Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi ido biyu da juna. Ya mike tsaye
cikin mamaki kuma a fusace, itama ta mike, ta
lura da haushinta da ya ji amma ita ba ta ' ma
gane shi ba. .
"Na lura yarinyar. nan ba ki da kunya, ba ki da
mutunci! Uban wa ya kawo ki Asibitin nan?"
Ta kalleshi sama da kasa ta buga mai Tsaki tare
da Harara ta ce, "Sa'a ka yi ban iya
Zagi ba da na ma ka wadanda ya fi naka ciwo.
Kuma karka'yarda ka sake zan min Uba".
Sai an Zaga me ki ka isa ki yi? Dama nemanki na
ke, yau sai na miki rashin mutuncin da ba za ki
manta da shi ba".
"Banyi tsammani ba".
‘ Ta ba shi amsa kai tsaye.
"’Me kike nufi?"
Ta kada mai Idanunta wanda sai da ya sa yaji
gabansa ya fadi. '
Wannan ne lokaci na farko da bama Mace ba,
lokaci na farko da aka taBa kallonsa ido cikin ido
ba tare da shakka k0 tsoro ba.
nace, "Ban tsammanin zaka iya ba. Ina nufin
yanayinka da alamunka bana zaton ka Iya rashin
mutunci , sabo da a yadda na ga alamarka girman
jiki ne kawai kayi, amma har yanzu tunaninka da
ayyukanka har kwakwalwarka ta yara ce ba su
girma ba.
Yaro k0 ban tsammanin ya san meye rashin
mutunci balle ya iya, sunansa kawai ka sani, don
haka ka bari in Kwakwalwarka da tunaninka
sun gama girma sai Ka zo mu kara rashin
mutunci, in ka gwada min na 'YAN BIRNI ni .kuma
sai in gwada ma ka na 'YAN KAUYE":
Tuni Sabeer ya kara harzuka, idonsa ya kada ya
yi ja ya kasa furta ma ta komai, kuma ya kasa
ma ta komai, sai azabar zuciya kamar za ta
kashe shi. .
Tun-tuni Ibrahim ya ji hayaniyarsu ya fifo ya
tsaya a kofar ya -harde hannu yana kallonsu
yana murmushi. . -’
Cikin qunar zuciya Sabeer ya Ce ma ta, "Fita
Asibitin nan tun da ba na Ubanki ba ne, ba zakiga
Likitan ba, kuma yau sai na nuna miki halin yarint
Ya- zaro- Belt dinsa da karfin tsiya ya kai ma ta
duka, ta yi saurin sa hannu kuwa ta tisge.
Mamakinta ya‘sa shi bude Baki.
_ "Bi a hankali Yaro kar (Body bulding) din da
kayi ya yaudareka; kar ka ganni Mace ka raina
min Wayo daga Kauye na ke, na ci Tuwon Dusa
na ci na Dawa, kar ka nemi raina ni.
Kuma da na san Asibitin nan na Mahaifinka ne da
ban soma takoshi ba."
Ta ja mai dogon Tsaki ta juya za ta fita, wani
kololon Bakinciki ya. tokare masa zuciya, ya rasa
me zai ma ta.
Ba ta ankara ba ko ta taka Sunul ta fadi qasa ta
daku. . -
"Wash Allah". Ta fada
"Wayyo! Bayana".
Sabeer ya Kyalkyale da. dariyar mugunta
yace,"Su Budurwar Kauye masu karfi an sha
Kasa".
Ya matsa dab da ita yasa kafa ya' takéta .sai da
tayi Kara yace"Duk karfin Budurwar Kauye ba ta
isa ta kai Namiji ba, musamman na Birni, BIRNIN
ma na GAYU Ya Kara taketa da Karfinshi ya ce,
"Dama neman‘ki na ke tun rashin mutuncin da ki
ka min ban manta ba, kin hanani sukuni kin
hanani
Bacci' kin hanani cin Abinci, kin sani yawan
tunanin wannan mummunar fuskar taki, har ta
zauna a kwakwalwata.
Yau wannan hannun da ya watsa min Nono sai
na Balleshi".
Nan ya kai daya Kafar ya danne Yatsun da qarfi"

Ta sa ihun Azaba, sai da hannun yayi jini sabo da
irin takalman da yasa ba na wasa ba ne.
"Wayyo Inna zai kasheni
Ibrahim ne ya matso wurin da sauri ya janyesa.
"Kai- Sabeer ba ka da hankali za ka kashe- 'yar
mutane?"
"Kyaleni in ma ta illa, gobe idan ta. ganni za ta
canja hanya. Kuma wannan kadan ma ta gani." ‘
Ibrahim ne ya taimaka ma ta ta tashi gami da
dressing din hannun cikin . gaggawa ya samu
jinin ya tsaya, amma bai yi nasarar tsayar da
jinin ba.
Hankalinsa ya tashi, gaba daya ya rude, bai taBa
tsammanin abin nasu zai yi tsanani haka ba da
bai bari hakan ya faru ba. '
Nan ya sa hannun cikin qankara ya sa ma ta
Magani sannan ya daure da Bandeji ya nufi ciki
don dauko Allura ya mata.
Bayan fitarsa Sabeer ya harareta ya ce, "Kalli
'yanda ki ka zama abin tausayi...azaba kadai ta
canjaki."
"Allah Ya isa Ta fada cikin zafin zuciya.
- "Kuma kai ne abin tausayi ba ni ba, don ni kam
ban iya bin 'yan fage in yiwa mutum illa ba sai
‘dai in fuskance "shi. Ka ji kunya da ka nuna
qarlinka akan Mace".
Ta ja Tsaki gami da matsawa dab da shi, bai
ankara ba ta ja farar Rigarsa ta goge Jinin da ke
zuba a hannunta gaba daya ta bata masa Rigar. '

Ya daga hannu zai Mareta, tuni ‘ta manta ciwon
da ke hannunta ta cafke Hannun ta gantsara
masa Cizo ta fita da gudu. " i
. Inna dai ba ta ankara ba sai ganin Deeda tayi ta
fito da gudu a rude ta bita. "Ke Deeda!!!”. ' Can
kuma sai ga Sabeer ya biyota da gudunsa. ‘ ‘
Inna fa hankalinta ya tashi, ta bisu tana,"Deeda!
Deeda!! Deeda! ! !" Daga qarshe dai ta gaji ta
hakura don ba‘ za ta iya gudunsu ba. ‘ - Sai da
suka yi nisa sosai har suka fita Asibitin sannan
Sabeer ya yi nasarar kamata ‘ Ba ta saurara
masa ba' ta yi na ‘maza turesa da qarfinta. ' Sai
da ya fada cikin wani ruwan dake a bakin hanya.
. Tana' ganin ya' kai qasa kuwa ta arta ana Kare,
ba ta tsaya k0 ina'ba sai da ta kai Gida, ta nufi
daki ta rufe tana haki gami da tuno abin da ya
faru kamar a wani Mafarki k0 Almara. . lnna dai
hankalinta a tashe ta nemi abin hawa ta kOma
bayan ta gama neman Deeda ba ta
ganta ba, ta tafi tana addu'ar Allah Yasa ta koma
Gida.
Sabeer ya mike cikin takaici da bakin ciki da
Bacin rai, duk’ Kunya ta kamashi da ya ga Yara
da wasu Mutane suna kallonsa.
Wasu 'yan Mata kuwa har dariya suke suna mai
da‘ yadda abin ya faru, da alama a idonsu aka yi.
Da kyar ya iya daga kafa ya miqe ya wuce kai
sunkuye takaici da kunya sun lulluBesa, ya rasa
ma ina za shi.
Shi 'dai bai gane hanyoyin ba, don haka dolensa
ya koma cikin Asibitin, ga‘ shi 'ba Waya a
hannunsa, haka' dolensa ya sunkuyar da kai yana
Boye fuska ya koma cikin Asibitin yana kaucewa
jama'a yana kulla tsiyar da zai ma ta Ibrahim
yana ganinsa ya fashe da dariya
ya ja shi wani Office da ba kowa ya ce, "Sabeer
kai ne haka k0 Ido na ne?"
Cikin zafin rai ya ce, "Wannan Aljanar Yarinyar in
na kamata k0 sai na harbe yar banza! Ni zata
yiwa haka?"
"Ya isa haka Sabeer. Yanzu dai abin da ya faru
ya faru ba yadda ka iya, ka koma Gida ka canja
Kaya ka barni in yi aiki Please tun da na san yau
ma kai kam ka tashi'ba za kuma kayi aikin ba"
Ya Bata fuska.
"Uncle IB ka san ni ban gama sanin hanyoyin
garinnanba, Please ka 20 ka mai da ni
Ibrahim ya cira kai ya kallesa ya ce, "'Ka yi
hakuri Sabeer ba zan iya barin aikina in yi naka
ba, yanzu mafa marasa lafiya na dakatar ina
sauraronka.
Please har yaushe komai sai an maka kai ba Yaro
karami bane, in ba zaka iya komawa ba zan ma
(Diver) din Office magana ya mayar da kai Gida,
amma ni dai ba zan bar aikina ba".
Sabeer ya yi fishi ya fisge Key din Motar ya fita,
Ibrahim ya bisa da kallo sannan yaci
gaba da Aikinsa da niyyar in ya gama’zai je inda
suka hadu da yarinyar nan ya nemi Gidan su.
%%%%%%%%%%
Sabeer kuwa, sai da ya gama zagaye_ kafin ya
kai ga gane hanyar Gida, ga shi ba dama ya kira
Abokansa za su masa dariya.
Haka ya yi ta shan wahala kafin ya isa Gida ya
koma ya samu Momi ta dawo, wato Hajiya
Amina, sai dai bai bi ta inda ta ke ba ya wuce ya
cire kaya ya shiga Wanka. .
Ya jima kwance cikin Ruwa a (Bat Tap) yana
tunanin irin abin da zai ma yarinyar nan da inda
zai sake ganinta, sai dai hakan ya gagara,
tunaninsa bai samu maganin matsalarsa ba.
Nan tunani ya fado masa, kawai ya kira
Abokansa don su tayashi nemanta da kuma ba
shi shawarar irin rashin mutuncin da zasu ma ta.
Bayan ya fito ya ji kiran (Door Bell) na
Bangarensa, bai kula ba sai da ya sa Kaya ganin
an matsa ya fita ya bude.
Momi ce tsaye tace, "Lafiya Saber tun dazu ina
tsaye, ina ka shiga?" ’ ' Ya dan sunkuyar da kai
yace, "Momi ina Wanka ne Shigo mana,'dama ina
shirin inna fita zanje in gaishe ki. Kin dawo laflya
k0?" : "Lafiya kalau". Ta amsa masa lokacin da
ta ke zama ta ce, "Yayunka duk suna gaisheka.‘ .
- ' ' Daddynku ya fada min komai' game da_
dawowarka, sai ka dage ka koyi 'Aiki, in da hali
ma harka Karo ilimi a fannin da kafiso, duk da
Asibitin muna da Likitoci, amma akwai bukatar ka
a Asibitin. _. Ina so ka daukeni kamar
Mahaifiyarka, duk abin da ya shige ma duhu ka
20 ka sameni Bangarena na Shawara k0 wani
abu. _ Sannan ina fatan ba ka da matsala da
Ma'aikata masu kula da Bangarenka da Abincinka
suna gyara ma ka Side dinka ya kamata, yadda
kuma ka ke so?, duk abincin'da ke bukata order
kawai za ka yi..."
"Na sani Momi ba sai kin bata bakinkiba Ya
katseta. "Nan Gidanmu ne Gidan Ubana ba sai an
bani ko ance in tambaya ba. . Sannan Sister ita
ce Mamana ita ce komai na, kar ki yi qokarin
zama Mamana ki zauna a matsayin .Matar
Babana ina ga hakan zaifi mana ni dake Sannan
Uncle IB yana tare da ni, duk - bukatata shi kadai
ya isa ba sai kin sa Baki ba‘ In koyi aiki k0 kar
in. koya, wannan ba matsalarki bane Batayi
mamakin halinsa ba, ta yi wani murmushi irin ta
manyan Mata da idonsu ya bude tace To shi ke
nan tunda haka ka ke so, muje a haka-tun da kafi
son in, rikeka a matsayin dan ‘Mijina‘ Fine, ni
kam na kware wajen iya,rike ‘dangantaka tunda
rikon dan kishiya kakeson nai maka ina
maraba'da hakan. inaso ka ,sani bani da matsaia
da kai, bazan cutar da kai,ba amma fa kar ka
shiga gonata kayi kokarin tsayawa a matsayinka".
"Kema ina son ki tsaya a iyakarki".
"Da kyau".
Ta fada tare da girgiza kai ta fita. Ya bita da
wani matsiyacin kallo gami da rufe gofar Falon ya
koma ciki. ,
Wani radadi yaji ya ziyarci" hannunsa, nan ya mai
da kallonsa kan hannun, ya yi jawur har ya soma
kumbura. '
Ya ja dogon Tsaki, haushin Deeda da tsanarta ya
Kara shigarsa, don gurin da ta gantsara masa
Cizo ne.
"Amma wannan akwai 'yar rainin wayo...ni 2a ta
fadawa bafar magana? Me take nufi da na girma
amma hAlayena ba su girma ba?
Tana nufin ni yaro ne
Nan ya mike yana kallon kansa a Madubi tun
daga sama har Kasa, duk ta yamutsashi
kwana biyu kawai.
banzar yarinya yar KAU YE mummunar yarinya za
ta sani a gaba... zan mata rashin mutunci To
amma me zan ma ta?”
Waya ya dauko ya bugawa Abokansa yana musu
neman gaggawa.
Cikin minti talatin suka hallara.
"Lafiya Sabeer irin wannan neman gaggawa?"
"Ba lafiya ba
Ya fada a qule.
"Wata Aljanar Yarinya ce ta sani a gaba, ta daga
min hankali",
Salim ya kalli Nura sannan ya kalli Nura sannan
ya kalli Sabeer din ya ce, "Ba dai mutuniyarka da
ta watsa ma No... ."
Wani mugun kallo da ya masa ya sa shi gum da
Bakinsa bai Karasa ba.
Ya ce, "Na ganota".
Sabeer din ya ce,"Shawara na ke so ku bani.
wane rashin mutunci zan ma ta?"
Nura ya ce, "Me zai hana ka yiwa banza lahani,
wato ka banke banza da Mata sai 'ta Karye ta
dawo me Kafa daya?" ,
Saber ya girgiza kai.
"Not Bad Kai kuma ,fa Salim, me ka ke gani?"
Salim yace, "Hakan da ya fada dai-dai "ne" k0 ka
kadeta ko ka yi hayan wasu su saceta ta, Bace
Bat na kwana biyu a rufeta inda k0 Hannunta ba
za ta gani ba don Duhu, ta Yini kwana da
Yunwa.." ' .
Sabeer ya ce, "1 Hope shawaranku ya yi aiki,
Nura ya ce, "In dai har muka yi yadda na ce dole
ya taBata. In ta zama Gurguwa ai ta .nakasa".
Sabeer yace "Ba wannan ba, samun inda take ma
bala'i ne". "Zamu nemota a same aren da muka
hadu da ita
zamu nemota, zan mata ,abin da ba za,,,,'yan
Samari". Muryar Ibrahim ne
suka mai da hankalinsu garcshi. 'yana wannan
murmushin nasa ya ce '-'.da;abin da zaku yi a
rayuwa kuke ku ke planing tsarawa da yafi
muku".
ya yi dariya gami da fadawa jikin unless ib yace
kaida Sister ’kune rayuwata (My whole world) ya
yi, murmushi ya ce kadai fadi, amma ba Uncle IB
bane zai zauna ma. da Mata 'yar KAUYE ba. Ka
tuna
ya fada tare da murmushi ya Bata fuska.
Ya ce, "Uncle IB karka Bata min rai, kasan na
tsani 'yar Kauyen nan da aure amma nafi tsanar
yarinyar nan (I hate her the most)". .
Ibrahim ya ce, "Ni zan fita dama na leko dubaka
ne zan fita ni ina da abinyi bani ’da' lokacin
tsanar wasu k0 daukan fansa, in kuma ba'ka bar
maganar ba sai na fadawa Sister". '
Ya langaBe kai. "
’Yace Uncle IB kar ka min haka mana".
"Na dai fada ma ka ka zaba daukar fansa
.ko Bacin ran Sisiter".
Nan ya fice ya barshi. Ya maida kallonsa kanSu
Salim ya ce,‘ "Guy plan cancel"
Nura ya ce, "Wai kana nufin kana tsoron Uncle IB
da Yayarka?"
Sabeer ya ce, "Sabeer bai tsoron kowa, bai kuma
shakkar kowa just that ina son Sister da Uncle IB
(and 1' respect them a lot) ban san Batawa Sister
rai, kuma sabo da wannan Aljanar ba zan 'Batawa
Sister rai ba, sai dai duk randa na hadu da ita sai
na ma ta illa fiye da wanda ta min".
Yana magana yana kallon inda ta dankara masa
Cizo.
£££££££££££££
da tambaya da bincike a Unguwar, Ibrahim ya
gano Gidan Tabawa inda‘
Deeda ke zaune. Tana daki k0 tana shirya kaya
ranta a Bace
sabo da washe gari za ta tafi Gidan Aikinta.
Yaro ya shigo. "Wai .ana sallama da budurwar da
ke
Gidan nan".
' Inna mai F ura ta kallo Yaron.
",Waye ne
"Wani me Mota ne". Yaronn ya bata amsa a
takaice.
"Jirani". ' ‘
Nan ta shiga ciki ta dauki Hijabi 'tabi bayan
Yaron.
"Mu je
Yana zaune cikin Motarsa a Kofar Gidan ya
hango Yaro da Inna. Mamaki ya kamashi. Ya yi
saurin fitowa daga Motar lokacin da suke isowa.
Innan ta kalleshi kallon tambaya. Kallon da take
masa ya sa ya sha jinin Jikinsa. Tabbas ko k0 ba
a fada masa ba ya san ko Uwarta ko Kakarta ce.
Ya kalli Inna da kyau, ya ga irin shigar: da tayi ' ’
A ransa ya ce "Lallai wannan yarinya ta san inda
ta yi gado..." . Inna ta katse mai tunani ta ce,
"Gani; naji an ce kana sallama da Budurwar
Gidan". . Ibrahim ya kalleta da kyau ya rasa ma
me zaice mata. ‘ Tsayuwar da ta yi ta riqe
kugunta yasa yaso tuntsurewa da dariya amma
sai dake yace "Budurwa' na'ce ba tsohuwa ba
Ta kallesa da kyau ta ‘ce, "A Gidan nice budurwa
k0 kana musu ne? Me ya kawoka, me ka ke?
nema?" '
ta tsareshi da ido. Gaba daya ma ya rude ya rasa
me zai ce ma ta.
yanata.soshe-soshe da kame-kame, can dai ta
tausaya masa tace, "jikata ka ke nema me za kai
mata ya sauke numfashi ya ce, "‘Dama ta je
Asibiti ganin Likita ne to sai suka samu saBani
da kanina ta taf1 ba ta ga Likitanba na 20 in ba
ta ha'Kuri kuma in ji meye matsalar don ni Likita
ne". ‘
ta zaro Ido ta washe Baki. "Aiban sani ba.
‘ wannan ciki za ka shigo. Dama haka Likitocin-
suke na birni har Gida suke biyi marar lafiya?
Ikon Allah, ai Deedan tana Ciki shigo
‘ har ciki. A tsakar gida ta shimfida masa
Tabarma sannan ta shiga Ciki‘ ta kamo hannun
Deeda.
ke fito ga Likita har Gida ya 20 duba ki". ‘
Deeda ta kalleta cikin mamaki.
"Likita?"
"EH". Ta amsa ma ta a takaice.
"Ashe da rabon za ki ga Likita kafin ki tafi Zo mu
je". ' ' Ta ja'ta har Tsakar Gida wurinsa.
"Likita ga Jikar tawa”.
Deeda ta kallesa cikin mamaki.
"Likita har Gida?"
Ta ja Kujeran- zama na tsakar Gida ta zauna, ya
yin da Innar ta zauna a gefensa.
Deeda ta gaisheshi Sannan ta tambaya.
"Anya ni kuwa ka zo nema? K0 ka Bata ne?"
"A'a ke na 20 nema. Sunana Dr. Ibrahim, ni ne
Likitan da ki ka zo gani da safe ku ka samu
saBani da Kanina".
' Ta girgiza kai.
"0h!" Gami da dan yamutsa fuska.
"Wannan qanin na ka?"
Ya yi murmushi gami da cewa, "Ina ji dai kuna da
(Allergy) da juna, duk lokacin da aka ambaceki
sai launin fuskarsa ta canja, ‘kema haka tun
randa ku ka' hadu jininku bai zo daya
Na 20 in ga hannunki ne in ba ki haquri sannan in
ji me ye matsalarki
Kallonshi ta ke tana murmushi. A ranta ta ce,
"Akwai bambanci tsakaninsa da qaninsa.
Shi mutum .ne mai sanyin hali da kirki. Haduwar
farko na gane hakan.
Shi ko wancan haduwar farko na gane halinsa
'mara kyau.
'Jin tayi shiru ba ta amsa ba Inna ta yi carab Ta
amsa.
"Likita hannunta dai da sauqi, mu Mutan Kauye
ne muna da. dabara da namu Magun'gunan irin
wannan CiWon. -
Zan dai' yi ma ka bayanin babbar matsalar duk
da yanzu taji sauki ciwon da kansa ya baje".
Nan ta soma zayyana masa ciwon Deeda tun
tana karama har zuwa girmanta da shigowar su
Birni ya soma bajewa da kansa a hankali.
Ya dan yi shiru na tsawon lokaci 'yana kallon
Hannayenta.
Ya so ya fuskanci matsalar sai dai duk da hakan
sai ya yi bincike.
Ya ce, "Na fahimta Kaka, sai dai duk da hakan
tana buqatar zuwa Asibiti sabo da a can ne zamu
yi duk wasu gwaje—gwaje don gane ainahin
ciwon, duk da dai yanzu ya washe ba matsala,
amma 'gaba zai iya dawowa, duk da ban
tabbatar da wane ciwo bane, amma dai ba abun
damuwa bane, in ma ta sha Magani to da yardar
Allah za ta rabu da shi.
Don haka gobe in Allah Ya kaimu ta sameni a
Asibiti karfe goma."
murna ta lulluBeta. ,
:Na gode Likita."
Mun gode, duk da goben zata tafi amma" zata
ganka. kafin ta tafi".
Ya mike yana fadin allah ya kaimu goben, Inna
tana ta godiya, deeds kuws kallonSa take tana
mamakin’ kirki iron nasa
“ya mike ya kalleta ya ce, 'miss Deeda inga
hannun naki?" .ta-‘ sunkuyar dakai ta mika masa
hannun ya kalla ba tare da ya taBata ba ya ce,
"Kina da jiki 'mai kyau don bai kumbura ba, in dai
yana miki radadi ki sha (Pain Reliver)
Paracetamol da
,to"Na gode"
Nan ya yi sallama da su ya wuce.
Deeda ta bishi da kallo ya yin da Inna ta rakashi
har iofa. Ta dawo ta samu Deeda zaune ta yi-
Tagumi. '
tace, "Deeda kina tunanin tafiya ne? Karki damu
Allah na tare da ke ina tare da ke
idan kin‘ ga ana saki abin da ba dai- daiba ko ba
kya so zan dauko ki mu dawo ". Ta“ dan yi
murmushi ta ce, "Inna haka ne, ina tunanin tafiya
sai dai na‘ fi tunanin barin karatuna duk da na
koyi abu da yawa na iya abubuwa da yawa
karatu da rubutu, turanci da ma abu da yawa.
Haka na samu ilimin Addini‘ sosai a Makarantar
wanda da ban san su ba..
- Alhamdu lillahi da zaman da na yi a {Gidan
Tabawa da gatan da ta min, sai dai ilimi ba ya
qarewa, yanzu na soma dandanarshi zan so in ci
~gaba'da samunsa.
Sai dai ilimi ana samunsa ta kowacce fuska,
duniyar ~gaba dayanta Makaranta ce, kamar
yadda na koyi wani abu yanzu na fahimta, akwai
mutanen kirki akwai na tsiya.
Inna duba bambanci tsakanin wannan Likitan da
qaninsa.
Mutum mai nutsuwa mai kirki mai mutunci.
Kaninsa kuwa..." ‘
Ta ja dogon numfashi. "Bana son ma tunashi
balle maganarsa.
Inna kar ki damu ina maraba da sabuwar rayuwar
da zan shiga, a wurina wani sabon Makaranta ne
na koyon wani sabon i‘limin
rayuwa. Idan Allah Ya kaimu gobe zan je Asibitin
zan roqi Tabawa mubiya tacan» sai mu wuce.
Insha Allahu akwai‘haske a tattare data tafiyar da
zan yi". ' .Inna ta yi 'murmushi. ‘ :"Na ji dadi
Deeda yadda ki ka kwantar da hankalinki ba ki
daga hankalinki akan tafiyar ba. Allah Ya taimaka
ya sa alheri. Muna gari daya, zan dinga zuwa
dubaki, za ki dinga zuwa kema in kin samu
dama". Haka suka kusan kwana- suna hira gami
da tsara yadda tafiyar za ta kasance. . Innan ta
ci gaba da yi ma ta nasiha da bata shawara akan
zaman rayuwa da kuma sababbin
mutanen da za ta tarar ta yi mu'amala da su.
ya kuke ganin zaman deeda DA saber zai kasance
a birnin gayu anyama zasu hadu kuwa?
h shared a profile .
birnin gayu
chapter6
Deeda kuwa ita ya fara gani, duk da kuwa akwai
wadanda suka rigata; sabo da ita ya fara cewa a
kira masa.
. Tare suka shiga da Inna. Ta yi sallama, ya dago
kai yana murmushi ya amSa ma ta sallamar.
Ya kalli Inna ya yi dariyar tsokana ya ce, "Su
Kaka 'yan mata, an iso?" .
Ta yi dariya ta ce "Ya ka ganni ras da ni, duk
Budurwar da mu “ka jera sai a 'daukeni an
barta". . Yace, "Kwarai kuwa..Ai Kaka-“kin yi
fice , 'Deeda dai kallonsu take tana dariya Kwarai
halayen Ibfahim yana burgeta, duk da‘ alamu sun
nuna dan masu hali ne ga ilimi ga wayewa amma
ba shi da girman kai sai saukin kai sannan, 'ga
dukkan alamu mutum ne mai halin kwarai. ‘ ‘ ' ' .
Bayan ya gama barkwancinsa da Inna ya mai da
hankalinsa kan Deeda ya ce, "Malama Deeda zan
fara da miki tambayoyi kafin in kai ga ‘ maganar
Ciwonki. ‘
Tambayoyin da zan miku kamar cikakken sunanki,
shekarunki da sauran‘ su, sabo da ina son bude
miki (Folder) don rubuta komai game da ciwonki,
ne nan gaba in kin zo sai a dauko koda
ba ni zan ganki ba wani Likitan ne in ya karanta
zai san komai game da rashin lafiyarki. Ina fatan
kin fahimta?"
Ta girgiza masa kai.
"Na .fahimta".
Cikin‘nutsuwa ya ke ma ta tambayar tana ba shi
amsa har suka gama, ya dinga ma ta tambaya
game da Tarihin ciwon na ta tana ba shi amsa,
amma wani lokacin Inna ta kan tsoma Baki har
suka gama suka je ya ma ta gwaje- gwajen da
ya dace sannan ya ba ta magani ya kalleta ya ce,
"Kar ki damu ba wani matsala ba ce na tashin
hankali, kamar yadda ki ka gani yanzu Fatarki ta
fara washewa in kin Sha maganin nan zai
taimaka miki sauran duk ilahirin jikinki ya
wartsake.
; Sannan' irin ciwonki ba a cika samunsa ta nan
ba, yana wuya a samu masu irin wannan
Ciwon, shi yasa ma ba za a fahimci mene ne ba
sabo da ba kowa ya san ko ya taba jin irin ciwon
ba sai Likitoci irin mu.
Jikinki da fatar jikinki baya son inda ki keda
yanayin wurin da ki ke zaune, misali;
Ruwan Garinku, yanayin Abincin wurin da irin
Iskar Garin da aka Haifeki ki ka girma, kina da
(Allegy) da wannan garin yankin wurin gaba daya,
don haka da ki ka bar garin ki ka shigo nan sai
aka yi dace jikinki ya karBi yanayin inda ki ka
dawo, don haka fatarki da jinin jikinki ya fara
washewa ya mike da kansa daga yamutsewar da
ya yi.
Ga mutum mai irin jikinki ba .kowanne irin Abinci
da ruwa zai karbe ki ba.
Kai hatta kaya zuwa mayukan da 2aki dinga
amfani da .,shi ba kowanne Jikinki zai karBa ba,
dan haka a duk lokacin da ki ka fara cin wani abu
ki ka fahimci canji a jikinki ki yi saurin kiyayewa,
haka kaya da sauran abin da ya Shafi‘ jikinki.
Daga.kin yi amfani da abu ki ka ga ya canji a
jikinki to ki yi saurin barin abun, in kin kiyaye
insha Allahu ba za a samu matsala ba.
Yanzu» ga Magani‘ da kuma sunayen irin Abincin
da ’za ki kiyaye cin su da kuma irin abin da ya
kamata ki dinga ci, duk ba wani abu mai ' wuya
bane da zai gagara". . Nan Deeda ta yi shiru tana
jinsa tana kuma tunanin Ciwonta
Wane irin ciwo ne da ba ta taBa ji k0 ganin me;
irinsa ba? Ikon Allah! Allah mai yarda ya so!!
"Allah Ya kare ya kuma ba ki laflya Deeda".
"Alhamdu lillah, Likita ina godiya, yau na samu
haske akan abin da ya shige mini duhu.
Na gode, Allah Ya saka ma ka da alkhairinSa". ' .
Deeda ta fada‘tana' kallonsa. Ya ma ta murmushi
yace,’ "Karki damu Allah Ya Yi
mana jagora ya bamu LAFIYA, sai ki kiyaye kuma
ki dinga shan magani".
"Zan kiyaye insha Allah. Na gode".
Inna mai Fura tace, "’Likita Kudi fa? Kamar nawa
za mu biya?"
Ya yi dan'daria ya ce, Kaka 'yan Mata nan
Asibitin ai, na kyauta ne, k0: farkon zuwanku ba a
fadi muku ba
"An fada mana Likita, sai dai in magani ma
kyauta ne da kudin Katin
Ya yi' murmushi yace, "Duk kyauta ne sai dai in
bamu da maganin mu rubuta a siya a waje". ,
"Ikon Allah! To yanzu Likita da kudinka ka ke
siyan maganin?
’ Inna ta fada, kuma ta sa masa ido alamar amsa
ta ke jira.
Ya yi dariya sosai ya yin da Deeda duk kunya ta
kamata saboda tambayar Inna.
Ibrahim ya ce, "Kaka 'yan mata ai nima biyana
ake, ina na ke da kudin daukan nauyin Asibitin
nan? . '
Ai Likitocin 'muna da yawa, ‘kowa da fanninsa.
Ni dai ina fannin Fata ne, wato masu matsala irin
na su Deeda da makamantansu.
Me Asibitin shi ke biyanmu da kuma sauran masu
kudi masu neman Lada, sukan ba ‘da
gudunmawar .Magunguna da sauran abin da
:Asibiti ke bukata k0 kudaden biyan Ma'aikata da
sauransu don neman Lada da taimakawa
Talakawa marasa hali."
"Ikon Allah!” In ji Inna.
. "Irinimu ke nan? Kai! Allah Ya saka musu da
alkhairi, Allah Ya yi musu albarka, Allah Ya sa
sauran masu Kudinmu su yi koyi da hakan
‘Amin". Ibrahim ya fada yana dariya. Suka mike,
Inna ta ce, "Mun gode Likita, Allah Ya yi ma ka
albarka".
Ibrahim ya amsa da, "Amin' Ya kara da cewa, "In
dai

6 Comments On BIRNIN GAYU
avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

??

avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

Perfect

avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

Good

avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

A

avatar
sadiya-umar

1 year ago

Reply

Good and interested

avatar
sadiya-umar

1 year ago

Reply

Good and interested

Please Login or Register in order to submit comment