Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*written by*
šŸ’…šŸ’… *sadnaf*šŸ’ž




Page 155

Tana shiga cikin gida parking space tafara dubawa taga Abba bai dawo ba, hamdala tayi, tayi cikin palo, Umma ta tarar tana ta zirga zirga apalo,kirjinta ne yahau dukan uku uku dan bata san karyar dazata shararawa Umma ba,sallama,tayi atsorace Umma ta juyo dasauri,"Fateema ina kika tsaya tundazu Daga siyan magani sai da kika samu awa daya duk kinsa hankalina ya tashi,ina tunanin ko wani abun ne yafaru," Umma wlh kaina ne ya matsamin da ciwo lokacin Dana fita shine na shiga gidan aunty Bilki na aiki almajirinta ya siyo min maganin,Dana sha bacci yadaukeni sai da aunty Bilki ta tasheni," ajiyar zuciya Umma tayi tace Allah ya sauke dadin danaji ma abbanku bai dawo ba,wuce kije kici abinci ki kwantar,dakinta ta wuce umma ita kuma ta zauna ta kamo tashar Arewa 24 tana kallo,tana shiga dakin ta dauki wayarta ta kunna takira tasleem,bugu daya ta dauka,"sis kun karasa gida ne cewar tasleem," ee Aunty mun karaso ya ma tafi," hope Umma batayi miki fada ba," batayi min ba,gidan Bilki nace mata na shiga,yauwa haka nakeso sis kiyi sallah ki kwantar gobe zan kiraki,yauwa Aunty inataso in tambayeki hope Yusrah batasan abinda ya faru ba? Batasani ba gaskia kuma bana jin el Bahrain zai fada mata,Allah yasa bata sani ba dan kinsan inta sani akwai Matsala, karki damu batasni ba,to shikenan aunty sai dasafen Allah ya tashemu lafiya ameen ta katse wayar ta ajiye agefen side bed ta zauna agefen gadon ta rike kanta, tana tunanin abinda yafaru,kwalla ne suka zubo mata,afili kuma tace Allah ya isa tsakaninmu dakai izzadeen.



Bangaren el Bahrain kua ahanya ya tsaya ya musu takeaway,yakarasa gida,bangarn Yusrah ya nufa,yana shiga dakinta yaje ya tarar still baccinta take bata tashi ba,kan gadon yakarasa ya zauna yafara tashinta,bude idanta tayi tana kallonsa,murmushi yayi yace na tasheki ko?girgiza kai tayi,yace tashi kiyi sallahr isha, nasiyo mana abinci, inkin idar kizo muci abinci,nima bari naje nayi alwalar ,to yaya tace tare da mikewa,tayi hanyar bandakin,mikewa yayi shima yayi yafita waje, dakinsa ya nufa ya daura alwala, yayi sallah,sai daya Dade yana. Musu addua zaman lafiya tsakaninsa da matansa yakuma roki Allah da ya karesu daga Sharrin izzadeen,sanan ya Shafa ya mike yayo waje,bangaren tasleem ya nufa,apalo yaje ya tarar da ita azaune ta zuba tagumi tana kallon waje daya da alama tunani take dan batasan da shigowarsa,sallama yakarayi akaro na biyu da karfi,tayi firgigit ta dago ta amsa,sannu da zua tace tana sunkuyar dakai,amsawa yyi yana Daga bakin kofa,zo muje muci abinci,mikewa tayi tace lah na manta ban Dora ba dan Allah kuyi hakuri, bari na dafa mana ko indomie ne,tace tana yin hanyar kitchen, kibarshi nayo mana takeaway,kizo mu tafi yace tare da juyawa," kamal" tsayawa yayi cak batare da ya juyo ba,takarasa gabansa ta durkusa dan Allah dan Annabi kayi hakuri bazan kara kwatanta fita batare da izininka ba,dagota yayi yace karki damu nahakura,wuce muje, yace tare da riko hanunta,palon Yusrah sukayi,suka tarar da ita azaune da hijab ajikinta ta dauko plates ta juye abincin tana jiransu,dagowa tayi ta amsa sallamar dasuka mata tasaki murmushin jin dadi data ga hanunsu arike Dana juna dan tasan sun shirya,tasleem zama tayi agefen Yusrah,el Bahrain shi kuma ya zauna agefen tasleem,atare suka fara cin abincin inda el Bahrain da Yusrah ne kawai ke cin abincin,tasleem tsakura kawai take bawani ci take ba, sai daya mata magana tafara cin abincin sosai,ahaka suka kamalla cin abincin,tasleem ta kwashe plates din takai kitchen, tadawo ta zauna, el Bahrain mikewa yayi yatafi dakinsa,Yusrah da tasleem suka bishi da kallo,tasleem saurin goge hawayen dake Neman zubo Mata tayi dan tasan el Bahrain kawai cewa yayi ya hakura amma da wani Abu azuciyarsa,Yusrah dawo da kallonta kan tasleem tayi, tace" Aunty tasleem wai mai kikayi wa yaya ne? hawayen datake ta boyewa ne suka zubo mata tarasa amsar dazata Bawa Yusrah, yi hakuri Aunty tasleem bansan tanbayar Dana miki zai bata miki rai ba,girgiza Kai tayi tace baki batamin rai ba,tace tana goge hawayen dasuka zubo Mata, bari nje na kwantar sai dasafe,Allah yakaimu Aunty tasleem,tayi waje, Yusrah ta girgiza kai tace Allah ya sasanta ku,ta mike tayi hanyar dakinta




Bangaren izzadeen kua sai daya tabbatar da tafiyarsu ya fito,suhaima dake tsaye adakin ta kwashe da dariya,tace Ashe mijjn nawa matsoraci ne har tsoron mace yake, azuciye yayi gurinta tana kokarin guduwa ya damkota ya rufeta da duka sai daya mata lilis ya watsar da ita waje,ya rufo kofar dakinsa,suhaima taringa jera masa Allah ya isa,izzadeen kua zama agefen gado,yana daya sani bai tari tasleem ba,gashi abubuwa sun kwabe, gashi jibi ne daurin aurensu da Mufeeda bai so suka samu sabani da el Bahrain ba,haka yazauna yanata tunane tunane,yaga ba tunanin ne mafita ba ya mike yje ya dauro alwala,yazo ya tayar da sallah


El Bahrain kua bayan yaje yayiwa tasleem sai da safe yadwo ya kwantar, tunanin yaringayi yanda zai nisanta tasleem daga wajen izzadeen,dan ya tsorata da kalmomin da izzadeen dan yasan halinsa tabbas zai Iya rabashi da tasleem, juyi yayi ya rungume pillow,Yusrah kua dama ba bacci take ba itama dan haka kawai taji bata jin bacci,yaya Ka kasa bacci ko,tace tana kallonsa,girgiza mata kai yayi tare da kara kankame pillown ya rufe idansa mirginawa tayi kusa dashi ta cire pillown ta maye gurbin pillow ykua rungumeta,aikua nan da nan bacci yayi awon gaba da ita,shikua ba bacci ne yadaukeshi ba sai daya samo wa kansa mafita,bacci ya daukeshi,karfe biyu da rabi ya mike afirgice yana sallati,dan mafarki yayi izzadeen yashiga dakin tasleem yadaukota akan kafadarsa ya gudu da ita,tasleem tana ihu tana Neman taimako,durowa yayi Daga kan gadon ya yi bangaren tasleem aguje,Yusrah ta mike tana sallati,dakinta ya shiga dagudu,tasleem dake zaune akan sallaya,ta mike tana sallati,nocsol md lafiya,maida numfashi yaringayi daya ganta,bakomai yace mata ya rufo mata kofar,ya koma bangaren Yusrah yaje a tarar da ita abakin kofa,yaya lafiya mai yafaru,bai Ce mata komai ba yayi hanyar bandaki yaje ya dauro alwala,yazo ya tarar da ita atsaye a inda ya barta,ki koma baccinki bakomai ya hau kan sallaya ya Tayar da sallah, Yusrah takoma ta kwantar tana tinanin mai ya tsorata el Bahrain,aranar kwana yayi yana nafilfili tare da adduoi na kada Allah yabawa izzadeen ikon cin galaba akansu,haka ma tasleem tarunga adduar zamn lafiya atsakaninta da el Bahrain Yakuma kare ta Daga sharrin izzadeen.
šŸ‘„LšŸ…°LšŸ…°TšŸ…°šŸ™Š


*written by*
šŸ’…šŸ’… *sadnaf*šŸ’ž




Page 156

Washegari da sassafe el Bahrain ya tafi gidansu yaje yasamu alhaji,yace mishi yana so yabashi mukullin gidansa dake Jan bullo yana so tasleem takoma can da zama,inda alhajin mamakin maganar da el Bahrain yagaya mishi ya rufeshi,tambayarsa yayi dalili,yace haka kawai, yakeso tasleem takoma can da zama,ganin maganar babba ne dole sai hajiya tashiga zancen ne yasa yakira hajiyar el Bahrain yakora mata maganar da el Bahrain yazo da ita,daka tsalle tayi tace akan me zai raba musu gida,fada tasleem da Yusrah sukeyi dayake so ya raba musu gida, yace aa haka kawai yake so ya raba musu gida,anan suka Ce indai ba fada sukeyi ba basu ga dalilin dazai sa yace zai raba musu gida ba,suna cikin zancen aunty luba tazo dan tayi musu sallama zata tafi abuja,tazo ta tarar da zancen da el Bahrain yazo dashi, daka tsalle tayi ta dire tace bai isa yaraba musu gida ba akan me,zai raba musu gida,ga laulayin da Yusrah ke fama dashi inya raba musu gida waye zai cigaba da dawainiya da yusrahn sanan inya raba musu gida rashin adalci zai ringayi atsakaninsu,Abu kamar wasa fa yazame gaske,dan luba fada taringayi sosai,inda el Bahrain yace shi yake da iko da gidansa shi yaga dama yahadasu aguri daya,yanzu kuma shi yaga damar rabasu,ganin abun na Neman zama fada ne yasa alhaji ya tsawatar musu yace su tsaya su saurareshi,wayarsa yadauka ya kira izzadeen yace yazo yana san ganinsa yanzun nan,gaban el Bahrain ne yahau dukan uku uku,dan baisan mai yasa Alhaji ke kiran izzadeen ba,dan in ma tambayarshi zai yi ko yasan dalilin dayasa yake So ya raba musu gida,baiso izzadeen yasan plan dinsa ba,wani takaici da bakinciki ne suka rufe el Bahrain, bangaren izzadeen kua hankalinsa bakaramin tashi yayi ba,dan duk atunaninsa el Bahrain zua yayi yagawa alhaji abinda ke faruwa,shiryawa yayi asanyaye jikinsa duk yabi yayi sanyi,yanufi gidansu el Bahrain,apalo ya tarar dasu azaune duk sunyi jungum jungum,el Bahrain ya sunkuyar dakai, luba sai girgiza kafa take,tsugunawa yayi har kasa ya gaishesu suka amsa,alhaji ya nuna masa guri yace ya zauna,ya Mike yaje yazauna yana satar kallon el Bahrain, tambayarsa yyi ko yasan dalilin dayasa el Bahrain ke san rabawa matansa gida,yadago da mamaki yana kallon alhaji, yakoma yana kallon el Bahrain daya dago yana jifanshi da mugun kallo,girgiza kai yayi yace baisan dalilin dayasa,kamal ke san raba matan nasa ba,Alhaji kiran sunan kamal yayi yadago yana kallonsa da idansa dayayi ja,"kayiwa Allah kayiwa Annabi kafada mana dalilin dayasa kake so Ka rabawa tasleem da Yusrah gida,sunkuyar dakai yayi ya rasa amsar dazai Bawa alhajin, luba Ce tace Abba bawani dalilin dyake dashi kawai so yake yara musu gida dan yana jin haushin yanda saurauniyar mata ke dauwaniya da Yusrah, dakata Lubabatu hajiya tace banasan tashin tashina, "kamalu haka kawai kakeso Ka raba musu gida? gyada mata kai yayi ya sunkuyar dakai ,kallon juna alhaji da hajiya sukayi,Alhaji yace kamal ni aganina matsawar ba wani Matsala kake fuskanta agurinsu ba kayi hakuri Ka barsu agida daya, dan kaga yanzu inka raba musu gida Ka kwari Yusrah, dan tasleem ke taimaka mata ko bhaka ba,haka ne el Bahrain yace cikin takaici dan bahaka yaso ba,yaso ace sun bashi goyon baya alhaji da hajiya nasiha sukayi mai sosai sukace inma wani abun suke mishi yaringa hakuri, yana kai zuciyarsa nesa,inda akarshe itama luba ta ringa bashi shawarwari cikin sigar lallashi,izzadeen dake zaune jikinsa yabi yayi sanyi, dan ysan duk sabida dashi el Bahrain kesan rabawa tasleem da Yusrah gida,jiyayi wani takaici da nadama sun lullubeshi,ahaka suka mishi naseeha yamusu godiya yace zai tafi, inda akarshe alhajin yake tambayarsu ya zaayi wajen daurin auren izzadeen gobe nan zasu zo ko Daga can zasu wuce, el Bahrain yace Daga can zasu wuce, alhajin yace Allah yakaimu goben, el Bahrain yayi waje izzadeen yabi bayansa Aunty luba tarunga tsokanarsu




.
El Bahrain na fita wajen motarsa yanufa yabude yahau rai abace,izzadeen yayi sauri ya bude gaban motar yahau ya zauna,juyar da fuska el Bahrain yayi,yace lafiya mai kake nema awajena," izzadeen kwantar dakansa yayi yafara magana cikin sanyin murya "kamal banida bakin dazan baka hakri nasan nayi maka laifin da bazaka Iya yafemin ba wlh tallahi abinda yafaru tsuatsayi ne bada gangan nayi ba,anan yakwashe komai yagaya el Bahrain yace karka ga laifi na,wlh tinda hakan yafaru narasa kwanciyar hankali,sai nake ganin kamar ina nemi yafiyar tasleem dakaina sai yafi da ace kai Ka nema min yafiyarta,Ka duba kagani tinda na auri suhaima nayi bnkwana da farinciki,kamal bazan boye maka ba wlh nayi nadamar abinda naringa aikatawa abaya tin Daga lokacin Dana auri suhaima Dana ga ba virgin bace,Allah ne yasan irin zafin danaji azuciyata,ashe duk matan danayi disvirgin dinsu haka mazajensu suka ji ranar dasuka fara kusntar su,auren suhaima yasa nayi nadamar abinda na aikata ta bakin nka baka isa kayiwa Allah wayo ba,dan Allah kadai ne yasan mata nawa na. LšŸ…°LšŸ…°TšŸ…° wa rayuwa, nayi dansani abinda nayi Dan haka nakeso Ka yafemin dan girman Allah idan in ma baka yarda dani ba,ni zan tashi nabar unguwar sabida ka saki jikinka dani,inyaso sai nakoma hotoro da zama,amma wlh bacin rai ne yasa nafada maka magunganun Dana fada maka jiya pls kamal kayi hakuri Ka yafemin,juyawa el Bahrain yayi yana kallonsa,pls abokina,dan ni ko Mufeeda ma da za a daura mana aure da ita gobe, ko ba a virgin nasameta ba zan hakura in zauna da ita haka dan abinda nashuka shi nake girba,bakomai na yafe maka amma karinga tunani kafin kayi Abu,tunda nariga nagaya maka nafadawa tasleem ta yafe maka mai nakara tararta ba ma Iya yafiyar Ka tsaya ba harda rike mata kafa amatsayinta na matar aure, kaga abinda kayi bai dace ba,hakane kamal nayi kuskure hakan bazata kara faruwa ba insha Allahu, to Allah yasa ni Bari na wuce gida sai Ka karaso mayi magana. Yanda zaayi Goben, to shikenan sai nakaraso izzadeen yace ya sauka Daga motar ya hau motarsa yanufi gidansu mussadiq
šŸ‘„LšŸ…°LšŸ…°TšŸ…°šŸ™Š


*written by*
šŸ’…šŸ’… *sadnaf*šŸ’ž




Page 157

El Bahrain nabarin gidansu direct gida ya wuce yana mai farincikin abinda yafaru dan da duk hankalinsa atashe yake da izzadeen yace zai rabashi da tasleem, yana zua gida bangaren tasleem yanufa dasaurinsa yaga bata nan yasauko yayi bangaren Yusrah, apalo ya tarar da Yusrah akwance,tasleem kuma tana mopping,sannu da zua sukayi mishi ya amsa yana kallon tasleem, wani so da tausayinta na ratsa shi dan Daga jiya zua yau har ta rame,kiranta yayi yace tazo ta zauna,ta ajiye moppern ta nufi inda yake zaune,tazauna akasa ta sunkuyar dakai,satar kallon Yusrah yayi yaga idanta nakansu,gyaran murya yayi yace suje su shirya zasu fita su zaga gari,Yusrah mikewa tayi tana murna tace yaya dagaske, zan muku wasa ne,mikewa Yusrah tayi tayi hanyar dakinta tana murna,dan dama tagaji da zaman waje daya,tasleem sakin baki tayi tana kallonshi da mamaki dan ko da asuba daya zo tashinta tayi sallah fuskarsa amurtuke take,mamaki taringayi mai yakawo sudden changes din,el Bahrain na ganin Yusrah tashige dakinta yaja hanun tasleem yyi bangarenta da ita,dakinta yakaita yafara yarufo kofa yafara aika mata da zazzafan kiss, yana bata hakurin abinda ya mata jiya,kwace jikinta tayi dakarfi data ga yana Neman wuce gona da iri yakuma damkota yacigaba da kissing dinta yana bata hakuri anan ya kwashe yanda sukayi da izzadeen yagaya mata yace dafatan zata yafe mishi ta yafewa izzadeen, hawayen farinciki ne suka zubo mata tace ta yafe musu,aranar wuni sukayi suna zagaya gari,inda yakaisu sukayi shopping tasleem taringa zabo kayan bebies,suka ringa mata dariya tace gwara tafara siya kafin Yusrah ta haihu,aranar bayan sun koma gida,sunyi sallah sunci abinci,sun dan taba hira, Yusrah ta mike tayi musu sai da safe, ta tafi dakinta ta kwantar dan tinda tasamu cikin nan take bacci da wuri,el Bahrain mikewa yayi yabi bayanta dan suyi sallama,kafin yaje har bacci ya dauketa,murmushi yayi ya gyara mata kwanciya ya lullubeta da bargo,yamata kiss agoshi yafito yarufe mata kofar,bangaren tasleem yanufa dan bai ganta apalon ba,yanufi dakinsa yaje ya watsa ruwa yasako kayan bacci yayi dakin tasleem,agaban mudubi yaganta atsaye tana fesa tirare yayi sauri yayi gurinta dan kwata kwata baya gajiya da tasleem dan kullum kamar Amarya yake jinta,daukarta yayi, yayi kan gado da ita yafara aika mata da sakoni aranar kwana sukayi suna farantawa juna rai.






Washegari karfe 11:30 aka daura auren izzadeen da Mufeeda, akan sadaki dubu hamsin,inda mussadiq yahadaw ango Izzadeen walima agidansa,Daga wajen daurin auren suka wuce can suka je suka ci abinci sukayi hotuna ,Karfe bakwai aka kawo amarya Mufeeda, inda motoci biyu ne kawai suka kawo mutanen Amarya daga el Bahrain sai mussadiq,dangin Amarya bayan sun kai Amarya dakinta,sun mata nasiha suka fito suka hau mota aka maidasu gida,ahanya el Bahrain yasiyi kaji da lemona aka mishi Leda biyu yakaiwa izzadeen guda daya yadauki daya yakai gida,Izzadeen aranar fargaba ne yabi ya cikashi yana tunanin watakila itama Mufeedar ba virgin bace,ahaka yashiga dakin Amarya ya umarceta data tashi Suyi sallah na godiya ga Allah,sukayi sallah ya juyo musu kazar da el Bahrain yakawo musu aplate yace Mufeeda taci taki ci dan duk atsorace take,ba yanda izzadeen baiyi Mufeeda tasha ko da madara ne taki, sai hawaye take,tabe baki yayi yaci yakoshi aransa yace data ci da kartaci ba abinda zai fasa dan shikadai yasan matsanacin halin dayake ciki na sha,awa yana kai plate din kitchen yadawo gurinta yace tashiga bandaki ta watsa ruwa tazo ta kwantar,nan ma kin tashi tayi dan wani irin tsoro ne yakamata dan tunda take bata taba kebewa da namiji ba sai yau,izzadeen kua ganin tana bata mishi lokaci gashi amatse yake yasa yajanyota yafara sarrafata yana cire mata kayan jikinta,jikin Mufeeda ne yahau rawa tasa mishi kuka,izzadeen kua ina yayi nisa dan yanda yadade rabonsa da mace ji yake kamar bai taba kusantar mace ba,atakaice dai aranar shi yfara sanin Mufeeda ya mace inda izzadeen sabida murna shi ya fara saninta ya mace yasa yafashe da kuka dan bai taba tunanin zai dace da auren virgin ba,jiyayi san Mufeeda na ratsahi sosai dan da baya wani Santa, amma asanadiyar kyautar budurcin data mishi yaji wani irin Santa na ratsashi aranar lallabata yaringayi kamar ya maidata ciki,ko kwawaran motsi bayaso tayi,shi yamata komai aranar,dadin hakan da Mufeeda taji yasa tacigaba da langwabewa, bangaren suhaima kua tana ganin ankawo Amarya,kiran Alhaji tanimu tayi tace mishi zata zo yajirata,tana ganin izzadeen ya kulle kofar palon sama tayi sadaf sadaf fita,itama aranar amarcewa tayi awajen alhaji tanimu,sai karfe goma sha biyun dare yadawo da ita.
šŸ‘„LšŸ…°LšŸ…°TšŸ…°šŸ™Š


*written by*
šŸ’…šŸ’… *sadnaf*šŸ’ž



Page 158

Kwanaki watani nata shudewa inda izzadeen da Mufeeda ke soyayya kamar su hadiye juna,inda el Bahrain da matansa zaman lafiya suke sosai suna gudanar da soyayyarsu cikin kwanciyar hankali,dan el Bahrain har wani ki'ba yayi ya ajiye tumbi Yusrah kua cikinta yafito sosai yamata kyau dan murmurewa tayi takara haske,cikinta nada wata hudu,akayi fara bikin masheeda inda akayi shagulgula sosai dan tasleem ma ba abarta abaya.ba sai data hada nata walimar,Yusrah kuma tayi mata gudumar kulolli masu tsada, el Bahrain kuma yabata gudunmawar dubu hamsin,ahaka akayi bikin mashida,inda Fateema Ce tashige gaba wajen yin komai, ,aka kai Amarya gidanta dake abuja,aranar da aka kaita dakyar aka rabasu da Fateema dan kankame juna sukayi sukayi ta kuka,ahaka suka juyo suka dawo,inda Fateema tazama shiru shiru kamar Mara lafiya,wanda shirun nata sai daya damu Umma takirata tace itama ta taimaka tafito da miji tayi mata aure ta huta,Fateema tace ita batada Wanda takeso,ahaka rayuwa tacigaba da tafiya yusrah tacigaba da rainon cikinta,inda tasleem tafara shiga damuwa narashin samun ciki,dan intaga yanda Yusrah ke tura ciki abun burgeta yake, bangaren izzadeen kua Mufeeda Amarya ma tasamu ciki,inda izzadeen yadorawa cikin san duniya,ko ina yaje yana makale da waya akunensa yana waya da Mufeeda yana tambayarta lafiyan babynta,bangaren suhaima kua cikinta ya tsufa haihuwa yau ko gobe,bata fita ko ina dan izzadeen warning yamata sosai yace bayasan yaga kafarta awaje, har ta haihu ya sallameta ta kara gaba,watarana el Bahrain na zaune dasu Yusrah apalon tasleem basu Dade da cin abinci ba Yusrah ta mike kafarta tasleem na Dana mata sabida kumbarar dayayi dan cikinta ya tsufa haihuwa yau ko gobe, tun da yamma tafara jin ciwon baya da Mara kadan kadan ta daure bata fada kowa ba dan tun a asibiti aka gaya mata alamomin haihuwa,matsa mata kafa tasleem tacigaba dayi suna hira da el Bahrain, Yusrah kua ta fara cije lebe,dan jitayi bayanta kamar zai balle,mararta ne yamurda mata tasaki sallati,el Bahrain ya mike ba shiri,lafiya Yusrah mai yafaru," yaya marata bayana wayyo Allah na yaya zan mutu, gigicewa yayi,tasleem ita kuma tafara tofa mata addua,tace el Bahrain yadagata sukai ta asibiti,riketa sukayi suka sauka kasa yaje ya bude mota dasauri yadawo ya riketa suka kaita mota,tasleem tayi Sauri tayi dakin Yusrah taje ta dauko akwatin da suka hada kayan haihuwa tadawo dasauri cikin motar,el Bahrain yaja motar a 360 suka nufi asibiti,tafiyar mintina ne yakawo su asibitin inda already nurses biyu na waje suna jiran karasowarsu dan el Bahrain yamusu waya, Yusrah sallati kawai take tana kiran sunayen Allah,tasleem kua sabida tausayi kuka taringayi,ahaka nurses suka shiga da Yusrah dakin haihuwa,el Bahrain yaji kamar ya bisu,zirga zirga el Bahrain yaringayi aharabar asibtin inda tasleem kuma taringa zuba adduoin Allah ya sauke Yusrah lafiya,atakaice aranar ba Yusrah Ce ta haihu ba sai da asuba inda ta haifi santalellen da namiji mai kama da el Bahrain, fadar murnar da el Bahrain yayi dashi da tasleem bata bakine dan har rawa tasleem taringayi,el Bahrain yaringa kiran en uwa da abokanan arziki, yana fada musu, kafin gari yawaye danginsu el Bahrain suncika asibitin,karfe 8 nasafe likita ya sallami Yusrah suka dungunzuma suka dawo gida,tasleem kua aranar tasha aiki ta gode Allah dan dangin el Bahrain cika gidan sukayi ciki kua harda su Aunty luba,inda dadi yabi yakashe luba,dan dama burinta Yusrah ta haifi da namiji,dan ko abanza tasan yanzu Yusrah Ce gida washegarin da Yusrah ta haihu,su Umma suka zo da Fateema,sukayiwa Yusrah barka inda suka zo da akwati cike da kayan baby da atamfa wajen kala hudu,da dubu goma inji abbansu,inda dadi yabi ya ishi Yusrah ta durkusa akasa tana zuba godiya,Fateema kua tunda ta rike bbyn tahana kowa, dan jitayi inama bbyn tasleem ne,dan san bbyn yashiga ranta ahaka suka wunan musu suka tafi gida,bangaren el Bahrain kua kudi yakashe sosai na hidimar suna inda yayiwa tasleem da Yusrah dinki kusan kala takwas,izzadeen ma ba abarshi abaya ba ya taka rawar gani sosai, dan sai daya siyi katon rago, musamman yace ayankawa mai jego banda uban kaya daya kawo wa Yusrah da babynta,ranar suna shagali akayi sosai inda aka sawa Bby sunan abban el Bahrain, aka ringa kiransa da daddy,Yusrah tasha kyau ta godewa Allah, inda tasleem itama ta zuba ado kamar Amarya, dangin el Bahrain suka runga mata adduar Allah yabata cikin itama dan bakaramin kirkinta suke gani ba lura dasukayi da irin hidimar datakeyi,mai jego kam fadar kyautatukan data samu bata bakine dan sai data rasa inda zata ajiyesu ahaka akayi taron suna cikin nishadi kowa ya watse ya nufi gida da Niki Nikin kayan da tasleem taraba, washegarin suna Aunty luba kiran el Bahrain tayi gefe tace mishi zasu tafi da Yusrah gida dan acan sai sunfi kula da ita.
šŸ‘„LšŸ…°LšŸ…°TšŸ…°šŸ™Š


*written by*
šŸ’…šŸ’… *sadnaf*šŸ’ž



Page 159

Kwanaki watani nata shudewa inda izzadeen da Mufeeda ke soyayya kamar su hadiye juna,inda el Bahrain da matansa zaman lafiya suke sosai suna gudanar da soyayyarsu cikin kwanciyar hankali,dan el Bahrain har wani ki'ba yayi ya ajiye tumbi Yusrah kua cikinta yafito sosai yamata kyau dan murmurewa tayi takara haske,cikinta nada wata hudu,akayi fara bikin masheeda inda akayi shagulgula sosai dan tasleem ma ba abarta abaya.ba sai data hada nata walimar,Yusrah kuma tayi mata gudumar kulolli masu tsada, el Bahrain kuma yabata gudunmawar dubu hamsin,ahaka akayi bikin mashida,inda Fateema Ce tashige gaba wajen yin komai, ,aka kai Amarya gidanta dake abuja,aranar da aka kaita dakyar aka rabasu da Fateema dan kankame juna sukayi sukayi ta kuka,ahaka suka juyo suka dawo,inda Fateema tazama shiru shiru kamar Mara lafiya,wanda shirun nata sai daya damu Umma takirata tace itama ta taimaka tafito da miji tayi mata aure ta huta,Fateema tace ita batada Wanda takeso,ahaka rayuwa tacigaba da tafiya yusrah tacigaba da rainon cikinta,inda tasleem tafara shiga damuwa narashin samun ciki,dan intaga yanda Yusrah ke tura ciki abun burgeta yake, bangaren izzadeen kua Mufeeda Amarya ma tasamu ciki,inda izzadeen yadorawa cikin san duniya,ko ina yaje yana makale da waya akunensa yana waya da Mufeeda yana tambayarta lafiyan babynta,bangaren suhaima kua cikinta ya tsufa haihuwa yau ko gobe,bata fita ko ina dan izzadeen warning yamata sosai yace bayasan yaga kafarta awaje,

Please Login or Register in order to submit comment