Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har ta haihu ya sallameta ta kara gaba,watarana el Bahrain na zaune dasu Yusrah apalon tasleem basu Dade da cin abinci ba Yusrah ta mike kafarta tasleem na Dana mata sabida kumbarar dayayi dan cikinta ya tsufa haihuwa yau ko gobe, tun da yamma tafara jin ciwon baya da Mara kadan kadan ta daure bata fada kowa ba dan tun a asibiti aka gaya mata alamomin haihuwa,matsa mata kafa tasleem tacigaba dayi suna hira da el Bahrain, Yusrah kua ta fara cije lebe,dan jitayi bayanta kamar zai balle,mararta ne yamurda mata tasaki sallati,el Bahrain ya mike ba shiri,lafiya Yusrah mai yafaru," yaya marata bayana wayyo Allah na yaya zan mutu, gigicewa yayi,tasleem ita kuma tafara tofa mata addua,tace el Bahrain yadagata sukai ta asibiti,riketa sukayi suka sauka kasa yaje ya bude mota dasauri yadawo ya riketa suka kaita mota,tasleem tayi Sauri tayi dakin Yusrah taje ta dauko akwatin da suka hada kayan haihuwa tadawo dasauri cikin motar,el Bahrain yaja motar a 360 suka nufi asibiti,tafiyar mintina ne yakawo su asibitin inda already nurses biyu na waje suna jiran karasowarsu dan el Bahrain yamusu waya, Yusrah sallati kawai take tana kiran sunayen Allah,tasleem kua sabida tausayi kuka taringayi,ahaka nurses suka shiga da Yusrah dakin haihuwa,el Bahrain yaji kamar ya bisu,zirga zirga el Bahrain yaringayi aharabar asibtin inda tasleem kuma taringa zuba adduoin Allah ya sauke Yusrah lafiya,atakaice aranar ba Yusrah Ce ta haihu ba sai da asuba inda ta haifi santalellen da namiji mai kama da el Bahrain, fadar murnar da el Bahrain yayi dashi da tasleem bata bakine dan har rawa tasleem taringayi,el Bahrain yaringa kiran en uwa da abokanan arziki, yana fada musu, kafin gari yawaye danginsu el Bahrain suncika asibitin,karfe 8 nasafe likita ya sallami Yusrah suka dungunzuma suka dawo gida,tasleem kua aranar tasha aiki ta gode Allah dan dangin el Bahrain cika gidan sukayi ciki kua harda su Aunty luba,inda dadi yabi yakashe luba,dan dama burinta Yusrah ta haifi da namiji,dan ko abanza tasan yanzu Yusrah Ce gida washegarin da Yusrah ta haihu,su Umma suka zo da Fateema,sukayiwa Yusrah barka inda suka zo da akwati cike da kayan baby da atamfa wajen kala hudu,da dubu goma inji abbansu,inda dadi yabi ya ishi Yusrah ta durkusa akasa tana zuba godiya,Fateema kua tunda ta rike bbyn tahana kowa, dan jitayi inama bbyn tasleem ne,dan san bbyn yashiga ranta ahaka suka wunan musu suka tafi gida,bangaren el Bahrain kua kudi yakashe sosai na hidimar suna inda yayiwa tasleem da Yusrah dinki kusan kala takwas,izzadeen ma ba abarshi abaya ba ya taka rawar gani sosai, dan sai daya siyi katon rago, musamman yace ayankawa mai jego banda uban kaya daya kawo wa Yusrah da babynta,ranar suna shagali akayi sosai inda aka sawa Bby sunan abban el Bahrain, aka ringa kiransa da daddy,Yusrah tasha kyau ta godewa Allah, inda tasleem itama ta zuba ado kamar Amarya, dangin el Bahrain suka runga mata adduar Allah yabata cikin itama dan bakaramin kirkinta suke gani ba lura dasukayi da irin hidimar datakeyi,mai jego kam fadar kyautatukan data samu bata bakine dan sai data rasa inda zata ajiyesu ahaka akayi taron suna cikin nishadi kowa ya watse ya nufi gida da Niki Nikin kayan da tasleem taraba, washegarin suna Aunty luba kiran el Bahrain tayi gefe tace mishi zasu tafi da Yusrah gida dan acan[truncated by WhatsApp]
πŸ‘„LπŸ…°LπŸ…°TπŸ…°πŸ™Š



*written by*
πŸ’…πŸ’… *sadnaf*πŸ’ž





Page 160

Cikin Yusrah Nada wata hudu Mufeeda ta haifi sankaceciyar yarta mai kama da izzadeen, inda akayi shagalgula sosai dan el Bahrain ma sai dayayi nashi taron agidansa,sunan mahaifiyar izzadeen aka samata akaringa kiranta da ameera,izzadeen tunda aka haifi ameera yadora mata san duniya dan ko kasuwa yaje sai yayita kiran Mufeeda yana tambayar ameera,bangaren suhaima kua tun ranar data haihu yabata takarda saki,ta tafi gidansu da da, inda yayenta suka nemi tayi musu bayanin abinda tayi aka saketa tace kishiyarta Ce tayi asiri aka saketa,yayyenta tausaya mata sukayi suka Ce Allah yasaka mata,anan suka Ce tunda abin nshi yazo da wulakanci ta maida mishi dansa,bijirewa tayi tace bata yarda ita zata rike danta,kyalleta sukayi suka Ce itace da wahala,bayan kwana biyun da komawarta gida,kiran alhaji tanimu tayi tace yazo su maganar yanda zasuyi aure,Daga nan ta samu ta raini danta,murna ne yabi ya ishi alhaji tanimu,yace mata yana nan zua,wani ikon Allah ahanyarsa na zua gurin suhaima, yayi hatsari atake Allah ya amshi ransa,suhaima dataji mutuwar tanimu hankalinta bakaramin tashi yayi ba,dan sai data kai ta kawo bata Iya bacci kwata kwata bata da aikin daya wuce kuka sai ayanzu taji tafara nadamar abinda take aikatawa ,ranar sadakar ukun alhaji tanimu dan data Haifa ma yace ga garinku nan,fadar tashin hankalin da suhaima ta tsinci kanta aciki bazai fadu ba,dan sai data kai ta kawo ko magana bata Iya yi,inda yayyenta sukaje suka samu izzadeen sukace masa yazo yadauki dansa ya binne dan Allah ya mishi rasuwa,murmushi yayi dayaji abinda yakawosu,anan ya kwashe komai ya gaya musu da dalilin dayasa ya saketa,hankalin yayyenta bakaramin tashi yayi ba dasuka ji gaskiyar lamari,murtala dayafi kowa bakin cikin abinda tayi, azuciye yakoma gida ya rufe suhaima da duka,inda abun yazo da tsautsayi belt din dayake dukanta dashi yasamu idanta,idanta yafara tsiyayar jini da ruwa,ataikaice sai da suhaima tarasa ido daya,inda bata da aikin daya wuce kuka da nadamar abinda tayi,dan acikin kankanin lokaci komai ya gagareta duk abinda take takama dashi babu abinda zataci ma wahala take mata,dn yayyenta ko inda take basa yi,inda duniya tayi mata zafi,anan tasan duniya ba mattabata bace,dan abinda take takama dashi duka babu,ahaka tacigaba da squatting agidan yayyen nata inda take fuskantar matsala na tashin hankali dan sai data zama er aiki awajen matan yayyenta karfi da yaji,
wanan kenan






Tasleem kua addua ta dukufa dayi tana rokon Allah yabata haihuwa,inda ta rike daddy kamar dan cikinta dan in basaninsu kayi ba tunani zakayi danta ne inda Yusrah ita kuma tacigaba da kula da cikinta har ya tsufa ya isa haihuwa,watarana da asuba takuma haifo danta namiji mai kama da ita, fadar murnar da familynsu el Bahrain sukayi bata bakine,dan mahaifin el Bahrain ne yadau nauyin komai da komai,ranar suna yaro yaci sunan abban Yusrah aka ringa kiransa da shuriem, wanan karin Yusrah bata je gida wanka ba gwago yalwa Ce tazo taringa kula da ita sunayin arbain ta tafi,tasleem kua rashin samun cikinta bakaramin damuwa yasata ba,dan duk inda takai da boye damuwarta sai da el Bahrain yagane,hakuri yaringa bata yace tacigaba da gayawa Allah,yana sane da ita,inda Umma itama kwantar mata da hankali taringayi tace mata watakila itama gado tayi dan sai data shekara 6 kafin tasamu cikinta da wanan maganar hankalin tasleem yakara kwanciya inda taringa tunanin itama in Allah yayi tana da rabo zata ga danta aduniya,atakaice sai da tasleem ta shekara biyar da aure ko batan wata bata tabayi ba,inda hakan yafara damun el Bahrain sosai wataran yana kwance da tasleem ya Mike ya zauna yace ta tashi ta zauna yanasan yi mata wata tambaya,mikewa tayi ta zuba mishi ido tana jiran taji wane irin tambaya zai mata haka da har sai ya Mike yazauna" tasleem" gabanta ne yafadi dataji ya kirata da sunanta dan tasan bakaramin Abu kesawa yakira sunanta ba,"naam tace tana sunkuyar dakai, "dan Allah tambaya zanyi miki karki boye min ki fada min gaskia kinji,gyada masa kai tayi kanta asunkuye,dan har hawaye yafara taruwa a idanta,lokacin dakike tare da izzadeen yana baki kwayoyyin hana ddaukar cikine? Kirjinta ne yahau dukan uku uku tarasa amsar dazata bashi hawaye yahau zubo mata
πŸ‘„LπŸ…°LπŸ…°TπŸ…°πŸ™Š



*written by*
πŸ’…πŸ’… *sadnaf*πŸ’ž





Page 161

Look tasleem ba kuka nace kiymin ba tambaya kawai na miki kibani amsa,dan akwai abinda nakesan sani ne,girgiza kai tayi zuciyarta na mata daci dan idan da akwai abinda ta tsana ayanzu bai wuce atuna mata da past dinta ba,kiyi hakuri da tambayar Dana miki heart beat,inaso nasan ko izzadeen yana baki kwayoyyin hana daukar ciki ne alokacin,sabida musan yanda zamuyi ko asibiti zamuje dan rashin samun cikin ki,bakaramin damuna yafara yi ba,dan agaskiya bnji dadin abinda Aunty Lubabatu ta miki ranan ba,(dayake bayan Yusrah ta haifi shuriem Aunty luba zua tayi gidan tace zata karbi daddy ya zauna agurinta,el Bahrain yabata hakuri yace mata daddy yana wajen tasleem inya karbeshi ayanzu bai kyautawa tasleem ba dan tana balain ji da daddy, Aunty luba masifa tafarayi taringa banbami tace wanan ba hujja bace ita tasleem ta haifi nata mana,akan me zata rike daddy,babu abinda ta sani kamar taci tayi kashi,dan haka sai ta tafi da daddy,aranar gori da wulakanci ba irin Wanda luba batayiwa tasleem ba,sai da el Bahrain yakira hajiya yafada mata,ita kuma takira luba ta rufeta da fada,aranar kaca kaca luba sukayi da el Bahrain kafin ta bar gidan) shiyasa kika ga na damu,amma abinda zaayi zamuje asibiti gobe adubaki agani kinji everlasting one pls ki share hawayenki yace yajanyota ya rungumeta,aranar tasleem baccin dabatayi ba kenan,dan sun rayya Daren,el Bahrain bacci ya daukeshi tsarkaka jikinta tayi tayi alwala,tazo tayi ta nafilfili tana kuka tana rokon Allah daya bata haihuwa,washegari el Bahrain yakaita asibiti aka dubata aka Ce kalau take haihuwar Ce dai batazo ba,da bayanin likita hankalin el Bahrain ya kwantar, tasleem kuma tacigaba da addua ba dare ba rana



Allah samiu dua,

Allah maji rokon bawansa



Bayan wata biyu da zuwansu tasleem asibiti,tasleem tasamu ciki,kuma cikin yazo mata da sauki ba laulayi dan ita kanta batasan tana da ciki ba sai data ga tasamu wata biyu bata ga period dinta ba sanan tasan tana da ciki,batayi gaggawan fadawa kowa ba har sai da ciknta yacika wata hudu tafadawa el Bahrain kin yarda el Bahrain yayi har sai daya kaita asibiti aka tabbatar masa da tana dauke da ciki har na wata hudu,atake agaban likita el Bahrain yayi sujadar shukur yana godewa Allah, tasleem kuma hawayen farinciki suka hau zubo mata dan ganin yanda el Bahrain ya ringa farinciki,el Bahrain kua bayan sun koma gida sanar da Yusrah yayi, Yusrah tasaki kabara ta rungume tasleem tana murna,el Bahrain kua tsabar farinciki hana tasleem yayi taringa kowa na aiki yasoma en aiki har guda biyu yace su ringa tayata aiki, tasleem bijirewa tayi tace zata Iya aikinta dakyar tasamu el Bahrain ya yarda, zata ringa girki,tasleem er gata tazama akowane bangare dan Umma kullum sai ta yo mata abun kwadayi,haka ma agidansu el Bahrain dan suma bakaramin murna sukayi ba da samun cikin tasleem, Fateema kua maida gidan tayi gidan zuwanta,akullum sai tasamu abun baby ta siya ta ajiye,akwana atashi babu wuya,watan haihuwa tasleem Yakama inda tasleem ta dage da addua Allah yasauketa lafiya inda kowane bangare keta shiri,dan ko. Iya gidansu tasleem shirin dasuke ba kadan bane,dan Daga kan tasleem zasu fara samun jika,inda uban gayyan tinda akayiwa tasleem scanning akace mace zata Haifa yarasa inda zai tsoma ransa dan dadi dan ya Dade yana adduar Allah yabashi ya mace dan arayuwarsa yana balain san ya mace dan aganinsa sunfi tausayi da jinkan iyaye,maza kua dama kasan mata Ka haifawa su


Atakaice dai tasleem ranar wata jumaa,ta haifi sankacecciyar yarta mai kama da ita amma ta dauko hasken el Bahrain,fadar murnar da el Bahrain yayi ba,a magana dan hana kowa daukar er yayi ya riketa ahanunsa yana kallonta,dan shi ganin kamaninta yake da tasleem,tururuwa aka ringa zua anayiwa tasleem barka ciki kua harda izzadeen da Mufeeda,inda suka zo da ameera alokacin tana da shekara uku da watani, takara kyau kamaninta da izzadeen yafito sosai,gayu suka mata sosai gata da gashi,mika mata hannu,tasleem tayi takuwa tafi gurinta tafara mata wasa,ko Daga kanta batayi ta kalli inda izzadeen suke atsaye ba shida Mufeeda, har suka gama ga gaisawa da mutanen dakin,el Bahrain dke tsaye da jinjira ahanunsa,mikawa izzadeen bbyn yayi, izzadeen yazuba mata ido yana kallonta, kiss yamata agoshi yamata addua akunne,ya dago ya kalli el Bahrain, abokina dan Allah kabarmin wanan er inhadata da ameera,dariya yayi yace akan me zan bar maka ita,sabida ina ganinta naji ina balain Santa tamkar ni na haifeta,atake el Bahrain yaji ransa yafara baci,yafara tunanin sabida kamanin da bbyn keyi da tasleem ne yasa yace yana santa, kwace babyn yayi Daga hanunsa,yace bazan Iya baka ita ba,murmushi izzadeen yayi dan yagano kishi el Bahrain yake, ganin yq cukule yaki sakin fuskarsa ne yasa izzadeen yace zasu tafi,el Bahrain yace to su wuce yarakasu dan shima ya kagu su tafin dan haka kawai yakejin bai yarda da izzadeen ba.




Taro yayi taro ran suna baby taci sunan mahaifiyar el Bahrain, inda zaa ringa kiranta da ammi,dan el Bahrain ne yazabi sunan dkansa,ansha shagali an cashe an watseπŸ˜‚ dan inace zan zayyano muku shagalin da akayi sai wayata sai ta dauke,kowane bangare dai sai da suka taka rawar gani,dan ko Iya abinda tasleem tasamu A gidansu bazai lissafu ba,inda izzadeen shima ya kashe makudan kudi yayiwa tasleem siyyaya na tashin hankali,dan sai daya cika akwati hudu da kaya biyu na mai jego biyu na baby ya Dora dubu hamsin akai,ganin irin kayan daya kawo ne yasa el Bahrain ya kwashe kayan yakai boys qtr ya kulle,aunty luba kua tunda tazo taga Bby bata koma ba har akayi suna,sai dai aike datayi da kayan barka.
πŸ‘„LπŸ…°LπŸ…°TπŸ…°πŸ™Š



*written by*
πŸ’…πŸ’… *sadnaf*πŸ’ž





Page 162

Bayan kwana uku da akayi suna,Aunty inna zua gidan tayi taroki el Bahrain zasu tafi da tasleem intayi arbain ta dawo,el Bahrain hankalinsa bakaramin tashi yayi ba,dan tinda sukayi aure da tasleem bata taba zua kwana awani gurin ba,bakuma yajin zai Iya jure rashinta akusa dashi,gashi tinda ta haifi ammi agurinsa take kwana,sai dai in tafarka zata sha nono ya kaita tasha yadawo da ita,rokon Aunty inna yahau yi yace su barta anan tayi wankanta,atakaice dakyar el Bahrain ya hakura yabar Aunty inna ta tafi da tasleem kamar yayi kuka,maraya yazama karfi da yaji,duk da yana zua yana ganinsu dan wani sain inya ga ayyuka sun ragu a office gidansu tasleem yake zua ya wuni,yana wasa da ammi,dan su aunty inna basu fiye barin tasleem tana zua gurinsa ba inya zo sai dai su kai mishi ammi,dan sunce mishi kamar Al,adarsu Ce basa bari miji yaga matarsa intazo gida wanka sai dai jefi jefi hka,inda hakan na damun el Bahrain sosai kawai bashida yanda zaayi ne dan bakaramin missing din tasleem yake ba,duk da Yusrah na Iya kokarinta wajen ganin tana debe shi kewa,hakan ne ma yasa abun yazo mishi da sauki,gyara sosai su Umma suka ringayiwa tasleem da gyaran jiki,inda tasleem ta canza kamar ba wacce ta haihu ba,dan ko irin lukucewa nan da mata kanyi inasun haihu tasleem batayi ba,inda baby ammi,taringa girma kamaninta Dana tasleem nafitowa,amma tafi tasleem kyau dan ta dauko gashin gidansu el Bahrain da haskensu,hakane yasa el Bahrain yaji yafi san ammi akansu daddy,dan nafarko kasancewarta mace gata kuma tana kama da heartbeat dinsa,ahaka tasleem tayi kwana 39 agidansu,washegarin ranar datayi arbain el Bahrain yazo dasassafe daukansu,dan aransa ji yake kamar irin lokacin dazai aureta yanda ya matsu ta tare hakan ne ma ayanzu,tsokanarsa su umma suka ringayi dasuka ga yanda yazo dasassafe,dan Ce mishi sukayi ai dole sai tayi kwana arbain da daya zai zo ya dauketa,ganin yana Neman yasa musu kuka ne yasa suka bashi tasleem suka tafi,zumudi da rawar kafa el Bahrain yaringayi akan tasleem, dan sabida kar ma wani Abu yahanshi jin dadi,yasa da safe dazai fito Yusrah yafara kaiwa gida yace tayi kwana biyu dan dama tadade tana rokonsa akan tana san zua gida ta kwana,inda shikuma ya shirga mata karya yace tafiya zaiyi sai yadawo zai dauko tasleem,aranar soyewar dasu kayi sai daya tuna musu da first night dinsu,atakaice dai kafin ammi tayi shekara biyu sai da tasleem ta kara haifo twins inda bayan kwana uku datayi da haihuwa Yusrah itama takuma haifo da namiji,readers basai na baku labari irin tsalle da murnar da el Bahrain yayi ba,kai dama dangi gabaki daya,asanadiyar haifar twins da tasleem tayi aunty luba taji tafara san tasleem, dan arayuwarta tana balain san twins,rana daya akayi taron suna,inda akayi shagalin suna a marhaba event centre, twins hassan da usaini, aka sa musu inda aka sawa dan wajen Yusrah taufeeq,kyautatukan dasuka samu su biyun bazai fadu ba,dan tasleem sai da baffa ya bata kyautar mota,adaren da akayi suna Mufeeda itama ta haifi twins duk mata,izzadeen jkinsa ne yayi sanyi dayaga mata Mufeeda ta haifo mata dan har ga Allah yaso ace maza ne dan yana tsoron wanan zamanin da muka tsinci kanmu aciki,aranar kuma suhaima taje nemansa,inda tana ganin ya fito tayi sauri ta zube akasa tafashe da kuka, tana Neman yafiyar izzadeen,jikin izzadeen ne yabi yayi dayaga yanda suhaima ta koma,jikinsa bai gama sanyi ba sai data bashi labarin rayuwarta, hankalin izzadeen bakaramin tashi yayi ba,yaji hawaye na zubo mishi, dan shi kansa ya tuna,dan baisan tsawon lokacin da yakai yana sabar Allah ba,zubewa yayi shima yaringa istigifari yana Neman yafiyar Allah, azuciyarsa kuma yana tausayawa yayansa dan yasan shima watakila wani ya. LπŸ…°LπŸ…°TπŸ…° masa yaya,dan Allah kadai ne yasan mata nawa ya LπŸ…°LπŸ…°TπŸ…° ahaka yaci kukansa ya koshi da suhaima ta tashi tafiya yabata kyauntan dubu dari tazube akasa tayi ta godiya,( rayuwa kenan abinda kafi karfinsa ada kanaji kana gani zaka ga yafi karfinka,illar bariki kenan) sunan da izzadeen baiyi ba kenan,amasallaci kawai akayi radin suna inda twins suka ci sunan hassana da husaina.
πŸ‘„LπŸ…°LπŸ…°TπŸ…°πŸ™Š



*written by*
πŸ’…πŸ’… *sadnaf*πŸ’ž





Page 163
Bangaren su tasleem kua bayan suna hada kan kudin da suka samu sukayi suka Bawa el Bahrain dan kudin da dan yawa,inda tasleem ta nemi daya bude musu private school suringa koyarwa,inda shawarar dasuka yanke yamishi dadi dan dama yanada niyyar bude musu makarantar, katon filaye yasiya guda biyu manya manya guda biyu aka Gina,inda yasa sunan ammi adayan *Ammi international schools * dayan kuma yasa sunan taufeeq (taufeeq academy nursery and primary school)* kwararrun teachers yasamu dasuke kware akowane subject yayi employing dinsu dan su ringa koyarwa amakarantun, yasamawa Yusrah admission a fce dan tacigaba da zua school tunda a Iya secondary ta tsaya,yasama mata nanny dazata ringa kula da taufeeq,inda ita kuma tasleem ita take kula da makarantun,kafin Yusrah tagama,itama tasleem tasamu admission a buk dan tacigaba da degree dinta dan itama Iya diploma tayi,dan spill taringa samu data fara degree dinta,dan gabadaya bata maida hankali ba alokacin,burinta alokacin bai wuce ayi mata aure ba,ahaka rayuwa tacigaba da tafiya inda tasleem tayi tsayuwar daka dan ganin tabawa yaran nasu tarbiyya,saboda ita kadai Ce mai dan samun lokaci,dan Yusrah bata da lokaci sabida makaranta,inda el Bahrain shima yakan dan taimaka mata inya samu time.



*17 years later*


Yayan el Bahrain duk sun girma inda yake balain ji da ammi dan bayan hassan da usaini tasleem bata kara haihuwa ba,inda Yusrah ita kuma takuma haifo da namiji Daga nan haihuwa ya tsaya mata,asanadiyar haka ne yasa ya dorawa ammi san duniya dan ita kadai ce mace,daddy da shuriem na kasar madina suna karatun Arabic, inda ita kuma ammi take ss1 awani tsadaddan private school, hassan usaini taufeeq da abubakr sadiq( junior dan Autan Yusrah ke makarantar da iyayensu suka bude, bangaren izzadeen kua bayan hassana da husaina mata uku Mufeeda takara haifowa inda aka sa musu,sadiqa,salma da tasleem,dan izzadeen alkawari yayi yace sai yasa wa ersa suna tasleem indai yakuma samun ya mace,jamaa ya labarin Fateema ne,Fateema dai tun lokacin da taga Mashida ta haifi yara sun kai biyu hankalinta yafara tashi, dan agarin 🌧 *ruwan ido*πŸ‘ (sunan novel din danake sa rai zan rubuta bayan wanan amma ban tabbatar ba dan gaskia typing akwai wuya) tarasa mai zua gurinta yanzu, ganin la,asar ta sameta gashi magriba na Neman samunta ne yasa ta hakura ta fito da wani mai mata biyu daya nace mata yana Santa da aure duk da ba sanshi take ba haka tahakura ta aureshi, inda shi kuma ya hadasu gida daya da matarsa dan cemata yayi bayaso yaraba kan yayansa dan yafiso yayansa su taso Kansu ahade,fateema kua bahaka taso ba dan bayanda zatayi ne,aikuwa tarewarta da sati biyu,tafara fuskantar Matsala da Zainab matarsa dan masifaffiya Ce ta tashin hankali duk masifar Fateema bata kaita ba,to readers gaba da gabanta,ganin Zainab ta dameta ta shanye a amasifa ne yasa kan dole ta saduda,tayi laushi kamar ba Fateema masifaffiya ba dan agida mamakin canjawarta akeyi inda tasleem ita kuma canjawarta yamata dadi,tasleem kua tin lokacin da ammi ta girma tafara period tafara damun el Bahrain akan a aurar da ita,yace akan me zai aurar da ita yanzu alhalin ko secondary bata gama,tabari Indai tagama secondary zai aurar da ita,dan akwai wani yaron abokinsa dayakesnta da aure kabir, yana Egypt shi ma yana karatu yasan shima zua lokacin da zata gama secondary shima yagama,inyaso sai adaura musu aure,tasleem bahaka taso ba dan babu yanda zatayi ne dan gabadaya atsorace take dan gani take kamar itama ammi irin halitar ta Ce da ita,bangarn izzadeen kua ganin duk yaya mata ne dashi yasa yasha alwashin aurar dasu suna gama secondary, inda yaringa yiwa ameera kulle dan tana da jikin girma sosai Daga Makaranta sai gida,ko kofar gida baya yarda taje,dan musamman yasamu wata taringa zua tana koya musu karatun qurani agida,boko kawai suke zua,



Ranar da izzadeen bazai taba mantawa ba wataran yakai su ameera makaranta yadawo gida,, mussadiq yakirashi yace masa yanzunan yaga ameera amotar wani an wuce da ita da uniform ajikinta,jiki narawa izzadeen ya suri motarsa yayi makarantarsu ameera da gudu yafito Daga mota ba takalmi yayi office din principal yakamoshi yana jijiga shi yana tambayarsa ina ameera take, shima principal cikin tashin hankali ya nufi ajinsu ameera,yaringa tambayar ina ameera take, duk shuru sukayi sai da suka ga izzadeen yafara shirin dukan principal, sanan Sukayi magana suka ce mishi ta tafi birthday din easy wani dan iska yaro a ss 3 kirjin izzadeen ne yafara dukan uku uku, ya nemi wani yaro acikin en ajin ameera yakarashi inya san gidan, ikon Allah ne yakai izzadeen gidan dan tukin gaganci yaringayi,tura kofar yayi da karfi yaji akulle, wani bangaza yakaiwa kofar sai data budu, abnda yagani ne yasa numfashinsa daukewa na wucin gadi yarsa ameera dayafiso arayuwarsa wani yasmu yake LπŸ…°LπŸ…°TπŸ…° da ita taku biyu yayi ya damko easy yamishi naushi biyu ya suma,yazube aksa afashe da kuka ameera kua tunda ta tashi ta rabe ajikin bango jikinta karkarwa yaringayi tana mamakin yanda akayi tabari hakan yafaru da ita
πŸ‘„LπŸ…°LπŸ…°TπŸ…°πŸ™Š



*written by*
πŸ’…πŸ’… *sadnaf*πŸ’ž





Page 164πŸ”š


Ciwon zuciya ne

Please Login or Register in order to submit comment