Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

by 9 duk sun hallara a parlon Abie.. "Iyayen nasu ma duk sun hadu.. Kowa kansa na kasa cike da ladabi.. Daddy ya bude masu taro da Addua... Abie yayi gyaran murya yayi sallama snn ya fara magana kamar haka.. "Nasan kowanen ku yasan dalilin wnn taron.. Wato akan wasu abubuwa da suka faru kuma suke kan faruwa..kuma idan aka barshi yacigaba da faruwa za'a iya samun matsala.. Kamar yanda kuka sani munan duk iyayen ku kuma mun dauke ku a matsayin abu daya.. Akwai wadan da muka sani dama tun can wasu kuma se ynx suke faruwa kamar kamar maganar Jiddah, yusrah da kuma kai Aliyu, sann hafsat dakuma Sadeeq.. A yan kwanakin nan kuma abubuwa dayawa sun faru tsakanin Farouq, sultan, kadeeja, fareeda da kuma sumayya, muna cikin hakan kuma sega wata wato Kai Aliyu da kuma khadeeja still,.. Shin dama can kasan ta ne?"..kan Amoon kasa yace "eh Abie".. "But for how long kuke tare wait a ina ma kasanta tun yaushe kasanta".. Amoon yayi kasa da kai "10yrs back".. Bama su Abie kade ba har su sultan seda suka dago suna kallonsa.. "Amoon" Dadd ya furta a kasan labban sa cike da mmkin dan nasa.. Daddy ya ringa kallon Amoon.. Mom kau tagumi kawai tayi tana kallonsa.. Abbu ne yace "ynx kana nufin tun shekara goma da suka wuce kasan inda Muhammad yake but bamu sani ba".. Amoon yace "Abbu tun lokacin da daddy yabar nan I put that on mind that inshaallahu sena san inda yake but i was just at the age at the age of 11... First surgery dina dana farayi a uk.. Na naga Abba yazo dubiya.. Before then nayi kokarin duba duk inda nasan zeyi aiki amma bn samesa ba.. Se luckily yazo duba patient din and nagansa shi kuma be ganni ba... Na bisa har na gane inda yake zaune da kuma inda yake aiki anan na gane cewar ya dena amfani da komai na family din nan dan kar a ganesa ya kuma toshe duk wata hanya da family din nan zasu gansa.. Naso na bayyana hakan amma har lokacin na fuskanci daddy yana cikin radadi sosai shiyasa nabar zancen lokaci lokaci kuma ina dubawa to make sure they're fne..nasan duk fushin da ze dauka dole ze sakko kuma yaji yana bukatar yan uwansa kodan sbd fannah hakan yasa na shiga rayuwar ta ina bibiyarta har ta shiga aji uku a jami'a.. Anan ya kwashe duk abinda ya faru ya fada masu snn duk rayuwar da sukayi ya kara da fadin..sugery din da nayi a spain wanda aka samu matsala shine yasa nabar uk.. Ganin ta hadu dasu farouq yasa koda nagama aikin yasa bn sake neman ta ba tunda nasan zan dawo I don't knw it will take me long kamar haka".. Duk kallon sa suka ringayi tabbas bakowane zeyi abunda yayi ba domin Amoon mutum ne me hikima.. Dadd yayi farin cikin abinda dan nasa Yayi shiyasa a koda yaushe yake alfahari dashi... shi kansa daddy se yaji Amoon din ya birgesa yayi abinda iyayensa basuyi ba ... Abba (Alh Aminu) yace "Amoon kayi kokari hakika kai abin Alfahari ne sede abinda muke so mu sani shine shin kana son khadeeja ne kokuwa sbd wnn family din ne ka shiga rayuwar ta.. ".. Kan Amoon a kasa yace "ina sonta Abba".. Abba ya jinjina kai "to kasan kuskuren ka anan".. Shiru Amoon yayi.. Abba yace "ka tafi kabar ta babu wani kiran waya.. karkaga laifin sultan da farouq dan sun so ta snn ita baka tunanin zata iya canxa ra'ayi akankan ka, ka tafi batare da ka waiwayeta ba ba tare da kayi tunanin wane hali zata shiga ba". Amoon de yayi shiru bece komai ba.. Abba yacigaba "and nasan de kasan da maganar su yusrah da jiddah ko.. Kasan de tun yaushe suke jiran ka anyi maka maganar amma kayi bris damu har ynx bamuji wani feed back daga gareka ba.." Shiru Amoon yayi bece komai ba.. Abba yace "snnku su farouq ya kuke ciki akan batun wnn yarinya" farouq yace "Abba ni na hakura zan auri sumayya inasonta".. Abba ya jinjina kai domin yaji dadin maganar farouq.. Ya dubi sultan.. Kan sultan kasa yace "ina sonta Abba.." "Toh fareeda fa?".. "Zan aure su duka Abba.." Sultan ya fada yana kallon Amoon da shima ya dago yana kallonsa da idanun sa da suka rikide.. Dauke kai sultan yayi yanajin duk abinda za'ayi sede ayi kodan sbd maganar da ya gaya masa ranar da fannah bata da lafiya da kuma farouq ranar a lambu... Abba yace ku tashi kuje zamuyi magana dasu yaran sede inaso dan Allah kada wnn yasa ku samu matsala da junan ku.. Duk godiya sukayi... Amoon ya fice ba tare da ya kalli kowa a cikin su.. Sadeeq ne yayi kokarin kiran sunan sa.. Juyowa Amoon yayi ya kalli sadeeq da Farouq karasawa sukayi inda yake sadeeq sadeeq na kallon Amoon yasan tabbas tunda yayi wnn dawowar yana cikin damuwa.. Yace "brother pls take it easy.. Kar wnn ya zama silar daze kawo matsala tsakanin mu".. Murmushi Amoon yayi sede baya son magana dan ransa a mugun bace yake.. Farouq yace "kayi hakuri da duk abinda ke faruwa inshaallahu everything will be settle..".. "Settle".. Amoon ya maimaita . . se ya danyi murmushi "everything will be settle amma idan wancan ya cire fannah a ransa... Sbd fannah tawace ni kade ba'ayita dan wani mahaluki ba"... Ya fada yana nuna sultan da fitowarsa knn.. Sultan ya karaso yanawa Amoon wani kallo snn yace "kai kana tunanin zanbar fannah ne sbd ina tsoranka let me tell kai baka isa ba kasan da kana sonta zaka tafi ka barta har tsawon lokutan nan kuma snn kana zuwa lokaci daya sena barma bayan muma muna sonta kamar yanda kk sonta".. Amoon ya dunga kallon sultan boiling from inside ya nuna sa yace "sultan Raddah na kula rigima kk nema nasan kasan nine Amah tuntuni but because of ur selfish ka tusa kanka, but get in to ur head idan ka cika shigewa fannah duk abinda nayi maka kaikaja".. .. Daga haka yabar wajen.. Sultan ma tabe baki yayi yabar wajen ....
Koda Amoon.. Ya shiga gida bebi takan kowa dake parlon ba yayi hayewar sa sama.. Chucu ta dubi mammah "mammah yaya yana cikin damuwa sosai".. Mammah ta lumshe idanu sosai take tausayin dan nata be cika saka abu a raiba wanda be damesa ba tunda taga ya damu tasan tabbas yana tsananin son fannahr nan.. Tasan ynx haka ko abinci da wuya yaci.. Dadd ne ya shigo.. Nan yake fada masu duk yanda sukayi da yan uwan nasa ... Mammah tace "I don't want to involved my self but yakamata a duba Amoon yana cikin damuwa sosai". Dadd yace "suma sauran ai kinsan suna cikin damuwa sbd farin cikin sa a baza'a kuntatawa wasu ba".... Ranar tunda Amoon ya shiga daki be fito ba babu yanda mammah, saleem da chucu basuyi dashi ba akan ya bude kofa amma yaki da kyar mammah ta samu ya bude shima ita kade ta shiga su chucu tsoran shiga suke sbd abinda zeje ya dawo..
Tashi chucu tayi gidan su Fannah taje a dakin ta tasameta .. Tana ganin chucu ta saki murmushi.. Chucu ta zauna daga gefen gado.. "Duk kin manta damu ko kamar duk fushi kike damu".. Fannah ta girgiza kai ko daya wlh kawai bana jin dadi ne".. Chucu tayi tagumi tana kallo fannah "yanxu dama all this while wnn Amah din da ake magana ba wani bane yayanane".. Dan murmushi fannah tayi se kuma tace "and that same Amah shine Amoon din da Yusrah da jiddah suke magana akai".. Chucu tace "kinsan yaya yasha fadamun cewa akwai khadeejar da yake so wlh yaya ke kade yake so".. Fannah tace "chucu ina cikin rudani". Chucu tace "Fannah yaya Amoon yana cikin damuwa sosai tunda yayi wnn dawowar yaki sakewa da kowa ko ynx yana can ya rufe kansa a daki"... Fannah ta kurawa chucu idanu can kuma tace "me kikeso nayi to nima fa kaina Allah kade yasan damuwar dake zuciyata".. Chucu ta mike pls koyaya ne kizo muje ki gansa nasan ze rage damuwar sa wlh duk yau bnga ya fito ba dan Allah kizo muje kila idan kece ya bude dakin.. Gaban fannah ya rinka faduwa tana tunanin wane hali yake ciki kuma.. Girgiza kai fannah tayi "srry chucu bazan iya zuwa ba". Chucu nason brother dinta sosai tana matukar damuwa idan har yana cikin damuwa tasan ze iya shiga wani hali... Chucu ta share hawayen ta "dan Allah fannah wlh tsoran damuwar yaya Amoon nake".. Fannah ta girgiza kai tana jin yanda zuciyar ta ke beating.. Mikewa chucu tayi zata tafi har ta kai kofa fannah ta dakatar da ita.. Sbd yanda zuciyar ta ke bugawa bazata taba natsuwa ba setaga halin da yake ciki....
Saleem kade suka iske a parlor yana ganin su yace "yauwa gwanda da Allah ya kawoki Pls dan Allah yana daki". Kallon sa Fannah tayi snn ta kalli chucu.. Chucu tace "mammah na gidan Baffa".. A hankali fannah ta fara hawa stairs gabanta na mugun faduwa.. Kofar dakin da take tunanin nasa ne ta tsaya jin kamar kafar ta bazata iya daukar ta ba yasa ta dafe bango.. Can de ta aro jarumta tayi knocking.. Jin shiru yasa ta tura kofar dakin a hankali.. Dan lumshe idanu tayi jin daddan kamshin turaren sa wanda ke mugun kwantar da hankali.. Bude idon tayi ta daura akan bayansa.. Yana zaune ya juya baya yana kallon window.. Kafin tayi magana taji yace "welcome wife".. Fannah ta jingina da kofa tana sauke ajiyar zuciya "what's wrong with you".. Juyowa yayi ya zuba mata idanunsa da gabadaya suka rikide wanda seda ta tsorata.. Yace "kece".... "Ni kuma?".. Ta tambaya "yes you're".. Ta zuba masa idanun ta.. Ya mike tsaye.. "Sbd ke din tawace ni kade amma ana a shiga gonata".. Fannah ta dauke kai "am srry to say amma ni dukan ku babu wanda zan aura na hakura da ku duka".. "Kin hakura damu kikace?.. Dama mu din har yawane damu? Ai inde ina raye babu wanda ya isa ya aure ki sbd ke din mallaki nace".. Idanun Fannah suka cika da kwalla "no Amoon kayi hakuri Amma bazan iya auren ka ba sbd ko badan sultan ba akwai jiddah sann akwai yusrah inason kwanciyar hankali da zaman lafiya kuma rabuwa da dukkan ku shine ze sama mana zaman lpy".. Bata san ya akayi ba kawai se gani tayi ya fizgota idanun sa sun rikide sosai "farin cikin su, kade kike so bnd nawa?, kwanciyar hankalinsu kade kikeso bnd nawa?, tell me ki fada mun Fannah talk to me...".. Fashewa da kuka Fannah tayi dan ya mugun bata tsoro a yanayin da yake magana.. Rugume ta Amoon yayi sosai ta kara karfin kukan ta.. He hug her very tight.. Muryan sa so broken ba kamar dazu ba yace "I love only you, I love you Khadeejah you're my peace of mind, don't say that again pls kasancewa dake shine kwanciyar hankali na pls love only me.. Zuciyata bazata iya daukar ganin ki da wani ba you are irreplaceable pls don't say that kin hakura dani again pls Fannah".. Yanda yake maganar kade ya isa ya tabbatar maka har zuciyar sa ne.. Tace "you didn't consider halin da zan shiga ka tafi ka barni no phone call nothing nothing bayan kasan inda nake".. Ya kwantar da kansa saman nata still hugging her a hankali yace "srry love pls love only me".. Kokarin turesa ta farayi jin yanda ya matse ta ga yanda zuciyar sa ke bugawa.. Muryar sa can kasa yace "no pls no Khadeejah".. "It's haram.."... Dan Murmushi yayi yana kara kwanta da kansa a nata yace "really haka fa.. Ashe ba'ayi auren ba... But suna so su rabu mu why not ayi a wuce wajen kawai kinga dole su auramin ke"... Sosai Fannah ta turasa yy baya ita kuma ta matsa tana zare idanu dariya Amoon yayi wanda har seda Fannah ta tsaya tana kallon sa.. Can kuma seta juya zata tafi yayi saurin kamo hannun ta.. "pls karki tafi".. Noke kafada tayi shi kuma ya langwabar da kai "love wai har ynx baki so na ne".. Kamar zatayi kuka tace "mummy fa batasan ina nan ba".. Ya ware idanu "harda satan hanya ko kin kasa natsuwa"... Da sauri ta rufe fuskar ta da tafin hannun ta.. Hakanan kawai taji wnn moment din da suke tare ya mata dadi but she have to go.. Yace "ki bari naci abinci se mu tafi"... Ta ware idanu "no pls kar mummy ta nemeni". Ya harareta "se kice kina dakin wanda zaki aura".. Fannah ta wani zaro idanu "wanda ma zan aura tabb".. Yana kallon ta with smile yace "umm mene a ciki".. Nide gsky tafiya zanyi.. Ya kamo hannun ta ta fizge.. Yace "ohk muje na karaki".. Fannah taji dadi da taga babu kowa a parlorn shikam Amoon haka kawai yaji ajikin sa ana kallon su kuma yasan su chucu ne.. Layin babu kowa daedae gate din gidan su Fannah motar su sultan ta wuce su da gudu su bama su kula ba.. Yana can yana tuna mata da farko haduwar su.... Yusrah ta dubi sultan dake driving ya nuna kamar ma bega su Amoon ba tace "yaya, ya Amoon ne fa nagani tare da Fannah nashiga uku knn da gske yaya Amoon son ta yake.. Wayyo Allah na wlh bazan yarda ba.". Sultan de ko kallon ta beyi ba bare tasaka ran ze bata amsa

More comments more typing......
Urs
✨✨✨
Nafeesatuu....😍😍
.....
*💫❤LOVE CYCLE✨*


Written by

*@nnafie🖤*
(Smll but mighty😉)

*writer of*
Saif
Adaan
Wata mafita
Saboda duniya
Love cycle......


Bismillahir rahmanir raheem

💫❤Love cycle❤ (25)✨
Da kuka ta yusrah ta fada jikin mom.. "Yau na bani yusrah lpyn ki kuma"... Sultan ne ya shigo mom na kallon sa tace "me tayi maka".. Ya ware hannu "mom babu ruwana ita da Amoon ne fa"... Mom ta fitar da iska tace "wani abu yayi mata ne". "Wlh yaya Amoon son fannah yake shknn nide bayan kince na kwantar da hankali na amma wlh mom baki gansu ba yau wlh inason sa".. Tashi kawai mom tayi dan ita ynx babu abinda zatace akan wnn lamari.. ..
Amoon na idar da sallah gidan baffa ya wuce .. Dakin umma ya shiga har lokacin tana saman abun sallah zuwa yayi ya kwanta saman gado ya lumshe idanu.. Umma na gama addu'o'in ta ta juyo tana kallon sa "lafiya kazo ka hayemun saman gado nifa wnn karon bana gayyar ka dan na kula bada mutumci ka dawo ba".. Amoon ya tashi zaune "umma pls kima Abie magana wlh fannah nake so".. Umma ta tabe baki "kaini raba ni da shirmen ku.. Inade fada maku gara ku samawa kanku mafita tun kafin baffan ku yasan da wnn zancen dan inde fada zaku cigaba dayi to wlh sede duka ku rasa".. Yace "umma dan Allah ki dena sakamun zancen sa anan shima rigima kawai yake nema"... Umma tace "rigima? To naji su yusrah ai kasan baza'a barsu ashara ba".. Amoon ya bata fuska "umma nazo maki da maganar fahimta kina kawomin wata magana.. Akwai wacce nace ta jirani ne... Kum.. " Maganar sa ta katse sbd shigowar Mom.. Tana kallon sa da kyau tace "bakace su jiraka ba ko? Ai ba kaine ka dora masu sonka ba.. Me ka dauki kanka ne Amoon to wlh baka isa ba bazaka maidamu shashashai ba. Maganar fannah kuwa idan bakayi wasa ba gaba dayan ku seku rasa ta".. Tashi Amoon yayi ya fice a wajen kofar fita yaci karo da yusrah.. Kewaye ta yayi ya fice.. Shiga tayi da sauri.. Maganar da Mom takene yasa ta tsinci wani abu a maganganun nasu.. Juyawa tayi tabi bayan Amoon da sauri.. Tana zuwa gab dashi ta kirasa hakan yasa ya tsaya ta karasa kusa da shi.. "Yaya dan Allah kayi hakuri pls yaya".. Yana kallon ta da kyau yace "inaso ki nemi wani wanda kikeso bani ba" daga haka ya wuce ya barta a tsaye ta bisa da kallo.. Se kuma ta fashe da kuka.. "Wlh. Babu wanda nakeso se kai kuma kai zan aura"....
fannah tun ranar da yusrah tazo akan maganar Amoon bata kara ganin ta ba daga ita har jidda tasan tabbas suna fushi da ita fareeda kam ynx komai ya wuce.. Ana fitowa sallahr juma'a ta nufi gidan baffa tare da hisam da dawowar sa knn.. A parlorn ta iske hafsat.. Tana ganin ta tace "oyoyo ya jikin naki".. Fannah tace "da sauki..".. Jiddah ta dake ciki ta nuna kamar ma bata ganta ba.. Itama din wucewa tayi dakin mama ba tare data kula jiddah ba.. Bayan sun gaisa da mama ta wuce dakin umma.. Yusrah na ciki Amma ta nuna kamar bata ganta ba... Itama bata kula ta ba ta gaisar da umma dake tsokanar ta.. Ta gaisar da da Mom data shigo ynx.. Snn ta mike hafsat tace "daga zuwa" fannah tace "wlh ko" daga haka ta nufi kofa.. Haka kawai yanda jiddah da yusrah suka mata setaji abun yayi mata ciwo.. Kuma ita bata ga laifin ta ba sbd kamar yanda suke bata lvrin Amoon haka take basu na Aliyu dan kuma kawai ya zaman to duk Amoon ne se suji haushinta....
Tana fitowa compound ta hadu da sultan daya fito daga motar sa... Sanye da manyan kaya da alama dawowar sa knn tun fitar sa massalaci... Yana ganin ta ya karaso wajen ta.kanta kasa ta gaisar dashi.. Ya amsa yana kallon ta.. Har zata wuce yace "fannah"... Tsayawa tayi.. Ya karaso wajenta.. Yace "kawai tunda Amoon ya dawo kika kuma gane shine Aliyun ki kawai ki watsar damu ba tare da kinyi considering halin da zan shiga ba bayan kuma kinsan ina sonki".. Fannah ta sauke ajiyar zuciya.. Kafin tace "I've already made it clear that na fasa auren ka yaya sultan I think be kamata ace haryanzu muna wnn maganar ba".. Zeyi magana kawai aka bude gate.. Gaban fannah seda yayi wani mugun faduwa ganin motar Amoon ce ta shigo... Kasa fannah tayi da kanta hoping kar a samu wata matsala.. Yana zuwa saitin su yadan zuje glass din ya kalleta snn ya kalli sultan daya wani hade rai.. Snn ya Kara gaba yaje parking yayi..
Fannah ta dubi sultan.. "Se anima".. "Muje na rakaki"... Girgiza kai tayi.. Tana kallon Amoon daya fito.. Yana sanyen cikin mayan kaya da sukayi mugun karbar sa haka hular ta zauna daram akan kwantaccen gashin kansa.. Duk da yanda gaban ta ke faduwa be hanata ganin yanda kyawusa ya kara fitowa ba.. Sbd bata taba ganin sa da manyan kaya ba.. Se taga ya Kara wani kwarjini.. Yana karasowa ba tare daya kalli farouq ba yayi mata kas kas.. "Kallon fa? Nayi maki kyau ne". Fannah ta tsuke fuska.. Kamar zatayi magana seta tuna sultan na wajen dan tunda Amoon ya fito daga mota ta manta da tsatuwar sultan a wajen.. Tayi kasa da kanta tana wasa da fingers dinta.. Amoon ya dubi sultan da zuciyar sa ke tafarfasa.. Yace "sannu".. Dauke kai sultan yayi.sbd yasan wulakanci ne kawai irin na Amoon... . Amoon ya ware hannuwansa.. In don't care yace "anyway.. Pls give us space.. Zanyi magana da feature wife".. Sultan nayi masa wani kallo yace "kai awa naga tare ka ganmu".. Amoon yace "what tare na ganku? Are you not stupid of ur statement? Na ganka tare da fannah bn damu ba cikin hankali nayi maka magana and you're telling me tare na ganku?".. Sultan yace "yes Amoon na fada maka do ur worst ita fannahr auren ta kayi dazaka mun iyaka da ita.. Amoon bari na fada maka kai baka isa kasaka mun rules ba kaman yanda kk sonta nima haka nake Sonya"... Tuni idanun Amoon sukayi jawur yanaji kamar ya kaima Sultan duka..sbd yanda yake fadin yana son fannah.. Ya nunasa da yatsa "sultan am warning you for last tym wlh koda wasa ka kara furta kana sonta zakaga abinda zan maka. Fannah tawace ni kade.. Ina gargadin ka da ka dena shiga gona ta inde kanason zaman lfy.. Idan ba haka ba.. Se kuma yayi kwafa... Sbd yanda zuciyar sa ke tafarfasa.. Shi me danne abubuwane amma zuciyar sa ta kasa jure ganin fannah da wani.. Fannah kam harta fara hawaye ganin yanda duk suka harzuka suna fada da junan su a kanta.. A harzuke sultan yace "an shiga gonar taka Aliyu do what ever comes to ur mind do it pls kai baka isa kahanani abinda nayi niyya ba".. Yanda Amoon ke kallon sa da jajayen idanun sa kade ya isa kasan zuciyar sa a kusa take.. Ganin haka yasa fannah kamo hannun sa "pls yaya Aliyu stop it banaso".. Sosai kuka ya kwace mata.. Ko lura da Abbu da Abba basuyi ba sede ji kawai sukayi abbu na fadin "subhanallahi what's happening here" dukkan su huci kawai suke kamar zasu danbatu.. Yanda Amoon ke fitar da nufashi kade zakasan jira kawai yake sultan ya kara wata magana.. Abba ne yayi masu tsawa "wai ba magana ake maku bane"... Duk basu tanka ba har lokacin kallon juna sukeyi a kufule.fannah de na gefe kuka kawai take.. Su jiddah dake parlor duk sum fito suna kallon ikon Allah.. Dama yaya Amoon da farouq suna da wata irin zuciya sede kafin kagani se ransu yayi mugun baci.... Mom ce ta daka masu tsawa.. Tare da fadin duk shigo ciki.. A hankali duk suka juya suka nufeta babu jima wa segasu Abie duk sun dawo harda baffa.. Su farouq ma duk ynx suka shigo... Baffa daya gane ma idonsa ya bukaci yana son ganin su Amoon har da farouq da sadeeq ... Da ita kanta fannahr snn da duka yaransa.. Su jiddah de nacan na kuka dan hankalin su yayi matukar tashi...
Baffa ya bukaci jin duk abinda ke faduwa.. Sadeeq ne yayi masa bayanin komai... Baffa ya jinjina kai.. Snn ya dubi yaran nasa yace "so duk wnn abun na faruwa amma bn taba sani ba?.. Ya dubi Amoon yace "kana sonta Aliyu?".. Gyada kai Amoon yayi snn ya dubi sultan yace "kaima kana sonta? " sultan ya gyada kai"..... Wani dan murmushi baffa yayi.. "Good and shine kuka aje duk wata alakar dake tsakanin ku kuke fada da juna". Shiru sukayi babu wanda yace komai.. Ya dubi fannah da har lokacin take hawaye yace "khadeeja ki kwantar da hankalin ki inshaallahu babu me kara daga maki hankali a cikin su.. "To baffa".. Daddy de se kallon diyar tasa yake tayi mugun basa tausayi yasan tana cikin rudani sbd duk bata saba da irin wnn ba...... Baffa ya dubi su Amoon.. "Aliyu da kai da usman tunda abun haka ze zama dukkan ku babu wanda ze aure ta zan sama mata wani daban.". Dago kai Amoon yayi yana kallon baffa zuciyar sa na bugawa.. A zuciyar sa ya furta "wani.." Ita kanta seda taji wani jiri.. Ta dago idon ta tana kallon Amoon bama ta kalli sultan ba bare ma tasan halin da yake ciki.. Suna hada ido ta sauke idon ta a kasa jin wasu sabbin hawaye na zubo mata... Baffa ya cigaba.. Kai Aliyu ga yusrah nan da Hauwa'u kasan da zancen su .. Tunda haka ne abun se ku shirya soon za'ayi dukan ku baiko Usman ga fareeda nan farouq ga sumayya nan sadeeq ma ga hafsat nan.. Khadeeja kuma zan samo maki wani inshaallhu kinji.. Ta gyada kai.... Nan yace "na sallame ku"... Duka tashi sukayi suka fita.. fannah bata saurari kowa ba gida kawai ta wuce.. Bama ta kula da mummy dake parlor ba ta wuce sama.. Fadawa saman gadon ta tayi tana kuka sosai fuskar Amoon kawai ke fado mata.. Kuka take sosai ta rasa dalili......
Mummy bata tashi tabi fannah ba har lokacin tana parlor kawai ta barta ne tayi kuka me isarta.. Daddy ne ya shigo.. Mummy tace "wai daddy meke faruwa ne".. Zaunawa daddy yayi.. "Tana

Please Login or Register in order to submit comment