage 'ba tare da ta
huta ba, tana gamawa kuwa ta fara na‘dakinsa. ,
_
Anan ta galabaita sosai, Sabceq ya dau tsawon
kwanaki yana, war gaza dakin, amma ya sa ta
gyaransa a lokaci daya: ‘
Yamma lis ta mai da komai mazauninsa ta
kimtsa komai_ ta ki‘ra masu Aiki aka gyara
WindoWs din da ya farfasa. Shi ya yi mamakin
yadda ta gyara. dakin yadda ya yi kyau‘ya tsaru
ma; ya f1 na da.
Ta gama ta shiga (Bathroom) shima ta hau aiki,
ta- gama ko‘ina ya'dau Ramshi‘da baske. "
‘ A KOfar‘Bayin ta zauna tana hutawa, ga gajiya
ta yi lis, ya shigo ya sameta, ya tausaya mara
kwarai', gyan-gyadi ya dinga' kwasarta, tayi sauri
ta miqe‘da ta tuna tana da girki, nan kuma ta nufi
Kicin donyi masa girki, nan ta shiga kaiwa’da
kawowa don bata san me za ta dafa ba, kuma ba
ta iya‘ girkin’su ba 'don‘ita ‘kO Momi ba girki
.take yi'ma ta ba
Ta yi tsaye ta rasa abin yi, ‘Ya shigo ya sameta,
.ganin dai a yau ya ma ta mugunta ya
wahalar'da ita’ da yawa yasa ya Ce ta r
tashi ta tafi ba sai ta girka ba
Nan ta circ kai- ta kalleshi gami da kafa mai
idanu tace, "Aikina ‘ne kuma saina yi, bana son
'wani tausayawarka ko’ sassaucinka
dai ‘ina'da raina lafiya ta to duk aikin da ka bani
yau kuma sai na yi".
. "Fine, ‘ki‘ yi".-Ya fada cikin fishi. me kika dauki
kanki? Don- kin samu na‘
miki saSsaui‘i shi ya yi miki dadi'ko ki yi girkin
- yanzun nan, ina-son in, ga ~.
dishis
Abinci kamar kaloli shida da home made drinks
nanda awa daya Nan ya banko' ma ta kafa ya;
fice, ta bishi da kallon tsana da harara ta ce
"Wannan gayen kasheni yakc son yi sai ‘dai zan
nuna masa bai isa ba". ' ‘ ' Nan; ta dinga kaiwa
"da kawowu, ga lokaci na tafiya, ga ba abin data
iya. . ' Nan dabara‘ta fado mata ta kira Ibrahim a
Waya, tayi sa'a ya dauka. ‘ Nan "ta fada masa
matsalar, ya yi murmushi ya ce, ".Daga jin
muryarki ba ki ‘sha'dakyau ahannun Sabce'r: ba".
Uhm! Ka rabu da Wannan'qanin na ka, ban san
da wane suna zan kirashi ba, ban 'yi‘
tSammanin yana da zuciya, ba ta ,dutse ne a
kirjinsa".
Ibrahim ya kwashe da dariya ya ce "Yanzu dai.
bari in fada miki abin yi kafin sabon Boss dinki.
ya 20 da Bulala",
Ta yi kwafa‘ta ce, ".Ai na ga alama abin ' da
yai'saura ya yike nan,‘ amma ni dai—dai na ke da
shi". - '
Nan Ibrahim ya fada ma ta; wani Site na girke—
girken-da za ta shiga a' lnternet, Wanda yawanci
da irin.girke-girkensu masu girki ke yin koyi. . .
Ya fada ma ta irin abincin da sabccr ya fl so, ya
Kara da ce ma ta, "I'dan‘wannan bai yi ba taje
gun. Chief Cook na gidan~ ta karBi Littafin girke-
girke da~ kuma Menu na Abinci, k0 kuma zai yi
Waya ya sa a kaWo ma ta",
" Nan ta yi masa gOdiya, Sukai sallama. Ta sha
wahala sosai 'wurin gwada dafa abin da ba ta
taBa yi_ba, amma duk da hakan sai data nace ta
yi komai kasancewar ta samu sauKi duk abin da
take nema akwai shi' kuma akwai electroniac na
girke girke kala—kala da haka 'ta “
***“———————-——-—-—--—-—an
. ta hada Abincin, amma kicin din ya yi kaca-
kaca ya koma sama__ da Rasa. Haka ta hadasu‘
gun‘ guda ta tura ta kai maSa, ya sha. mamakin
yadda ta gama a lokacin da ya bata, a gabanta
ya bude ya dandana.. Tabbas Abincin ya yi dadi
amma tsabar yar bata mata rai, ya sa kafa ya
ture Abincin gaba daya ya zube
Taji Bacin rai da wani irin. bakinciki, amma sai ta
shanyeshi ta‘ce, "Allah Ya huci zuciyarka, zan
sake wani yanzu".
. . .haushinta ya ji ya Kamashi kamar ya ruféta
'da duka, burinshi guda yanzu ya ga ya quntata-
ma ta ya bata mata rai, ’amma yarinyarnan k0 a
jikinta, bayan ta kwashe‘ za ta fita yace ma ta,
"Ba saikin Sake ba, bana buqata
Ba ta‘kulashi' ba'ta fita ya bita da kallo, k0 me
take ji da shi oho?
"Ka ’ga 'yar Talaka da nunawa mutane Attitude".

Ba ta jima da fita ba ta sake dawowa ta
'ce"YallaBai akwai wani aikin?"
"Babu". Ya fada a hasale.
"Na ga alama kina enjoying aikin ne".
Ba ta- kulashi ba ta juya har ta fara tafiya ta
tSaya ta Juyo ta 'ce, "YallaBai .an .kira' sallar
magariba kar ka rasa jam'i, 'na ji ana‘kOkarin
Shiga, na gyara bayin- sosai, za kaji ‘dadin yin
Alwala". Ta fadi cikin sanyin murya.
"Naji". Ya fadi, "Zan‘ yi- yanzu, na gode
Murmushi ta yi masa tare. da daga masa kai ta
fita. ' ‘
Ya tsinci kansa da tashi ya” yi Alwala, rabon da
ya yi" sallah a jam'i ya manta.
Nan ya zauna har iSha, .sannah ya dawo ya
kwanta yana‘ tunani. '
Dccda kuwa tun data koma dama dai tana hulun
sallah, kawai zubewa tayi a gado, bacci mai Karfi
ya dauketa, wurin ka'rfe goma ta tashi, ta ji
ko‘ina a jikinta ciwo‘ yake
Wanka ta. shiga ta yi da ruwa mai zafi sannan
ta'hau Computer don dUba lecrures din da aka yi
na wannan ranar.don .bata Samu leqawa ba. tun
safen. ‘ . -
bayan ta gama abinda take ta dauko laptop ta
lissafa kudaden hajiya‘tare da yi mata“Transfer-k
amar yadda take mata a koWanné, ciniki Sannan
ta dauki 'Waya “taga miss call din Ibrahim, tare
dai Message dinsa, ~yana ma ta'sannu da yi ma
ta‘addu,a da kuma fatan alkhairi. : a Murmushi ta
yi'bashi ta bashi amsa da cewa"Na gode". ’
it I if. Q ii .it v 4*
,lbrahim yaje side din 'Sabccr,‘ yadda‘ ya‘ga ’
gurin ,-._ya tabbalar Dccda‘tayi aiki.‘ ‘ "
"Allah Sarki.baiwar Allah!"
Ya kalli Sabccr yace, "Amma naji dadi yadda
nAga wurin nan da‘alamar ' zamu shirya‘ga-
wayarka da komanka na dawo
dasu, amma fa har yanzu sai dai in office zaka
koma
sabccr ya ba shi amsa. ' ' .
"An fada maka. Waya daya ce. gareni
Kuma dama office ko baka fada ba, ina nan
dawowa, ‘ _
Sannan masu aiki 'da kake da ikon hanasu yi
mini aiki, to na sa wanda na "ke da ikon sata
aikin, kuma ‘ta yi. Na san dai za ka ji haushi in
na 'cé maka ba ni na gyara wurin kamar
yadda’na bata‘ba"
"Sabccr take it easy; ni fa ba abokin gabarka
bane", " "
"Mallam' fita bana bukatarka”.
Ibrahim bai masa musu ba. ya tashi ya bar
. Sabccr ya dauki Wayar‘sa, Farida ya kira. Ya
jima yana yi mata korafi akan Ibrahim, da kyar ta
lallashi ya hakura.
Nan 'ya‘ ce ' mata: 'yana . nan hanyar zuwa
wurinta amma sai .ya gama "abin da' ya yi
niyYa- ,
' Taji dadi sosai, sannan tace masa ita ma tana
nan daWOWa ta' samesu, zata daidaita
tsakaninsu da Ibrahim. " '
‘*v* _*v* ' .*b*
qarfc bakwai dai—dai Dceda na side din Sabccr
sai dai harta gama gyaran, ' falon da kicinsannan
ta hau saman,‘ Kayan'sa ne ’a ‘watse tun daga.
kan Takalma, kayans’a, _Waya, system _
Ta'tattara koma'i ta gyara sannan ta buga Rofar
dakin amma baitashi ba. Ta jima a’tsaye 'tana-
jiransa amma shiru. Ibrahim neya bugo mata
waya,’ bayan sun gaisa, tace masa',‘ ta yi_ ta
bUga qofa sabir shiru". ' v Ibrahim'yayi daeiya in
dai Sabccr ' ne za ki kwana k'ina-jira, dole kisan
dabarar da
zaki yi ya tashi..Ni ina da marasa lafiya, sai an
jimau' . r
Shiru tayi tana tunanin abin yi.
Can ta mike ta nufi Kicin ta hado masa kayan
Tea da da Ginger .Tea"tare da Milk ta'hado da
Ruwan zafi, sannan ta yanka Fruit ta nufo
Dakin‘sa.
ta jima tana tsaye a wurin, ta 'shiga k0 ta fasa. '
' ‘ ‘
Can dai' ta daure ta tura KOfar, a, bude ta ke,
duhu ne ya mamaye d'
akin tamkar dare. -
Nan ta aji‘ye kayak break din ta nufi Window ta
zuge Labulen ’nan 'haske ya bayyana a Dakin,
fuskar Sabeer 'da ke kwance yana fuskantar
Window ya ji haske ya takura masa,-Tsaki ya' yi
ya juya kai ya sake gyra kwanciya.
Bata kulashi 'ba sai da ta. gama tattara dakin ta
kimtsashi ta bude Fudge don gyara ciki, nan ta yi
Ido biyu da abin da ya daga ma ta hankali. ,
Kwalaben (Strong Wzlsky) ‘guda " biyu ta gani,
zuciyarta. ta ma ta zafi
Wato Sabeer har yan‘zu yana da. hanyar da' »
yake bi ya sha Giya tak0 tausaya 'masa don shi
‘bai san illar da yake -"'yiwa_ kansa da
rayuwarsa ba; DA bai shaba
ta tattarasu waje daya taje ta zubar ta ma’ye
gurbinsu da Joice da‘ kuma ruwa, sannan ta
shiga Ta gyra ta fito.
Har yan'zu bai tashi ba, duk" shiga da fitar da
take yi, bayan ta. gama'komai ta matso hannunta
like ‘da Cup din tana ‘taya za ta soma
tashinSa? .'
Can dai ta matsa dafda shi tana kiran sunansa' '
"Sabeer‘!~ SabeerH Sabeer!!!" Ta ja Tsaki ta Bata
fuska‘tace, "Yanzu'in yaji ya 'tada bala’i ya ce
shi Ogana ne. Sarkin yan gadara da mulki".
Don haka ta‘canja salo.
"YallaBai yallabai har yanZu'Shinru ‘sai ma gyara
kwanciya da ya sake ‘
Nan dabara‘ta fado'mata ganin yadda ya. kwanta
ya bude. Baki ‘ kamar wani baccin
qaramin Yaro ya sa ta dauko Cokali ta cikaShi da
Tea ta juye masa a baki. Nan take ta ga ya soma
lashe Baki.
, Ta sake kai masa na biyu;'t‘a lura bude bakin
ya qarayi ta’zuba masa yana, kuma fito da
harshensa yana bi. yana lashewa. ’ ' Hakan ya
bata. dariya ta matso daf da fuskarsa tana zuba
masa can ta kuma qura masa ido tana ganin
yadda ya ke sha tana dariya, tana kuma enjoying
kamar Wacce ta samu tV.
Ba ta ankara ba sai gami ta yi ya bude ido ya
zura mata idanu Cikin mamaki ganin yadda ta
sunkuyO daf da shi tamkar mai masa rada, hakan
yasa. ya yi firgigit! Ya tashi ita kuma hakan ya
tsoratata, gashi ya miqé ya fito daga' cikin Bargo
daga ‘shi sai' Gajeren Wando, hakan ya sa ta
buga ihu tare da sakin Kotin Shayin ya zube a
jikin lallausar fatarsa da bai .saba. da wuya ba,
wohoho sai zafi. ‘
Shima' wani Kara ya' saka, Karan azabar ruwan
zafin ya. mike tsaye-yana tsalle.
Dariya. ya bata, ta-kasa ‘daurewa ' ta zalle da
tana cewa, ",Ka yi haKuri
don Allah, .Wallahi ba da niyya na yi 'maka ba
.Haushinta ya kara kamashi, ganin tana mai
dariyar Mugunta, ya bita ta ruga da gudu, ya
sake cin tuntube da sauran Ruwan Zafin' da ta
ajiye a Tire din ya sake Zube'masa a kafa, gashi‘
daga‘ shi. Sai ‘gajéren Wanda. Wani ihun ya sake
sakawa',’ :
"wayyo Allah na
Ganin hakan yasa ta debo ruwan' Sanyi ta sake
watsa masa a Cinya tana ceWa, "Sony. Sir; Sannu
YallaBai".- ‘ ‘
' Ihun ruWan sanyin ya sake bayan na zafin.
Ba'ta ankara ba ya cafko Dankwalinta tare da
gashin ‘kanta ya hada ya damke ya.ja. da qarfi,
ta sa Kara: itama tana kokarin‘ kwacewa‘ ya ce,
"Muguwa Aljan'a"yar Kauye, so ki keki ‘ kaSheni
da azaba? "
Ki ka sake shigo min-daki sai na. cire miki gashin
kanki 'na karya yatsun Kafarki~ daya- Aljana
kawai!" Ya‘ ‘fadi‘ lokacin .da - yake kokarin cillar
da ita.
Sai da tata bugi'Gini ta tsugunna a wurin tana.
maida numfashi da
Ya yin da kuma sabeer ya nuf1 Fridge ya dauko
qanqara'yana shafawa a inda (ruwan' Zafin ya
zube 'masa. Wurin 'ya yi jawur! Kamar jini zai
Bullo.
Nan ’ya lura ‘ba Kwalabensa na (Strong
Wisky) a cikin Fridgege din. ~ Tana‘kallon‘sa ya
nufota 'da masifa. "InaKwalabe na? Ubanwa ya
ce ki ta am n
Frdge dina?" ‘ "Ba uban koWa’ ya ce in taba .
sai‘kai.
Nimai Aikinka ce, don biyana za ayi‘, aikina
ne cire datti da daudar da ke cikin' Fridge dinka.
Wannan' Giyar_ .da. ka san Kazanta da' illarta da
ba zaka yi ta durawa cikinka_ita ba, ka sani na
debésu na' zubar da su gaba daya, kuma k0 gobe
ka sake ajiyewa sai na sake dibewa; na zubar da
su!" ' "
"Ke kin isa ki taba abin da na ajiye ko ki hanani'
‘shan abin.._da' naga dama? Kin san TSadar su
kuwa?
Da ke 'da duk zuriarku duka in kun taru ba ,
za ku iya sayansu'ba.."
"Oho ,dai K0 me ma ka ceni dai na zubar, kuma
k0 yanzu ma kasa- sai na fasa"
Kafa ya daga zai‘ shureta; .Ta ruga da gudu, ya
bita: Ganin -bazai : kamata' ba ya‘ sa' ya ~‘
wurgeta da wani karfe “ya sameta k0 ta fadi‘
ta kama mayafalitana,‘ "Wash! Allah Mugu Allah '
Ya saka min,kuma yau ba zan karasa ma ka ba;
kuma gobe sai na kuma.'.."
.Ganin ya nufota yasa'ta mike da'dingishi
ta yi ciki tuna cewa, "Na san dai ba kai ,Sallah'
ba, dama 'kayi Alwala ka yi Sallah k0 za ka.
samu saukin zuciyarka, duk
rashin Sallah ya hanaka samun nutsuwa da
sukuni kullum kana'cikin fishi. Gwada yin sallah
akan' lokaci, 'ka ga yadda za ka dinga samun
nutsuwa." Tana maganar ba, ta daina ba‘har ta
‘bace.
Ya yi tsaki ya ce, "Aljanar Yarinya duk_ ta gajiyar
da ni'.‘.
Ya koma yana tattara kayan da‘ suka watse a
dakin, ya dora a tray din yana yin mita,
"Aljana na duaketa aiki; amma ni take sa
Aiki."Yar banzan Yarinya harta isa ta zubar min
da..." -
Ya_ kama kai lokacin da yaji kanshi mass zafi ,
wajen da ruwan Zafi ya konashi yana masa
radadi. ' . a
‘Wayyo Allah Na tsani Yarinyar nan. (I hate this
Girl]
ya dauki Wayarsa ya kira AbokansaNura da
Salim, don su sukai mitin akan abin da zai
mata wanda Zai ma ta ciwo, sannan ya kuma
kiran layin Momj ya ce ma ta yana son lambar
Deeda.
Cikin minti biyu'ta turo masa.. A lokacin da Ya
kirata..Ta samu ta isa tana jinyar kafarta tana
“‘ ' Wayarta ta yi Kara, da- 'kamar ba za ta
dauka ba don ba ta gane Layin ba.
Can‘ ta daure dauka. Kafin ta ce wani ,abu ya
rigata. ' ' . "Deeeda. » ' _ Ta gane muryarsa don
haka ba ta ce komaiba' "Deeda!" Ya Sake kiranta
da kuma karfi. " “Ta'amsa. ' "Me ye, ni kam kar
ka fasa min Kunne", Haushi ya ishe shi_ ya rasa
ma me zai .ce ma ta. Ya manta ma abinda ya sa
ya kirata"Na tsaneki Deeda". Ya ce a basale.
"Na-tsaneki! Ihate you... .- "Nima haka". Ta
bashi amsa. Cikin yanayi da alama na k0 in kula
tace, "1 hate you toa. , ' Dama abin da ya sa ka»
kirani ke 'nan? Daga ji na san. bu ka yi Salla ba,
don da Ruwan Alwala ya_ taBa, jikinka, hasken
Sallah ya taBa zuciyarka na san -da zuciyarka ta
yi sanyi. Don haka Oga je ka yi sallah. Su
YallaBai fitina, Sabeer rigima". . Ta ‘fada‘ cikin
sigar‘ tsokana. da dariya‘. Ta kashe wayar. ‘ ~
ba tare DA ya bata amsa ba. zuciya da
Wani ihun bakinciki yasa da Bacin rai. Ya yi wurgi
da Wayar. .
"Wannan Aljanar yarinyar sai ta. kasheni wata
rana, ba ta jin komai »a~rayuwa, komai baya
taBata. Anya ma Mutum -ce kuwa?" .
Nan ya bude Fridge ta dauki Ruwan Sanyi ya sha,
ya kuma watsa a kansa ko zai‘ samu sanyi a
zuciyarsa, kansa ya yi masa sanyi.
Wurgi' ya yi da Robar sannan ya shiga Wanka. —,
, Ya jima kwance cikin bab sannan ya fito. Ganin
ya kasa, samun kwanciyar hankali .da sanyin
zuciya yasa' ya ‘yi Alwalar‘ ya fito ya yi Sallah
ya kwanta akan .Sallayar idonsa a rufe, tunaninta
kawai yake Wanda ba abin da ya tsana banda
ganin mummunar fuskarta a nashi fadin
Amma ta shiga zuciyarsa ta zauna sabo' da
yadda ya satunaninta a gaba‘ da yadda zai yi ya
qular da ita ya ga taji haushi
Wannan yasa awa ashirin da hudu tana maqale a
kwakwalwarsa da zuciyarsa. Deeda ta
tayi Waya tana bawa Ibrahim ‘labarin tsiyarda
suka kwasa da Sabe’er tana-yi yana Mota, Dariya
ya dinga‘yi' ya‘ ce,."Na fada miki :Sabeee ba‘
sauki zaku kwashe da' shi ba,kuma ta da Sabcer
daga Bacci shi 'yaf1 komai Wuya'
- Ta ce, 'Wallahi Ibrahim Sabecr nada matsala‘. .
.. t
r'Sam‘baya .son Sallah,:yana wasa da Sallah, sai
lOkacin 'da ya 'ga damayake Sallah, ga shaye—
shaye.. Wallahi . rayuwarsa na cikin hadari". , ' .
"'hakane .Deéda, wallahi nima abin .na damuna. .
Sai dai na yarda da ke Dccda, na San. za‘ ki sa
Sabeer a hanya".
"Ibrahim ba abu mai sauki bane. 'Kana ganin ni
‘da Sabccr kamar Wuta da AudUga~ muke? .Ya
tsane ni; ni'kuma na tSani halayensa.
"Za ki 'gyara halayyar da ki ka tsana Deeda". ' ' '
Ajiye Wayar ta yi, don shi Ibrahim bai san
wahalar da _take sha a hannun Sabecr‘ ba ne.
A ranar da yamma Momi ta, taho da Inna _ mai
Fura. Murna a gun Dccda kamar Sallah. A jikin
inna ta yini a Wannan. rahar tana murna. Bangare
guda Hajiya ta ware musu a Bangarenta daki da
falo da kuma Bayi. Akwai komai a wurin da Zasu
bukata; , Tuni Inna.‘ mai Fura ta maye .gurbin
"Decda wurin' aikin Momi na‘ gyaran Bangarenta'
da kula da Side dinta. Kuma'Momi na jin dadin
hakan,tana jin ‘ :dadin zama. da‘ Inna, don
tsabtarta‘ 'duk da tsohuwa ce amma da sauran
karfinta kuma ba ta da qazanta, kuma ba ta ma
Hajiya shos‘shigi, hakan ya burge Hajiya. 1 ‘
Sannan Deeda ta cigaba da kula mata da lissafin
kudin Business dinta da kuma side din Sabeer‘
Wanda kullum cikin fada suke ba Wani jituwa. a
tsakaninsu
Sabccr ba karamin wahalar da Deeda ya ke ba,
haka kawai tana tafiya saiya sama ta
kafa ta fadi k0 ya jawo .hijabinta da karfi ya sake
sai ta fadi, k0 kuma tana tafiya haka kawai ya
watsa ma ta 'ruwan. sanyi, ya yin ,da ita kuma
ba ta nuna mishi ta ji haushi
hakan ya ke Kara qular da‘ Shi.
Wani lokaCin ta Ce mishi yaro ne shi bai da wayo
shi ya sa'yake'halin Yara k0 ta ce masa ' bai iya
komai ba sai kashe kudi da. fada, .itabA'
cikakken namiji bane da zai'tsaya yana Wahalar
da Mace, jarumin Namiji sai dai ya fuskanci
Namiji dan uwan‘sa, ,
' Abin da yadi, ba shi haushi shine, kullum tana
kwatanta real man da Ibrahim. ' Wani lokacin tare
da Inna mai Fura suke zuwa Bangarensa kuma
.da sassafe; duk Baccin da yake sai ya ta'shi k0
kuma, tasa Wa‘azi da ke magana kan’hukuncin
wanda baya‘ sallah

6 Comments On BIRNIN GAYU
avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

??

avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

Perfect

avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

Good

avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

A

avatar
sadiya-umar

1 year ago

Reply

Good and interested

avatar
sadiya-umar

1 year ago

Reply

Good and interested

Please Login or Register in order to submit comment