Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

komai ba,illa ma kowace da tunanin datake azuciyarta,sai kutashi mushiga ciki,tinda sun shige Fatima tace,sis,dan Allah karkiyiwa izzadeen komai dan nasan halinki,kinsn el Bahrain baisan komai ba,kina wani abun zai gane, naji Ku tashi mutafi tace tana sauka Daga motar ai wlh ko yaya ne sai na mai rashin mutunci,tace azuciyarta,jerawa sukayi suna taku dai dai,Mashida da Fatima sai juya duwawu suke sabida uban hill din dasuka sa,tasleem takalmin datasa bai kai nasu tsini ba,ahaka suka karasa hall din,suna shiga hall din ido yadawo Kansu dan tasleem suka sa atsakiya kasancewar shigar white tayi su Fatima sukayi black sai sukayi ta daukan ido,el Bahrain dake zaune da Yusrah yana hango tasleem yafara murmushi dan bakaramin kyau tamasa ba,dan gashinta twisting dinshi tayi tayo gefen wuyanta dashi,itama murmushin tayi masa takarasa gurin hajiyarsu el Bahrain ta tsuguna har kasa ta gaisheta,kamo hanunta tayi tana murmushi,taringa nunawa dangi ita,ahaka ta rike hanunta suka karasa gaban ango da Amarya,el Bahrain kua sai binsu yake da ido, gefen Yusrah takai tasleem ita kuma ta tsaya agefen el Bahrain aka fara musu hotuna,atsakiya suka sa hajiyarsu el Bahrain aka daukesu,aka dauki el Bahrain yasa su atsakiya,Fatima da mashida suma shiga sukayi akayi,akayi hotunan dasu ganin sunfara Jan hankalin mutane yasa hajiyarsu tasleem tarike hanun tasleem suka bar wajen mashida cokala wayarta tayi aselfie stick sukayi ta hotuna da ango da Amarya duk abinan da ake izzadeen yatafi anso cake din da Amarya da ango zasu yanka,mashida da Fatima bakaramin tafiya sukayi da imanin abokanan el Bahrain ba,dan bayan sungama hotuna suka fara bude gurin da rawa, inda aka sa wakar kujerar tsakar gida,Mashida sai juya mazaunai take,liki akafara musu sosai ciki harda ango da Amarya,da hajiyarsu el Bahrain video da hotuna akayi ta musu sabida bakaramin burge mutane sukayi ba dan rawa iri daya sukayi tayi,dakyar Dj yace abar Amarya da ango suma suzo su taka,watsewa akayi akabar Amarya da ango afilli dan suyi rawa,Daga el Bahrain har Yusrah kamewa sukayi kamar bishiyar da aka dasa,Yusrah ta sunkuyar dakai kamar zata shige kasa,rufuwa akayi akansu aka fara musu yayyafin kudi,tasleem ma ba abarta abaya ba,en Dari Dari taringa lika musu dangin el Bahrain dasuka San itace amaryar dazai aura, koma kanta sukayi suna mata liki,ahaka mc yakara bukatan amarya da ango su koma su zauna,yana San aminin ango yazo yabada tarihin ango,sunan izzadeen aka ringa kira akaji shiru,har ankoma wajen el Bahrain dan yabada sunan wani sai gashi ya shigo,wani nabiye dashi abaya da cake ahanunsa,lokacin su tasleem na zaune aguri daya, karba lasifikar yayi Daga hanun mc,yayi sallama,ya bude taro da addua,yafara bada tarihin ango,Rabin en Matan gurin jisukayi suna San izzadeen, inda Nabeela taringa fiili da iyayi wai ita ga mai saurayi,tasleem kua lumshe idanta tayi muryarsa na tuna mata moment din dasukayi,mashida ma hka,Fatima kua sai zabga masa harara take kamar idanta zai fado kasa,ahaka yagama bada tarihin ango yamusu fatan zaman lafiya,ya mikawa mc lasifakar,aka tafa mishi, aminiyar Amarya aka kira nabeela dan tabada tarihin Amarya itama tafito tana wani fari,ta makale murya dan kanaji kasan makala muryar tayi tana fara magana Fatima da mashida suka kyalkyale da dariya,sai da tasleem tamusu magana suka daina,ahaka ta bada tarihin Amarya ta koma tazauna...

šŸ‘„LšŸ…°LšŸ…°TšŸ…°šŸ™Š



*written by*
šŸ’…šŸ’… *sadnaf*šŸ’ž




Page 84


Ta bada tarihin Amarya takoma ta zauna,mc kuma kiran Amarya da ango yayi dan su taka kafin aci abinci,dakyar Yusrah ta yarda haka ma el Bahrain,tun kan sukaraso filin izz yafara musu liki har suka karasa filin,mahaifiyar izz ma data samu hallatar zua sai data mike tafara yiwa el Bahrain likin en goma goma,jin dadin abinda tayi ne yasa hajiyarsu el Bahrain yi mata liki,tasleem mikewa tayi dan itama tayi likin Fatima ta riko hanunta ta girgiza mata kai,komawa tayi ta zauna Fatima da mashida suka mike,Fatima adai dai kunan tasleem tayi mata magana,aunty kiyi zamanki,banaso dan iskan can yaganki,duk da nasan Abu ne mai wuya,ace har mu bar gurinan bai ganki ba bari muje mu lika sauran kudinan mu dawo,ta ja hanun Mashida suka nufi filin magana tayiwa mashida kasa kasa ta gyada kai tana murmushi suka karasa inda ake rawan,alokacin abokan ango da Amarya sun dukufa suna liki dan abin kamar gasa yakoma,izz dai yana tsakiya zaro kudi kawai yake Daga aljihunsa yana likawa,kutsa kai suka ringayi har suka samu nasarar tsaya agefen izz,mashida Daga hagu Fatima Daga dama,rawa suke sosai suna liki,Fatima harda kamo hanun Yusrah tana girgizawa ahankali ta matsa kusa da izz sosai ta take masa kafa da takalminta mai tsini ta ringa murza takalmin akafarsa,juyawa yayi dasauri ya kalleta,ganin Fatima Ce yasa gabansa faduwa tsoro ya ziyarceshi,haka ma mashida tayiwa daya kafar,runtse idonsa yayi dakarfi,dan wani mugun zafin da kafarsa ke masa,fatima sabida mugunta,harda dan tsallanta,wai nan duk rawa take,el Bahrain ganin izz ya tsaya cak,da hanunsa yasa yadago ya kalleshi,ganin ya runtse ido ne yasa yafahimci akwai matsala kallonsa yayi daga sama har kasa,yaga yana kokarin janye kafarsa daga takun dasu Fatima suka masa,kallonsu Fatima yayi ya girgiza musu kai,mashida tayi sauri ta janye kafarta,Fatima kua kafin ta janye,sai data kara murza kafar dakarfin tsiya tasa hannu ta bugi gabansa ta wayance tacigaba da rawa,Wanda tsabar zafin dayaji sai daya saki ihu,dan kidan dake tashi ne amma da bawanda baizai ji ihunsa ba,el Bahrain da a idonsa akayi komai,kallon mamaki yabi Fatima dashi,ita kuma takane mai ido daya,tacigaba da rawa,harda sunkuyawa haba wa ganin yanda ta sauya salon rawanta ne yasa aka koma kanta ana mata liki,ahankali izz yaja kafarsa yana dingishi yayi hanyar waje, hango shi da tasleem tayi taga yana dingishi yana cije lebe,yasa tagano akwai abinda Fatima tayi masa,ahaka yabar hall din yasamu wani guru yazauna yana kallon yanda Fatima ta fasa masa kafa da tsinin takalminta,gwara mashida ma bata ji mai rauni,yanda Fatima taji masa ba,Allah ya isa yaringa jawa fatima,tasleem kua tana ganin ya fita, tanufi filin, dan el Bahrain sun koma sun zauna,Mashida da Fatima kua sai zabga rawa suke, dan ansa musu wakar da suke masifar so,"shake body" janyo hanun Fatima tayi suka bar filin mashida tabi bayansu,wani guri tajata inda babu hayaniya sosai,ta daura fuska,mai kikayiwa izz?Aunty bangane mai nayiwa izz ba ni mai ruwana dashi ba kin magana ba,Fatima banasan irin wanan kinsan nasan halinki sarai,wlh ganinsa kawai danayi nasan akwai muguntar da kika masa,ke kuma mashida bai kamata kiringa biye mata ba kuna rashin hankali,kuma kunsan dangin el Bahrain gabadaya suna nan,duk abinda zamuyi idansu na kanmu,sabida haka tunda so kuke Ku zubar mana da mutunci,Ku wuce mu tafi gida,hakuri suka hau bata, dakyar tahakura taja musu warning, suka koma suka zauna, izz kua bayan ya daure babban yatsan kafarsa,da Fatima ta fasa masa, gwara inkoma ciki incewa Umma tazo mutafi tun kan azzalumar yarinya nan takara jimin wani raunin, yamike yakoma ciki

šŸ‘„LšŸ…°LšŸ…°TšŸ…°šŸ™Š


*written by*
šŸ’…šŸ’… *sadnaf*šŸ’ž




Page 85

Yana shiga sukayi kicibis da wani abokin el Bahrain mustapha,yace masa el Bahrain nakiransa,suka karasa wajenshi,ya zauna kusa da el Bahrain, friend zan kai Umma gida,naga dare yafarayi,kasan bakowa agida,ina mikata sai nadawo yafadi hakane dan kar el Bahrain yadagoshi,aa banyarda ba ko dan abinda Fatima tamaka dazu ne yasa kakeso katafi,ko daya wlh zan dawo ai,yanzu dai kaga lokacin cin abinci ne,tunda serve yourself ne,jeka zubawa umma ka kai mata intaci sai ka kaita gidan,bayasan yiwa el Bahrain musu shiyasa ya mike amma ba haka yaso ba,alokacin har wasu sun fara zubowa suna ci,layin maza daban na mata daban dan babu irin nauin abinci da babu kama Daga na turawa har na gargajiyar,komai anutse akeyi duk wanda ya zuba abincin sai yakoma ya zauna,hotuna su Fatima sukayi tayi da mashida,tasleem kuma ta kau da kanta gefe dan tana Daga ido, zata ga el Bahrain na kallonta,ita kuma jitayi ta takura,fatima hango izz datayi da plate ahanun yasa,tayi sauri ta ajiye wayar,ta wayance,aunty bari muje mu zubo abinci,ko zaki zo mutafi,haba Fatima kibari mutane su ragu mana,sai kuje,amma yanda akayi layinan zaku wani je karbar abinci sai kace mayunwata,kai aunty wlh nagidan biki yafi dadi nidai inbazaku je ba,kunga tafiyata,tafara tafiya,alokacin izz mutane biyu ne agabansa,dasauri Fatima tadauki plate taje tasamu wacce take kan layi ta roketa tabari ta zuba yunwa takeji sosai murmushi yarinyar tayi ta matsa mata ta zuba fried rice tayi gaba ta zuba pepper chicken,agefe tayi sauri taje gurin dazata dauko cokali,izz alokacin har ya zuba,yajuya ya tuna bai dauko cokali ba,kokarin juyawa yake yaje yadauko,Fatima da idanta nakansa,itama tayi sauri ta taho tana sunkuyar dakai,sai data daidaici tazo kusa dashi,shikuma kokarin kaucewa yake ta goce kafarta ta watsa mishi abincin ajikinsa asanadiyr faduwar datake kokarin yine yasa ta bugi plate din hanunsa ya fadi,bin jikinsa yayi da kallo,yaga yanda abincin ya bata masa kaya,cije lebe Fatima taringayi,tana rike kafarta,kai mahaukacin ina ne,dazaka zo ka bangajeni baka kallon gabanka ne,kallonta yake cikn takaicin abinda tamasa,hawayen na kokarin zubo mishi, mutane idansu yadawo Kansu,wasu suna ganin laifinshi ne,wasu suna ganin laifinta ne,y Fatima? Y are treating my like this,murmushi tayi u have not seeing anything what is best for you u better leave this place if not u can't bear to see what am going to do to you,duk maganar dasuke ahankali suke maganar,wucewa tayi ta gefensa,takarasa wajen su tasleem,duk abinda yafaru a idan el Bahrain da mashida,tasleem kua tunda ta sunkuyar dakanta bata dago ba shiyasa bata San asalin mai yafaru ba,aunty kinga dan akuyanan na zubo abinci ya barar min ko,yanzu nayi magana kice ni na tsokaneshi,kallon wajen da izz yake tsaya tayi,taga yarike Riga ahanunsa yana kallon fatima,karap suka hada ido da tasleem,dauke kanta tayi,izzadeen shikuma yasaki rigarsa yana kallon tasleem dan baitaba tunanin Tazo bikin ba,kokarin karasawa yake gurinta,Fatima ta galla masa harara,yayi sauri yayi waje, hakuri tasleem tabawa Fatima,tace sutashi su tafi Umma nakiransu awaya,sallama sukaje sukayi wa Amarya da ango,el Bahrain yanaso yayi mata magana amma bayaso Yusrah taji haushi dan yaga fitar izz bayaso yaje ya tare tasleem sai daya tuna suna tare da Fatima hankalinsa ya kwanta dan yasan Fatima bazata yarda tasleem ta kulla izz ba,ahaka suka musu sallama suka fita waje suka hau motar suka tafi gida,izz kua yana fita rigar jikinsa yacire ya canja amota,yana ta adduar Allah yabashi ikon kebewa da tasleem batare da Fatima tasani ba,yana kokarin fitowa Daga motar, yahango sun fito sun shiga mota sun tafi,fitowa yayi Daga motar yakoma ciki,ahaka aka gudanar da bikin cikin kwanciyar hankali..





washegari karfe 5 na yamma aka fara shirye shiryen kai Amarya,Fatima da mashida ma sai dasuka je wai suna so suje suga kwakwap,motocin daukan Amarya ne sukayi ta shigowa layin ciki kua harda izz,en mata ne suka fara fitowa suna duruwa amotocin,izz ganin su mashida sun fito Daga gidan ne yasa shi reverse dan bayaso su ganshi, dabara Ce tafado masa,yana ganin wanan shine lokacin daya kamata yaje gurin tasleem tunda basa tare da Fatima, shawarar daya yanke kenan yadauki hanyar gidansu tasleem....

šŸ‘„LšŸ…°LšŸ…°TšŸ…°šŸ™Š



*written by*
šŸ’…šŸ’… *sadnaf*šŸ’ž




_wanan page din naki ne aunty sis Allah ya kara girma da daukaka,dan hakika Wanda bai sanki ba shine zaiyi tunanin you are bad,but for me nasan wacece ke,you are such a nyx person after all that happened you still find a space in your hrt and forgive my fans,tanx for everything,I do respect you,Allah yaraya sultan_




Page 86

Yana isa kofar gidansu tasleem yasamu basiru azaune akan benci azaune,wajensa yakarasa ya mika masa hannu,ranka ya Dade kwana biyu najika shiru,bana ganinka inaso na tambayi aunty tasleem amma ina tsoro,bana nan ne nayi tafiya,Allah ya Sarki,dan Allah kacewa tasleem tazo inji dan makarantarsu,yallabai kaima kasan auranta zaayi kenan? ji yayi kirjinsa na bugun uku uku,wayancewa yayi dan bayaso basiru yagane,ee zua nayi namata Allah yasanya alheri,shiyasa ma nace kace dan makarantarsu sabida kar taki zua intaji nine,toh shikenan bari nagaya mata,yauwa ko kasan wa zata aura? E nasan shi,wani ne mai mutunci wlh amma na manta sunansa,dan sunan larabawa larabawa hake naji ana kiransa dashi,Allah Sarki,jeka to ka gaya mata,intace yasunan fa mai zance,kace mata Ali, yace hakane dan yataba jin Ali ya kirata akan assignment din dazasuyi,ta tambayeta tace dan ajinsu ne,tasleem lokacin ta gama girki kenan tanufi dakinsu taji sallamar basiru,ta amsa,ya akayi,Aunty tasleem dama wani dan makarantaku ne yake sallama dake,dan makarantarmu? Ee,ya sunan shi,Ali sunan shi,Ali ya akayi bai kirani awaya ba,kai shi dakin baki kace masa ina zua,daki tashiga tasako hijab dinta,ta fita waje dan umma batanan ta tafi siyo kayan gyaran jiki,dan tun da aka sa rana tafara gyara tasleem ciki da waje, shiyasa bata fiye zama ba,kullum tana hanyar kasuwa dan tunda tasan halin da tasleem take ciki tasha al washin gyara tasleem dan dama ta Iya,kawai batasan taringa yiwa mutane sabida abbansu tasleem bayaso,kanta kawai takeyiwa,sai yanzu datafara yiwa tasleem, izz kua bayan basiru yakaishi dakin baki,duba daya yadauka yabashi yaringa zuba mishi godiya,yana fita,yafara zarya apalon yana tunanin wa tasleem Zata aura, sallama tayi Daga bakin kofa yajuya dasauri ya amsa dasauri tare da karasawa wajen datake atsaye,allahuma ajirni fi musibati wa aklifnin khairin minha,kalu innalillahi wa innal ilahi rajiun," Izzadeen" mai yakawo ka gidanmu tace atsorace tana ja dabaya,zubewa yayi akasa pls tasleem ki tsaya ki saurareni,dan girman Allah badan halina,rufe ido tayi ta nuna kofar fita kafin na bude idona ka fita kabar gidan nan,dan iska mayaudari,sabida bakada cikakken hankali bakada kunya har zaka kuma Iya takawa kazo inda nake ,wlh izzadeen na tsaneka banasan in budi ido inganka arayuwata,kuma abinda kayimin bazan taba yafe maka,koda yafe makan dazanyi shine zai sa ka shiga aljana,I so much hate you,and insha Allah all the pain I went through because of you,wlh sai Allah ya jarrabceka ta silar yayanka,tunda tafara magana hawaye ke zubo mishi,tabbas Nasn nayi miki ba dai dai ba nasan dafarko yaudararki nayi niyyar yi,amma tun ba,aje koina ba Allah ya jarrabceni dasanki,tasleem pls find a space in your heart and forgive me give me one more chance pls,toshe kunanta tayi da hannu biyu, God forbid tace tana tofa masa yawu afuska,get out before I do something stupid, tace Tsawace, zai kara magana takuma cewa out dakarfi tana nuna mishi kofa,ganin bazata saurareshi ba yasa ya mike jiki asanyaye yazo ya wuce tagabanta yana kallonta,hankadashi tayi da karfinta har yana Neman faduwa,I love you tasleem and I will always do,cire takalmin kafarta tayi ta wurga masa sai akeyarsa,dagudu yafita gate yaje yatayar da motarsa ya tafi,tasleem kwalawa basiru kira taringayi rai abace,,yashigo aguje,yaushe kaima kafara munafinci,izzad een,ne Aliyu,wlh duk ranar daka karamin haka sai na saba ma,inya kuma zua kofar gidanan kasa yara su jefeshi,hakuri yaringa bata,tajuya afusace tashiga cikin gida dan wani mugun zafi zuciyarta kemata dan sai yanzu ma tafara jin zafin abunda izzadeen yamata
šŸ‘„LšŸ…°LšŸ…°TšŸ…°šŸ™Š


*written by*
šŸ’…šŸ’… *sadnaf*šŸ’ž



Page 88

Izz na barin gidansu tasleem,kiran el Bahrain yayi awaya ya tambayeshi yana ina,yace masa yana family house dinsu,yace mishi gashi nan zua ya kashe wayar, yawuce, family house dinsu el Bahrain, yana isa bangaren da mazan gidan suke,yayi yaje yasamu el Bahrain azaune da kofi ahanunsa yana shan milk shake,ango ango,kaine angon ai,kana daga nan mun kaima Amarya,kun kyauta ai,bismillah fa yace yana mika mishi kofin hanunsa alhamdulillah,abokina ina tayaka murna fa yau zaka shiga sahun manya,da asahun yara nake,emana kai da bakasan mace ba,yau zakasan sweet 16,kaga bansan iskanci ka dauka kowa irinka ne mtss yaja tsaki,Allah yabaka hakuri,baice masa komai ba yacigaba dashan milk shake dinsa,abokina kasan kua Daga gidansu tasleem nake,banje kai Amarya ba,duuum gabansa yafadi kofin hanunsa ya subuce Daga hanunsa,subhanallahi ta akayi ka saki kofin,subucewa yayi yace rai abace,inajinka dakaje ta fito,ta fito mana,wai ni nan dabara nayi danaga Mashida da Fatima,sunje kai amarya naje gidan dan nasamu mu sasanta amma kasan abun mamaki duk atunanina San da tasleem ta ke min bzai Iya sawa tamin rashin mutunci ba,amma abun mamaki bakaga Koran karen datamin ba,harda jifana da takalmi wlh saura kiris ta fasa min keya,el Bahrain kwashewa yayi da dariya, hmm dariya kake min ko,ai tamaka dasauki dabata cire ma hakori ba,yauwa friend inata so intambayeka ya akayi su tasleem suka je bikinka? waye ya gayyacesu?nine na gayyacesu, yaushe kuka San juna dahar suka shaku dakai haka,ai akwai alaka mai karfi atsakaninmu dasu,bangane ba,zaka gane sai nan gaba,ruko hanunsa izzadeen yayi abokina pls ka taimkeni nasan tasleem tana ganin mutuncinka pls kamata magana ta saurareni pls,wlh Allah ya jarrabceni dasanta,zame hanunsa yayi Daga rikon da izz ya mishi,in baka shawara izzadeen? Gyada masa kai yayi, ka hakura da tasleem Dan tanada mijin dazata aura,nasani danaje angayamin,amma ai ba a daura musu aure ba,inada chance, hmm to shikenan rabon kasha wuya ne,haba abokina yanzu bazaka Iya taimaka min ba,zancen kakeso,to shikenan ai bari inje gida inyi wanka,anjima zanzo muje siyan bakin Amarya,wa kayi zamanka wlh bana bukatar rakiyar kowa, kana nufin kai kadai zakaje? kwarai kua,haba kai kua,ni ai na gida ne,koma na dakine ni kadai zanje, uhmm basa bamba,anyi Amarya sai rawar kai ake,kanka akeji,gobe nazo naci girkin amarya ko shima kar nazo,hmm kai kasani fa ni bari inje inyi wanka kana batamin lokaci,ya tashi yashiga bandaki,yabar Izz atsaye shima hanyar waje yayi, yaja motarsa yatafi,el Bahrain na fitowa Daga wanka, shiryawa yayi cikin green din shadda yakafa hula kana ganinsa kaga ango,gidansu yaje,dan alhajinsu nata kiransa,yana zua palon alhaji yaje yasamu alhaji da abban Yusrah ,sai hajiya da Auntyn Yusrah, durkusawa yayi ya gaishesu,alhaji ne yafara masa nasiha daya rike Yusrah da amana,Yakuma zama adali,kar yasake yayi rashin adalci inya auri tasleem, haka dai dukansu suka mishi nasiha,suka Ce ya tashi yatafi,godiya ya musu, ya tashi yayi waje, sai dayaje bangarensa,yadauki abubuwansa masu mahimmanci irinsu litattafan adduoinsa,yafito ya nufi mota yadau hanyar sabuwar gandu inda ake siyar da Kazan amare,ya siyo guda hudu yace a ware masa guda biyu,yabiya kudin,yanufi hanyar super market, dake kusa da gurin yasiyo manya many an yoghurt da lemona masu sanyin gaske,yasa abayan seat din motar yadau hanyar Jan bulo,kiran tasleem yayi awaya yace gashi nan zua,tasleem kua tace yabari gobe yazo, yace bai yarda ba yau zaizo, ya katse wayar, tashi tayi dasauri tayi kwalliya tasaka wani Riga da skirt black and pink bakaramin kyau tayi ba,bata fesa turare ba dan tunda Umma tafara mata gyaran jiki,tadaina fesa turare dan jikinta kamshi yake na musamman,kiranta yayi yace mata yakaraso,ta mike takara kallon kanta amudubi,ta gyara mayafinta ta fita gurinsa,yana zaune yana yana yiwa Yusrah TeX akan gashi nan zua tashigo,amsa sallamar data masa yayi, bai dago ba sai daya yi sending,yadago,tasleem kua zuba mishi ido tayi taga yanda yayi masifar kyau,take taji wani masifaffen sanshi da kishinsa yakamata, yana dagowa murmushi yasakar mata,ya zuba mata ido,yaji wani Santa na ratsa shi...
šŸ‘„LšŸ…°LšŸ…°TšŸ…°šŸ™Š


*written by*
šŸ’…šŸ’… *sadnaf*šŸ’ž



Page 87

Bangaren Amarya Yusrah kua abbansu Yusrah sun mata fada sosai,tana kuka haka aka fito da ita aka dau hanyar jan bulo,Fatima da mashida sabida iyayi sai dasuka San yanda suka hau mota daya da ita,akofar gidan motocin sukayi ta parking en mata na fitowa suna shiga cikin katafaren gidan,waw friend gaskia gidanan yahadu,wlh habibaty Allah yasamu adanshinsu,ameen,wasu tsofaffi biyu ne suka ruko hanunta suka Ce tayi bismillah tashiga da kafar dama,video Fatima tafarayi tundaga harbar gidan dake zage da flowers har zua inda akayiwa Yusrah Jere,Palo biyu sai dakuna uku,kitchen da store aciki,kowane bedroom da toilet, haka ma palon,farkon palon brown and milk colour aka mishi fenti kayan dake cikin palon ma haka,gaskia bakaramin kudi alhajin el Bahrain ya kashe ba,karamin palon kua yafi kowane tsaruwa nan ne palon el Bahrain, komai naciki white and pink, ga manyan manyan frame mai dauke da ayyatul kursiyyu da aka rataye abango,palon shi bai kai na Yusrah girma ba,masha Allah komai na gidan ya tsaru ko ina dauke yake da console, dakinta aka wuce da ita tanata kuka,mashida da tasleem ba inda basu shiga ba,Fatima sai video take dan tanaso ta nunawa Umma su San shirin dazasuyi,dan gaskia kowace Ce tasamu kaya irin na Yusrah sai ta godewa Allah, ahaka,abokanan el Bahrain suka fara horn, dan kowace tafito badan ransu yaso ba,suka farawa fitowa dan basu gama kashe kwarkwatan idansu ba,mashida da Fatima kua kin tafiya sukayi sai da suka gama zagaye koina na gidan har saman dasuke kyautata zaton na tasleem ne sai dasuka shiga,tana video tana turawa tasleem ta watsapp dan gani take gwara tafara gani kafin takarasa gida,tabata labari, sai da ta kira tasleem awaya tace tahau watsapp ta turo mata sako,tasleem da tunda izz ya tafi takoma cikin daki ta kwanta ranta abace amma Fatima nakiranta tace tahau ta turo mata sako jikinta yafara rawa dan dama burinta taga irin kayan dazaayi wa Yusrah,tana bude videon tafara ware idanduna tana kallo data ga uban dukiyan da aka kashewa Yusrah,turkashi tace afilli tacigaba da kallo,sai da drivern gidansu mashida yazo suka sauko Daga sama sukaje suka samu Yusrah da still kuka take Daga ita sai kawayenta guda biyu,sallama suka mata taringa musu godiya muryarta dakyar take fita sabida kukan datasha,suna fita Nabeela kawar Yusrah tabi bayansu da harara,wai ni Yusrah a ina kika samo uwayen matan nan ne wlh haka kawai natsanesu sunfiye iyaye munafikai kawai sai video suke,banasan irin wanan Nabeela kikasan yanake dasu,Allah yabaki hakr Nabeela tace tacigaba da Dana wayarta,suna fita Fatima ta doka tsaki,kukan munafinci take fa,kai habibaty gaskia kinada zafin kishi duk Anty sama aunty kasa da Yusrah take cemana sai kince mata munafika,ke dalla can Dan kinganta haka slow poison Ce munsan irinsu,ahaka suka karasa cikn mota suka fara ajiye Fatima suka wuce gida jiki narawa Fatima tashiga dakinsu,ta tarar da Tasleem na kokarin tada sallah da gudu taje gabanta aunty kinga duniya ko,nagani sis, hmm bari nayi sallah dan bamuga tazama ina Umma take dan itama tasan shirin dazatayi ke dazakije gidan kishiya wlh kamata yayi ace kinfita komai,barni sis wlh jikina yayi sanyi,anya Abba zai Iya min irin kayan nan kua,tab Aunty wlh zamuyi Wanda yafi na Yusrah insha Allah, dan kinsan Umma tanaso taga yayanta sune on top,wlh aunty inta kama Umma tasiyar da filinta na gado nasan zata siyar dan ta fidaki kunya,ke nibanki bama insiyar da sarkata da zobe, wlh ahada asiya miki Abu, Allah Sarki sis,kina sona wlh amma karki damu duk kayan dana samu zan godewa Allah, Dan dama kafi wani,wani yafika,hakane kuma amma insha Allahu zama kifita,Allah yasa bari nayi alwala,tanufi bandaki, tasleem ta tayar da sallah..

šŸ‘„LšŸ…°LšŸ…°TšŸ…°šŸ™Š


*written by*
šŸ’…šŸ’… *sadnaf*šŸ’ž





Page 89


Ganin yanda ya tsura mata ido ne yasa ta sunkuyar dakai ta gaishe shi cikin sanyin murya,takowa yayi yazo ya zauna akasan carpet yana fuskantarta ya tallafa fuskarsa da hannu biyu yana kallonta,mayafinta taja ta rufe fuskarta,yau kuma rowar fuskarki zakimin heart beat,to bakaine kake ta kallona ba kamar baka sani ba,tace ashagwabe,murmushi yayi yana kallon kunshin hamunta,heart beat kinga yanda kikayi kyau kua,dan Allah gayamin sirrin,bawani kyau danayi zolayata kake,am serious,hmm duk kyauna ai ban kai aunty Yusrah ba,kyalkyalewa yayi da dariya wai aunty,hmm dan Allah ki bude fuskarki mana inganki sosai inji dadi,zame mayafin tayi Daga fuskarta ta sunkuyar dakai,murmushi yasakar mata dasuka hada ido,yabi tabon sallahnta da kallo,gaskia heart beat ina mutukar

Please Login or Register in order to submit comment