Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[5/31, 21:17] LEEMA: *🅱RILLIAT WRITER'S ASSO....*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*☠ƘUNGIYAR ASIRI☠*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*NA*

*L££MAT*


_Sadaukarwa gare ku_👇🏻
*_MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)_*

*_REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)_*

*_{ƙirƙirarren labari}_*



*🅿1-2*




Wata mace ce wacce ba zata haura shekaru talatin da biyar ba a duniya cikin kitchen tana ta yanke yanken da alama girki zata ɗaura tana sauri sai faɗin take,"Mami dear miko mun cabbage cikin fridge..,shiru babu amsa"

"Mami!!!"ta furta da ƙarfi
"me kike tunani haka tun dazu ina magana bakya jina"?

Murmushi yar yarinyar da ba zata wuce shekaru goma ba tayi tare da sauke ajiyar zuciya!
"mum kin san me"? amsa mata tayi da
"A'a sai kin faɗa!"

"Kawai nayi wani tunani ne akan wukar dake hanun ki kamar na amshe na soƙa maki a ƙahon zuciya sai in jawo shi har cikin ki da ƙarfi sai kawai jini ya fara fita kina bani hakuri ina ƙara chaka maki shi sai naji bakya numfashi sanan in kwashe kayan cikin ki in zauna inaci a matsayin abinci,jinin kuwa ya zamo ruwan sha na"!!
Tana kai nan,ta fashe da wani irin dariya mai ban mamaki....

Hannu biyu zainab ta ɗaura a kai tare da kurma ihu har sai da Muhammad mijinta dake parlour ya shigo a guje yana faɗin"lafiya dai sweet?"

Mami ta nuna mashi tana hawaye tare da girgiza kai....

Cike da tsoro ya rungume yar shi yana tambayar ta
"menene ya same ki mami na"?

Dariya ta ƙara yi sanan ta maimaita mashi abinda ta gama faɗa kuma tana kwatanta yadda zata yi amfani da wukar a cikin mum d'in ta...

"Subhanallah,kada ki sake irin wanan hasashe bashi da amfani kwata kwata kin ji mamata"? haka ya fadi cikin tsantar mamaki..
Kuka ta fashe da shi tana fadin
"Gaskiya ba zan yarda ba ni daddy kullum idan inason yin abinda zuciyata ke so sai ka rinƙa hana ni"!katse ta yayi ta hanyar cewa

"Shiiiiii!,kada ki sake faɗin haka domin zuciyar ki a kullum babu abinda take dasa maki sai mugun nufi wanda ba daidai bane,yanzu canza kaya mu fita ki sha ice cream ko"?da murnar ta ta ce

"Yeeeeeeeeeeeh,shi yasa nake sonka Daddy saboda kafi mum sona kuma idan na shiga
*ƘUNGIYAR ASIRI* ba zan sha jinin ka ba,ke kuma"ta nuna mum ɗin ta",Sai na farka cikin ki da wuka na cinye naman ki ɗanye"!!tana kai wa nan ta ruga zuwa d'akin ta....

Kuka mai ciwo zainab ta fashe dashi sosai, gaskiya lamarin yarinyar nan yana bata tsoro sosai kullum abu sai gaba yake yi?
"Kana ji fa bata da magana sai zama yar *ƘUNGIYAR ASIRI"*!?abin da Zainab ta fada kenan cikin karayar zuciya..

Rungume ta yayi sosai yana shafa bayanta cikin tsigar rarashi yake fadin..,
"Ki yi shiru haka nan zainab quruciya ke damin Mami kuma babu abinda zai faru dake da iznin Allah kin ji"?

Alamar shigowar ta suka ji...tana sanye cikin doguwar riga yar kanti wace ta wuce gwiwa kaɗan, sai head band sumanta a nade tsakiya wanda hakan ya ƙara mata kyau ainun.

Shiru ya biyo baya,suna ƙare mata kallo cikin so da kauna.

Murmushi suka sakar wa juna da dad d'in ta yace..
"My angel kinyi kyau sosai!".
"Thank you daddy na"abin da ta ce kenan daga haka ya riƙe hanunta yana faɗin
"Honey sai mun dawo ko"?

Hannu kawai ta daga masu zuciyarta a dagule har taji tashin motar shi alamar sun fice daga gidan ba tare da wata ƙwaƙwarar motsi ba!

Kashe gas cooker tayi tare da yin zaman dirshan a kitchen ɗin tana cigaba da kuka tare da waiwayen rayuwar su na baya.


*******************
Zainab shanono shine asalin sunan ta,iyayenta yan Kazaure ne suna da rufin asiri irin nasu wanda hakan ya basu daman kula da tarbiyyar ta da sauran yan uwanta har ta samu ingantaccen ilimi zuwa matakin karatun jami'a!

Kwatsam Allah ya haɗa ta da Muhammad a wurin bautar ƙasa a garin Abuja inda soyayya mai ƙarfi ta ƙullu a tsakanin su.

Ba'a ɗauki lokaci mai tsayi ba iyaye suka shigo kan gaba akayi shagulgula mara misaltuwa!,Tun daga lokacin zainab ta samu karɓuwa wurin ahalin mijinta,gefe ɗaya kuma rayuwar aure mai cike da dimbin kyautatawa juna da kulawa suke gudanarwa a gidan su.

Matsala ta farko da suka fara fuskanta shine rashin haihuwa!

Wanda mahaifiyar Muhammad ta fara nuna damuwarta ƙarara.., basu ɗauki abun da wani muhimmanci ba domin sun riga sun tsara yadda zasu gudanar da rayuwar su!

Kwanaki na tafiya,shekaru na ja, ma'auratan suka fara shiga damuwa, duba da yadda dangin miji suka sata a gaba da habaici iri iri...

Wasa wasa har suka shekara biyar da aure babu labarin haihuwa,wanan dalili yasa mahaifiyar Muhammad ta shata mashi layi akan koya saki zainab ya auro wacce zata haifa mata jika,ko ta tsine mashi!

Faɗin irin tashin hankali da suka shiga ba'a magana!

A dalilin haka wata yar uwar Muhammad _Dr faiza_,wacce babban likitar mata ce tana aiki karkashin wani qungiya na turawa(UNICEF) a nan Abuja,shawara ta basu mai zai hana su same ta a Abuja akwai shawarwari da zata basu ko Allah zai saka su dace .

Ba tare da bata lokaci ba suka shirya zuwa offishin ta ....,,ta haɗa su da wani kwararran likita Bature domin ayi masu gwaji na musamman.
Tun daga kan maniyi,jini zuwa fitsarin su babu wanda ba'a diba ba domin yin gwaji..

Lokacin da sakamako ya fito aka gano matsalar daga wurin zainab ne saboda ta taɓa amfani da wani hanya na tsarin iyali mai suna _Tubal ligation(wata hanya ce da ake daure ko hana ko katse hanyar wucewar kwayayen halittar mahaifar mace da haduwa da maniyin da namiji da nufin hana daukar ciki)_,shine dalilin da yasa maniyyin mijinta baya wuce wa cikin mahaifa idan sun yi kwanciyar aure!.

A lokacin ne suka tuna dalilin da yasa suka yi tsarin iyali a farkon auren su domin zainab dake burin zuwa makarantar lauya domin cikar burin ta na zama cikakkiyar lauya.

Faɗa sosai Dr faiza tayi masu a matsayinta na babban likita kuma yar uwa a gare shi!.

Shawara biyu ta basu wanda sune kawai mafita a gare su;
Na farko shine; _IVF_(wata hanya ce ake amfani da fertilized egg wanda ke aje cikin lab a sakawa mace cikin uterus/mahaifa,iyaka ta raini cikin ta haihu)..

Hanya ta biyu;shine _artificial insemination_ (wanda za'a dibi sperm din mijin ki a haɗa da na wata mace sai a haɗa wuri ɗaya shima ayi placing cikin uterus din ki.

Akwai mata kala kala wanda suke bada maniyyin su a biya su, already an riga an masu Physical examination,an gwada jinin su tare da sperm analysis domin kariya daga cuta.

Tsoro ya kama zainab tana ganin kamar yiwa Allah shishigi ne a haɗa maniyyin mijin ta da na wata macen da ba muharraman shi ba a saka mata a mahaifa ta raina kuma ta haifa,kenan menene matsayin abinda zata haifa,ɗan halak ko shege?

Ganin hankalin ta ya tashi yasa Muhammad ya karfafa mata gwiwa a ganin shi wanan shine kawai mafita a gare su,idan kuma ta aminta a raba auren su shike nan su koma gida!

Babu shiri ta nuna amincewar ta ba don taso ba sai don kare martabar auren ta.

Cikin kankanin lokaci aka samo wacce zata bada maniyyin ta bayan an dibi nashi,an diba nata an auna yayi daidai aka saka wa zainab cikin uterus nata tare da basu shawarwari masu inganci.

Kuɗi Naira miliyan ɗaya ya biya na wanan aiki yana mai cike da farin ciki suka dawo gida..

_Gare ku ma'aurata masu neman haihuwa ko ta halin yaya,wallahi wanan abun da turawa suka kirkira bai halarta ba a addinin musulunci,sanan kuma ire iren wanan shishigi da ake yiwa Ubangiji ke sa a haifi ɗan da zai zama fanɗararre a rasa gano inda ya kwaso mugun hali,bayan iyaye na matuƙar ƙoƙarin ganin sun bashi ingantacciyar tarbiyya!,wace aka haɗa maniyyin ta dana mijin ki har aka samar da ɗan basu san asali,nasaba,halaye da kuma dabi'unta ba.haihuwa,aure,mutuwa da arziki duka lokaci ne idan Allah bai baka ba,bawai ya manta dakai bane maybe rashin shi,shine mafi alheri a gare ka domin da wata haihuwar gwara babu wallahi_


Tun daga lokacin da aka yi wanan aiki zainab bata sake samun cikakkiyar lafiya ba,azabar yau daban,na gobe daban!

Ga dai buri ya cika an samu ciki,yan uwa kowa na farin ciki amma ita kaɗai tasan azabar da take sha har ciki ya isa haihuwa da kyar ta haihu lafiya aka samu Baby girl mai kama da ubanta wacce taci sunan mahaifiyar shi(Aminatu).

Wani irin so da kauna suke yiwa Aminatu wanda baya misaltuwa, tun tana jaririya abubuwan al'ajabi ke faruwa akanta wanda ake firgita zainab har ta kai munzalin shiga makaranta aka saka ta nursery 1,lokacin tana da shekaru uku a duniya.

Abubuwa take aikata kamar wata babbar mace,tun daga kan mallamai har ɗalibai ta fitine su kamar wata iblis kullum cikin kiran iyayen ta a makaranta!

Daga ta fasa wa yaro kai,ta yanki wata da razor,ta caka wa wata pencil a hanci da sauran su..
Kusan ko wane term sai an canza mata makaranta wanda da kyar ta kamalla primary school!

Wani babban abin mamaki har iyayen ta bata bari ba domin kusan kullum sai ta saka zainab kuka,idan bata haɗa iyayenta faɗa ba hankalin ta baya kwanciya,abubuwa nata gaba dai har zuwa wanan lokaci data cika shekaru goma a duniya zata shiga jss1 kenan idan an koma hutun karshen zango.

********************

Cikin kuka ta ɗaga hannayen ta sama tana mai kaskantar da kanta..
"Ya Ubangij,gare ka na dogara kuma a gare ka nake neman taimako,nasan Ni mai laifi ne,kuma baiwar ka mai rauni,ka dube mu da idanun rahama ka shirya mana zuri'a,Allah ka kare mu da wannan yarinya tamu,Allah ka shirya ta ka kawo mana karshen wannan tashin hankali.....

************
Bayan fitar su daga gidan sun hau titi sosai Mami ta kalli daddyn ta ta ce,.
"Kasan me daddy na"?hankalin shi na kan hanya ya ce.
"A'a sai kin faɗa mamata".. cigaba da magana tayi
"Dama motar nan ta kama da wuta kawai na fita da gudu,ta kone da kai yadda ba za'a iya kashe wa ba har sai ka mutu a ciki"!!..da sauri ya taka burki yana maimata
"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un"cikin zuciyar shi yana faɗin wanan wace irin masifa ce!
"Daddy me yasa ka tsaya"?ta mai tambayar tana son sanin dalilin sa na tsayawar
A zafafe ya ƙure ta da idanu cike da ɓacin rai domin ji yake kamar ya faffala mata mari!

Jin horn yayi yawa ta ko ina yasa ya juya hancin motar zuwa hanyar gida ...

A zuciye ta kalle shi ta ce..
"Saboda na fadi abinda ke zuciya ta shine zaka koma gida daddy"?
Banza yayi da ita kamar ma bata wurin ya cigaba da tuƙi a tsiyace..., ƙoƙarin buɗe murfin kofa take yi zata fita ya fincikota da ƙarfi tare da danna lock ta gefen shi!
Naɗin suman kanta ya riƙe da ƙarfi da hannu ɗaya cikin ɓacin rai ya fara magana;

"Ke wace irin shaidaniyar yarinya ce? baki da magana sai mugun furuci? menene laifin mu a gare ki da a koda yaushe baki da buri daya wuce kiga bayan mu?na san maganin ki,wallahi makarantar kwana zan kai ki kowa ma ta huta da iskancin ki"!!.

Tunda ya fara faɗa runtse idanun ta tayi tare da cije lips nata azaba na shigar ta amma taurin zuciyar ta ya hana ta bada hakuri bare ta nuna alamar tayi nadamar furuncin ta.

Sai daya gaji don kanshi ya sake ta,nan take tayi kwafa dai-dai sun iso gida har mai gadi ya buɗe masu gate.
Zuciyarta na tafasa burinta kawai ta sauke wanan ɓacin rai a kan mum ɗin ta!..
Har ya buɗe kofa ya fice zuwa cikin gida bata lura ba,sai daga baya ta sake yin kwafa sanan ta fito zuwa ciki....

Zainab na mashi sannu da zuwa amma ko kallon ta bai yi ba domin duka laifin a kanta yake daurawa,a ganin shi itace bata kula da tarbiyyar mami yadda ya kamata ba shi yasa aka samu taɓara a ɗabi'un ta.


Tana tsaye inda ya barta taji shigowar mami a guje wace ta wuce d'akin ta ba tare da ta kula da maganar da zainab ke mata ba....

Wani tashin hankalin zainab ta shiga domin ta rasa wurin wanda zata fara zuwa,gashi ta haɗa masu abinci mai kyau su kawai take jira.

Cikin su tasan halin kowa; Muhammad idan yayi fushi yafi buƙatar keɓewa shi ɗaya na wani lokaci.

Ita mami kuwa taurin kai ne da ita sosai,tasan koda taje ba zata taɓa kallonta ba bare har ta amsa ta!
Tun tana faɗa da duka har ya gaji ta zuba wa sarautar Allah idanu kullum cikin addu'a take Allah ya shirya mata zuri'a..!!!

Wani irin ihu ta jiyo daga cikin gidan...,saboda tsabar rude wa ta rasa ina zata nufa!

Daidai kofar dakin mami ta tsaya turus hango jini na biyo Ƙasan kofa wanda ko tantama babu jinin mutum ne!!!



*~Banyi alƙawarin typing kullum ba,haka zaliki banyi alƙawarin typing da yawa ba saboda halin yau da kullum~*


*HALIMATUS SADIYA MUHAMMAD*📚🖊
[6/1, 21:04] LEEMA: *🅱RILLIAT WRITER'S ASSO....*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*☠ƘUNGIYAR ASIRI☠*
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_{ƙirƙirarren labari}_

       *NA*

          *L££MA*
wattpad
@leemamuhammad826

  _Sadaukarwa gare ku_👇🏻
*_MUHAMMAD KAREEM KD(DADDY)_*

*_REAL HASEENA NABULISI BAKO(DR OGANNIYA)_*

p3-4

_Da sunan Allah mai Rahama Mai jin ƘAI_

  
     Jiki a matuƙar sanyaye take ƙoƙarin kai hanunta ƙasa inda jinin yake da niyar dan gwalawa wai irin jiri taji ya ɗebe ta nan take ta zube ƙasa sumammiya...

  Jininna daɗa kwararowa daga ƙasan ƙofar zuwa inda take kwance ya mamake dukan jikinta!

  ɗumin jinin ya farko da ita daga suman da tayi nan take falon ke juya mata  kujeru na canzawa daga muhalin su zuwa gefe ɗaya kuru kuruwa ke tashi daga cikin ɗakin mami na muryoyin mutane suna magana cikin wani irin yare da bata fahimta baa.

Allah cikin ikon shi ya bata sa'a tana maimata''Auzubikalmatillahi tabbat min sharri ma kalaƙa...''

Wani irin ƙarfi ne yazo mata cikin zafin nama ta nufi ɗakin baccin mijinta a guje wanda ke sharar bacci hankali kwance(dama idan ranshi ya ɓaci da ya samu bacci shike nan).

Saman jikin si ta faɗa tana jijjiga shi''my happiness  ka tashi kaga abun da nake faɗa maka kullum yana yawan faruwa a gidan nan idan kayi tafiya,amma kana ƙaryaata wa!''

Cikin bacci yake jinta sama sama bakin shi ɗauke da salati ya buɗe idanu a hankali fes a kanta yana nazarin wani abu duba da yadda ta firgice lokaci ɗaya.

Rumguma mai kyau ya mata tare da sauke ajiyar zuciya!

Mum mami meke damun kine wai?, kullum idan baki tayar mana da hankali ba naki hankalin baya taɓa kwanciya ko?

Wani kuka mai cin rai ya kufce mata....,saboda Allah menene yasa a kullum kake ƙaryata ni ne?,menene ribata idan na aibata mami?

Ɗan yatsan shi ya ɗaura saman lips nata"shiiiii" ya isa haka  yanzu meke faruwa kuma?

Ɗago kanta tayi tare da yunkurin sauka daga saman jikin shi tana riƙe da hannun shi"muje ka gane wa idanun ka"...,babu musu yake biye da ita baki sake kamar wani soko har zuwa falo.
Wani abun al'ajabi,koda ta duba da kyau wuri ya koma tsaf dashi kamar babu wani abu da ya faru!
Ni banga komi ba a nan zee!"cikin ɗaga murya yake magana".

Ware idanu tayi da kyau ta duba ko ina fes har jinin dake ƙasan ɗakin mami ko alama babu.

Ƙasa ta zaun dabas tana nazari....,tambayar ki nke fa?

Cikin wani irin jarumta da ƙarfin hali ta miƙe,kayi hakuri na ɓata maka bacci in SHAA ALLAH ko kashe ni za ayi cikin gidan nan ba zan sake magana ba"tana kai Nan ta nufi hanyar ɗakin baccin su!".

Jikin shi yayi sanyi saboda baya jin daɗi yadda a kullum zee ke ƙoƙarin aibata nashi gudan jinin shi wanda suka samu a wahalce.

Ɗakin mamin ya buɗe a hankali ya shiga hankalin ta kwance tana sharar bacci ..,wuri ya samu saman gadon ya zauna yana shafa kanta a hankali cikin so da kulawa har ta buɗe ido fuska ɗauke da murmushi.

Daddy na!

Na'am mamin daddy a tashi haka nan ayi sallah ko?
Tau ta furta tana ƙoƙarin sauka daga saman gadon...

ɗakin baccin su ya koma kasancewa magrib ya gabato....,koda ya shiga zainab na ban ɗaki alamar wanka take yi ya nemi wuri ya zauna zuciyar shi cike da sake sake,yana ganin ya kamata ya dubi lamarin zainab da idon basira.

Tunda mami ta fara wayau kullun cikin tayar masu da hankali zainab keyi tun yana biye mata har ya tattara ya watsar.

A dalilin irn wanan saɓani da suje samu yasa hajiyar shi tayi niyyar ɗauke mai ta koma wurin ta ya bata hakuri da zasu duba lamarin a tsanake.

A iya sanin shi dai sun kai ta asibitoci iri iri an dubata baa ga wata matsala tattare da ita ko ƙwaƙwalwar ta baa!

An dangana da mallamai babu wani jinnu ko iska dake jikinta!

Tun daga lokacin ya yiwa zainab gargaɗi mai ƙarfi da kakausar murya akan duk abunda ya sau ɗiyar shi ba zai kyaleta baa,idan ta sake tayar wa yan uwan shi da hankali bai yafe baa!

Fitowar ta daga wanka ya mai do da hankalin shi wurin ta yadda tayi wai irin sanyi ba kamar zainab ɗin da ya sani ba.

Bai wani tsya ɓata  lokaci ba ya shige ban ɗaki domin an fara kiraye kirayen sallah a wasu wuraren....,a hanzarce ya watsa ruwa tare da ɗauro alwala ya nufi masallaci.

A tsanake ta gama shirin ta daga bisanj ta gabatar da sallah...,bayan ta idar take nazarin littafin hisnul muslim cikin natsuwa sai taji ana buga ƙofa a hankali.

Gyaran murya tayi tare da furta"Bismillah",Mami ta shigo bakinta ɗauke da sallama ta nemi wuri kusa da mumyta ta zauna.

Rufe littafin tayi suka shafa addu'a tare"ina wuni mummy?"

Shafa fuskarta tayi fuska ɗauke da murmushin yaƙe"lafiya lau mamin mu ya akayi ne kin yi sallah?"

Eh mumy yunwa nake ji!

Bari daddyn ki ya shigo muci abincin ai.

shigo na ɗan lokaci tna nazarin yanayin taa...,babu wani alamana tashin hankali ko damuwa a tattare
d

a ita.

Mummy yaushe zamu tafi wurin kakan kazaure?

Kina son ganinta ne?

EH mummy dasu mumy safiyya(sister zainab).

Zanyi magana da daddyn ki tau sai mu shirya a tafi haka ya maki ko?

Cike da farin ciki ta amsa da kai tare da miƙewa ta ɗauko wayar zainab dake a gefen gado"zan kira mummy safiyyah in faɗa mata zamu zo".

Murmushi ta saki"daɗi na da mami zumuɗi".

Tun daddyn ki bai amince ba zaki yi shela!

Hello mummy safiyyah ina wuni?,lafiya lau yariyar kirki ina mummyn ki?,gata nan kusa nace mata inaso a kawo ni wurin ki da kakan kazaure.

Yawwa Allah yasa kada su maki wayau yanzu dai hutu ake ba wani uzuri da zasu bamu ko?,"gyaɗa kai tayi kamar tana ganin ta".

Bama kaka waya....,kakan kazaure me da me zaki aje mun zan zo?,duk abunda kike so yar albarka ina iyayen naki ne?.

Daddy na masallaci ga mummy nan!,bata wayar tau.

Assalamu alaikun ma ina wuni?

lafiya lau ya kuke da fatan ba wata matsala kuma?,ajiyar zuciya ta sauke!
Da sauƙi dai,idan Allah yasa ya aminta mun zo zamu sake tattaunawa domin ba magabmnar waya bane ma lamarin kullum gaba yake tafiya.

A sanyayye ta furta,kada ki karaya zainab Allah na sane damu in Shaa Allah komi zai zo ƙarshe,matsalar dai maigidan kine kwata kwata yaƙi bada haɗin kai da an kaita wurin wani mai maganin mayu da naji ana magana cikin gari ko za a dace.

Ma kema kin san halin shi ba zai taɓa yadda ba hasali ma gani yake na tsane ta ne shi yasa nake laƙaba mata abubuwa yanzu haka ma....

Jin alamar shigowar shi yasa ta miƙawa mami wayar wacce ta ƙure ta da idanu"cigaba da magana zan haɗa abinci daddyn ki ya dawo''.

Hijab ɗin ta cire ta nufi hanyar palo..."ina mami?",shine tambayar da ya fara jeho mata.

Taso mayar mashi da ɓakar magana sai taga yin haka ba zai haifar masu da ɗa mai ido baa,dole ta rarashe shi ya aminta da zuwan su kazaure.

Fuskar shi ta shafa cikn wani irin salome,daddyn mami tana ɗaki na suna magana da ma ne.

Cike da zargi yake kallon ta"ba dai wani labarin kika shirya masu akan ƴa ta ba?",uhm ko ɗaya!mamin ce m ta kira safiyyah.

Ranka ya ɗaɗe barij shirya mana abinci ko mami najin yinwa?.

Ba damuwa barin duba ta...

Kulolin abinci  data shirya  a kichen ta shirya saman teburin cin abinci gaba ɗaya dai dai sun fito a tare kowa ya zauna.

Plate biyu ne;ɗya mami da daddyn ta wanda a baya duka a wuri ɗaya suke ci kwatsam da matsalolin ta suka fara bayyana ya hure mata kunnu wai mummynta bata sonta shi ɗaya ya damu da ita saboda haka kada su sake cin abinci a tare.

Ranar daya faɗa wanan magana matuƙa ya mata ciwo tayi kuka daga bisani ta bar wa ALLAH!

Tana gama zubawa suyi addu'a kowa ya fara ci cikin natsuwa...,daddy!

uhm ya furta bakin shi cike da abinci.

Inason zuwa wurin kakan kazaure kaga an daɗe ban ganta baa,mummy safiyyah kuma kullum tace zata zo har yanzu taƙi zuwa.

Cigaba yayi da cin abinci yana zancen zuci domin baya so tana yin nisa dashi bare irin wanan tafiya mai nisa ABUJA zuwa KAZAURE!

Daddy bakace komi baa?,ba a magana idan ana cin abinci ko mummynki bata faɗa maki baa?

Kallon ta tayi cikin ɓata rai"ni bata faɗa mun komi!"

Ya za ayi ta sani kuwa tunda kayi kane kane ka hana yarinya zuwa islamiyya!"ta bashi amsa a tsanake".

Ko a jikin shi ya juya yana fuskantar mami"kazaure kike son zuwa ko?"

Eh daddy!,yau laraba

Please Login or Register in order to submit comment