Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wlh mai zaayi da k'iba,aunty hope bakya fuskantan matsala Daga wajen low class girl din can da yaya kamal,bakida mutunci wlh ai kua high class girl Ce tunda tabawa el Bahrain abinda nagaza bashi,kinga ni ce low class girl, mtss ai nasan sai kindawo da abinda ya wuce wateva dai nasan gyaran da Umma da amabuwa suka miki bawasa bane,kema kin bashi abinda bata bashi ba,hmm abar zancen sis,ina sakon da Umma tace ki kawo min,lah kinsan kua har na manta,tab abunda ya kawoki kenan fa har kike mantawa,dauko Jakarta tayi tabude,ta dauko wani dan karamin kwalba ta mika mata,wanan turare ne tace kadan zaki Shafa ki kuma tabbata sai zaki kwantar zaki Shafa,sai wanan tace tana mika mata wani roban yoghurt,wanan kuma tace kisha rabi dasafe kin shanye sauran da yamma,wanan kuma tace ki tafasa kiyi tsarki dashi,tace tana mika mata wani bakin Leda,kai Umma ta kyauta wlh Allah ya saka mata,ki kai dakinki ki ajiye dan yanzu uwargida zata shigo tace min zata shigo inta shirya,mikewa tayi tanufi daki taje ta ajiye ta dawo,sis kishiga ki dafa koda indomie ne kafin nadora mana girki,auntyna karki damu,bana jin yinwa anjima inafara jin yunwa sai na dafa,yauwa Aunty na manta ban tambayeki ba,Amarya suhaima ta tare jiya ko,wacece haka,amaryar dan akuya mana,au wai dama sunanta kenan, ee mana,lailai ni ina nasani daxu dai naga yazo wajen kamal bansan me yazo yi ba,dariya Fateema ta kwashe dashi tace watakila karar suhaima yakawo wajen yaya kamal, bangane ba, hahahah ai auntyna dayake Allah ba azzalumin Sarki bane,izzadeen karuwa ya aura, bangane ba tasleem tace tana waro ido,ina ranar mother's night dinsu,aranar bayan munkoma gida nakira wanan kawar suhaima data bada biography dinta dan nakarbi lambarta nace mata style dinta ne yamin kyau taban number ta zan kirata tamin kwatancen gidansu shine fa nasamu contact dinta bayan nadawo gida nakirata nace mata tamin kwatancen gidansu suhaima inaso zan bata sako shine tamin kwatance,naje gidansu adaren,,tana ganina ta ganeni,tace dama tana nemana tanaso ta tambayeni akan izzadeen,nikua dama abinda yakaini kenan,nafada mata halinsa kaf,nace mata gwara tin wuri tafasa,amadadin hankalinta yatashi,murmushi tayi tace kar na damu duk kanwar ja Ce,anan tafada min komai akanta,kinsan murnar danayi kua aranar shege yana murna ya auri virgin Yar yarinya baisan karuwa ya aura ba, alhamdulullahi naji dadin wanan lamari,saura cuta dazata sa masa dan wlh sis kullum natuna izzadeen sai namasa allah ya isa,dai dai kenan auntyna nima ina tayaki tsine masa,sis izzadeen yamin tabon da bazan manta ba,shareshi auntyna,gashi yafara girbar abinda ya shuka saura ma yayan cikinsa,Yusrah ce tayi sallama tare da shigowa da plate ahanunta,amsawa sukayi da murmushi afuskarsu,sanunku da hira yauwa Yusrah tasleem tace,ajiye plate din tayi agaban Fateema, ga wanan kifara ci kafin nagama abinci,kai harda wahala angode, bari naje na karasa girki,kizauna mana muyi hira,inyaso sai muje mutayaki girkin tasleem tace,lah kubarshi wlh nakusa gamawa tajuya tafice Daga palon,bin bayanta sukayi da kallo,,fateema tace lebashanty ba gaba ba baya,bakida m wlh,ni dalla kici abinci,Allah yasa ta Iya girki,ta dau cokali ta debo indomien takai bakinta,yamutsa fuska tayi yanaji gishiri,Kai fateema da sharri kike dama anasa gishiri a indomie,to gashi dai tasa,hmm Allah yashiryeki..
πŸ‘„LπŸ…°LπŸ…°TπŸ…°πŸ™Š



*written by*
πŸ’…πŸ’… *sadnaf*πŸ’ž



Page 127


Ahaka suka cigaba da hirarsu,Yusrah ta kuma kawo musu abinci,suka nemi ta zauna suci tare,zama tayi suka ci abincin tare,suka cigaba da hira,karfe biyar na yamma el Bahrain yadawo alokacin Fateema tafara shirye shiryen tafiya,bangaren tasleem yanufa,yaje ya tarar da Yusrah ma abangaren,suna ta hira,sallama yamusu, gabadaya suka juyo suka amsa,sannu da zua suka mishi ya amsa,yasamu guri ya zauna,uwargida da Amarya kunyi kyau,yace yana kallonsu dan akujera daya suka zauna Fateema kuma atsaye da jaka,dayake sun kara wani wankan,Yusrah doguwar Riga tasa,tasleem kuma tasa atamfa Riga da skirt fateema Tamata dauri harda kwalliya,murmushi sukayi,basu Ce komai ba,idansa nakan tasleem sai magana yake mata da ido ta kau dakanta kamar bata san mai yakeyi ba, Fateema kua na lura dasu dadine yabi ya lullubeta,deserved one muje kihada min ruwan wanka dan nagaji,kanwata hope ba yanzu zaki tafi ba? Ai ganina dakayi atsaye tafiya zanyi su suka tsayar dani,ai sun kyauta,ki jirani inyi wanka dan muma zamu fita shopping sai mu saukeki agida, shikenan yaya kamal bari na jiraka,ta zauna yayi waje Yusrah tabi bayansa,suna fita,Fateema tadawo kusa da tasleem da saurinta,Aunty wane suna naji yaya kamal yakira Yusrah dashi yanzu,murmushi tasleem tayi tace deserved one,desverd one kuma yaushe tabar little din takoma deserved one,ranar datayi mishi gagarumin kyauta,tsaki Fateema tayi nasan bazai wuce kice virginity ba,amma wanan kamal din da iyayi yake dan maida dogon wuya,pillon kujera tasleem tadauka ta jefeta dashi, dan bakida m mijinawa ne mai dogon wuya,Allah Aunty. Yaban haushi ita kuma siririyar harda wani murmushi ance mata deserved one,ko nice sai na murmushi dan they deserved each oda,badan yana sona ba wlh bai dace da mace Irina ba tace hawaye na zubo mata,share hawayenki Aunty nima karki sani kuka,wlh babu macen data wuce irin haka yafaru da ita Aunty, kuma ki godewa Allah daya baki miji mai sanki tsakani da Allah, shawarar dazan baki Aunty akwai banbanci tsakaninki da Yusrah kinga kinfita wayewa kin fita shekaru,so kibi duk wani hanya daxaki bi kizama star azuciyarsa,duk da naga alama yafisanki,hmm da kikasani Fateema amma yanzu yafisan Yusrah bakiji sunan daya samata bane,wace ta cancanta fa,ko anan ma kinsan da banbanci,bazan boye miki ba Fateema cos banida sama dake, har yanzu ba abinda ya shiga tsakanina da kamal,what Fateema tace tana mikewa tsaye,zauna mana kiji,zama tayi tace bangane ba abinda ya shiga tsakaninku ba,ya akayi hakan yafaru,kwashe komai tayi tafadawa Fateema,haba Aunty ai duk laifinki ne wlh,wane irin tsoro kuma,no Wonder shiyasa banga yana rawar jiki akanki ba,kinsan kua bakaramin kudi umma takashe ba wajen gyaraki,dan ni nasan da el Bahrain ya kusanceki wlh my life zai sa miki,hmm Fateema kenan gyaran da aka min bashi zai sa nataba zama virgin ba,wlh duk wacce tayi nasarar kai budurcinta gidan mijnta ta godewa Allah, dan kowane namiji zai so ace shiya fara sanin matar daya aura,shiyasa wani sain sai ina zauna na tuna,Fateema ni nasan irin kuncin danake shiga ina tuna ba mijin aurena ne zai fara sanina ba,wani yarigashi,kinga Kua babu yanda ma zaayi kihada matsayina Dana Yusrah,duk san da kamal zai nuna min wlh ni nasan Yusrah tana da matsayi na musamman azuciyarsa,duk nagane aunty ya zakiyi haka Allah ya kaddara miki nidai ki ajiye tsoro agefe ki rungumi mijinki,in bahaka ba wlh infadawa Umma,sabida bakida hankali ba,nidai naji gud news dan Allah inaso ki kirani kicemin zaku tafi honeymoon, Allah yasa kiji gud news din Ameen, el Bahrain ne yashigo tare da yusrah,ya rike hanun Yusrah gam,da alama rike hanunta yyi da Iya karfinsa dan mutsu mutsu takeyi da hannu ta sunkuyar da Kai, el Bahrain ya canza shigarsa zua kananan kaya,haka ma Yusrah tasa wani atamfa riga da zani,heart beat sako mayafinki mu tafi,tashi tayi tayi hanyar dakinta ta dauko mayafi da jaka da takalmi,tadawo gurinsu,sis tashi mu tafi mikewa Fatima tayi tadau jakrta,suka jeru ita da tasleem taringa zubawa el Bahrain harara,azuciyarta kuma tace mai dogon wuya kawai harda wani rikewa wanan siririyar hannu,ahaka suka sauka sukayi wajen dayayi parking din mota yacika hanun Yusrah yafara kokarin bude motar, Ku shiga muje,dukansa kofar baya suka bude yajuyo ya kallesu. Nadai zama drivenku ko mutum daya yadawo gaba,dukansu ki sukayi,tasleem tace uwargida yakamata ta zauna agaba,Yusrah taki,cewa yayi tasleem ta dawo gaba tunda Yusrah taki,itama taki,Fateema kua tahau mintsininta data koma gaba,ganin suna bata mishi lokaci ne yasa yace Fateema tadawo gaba tunda bata masa lokaci sukeyi, gaba takoma ta zauna,Yaja motar suka bar harabar gidan ,adaidai lokacin da izzadeen shima yabude gate dan yafito da motarsa ya fita fuskarshi adaure dan fada sukayi da suhaima sosai daya debo mata kayanta ta tafi gidansu,tace ba inda zataje,dan inya dage sai ta tafi sai taje tayi mishi sharri agurin mahaifiyarsa tace mata sun dade suna watsewa awaje dan har ciki yamata sau biyu ta zubar,sabida haka zabi yarage nashi,bakin cikin abinda Tace ne yasa ya rufeta da duka,yamata lilis yace mata tayi ta zama aure zaiyi nan da kwana 6, kuma sai yamata rashin mtnci,yafice yabar mata dakin,yaje ya shirya Dan yafita ya nemi matar dazai aura dan bazai Iya zama da suhaima ba,dasauri Fateema ta leko dakanta ta window motar,ango kasha kamshi, wanan kamshi haka tace tana kyalkyalewa da dariya,el Bahrain ma kunshe dariyar daya taho masa yayi ganin yanda Izzadeen yadaure fuska,duk da baisan meyesa Fateema take tsokanarshi ba,wani mugun harara tasleem taringa jifanshi dashi, izzadeen kua sanin halin Fateema dayayi ne yasa ya maida gate din ya rufe, Fateema ta kwashe da dariya,el Bahrain ya juyo ya kalleta yace mata kin matsawa abokina fa tam..

[2/12, 4:20 PM] β€ͺ+234 703 962 5239‬: πŸ‘„LπŸ…°LπŸ…°TπŸ…°πŸ™Š


*written by*
πŸ’…πŸ’… *sadnaf*πŸ’ž





Page 128

Fateema dariya tasa tace dan nace mishi ango shine na matsa masa,kindai matsa masa gaskia gashi kinsa yafasa fita,Dama baiyi niyya fita ba,suna tafe suna hira har suka karaso kofar gidansu tasleem,tun kan yayi parking sosai tasleem ta fito Daga motar tayi cikin gidan da gudu,el Bahrain yasaki baki yana kallonta,kinganta ko sai taje taji ciwo,yaya kamal duk murnar ganin Umma ne fa, lailai kam,futowa sukayi Daga motar gabadaya,sukayi cikin gidan,tasleem nashiga palon tafara kwallawa Umma kira,Umma dake kitchen tafito dasaurinta,tasleem mai kikazo yi? Ina Fateema,rungumeta tayi nayi missing dinki Umma na,Fateema CE tashigo hade da sallama,el Bahrain da Yusrah suma sukayi sallama,aa tasleem Ashe duk tare kuke,sannunku dazua,tsugunawa sukayi suka gaisheta ta amsa da fara,arta tace Fateema ta dauko musu ruwa,suka CE ahanya suke dama Fateema suka kawo gida,daganan zasu tafi unguwa, Umma tace Allah Sarki kun kyauta ai,tinda gashi naga tasleem tace tana kalln tasleem data kwantar ajikinta,el Bahrain tambayar abbansu tasleem yayi, Umma tace bai dawo ba,toh Umma mu bari mu wuce,marairaicewa tasleem tayi tace dan Allah kabari anjima mu tafi,aa tasleem ina laifi ma yakawoku mun gaisa ai ya kyauta,Yusrah kua tunda ta zauna ta sunkuyar dakai,azuciyarta kuma tana cewa dama itama tanada uwa araye dataji dadi, dan yanda ummansu tasleem ke kula da yayanta ya mutukar burgeta,umma nasiha tayi musu gabadaya tace kamal yaringa kwatanta adalci,su tasleem kuma su bishi sau da kafa,godiya suka mata el Bahrain ya mike Yusrah itama ta mike,tasleem kuma tayi dakin Fateema dan tunda suka shigo tayi dakinta,Umma kuma tace musu tana zua,wani bakin Leda ta dauko tabawa Yusrah tace mata ba yawa,Yusrah ta tsuguna har kasa tayi godiya,wai har yanzu tasleem bata fito ba,ina zua bari nakirata tayi hanyar dakinsu Fateema,tana tura kofar tace ke wannan wane irin shashanci ne kin bar mutane atsaye suna jiranki,tacewa tasleem dake tsaye da Fateema suna magana ,Umma gani nan fitowa magana muke ne,zo ki fice ana jiranki,yauwa dazu na manta bangayawa Fateema tafada miki ba,kina jina,ee Umma kiringa dafa Lipton da kayan kamshi ki juye, sai ki fasa kwai aciki ki kada sosai ki shanye,inkina so ma zaki Iya sa madarar ruwa,hadine mai kyau sai zaki kwantar sai kisha yanda zai tsumu( matan aure ku rike wanan sirri tested and trustedπŸ‘) to Umma zan ringayi insha Allah, yauwa kifito Ku tafi,ta fice Daga dakin tasleem tabiyota abaya,Fateema itama ta fito dan ta rakasu,har bakin mota fateema ta rakasu,sai da suka tafi ta juya takoma ciki,suna barin gidansu tasleem,shoprite yakaisu,yace kowace ta dauki abinda takeso,shi kuma yayi gurin da ake siyar da sarka da kunne, ya siyi wani set din sarka da kune na daham Wanda kudinsa zai Kai dubu Dari da hamsin,sanan yadauko wani zobe mai girman gaske Wanda kudinsa zaiyi dubu Dari da ashirin ya biya kudin ya sa a aljihunsa yaje ya samesu atsaye duk sun zabi abinda suke so,suka je gun da ake biya,ya biya kudin,suka tafi,awani restaurant ya tsaya ya sauka yaje ya yo musu take away,suka koma gida,el Bahrain bangaren Yusrah yayi dan yayi sallah,tasleem itama tayi nata bangaren,bayan sunyi sallah,el Bahrain yace Yusrah takira tasleem suci abinci,tashi tayi tafi kiran tasleem,tana zua palon tayi sallama taji ba a amsa ba tayi hanyar dakinta,tura kofar tayi hade da sallama,tasleem ta juyo ta amsa,tana kan sallaya tana Jan carbi,Aunty yaya yace kizo muci abinci,OK gani nan zua,Yusrah ta juya takoma,tasleem sai data gama adduointa ta Shafa,ta cire hijabin jikinta tayi bangaren yusrah,apalon el Bahrain ta samesu azaune,Yusrah akasa azaune,el Bahrain akan kujera da romote ahanunsa yana canza tasha,sallama tyi suka amsa, itama tasamu guri ta xauna akasa,tasowa yayi ya zauna shima,Yusrah ta juye musu abincin awani katon faranti,ta zuba musu lemon,tace bismillahnku,an gaisheki uwargida,Amarya bismillah yace yana daukar cokali,murmushi tasleem tayi tadau cokalin sukafara cin abincin,el Bahrain yana ci yana kallonsu,aransa kuma yana godewa Allah daya bashi Yusrah da tasleem amatsayin mata,ahaka suka kammala cin abincin,tasleem tayi hamdala tamike,tace zataje ta kwantar, alokacin Yusrah tadauki farantin abincin tayi kitchen dan ta wanke,haba heart beat ki tsaya muyi hira mana,wlh bacci nakeji Dana zauna munyi hira,toh bari inje in rakaki,aa yi zamanka na yafe,tayi waje dasaurinta tyiwa Yusrah dake kitchen sai da safe tayi bangarenta,Yusrah nagama wanke wanken,itama dakinta tayi dan tayi wanka,tana fitowa Daga wanka ta tsaya agaban mudubi tana Shafa mai,el Bahrain jin dayayi Yusrah shiru shiru bata dawo ba yasa ya Mike yayi hanyar Dakinta,yana shiga,yaganta atsaye tana Shafa mai,gurinta yayi,ya rungumota ta baya,deserved one wanka kikayi ko kirani in miki,sunkuyar dakai tyi tana jin kunya,deserved one is high time daya kamata ki ajiye wanan kunyar taki dan mun Riga mun zama daya,yakai mata kiss awuyanta,I have a gift for you am coming, yacikata, yayi waje,tayi sauri tadauko wani doguwar rigar bacci tasa,el Bahrain yadawo da dan karamin kit ahanunsa,hanunta yaruko yakaita gaban mudubi ya tsaya Daga bayanta,yabude karamin kit din yadauko sarka da dan kunnen daya siyo dazu,yasa mata sarkar da dan kunne yarungumeta,yafara mata magana akunne,wanan shine kyautar Dana baki,amatsyin kyautar dakika bani jiya,Allah yabarmu tare deserved one, bari inje inyiwa heartbeat sai dasafe indawo,juyowa tayi ta rungumeshi,yayana nagode,Allah ya,shhhhh banason godiya cos you deserve it,am coming yayi waJe,Yusrah taringa daka tsalle tana Shafa sarka..
[2/12, 4:20 PM] β€ͺ+234 703 962 5239‬: πŸ‘„LπŸ…°LπŸ…°TπŸ…°

*written by*
πŸ’…πŸ’… *sadnaf*πŸ’ž





Page 129


Yana shiga dakin tasleem,itama adai dai lokacin tafito Daga wanka Daga ita sai dan karamin towel,tsayawa yayi abakin kofa,ya zuba mata ido yana kallonta tundaga sama har kasa,tasleem kua sunkuyar dakai tayi dan shima warning yamata yace ko aya yaganta,tadaina guduwa shi mijinta,ne,cinyoyinta ya ringa bi da kallo,dan ba laifi tasleem akwai diri,karasawa yayi inda take atsaye,yajanyota yafara kissing dinta dan bakaramin sha,awarta ne yakamashi ba,ganin yafita hayyacinsa sosai har yana kokarin kaita kan gado yasa ta tureshi da Iya karfinta tayi bandaki da gudu,heart beat tsaya in miki gudnyt kiss pls yace murya na rawa,aa Wanda kamin ma is OK,sweet drms,tace Daga bandakin kifito mana tafiya zanyi,aa sai da safe,Kk love you,yayi hanyar waje,tanajin alamar ya fita ta fito Daga bandakin taje ta kwantar akan gado,ta lumshe ido tanajin wani irin feelings,pillow tadauko ta rungume akirjinta,tana tunanin el Bahrain.



El Bahrain nabarin wajen tasleem dasauri yakoma dakin Yusrah dan wani irin sha,awa yakeji,Yusrah na tsaye agaban mudubin tana cire sarka da dan kunnen yfado dakin kamar anjefo shi,janyota yayi yafara kissing dinta yakaita kan gadon,aranar kwana yayi yana kashe arna πŸ˜‚πŸ˜‚yusrah kua ta daure duk da bataji zafi kamar jiya ba,sai wajen karfe uku na dare,ya cikata bacci mai dadi yayi awon gaba dasu,tasleem itama Daga wannan kwanciyar bacci barawo y saceta,kiraye kirayen sallah ne yatasheta Daga bacci,ta mike tare da sallati,taje tayi alwala,tadauko Quran tafara karantawa kafin lokaci yayi,el Bahrain da Yusrah kua bama su san ankira sallah ba baccinsu kawai suke,tasleem da tariga ta saba el Bahrain sai yazo yatasheta tyi sallah duk da baitaba zua ya tarar da ita tana baccin ba yasa tafara tunanin ko mai yahana yazo ya tasheta,tayi sallarta,tayi adduointa ta Mike,window dakin taje ta leka,taga ko makara yayi ya tafi massalaci taga ko alama ba a bude kofar ba,wani irin zafi taji zuciyarta namata wato sabida tsabar soyewa dasukayi basu tashi ba ,ganin inta biyewa zuciyarta ranta ne zai ta baci abanza yasa ta tsiri aiki,tana karatu nan take taji zuciyarta na sanyi





El Bahrain kua sai da suka kai karfe goma basu tashi ba,juyi el Bahrain yayi yaga hasken rana ya dalle masa ido,mikewa yayi dasaurinsa yana sallati,Yusrah Yusrah tashi mun makara,ya duro Daga kan gadon yayi dakinsa da gudu,Yusrah itama ta Mike tayi hanyar bandakinta dasaurinta,tayi wanka tayi alwala tazo tayi sallah,ko addua bata tsaya yi ba,tayi waje dasaurinta,kicibis sukayi sa el Bahrain akofa,yi sauri ki Dora mana breakfast mun makara bari naje mu gaisa da tasleem,ji sukayi ana kwankwasa kofa,suka juyo atare suka kalli juna,jeki Dora bari induba waye,yayi hanyar waje,yana budewa yaga tasleem atsaye taci kwalliya da wani Jan material tana dauke da faranti ahanunta,dan tana gama aikace aikacenta,taga har karfe 9 basu tashi ba,yasa tayi deciding ta Dora musu breakfast,tana gamawa tashiga wanka,tafito ta shirya ta zauna apalo,ganin shiru shiru ba alamar sun tashi,tasan kuma el Bahrain zaije office yasa ta dauko abincin ta sauko kasa,murmushi tasakarwa el Bahrain tace wanan bacci haka da kuke sha,ko Ka manta zakaje office ne,wani irin kunya ne Yakama el Bahrain, dan ana ganinsa ansan yasha harka,wlh kinga bamu,is OK tace ga breakfast nayo mana basai Yusrah tasha wahala ba,kayi sauri kaci ka tafi office, zuba mata ido yayi yace ngd heart beat,I love you, Yusrah fitowa tayi Daga kitchen dan ta duba da wa el Bahrain ke magana taga tasleem atsaye da faranti ahannu,dasaurinta tafara kokarin komawa dan kar tasleem taganta,dan ta cire hijbin jikinta,kanta kuma ajike yake, Yusrah tasleem takirata,ga breakfast nayo mana basai kinsha wahala ba,tace tana shigowa cikin palon,dasauri ta shiga kitchen tadauki hijabinta data rataya akan kofa,tasa tafito tana sunkuyar dakai,tasleem kua duk abnda takeyi karfin hali take,dan wani irin kishi kecinta,gaisheta Yusrah tayi ta amsa,tace tasauko su ci abincin,tabude kulollin tafara zuba abincin aplate,el Bahrain kua tunda ya zauna akan kujera yaringa bin tasleem da ido,santa nakara linkuwa azuciyarsa dan bakaramin burgeshi tayi ba,saukowa yayi yafara cin abincin,tasleem kua cin abincinta take anutse,Yusrah kuma sai juya cokali take,dan kunyar tasleem takeji gani take kamar tasan abinda yafaru,el Bahrain ne yafara mikewa,yayi hamdala,yakara godewa tasleem data taimakesu da yanzu yamakara zua office, yatafi dakinsa yaje yashirya ya dawo yasamesu azaune alokacin Yusrah ta kwashe kayn takai kitchen,to ni zan wuce office, akwai mai matsala girgiza kai sukayi,dan tasleem tana sane taki tafiya bangarenta bayan sunci abinci,dan tasan el Bahrain sai ya biyota ita kuma bataso yasan halin datake ciki,dan zata Iya kuka intaga Daga ita sai shi,to shikenan na tafi,Yusrah ta mike dan ta rakashi,heart beat ke bazaki rakani ba,adawo lafiya Allah ya kiyaye tace tana Daga zaune,murmushi yasakar mata,yajefeta da wani irin kallo yace Allah yasa,yafice Yusrah tabi shi abaya...
[2/13, 8:45 AM] β€ͺ+234 703 962 5239‬: πŸ‘„LπŸ…°LπŸ…°TπŸ…°πŸ™Š


*written by*
πŸ’…πŸ’… *sadnaf*πŸ’ž





Page 130

Bangaren izz kua Neman yarinyar dazai aura yake ido rufe,yakira abokanansa dayasan suna Hulda dashi yace su sama mishi yarinya daxai aura nan da en kwanaki,sukayi ta mamaki suna tambayarshi dalili yace badai ruwansu,su nema mishi,Indai ansamu su mishi magana ashirye yake,baya bukatar akawo masa komai,washegarin ranar daya Zane suhaima,dasafe yashirya yanaso ya fita,suhaima ta fito Daga dakinta dagudu tana amai,ko kallonta bai yiba yayi waje, yana kokarin tada motarsa,tafito tasameshi,dan Allah izzadeen Ka kaini asibiti banida lafiya,wlh tin jiya amai nake,wani mugun kallo yaringa mata in kaiki asibiti ke awa kenan,ki kira kwaratanki sukai ki asibiti dan zaman kanki kike ba nawa ba,dan Allah Ka taimaka min wlh har wani jiri nakeji tace rike kai,dalla mallama matsa Daga jikin motata kar na takaki,wuf ta bude kofar motar ta shige,wlh Ka kaini asibiti ko inje in kala maka sharri,agurin Abu,sakin baki yayi yana kallonta sunan mahaifiyata kike kira haka sabida bakida mutunci,to ba Abu sunanta ba,suhaima ki sauka Daga motar nan tun kafin naji miki ciwo,zancen kke so,tace tana kwantar da seat din motar,amma tinda nake ganin en iska bantaba ganin tantariya irinki ba, sauka in baki kudin mota kina bata min lokaci,wlh kai zaka kaini,ina matar mai kudi agani a adaidaita sahu,to dan ubanki inzanki asibitin ahaka zan kaiki ba mayafi,eee dan ubanka haka zanje asibitin,ba abunda yashafeka,wai suhaima dama haka kike kika ringa nuna min ke Salaha Ce,nafi haka ma,ayanda kazo min nazo ma,ganin inba kaita yayi ba haka zasuyi ta CeCe kuci yasa yaja motar suka tafi,yaringa zaginta yana tsine mata,itama taringa ramawa,suna isa bakin asibitin,tacire mukullin motar,tafita dga motar,kallon mamaki yabita dashi,shima yafito Daga motar,bni mukullin motarta tunda nakawoki,sai naga likita kai maidani gida sai nabaka,wai meyesa ke dabba Ce kince nakawoki nakawoki yanzu ma nakawoki sai najira kinga likita namaidaki gida,gaka babban dabba Wanda bai san darajar matarsa ba,ganin inya biye mata haka zasu cigaba ta Tara musu jama,a yasa,ya nufi cikin asibitin,tabishi abaya,kati suka yanka,suka dan suga likita,wata nurse takaiwa likitan katinsu,tace su shiga,izzadeen ne agaba,suhaima abaya,zama sukayi izzadeen yamikawa likitan hannu suka gaisa yace matarsa Ce ba lafiya yakawota adubata,likitan kallon suhaima yayi yace mai ke damunta,ta mishi bayanin abinda takeji,daukar wayar dake kan table yayi ykira yace wata nurse tazo, minti biyu da ajiye wayar,nurse din tashigo,pls jeki mata gwajin fitsari ki kawo min result din,gaban suhaima ne yafadi,dataji abinda likita yace,sai yanzu ta tuna bataga prd dinta ba last month,mikewa tayi tabi bayan nurse din jikinta asanyaye,izzadeen kua sai zuba mata harara yake, nurse din nakarbar fitsarinta tace takoma office din likitan ta zauna,kamar ta Ce mata bazata koma ba,sai taga result din,sai tafasa takoma office din ta zauna tayi tagumi tana tinanin Allah yasa ba ciki bane, izzadeen sai Dane Dane yake awaya yana cika yana batsewa,nurse din Ce ta shigo ta ajiye,wani farin takarda agaban likitan,ta juya ta fita, likitan yadauki takardar ya duba,yadago yana murmushi, suhaima gabanta yahau faduwa,izzadeen kua bai ma san mai likitan yakeyi ba dan Dane danensa yake,maigida inatayaka murna matarka tana dauke da juna biyu,wani irin cili izzadeen yayi da wayarsa ya mike yace ju me, suhaima kuwa zare ido tafarayi itama ta mike,juna biyu kuma likita,mamakine ya bayyana afuskar likitan kwarai kua juna biyu ga result din ma positive,kutumar uba suhaima dama da ciki kika zo gidana,bangane ba,ba cikinka bane dazaka Ce min da ciki nazo gidanka,inna lillahi wa inna ilahi rajiun suhaima ajiya na miki ciki, sai kayi kuma ciki dai naka ne,amma bakaramar Tsinaniya bace ke,wlh bazaki koma gidana ba,kitafi gidanku na sakeki saki biyu,shegiya karuwa,kijeki nemi Wanda ya miki ciki tun wuri,Kaine kamin ciki kuma wlh zakayi mamakin abinda xanyi ma,afusace izzadeen yabar office din,likita kua tinda suka fara musayar yawu ya saki baki yana kallonsu,ganin izzadeen yabar office din yasa yace baiwar Allah ya akayi haka tafaru,bansani ba munafiki kawai duk bakai kajanyo ba,ta zuba mishi harara,tafice,girgiza kai likitan yayi yace Allah ya kyauta,suhaima nabarin asibitin gidansu izzadeen ta tafi tundaga bakin kofa, ta Dora hannu aka taringa zunduma ihu tana tashiga uku ta lalace,ummansu izzadeen dagudu tafito Daga bandaki,tana gyara daurin zaninta,innalillahi wa inna ilahi rajiun suhaima lafiya? Mai yafaru? kwanciya suhaima tayi akasa taringa burgima,nashiga uku Umma izzadeen ya sakeni,dafe kirji Umma tayi mai kikace,Umma yasakeni,innalillahi wa inna ilahirajiun mai kika masa ya sakeki,Umma dan munje asibiti ance inada ciki shine yasakeni,suhaima kina da hankali kua,ciki fa kikace ba shekaran jiya kika tare ba a ina kika samo cikin? fashewa takarayi da kuka,tafara shimfidawa Umma karya tace izzadeen ne ya yaudareta

Please Login or Register in order to submit comment