Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nayin haka ba tukunna....
Fannah ta fito tare da Hisam babu tambayar da Mummy bata mata ba ta fada mata dalilin kukanta amma taki.. Shiyasa ta korota.. Tana ganin farouq daya fito daga gida ganin su yayo inda suke shiyasa tayi hanyar gidan su farida.. Kiranta yy ta tsaya batare data juyo ba... Ya karasa kusa da ita ganin yanayinta yasa yace "meke damunki".. Juyowa tayi tace "babu abinda zakuce mun ynx ni har na isa na hadaku fada" seta fashe da kuka "jiya duk naji maganganin ku kaida yaya sultan.. Kuma kasani nafasa auren sultan kai zan aura".. Daga haka ta shige gidan su farida tana kuka.. Jimm farouq yayi zuciyar sa nayi masa babu dadi.. Se kuma ya kama hannun Hisam suka shige gidan baffa.. Dakin fareeda ta shiga.. Bata ciki sede karar ruwa a toilet.. Zaunawa tayi saman gadon ta tana share hawaye.. Idon Fannah ya sauka akan wani diary me kyau vaneesa ta taba bata kalar sa janyosa tayi tana dubawa.. Kafin ta bude a hankali tana dubawa tafi kusan kusan minti uku kafin fareeda ta fito.. Turus fareeda ta tsaya ganin ta da wnn diary din jiya dashi ta kwana ta manta yau bata dauke ba.. Gabanta ya dunga faduwa.. Fannah ta dago idanun ta cike da hawaye.. "Fareeda is this real?".. Da sauri fareeda ta girgiza kai tana kokarin kabar diary.. Fannah ta fisge "you mean duk wnn da kk fadamun kinaso dama ba wani bane sultan ne amma baki taba fadamin ba fareeda wane irin kallo kikemun ne"... "No Fannah don't quote me wrong". Fannah ta fashe da kuka sosai.. "Na shiga uku da wane zanji.. Wlh na fasa auren sultan.. ".. Fareeda ta riko hannun ta "pls Fannah ki tsaya ki saurareni ni na hakura da sultan tunda ke yake so ni na hakura ".. Kuka Fannah take sosai ta fizge hannun ta daga rikon da fareeda ta mata.. Ita tayama zata auri sultan wlh ta hakura dashi.. Daga haka ta fice tana kuka hankali tashe.. Gida ta wuce ... Dan gaba daya hankalin ta ya tashi.. Karo ta kusa ci da daddy ze fito... Hankali tashe yake tambayar ta lpy sbd yanda yaga tana kuka.. Ta fada jikinsa "daddy na fasa auren sultan bazan aure sa ba bazan iya ba daddy..." Da confusion ya jata suka zauna saman kujera ya kwantar da ita a shoulder dinsa seda yabari tayi me isar ta snn yace "now tell me meya faru".. Nan tayi masa bayani na komai da yake faruwa.. Shi kansa daddy kasa magana yayi sede yace taje ze duba lamarin.. Amma seda ya tabbatar tayi breakfast snn ya fita..
Ko a ranar duk yanda farouq ko fareeda suka so ganta ki yarda tayi.... Tsab abiee ya gama fadawa yan uwansa yanda sukayi da farouq, nan ma daddy ya fada masa yanda sukayi da Fannah.. Dadd yace "ikon Allah but ya kuke ganin za'ayi..." Mom tace "akira su muji ta bakin su".. Nan da nan kowa yy kiran dan sa... Farouq ne ya fara zuwa se sultan.. Sultan na shigowa seda gabansa ya fadi ganin harda farouq... Abbu ne yace "farouq maimata abinda kaje kafadawa mahaifinka".. Babu bata lokaci ya fada.. Sultan ya dinga kallonsa.. Dad yace "kana da labarin cewa Fannah tace ta fasa auren ka".. Wnn karon ba sultan kade ba har farouq seda ya dago... Abie yace "sure tace farouq zata aura.. Snn kuma fareeda na sonka baka taba sanar mana ba".. Sultan ya dago with shock.. Dama har ynx fareeda na sonsa.. Shi besan da wnn zancen ba tabbas yaso fareeda tun besa mene so ba Amma ynx Fannah yake so kuma bayajin ze iya barwa koda Amoon ne bare farouq"....

More comments more typing......

Urs
✨✨✨
Nafeesatuu....😍😍



*💫❤LOVE CYCLE✨*


Written by

*@nnafie🖤*
(Smll but mighty😉)

*writer of*
Saif
Adaan
Wata mafita
Saboda duniya
Love cycle......


Bismillahir rahmanir raheem

💫❤Love cycle❤ (21)✨
Sultan ya girgiza kai... "Bnsani ba nima Abbie se ynx"... Dad yace "to ynx ka sani kana sonta koko"... Sultan ya runtse idanu zuciyar sa na beating ... Mom tace "magana fa ake maka".. Sultan ya sunkuyar da kansa.. "Inason fannah sosai Abbie"..... Daddy de kallon su kawai yake bece komai ba.. But yafi jin farouq din tunda diyar sa tace shi take so sede baze ce komai ba se abinda yan uwansa suka yanke.....
Abbu ne yace "ku tashi kuje zamu neme ku"..... Tashi duk sukayi suka fita .. Dad yace "yakamata a duba lamarin nan".. Abie yace "tabbas tun kafin azo a fara samun matsala.. Ya maganar shi Aliyun"... Dad yace "ranar ita yau zasu dawo inshaallahu"...Abu yace "inshaallahu se asan abunyi zuwa dawowar tasa...
Farouq na fitowa sultan ya tare sa.. Hakan yasa farouq ya tsaya yana masa wani kallo . sultan ya tape hannu "well aikin ka yayi kyau sosai kaje ka fadawa su Abie and bn san me kafadawa fannah ba da har tace ta fasa aure na... But let me tell you ynx aka fara wasan na rabata da Amah ma bare kai"... Farouq yayi wani murmushi... Snn yace "I don't knw what you're turning to usman but am ready for you zan nuna maka kaiba komai bane" daga haka ya wuce yabar sultan... Wani murmushi yy kafin ya koma ciki.....
Fannah ta dago tana kallon fareeda data shigo dakin ta.. Tun jiya takeso su hadu amma Fannah taki bada damar hakan... fareeda ta jingina da kofa tana kallon Fannah... Can tace "why did you did that".. Fannah na kallon ta tace "menayi",. Fareeda ta lumshe idanu. "Idan ma kin hakura da sultan sbd nine da bakiyi hakaba dan ni na hakura dashi sbd sultan ke yakeso bani ba".... Fannah tace "ko sultan ni yake so ko bani yakeso ba kisani na hakura da sultan bazan aure sa ba"... Fareeda ta girgiza kai.. "Dan Allah idan ma sbd ni kikayi haka Fannah ki janye"... Tashi Fannah tayi ta kamo hannun ta seda suka zauna saman gado snn tace "tell me baki son sultan ne kome nasan kina sonsa"... Fareeda yace "yes Fannah I love him tunda na taso shi zuciyata ta fara so dashi kade na taba soyayya but ni naja sultan ya barni.. Ko ynx yace baya sona bazan ga laifin sa ba"..... Dan murmushi Fannah tayi zuciyar ta nayi mata babu dadi haka kawai taji haushin sultan take Ji kodon maganganun da taji yana fadawa farouq knn kansa kawai ya sani..".. Ta dubi fareeda "inshaallahu sekin auri sultan din da kika bata nakin kula kowa baze tafi abanxa ba". Zatayi magana Fannah ta rufe mata baki..... Shiru Fareeda tayi tana sauke kananun ajiyar zuciya... Da fareeda zata tafi har bakin gate ta rakata.. Sultan da shigowar sa knn.. Fannah na ganinsa tayiwa fareeda sallama ta koma cike da jin haushinsa... Fareeda tayi kasa da kanta zuciyar ta na bugawa ta wuce sa... Ya bita da kallo yama rasa tunanin da zeyi....a hankali ya shiga gidanasu Fannah ya aika me gadi ya kirata.. Sakon data aiko masa shine bazata zo ba... Sultan ya koma zuciyar sa babu dadi.. Wajen mom ya tafi.. Yana zuwa ya marairaice mata... "Mom Fannah bata kulani..".. Mom ta ture sa kaini rabu dani kar kusamin damuwa dawa zanji kai ko yusrah... Sultan bece komai ba ya tashi ya wuce daki... Mom ta bisa da kallo..
Yusrah bataji dadin abinda Fannah tayi ba dan haka kawai taji tana taya yayanta kishi kodan sbd damuwar daya shiga kwana biyu.. Ita ba wai bata son farouq ba amma dalilin ta takeson sani... Koda ta samu Fannah da maganar.. Hakuri kawai ta bata cewa baxata iya hada kanta da fareeda ba ta barmata ai tare ta gansu.. Yusrah taji dadin maganar.. She wish ace jiddah zata iya mata haka amma tasan ko dame take yawo jiddah bazata iya barmata Amoon ba... Yusrah tace "kin kyauta Fannah amma inaso ki sani yaya sultan na sonki.. Sede ina bayan ki akan abinda kikayi abinda nida jiddah dani muka kasayi knn.. Fannah inason yaya Amoon wlh da zan iya barwa jiddah shi da tuni na barmata".. Yusrah ta share hawaye ... Fannah tace "ki dena kuka inshaallahu komai ze dedeta".. Yusrah tace "wnn kukan da nake kadan ne akan idan yaya Amoon ya dawo.. Duk da inaso ya dawo amma ina tsoransa.. Fannah dan Allah idan har taku tazo daya da yaya Amoon ki fada masa wlh ina sonsa kuma zan iya yin kome akansa".. Sosai Fannah taji yusrah ta bata tausayi ita da jidda bata san Wanda yafi son Amoon din nan ba...
Ba sultan ba harta farouq Fannah tayi masa wuyar gani dan gaba daya ta tattara su ta share ko wayar su bata dauka gashi bata zuwa ko ina ko gidan baffa zataje seta daidaici duk sun fita snn take zuwa gaisar dasu mama... Daddy da mummy sun lura da yanayin ta.. Shi kansa sultan saukin dayasamu shine ganin har farouq ma bata kulasa...
Ynx ma haka seda ta daidaici basu nan snn taje ta gaisar dasu mama sama sama suka gaisa ta fito sbd bata ayi mata maganar.. Tana fitowa suka hadu da farouq shi kuma ze fito... Kasa tayi da kanta ta raba ta gefensa zata wuce ya kamo hannun ta.. "Fannah nayi maki wani laifi ne".. Fannah ta fashe da kuka "yaya farouq meyasa ka boyemun abinda faruwa ynx nan duk sbd ni kuke fada kaida yaya sultan"... Yace "look ki saurareni ni bnyi fada da sultan ba sbd ke kawai shine ke takalata ko kishi yake bn sani ba amma bana shiga harkan sa akan maganar yes I love you tun ranar dana fara ganin ki but I want the best for you tunda zuciyar ki na tare da wani I have nothing to do than to support you wnn shine son da zan iya nuna maki but abinda sultan yake mun yayi yawa shiyasa zan nuna masa iyakar sa".. Fannah ta rika kallon farouq hakika ya cika mutum me adalci da tausayi da kowa irinsa ne da anji dadi... Tace "yaya farouq kai zan aura na hakura da sultan".. Dan murmushi yy "ohk naji to yimun murmushi mana.. Rufe fuskar ta tayi yace "ohk muje na rakaki".. Tare suka taho.. Haka kawai Fannah taji ta dan samu wani relief.. Har gida ya rakata snn ya dawo....
Dad ne zaune a wani dan karamin parlo dake gidansa wanda yaji kayan more rayuwa tare da ilansa suna break daddy dake cike da fada.. Ya karashe maganar dayake "nide na fada maka kar kawuce ranar danace maka".. Daga haka ya katse wayar sa yace "wlh Aliyu bazai maidamu wawaye ba.. Idan har ya wuce ranar danace masa sena saba masa".. Mammah tace "inshaallahu baze tsallakeba kasan de baya tsallake maganar ka".. Dadd yace "inde har yasan dalilin zuwan ai ze iya zillewa".. Mammah tace "amma kana ganin Aliyu ze amince da abinda kuke shirin yi"... Dad ya mata wani kallo "ai se yaki tunda ya haifemu.. Dama duk abinda yakeyi nasan harda karin hadin bakin ki".. Mammah tace "ni kuma duk abinda yake inace halin ka ya dauko..kuma kasani Aliyu yace mun akwai wacce yake so.. Dama babu toh kila ya yarda da kudirin ku amma tunda har ya bude baki ya fada nasan baze amince da wata ba".. "Tunda shiya haifemu ai seya ki amincewa".. Itade mammah bata ce komai ba... Dad yace "ynx wata Matsala ce ma ta taso".. Mammah ta kallesa matsalar mene" nan Dadd ya kwashe komai yanda sukayi da Akan zancen Fannah.. Tun kafin ya gama chucu take zufa hankali tashe .. Excusing kanta tayi.. Ta tashi wai zataje toilet ... Aikam tana shiga ta fashe da kuka... Ynx duk dakonn soyayyar farouq da take.. Har an fara maganar sa da wata ba itaba.. Ta fashe da kuka hakika Fannah mutum ce kuma tayi alkawarin hakura da farouq inde har zasu zauna lpy da Fannah but dole ta nisanta kanta da Fannah da kuma farouq dan ta samu damar bawa zuciyar ta hakuri..
Duk yanda sultan yaso su hadu da Fannah taki yarda babban tashin hankalin sa shine yanda yaga ynx suna haduwa da farouq alamun sun shirya knn .. Fannah kau tana sane da yanda sultan ke se su hadu amma take dodging dinsa... Ko fareeda ma ynx basu haduwa.. Chucu ce ynx bata gani...
Zaune take a wani dan karamin garding dake gidan su taji anyi mata sallama daga kai tayi ta kallesa kallo daya ta dauke kai.. Cki cki ta amsa sallamar sa.. kujerar dake kallon ta ya zauna... Yace "shin dama Fannah so na zama kiyayya.. Sonki nake fa" ba tare data kallesa ba tace "ina amfanin son dazaka ka rinka fada da dan uwanka akai na"... Ya tabe "baki wnn dalilin ne yasa kikace kin fasa aure na knn".. Tace "sure bashi kade ba" yace "sbd fareeda".. Tace "sure banason samun matsala da kowa"... Yace "amma ki sani ina sonki kuma duk abinda nayi sbd inasonki ne"... "Yaya sultan koda inasonka zan hakura kodan sbd fareeda".. Yace "well inde ko sbd fareeda kika rabu dani kika amince da farouq to ki sani chucu tanason farouq"... Fannah ta rinka kallon sa without blinking yace "yes chucu nason farouq fiyema da son da fareeda kemun kuma kisani ina sonki ina kishinki shiyasa nake kasa jurewa idan farouq na shige maki"... Daga haka ya fice yabar ta da tunani iri iri a ranta... Knn shiyasa chucu ta dena neman ta duk sbd da wnn dafe kai tayi sbd yanda taji yana sara mata. Se kuma ta mike da sauri... Hijab dinta ta dauka ta fito domin zuwa gidan su chucu.. Ganin farouq da sadeeq sun fito daga gidan baffa yasa ta karasa wajen su da sauri idanun ta cike da hawaye... Kallon ta suka dungayi harta Kara so... "Yaya farouq ashe dama chucu nasonka bn sani ba baka taba fadamun ba.. Kasa zata kullaceni".. Farouq ya rinka kallon ta dan shi be fahimce ta ba.. Sadeeq ne yace "ya akai kika san da zancen nan".. Fannah ta fashe da kuka kun sani shine kuka boyemun... Wucesu tayi gidan su chucu ta shiga suka bi bayan ta.. A balcony ta iske chucu zaune pressing her phone.. A yanayin da chucu taga Fannah seda gaban ta ya fadi... Fannah tace "pls meyasa kuke boyemun abu kamar ni ba er uwarku ba knn shine dalilin dayasa kikabar nemana... Fannah ta share hawaye.. Dan Allah kiyi hakuri nafasa auren kowa daga cikin su.. Kiyi hakuri bn sani ba" daga haka ta fice tana kuka sosai.. Chucu ta rinka bin sadeeq daya shigo da kallo.. Ya girgiza mata kai alamar bashi ya fada ba.. Snn ta dubi farouq da yake ta kallon da... Dan share guntun hawayen ta tayi tace "yaya farouq ina sonka tun can har yau sonka be ragu a raina ba kullum duniya da sonka nake kwana nake tashi but ynx sbd da Fannah yasa na hakura kana son Fannah itama naga kamar ta aminta da kai.. Babu abinda bazan iya yi mata ba shiyasa na hakura na barwa zuciya ta bayan sadeeq da yaya Amoon babu wanda yasan da wnn zancen.. Wlh yaya farouq na hakura bana son wani tashin hankali... Daga haka ta shige ciki tana kuka sosai.. Farouq ya rinka kallon sadeeq.. Shi be taba sanin da zancen nan ba.....
Fannah tana zuwa dakin daddyn ta tafi ta fada masa komai.. Shi kansa hankalinsa ya tashi dakyar ya samu ya lallashe ta..
Washe garin ranar bayan angama breakfast abie ya bukaci ganin su Fannah dasu farouq.. Duk sun halitta wajen.. Nan abie ya tambayeta.. Tayi masu bayanin komai snn karshe da fadin ita da fasa auren kowa a cikin su tanada Amah shi take so... Abbu ne yace "bnd abinki ai bazamu tsaya jiran wanda bamu san ranar zuwan sa ba ki sani kefa mace ce... Sultan ne yace "Abbu wlh inasonta zan aure ta.. Fareeda ta rinka kallonsa.. Bama ita ba kowa na wajen.. Kafin Abie yace "ku tashi kuje zamu duba lamarin".. Fannah ce ta fara fita dan bata son haduwa da kowa cikin su... Jikin chucu yayi sanyi sosai.. Tasan Fannah ta dauka ada gaba ta dauka da ita bata san ba haka bane.. Dole taje ta bata hakuri suyi magana amma seta huce.. Ranar Fannah kulle daki tayi ta kashe wayar ta dan bata son ganin kowa... Sema da daddare ne takejin lvrin wai Amoon da Saleem sun dawo wajen su daddy.... Wai idan ya natsu zuwa jibi zasu zauna akan maganar sa shida su yusrah.. Fannah de batace komai ba.. Dan ita bama Amoon ba kowa ma bata son haduwa dashi...
Washe gari small mom tazo.. Seda tazo snn Fannah tadan sake.. Dan mom dinma dakin Fannah ta sauka kuma sosai ta zauna domin kwantar mata da hankali har Fannah ta sake.. Koda zata tafi se Fannah tace zata binta zatayi hakan kau akayi tare suka tafi.. Har ranar bata kunna wayar ta ba sede taje gidan small mom din tata.. Shima seda daddare.. Taci karo sosai da messages din su chucu na bn hakuri da su farouq Fannah ta runtse idanun ta ita kanta tasan tana son yan uwanta.. Matsalar nan ce bata so.. Amah ne ya fado mata tayi murmushi she wish ace ya dawo rayuwar ta da duk ta huta da wnn ruguntsimin...
Washe gari bayan la'asar small mom tasa driver ya maida fannah gida.. Bayan sun gaisa da mummy tace "yakamata kije wajen sumayya sau uku tana zuwa baki nan.. Pls fannah take things easy".. Fannah ta mike bari naje mummy.. Tashi tayi ta nufi gidan su chucu.. A balcony suka hadu da yusrah ta fito tana kuka.. Tana ganin fannah ta fada jikin ta.. "Fannah yaya Amoon baya sona kwanan sa biyu tunda ya dawo ko kallo bn ishesa ba bare yamun magana". Fannah da shaf tama manta da wani Amoon ya dawo tace "zomuje ciki to".. Yusrah ta girgiza kai "no bazanje ba idan kin fito zamuyi magana.. Daga haka ta wuce tabar fannah gaban ta na faduwa dan ita tun kafin ma taga Amoon din nan tsoransa take ji.. A hankali ta shiga da sallama.. Babu kowa cikin parlor se wani matashi me kama da mammah.. Fannah ta rinka kallon sa dan a tunaninta ko shine Amoon din.. Tace "yaya Amoon brk da zuwa".. Ya ware idanu.. "Amoon kuma saleem de kin wuni lpy sistern mu".. Dan murmushi tayi yace "tun ranar da muka dawo nake nemanki wai baki nan"... Ta gyada kai... "Chucu fa".. Ya nuna mata sama tana dakin mammah.. Ta juya knn zata nufi stairs taja wani burki.. Sbd kamshin turaren da taji irin na Amah... Lokaci daya kuma ta sauke idonta a kansa.. Yana sauka steps din a hankali.. Sanye yake cikin wasu milk kaya masu taushi da suka dace da fatar jikin sa data kara wani haske rigar me gageren hannun wandon kuma 3quater.. Kafarsa sanye da wani sleepers me taushi.. Ta daga idanun ta a hankali tana kallon fuskar sa... Fannah daskarewa tayi a tsaye wnn ai ba wani bane Amah dinta ne babu abinda ya canza da zata kasa gane masa sede kyau da haske daya kara.. To me yake anan.. Kode shine Amoon din kar de ace mata Amah dinta shine Amoon din da ake magana... Abubuwa dayawa suka rinka dawo mata ta rasa wane tunani zatayi.. Ta ringa binsa da kallo shiko kallo daya yayi mata ya dauke kai... Fannah ji tayi miyan bakin ta ya daskare.. Dakyar ta iya hada maganar bakin ta tace "Dr Amah".. Tsayawa yy tare da juyowa yana kallon ta.. Kafin a hankali yace "yes".. With shock fannah take kallon sa ganin yanda yake mata magana kamar be gane ta ba kode ba shi bane.. Amma idan ba shi bane yaza'ayi ya amsa sunan data kirasa... Tace "dama kaine Amoon Radda" dining ya tafi ya zauna kafin ya dago yana zuba mata lumsassun idanunta yace "sure nine did you knw me?".. Wani dumm fannah taji ganin tambayar da yake mata cikin rawar murya tace "you mean baka gane ni ba har ka manta dani Aliyuu"... Dan rolling eyes yy kafin a hankali yace "did i knw you.." Fannah ta fara ja da baya gaban ta mugun faduwa yace "wait but ur face looks familiar kamar na sanki ko".... Fashewa da kuka fannah tayi ta juya ta fita da gudu..
Saleem ya kalli yayan nasa "but why did you do that thought you're waiting for this day kuma ka nuna baka gane taba".. Chucu take bakin stairs ta karaso da sauri.. Tana zare ido cike da mmki tace "Yaya dama kaine Aliyun da Fannah ke magana"... Kallon su yayi gaba daya kafin yace "sure nine". Kamar zatayi kuka tace "but why did you do that. Lyk yanda ta damu da kai be kamata ka mata haka ba she love you".. Dan tabe baki yayi "I have to punish her she give a door for mens"... Chucu ta girgiza kai "no wlh har gobe Fannah na sonka" yace "iknw but I have to punish her.. I never fall for any girl except Fannah..I love only her.. I never give a door for others. So yanda nake son ta ita kade itama ni kade zataso Sbd itadin tawa ce ni kade ita din mallaki na ce.. Babu kuma wanda ya isa ya rabani da ita.. Bama sultan ba kowaye yace ze shiga gona ta seya gane kurinsa"
....
More comments more typing

Urs
✨✨✨
Nafisatu...😍😍

*💫❤LOVE CYCLE✨*


Written by

*@nnafie🖤*
(Smll but mighty😉)

*writer of*
Saif
Adaan
Wata mafita
Saboda duniya
Love cycle......


Bismillahir rahmanir raheem

💫❤Love cycle❤ (22)✨
Amoon ya kurbi tea din kadan yana kallon chucu da itama shi take kallo... Ya dage gira "what?".. Chucu da langwabar da kai "yaya Fannah ta damu sosai da kai nasan hankalinta yayi mugun tashi daka nuna baka gane ta ba...".. Dan murmushi Amoon yayi kadan shi kansa yasan bakaramar juriya yayi ba wnn er rabuwar da sukayi.. Sede wnn kadan ce akan wacce yayi a baya.. Ya dubi chucu da har ynx idon ta na kansa yace "na fara son fannah tun kafin tasan kanta.. I loved her for over 19yrs.. And I still love her today and always...and luckily she love me too".. Chucu ta zauna tayi tagumi "to yaya hope de kaji abinda su Abie suke shiryawa ko.".. Dan tabe baki yayi be kuma ce komai ba.. Sanin baze sake magana ba yasa tayi gumm da bakin ta....
Sa'ar Fannah daya har ta isa dakin ta bata hadu da kowa ba . da alama ma gidan babu kowa kilan ma mummy tana gidan Baffah.. Yanda zuciyar fannah ke mugun bugawa abun ba'a magana.. Bata taba shiga tashin hankali da rudani irin na yau ba.. Tama rasa wane tunanin zatayi se zagaye daki take tana hawaye.. Karshe ma durkushewa tayi ta dafe kai ta fashe da kuka.. Idan kaga fannah a lokacin seka dauka mutuwa aka mata.. Gaba daya ta rude... Tsayawa tayi tana demonstrating da hannu ta tana fadin "Aliyu Ahmad Amah shine Amoon?".. Girgiza kai tayi har lokacin tana kuka se kuma tacigaba da fadin "and that same Amah is the Amoon yusrah and jiddah talking About.they are not talking to each other because of that Amoon.. And Amoon is Amah, the person I love and want to spent my lyf wit" ta dafe kai tana kuka domin duk wnn bayanin da takewa kanta ta kasa fahimtar sa... Can kuma ta tsaya "so Aliyu is my cousin brother all rayuwar da mukayi dama he's my cousin. Nayi rayuwa da dan uwana batare da na sani ba"... Sake fashewa tayi da kuka.. Ynx ta fara fahimtar komai ynx komai yake ware mata yanda zata fahimce shi... Kifa kanta tayi jikin gado tana kuka sosai .. Zuciyar ta nayi mata wani irin zafi kanta ya daure gaba daya.. Ita ama kauda maganar su jiddah yanda ya nuna be gane taba shine babban tashin hankalin ta.. Kode bashi

Please Login or Register in order to submit comment