Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa ya lumshe.. Yana sauke numfashi.. Ynx 9:30pm.. Nan da 48hrs inde har maganar baffa ta tabbata Fannah ta zama matar wani ba tasa ba knn.. Hannu yasa ya dafe saitin zuciyar sa dake masa wani kalar zugi.... Tashi yayi ya sakawa kofar key snn ya dawo ya kwanta da sauri sbd jirin dake dibar sa.... A ranar Amoon beyi bacci ba yanda yaga rana haka yaga dare.. Sede ya bude idon sa ya kalli agogo snn ya maida.. Se addua kawai yake cikin zuciyar sa.. ga kirjinsa da kansa dake mugun sara masa .. Kafin Asuba zazzabi ya rufe sa sosai... Da kyar ya iya tashi yayi sallahr Asuba.. A daddafe snn ya koma ya kwanta yana rawar sanyi.. Da kyar ya iya janyo blanket ya rufe har kansa... Yanaji anayi masa knocking Amma be motsa ba... Haka aka rinkayi aje a dawo amma yaki tashi.. Muryar saleem yaji yana cewa ya bude amma yaki koda motsawa.. Kawai de ya bude idanun sa ya kalli tym yaka goma saura.. Babu jimawa can yaji muryar Abie da Dad dinsa... A hankali ya tashi kansa na juya masa.. Ya murda key din ya dawo ya sake kwantawa.. Su Dad suka shigo harda Baffa.. Kallo daya Amoon yayi masu ya maida idon sa ya rufe.. Baffa ya dafa kansa... "Subhanallah kira doctor".. Abban sageer ya dauki waya yana kiran doctor... Mom ta shigo rike da breakfast.. Kamar Amoon baze tashi ba se kuma ya tashi bisa ga umarnin Abie.. Mom ta basa break din ya karba yanaci kawai amma ba da son ransa ba shi yama fi so su fice daga dakin gaba daya....
Bayan doctor ya gama dubasa ya basa duk wani taimako daze basa dan harda allurar bacci ya masa ga karin ruwa.. Snn ya fito yana kallon su baffa.. "Jinin sa ya hau sosai na masa allurar bacci tare da magunguna inshaallahu zasu taimaka masa ynx yana bukatar hutu ne bnd hayaniya snn se an kula sosai gsky".. Daga haka sukayi masa godiya ya tafi akan zuwa an jima..
Yau tunda Fannah ta tashi kanta ke yi mata ciwo ko breakfast din da mummy ta kawo mata bata ci ba.. Idan ta tuna gobe za'a daura mata aure se hankalin ta ya tashi.. Hawaye yaki tsaya mata.. Tunanin Amoon kawai take bata san wane hali yake ciki ba.. Kilan da taga wani ma ta tambayesa se hankalin ta yadan kwanta .... Tashi tayi duk da yanda kanta ke sara mata ta fita zuwa main parlor babu kowa harta juya zata koma taga farouq ya shigo ynx.. A hankali tace "yaya farouq".. Dagowa yayi.. Se kuma ya karasa wajen ta "sister are ohk".. Tace "kaina ke ciwo".. Yaji tausayin ta dan yasan tana cikin damuwa.. Yace "sannu ina zuwa".. A hankali tace "Yaya Amoon fa".. Farouq ya danyi murmushi "yananan".. Tace "kaini wajensa".. Yace "karki damu yana lpy fa".. Kamar zatayi kuka tace "ka kaini wajen sa".. Ynx haka daga dakin Amoon yake ko shiga ba'ayi yace "lil sis calm down baya nan ai".. Ita hakanan taji duk bata yarda da Farouq ba.. Ta fara hawaye "dan Allah take me to him I want see him".. Dan jim yayi se kuma yace "ohk"... .. Gaba yayi tana binsa a baya.. Har suka karasa kofar dakin Amoon.. Ya kalleta ya nuna mata window "zaki iya ganin sa but don't make any sound"..gaisar sa su sadeeq tayi snn a hankali ta leka tana kallon sa ta windon.. Dan rufe bakin ta tayi. Tana kallon sa yana bacci.. Sosai tayi kokarin ganin ta hana kanta kuka sede hawaye dake zuba sharrr... juyawa tayi tana kallon farouq "pls let me in I promise not to make any sound".. Girgiza mata kai yayi.. Itama ta girgiza kai "pls don't say no".. Zeyi magana mammah da shigowar ta parlorn knn tace "farouq let her"... Da sauri Fannah ta juya tace "thank you mammah".. Tura kofar tayi a hankali ta shiga tana kallon sa.. Idonta na kansa har lokacin hawaye take.. Ganin bata iya jurewa ne yasa ta juya zata koma sbd kukan dayaci karfin ta... taji muryar sa a shake yace "Khadeeja".. Cak ta tsaya.. Se kuma da juya ta karasa kusa da gadon tana kuka tace "Aliyu"... Bude idon sa yayi da sukayi jawur kamar an zuba jan abu a ciki yana kallon ta.. Fannah bata san sanda ta zube bakin gadon tana kuka ba "Aliyu what's this menene haka dan Allah"... Maida idon sa yayi ya rufe ba tare daya Amsa ta ba... Hannun sa ta kamo ta runtse sosai cikin nata, "please Amoon talk to ne dan Allah kayi magana" ta fada cikin kuka sosai... Gyara kwanciyar sa yayi yana facing dinta... Kafin a hankali yace "may be that's how our destiny is, may be kedin ba matata bace, I love you with every breathe of my life but babu yanda muka iya da kaddara.. Haka Allah ya tsara mana".. Ta girgiza kai tana kuka sosai.. Ya runtse hannun ta sosai cikin nasa, yace "stop crying pls stop".. Ya fada muryar sa a raunane".. Kara fashewa da kuka tayi sosai.. Yace "Fannah".. Dago wa tayi tana kallon sa da idanun ta da suka jike da hawaye.. Yace "pls pray for me".. Tashi Fannah tayi da sauri ta juya tana kuka sosai ta fita daga dakin.. Amoon ya tashi zaune.. Cizge karin ruwan da akayi masa yayi ya shige toilet... Su farouq de har lokacin suna tsaye basu bar wajen ba.. Kuma duk suna jinsu.. Cike da tausayin su.... Ruwa ya watsa ya fito rufe kofarda key yayi ya dawo ya kwanta... Yanaji ana knocking ya tashi cike da karfin hali yace "pls I need to be alone let me bana son ganin kowa you should all go away go away pls".. Daga jin muryar sa kasan karfin hali yake..
Da kyar Fannah ta karasa daki sbd wani jiri dake mugun dibar ta.. Ta zauna saman gado tana sauke numfashi "no pls Amoon stop".. Ta fada muryar Amoon na dawo mata.. Se kuma ta fashe da kuka sosai "ta janyo pillow ta rungume "I love you Amoon you're the only person I love"..tashi tayi ta karasa wajen daddy daya shigo ynx ... "Daddy pls Amoon ze mutu pls dadd I love him wlh shi nake so.. " se kuma ta rugume daddy tana kuka sosai...
Kafin dare zazzabi ya rufe ta sosai kuma har lokacin bata bar fadin Amoon ba....
Amoon kau duk yanda Akayi masa knocking Akan ya bude kofar sa a ranar kin budewa yayi.... Hankalin mammah ya tashi sosai.. Haka mummy dan Fannah se kyarma take jikin ta yayi mugun zafi... Ita kanta fareeda zazzabin dake.. Sultan kau ba'a magana dan shi bema san wacce za'a aura masa ba. Ya rasa inda se saka kansa sbd tashin hankali gashi fareeda taki koda saurarensa..chucu kam yanda kasan harda ita za'a aurawa wanda bataso.. Har su sadeeq hankalinsu ba'a kwance..yake ba.. Dan sadeeq na wajen fareeda shike kwantar wa kanwar tasa da hankali... Dayawa a cikin su yanda sukaga rana haka suka ga dare.. Se bayan asbah snn bacci ya dauke Fannah shima seda aka mata allurar bacci...
Friday kamar yanda baffa ya fada sega baki Anata zuwa domin daurin aure.. Kuma har ynx Amoon be bude kofar sa ba bugun duniya anyi amma yaki ya bude gashi a jiki yabar key din.. Har dad dinsa seda yazo Amma yaki.. Kuma duk yana jinsu yayi biris dasu... Wajen karfe 12 baffa da kansa yazo tare dasu Abie.. Amma Amoon yaki budewa Dad daya fusata yace "Amoon don't let me repeat my self I said open this door".. Abie yace "let him hakan bazesa a canza komai ba kuzo muje".. Baffa dama already yayi gaba tun kafin dad ya fara fada... Seda ya tabbatar duk sun tafi snn ya tashi toilet ya shiga ya watsa ruwa ya fito ya saka kayansa.. Yasan dayawa mazan gidan ynx kowa ya fita sbd sallahr juma'a.. Inda yayi mmkin ganin gidan da mutane dayawa.. Ta baya yabi ya fita. Ya shiga motar sa
Wani masallacin daban ya tafi ba wanda ake daurin auren ba.. Dakyar ya iya driving kansa zuwa can.. Ana yin sallah ya juyo ya dawo gabansa na wani irin faduwa.. bacin baze iya dogon drinving ba da yau se yabar garin nan.. Hakanan de ya daure yayi driving zuwa gida.. Tun kafin ya karasa yake ganin motoci a kofar get din gidan zuciyar sa kamar ta fito tsabar yanda take bugawa.. Shiknn ynx Fannah ta zama mallakin wani ba tasa ba.. Jiyayi baxe iya karasawa ba yayi parking anan yana sauke numfashi da kyar da kyar.. Kafafunsa har wani rawa suke masa... Kamar ance ya daga kansa.. Ya hango duka angwayen sunnufo motar sa.. Kowa yaci gayu aciki shi kade ne babu..... Ya maida idon sa akan yusuf.. Yana kallon sa na second ya maida kansa a jikin sitiyari.. Baya fatan su karaso inda yake dan komai ma ze iya faruwa.. Suna karasowa sageer yayi knocking glass dinsa "common wnn wane irin Ango ne".. Kamar Amoon baze bude ba se kuma ya bude ya fita idanun sa jawur yana kallon su... Farouq yace "oh god kaikuma haka kake murnar taka wadan nan jajayen idanun fa".. Amoon ya hadiye wani abu da kyar yana kallon Yusuf da jajayen idanunsa... Ganin haka yasa yusuf saurin mika masa hannu "congratulations Angon Fannah.. Khadeeja is urs finally Happy married life bro".. Seda jijiyar kan Amoon ta dena aiki for some seconds jin Abinda yusuf ya fada.. Sageer yace "miji Fannah finally ka auri Fannah yaude an daura auren Aliyu Ahmad da khadija Muhammad munan duk sheda ne sadaki kuma ga ATM dinka mun cira duba wayar ka zakaga debit?" Sageer ya fada yana nuna masa Atm... Amoon ya rasa wani tunani zeyi yace "wai how comes tayaya kumin bayani".. Sageer yace "anki din waya hanaka zuwa".. Farouq yace "bari na fada maka... Ganin kuna ta rigima kun manta duk wani zumunci tsakanin ku akan mace kuna fada.. Shine Abie yace he have to punish you guys be kamata ku rinka manta wa da zumunci kan wani dalili ba.. Yusuf family friends ne shida Abbu kanwar hafsat yake so lubna hakan yasa Abie ya kawo sa.. Dukanmu bamu san meke faruwa ba se jiya abie ke fadamana nida sadeeq.. Idan kaga yanda sultan yazo yana kuka akan fareeda jiya sekasha mmki.and yau kuma aka aura masa ita fareedar kaikuma Fannah...Amoon yace "yusrah fa".. Sageer ya tabosa ya nuna kansa "nine nan mijin idan bazaka manta ba I once told you inason yusrah but bn taba fada ba se wnn zuwa.." Ya dafe kai "but beb din nan ta bani ciwon kai dayawa sena rama nasha wahala se kuma lokaci daya tazo tacemun ta Amince.. Inajin ciwon kai ka bata".. Murmushi Amoon yayi se kuma ya rungume farouq cike da farin ciki dayama kasa fasaltawa tabbas abie da duka sauran iyayen su sun kyauta da suka tunatar dasu suka kuma hukuntasu akan abun da suka manta .. Sultan ya rungume Amoon "srry bro I caused us all this I'm srry".. Amoon na buga bayan sa yace "am srry too bro".. Idan kaga fuskar kowa acikin su kasan yana cikin farin ciki.. Amoon ya juya yaba yusuf hakuri.. Amma fa beyi danasanin abinda yayi ba sede yaji kunya.. Nan su sageer suka rinka tsokanar sa.. Amoon suka gaisa tare da khalifa...
Amoon da bayan son shiga mutane.. Ya kamo farouq murya can kasa yace "I need to dress lyk Ango".. Duk dariya sukayi farouq ya duguri kansa.. Juyawa sukayi shida farouq sukabi ta inda bazasu hadu da mutane ba.. Suna shiga yace "farouq I want to see her".. Farouq ya gane yace "tana dakin mummy babu kowa ynx zaka iya zuwa".. Amoon ya ware idanu... Yana murmushi gaba daya se yaji duk wata damuwar sa ta kau.. Duk wani bakin ciki ya koma farin ciki.. He couldn't believe this se smiling yake.. Is he witnessing dis day.. Ya lumshe idanu "thanks baffa, thanks Abie, thanks my parents.. Dakin mummy ya karasa gaban sa na faduwa.. Ya Bude babu kowa se ita kade dake kwance tana bacci.. Tsayawa yy yana kallon cike da farin ciki with smile on his face.. Fuskar ta tayi fayau kyanta ya kara fitowa... Ynx nan shine mijin Fannah? ynx nan ita din tasa ce? Har ya mallake ta?.. Dan murmushi yayi kafin ya furta *"finally"* snn ya nufi gadon...
More comments more typing...
..
Urs
✨✨✨
Nafeesatu...😍😍
.....
*💫❤LOVE CYCLE✨*


Written by

*@nnafie🖤*
(Smll but mighty😉)

*writer of*
Saif
Adaan
Wata mafita
Saboda duniya
Love cycle......


Bismillahir rahmanir raheem

💫❤Love cycle❤ (31)✨
Karasawa yayi kusa da ita yana kallon fuskar ta.. Hannun ta ya kamo a hankali ya rike cikin nasa still idanun sa akan fuskar ta.. He can't believe cewa yau ya mallaki fannah.. Is he dreaming. Gsky idan mafarki yake to baxe so ya farka ba... Wani irin farin ciki yakeji mara misaltuwa.. Hannun sa dayan yasa ya shafi gefen fuskar ta dayan kuma na cikin nata hannun yana murzawa.. A hankali ya kai fuskar sa dede tata.. Yace "wife wake up let celebrate this day.. This special day".. Ita de baccin ta take bama tasan yanayi ba ... Ya daura forehead dinsa saman nata yana kallon lumsassun idanun ta.... Lumshe idanu yayi tare da daura lips dinsa saman nata a hankali.. Ya cire tare da bude idon yana kallon ta har ynx de bacci take.. Dan murmushi yayi.. Se ya tuno ranar da suka fadi a sch yayi kamar ze kissing dinta taji tsoro a tym din yace mata "not today but one day".. Now the day has come not only for today but for their whole life today is the beginning Alhmdllh he witness it.. Lumshe ido yayi tare da maida lips din sa saman nata.. Yana kissing a hankali... Kamar a mafarki fannah taji ana kissing dinta tun tana tunanin mafarki ne harta farka jin mutun a kanta yasa ta bude idon ta bata gane wanene ba amma lokaci daya kamshin sa ya sanar da ita ko wanene... Kauda Fuskar ta tayi tana kokarin tashi.. Hakan yasa Amoon taimaka mata ta zauna.. Kallon sa tayi cike da tsoro.. Se kuma ta kalli agogo da sauri.. Inde har hasashen ta gsky ne to ynx ta zama matar yusuf.. Kamo hannun ta da Amoon yayi ne yasa ta juyo ta kallesa da sauri.. Se kuma ta fashe da kuka "Aliyu what are doing nifa ynx matar wani ce".. Janyo ta Amoon yayi tana kokarin kwacewa.. Ya janyota da karfi ta fado jikin sa.. Ya rumgume ta sosai tare da daura kansa saman nata.. Fannah na kuka tace "Aliyu stop this its haram I'm someone's wife pls stop".. Yana kara rungumeta sosai yace "its not you're my wife you're my halak not haram khadeeja I'm ur husband".. Cak fannah ta tsaya da kukan da take gaban ta na faduwa.. "Did Aliyu knws what he's saying anya yana cikin hankalin sa kuwa.. No Amoon is not on his ryt sense".. Turesa ta fara kokarin yi. "Pls Aliyu stop this ka dawo cikin hankalin ka mana...".. Kafin yayi magana suka ji ance "kwankwan" sakin ta yayi suka juya.. A tsorace fannah take shiyasa bama ta gane muryar maryam ba seda ta hada ido da ita.. Da mmki take kallon ta dan ita bata fada mata ba.. Maryam ta karaso tana kallon su.. "Amarya da ango".. Fannah ta rinka kallon maryam da mmki.. Maryam tace "so you guys are here making love tun ma kafin a tare.." Amoon ya sosa kai.. Fannah de sakin baki tayi tana kallon su dan ynx kuma ta kasa fahimtar inda zancen ya dosa.. Maryam tace "both Amarya da ango babu wanda ya shirya.. Both sauran Amaren duk sun shirya.. Common kuje ku shirya kar a barku a baya.. Amoon yace "kuma fa haka pls dress her lyk a queen inason tafi kowa".. Maryam tace "bakada Matsala".. Amoon yace "do you need anything" maryam tace "no kaje kawai ka shirya".. Dan kallon fannah da tayi tsaye yayi snn ya fice.. Ransa fess kamar babu wani abu daya taba faruwa....
Dakin sa ya shiga ya rufe saleem ya kira a waya yasa yayi masa ordern kayan da ze saka ya masa bayanin kalar wanda yake so snn ya kashe wayar.. Ya tusa hannun sa cikin gashin kansa.. Kafin ya fada saman gadon ya lumshe idanu.. Gabadaya duk wasu ciwuka da ya ke ya nemesu ya rasa wlh ko ciwon kai babu.. Ya dan bude ido yana kallon sama knn ynx de fannah matar sa ce.. Pillow ya janyo ya rungumeta yana murmushi.. Ya dan shafa lips dinsa "his first kiss with fannah and she's his wife halak dinsa Alhmdllh".. Ya sake lumshe idanu yanajin wani farin ciki from no where.. Tashi yayi ya kalli gabas sujjada yayi yana godewa Allah daya nuna masa wann rana.. Tashi yayi ya shiga toilet wanka yayi sosai a matsayinsa na ango ya fito daure da bathrobe.. Ya zauna gaban mirror ya cigaba da shafe jikinsa da mayunkasa masu tsada hade da turarurruka.. Knocking akayi masa yace "come in".. Saleem ya shigo rike da ledar company din da Amoon yayi ordern kaya.. Saleem ya aje kayan yana kallon bro dinsa dake gyara lafiyayyar sumar sa.. Bayansa yaje ya rungumesa.. Congratulations bro how is ur health.. Amoon ya kalli saleem ta mirror kafin yace "zakaci gidanku mammah fa?".. "Tana tare da dadd".. Gyda kai yayi snn ya shafa kan saleem "tnx bro".. Saleem ya fice yaja masa kofar.. Kiran ya shigo sadeeq yayi ya kalli wayar.. Be dauka ba.. Ya ciro kayan ya saka ya saka hular a kansa. Shi kansa ko ba'a fada masa ba yasan yayi kyau.. Ya Kara sakawa kansa turare snn ya dauki babbar rigar sa ya rike a hannu... Dakin dad dinsa ya shiga.. Suna tare da mummy duk binsa sukayi da kallo.. Kamar bashi bane dazu ya rufe masu kofa ba.. daka gansa kasan yana cikin farin ciki.. Ganin irin kallon da suke masa duk se yaji kunya.. Ya shagwabe fuska.. Dadd ya hararesa.. Da sauri Amoon ya fada jikin daddynsa.. "Dadd barka da juma'a" dungure masa kai dadd se ynx kasan da ka gaisar dani.. "Srry dad am srry.. Farouq told me everything thank you dad I really appreciate".. Dad na murmushi yace "bani zaka godewa ba ka godewa sauran iyayenka and baffa"... "I love you Dadd".. Dad ya mike "I love you too kayi sauri ka fito jama'a nason ganin ka".. Gyada kai yayi dad ya fita..ya juya ya kalli mammah se kuma ya ware idanu da hannuwa.. "Wow momm what's a day danki ya zama ango".. Se kuma yaje ya rungumeta ta suna cikin haka aka turo kofa.. Saleem ne tare da chucu.. Tayi kwalliya Daka ganta kaga Amarya tayi mugun kyau.. Ta rinka kallon yayan nata tana murmushi yayi kyau sosai.. Hakika yau kade ita sheda ce akan sonda yakewa fannah banda Annuri babu abinda ke fita a fuskar sa.. Tace "yaya".. Yana murmushi yace "finally chucun farouq" karasawa tayi ta rugumesa cike da farin ciki se kuma hawaye.. Ya dago ta yana murmushi "don't do that karki bata kwalliyar tun kafin farouq ya gani".. Tace "congratulations bro".. "Congratulations autar mu".. Rumgumesa tayi tana dan murmushi. Saleem yace "nifa".. Chucu tayi masa gwalo.. Mammah tace "ynx shine auta" duk dariya sukayi.. Saleem ya amshi babbar rigar ya taya yayansa sakawa.. Snn suka fita suka bar chucu tare da Mammah...
"Pls maryam meke faruwa kiyi mun bayani".. Maryam tace "bayanin me zan maki keda ko fadamun baki yi ba.. Ita de fannah gaba daya kanta ya daure".. Turo kofar akayi aka shigo.. Duk suka juya suna kallon wadan da suka shigo.. Fannah ta rinka kallon wacce ke kama da hafsat da farko tama dauka hafsat ce se ynx taga wnn zata girmi hafsat.. Humaira tace "ina matar kanin nawa".. Tana kallon fannah tace "come to me dear" a hankali fannah ta karasa jikin humaira.. Rungumeta tayi tace "masha khadeeja.. Baki sanni ba ko".. Fannah ta gyada kai.. Tace "ni sunana humaira kanwar sadeeq, farouq, snn yayar Sultan da mijin ki wato Amoon".. Lokaci daya fannah ta ganeta itace macen da aka haifa tare dasu Amoon.. "Tun jiya nazo but both of you ware busy daga ke har mijin naki babu wanda yake cikin hankalin sa.. So finally an daura aure".. Murmushi fannah tayi. Ynx kuma ta fara fahimta knn Aliyu ne mijin ta ynx shi ta aura.. But how tayaya.. Bata da me bata amsar.. Humaira tasa wadan da suke tare a hadawa fannah ruwan wanka.. Da kalar turarurrukan su na sudan ta sukayi yanda tace.. Hade da sabulai.. Fannah ta shiga toilet din domin wanka kanta kasa.. Humaira tace zaki san kunya bari lokacin biki yazo ni zan maki gyara na musamman da kaina... Bayan ta fito humaira da kanta tayi mata make up mara hayaniya dan bata yarda ta boye mata asalin kyawunta ba..
Ta dauko mata kayan ta ta shirya ta.. Sega fannah ta fito sak a matsayin Amarya.. Se wani shining takeyi kamar wata queen.. Humaira tace "oh ni Amoon dole yake rudewa.. Kuma bari zan gansa seya biyamun motar yusuf daya fasa da kudin kwalliya duk ya kawo.. Ita de fannah kanta kasa tama kasa dagowa.. Hannun ta suka kama zuwa dakin daddy...
Amoon ya karasa kusa da yan uwan nasa angwaye.. Suna ganin sa suka fara tsokanar sa shide murmushi kawai yake.. Sadeeq yace "so ka iya murmushi haka.. Dazu fa daya fito daga mota kiris yake jira ya kai mana duka.." Duk dariya sukayi.. Suna gaisawa da Abokanan su.. Fuskar Amoon kasa boye farin cikin sa tayi duk inda zaka gansa murmushi yake dayawa ma basu saba ganin fuskar sa cikin irin wnn yanayin ba.. Dama sultan da farouq duk sun fisu fara'a...
Har seda suka gama walima da sadeeq ya shirya masu snn suka dawo gida.. Dakin Baffa suka wuce.. Duka iyayen nasu nacan yawancin manyan family din ma kansu a kasa suka shiga.. Babu jimawa sega Amare an shigo dasu Amoon ya daga idanunsa be sauke akan kowa ba se fannah.. "Ya Allah" ya furta sbd wani mugun kyau da tayi masa.. He wish ace babu kowa a wajen da seyaji ya rugumeta and give her a perfect kiss".. Sageer ya zuguro sa.. Hakan yasa yayi kasa da kansa.. Sageer yace "easy mana kai baka ga hararar da Humaira keyi maka ba".. Dan daga kai yayi suka hada ido da Humaira.. Harara ta sakar masa.. Yayi kasa da kansa yana murmushi "yaushe wnn almasifatun tazo".....
Abie ne ya fara magana cike da dattaku ya fara yi masu nasiha.. Da nusar dasu menene zumunci.. Sosai yayi masu fada Wanda dukansu seda ya shigesu ya nuna masu illar yadda zumunci da sukayi.. Jikin su duk yayi sanyi.. Barin Amoon da sultan snn jiddah da yusrah..,sosai Abie ya birgesu bisa ga abinda yayi shida yan uwan nasa. Amoon kam yanaganin dole ma yaje yayi masu godiya bisaga abinda sukayi masa... Daga karshe kuma ya idasa da fadin.. "Alhmdllh an daura aure.. Sbd da matsololin da sukaso faruwa Amma ahamdulillah ynx komai ya dedeta.. Tarewa da biki inshallahu zasu biyo zuwa bayan sallah babba.. Nan aka saka date da komai.. Amoon ya lumshe idanu.. Bayajin ze iya barin fannah se bayan sallah bayan yana ganin ynx ya mallake ta.. Anyi me wuyar tunda an daura aure... And bashi kade ke tunanin ba kusan duka angwayen tunanin su daya... Bayan Abie ya gama su Dad ma suka daura da nasu daganan aka sallamesu . Humaira ta kwashi Amaren suka koma inda suka fito... Suma su Amoon tashi sukayi duk suka cigaba da harkokim gabansu....
Ynx fannah ta gane yanda abin yake Aunty Humaira tayi mata bayani.. Kuma da suka hadu da sauran Amaren ta kara fahimtar komai.. Sosai yusrah ta rungumeta take bata hakurin Abinda ya faruwa.. Itama tace komai ya wuce ta roke su yafiya.. Daga nan kuma suka koma tsokanar juna tuni lokaci daya suka ware

Please Login or Register in order to submit comment