Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*😢DAREN AURENA💔*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*Daga alk'alamin 'yar mutanan zazzau Naanah M Sha'aban💖*

_Labari mai tab'a zuciya😭_

_Wannan littafin sadaukarwa ne ga k'ungiyata da kuma jaruman cikinta💖_


*Wannan labarin k'irk'irarran labari ne ban yarda a juya min littafi na ta kowacce hanya ba😇*

Shafi na 1

.............📖Kuka take tamkar ranta zai fita kwance take a kan d'an k'aramin gadon d'akin ta duk'unkune a cikin bargo ta rintse idonta zuciyarta nayi mata wani irin zafi da k'una cikin da sasshiyar muryarta ta fara magana "tabbas nayi dana sanin, sanin Jabir a rayuwata, ka cuceni, ka yaudareni bazan tab'a yafe maka ba har duniya ta nad'e, Insha...insha Allahu, Allah sai ya saka min abin da kayi min Kuma....." Sai Kuma ta kasa k'arasawa saboda irin kukan da ya shak'eta.

Aunty Murja ce ta shigo d'akin da sallama d'auke a bakinta zuciyarta cike take da tausayin k'anwarta ta saboda Jabir yabar mata mugun tab'o Wanda bazan tab'a gogewa a cikin zuciyarta da ma rayuwarta gaba d'aya, yayi mata abinda ba za ta tab'a mantawa ba a daren aurensu.

Zuwa tayi kusa da ita ta zauna tare da jawota jikinta suka k'ank'ame juna suna kuka, sun d'auki kusan mintuna biyar suna kukan Aunty Murja ta had'iye nata kukan domin ta samu ta rarrashi k'anwarta ta, Cikin muryar rarrashi ta fara magana "Khadijatullah nasan akwai zafi sosai a cikin zuciyarki, abin da Jabir yayi miki sai dai muce Allah ya saka miki domin kinsan mu ba wani arzik'i ne damu ba, barantana muce zamu kai shii k'ara kotu abi miki hakk'inki, Kuma ko min kai Jabir k'ara a zamanin nan na yanzu babu abinda za'ayi Masa saboda Yana da kud'i, Dan Allah Khadijatullah kiyi hakuri kinsan yawan kukan nan zai iya haifar miki da wata matsalar Ina tsoron kar in rasa ki kamar yadda muka rasa iyayanmu ke kad'ai nake kallo nake jin dad'i a cikin zuciyata" ta k'arasa maganar hawaye na zuba daga cikin idanuwanta.

Khadijatullah ta d'auki kusan mintuna goma tana kok'arin tayi magana Amman kukan da take ya hanata tayi dakyar ta samu ta sassaita kanta ta fara magana cikin sark'ewar muryar "Aunty Murja nasan bakya son kina ganina a cikin irin wannan yanayin, Amman Aunty Murja Ina ga ba zan tab'a daina kuka ba, zuciyata ba zata tab'a daina min zafi ba, saboda yanzu mun d'aura k'awance da tashin hankali, Aunty Murja wallahi ina ga bak'in cikin Jabir ne zai kasheni" wani sabon kukan ne ya kwace Mata Aunty Murja ta k'ara rumgumeta sosai a jikinta, Khadijatullah ta d'auki kusan mintuna biyar tana kukan kafin ta cigaba da magana "Aunty Murja wallahi na tsani Aure kuma na tsani maza, wallahi da za'a bani dama da sai na kashe duk wani namijin da yake duniyar nan tabbas na yarda da maganar hausawa da suke cewa namiji ba d'an goyo bane duk yadda ka Kai ga goya shi wata rana sai yayi maka abin da ba kayi tunanin zai yi maka ba, Kuma idan kaga namiji a rana karka sake kace zaka jawosa inuwa idan kuwa ka jawosa wata rana kai zai tura cikin ranar, Aunty Murja namiji yayi min abinda har abada ba zan manta dashi ba a DAREN AURENA". Duk tana kuka take maganar zuciyarta na cigaba da yi mata zafi.

Aunty Murja kuwa bata iya cewa komai ba, ta cigaba da rarrashin k'anwarta ta har ta samu baci b'arawo ya saceta hamdala Aunty Murja ta shiga yi a cikin zuciyarta domin ta samu yau Khadijatullah tayi bacci Wanda rabon da tayi bacci tun ranar DAREN AURENTA wanda yau kwana uku kenan.

*'BANGAREN GIDANSU JABIR*

Zaune yake a kan kujera wacce ake iya kwantar da ita a kwanta, a farfajiyar gidan ya saka shisha a gaba yana zuk'arta a hankali daga shi sai wani gajeran wando dan ko riga babu a jikinshi, fari ne tas wanda kana ganinshi za kasan balarabe ne, gashin kansa ya kwanta luf sai shek'i yake yi yana da manya_manyan idanuwa wad'anda farare ne tas, dogon hancinsa yayi matuk'ar dacewa da d'an k'aramin bakinsa, wayarsa wacce take gefensa ce ta shiga ruri hannunsa yasa ya d'auketa tare da duba screen d'in wayar ganin wanda yake kiran nashi *Teemarh namo* ya gani, wani gajeran murmushi yayi sannan cikin sanyayayyar muryarsa ya ce "yau akwai harka kenan" d'aga kiran yayi ba tare da ya ce komai ba, daga b'angaren Teemarh namo kuwa cikin shagwab'a ta fara yi magana "baby shine jiya ba ka zo club ba ina ta jiranka, kuma bayan kasan kwana biyu nayi missing d'inka sosai" ta k'arasa magana cikin nark'ar da murya, Jabir ya d'auki kusan mintuna biyar kafin ya ce "Am so sorry dear wallahi na d'an je wani guri ne kuma ban dawo da wuri ba". Cikin nuna tsantsar kishinta a fili ta ce "ina kaje? kodai kaje gurin wannan tsohuwar matar taka" wata iriyar dariya Jabir yayi wacce kana jii kasan ta tsantsar mugunta ce yana dariyar ya ce "haba dai ai wannan ta riga da tayi expired, please ki kwantar da hankalinki, ai yayinta ya riga da ya huce tuntuni" Murmushi teemarh namo tayi ta ce "to shikenan baby yanzu yau dai zaka zo ko? Kasan wallahi nayi missing d'inka sosai i miss your hug i miss you so so much" murmushi Jabir yayi ya ce "zan shigo da daddare yanzu ina d'an hutawa ne" yayi maganar kamar wanda ake yi masa dole "Ok to shikenan sai da daddaren ina nan ina jiranka"
"Ok" yayi maganar a takaice.
"i love you"
"thanks you dear"
Daga nan kowannan su ya ajiye wayarsa Jabir ya cigaba da zuk'ar shishar.

*'BANGAREN KHADIJATULLAHI*

Ta d'auki kusan awa d'aya tana bacci a jikin Aunty Murja dan ita ma har baccin ya d'auketa kamar an tsikareta ta farka a gigice, irin yadda ta farka ne yasa Aunty Murja ita ma ta tashi ta rikota "Khadijatullahi meya faru"
Kallon Aunty Murja take hawaye na kok'arin zubowa daga idanuwanta "bakomai" tayi maganar cikin muryar kuka rumgumeta Aunty Murja tayi tana bubbuga mata bayanta tana cigaba da yi mata nasiha mai ratsa zuciya daga waje suka jii anyi sallama ana kok'arin shigowa d'akin "Assalamu alaikum" Mai shigowar ta fad'a tare da tura kofar d'akin ta shiga, Murmushi Aunty Murja ta sakar mata tare da amsa Mata sallamar "Wa'alaikissalam Amatullahi"
"Ina wuni Aunty Murja" Amatullahi ta tsugunna har k'asa cikin ladabi tana gaisar da Aunty Murjan
"Lafiya kalau ya kike"
"Lafiya alhamdulillah"

Sai kuma ta komar da dubanta kan Khadijatullah wacce tayi luf a jikin Aunty Murja.
"K'awata ba dai har yanzu kuka kike yi ba, haba Khadijatullah dubi yadda fuskarki ta koma idanuwanki duk sunyi ciki_ciki saboda kuka ya kamata kisan cewa wannan k'addara ce Allah ubangiji ya d'ora Mana, Kuma dukkan musulmi ya kamata ya rumgumi duk iriyar k'addarar da tazo Masa Mai kyau ce ko akasin haka".

Shuru kawai Khadijatullah tayi tana sauraronta tana sauke ajiyar zuciya idanuwanta na cigaba da zubar da hawaye, tabbas tasan su Aunty Murja ba zasu tab'a fahimtar irin tashin hankali, bala'i da masifar da take ciki ba, taya za'ayi a daketa Kuma a hanata kuka, bayan sun san irin cutar da Jabir yayi mata tana jin labarai a gidan t.v, kuma tana jin labarai iri_iri wad'anda maza suka yiwa matayensu na cin mutunci, Amman ita Bata tab'a jin labarin irin abin da Jabir yayi Mata a DAREN AURENSU ba, ta yaya za'ayi ta manta da wannan daren, wanda take kiransa da bak'in dare domin ita DAREN AURENTA ya kasance Daren bak'in cikinta, Wanda har yanzu take cikin bak'in ciki.

Amatullahi ta saka hannunta a kan fuskar Khadijatullah tana goge Mata hawayenta,nan ita da Aunty Murja suka sakata a gaba suna yi Mata hira domin su samu ta hak'ura, ita dai kawai jinsu take Amman a wannan karon tayi kok'arin had'iye kukanta domin ta fahimci kukanta Yana jefa masoyannata guda biyu cikin tashin hankali, Aunty Murja ce ta tashi ta d'auko musu abincin da ta girka a wani d'an k'aramin kwanon silba, ta dawo gurin da take ta zauna tare da bud'e kwanon shimkafa da Mai da yaji ce, "Kash! na manta ban d'auko cokula ba" Amatullahi tayi murmushi "To Aunty Murja bari in d'auko miki" mik'ewa tayi ta nufi inda kwandon kwanukansu yake wanda babu wani kayan kirki a cikinsa, ta d'auko cokula guda biyu wad'anda kana ganinsu zaka san sunyi mugun dad'ewa domin har sun fara lank'washewa, zama tayi tare da mik'awa Aunty Murjan cokulan "Gashi Aunty Murja" cokali guda d'aya ta k'arb'a sannan ta ce "to matso sosai muci abincin" Da sauri Amatullahi ta girgiza kai domin abincin dake kwanon bama zai ishesu ita da Khadijatullah ba, saboda bashi da wani yawa "Kaii Aunty Murja Alhamdulillah wallahi sai da naci abinci sosai kafin in zo" sai kuma ta mik'awa Khadijatullah cokalin tana fad'ar "gashi nan kici abincin" girgiza kai ta shiga yi alamar bata cin abincin, cikin d'aurewar fuska Aunty Murja take magana "wato abin da kike son ki tsira kenan rashin cin abinci, ai shikenan tunda haka kika zab'ar wa kanki" sai kuma ta fashe da kuka, cikin tashin hankali Khadijatullah ta karb'i cokalin hannun Amatullahi "Aunty Murja Dan Allah ki dena kuka zan ci" ta fad'a tare da saka cokalin a cikin abincin, shuru Aunty Murja tayi ita ma ta shiga cin abincin loma biyar Khadijatullah tayi ta ajiye cokalin, ta zame ta kwanta a kan yaloluwar katifar da take kan gadon ta rufe Ido domin Bata so Aunty Murja ta k'ara takura Mata taci abinci, Aunty Murja ma Bata ce Mata komai ba, Amatullahi kuwa mik'ewa tayi tare da cewa "to Aunty Murja zan tafi".
"Amatullahi yau tafiya da wuri haka" murmushi tayi ta ce "wallahi Aunty Murja zamu je Unguwa ne da Mama shine nace Bari inzo na ganku kafin mu tafi" Aunty Murja ta ce "Allah sarki Amatullahi to mun gode sosai" "Haba Aunty Murja bakomai ai" zagayawa tayi dai_dai saitin kan Khadijatullah ta shafa fuskar ta ta tana cewa "To k'awata sai na sake dawowa gobe idan yau min dawo da wuri zan k'ara dawowa na ganku" Kai kawai ta d'aga mata, Amatullahi ta k'ara yiwa Aunty Murja sai anjima sannan ta fita daga gidan da saurinta, Aunty Murja ta tashi ta shiga gyara d'akin daga nan ta dawo kan gadon ta kishim gid'a tana sauraron radio da ta kunna a wata matatciyar radio duk rayi raga_raga.

*'BANGAREN GIDANSU JABIR*

Shirye yake cikin wasu k'ananun kaya, kyau iya kyau ya gama yi, turarurrukan dake kan madubin d'akinsa wanda kamar shagon kanti saboda yawansu, ya shiga fasawa a duk jikinsa saboda duk yawan turaren nan sai da ya bisu d'aya bayan d'aya yana fesasu a jikinsa, wani d'an k'aramin kum ya d'auka k'irar dubai shi kanshi kum d'in abin tsayawa ka kalla ne, ya shiga taje kannasa da kum d'in a hankali tamkar wanda a kace dole sai ya taje kannasa, sai da ya d'auki kusan awa d'aya yana shiryawa, sannan ya nufi hanyar fita daga d'akin, ko kulle d'akin bai yi ba haka ya nufi b'angaren Mami Yana taku d'aya_d'aya kamar wanda yake tsoron tafiyar, a haka har ya isa part d'in Mami to sallama bai yi ba haka ya tura kai cikin falon nata a zaune ya tarar da ita tana kallon wani film a zee word, da sauri ya k'arasa kusa da ita ya rumgumeta tare da yi Mata kiss a kumatunta, Murmushi Mami tayi tare da shafa kansa "Wow my son you look so Masha Allah" Murmushi yayi tare da cewa "Thanks you Mum I really love you so much" Mami ta ce "Me too My son I love you so much" Mik'ewa tsaye yayi tare da cewa "Mami zan tafi club sai na dawo a chan zan kwana naga magriba tayi ana ta nema na akwai Abu Mai muhimmanci da zanyi me" yayi maganar cikin Yana yin shagwab'a "To sai ka dawo, Allah ya kaika lafiya, Amman goben ka dawo da wuri saboda Aliyu zai dawo daga dubai Kuma da wuri sai sauka" cikin yanayin farin ciki Jabir ya ce "Kaii d'an uwana Aliyu Ashe dai zan k'ara ganinsa kaii kamar ma kar inje club d'in saboda naga d'an uwana nayi ten year fa ban saka shi a idona ba".
Murmushi Mami tayi "Ai sai gobe zai dawo kaga bai kamata kak'i zuwa club d'in ba saboda kace akwai abinda zakai Mai muhimmanci ai sai gobe zai dawo ai har ka dawo ma" cikin yanayin jin dad'i ya ce "please Mami karku je d'aukoshi har sai na dawo" wani k'ayatatcen murmushi tayi ta ce "karka damu zamu jiraka" wani irin tsalle yayi sannan ya nufi kofar fita daga falon Yana fad'ar "Yawwah Mami nagode sosai" da murmushi ta bishi sannan ta cigaba da kallonta hankalinta kwance, shi kuwa Jabir Yana fita kai tsaye wajen da aka tanada d'an ajiye motoci ya nufa, ya shiga sabuwar motar da Abbansu ya Aiko Masa da ita, Mai gadi ya bud'e Masa gate ya fita da gudu daga gidan bai zame ko ina ba sai club, ai kuwa Yana isa club d'in tun kafin ya fito daga mota aka saka Masa ihu, Yana fitowa daga cikin motar zee namo tazo da gudunta ta rumgumeshi tana yi Masa kiss ta ko ina a jikinsa, d'aukarta yayi cak dan Daman Shima a matse yake yazo club d'in ya huta da zee domin Yana jin dad'in yarinyar sosai hotel d'in club d'in ya nufa da ita, ana fa guri ya k'ara hau tsinewa da ihu, shi kuwa Jabir bai bii ta kansu ba domin burinsa kawai ya samu ya biya buk'atarsa da Zee d'in, d'akin da aka basa ya shiga, ya ajiye zee d'in a kan gado, ya cire mata kayan jikinta daman ba wani kayan k'irki bane a jikin nata rigar bacci ce wacce ko gwiwarta Bata Kai ba, Bata da hannu d'an haka ya zama duka rabin k'irjinta duk a waje suke, Anan ya shiga tsotsarta ta ko ina tamkar ya samu wata alewa, Zee abin nema ya samu dan haka ta sakar Masa dukkanin jikinta Yana tsotsarsa, Anan dai sukai ta shek'e ayarsu (ni kuwa 'yar mutanan zazzagawa nace Allah ya shiryeku Amin) sai wajen isha'i sannan ya sauka daga kan Zee d'in Amman ita Zee d'in sam Bata so haka ba, saboda bata gama dawowa dai_dai ba, toilet ya shiga da niyyar yin wanka, Zee ya mik'e ta shiga cikin toilet d'in, ta tarar da Jabir har ya fara yin wankan bayansa ta hau ta fara shafashi a hankali "Baby kasan fa baka gama dani ba, dan ni ban koshi ba".
Jabir dai shuru yayi domin ya rasa masifa irin ta Zee kullum idan yayi sex da ita duk irin dad'ewar da zai yi a kanta sai tayi Masa korafin Bata koshi ba, janyota yayi ta dawo gabansa Yana kallonta tana kallonsa tana wurga Masa wani shu'umin murmushi.

Jabir ya ce
"Baby ki barni nayi wanka, zuwa anjima zamu had'u,karki manta fa muna tare yau gaba d'aya" yayi maganar cikin salonsa wanda yake rikita yammata, narke masa tayi a jikinsa ta lumshe ido bata k'ara magana ba, Jabir yayi² ta rabu dashi yayi wanka amman sam teemarh tak'i barinsa sai ma k'ara nanik'e masa da tayi, haka ya kyaleta ya shiga yin wankansa teemarh na jikinsa tamkar cingum ta mak'ale masa tana cigaba da shafa jikinsa.

D'aga ta yayi suka fita daga cikin toilet d'in, a kan gado ya samu ya kwantar da ita, sannan ya shiga saka kayansa, ita dai teemarh da kallo take binsa idanuwanta sunyi jawur tana wani lumshesu tana lasar bakinta tamkar mayya tana k'ara zubawa surar jikin Jabir d'in ido, shi kuwa Jabir yana gama shiryawa ya dawo kan gadon yana shafa dukkanin jikin teemarh kuma ya tsotsarsa, haka dai sukai ta aikata Alfasha har kowannansu bacci yayi awan gaba dashi, basu suka tashi ba sai wajen k'arfe shida na safe, ko sallar asuba basuyi ba, haka suka tashi suka shiga wanka a tare, suka fito Jabir ya fara shiryawa da sauri saboda yana tsananin son ya ga d'an uwansa tunda Mami ta fad'a masa cewa yau d'in Aliyu zai dawo da kyar ya iya bacci saboda gani yake kamar idan yayi bacci bazai tashi da wuri ba, ita ma Teemarh shiryawa tayi cikin doguwar rigar baccinta, a tare suka fita daga d'akin Jabir ya rufe d'akin, suka nufi motar, A hanya ya sauke Teemarh domin kuwa baya son ya k'arasa wannan matatciyar unguwar tasu, ya ja motar da gudu bai tsaya a ko ina ba sai a gida, mai gadi ya wangale masa k'aton gate d'in gidan ya shiga da gudu har yana kok'arin yin ciki da mai gadin, Allah ya taimakeshi ya buga wani mugun tsalle sai da ya fad'i a k'asa har ya fasa goshi.

Da saurinsa ya fito daga motar ya nufi hanyar da zata sadashi da tafkeken falon, yana shiga ya tarar su Mami da k'annansa guda biyu dukansu mata ne Shahida da Nihal, wad'anda baza su huce shakara sha bakwai ba, da gudu Nihal ta k'arasa gurinshi tana fad'ar "Yawwa bro daman kai muke ta jira yanzun nan Mami take kok'arin kiranka" murmushi yayi tare da rumgume k'anwar tasa "to darling sister ai gani nazo kawai mu juya muje mu d'aukoshi k'ar jirgin nasu ya sauka, bamu k'arasa ba" Mami tayi murmushi tare da cewa "Ai yau dai kam naga ana kok'arin mantawa dani, dukkanku kuna d'aukin ganin d'an uwanku" da sauri Jabir ya saki Nihal yaje ya rumgume Mamin "haba Maminmu taya zamu manta dake you are so speacial to us" haka su Nihal da Shahida ma duk suka rumgumeta, Murmushi take ta faman sakarwa 'ya'yannata, "Thanks you so much my darlings ina 'kaunarku sosai, yanzu dai muyi sauri mu k'arasa Airport kar Aliyu su sauka bamu k'arasa ba, tunda ya ce 7:00am zasu sauka, yanzu kuma 6:30am daga nan suka dunguma zuwa Airport mota d'aya kawai suka d'auka, k'arfe 7:00am suka isa filin jirgi dai-dai lokacin jirgin su Aliyu yana sauka, haka ya fito cikin takunsa na isa da k'asaita sai zuba kamshi yake yi, kaii masha Allah kyau iya kyau Aliyu yayi domin duk irin kyan Jabir, idan kaga Aliyu zaka san gaskiya Jabir ma mummuna ne, domin kuwa ya ninka Jabir a kyau sosai idan ka ganshi za ka yi tunanin wani balaraben ne, Nihal da Shahida suna ganinsa suka tafi da gudu suka rumgumeshi "We really miss you darling brother" Wani kayatatcen murmushinsa mai tsada ya sakar musu, cikin muryarsa wacce kamar wanda yake yin rad'a ya ce "Me too i really miss you" ana dai suka k'arasa gurin Mami ya rumgume ta tare da sumbatarta a kuncinta, "Mum i miss you so much", "me too i miss you my son" Jabir wanda yake tsaye ya hard'e hannunsa a kan k'irjinsa ya ce "Lallai yau ina ganin san kai" sai a sannan Aliyu ya lura ashe har da Jabir a kazo "Wayyo Allah na, Bro Jabir ashe har da kai aka zo" ya fad'a yana k'arasawa kusa dashi da niyyar ya rumgumeshi, Jabir yayi saurin ja da baya tare da hararar Aliyun "A'a banda ni aka zo saboda tsabar rainin hankali ma baka ganni ba, ni na kasa bacci ina ta son gari ya waye nazo na ganka shine zakai min izza" yayi maganar cikin jin haushin Aliyun "sorry brother kayi min afwa nayi laifi kasan fa kaii d'in jini na ne" Murmushi suka yi gaba d'aya tare da rumgume junansu daga nan suka shiga mota, domin tafiya gida.

Suna zuwa Aliyu ya tarar da jerin abinci kala-kala a kan dining table, ai kuwa daman ya kwaso yanzu ya zauna, ya d'ebi fried rice wacce taji naman kaji ya shiga ci, suma duk suka zauna suna cin abincin suna yin hirarsu abin ban sha'awa.

*BAYAN WATA BIYU*

Amatullahi ce zaune a gaban Aunty Murja cikin nutsuwa Amatullah take magana "Aunty Murja daman nazo ne na nuna miki admission d'inmu na makarantar da muka samu" ta mik'a mata admission letter cikin nuna tsantsar farin cikinta mara misaltuwa Aunty Murja ta fara magana "Kai Alhamdulillahi masha Allah, Allah ubangiji ya tsareku ya baku sa'ar abin da zaku je nema" cikin jin dad'i Amatullahi ta amsa da "Amin ya rabbil'alamin" Aunty Murja ta ce "Amman wace makarantar ce? Kuma ke dawa kuka samu?" Wani kayatatcen murmushi Amatullahi tayi ta ce "Anan makarantar poly ta gadon k'aya, kuma ni da Khadijatullahi ne" ciki nuna mamaki Aunty Murja ta ce "wace Khadijatulla d'in?", Amatullahi ta nuna Khadijatullahi wacce take kwance tana jin duk abin da suka cewa, amman bata tanka musu ba, sai a wannan karon da taji k'awar ta ta, tazo musu da abin ban mamaki, da kyar ta samu ta mik'e idanuwanta na kan Amatullahi domin so take ta tabbatar da gaske take yi ko kuma wasa take musu, sannan ta ce "Aunty Murja wannan Khadijatullah d'in nake nufi, nayi hakan ne kuma domin na fahimci ta hakane kawai zamu samu ta rage tunani da koke-koken da tayi kullum ba dare ba rana, idan muna zuwa makaranta zata dinga samun sauk'in damuwarta" cikin zubar da hawaye Aunty Murja ta fara magana "Ni ban ma san da wane irin baki zan yi miki godiya ba, a gaskiya ke k'awa ce ta gari samun irin ki a wannan zamanin sai an tona domin zai yi wahala sosai mun gode mun gode sosai", hannu Amatullahi ta saka tana sharewa Aunty Murjan hawaye "Haba Aunty Murja menene na kuka ni

Please Login or Register in order to submit comment