Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunanin daga Ina ball din take ba taga wani ya duka ze dauki ball din.. Yana sanye da kayan sport.. Da suka mugun amsar jikinsa snn suka dace da fatar jikinsa wacce take ita ba baka ba, ba fara ba, ba kuma wanka tarwada ba. Dan tafi ta wankan tarwada haske.. Irin golden brown skin nan ne me shining wacce ta hadu da hutu snn kallo daya zaka mata kasan tana samun kulawa ta musamman... Jikin sa a mummurde dan daga gani yana sport da gym.. Dagowa yy bayan ya dauki ball din ya juya ze tafi.... Ware idanun Fannah tayi ganin guy din jiya ne daya bigeta... Da sauri Fannah tasha gabansa cike da fushi tace "hey you"... Tsayawa yy tare da Zuba mata manyan idanun sa da suke farare tass snn ya dage gira daya alamar what.? ... hakan ya kara kular da ita ganin yanda ya mata cikin kuluwa tace "what's ur fucking business with me why are trying to ruin me?"...... hannun sa daya tusa cikin sumar kansa tare da dan cizar lips dinsa wadan da suke pink sosai.. Kafin a hankali ya bude baki in a very low voice yace "did I knw you?"..... Ji tayi kamar ta kifa masa Mari ganin bnxar tambayar daya mata.... ganin yana niyar tafiya ya barta tsaye yasa ta kara shan gabansa kamar zatayi kuka dan har muryar ta ya fara rawa cike da masifa tace "which kind of stupid question are you asking who knw's you too who even care about you just stay away from me stop pretending that you don't knw what you did the other day and look at what you did to me today" ta fada tana nuna kayanta da suka baci da drink tace "you hit me with ball and you can't even look and say srry which.... " "shhhhhhh" ya katse ta ta hanyar daura soft fingar dinsa a kan tattausa lips dinta.... Ya dan ya mutsa fuska murya kamar amma sa dole yace "don't shout I feel headache"..... Daga haka yy gaba ya barta tsaye cike da mmki da haushi.... Tabi bayan sa da kallo a hankali tace "who is he.. Where is he from".... Ta tambayi kanta... Shide Na farko ba English bane ba Indian bane ba kuma African bane snn ba American bane.. But he looks like irin kyawawan black Americans din nan ko kuma yan sudan kokuma Nigerians din nan da kudi da hutu ya masu yawa... Taba ta akayi shiyasa ta juya da sauri.. Maryam ta gani tace "ya baki shigo ba wai zomu shiga pls" fannah ta fizge hannun ta tace "dallah malama rabu dani ai duk ke kika jamun abinda akamu... Se a lokacin ta lura da kayan Fannah da suka baci.. Rufe bakin ta tayi tana hana dariyar ta fitowa.. "Ya haka Fannah what happened to ur cloth" fara tafiya fannah tayi tana fadin "nayi gaba idan baki biyoni sekin taho"... Binta maryam tayi tana tura baki can kasa kuma dariya ce ke cinta.. Fannah kau tunanin yanda zata rama Abinda wnn bawa ya mata take.. Suna shiga mota maryam tace "wai meya faru" ... Bnx Fannah tayi da ita.. Ta kunna motan hakan yasa itama maryam tayi shiru...... Reverse Fannah tayi... Taji maryam tace "wow what's a handsome guy gsky guy din nan hadu".. Kallon maryam da ta wani dunkule hannu tana ware ido fannah tayi... Kafin ta kalli inda take kallo.... Da mugun mmki take kallon guy din nan na dazu ne.. Batasan lokacin da ta figi motar tayi gadan gadan wajesa ba ba.... A rude Maryan tace "ke are you ohk" tana zuwa gab dashi kamar zata bigesa ta danna masa wata irin hon... Hakan yasa ya juyo yana kallon motar... Fannah ta zuje glass din tana masa wani bnxan kallon dan mugun haushin sa take ji rasa mema zata masa tayi kawai seta dauko tissue din dake gaban motar ta ta jefa masa tace "stupid" tare da jan wani dogon tsaki snn taja motar ta da mugun gudu tabar wajen... Dafe kai maryam tayi kamar zatayi kuka tace "kee me kike tunanin kin aikata what's wrong with you ki jefi mutum ki masa tsaki kinsa kuwa wnn babban wulakanci ne" dan murmushi Fannah tayi dan ko ba komai taji sanyi a ranta... Maryam tace "amma kinsan abinda kikayi ba kyautawa bane ba ko"... Kamar Fannah zata maketa tace "ni abinda ya mun kyautawa ne ai ko" ta fada tana nuna jikin ta... Maryam tace "wai dama shine"... tabe baki Fannah tayi tace "wnn ma ba shine na farko the other day bugeni yy ya tafi ya barni da kwashe takardu yau kuma he hit me with ball and just pass kamar be ganni ba dana masa magana se cemun yy zan saka masa ciwon kai who is he.. who the hell he is da zan zauna yana mun abinda ya ga dama na kyalesa wlh kadan ya gani... Mtswww" dariya sosai maryam tayi tace "well i like this game bana so ya kare dan ina son kara ganin guy din nan da ya hadu over"... Tsaki Fannah tayi tana jin haushin maryam din....
A apartment din maryam tayi wanka ta saka kayan ta snn ta fito dama already maryam ta dafa masu abu me sauki kafin ta fito...zama sukai suna ci.. Maryam ma tsakura kawai take dan rabi waya suke da khalil... Can Fannah ta dago tace "ke madam kici abinci wayar ta isa haka" dan ita Fannah bata cika son waya ba bata ma da wani tym din samarin bare tayi wata waya dasu... Maryam tace "yace ya kusa zuwa ya gudu Nigeria dake ciranin a kasar wasu ta isa haka yakamata a dawo gida"... Dariya sosai Fannah tayi tace "kice masa yazo ya tafi dani"... Maryam ta fada masa snn ta dago tace "yace ai na kusa komawa se ki bini.... " dariya kawai Fannah tayi batace komai ba. Se taji inama ace ta bita.... Bayan sun gama cin abincin maryam tace "ke wlh so nake naje gida I tried alot dan mun gama wadan nan practicals din da zamuyi zan je nayi ko sati ne kokuma idan mun samu intervals"... Fannah na gyara veil dinta tace "Allah ya kaimu" daga haka ta dauki bag da keys dinta tayi gaba maryam ta rakota ta shiga mota ta tafi gida.... Tana shiga parlor hisam dake zaune yana kallon cartoon ya rugo da gudu ya rungume ta.. Itama rungume sa tayi cike da son yaron tace "Autan har ka dawo" gyada mata kai yy.. Ta jasa suka wuce bedroom din mummy... Gaisar da ita tayi.. Mummy tace "ur food" dan ya mutsa fuska tayi tace "mom I've already eaten a wajen maryam may be later ynx bacci nake ji I need some rest"....
Bedroom dinta ta wuce ta canza kayan jikin ta tare da fadawa saman bed dinta mai taushi. Tana lumshe idanu.. Gaba daya se taji duk ba dadi da maryam tace mata zata tafi tasan she will be so lonely dan da ita kadai ta saba se vaneesa da suke good tym sauran sede gaisawa sama sama.. Setaji kamar ta bita itama taje taga family dinsu taje tace masu itace Khadeeja diyar Muhammad Radda suyi yanda zasuyi da ita... Ita de a yanda dadyn ta yace mata da ta matsa tana son sanin danginsu yace sude baban su sunan sa Alhaji Aliyu Radda su yan katsina ne but suna zaune a Abuja sede sallah da duk wani taro na family suna yinsa A katsina suna da family house a Katsina da Abuja.. Alhaji Aliyu Radda ba ba boyeyyen mutum bane sananne ne sosai dayawa an san family din Radda a Nigeria.. Matan Alhaji Aliyu biyu Amina da khadija snn yaran sa takwas biyar maza uku mata... Amina nada biyar (Ibrahim, maimuma, Ahmad, Aminu, da kuma sa'adatu) khadeeja kuma nada (Rabiu, Muhammad se autar su Raheena)... Ibrahim ne baba se maimuna se Ahmad se Aminu shida Rabiu kusan sa'anni ne se Muhammad se sa'adatu da auta Raheena.... Duka matan Alhaji Aliyu basu da matsala mutane ne masu sanyi snn suna hakuri da juna shiyasa suke zaman lafiya ba'a jin kansu Alhaji Radda kau yana da zafi sosai snn yanada tsatstsauran ra'ayi ya matukar son yaransa sosai snn tsaye yake a kansu be yarda kayi ba daidai ba se ka karbi hukunci wnn dalilin ne yasa suke kiyayewa... Kuma kusan duka yaran shi suka dauko zafi Ibrahim, maimuna, Ahmad, Rabiu, Aminu da Raheena duk zafin sa suka dauko Muhammad ne kawai se sa'adatu sune suka biyo iyayen su mata amma duk in sukayi fushi ba kyau...duka yaran sa a kashen waje suke karatu mata ne suke yi a Nigeria Alhaji Radda tsaye yake wajen karatun yaransa both boko and islamiya..duk wanda ya dawo se yanemi mata cikin yan uwa can katsina ya aura .. Hakan kau Akayi.. Baffa dan sunan da suke kiran Alhaji Radda knn.. Yana mugun ji da Muhammad dan shine autan maza da kuma kasancewar sa me hakuri yawanci duka yaran sa kasashen larabawa suka tafi karatu sbd yana ganin kasashen turawan nan lalacewa yara suke shiyasa be yarda ya kai dansa can ba.. But daga kan Ahmad ganin shi yaje America ya samu da kyar ya yarda yaje can ganin har yagama karatunsa be lalace ba yasa ya yarda ya kai Muhammad england da ya samu.. sosai Muhammad ya mayar da hankali a karatunsa be dawo gida ba se bikin yayunsa Aminu da Rabiu lokacin Family din sun dan fara samun yara sbd yaran Ibrahim da maimuna da sa'adatu duk mata matar Ahmad de bata haihu ba.. Da yake kowa yana da katon gidan sa a wajen se yy kamar wata estate dan Baffa baya so yaran sa suyi nisa dashi duk da idan kayi aure zaka iya tafiya kasar da kaga dama ka zauna Amma be yarda ka zauna can ba... A lokacin ne akayo wa Muhammad caa akan daya dawo zasu sha biki dan ga matar sa nan sakeenah datake bala in sosai tana jiransa murmushi kawai yy dan shi kodaya baya son sakeenah halinta be masa bayajin ze iya auren ta sede yasan da wuya yan uwa su yarda yaki auren Sakeenah sede su bazasu gane me ya gani tattre da ita ba kodaya tarbiyyarta bata masa ba hasali ma yana da wacce yake so da suka hadu anan Uk din sede ita din ba muslma bace........

More comments more typing.......
✨✨✨
Urs
Nafisatu😍

........
*💫❤LOVE CYCLE✨*


Written by

*@nnafie🖤*
(Smll but mighty😉)

*writer of*
Saif
Adaan
Wada mafita
Saboda duniya
Love cycle......


Bismillahir rahmanir raheem

💫❤Love cycle.. (3)✨
*Not edited*
Bibdiya a UK suke saune su yan bautar rana ne sun hadu da Muhammad lokacin tana shekarar ta ta farko a sch shikuma yana ta uku sun fara ne daga abota har abin ya zamar masu soyayya.. Bibdiya bata yarda da addinin su ba KO daya ta dade ta naso ta shiga Addinin musulunci sede tana tsoro dan tasan yanda iyayenta suka tsani musulmai har kashe ta zasu iya yi.. Tunda suka hadu da Muhammad ta nuna masa tana son Addininsa ya dauki aniyar ze musuluntar da ita kuma ze aureta..... Wnn knn
Lokacin da ya koma bada jimawa ba sukaje wajen wani malami bibdiya ta karbi Addinin musulunci inda ya saka mata suna Halimatu.... A boye Ta fara Addinin ta a gidan su batare da sanin kowa ba... Sede watarana Muhammad na gida bibdiya tazo wajen sa tana kuka jikin ta duk sahun bulali wani waje duk ya farfashe tace iyayen ta sunce se sun kashe ta inhar bata bar masu gida ba tayi tayi ta fahimtar dasu amma sunki... Daukarta Muhammad yy zuwa gidan su amma se iyayen suka masu korar kare suka ce basu ba ita... Daga nan zamanta ya dawo wajensa gidansa take kwana take komai sede yasan zaman su haka baze yiwuba babu aure hakan yasa ya yanke shawarar idan yaje gida ze sanar da iyayensa game da Halimatu yasan zasu ji tausayinta su aura mashi ita.... Sun dade kafin Muhammad ya samu waya daga gida na cewar family dinsu an haifi maza da aka dade anaso wato jikoki maza dan duk mata ake haihuwan masu.. Matar Ibrahim ta haihu haihuwa ta uku knn maimuna haihuwa ta uku knn ta se Ahmad da yy ta farko wanda se ynx ya samu haihuwa matar sa ta haifi namiji itama se Aminu da be dade da aure ba shima namiji matar Rabiu ce kawai ta haifi mace ita tabiyo maza duka befi kwana bibiyu ba tsakani.. Hakan yasa Baffa ya shirya gagarimun suna dan murnar wnn haihuwa da ya samu a lokaci daya...bikin sunan aka hade su gaba daya shiyasa duk wanda baya kasar ma ya dawo wato Muhammad da Ahmad knn shi dama Ahmad matar sa a can America ta haihu haka ma matar rabiu a Sudan... Dan haka kowa ya dawo wnn biki na suna .. Taro akayi sosai nagani na fada inda yara sukaci sunan su yaron maimuna (Usman) suna ce masa Sultan yaron Ibrahim (Umar) suna ce masa faruq yaron Ahmad (Aliyu) suna ce masa haydar but sbd sunan baffa ne se suke ce masa Amoon, yaron Aminu (Abubakar) anace masa sadeeq, yarinyar (Aisha) suna ce mata humaira.. Ahaka ya saka duk sunayen sahabbai... Alokacin ne aka tasa Muhammad gaba akan ya shirya ba dan saura shekara daya ya gama karatun fa ga sakeenah nan tana jiran shi dan a hada dana Raheenah... Anan ne yake ce wa mamansa yana da wacce yake so ya mata bayanin ta da komai nan tace fafur bata yarda ba karma ya kawo wnn tunanin dan baffansa baxe saurare sa ba hakan yasa yace "to shi ne nan da shekara biyu dan yana so yadan fara aiki a can ne sbd shi tun ma kafin ya gama harya samu upper yanaso yafara aikin kafin yy aure.. Da wnn suka yarda shikam jikin sa yy mugun sanyi yana so daga haka ya kara shekara daya lokacin halimatu ta kara tun ta daga nan tasamu abinyi amma yasan ynx yy aure besan inda ze aje ta ba.... Koda ya koma sosai suka shaku da Halimatu seda ya share shekara har uku be dawo ba ko bikin Raheenah daurin aure kadai ynxo be tsaya sunyi magana a kansa ba..a lokacin kuma ankara haihuwar yara maza Rabiu yy fu'ad Ahmad ma ya kara salim snn sa'datu tayi Habib... Hakade...
Ganin Muhammad yana shirin share shekara ta hudu ne yasa Baffa ya dasa Aya a kansa ya fara tunanin something is wrong duk da yasan aiki yake se yaji gama daya hankalin sa be kwanta da zaman sa can ba aure ba.... Muhammad kau aiki yake sosai kudi sun zauna har yagama gida halimatu ma suna exams dinsu ta karshe ne yanaso ya gabatar da ita ga iyayen sa amma yana tsoro baze iya aure ya barta ba sbd besan yanda zatayi ba zata iya komawa ruwa Ranar kwatsam sega baffa shida Ibrahim a parlor suka iske Halimatu tana karatu... Wani kallo ya mata kafin ya daka mata tsawa yace mata daga da ina... Tsawar da baffa yy ita tafito da Muhammad daga daki... Cak ya tsaya ganin su Baffa... Baffa yace "me wnn take a gidan nan" kasa magana yy gaban sa na faduwa baffa ya girgiza kai yy yace well LA kyau ta to ta gaggauta barin gidan nn kai kuma kafin jibi na ganka a Nigeria amma ma bani kunya... Daga haka suka fice cike da fushi.... Zubewa Muhammad yy a wajen yana kallon Halimatu data rude cike da tsoro.. Yama rasa me zeyi kawai ya yanke shawarar ya tafi da ita ya masu bayani haka kau akayi a ranar suka wuce Nigeria da Halimatu da take cike da tsoro... Muhammad tawa baffa bayanin komai da kudinsa akan halimatu se baffa yace "Allah ze bashi lada amma baze yarda ya aureta ba dan baze iya hada jini da ita ba nan Muhammad yace shifa se ita dan baze iya auran wata ba baze iya rabuwa da itaba sbd shine silar rabuwar ta da iyayen ta nan Baffa yace sede yanemi wani uban bade shi ba... Hakan ya daga hankalin Muhammad gashi duk yan uwansa sun juya masa baya seda Muhammad ya hadasa da Liman da kuma wani malam hamisu snn ya yarda aka daura auren Muhammad da Halimatu sede me a ranar Baffa yace yabar gidan ya cire sa daga cikin jerin yaran sa baya bukatar ganin sa shide be masa baki ba amma baya son ganin sa kusa dashi.. Hankalin Muhammad ya tashi gashi cikin yan uwansa babu me masa magana se sa'adatu da Raheenah... Yana ji yana gani yabar gidan mahafinsa sukazo suka ci gaba da rayuwa da Halimatu tana yawan cewa su su koma su roki gafara yasan zasu hakura yace aa ta bari se sun haihu yasa baffa ze yafe masu... Halimatu bata haihu ba seda suka shekara hudu ta haifi yarta kyakkyawa ya sakawa yarinyar sunan mahaifiyar sa wato khadijah.. Daga nan suka dauko hanyar dawowa Nigeria cike da farin ciki da kuma sa ran baffa ze amshe su.. Lokacin yaran duk sun girma da dan wayonsu .snn an hafi suma mata yan jarirai dasu akwai yusrah, sumayyah, jidda, fareeda, da Hafsat.. Duk kwanaki ne tsakanin su.. .. Yanda Muhammad yy tunani ba haka bane dan baffa cewa yy ya bar masa gida baya bukatar sa baya bukatar ganin sa yacire sa daga jerin yaransa da haka yatafi ya basa waje... Kuma ko yan uwansa babu wanda ya nuna yy farin ciki da ganin sa kodan baffa ya nuna baya bukatar sa knn... Hakan ba karamin cin ran Muhammad yy ba yaji shiko baze kara zuwa wajensu inhar basu neme sa ba yaji kasar ma bayason ta... Tun daga nan suka dawo UK da zama suka cigaba da kula da khadeeja da suke cema fannah sosai Muhammad yake son fannah dan yana ganin bashi da wata dangi sama da ita se matar sa dake mugun yi masa biyayya yana matukar alfahari da ita mace ce mai roko da addini da sanin yakamata ya daga sosai wajen koya mata hausa ta kau rike kamar yarenta.. Snn wasu al'adun hausar ma duk sunayi dan yanaso Fannah ta san yaren ta kuma alhmdullah ta taso cikin sa.. Duk wata soyayyar su na kan fannah dan ita kade suke kallo a matsayin dangin su snn ita kade suka haifa se da ta shekara tara snn suka mata kani Aliyu suna ce masa hisam suke nan su hudu suke rayuwar su se abokanai na mutunci tun mummy na masa maganar komawa Nigeria harta dena dan tasan beso koda Fannah ta matsa tana so ta tasani dakyar yabata lvr ranar kau yini yy suku ku dan kamar an fama masa inda yake masa kai kayi.. Shekara goma shatara knn be taka kasar sa Nigeria snn be ga wani dan uwansu ba... Amma yana dan jin lvrin su kamar Ahmad yana US dan rabi rayuwar sa anan yake rabi kuma a Nigeria shida iyalansa rabiu ma yana dan zama sudan haka ma Ibrahim yakan dan zauna Us amma ba kamar Ahmad ba... Sede basu taba haduwa ba.. Snn babu wanda yasan gidan sa... Daddy yy arziki sosai kamar yanda yasan suma family dinsu sun kara akan dan familyn Radda ya kara bunkasa wurare dayawa ansansa shiyasa shi ya dena amfani da Radda sbd bayaso wani yaji lavarin sa koyasan inda yake haka ma su fannah baya musu amfani da Radda duk da wasu sun riga sunsan sa da Radda amma abin da sauki... Wnn knn
....
Dan lumshe idanu tayi a hankali bacci ya dauketa....
Se gab da azahar ta tashi snn tayi sallah ta tafi dakin mum can suka zauna har daddy ya dawo sukayi dinner tare.. Snn ta koma dakin ta tahau chat... Bata wani jima tanayi ba ta sake kwanciya wani baccin se safiya washe gari friday basu da lectures dama practical ne zasuyi ta an daga se Monday dan wani sabon doctor ne ze zo ya masu bayani akan wani surgery na ido... Weakend dinta maryam ce tazo sun dade suna fira da shirme a gida kafin su tashi suje gidan su Vaneesa daga nan suka fancama yawo cikin gari... Ranar Sunday kuma wuni tayi tana research game da surgery din da zasuyi gobe dan ita tanaso taga tana communicating a class Fannah yarinya ce me kokari da ko a department dinsu masu irin kanta kadan ne....
Monday...
Tsaf ta gama shirin ta ta dauki komai da take bukata ta dauki labcoat dinta ta fita.... Koda taje apartment din maryam har ta gama shirin ta a nan wajen maryam tayi breakfast daganan suka wuce a babban teaching hospital din dake sch din tayi parking suka shiga ciki sunzo gab da zasu shiga lab din ne ganin kowa da labcoat yasa ta fara zare idanu ganin babu tata a hannunta maryam ta kalleta tace "hey girly where is ur labcoat?" Dafe kai Fannah tayi "oh god na barshi a apartment dinki" maryam ta zaro idanu tana duba wrist watch dinta snn tace "huh is already tym bamu san halinsa ba kar mu fita ya shigo kokuma bari na kira maid dita seta shigo taxi ta kawo ko" gyada kai Fannah tayi tana tunanin Allah yasa kar ya shigo dan bata sani ba ze barta ta zauna ba labcoat koko... Bakin kofa suka tsaya suna jira da adduar Allah yasa tazo kafin doctor din ya shigo... Sede addu'ar ta bata karbu ba dan mutane ne suka fara shigowa ana natsuwa cewa gashi nan... Zuwa sukayi suka zauna gaban Fannah se faduwa yake mutane se kallon ta suke ganin bata da labcoat.... Tsit akayi sbd shigowar sa.. Yayinda lokaci guda gaban Fannah ya yanke ya fadi lokacin da ta daura idon ta akan guy dinta da ta gefawa tissues sanye cikin suit blue black da suka matukar amsar sa snn suka dace da fatar jikin sa gashin kansa da yake baki yasha gyara inda ya kwanta lufluf kyawawan idanunsa sanye cikin farin glass se yakara ma fuskar sa wani kyau lips dinsa da suke pink se ya kara wani haske... A tare maryam da Fannah suka kalli juna cike da tsoro.. Kallon sa sukayi jin cool voice dinsa na ratsa kunnen su... "Am Dr. Amah nice meeting you all" a tare akace "welcome sir"... Dan binsu ya rinkayi da idanunsa yana nazarin su kafin ya sauke su akan Fannah.. A lokacin ji tayi kamar ta shide sbd tsoro ko maryam da ba ita ake kallo ba dauke numfashi tayi.. Yana kallon ta da kyau yace "hey you".... Daga mayan idanun ta tayi ganin ita yake kallo yasa Muryar ta na rawa tace "si...sii.. Sir" yace "where is ur lab cloth" wani miyau ta hadiye ganin yanda kallo ya dawo kanta tace "sir.. I.. I.. Forget ..t..it but its on the..way.." Katse ta yy yana daga mata hannu kafin ya dubi sauran yan class din yace "class a medical student is coming into the lab for practical without lab cloth is that student a serious student" a tare akace "no sir"... Juyowa yy yana kallon ta tare da nuna mata kofa yace "out of my class" muryar ta na rawa tace "sir.. am srr... " "I said out my Frnd".. Ya katseta cikin tsawa... Da sauri ta fita tana danne kukan da ya taho mata... Bata son missn class din nan ko kadan ko daya batayi marhabun da cewa wnn shine doctor dinsu ba bata fi minti biyu da fita ba aka kawo mata labcoat din ta dawo tana kuyo cool voice dinsa inda yake bayani cike da kware.. Seda ta saita natsuwar ta kafin tace "permission to join the class sir".. Wani kallo ya juyo yana mata kafin ya dauke kai yace "come in but stay by the door and keep standing ur punishment for coming late".... Tsayawa Fannah tayi tanajin kamar ta tafi

Please Login or Register in order to submit comment