Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Dad)". Wato
ina ina kwana?"
. Yavfada da murmushinsa ya amsa da‘,
"(Morning Son). Na ji dadin ganinka kWarai;
alamar ’ dai baka son in auto maka 'yar Kauyen
mu"..
Sabeer ya Kara bata fuska ya dauki. Coffée din da
aka riga aka hada masa yana kokarin kaiwa Baki
ya ce "Ni dai an takura min‘kawai, lokacin dana
ke Medicine mun yi da kai
da sharadin ba. zaka sani yin aiki dole ba, kace
min ilimi kawai ka keso nayi, kana'so in cika
maka burinka in zama Likita,’ duk da bana so
sabo da kai na daure na jure wahalarsa na yi ta
karatu ba ji ba gani na takura kaina, amma shi ne
yanzu ka Bullo mintanan. . Gaskiya Daddy ba ka
min adalci ba, ni gaskiya bana son wani wahalar
aiki". Kalamansa sun ‘Batawa Mahaifinsa ,rai sun
‘ kuma kufulashi. Ya matsa kusada shi ya ce,
"Inbakayi aiki ba. me zakayi?"Ya fada cikin'
basala. ' . .koso "Kake ka kare rayuwarka a haka
ba zakayi . komai,ba‘ baka da exPRIENCE) baka
da wata dabara‘, . inna mutu wa2ai kula Ma da
dukiyar? . Ka san yadda zuciyata kemin inna .
ganka haka baka komai sai Sakarci? ‘ ' Lokaci ya
yi da za ka nitsu kasan Ciwon kanka Sabir ya
kufula shima ya hau dokin zuciya ya ce, "Me yasa
zan yi aikin wahala in nemi > kudi tunda
Mahaifina nada kudi, 'yan uwana na da
Sabo da me zan nemi kudin yanzu ba lokaci bane
da zan nemi kudi, lokaci ne da zan more .
rayuwata, inji dadi Haka kawai rana tsaka kace
zaka shiga tsakanina da jin dadina ka zama ,
kana so ka doramin nauyin da, ba naWa ba, in ka
takura min da maganar aure da a'iki Daddy
bazamu‘ _ _,shiryaba,mezakayi? 1‘ 'Mezakayi me
zaka iya yi- inji Daddyn ya..." Ya fada ' cikin
zafin rai. . . "Bari in fada ma ka, kudin da kake
gani ka’ke gadara da su nawa ne ni na nemesu
da gumina da
wahalata ba zan bari ka Barnatar dasu a banza
ba, idan zaka nutsu ka san me kakeyi, ka nutsi,
inba hakaba kuwa za ka sha mamaki." ‘
Wane mamaki zan sha? Nima bana bukatar
kudinka, nima ina da nawa kudin, kudin da
Mahaifiyata ta mutu ta bar min,
"Sabir
ibrahim. ya kirashi cikin tsawa. Ya yin da ‘
Mahaifinsa ya wanke shi da mari.
Tsananin Bacin rai bakinciki ‘ya hanasa magana.
Ya yin da Sabir din ya juya rike da fuska zai tafi
Ibrahim! ya tsai da shi. Sabir ya jawo hannunsa
zuwa gaban Mahaifin nasa ya ce"Ma za ka bashi
haKuri,‘ kar ka kuskura ka. sake yiwa Mahaifinka
irin wannan magana in kana so ka gama da
duniyar nan lafiya.’
Ba Mahaifinka. kadai .ba, ka koyi girmama
manyanka ‘na gaba ‘ da kai, kuruciya da iskar
samartaka' ba. hauka bane, kowa ma ya yi
Wannan lokacin ya wuce, meye laifin Mahaifinka
don yana nuna maka Kauna,’ ya damu
da'rayuwarka, yana so kasan ciwon kanka da
zafin kanka shi ne zaka dinga yi masa magana
cikin wannan harshen?
Ka yi hankali da duniya, maza. ka bawa
Mahaifinka hakuri".
Kansa sunkuye idonsa ya yi ja zuciyarsa kamar
za ta kashe shi ya bawa Mahaifinsa haquri (Sorry
‘ Daddy Ya kama kunne. Ba zan sake ba, ka yi
hakuri
Daddy ka yafe min» ' Tausayinsa da Kaunarsa ne
suka shige shi lokaci guda. , '
Ya dafa kafadarsa yace "Na yafe maka Sabir.
Ina‘ so ka sani Babanka na sonka sosai (Just)‘
how that i love you) girgiza masa kai ya yi ya
fita ya bar falon, Babansa ya bishi da kallo cikin
tsananin son dansa da kuma tausaya masa...in
akwai abin da ya tsana bai wuce Bacin ran dansa
ba. Bayan fitarsa ya mai da kallonsa kan
Ibrahim? cikin damuwa ya ce, "Ibrahim na yi
kuskure, na yi. “ babban kUSkure-~iyayena sun
min 'gata amma' ba kamar yadda na yiwa dana
ba, son dana yasa nayi . ~ babban kuskure na
Bata masa rayuwa, ban san ta yaya zan soma‘
gyara wannan kuskurenvda na yi ba, soyayyata
gareshi ya: Bata tarbiyyarsa. ’
_ Ibrahim ya kallesa cikin tausayawa ya ce
Kwarai Daddy kayi .kuskure sosai wurin tarbiyyar
‘ ~ Sabir,‘ yanzu gyarashi ta hanyar tsawa ko
fada ba zai yi gareshi ba, don ba zai taBa fahimta
ba
Yace yayi nisa canja tunaninsa zai yi wuya sai
anbi Wasu hanyoyi cikin dabara da. kuma masa
adddu'a harmu cimmasa
Karka damu Daddy inshal AllahuSabir Zai
fahimta‘ a hankali ya isa garesa ya ,zaunar da
shi Daddy ka kwantar da hankalinka, kar
ciwon hawan jininka Wanda bayason yawan
tunani ya tashi na san ma dai baka sha magani
ba,
nan ya'dauko maganinsa tare'da‘ruwan ya mika
masa
_ ya sha sannan ya rakashi daki ya kwantar'da
shi yace daddy ka kwantar da ’ka huta kadan
kafin ka fita office
, . Sabir ne zaune a karamin falonsa'cikin idonsa
jawur kamar zai zubar da hawaye. ' Ya dauko
Wayarsa don ya kira ‘wacce ke kwantar masa da
hankali. Sister ya kira sunanta'cikin.., muryar
kuka. Sister please ki dawo ki zoki daukeni ina:
missing dinki' sosai, Daddy baya sona, yanzu
quntata min yake son yi. Sister bana son zama a
Nigeria ki dawo please, Daddy da Uncle IB fada
suke min, basasona. Yi‘ shiru Sabir
takatseshi.“Kayi hakuri .ka ga duk hankalina
yatashi, wa ya fada maka Daddy baya sonka, .ka
san Daddy yafi sonka akan kowa, kuma Sister na
sonka, « yanzu- kaifa ba yaro bane, 'Sabir
dina‘yanzu babban .
mutum ne
ka manta~ ‘ .alkawarin da kai yiwa Sister
dinkane...ka manta kace ‘ min zaka nunaWa
Daddy cewa ka girma kaima za-ka ‘ iya daukar
nauyin Asibiti da kulada Business dinsa? .me
yasa tun daga yanzu ka soma nunamin
kasawarka? Sabir dine yanzu, zaka iya komai, ‘
ga Uncle IB yana tare da‘ kai, zai taimaka maka
Sabir ka san‘. Sister na sonka sosai, damuwarka
'zai daga min‘ hankali har in kasa mai‘da hankali
akan abin da- ya kawoni in yi a nan Sabir ka yi
kokari ka daure kayi abin da Daddy keso..kanajina
"Eh ina .ji Sister". Ya fada cikin sanyin murya. ‘ ‘
\ . . . zan yi kokarin danne zuciyata , nan gaba.
Ki; kula da kanki Sister (llové you) ta yi ‘ dariya‘
ta ce ka kula da kanka da Daddy da Uncle IB ‘
zan yi duk abin da kika ce Sister na san Sabir
dama ‘ yana jin maganata yanzu zan shiga Asibiti
kai ma ka tashi ku shiga Asibiti'“To Sister sai an
jima"Nan sukai,sallama ya dago .kai’ gami da -
jan:dogon numfashi.
"Kaje ka tabbatar .masa da kaima' kana
kaunarsa, kuma za ka yi duk abin da ya‘ ke so
Bata fUSka yayi” ' Uncle lb kaima ka san abu mai
wuya ne yin abin da Daddy yaks so".
"Na sani Sabir". Ibrahim ya katseshi. Amma duk
da hakan kaje ka fada mai don kWanciyar
hankalinsa". ‘ Ba‘don yaso ba ya mike yanufi
falon Dadin‘ ya ’sameshi kwance rufe a gadonsa
da hannunsa.
daya... Sabir ya durkusagabansa ya jawo
hannunsa yace am “sorry dadi. Ya fada murya
kasa-kasa."Daddy ka yafe min ba .zan sake ba,
Mahaifin‘ nasa ya yi murmushin'jin dadi, duk“ da
ya san ba har‘ zuci yake fada ba, ganin
kulawarsa garesa ya faranta ransa. Yace"Allah Ya
taimaka Sabir Yau zaka' fara xuwa Asibiti da
Ibrahim, ina fatan za ka ba da himma da kOkari
Wurin duba marasa lafiya Kar kasa wasa k0
sakaci da rayukan al'umma" Ya kau da kai
alamar bai son maganar ya ce"Daddy zan je dai
in fara koyon aiki ba in kai ga duba mara
lafiyar,,,,,
‘ "Sabir abin da ka‘karantane sannan da ka gama
ka yi (Service) wane koyon aiki ya yi ma ka
saura?” .
Ibrahim ne ya shiga tsakani ya ce "Daddy ka san
ya jima da yi, kuma ba (Practics) yake yi ba,
amma dai a hankali zai gane ai muna tare yanzu,
dolensa zai koya sabo da Daddy da kuma gujewa
auren 'YAR KAUYE!" Ya fada cikin" tsokana.
.Sabir ya qufula ya- fisge Key din Mota. a hannun
Ibrahim din ya fita tare da fadin, "Ina mota zan
jiraka‘in 'ka gama da Daddy din". ‘ .
Suka bishi da kallo har ya fice. Daddy ya mai
da kallonsa kan Ibrahim ya ce"Na rasa me ke
damun Sabir, wace irin rayuwa ’ya ke sowa
kansa, yana girma amma yana gudun
(Responsibilities) dinsa Ibrahim don Allah ina so
ka taimaki Sabir ya '‘san me yake yi, ya zama
(Seriousc). Ibrahim ina
.kishi da kyashinka, ina kyashin me yasa Sabir ba
kamarka bane?
Ina kishin me yasa dana ba irinka bane? Me yasa
jinina ba zai zama irin ka ba sai dan riko?
Ibrahim kullum kana cewa na da zuriata don haka
komai zaka iya mama muddin bai sabawa‘
Shari'ah ba, ka‘tuno kalamanka Ibrahim
Dr. Sulaiman ya fada yana kallonsa ido cikin ido.
Ibrahim ya girgiza kai tare‘ da fadin, "Eh Daddy
na tuno komai ban manta ba, banda kalamai
nama harda irin taimakonku da alkhairinku kun
kyautatama rayuwata, kun min duk abin da iyaye
za su yiwa dansu, don haka na yiwa kaina
alkawarin yi muku biyayya da yi muku duk wani
abu da da nagari dan halal zai yiwa iyayensa da
zuciya daya ba cuta ba cutarwa".
Dr. Sulaiman ya yi ajiyar zuciya ya ce, “Na ji
dadin haka. Ibrahim lokaci ya yi da mu ma zaka
mana (F avour) taimako kamar yadda muka yi
maka, a matsayina na uba na yi kuskure nayi
kokarin gyara' kuskurena ,amma hakan ya gagara
sabo da rashin’ fahimtar da ke tsakaninmu da
dana Sabir.
Ibrahim ina so ka mai da sabir kamarka, ina so
Sabir ya zama kaman. Ibrahim (Smart, lntelegent)
mutum mai kwazo, hikima da dabara wanda ya
san ciwon kansa,. za ka iya Ibrahim?"
"zan yi iya dukkan qokarina Daddy k0 ba ka '
fada ba Daddy dama wannan ita ce niyyata na
taimakawa, Sabir ya samu ingantacciyar rayuwa
kuma ya samu tsira har a gobe Kiyama, ba
duniya kadai nake so in taimakawa Sabir ya
samu ba, har da Lahira wanda ita ce Matabbata.
Kafin kai na yima wata wannan alkawari kuma na
yiwa kaina.
Sai dai dama tuni kaine ka shiga tsakanina da
’cika wannan alkawarin sabo da k0 ya ya ba ka
so a batawa Sabir k0 a cusguna masa, kai ka
kyale Sabir ya yi duk abin da ya ke so ya yi duk
abin da ya ga dama, wani bai isa ya hanashi k0
ya sa shi ba, don haka wannan magana da ka
fada min yanzu ya kawo
min sauki sosai, kuma na ji dadin hakan, Sai
ka’bimu‘
da addu'a'da fatan Allah Ya bamu ikon inganta
masa
rayuwa. . Sabir ina jin’sa tamkar‘ Kanina na jini,
ina
matuqar kaunarsa kamar yadda ka ke kaunarsa,
don
haka zan baka karfina da kokarina dari bisa dari ;
wurin inganta masa rayuwa da fatan za ka bani
hadin kai sosai." Dr. Sulaiman ya fada, "Zan baka
dukkan wani hadin kai. Sai dai don Allah ka bishi
a hankali i ‘ kar a Bata masa rai Ibrahim ya yi
murmushi ya Ce, "Daddy sai ka kau da kai". ‘ Dr.
Sulaiman ya ce, "Ba zan iya ganin Sabir cikin
bacin rai ba, sai dai ina ga zan yi tafiya ma‘ sabo
da kar ma in ga wani hali da zai shiga, zan barshi
(In your care) ka kula da shi, duk da zan yi
kewarsa -‘ gara in yi kewarsa da in ganshi cikin
yanayi na. quntata ko na takura." ' ‘ Ibrahim ya
ce"Duk yadda ka yi daidai ne ‘ Daddy. Bari muje
Asibitin".To Allah Ya taimaka, Ya bada'sa'a". ‘
Nan sukai sallama Ibrahim ya fita, ya yin da Dr.
Sulaiman ya kwanta yana tunanin dansa a ransa
da yadda rayuwarsa za ta kasance
sabir
ya fito daga zuriar ALHAJI BALA-RABE
ABUBAKAR Wanda ake_ma Zuri'ar lakani da
BIRNIN GAYU. Ba don arzikinsu kadai ba, har da
shaharar da suka yi da ilimin zamani wanda a
wannan lokaci ba kowa ke yi ba. ' Alhaji Balarabe
Kaka ne ga Mahaifin Sabir Dr. Sulaiman. Ya yi
zamani da' Turawa, kuma ya yi rayuwa ~dasu, ya
yi zama da su a engla ' Asalinsu mutanen Kano
ne. Sunada
' zuriarsu a gauraye suke Hausa-Fulani
Lokacin da Alhaji Balarabe ya dawo daga
ingila ne bayan ya yi karatu kuma ya yi aiki da
su harna tsawon shekaru ya dawo Kano tare da
Matarsa da 'ya'yansa. .
‘ Ya dawo da kudi maSu yawan gaske, ya sayi
makeken Fili ya ' gina gida a Estate guda Wanda
a wannan lokaci ya zamana abin kallo da
‘sha'awa sabo da gini ne irin na kasar waje' da
da yawan mutane akan gidan suke fara ganin ‘irin
wanna“ gidan... Wannan yasa -' akai ma gidan
lakabi' ‘daBIRNIN gAYU saboda irin yanayin'
ginin, da tsarinsa da kyansa da .kuma yadda‘ ~'
suke rayuwarsu irin na Turawa'ne tamkar ba
Hausawaba"
'Tsarin ° rayuwarsu ba irin
. tsarin rayuwar Bahaushe, bane haka dabi'unsu
da ; akidarsu.
A hankali zuri'ar Alhaji Balarabe ta cika" da yara
‘maZa da mata, shi da qannensa da sauran
danginsa sukai ta hayayyafa, Zuri'a ta girma ta
'cika, ta bazu kota ina,rasuwarsa, 'ya'yansa ,
‘ ,suka ci gaba da tafiyar da ,tsarin rayuwars kan
yadda ya‘bari.
Zuri'a ce mai cike da 'yan: Boko, 'yan
Kasuwa, 'yan Siyasa. Ba dai kalar da babu.‘
Hatta
masu (Uniform) akwai a zuriyar, wato manyan
Sojoji; 'yan Sandadasauransu
A hankali Suka dinga fita daga BIRNIN GAYU,
wato gidansu na gado, kowa'ya kama gabansa
yaje yayi irin kalar gininsa da yake so. Amma sai
ya dora BIRNIN GAYUN nan sbd sunan laqani ne
da shaida na zuriyar
Yawancin auren gida suka dinga yi, wato, AURE‘N
DANGI, shi'yasa kusan kowa dan uwan kowanene
azuriyar.
Dr. .Sulaiman 'ya kasance babba a cikin gidansu,
wurin nasu‘ Mahaifin su"uku, ne da- qannensa
duka maza. . "
lyayensu duka sun' rasu; saidai kafin su rasu
kowa‘ ya kama gabansa dukkansu kowanne- da
matarsa suna da yara suna zumunci ta hanyar
ziyartar' juna in Sun .samu‘". lokaci daga
harkokinsu sai dai gaskiya ba wani shaquwa a
tsakanin yaransu, in an yi la'akari irin akidar da
suka tashi da ita ba ruwan koWa da kowa ba mai
shiga harkar wani sai-ta kama, don haka Dr
Sulaiman yake nasa rayuwar daban da
yaransa
Dr. Sulaiman- ya riqe manya-manyam mukaman
Gwamna‘ti a cikin tarihin rayuwarsa. Bayan ya
kammala karatun Digirinsa na uku ne a kasar
Sweesland ya cancanci zama (Doctor sai ya
dawo qasa Nigeria. da zama inda nan ya gina
wani qaton Asibiti da ya yi masa lakabi da sunan
Mahaifiyarsa HAJIYA RABI HOSPITAL sabo da
sha'awarsa‘. ga taimakawa qasarsa. lYa riqé
mukamin comisionan ilimi na Jiha har tsawon‘ ‘
shekara takwas. Bayan shudewar Gwamnatin ne
sabuWar gwamnati ta sake nadashi a matsayin
kWamishinan lafiya, inda bai dade ba da wannan
mukamin Sunansa ya fito cikin jerin mutanen da ;
‘Fadar Shu‘gaban Kasa ta lissafa a matsayin
.Ministoci. ' ' Anan ma dai Gwamnatin Tarayya ta
sake : nadashi ;Ministan Ilimi na qasa gaba daya
har zuwa qarshen zangin Mulkin na' wannan
qarnin
Alhaji Dr. Sulaiman ya mallaki manya~ manyan
Kamfanunuwan da ake ji dasu a kasarnan. , ._dr
Sulaiman ya yi matan aure uku. ' Matarsa ta
farko ita ce Hajiya Sande wacce 'yar uwarsace;
Ita ta°fara haifa masa 'ya Mace mai suna '
Farida, wacce Dr. Sulaiman ke‘ ji da ita sosai.
Tana da shekara biyar a duniya Allah Ya yi ma ta
rasuwa, ba tare da ta sake haihuwa ba. Anan' Dr.
Sulaiman ya sake auren Hajiya Amina. .
’wannan karon ba' 'yar— uwarsa bane, 'yar
aminin Mahaifinsa ne ya ba shi ita. . . Bayan
Hajiya Amina ta haifa yaran ne Zulaiha da
Rufaida rikon Fadila ya gagareta, _. rainonta ya
Kare ahannun 'yan aiki. '
farida ta kasance cikin kewa da kadaici sabo ba
mai janta a jiki' sai Mahaifinta wanda kullum
baya nan, harkokin gabansa basa bari ya ‘
kusanta da ita, ’
Zuwan Ibrahim 'gidan ya dan kawo ma ta
sassauci. Wanda dane. ga abokin Dr. ‘Sulaiman
wanda ya samu hatsarin Mota shi da Matarsa
suka- rasu a.take.
A cikin zuriyarsu 'akai' ta kame-kamen mai
rikonsa, don haka Dr. Sulaimanya daukoshi ya
kawoshi. gidansa ya bawa Hajiya Amina amana
don shi bai san‘ma irin rikon da ake yiwa yarsa
ba. Farida na da shekara bakwai,‘ Ibrahim nada
shekara hudu
Shi ya zame mata abokin ‘wasanta, yana" debe
mata kewa, har goyo tana masa, ta bashi
abincisuje Ma‘karanta tare, yana rabin Aji
.itakuma tana Aji uku, ya yin da kulawarsu,-kayan
sawarsu da kOmai na hanmin masu Aiki. ‘
. Wata Kanwar Dr. Sulaiman neta~zo gidan taga
irin halin‘ da suke ciki,"tayi saurin sanar _ shi,
sai» suyi ciwo su kwanta ma Hajiya’ Amina .ba ta
da labari,‘ ita da yaranta kuwa basuma cika
zama qasarba kasar yarda take ta naci da‘
qokarin samun da namiji, amma ikon Allah k0 Ciki
bata
- sake yiba.
Bayan Dr. Sulaiman ya samu labarih abin da ke
faruwa, ranshi ya baci, ya yi niyyar yin maganin
Hajiya Amina, tana qasar waje k0 sai ji ta yi ya yi
aure, ya _auro Hajiya Fatima 'yar hamshakin mai
kudi Bafillatana"fara sol, kyakkyawa mai ilimi', ga
Wayewa
_Riqon 'Farida da 'Ibrahim ya"—koma hannunta
ta rungumesu. ko— hannu ~biyu kamar yayanta
So, “Kauna' da — Kulawa da 'Gata ba Wanda ba
ta‘ nuna musU' har suka manta da rayuwar ‘
kadaicinsu.
Hakan ya jefa soyayyarta ‘a'Zuciyar Dr: Sulaiman
sosai. Suka yi wata irin shakuwa.
Dr Sulaiman ganin ya» gama .sauka a
Mukamansa, kuma ya tara dukiya .mai-dumbin:
'_ yawa, ga kuma._ manyan - Kamfanoninsa‘ da
Asibitinsa na aiki yadda ya kamata, hakan ya
tattara Yaransa da Matansa Hajiya. Fatima da
Kasuwancinsa ya ‘koma kasar Canada, ya yin da‘
ya bar Hajiya Amina a Nigeria da Yaranta.
shi kansa Dr. Sulaiman sai dai -wayewar ta
ratsashi sosai, haka bokon ya shigesa sosai akan
addini. Tana burin gyara rayuwar gidan ' Wannan
magana na Hajiya Fatima» ya shiga
kwakwalwarSu sosai, musamman Farida da
takeda'wayo so Sai dai burin Hajiya Fatima bai
kai ga cika
ba allabYa karBi ranta ta hanyar haihuwar Sabir
Kwarai - Fatima da Ibrahim sunyi kuka"
Sun yi rashin Uwa' mai .sonsu da qaunarsu Haka
suka ’shiga’halin MARAICi da shi ’" da yaransab
dukda Yana da‘ wata-Matar, amman
" jinta yake ba kamar Hajiya Fatima,ba
‘ Rainon Sabir 'ya koma hannun‘ farida
qanuwar Dr. Sulaiman, musamman ya
daukota-‘ta dawo Canada’sabo da rainon Sabir,
don kuwa bata da aure, tana gida ta samu saBani
da Mijinta
har auren ya mutu. Tare suka zauna' su Farida
da
shared a profile .
birnin gayu
chapter4
Ibrahim. suka yi rainon sabir. Yana da shekara
uku a duniya Auntynsa ta yi aure.) ' , Farida da
Ibrahim da masu aiki da shi kansa Dr. Suleiman
din sun: sukaita rainon Sabir ya saba dasu sosai
ya shaqu da Farida sosai, komai Sister: haka ya
dauketa tamkar uwarsa, bashi da magana da‘ ya
wuce na Sister.
‘Sun dauki son duniya sun daura masa ,
musamman Dr. Sulaiman yadda yake Bata Sabir
abin ba,a magana duk abin da yake so shi zai'yi,
ba a sa shi ba a hanashi. Haka ya tashi sakale,
gata ya yi masa yawa. a wajen
Dr. Sulaiman tamkar bashi da wasu ‘ ‘ya'yan. duk
da yana kaunarsu amma soyayyar Sabir daban
take a zuciyarsa da ransa, don haka duk abin da
Sabir keso ya zauna ba mai hanashi.
Farida abin na damunta, duk yadda ta yi kokarin
gyara Sabir sai Daddy ya rushe, tana matuqar son
sabir; haka nan bata mance kaunar da
Mahaifiyatsa ta nuna musu, sannan nasiharta
da burinta yana nan a tsakar kanta.
Farida, Ibrahim, Sabir tare suka tashi, suka girma
cikin so da shakuwa, ya yin da farida ke musu
komai a matsayinta na babbar yayarsu.
Sun taso kuma sun girma a Canada, anan suka
yi, karatunsu, daga Farida har; Ibrahim Medicine
suka karanta, don dukkansu wannan' ne burinsu.
' ‘
Haka- tana da burin ta dawo gida Nigeria ta yi
aiki a'Asibitin.‘ Mahaifinta.
Kullum tana; cikin .katu bin.cike akan Mata; ta
kware akan sanin ciwon Mata da matsalolinsu
Ya yin da’ 'Shi kuma Ibrahim ya karanci bangaren
fata bayan ya zama cikakken ,Likita ya Sake
kOmawa karatu na, ‘ shekara uku don kwarewa
akan sanin ciwon Fata
Shi kuwa Sabir, bayan ya gama Secondary -
School dinsa da yaki karatun ma sabo da duk-
abin da yake'so a duniya yana da shi, kuma zai
samu sabir
Mutum ne Wanda ya ki jinin wahala k0 kadan,
baya'son abinda zai Wahalar da shi‘. '
Cikin‘dabara 'Farida da Mahaidinsa suka sa ya
fara karatu Da da farko Business‘ya soya';
karanta amma ; sai ' Farida‘ tace ‘masma" 'yana,
da kwakwalwa ‘mai zai hana ya Zama Likita
kamar:
yadda ita da Ibrahim suka karanta (Medicine) sai
, su tari su riRe Asibitin Mahaifinsu. ,ta Kara nuna
masa cewa burin Mahaifiyarsa ce hakan Sabir ya
amince ya ; ‘ fara karatunsa na Medicine " a
University of Albena da ke Canada. ’ ; ' Bayan
gama karatunsa ne‘ Mahaifinsa‘ ya ~ shirya
musu tafiya hutu tare dan-Shi, suka tafi
yawon bude ido qasashe daban-daban suka yi
Umarah a Saudi sannan suka Wuce Nigeria»
Wannan karon shi ne karo na farko da
Sabir ya zo Nigeria yaga 'yan uwansa da
danginsa na gun Uwa da Uba. Basuf1 Sati ba ya
daga musu hankali
suka koma Canada.
Zulaiha da Rufaida na tare da Mahaifiyarsu a
Nigeria haka nan duk sun gama ‘ ‘karatunsu‘
suna aiki a Kamfanin Mahaifinsa
, kafin su yi aure.
dr Sulaiman ya kasance tsakanin Canada 'da
Nigeria. _ Farida da Ibrahim na son dawowa
Nigeria amma Mahaifinsu ya hanasu sabo da
kawai su zauna da Sabir a Canada, .don ya ce
shi ba zai dawo Nigeria ba, rayuwar da- Sabir ke
yi a Canada yana mugun dagawa Farida hankali.
Ta shiga‘ damuwa sosai saboda ‘ko ta hanashi
bazai hanubA, haka Daddy ya hanasu’ takura
masa k0 su yi mishi abin da’baya so. .
Sabir kyakkyawan Matashi ne, dogo fari tas
sakalalle dan masu naira mai ji ‘da. ilimi 'da
kuma wayewa, wanda gata ta masa yawa, '
Yana yadda yake so da naira, ya shiga Mota mai
tsadar da ya ga dama, ya sa mai tsada,’ ya taka
mai tsada, ba shi da wata rayuwa da ya. wuce na
jin dadi da hOlewa.
Addini dai bai damesa ba, yana dai Sallah, lokacin
da ya ga dama, haka 'yan mata kuwa canjasu
yake'kamar riga.
’ Duk wata 'yar mai kudi da ke ji da kanta wurin
kyau da ilimi da aji irin wanda iyayensu ,
ke‘turosu karatu daga Nigeria; ba wacce Sabir bai
yi yayinta ya kyaleta ba. Tsananin suyi wata biyu
zuwa uku da Mace ya yar da ita.
Haka ma sauran Matan fararen Fata, ba kalar
Mace mai kyau da Sabir bai yi yayinta ya zubar
ba.
Hat gobe 'yan mata binsa-suke, yana musu .
yadda ya ga dama. A cewarsa shi yanzu ya gaji
da 'yan mata . wai kyawawa sun kare, shi k0
mutum ne mai son abu mai kyau, komai nasa a
rayuwa mai kyau da sha’awa yake so. _ Ya yin
da yaki jinin mummunan abu, k0
da kuwa dabba ne k0 Sutura.
‘ A fili ya ke nuna kyamar mummunan abu.
Wani lokacin in ya ga mummunan dabba bayan
kyamarsu ma‘har da tsoronsu yake
' Akwai ran da yaje Asibitin da su Farida da
Ibrahim ke aiki suka samu an kawo hatsari ba
kyan gani, mutumin kansa ya kumbura ” sosai,
gaba daya halittarsa ya canja'. Koda Sabir - ya
ganshi, ‘ ya yi tsananin firgita, sai da ya suma
sabo da firgita. a
Haka ranar yakwana a tsorace yayi ba bacci haka
ya qankame Ibrahim a jikinsa ya' kwana
Farida na masa addu'a. Da‘ taimakon Allurar
Bacci ya‘samu bacci da kyar
saida ya kusa sati kafin ya dawo daidai tun kuwa
daga wannan ranan bai sake zuwa Asibitinba ko
da wasa ba
. .' ’Wannan rayuwa ta'Sabir yana mummunan
,daga hankalin Farida. Sam bai san meye rayuwa
ba
, 'Su tsoratar da Sabir ga ‘ mutuwa. ya san
kwanciyar Kabari, su inganta‘
. masa' rayuwarsa ta duniya da lahira _tun kafin
'~ ‘lokaci ya kure musu gaba daya. ‘
_ Wannan ne yasa ‘farida ta ‘fuskanci’"
Mahaifnsu ta sanar da‘ shi illar rayuwar da ya '
kyale Sabir yana yi, dole ya san na yi da amanar,
da Allah Ya ba shi na 'ya'yansa. ‘
Farida ta 'yi iya qokarinta sosai nason ganin jawo
hankalin Daddy ya fahimci ‘ halin da 'Sabir yake
ciki- ammai sai ya kasa ganewa har’ zuwa
lokacin da suka dawo Nigeria don yin auren
Farida da kannenta Rufaida-da Zulaihat.
Da‘kansa ya lura da rayuwar da Sabir yake ba
abin da ya tayar masa 'da hankali kamar yadda
ya ga Sabir yana shan giya kamar ruwa
.Haka nan Sabir sosai akan abin da ya ke so in
an hanashi
Ranar ‘da Daddy ya kamashi da giya ya hanashi
sha rana ta farko ke nan da ya fara hana
shi wani abu a rayuwa.
Ranar ko ya ga rigimar. Sabir, nan da nan. ya
birkice musu, 'ga Sabir da wani irin fishi da
zuciya mara kyau. '
' ‘Sai da ya dagawa kowa hankali a ranar. ' ‘ Tun
daga lokacin hankalin Baban nasu ya fara
tashi sabo da ‘yadda ’ya ga Sabir na shan
giya;ne kuma ya saba da' ita haka to zata iya
taba lafiyarsa~
' 'innalilahi' Wa inna ilaillinaju ’un Abin' da Daddy
ke fada kenan cikin tashin hankali. '
Farida ta matso garesa tare da Ibrahim 'ta ‘ ce,
"Daddy abin» da nake kokarin- ka gane ke nan
tun-tuni ka kasa. ‘
Dubi~ irin rayuwar da Sabir yake, wannan ‘ kadan
ma ka gani, mu da ke rayuwa da shi-mu muke
ganin rayuwarsa. ..
Daddy kai iyayenka sun maka yadda kai ina
Sabir'kuwa? Na yarda suna da wani irin ' akida,
amma ba‘ su hallaka ma ka rayuwa ba, don da
sun maka haka da yau ba ka kai matsayin da
kake ba. . ' '
- ' Kai mutum ne da ya san'me yake, mai ilimi,
hikima da basira. “
Kowa ya san kai dattijon kirki ne, kowa- ya San
kai na Kwarai ne.
Daddy‘ ka dubi Sabir, kana ganin inya girma ya
kai shekarunka ba za a dinga yi mishi kallon’
dattijon banza‘ ba?‘
Daddy wannan soyayyar da ka ke yiwa Sabir ta
hallakar da shi, ta kashe masa rayuwa. - Daddy
duba da sauran yaran Abokanka wandanda suke
sa'annin juna da Sabir, dubi yanayin hankalinsu
da nutsuwarsu, sunanjin maganan iyayensu‘, suna
ginnama na gaba dasu ‘ ' Daddy ~ kana Mahaifin
Sabir ammn yanzu baka isa ka sa shi ko‘ ka
hanashi k0 ka tsawatar masa ba, sabo da tun
yana yaro baka mai haka ba sai yanzu Daddy
wannan' rayuwar ba shi ne wacce Mahaifiyarsa
taso masanba da shi“ da mu. .duka, haddakai.
Tana son nuna mana kyakkyawar rayuwa don!
muci ribar duniya da lahira‘. . Ina jin takaicin
rashin cika burinta sabo da baka bamu dama‘ ba,
duk da na yi aure zanci gaba da rikon Sabir
kamar dana,ne ,Mijina ba shi da matsala, ka san
zai iya yiwa Sabir komai; zamu yi Kokarin gyara
masa rayuwa "in har ka‘
amince".
. Hawayen nadama ya zubowa Daddy yace‘
"Tabbas na' tafka kuskure" babba, ’ zan-
yi"kokarin gyarawa. ‘ Ban san na yiwa Sabir illah
ba; sai da._, na gani da idona Tabbas sa'anninsa
sun masa, fintinkau A wurare da dama, duk da ya
fisu da komai, ba abin da ya rasa tun daga kan
dukiya, .asali, gata, kyan halitta." . Sai' dai Sabir
yana sakarci,

6 Comments On BIRNIN GAYU
avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

??

avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

Perfect

avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

Good

avatar
hafsat-6-4-5

1 year ago

Reply

A

avatar
sadiya-umar

1 year ago

Reply

Good and interested

avatar
sadiya-umar

1 year ago

Reply

Good and interested

Please Login or Register in order to submit comment