Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Bata fada mata komai game da ganin family din nata ba.. Ita kuma maryam ta dauka duk dan zata tafi ne da yake duk in zata tafi haka suke barin ma hutu me tsayi irin wnn.. Haka de taita lallashin ta... Karshe ma fannah kuka ta fashewa maryam dashi... Abubuwa da yawa sun mata gana Amah gana Family dinta ga kuma maryam ma Zata tafi.... Da kyar maryam ta lallaba ta dan itama seda ta sakata kukan ....
Fannah ta rakata har airport din snn ta juyo ta dawo gida.. Mummy ta iske a parlor tayi shiru.. Zuwa tayi ta kwanta saman cinyar mummy kafin tace "mummy pls do something"... Shiru mummy tayi bata san dalilin daddy nayin haka ba but tasan cike yake da son ganin yan uwansa ita ynx hankalin ta duk a tashe yake sbd bata san wane hali yake ba a ynx....
Tashi fannah tayi ta koma daki.. Tana zuwa ta ciro sakon da Amah ya barmata ta karanta.. Tana hawaye kafin a hankali ta furta I love you.. Pls come back to me"...
Ranar gidan babu wanda yabi ta kan lunch har dinner ma seda mummy ta mata da gske snn tasakko kuma har lokacin daddy be dawo ba... Gaba daya hankalin su a tashe yake... Suna gamawa yana shigowa... Suka masa sannu da zuwa ya amsa ciki ciki snn ya haye Sama... Fannah kara fashewa da kuka tayi snn ra wuce dakin ta... A haka ranar suka kwana kowa da abunda yake damunsa a rai..
washe gari andade da gama breakfast amma babu wanda ya sakko yy har wajen 12... Da kyar mummy ta lallaba daddy yasakko snn ta kira fannah a waya... Har suka kusa gamawa fannah bata sakko ba.. Daddy ne na kansa ya dauki waya ya kirata... Tana dauka yace "I want to see in lessthan 2mnts" daga haka ya kashe wayar... Ai kau se gata dakaga idanun ta kasan tayi kuka.. Abubawa da yawa sun mata yawa to... A hankali ta zauna tare da gaisar da iyayen nata mummy ce kawai ta amsa amma daddy sede kallon ta yy ya basar... Har cikin har sa bayason yanda ya ganta... Kodaya bayason ganin ta a damuwa... Itace babban farin cikin sa a duniya shiyasa a duk lokacin da yaganta cikin damuwa zuciyar sa take karaya...
Juya abincin kawai take har lokacin ta kasa kai ko tea bakin ta... Ganin abinda take ne yasa daddy fadin.. "Kar ki bari na gama break ba tare da kin cinye abinda ke gabanki ba you better behave ur self" gyada masa kai kawai tayi tana tura abincin tana hawaye.. Suna cikin haka ne sukaji an danna bell.. Daddy ya umurci maid dinsu akan ta bude...
Tana budewa.. Farouq ya shigo da sallama cikin shiga hausawa wacce ta fito da anahin kyaunsa.. Sultan ma ya shigo cikin shiga irn ta Farouq sunyi matukar kyau da kagansu kaga kyawawan asali.... Da sauri fannah ta mike cike da farin cikin ganin yan uwan nata.. Sede kafin tayi step daya.. Idanun ta ya sauka akan wani kyakkawan dattijoh cikin shiga ta alfarma kamannin sa da daddyn ta sun bayyana haka kuma suna tsananin kama da Farouq... Wanda ya shigo daga bayan sa seda gabanta ya fadin ganin shima kamannin sa da daddy sun fito a fuzge kuwa da Dr. Amah dinta yake kama.. Next ma wani ne ya sake shigowa kammanin sa sak da daddy... Ai ba ita kade ba harta Daddy da mummy seda suka mike..... Gaba daya daddy jiyayi jijiyoyin jikin sa na saki ganin yan uwan nasa gabansa bayan tsawon shekaru 19 se yake ganin kamar a mafarki... Ko a yanda numfashin sa ke sauka kasan yana cikin wani yanayi... Sauran yan uwan nasa da hawaye ya cika idanun su ganin little kanin nasu kamar a mafarki.... Cikin raunanniyar murya Alh. Ibrahim yace "Muhammad"... Fashewa da kuka daddy yy ya nufi dan uwan nasa da sauri ya fada jikin sa suka rungume juna.. Cikin rauni da kewa daddy yace "ya..ya..na" ya kara fashewa da kuka.. Alh. Ahmad ma da kukan yaci karfin sa ya rumgume su hakama Alh. Aminu... Kuka suke cike da kewar juna.. Idan ka gansu a yanda suke se sun baka tausayi sbd da kagani kasan suna matukar kaunar junan su to be separated from each other is something else musamman ma idan kuna kaunar junan ku.. Koda baku kaunar juna kuka rabu irin haka for years bakwa ganin juna se kunji kuna kewar juna ballantanama wanda kukeson juna.. Fannah ma rungume mummy tayi tana kuka watching her parents crying.. She's can't believe cewa daddy dinta take gani tare da yan uwansa... She have been dreaming this for so long tunda tasan kanta.. But nayau is different.. Na yau is reality.. Idan ma mafarki take bazata so ta farka ba let her continue dreaming till her last breath.. But her Dr. Amah should be included she can't wait to go back to Nigeria taga yan uwan ta.. Kilama acan zata hadu da Amah dinta.....
so how is it? .... Is it sweet?. If yes se ku karamin yawan comment and ku danna mun vote.. . Bakuga komai ba inde a littafin love cycle ne.. I knw you will enjoy it more than ur expectation.se kunji kamar karna gama just need ur support more comments dan hakan na karawa duk wani writer kwarin guiwa.. So more comment more typing..... Kar ku manta nice taku Nafeesatuh😘 popularly as...
✨✨✨
*ANNAFIE😍*


......

*💫❤LOVE CYCLE✨*


Written by

*@nnafie🖤*
(Smll but mighty😉)

*writer of*
Saif
Adaan
Wada mafita
Saboda duniya
Love cycle......


Bismillahir rahmanir raheem

💫❤Love cycle❤ (10)✨
*Not edited*
Daddy yace "yaya I missed you so much kun gujeni without knowing halin da zan shiga" Abie ya dago dan uwan nasa yana share masa hawaye "we are srry lil bro muma munshiga halin rashin ka for so many years".. Daddy ya share hawayen sa yace "ina baffa na" Alh. Ahmad yy murmushi.. "Baffan ka yafi kowa damuwa da rashin ka tsawon 19yrs da be ganka ba yanacikin tsanin damuwa ynx ma besan mun taho ba da tare dashi zamu taho"...cike da farinki yace "ynx baffa yana son ganina Ina mamana ina umma da sauran yan uwana".. Daga ganin yanda yake magana kasan yana cikin farinciki da kewa Alh. Aminu yace "eyee is that how you miss us shine ka barmu".. Dan langwabar da kai daddy yy kamar yanda ya saba masu kasancewar sa karamin su yace "I don't think zaku sake kewa ta sbd yanda har nayi 4yrs na koma amma baku bukatar gani na.. I thought sona ya fita a ranku.. I thought kun barni har abada bazaku sake yafemun ba"..yafada a raunane Alh. Ahmad yace "common bro we loves you kasani kawai de lokacin idanmu ya rufe ganin yanda ran baffa ya bace but kafimu gskiya".. Abie ya shafa kansa yace "se bayan ka tafi muka fahimci cewa kafi mu gsky liman ya samu baffa yamasa nashiha ya nuna masa abinda kayi daidai ne.. baffa ya shiga damuwa tun yana saka ran zaka dawo har ya cire but kullum yana maka Adduar gamawa da duniya lpy.. Kullum kaine mafarkin sa ... Kuma be taba cire ran zaka dawo ba duk kyautar dayamana har da kai".. Daddy da farin ciki ya ishesa se juyawa yy ina matarsa da yaran sa suke.. "Halimatu. Mamana kunga yan uwana sun dawo hisam zo".. Duk tahowa sukayi kowa idonsa na zubar da hawaye... Abie na kallon fannah yace "masha Allah yarinya ta ta girma".. Murmushi tayi kanta kasa.. Alh Aminu yace "come to ur parents we really miss you".. Suka rungume hisam ita kuma suka shafa kanta.. Daddy is so excited he can't believe ranar nan zata zo... He can't wait yaga mahaifinsa sa ji yake kamar yy tsalle ya gansa a Nigeria yaga mammansa da sauran yan uwansa....
Bayan komai ya lafa aka gabatar masu da abinci sun roki kafarar mummy da shi kanshi daddyn har fannah da take jin kunyar su sun roki tata kafarar kuma duk sun yafe mata.. Daddy ya shige cikin yan uwansa se fira suke yana tambayar yan uwansa da yaransa.. Aka kira haj. Maimuna da Alh. Rabiu bade a kira su sa'adatu ba sbd suna son surprising dinsu amma sauran ya gaisa dasu a waya kuma yaji kalar farin cikin da suke.. Se daddy yaji duk be kyauta ba dama ya koma da be zauna cikin kadeci na shekaru ba.. Fannah kau se kallon daddyn take ganin yanda ya sake da yan uwansa kamar bashi ba dan is hardly ya sake da jama'a inhar basu ba.. Ynx ko koyanayin maganar sa ya chanza se yar shagwaba yake masu dade kagani kasan dama shine karamin su kuma dan gata... Fannah kasa sakewa taci abinci tayi sbd yanda idanuwan sultan da Farouq ke yawo akanta.. Kara daga ido tayi suka hada idanu da Farouq.. Ta ware masa idanu shi kuma ya sakar mata murmushi tare da kashe mata ido daya.. Ta dauke kai tana murmushi.. Suka hada ido da Alh. Ahmad.. Da sauri tayi kasa da kai dan hakanan taji tanaji matsanaiciyar kunyar sa fiye da kowa a wajen... Wayar Alh. Ahmad ne tayi kara yana dubawa ya kalli daddy yace "danka ne kekira" "me sunan baffa".. Daddy ya fada yana murmushi... Alh. Ahmad ya dauki wayar bayan sun danyi magana kadan ya mikawa daddy suka gaisa snn mummy.. Daga nan ta mikawa Alh. Ahmad se yace "ga kanwar ka ku gaisa toh"... Shru yy kafin can yace "ohk to Allah ya kaimu ya bada sa'a".... Ya kashe yana kallon fannah "wai dan uwan naki busy yake but idan ya zama free ze kira ku gaisa"... Gyada kai fannah tayi kawai a ranta tace "wato shine kade baze gaisa da ita ba bayan kowa dokin yake abasa ita su gaisa yaji yanda ta girma.. Amma shi busy yake...."
... A ranar su abie sun dade kafin suce yaushe ze koma.. Daddy ji yayi kamar ya bisu but yace "gobe inshaallah kasata zata amshi bakuncina nida iyalina"... fannah couldn't find it but smile... Jin cewa gobe zataje Nigeria abun kamar a mafarki.. Kowa se kallon juna suke suna murmushi sun kasa magana.. Alh. Aminu ne yy karfin halin fadin "lallai gobe munada manyan baki lallai gobe ilahirin family din Radda suna cike da farin cikin dawowar dan uwansu bayan tsawon shekaru".. Duk murmushi sukayi Farouq yace "su wata za'a bar kauye aje birni".. Fannah ta tsuke fuska tana hararan Farouq sultan yace "Allah yasa karta mana kauyanci dukda nasan ma wnn aje take".... Abie yace "rabu dasu daughter ne ai sune yan kauye keke birni bakiga idan zasuzo bude ido nan suke zuwa ba".... A hakade sukai ta wasa da dariya daddy ya zagaya dasu cikin gidan sa ya fada masa nasarori da arzikin da ya samu bayan barinsa gida.. Sun jinjina masa kuma sun saka masa albarka...
Gabadaya tare suka rakasu airport fannah kamar ta bisu haka take ji dan gani take kwana dayan nan kamar shekara daya ne.. Ganin yanda jikin ta yy sanyi yada sultan kamo hannun ta yace "lil sis are you ohk?"...kamar zatayi kuka tace "I just can't wait jinake kamar na biku"... Yy murmushi "see you inde Nigeria ce seta isheki"... Itama murmushi tayi ya kashe mata idanu.. "Keep smiling cutie you look more beautiful".. Kasa tayi da kanta ganin yanda ya zuba mata manyan idanu....
Kiran su da aka farayi ne yasa bama fannah kade ba hatta daddy seda jikinsa yy sanyi dan gani yake kamar baze kara ganin su ba ya rungume su.. Fannah ta kalli Farouq dake kallon ta ya girgiza mata kai alamar kartayi kuka.. Itama seta gyada masa kai tana masa murmushi.. Ya kashe mata idanu... Yanda yayi din seya mata kama da Amah... Suka daga masu hannu suna gani har suka shige snn suka juyo...
Fannah ta dubi daddy dake driving tace "daddy ynx Nigeria zamu koma".. Yace "sure daughter gobe zakiga baffa ba da mamana da umma and other of ur relatives" farin ciki kamar me....
Suna komawa gida suka fara shirye shirye daddy yace ba wasu kaya dayawa zasu dauka ba idan sunje duk zasu siya nacan Nigeria.. Ranar suka gyara gidan komai aka ajesa a inda ya dace wanda ze lalace suka bayar dashi daddy ya masu booking flight.. Kafin dare sun gama shirya komai .... Ranar ma duk basuyi wani baccin kirki ba daddy hankalin sa gaba daya ya koma kan iyayen sa.. He just can't wait ya gansa tare da mahaifinsa mamansa da sauran kannensa...
Fannah ma murna da farinciki da dauki ya hanata bacci.. Ta rungume pillow tana tsara yanda zatayi surprising maryam.. She wish ace ta hadu da Amah acan tasan zeyi mmki..A haka de bacci ya dauke ta...
Washe gari jirgin su ya daga zuwa Nigeria.. Fannah tana cike da doki daddy kau da mummy tunanin su daya ne babu wanda ya manta last tym da suka hau jirgin Nigeria shekara 19 knn lokacin fannah na jaririya.. Gaban mummy se faduwa yake musamman ma da tasan itace silar komai fahimtar hakan da daddy yy ne yasa ya kamo hannun ta.. Ta kalle sa ya girgiza mata kai kafin yace "inshaallah komai yaxo karshe".. Ta gyada masa kai.. Ya juya ga Fannah da tayi bacci with smiling face... Yace "kinga diyarmu bacci take cikin farin ciki.. Wancan tym din da muka baro da ita bata san komai ba.. But now she's happy"... Mummyn ta kalli diyar tata cike daso da kauna tana murmushi.. "Inason yarana yaya iyayen mu sukaji da suka rasa mu"... Daddy ya kwantar da ita a shoulder dinsa yana dan buda bayan ta.....
*⭐⭐NIGERIA⭐⭐⭐*
Nnamdi Azikiwe International Airport Abuja...
A hankali fannah ta lumshe idanu tana shakar iskar kasar tata wani irin farin ciki yana lullubeta she can't believe itace tayi stepping in a Nigeria.. Iskar yammacin tana dan kadawa a hankali taitabin jama'ar wajen da kallo inda take ganin kamar mafarki take... daga inda sultan yake yana hango su tunda suka fito sunyi wani kyau da kagansu kasan suna cikin hutu .. Ya sauke idanun sa akan fannah.. Tayi matukar yi masa kyau acikin arebian dressing dinna ta seta fito sak balarabia kyawunta is unique ta hada komai sede abinda ba'a rasa ba.. Fannah a bangaren kyau babu macen da bazata iya gogawa da ita.. Gashi kallo daya zaka mata ta shiga ranka... Sultan yadan lumshe idanu yana kara jin son fannah acikin ransa wanda tun randa ya fara ganin ta yakejin sonta... A hankali ya bude motar ya fita yakarasa inda suke... Hisam ne ya fara ganin sa yaje ya rumgumesa... Duk su daddy suka juya gare su... Ya gaisar da su dady snn ya dubi Fannah tana murmushi ta gaisar dashi... Yace "eyee muje gida"... Daga haka suka shiga.... .. Fannah ta zage se kallon hanya take kamar wata bakauya ko ina yana mata kyau wai ynx nan zataga yan uwanta.. Sultan ya kalle ta.. Yace "kalle kallen fa ko tafi UK".. Murmushi kawai tayi dan tasan babuma hadi... Kusan 26mnts suka iso cikin unguwar cikin silent unguwar tasu dake dauke da manya gine gine daka gani kasan anguwar ta manya ce .. Batayi mmki ganin inda sultan ya tsaya yana hon ba domin kau tasan arzikin kakan nasu ya wuce haka... Tasan daddy ta nada arziki iya arziki amma be kama kafan babansa ba... Daddy kau tunda ya suka shigo yake tabin ko ina da kallo ganin yanda aka kara kawata kasar tasa da kuma irin cigaban da suka samu... Lumshe idanu yy jin sun karaso kofar gate din gidan nasu har ynx suna nan inda suke but kamai ya canza kamar anrushe gidan an sake gina nazamani kuma an kara gine gine... Babban wajene me dauke da manyan duplexes na zamani ga shuke shuke da suka kara ma wajen kyau... Daka gani kasan naira ta zauna.. Ga wajajen shakawata ta ko ina.. Wajen yy kamar wata estate.. A parking space din baffa yy parking kowa ya fito suka nufi babban duplex din wanda yake shine na baffa.. Zuciyar daddy ta rinka tsitstsinkewa gani yake kamar ya ba gaskiya bane.. Sultan yy gaba suka bisa a baya...binsa suke kamar baki... Har ynx daddy beci karo da kowa a yan uwansa ba se yan aiki da suketa ma gidan hidima... Wani babban parlor suka shiga me cike da kayan more rayuwa.. Anan ya iske dukkan yan uwansa maza idan kacire Alh. Rabiu... Duk suka mike tare da ware masa hannuwa.. "Welcome home bro"... Zuwa yy ya rungumesa hawaye cike da idonsa kafin yace "tnx ina baffa na".. Sukace muje.. Duk suka dunguma zuwa sama... A wani matsakaicin parlor me na hutawa suka iske mahaifin nasu... Wani farin tsoho kyakkawa wanda shekaraunsa sunja amma sbd tsabar hutu da kwanciyar hankali ba gane hakan.. Bazakace ya haifi daddy bama ballantana Abie... Koda suka shigo amsa sallamar su kawai yy batare da ya dago daga kallon jaridar da yake cikin expensive farin glass dinsa wanda yake taimakawa ganin sa ba... ...daddy couldn't help it out gani yake kamar wasa.. Inhar wnn mafarkine to baya so ya farka.. His father, his best frnd da suka rabu tsawon shekaru ne agaban sa... He's just as he is before... Gani yake kamar idan ya juyo ya gansa baze yi farin ciki ba gani yake kamar ze nuna masa hanya yace su fita.. Se yaji baya so ya juyo ya gansa a ya koresa gara suyi tazama a haka... He loves his parent but stay far is better.. Bayason baffan nasa na masa fada dan be saba masa ba..zuciyar sa bata iya dauka... Alh. Ahmad ne ya dafa kafadar sa.. Sukalli juna ya gyada masa kai cike da kwarin guiwa.. Daddy ya kalli baffa.. Idanun sa cike da kwalla cikin rawar murya yace "Baffa nah".... Cak Baffa ya tsaya daga karatun da yake jin muryar Muhammad dinsa kamar saukar aradu sede be juyoba domin yana son tabbatarwa cewa ba mafarki yake ba...
Ganin baffan nasa be juyoba yasa ya runtse idanun sa hawaye na fita yace "baffana am back ur Muhammad is back to you baffah... Pls don't send me back I miss you I miss my family.. I want live with you.. Ina son zama cikin yan uwana kamar kowa pls don't separate me again.. Am ur son I knw you still love.. Don't separate me it pain me... Am back to you don't send me back pls dad.. Kowa nada family but i'm separated from mine that hurt me...is not easy to be saperated from someone you love..dad do you knw how i feel without you.... Forgive me baffa.... Welcome me dad.. Hug me and tell me welcome.. If you send me back for this tym I knw my heart can't take it anymore.. Pls brothers talk to him ask him to forgive me.. Nima inaso na rayuwa cikin yan uwana I miss them so badly pls forgive me baffa..... Kuka yaci karfin sa...
Tsam baffa ya mike jin da gske de ba mafarki yake ba Muhammad dinsa ne ya dawo... He's beloved son is back he can't believe what's just happening.. Ya juya yana sauke idanunsa akan dan nasa da kansa ke kasa yana kuka..... Idanun sa ya cika da hawaye cike da dauriya karda yy kuka yace "Muhammad my son"... Da sauri daddy ya dago yana kallon mahaifin nasa... Baffa yace "are you, my son are you back to me.. Is this real, is this my Muhammad.. My Little very own son?... Daddy ya gyada kai "yes dad am back pls forgive me"... Baffa ya ware masa hannuwa "come to me my son come and hug ur baffa pls come son ur baffa miss you so badly".... Da sauri daddy yaje ya fada jikin mahaifin nasa tare da fashewa da wani sabon kuka ... Gsky dumin iyaye daban ne duk wanda bashi da iyaye yy rashi abin tausayi ne.. Daddy ji yayi wani sanyi na ratsa dukkan gabobinsa.. Yaji wani kututu daya tokare masa makoshi ya wuce se yaji wani wasai.. Baffa kau hawayen farin ciki kawai yake soyayyar mahaifa dabance.. Ya bubbuga bayansa "stop crying son.. Ur dad need more.. Ur dad loves you.. Don't leave us again.... Ur family loves you.. Our lyf is dark without you.." Daddy ya gyada kai yana kara shigewa jikin mahaifin nasa "yes baffa na dawo gaba daya kawai ya yafemun ya fada cike da shagwabar da ya saba yiwa mahaifinsa...".. Baffa ya dan dungure masa kai.. "Ja'iri kaga yanda ka girma..".. Daddy yy dariya kai baffa nine karami fa...
Duk sauran dake cikin parlorn kuka suke hade da dariya na farin ciki.. Baffa ya dago idonsa ya sauke akan fannah.. Yace "uhmm matar haka kika girma.. Na kawo sadaki kawai....." Duk dariya sukayi ya kamo hannunta ita da hisam "you're welcome my grand children.... Ur grandfa loves you... ".. Duk murmushi sukayi cike da jin dadi .... Baffa ya aika kira masa matan sa da sauran yaran sa su sa'adatu dake cikin Abuja.. Koda iyayen nasa mata suka shigo da fannah suka fara cin karo... Mama ta kalle fannah na kusan minti daya kafin ka kalli mijin nata tace... "Alhaji wnn wacece nake gani kamar jinin Muhammad dina".. Murmushi baffa yy kawai.. Tace "duk inda wnn ta fito jinin danace kuma babu tantama wnn khadeeja ce tabbas diyar Muhammad ce kar kucemun mafarkina na jiya ya tabbata.. Cewa Muhammad dina ya dawo....".. ".. Tabbas mama na dawo".... Da sauri ta juya inda taje jiyo muryar sa.. Lokaci daya idon ta ya sauka akansa shida matar sa.. Ta toshe baki kuka na neman kwace mata "da gske kaine".. Da sauri yazo ya runmguta..umma kuma da rungume mummy....
Kowa ka gani ranar yana cikin farin ciki senan da nan ake dasu mummy ita da yaran ta yayinda kowa ya roki gafarar su musamman mummy da itace silar komi ansan ba'a kyauta mata ba se kowa yake kara kaunar ta ita kuwa da shige cikin su kamar sun saba .. Farin cikin da sa'adatu da Raheena suka shiga ba'a magana... Fannah taga yan uwanta da yawa sede har ynx bata ga sa'annin nata ba sede wadan da suka girme ta da wanda ta girma.. Ko sultan bata kara gani ba bare sultan.. Ta zama yar gata kowa se nan da nan yake da ita umma ta kama ta rike duk meson ganin ta sede yaje wajen ta mummy kau na tare da mama.. Setake gani kamar mahaifiyar ta.. Hisam ya shige cikin yan uwansa yara dukda ba wani sabawa yy da shiga mutane ba... Daddy kau na tare da baffansa da yan uwansa maza harma da matan suna tare... ..abie yasa aka gabatar da abinci me rai da lpy daddy yai taci yana santi... Kowa ya zage yaci abinci hakan yasa suka ji dadi suka sake kamar dama sun saba...
Kowa burin sa yaga fanna da yazo ita kam tana dakin umma tare da iyayen nata mata mom sa'a da mom raheena.. Yanda suka jawo ta ajikine yasa ta sake dasu ko takan sauran yan uwanta bata bi ba... Se magrib snn ta samu saukin mutanen dake shigo mata .. Bata tashi daga abun sallah ba se isha'i... Tana idarwa ko tashi daga inda take batayi ba akayi sallama.. Wata kyakkawar budurwa ce ta shigo wadda zasuyi tsara da Fannah.. Tana gannin Fannah ta kara fadada fara'ar ta.. Da sauri ta kasaro ta rungume Fannah.. You're welcome sister.. Fannah taji wani dadi ashe haka family dinsu suke da sanyi da mutunci.... "Ke meyakawoki inace kince baki kara zuwa" muryar umma ta katse wa Fannah tunani.. Murguda baki yarinyar tayi tana kwabe fuska irn na shagwabbun nan kafin tace "ni wajen ki nazo wajen yar uwata nazo da baki rike mana ita ba ai da baki ganni ba".. Ta juya ta kalli fannah tace "kinga tashi muje kafin ta fara mintsinin ki ynx na marmari take maki"... Mom raheena tace "wato sbd kinga yar uwarki ko kallo

Please Login or Register in order to submit comment