Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

son Aliyu sosai nasani shiyasa take wnn kukan amma hukuncin da baffa ya yanke kawai is the best tayi hakuri da duk wanda ze zaba mata kokuma ta nemi wani fakat shine kwanciyar hankali.. Duk wani sauki daza'a samu daga gareta ne.. Inda abun yazo da sauki ma hutun nasu ba wani bane next week zata koma sch kila hankalin ta yafi kwanciya idan bata ganin su".. Mummy ta gyada kai.. Dan itama tana tunanin hakan shine zefi.. Kodan sbd su jiddah...
.. Maganar wanin da baffa ya fada ne take tayiwa Amoon yawo a ransa.. Sadeeq ya kama hannun sa.. "Pls take this easy".. Kamar jira Amoon yake yace "sadeeq I will not wlh wlh kaji na rantse babu me auran min mata kuma tabbas duk wanda yayi gigin haka sena batar da kowaye fannah tawace ni kade kuma babu wacce zan aura a cikin su babu wacce nace inaso dan haka babu wacce zan zauna da ita a cikin su kuma kowaye ake shirin bama fannah yazo ina jiransa"... Daga yanda yake magana kasan a he mean what he said.. Su jiddah dake parlor suna jin abinda ya fada duk suka juyo suka kallesa.. Nunawa yayi kamar be gansu ba har ze fita yaji muryar mom.. "To shugaban masara kunya.. Da ba'a fada maka abinda zuciyar ka bataso shugaban yan kafiya.. Dan Allah idan an aura maka su ka maido mana su a ranar.. Se musan ka isa.. Muga iya karshen takama.. Shashasha kawai.. Wlh tallahi Aliyu ka kiyayemu.. Wato kai idan ka kafe babu me tankwara ka.. Mu zuba mugani mu da kai".. Ko kala bece ba yayi ficewar sa ba tare daya kara kallon kowa dake parlorn ba.. Dad yabi dan nasa da Kallo.. Shide yasan yanada kafiya Amma Amoon ya takesa ya murje.. Dan duk family dinsu babu me kafiyar Amoon.. Be cika shiga abubuwa ba amma fa idan ya tsaya a A to dole A din nan za'a tsaya haka yake shi tun yana karami..
More comments more typing...
Urs
✨✨✨
Nafeesatuu...😍😍
.....

*💫❤LOVE CYCLE✨*


Written by

*@nnafie🖤*
(Smll but mighty😉)

*writer of*
Saif
Adaan
Wata mafita
Saboda duniya
Love cycle......


Bismillahir rahmanir raheem

💫❤Love cycle❤ (26)✨
fannah ta kalli wayar ta dake ringing... Numbern da Amoon ya tura mata message ranar nan ta gani..seda gaban ta ya fadi.. Ganin ta kusa tsikewa yasa ta dauki wayar tare da yin sallama.. Daga can ya Amsa tare da fadin "Aliyu Raddah".. A hankali tace "na gane ai" yace "good..why did you say yes akan batun Baffa?"... Tace "because that's the best for both of us"... Amoon yadan tabe baki yace "do you think cewa wani ze iya auren ki ina raye"... "Me ze hana hakan faruwa".. yace "khadeejah I have one heart and it beat for only you, in my hope you're my future.... Dan haka duk wanda yake tunanin zeyi rayuwa dake bayan ni ina jiransa".. Daga haka ya kashe wayar.. Dan tabe baki kawai fannah tayi a aje wayar...
Sultan ma ya kirata bata dauka ba dan gabadaya haushi yake bata Amoon kau daya fado mata sede ta tura baki... Tama kosa kawai ta koma sch ko zata samu salama.....
Tundaga ranar Amoon be sake kiran Fannah ba kuma bata sake ganin sa ba..shirin ta kawai take na komawa.. Har gida farouq yaje ya lallashe ta ya kuma kwantar mata da hankali hakama sadeeq.. Fareeda kam sun koma kamar da chucu ma haka .. Jiddah de har ynx basa magana ita da Yusrah... Har Fannah ta gama shirin ta duk anzo mata bankwana amma bnda su yusrah haka ma Amoon.. Sultan dama bata bukatar ganin sa...
Ana gobe zasu tafi dayake harda su mummy ranar ta fito parlor .. Har ta sakko bata lura da wani a parlorn ba seda tazo gab.. Snn taji kamshin turaren sa.. Juyawa tayi da sauri dai dai shima ya dago kai.. Suka hada idanu.. Ware idanu tayi cike da mamakin ganin sa tace "kai".. Ya dage gira shima yace "ke".. Dan tura baki tayi se kuma tace "me kazo yi".. Ya dan harareta "nace wajenki nazo ne?".. Ta hade rai.. Tace "toni ina ruwana".. Daga haka ta juya a stairs nan ta hadu da mummy ta hisam ya kira kanta kasa ta matsa ko kallonta mummy batayi ba snn ta wuce.. Fannah ta shiga daki tana tura baki.. Allah yaso ta ma ba wani banzan dressing tayi ba.. Dan murmushi tayi domin kullum Amoon sonsa sabo yake koma mata.. Can kuma ta hade rai data tuno su jiddah da Yusrah da kuma sultan duk haushi suke bata ynx.. Tashi tayi tana kallon window ko zataga fitar sa.... Ji tayi an bude kofa hakan yasa ta juya da sauri.. Mummy ta gani tsaye.. Murmushi ta kakalo tace "mummy".. Dan tabe baki mummy tayi snn tace "kije kuyi sallama"... Daga haka ta fita... Fannah ta dan tura baki.. Kusan 2mins snn ta mike ta dauki well iron hijab dinta snn ta fita... Baya parlor.. A ranta tace kode ya tafi... Tasan halin kayan ta fa kilan ma ya tafi.. Bude kofar parlor tayi zaune ta gansa cikin daya daga cikin kujerun balcony din.... Zaunawa tayi.. Tace "kace ba wajena kazo ba?".. Ya dago manyan idanun sa ya zuba mata kafin yace "to na kiraki ne".. Sakin baki tayi tana kallon sa.. Yace "ni ai bn kiraki ba".. .. Hade rai tayi... Se kuma ta mike ta juya zata shige knn yayi saurin riko hannun ta.. "Oh srry wife".. Ta murguda baki "ga matan ka can amma bani ba" ta fada tana kokarin fisge hannun ta.. Ya rike hannun sosai sbd yasan zata iya shigewa ta barsa.. Yace "no kema harda ke ai" tace "what?".. Tana hade rai.. Ya ware idanu "yes kinga yusrah uwar gida se jiddah and you Amarya".. Tace "tabdi kaje ka aure su ni na barmasu.." Ta fada kamar zatayi kuka.. Ya dan dage gira "Da gske kin barmasu na aure su sukade".... Muryan ta na rawa tace "to dama na taba cewa zan aure ka ne pls ka sakeni".. Yace "ni kuma sena aureki.. Kawai inason na hadaki da yan uwanki ne se ku kara kulla zumunci".. Kasa magana tayi sbd tasan tanayin magana zata iya fashewa da kuka.. Yace "kinyi shiru". Ta hade rai tace "kaga ka sake ni".. Ya noke kafada yana dan murmushi da yake mugun kashe ta tare da kwantar da murya kamar tata "uhm uhm ni bazan sakeki ba".. Fannah ta zauna saman kujera.. Ta kifa kanta ta fara kuka a hankali... Zaunawa yayi gefen ta still yana rike da hannun ta yana dan murzawa.. Murya can kasa yace "are you jealous".. Kin dagowa tayi yace "babee".. "Pls Aliyu let me"... Yace "uhm uhm sekin ce zaki aure ni".. Ta fizge hannun ta ta mike.. "Yaya Amoon pls rayuwar da mukayi a baya ka ajeta.. Babu wani relationship ynx tsakanin mu sena yan uwantaka.. Baffa yace ku rabu dani so pls let me".. Daga haka ta shige... Dan murmushi yayi yaga sonsa karara a idanun Fannah duk da bata taba furta masa tana sonsa ba.. Kuma tabbas yana matukar son ganin wnn rana he just can't wait yaji kalmar so daga bakin Fannah....
Washe gari bayan sunyi sallama da kowa farouq da chucu suka kaisu airport.. Fannah se kallon gidan su Amoon take taga ko zata gansa.. Tunawa tayi da jiya seta hade rai tare da dauke.. Hada ido sukayi da farouq ta madubi yadan daga mata gira.... Tayi kasa da kanta tana murmushi..
A can airport din suka hadu da maryam.. Farouq ya matso kusa da ita.. So finally the Amah is Amoon.. Ta dan tura baki "ni ai bazan aure sa ba"... Murmushi yayi yace "wnn zancen ba har zuci ba gsky.."... Dan murmushi tayi tace "kaide ga chucu nan".. Juyawa yayi ya kalli chucu da ta rike maryam suna magana.. Murmushi yy.. Kamar chucu tasan me suke suke seta juyo.. Ganin kallon ta suke seta dage gira alamar what?.. Yanda tayi din kamar Amoon.. Duk dariya sukayi... Su Farouq na nan har jirgin su ya daga..... Snn suka koma gida.... Gidan su Baffa sukaje.. Yusrah na ganin chucu tace "hmm ynx sbd kin samu wata ynx an watsar damu".. Chucu na kallon ta da kyau ni bn watsar da ku ba".. Yusrah tace "gashi nan ynx kamar ma baki sonmu da yaya Amoon".. Chucu ta ware hannu "ni bazan hana sa yaso wacce yake so kuma take sonsa ba ku kanku baku san zaman lpy ne inda za'a maida komai ba komai ba a cire son rai.. Dama duk wnn matsalolin basu kawo ynx ba.. " daga haka ta wuce dakin mama ko kallon sultan daya shigo ynx batayi ba sbd mugun haushi yake bata.. Tana mugun son yayanta tana son farin cikin sa..tasan yanda yake inde har yana cikin damuwa.. Sune ke masa kallon me taurin kai amma yana da hakuri".....
..
Tare da maryam suka wuce gidan nasu...Fannah ta dubi hisam dake tayin fushi waishi bayason tahowa... Tace "to kode zaka komane..."... Kai ya daga mata da sauri.. Tayi dariya "lallai ma yaro"... Kasancewar daddy na zama a gidan seya kasance fess.. Abubuwa kadan suka gyara... Sukayi ordering abinda zasuci.. Kasancewar da dare su isa suna ci suka fara shirin bacci.... Fannah na gama setting wayar ta message din Amoon ya shigo.. "Wife is safely at UK miss you dear"... Dan tura baki tayi kamar bazatayi reply ba se kuma ta tura masa.. "Am not ur wife"... Babu jimawa se ya turo mata "ke ce Amarya fa".. Fannah ta hade rai.. Se kuma ta cillar da wayar.. Maryam dake waya da khalil da kalli Fannah se kuma ta dauki wayar tana dubawa.. Fashewa da dariya tayi.. Ta dubi Fannah "Amarya Amarya"... Fannah ta dauki karamin pillow ta gefi maryam dashi.. Dariya sosai maryam tayi.... Fannah ta dauki wayar ta tare da juyawa maryam baya ta lumshe ido kamar me bacci... Abubuwa dayawa suka ringa dawo mata.. Se take ganin komai kamar a mafarki.. Ta danyi murmushi.. Kenn tun a wancan lokacin Aliyu yasan wacece ita amma ya rinka mata rashin mutunci.. Daga baya kuma yazo ya koya mata son sa.. Kawai tana so tasan meyasa ya boye mata kansa .. Da kuma dalilin ta fiya ya barta...... Haka Fannah ta rinka tunanin sa.. Message ne ya shigo wayar ta . dubawa tayi da sauri dan tasan may be shine.. "Are you missing me?".. Fannah ta zaro idanu tana kallon maryam dake bacci.. Se kuma ta tura baki.. Ta tura masa reply "don't ever think of that"... "Ohk then.. Why are you still a wake?".. Cije lips dinta tayi.. Sekuma ta je wayar ta juya baya tana tura baki... Can babu jimawa ta sake jin karar message.. Da sauri ta juyo ta kara daukar wayar ta duba... "Pls love don't ignore".. Kin yi masa reply tayi.. Babu jimawa ya sake tura mata message .. "babee you knw what?".. Duk da tana so taji amma ta share.. Ta rinka kallon wayar ko ze ze sake turowa amma shiru.. Har ta cire rai.... Se ya kara shigowa.. dubawa tayi da sauri "A day is coming that maryam won't the person beside you, I will be that person.. And you will sleep on my chest and hug me lyk pillow.. Can't wait just can't wait....".. Fannah ta zare idanu se kuma ta juya ta dubi maryam... Dake bacci.. Tabb ynx akwai ranar da zata zo ta kwana da wani namiji......runtse idanu tayi.. Massage ya kara shigowa.. "Any way god nyt babee pls don't think of anyone think of me. I love you"... Rugume wayar tayi a hankali ta furta "I love you too"..... Daga haka bacci ya dauke ta... Me dadi baccin da rabon ta da irinsa harta manta . da kyar ta iya tashi tayi sallah snn ta sake komawa wani bacci... Ranar sunyi baccin gajiya sosai dan se 1 suka tashi sukayi sallah.. Snn sukayi duk wani abu daya kamata tare dayin breakfast.. Apartment dinsu maryam sukaje ta dauko duk wani abu dazata bukata suka dawo dan tare dasu zata zauna an riga an zama daya.. Ranar abu kadan se Fannah tayi shiru .. Duk message din da Amoon ya turo mata suna dawo mata.. Ko kuma ta dauki wayar tana sake dubawa .... Har morning message ya tura mata amma batayi masa reply ba...
.....
maryam dake driving dinsu zuwa sch ta dubi Fannah... Ta fashe da dariya.. Fannah ta dube ta.. "Lpyr ki".. Maryam tace.. "Wato gaba daya Amoon ya gigita taki naga alama dama haka soyayya take bakya tunanin kowa se nasa".. Fannah ta hade rai "ce maki akayi tunanin sa nake".. Maryam ta tabe baki "oho zamaki fadi gsky malama".... Har suka karaso Fannah bata kara kula maryam dake tsokanar ta ba. Inda suke lectures suka shiga.. Ana ta gaisawa an dawo hutu.... Duk da ba wani dadewa sukayi da komawa ba... Jin anyi tsit yasa kowa ya natsu.. Ita kanta Fannah tun kafin ta dago seda gabanta ya fadi sbd jin kamshin turaren sa.. Lokaci daya kuma ta sauke ido a kansa... Fuskar sa cike da murmushi ba kamar yanda suka saba ganin sa da ba.. Dayawa a wajen sunyi murnar ganin sa kowa se gaisar dashi yake yana tambayar ina ya tafi.. maryam ta zunguro Fannah "ke wnn yaya Amoon din Aljani ne".. Fannah ta daga ido ta kallesa.. Suka hada idanu dashi dan kashe mata ido yayi.. Hakan yasa babu shiri ta gaisar dashi... Kallon ta yayi na yan second tama dauka baxe ce komai ba se taji yace "khadija Raddah".. Dauke kai tayi gaban ta na dan faduwa..
Yanda kowa ke nuna farin cikin ganinsa ya isa yasa ka fahimci anajin dadin class dinsa.. Bayan duk an gama gaishe gaishe kowa ya natsu snn ya fara masu class kamar yanda ya saba cike da kwarewa yanda kowa ze gane bayan ya gama yace "class rep should wait" seda gaban Fannah ya fadi.. Maryam kam wani murmushi ta saki...a hankali tace "za'a danyi soyayya knn".. Da sauri ta wuce Fannah kafin ma ta kamo ta tana dariya kasa kasa.. Har ta fice.. Seda kowa ya fita Fannah data hade rai ta karasa kusa dashi... wata rigar sanyi ya mika mata mara nauyi wacce ya cire saman rigararsa.. Kallon jacket din tayi snn ta kallesa tace "for what?.." Dago manyan idanun sa yayi ya zuba mata.. Dan tura baki tayi ta karba.. Hakan yasa yayi murmushi ta marairace "wai mene".. Tabe baki yayi ya mike "lets go.." Daga haka yayi gaba ta tabi bayan sa tana wani hade rai.. Bayan sun fito yadan rage sauri suka jera.. Bade tace komai ba.. A hankali yace "babee".. Dan cizon libs dinta tayi ba tare data kallesa ba.. Yace "you're not replying my message why".. Ta tura baki "to ni me zance".. Yace "ni me nake cewa".. Tace "baffa yace ze bani wani sbd zaman lpyn dukkan mu mu aje maganar soyayya mana because he have make it clear that dukkan mu hukura ze samomin wani kaima haka ga.". "Stop it".. Ya katse ta a dan fusace..idanun sa har sun fara sauya kala "this should be the last tym da zakimun maganar wani ko wata.. Baki da wani miji sama dani".. Daga haka ya juya.. Da yake suna kusa da parking space ya shige motar sa.. Cikin seconds yabar wajen da mugun gudu.... Fannah tabi motar da kallo idanun ta cike da kwalla ita kanta tana fada ne kawai amma har cikin ranta tasan rabuwa da Amoon abu ne me wahala... Ta kalli jacket din daya mata.. Kamshin turaren sa me dadi dake jikin rigar duk ya cika mata hanci.. Rungume jacket din tayi hawayen idon ta na gangarowa......
More comments more typing....

Urs
✨✨✨
Nafeesatu...😍😍

...


*💫❤LOVE CYCLE✨*


Written by

*@nnafie🖤*
(Smll but mighty😉)

*writer of*
Saif
Adaan
Wata mafita
Saboda duniya
Love cycle......


Bismillahir rahmanir raheem

💫❤Love cycle❤ (27)✨
Karasawa tayi wajen motar ta... Maryam na ciki tsokana ce cike da bakin maryam but ganin yanayinta seta gumtse abunta ta koma lallashi . Tana bada hakuri da kwantar mata da hankali .. Ita de Fannah batace komai ba amma ranta gaba daya babu dadi.. Bata taba tunanin zata sha wahalar soyayya irin haka ba... Suna karasawa gida sallah kade tayi ta kwanta.. Maryam tace ta taso suyi lunch tace bazataci ba kanta ke mata ciwo.. Nan fa hankalin maryam ya tashi.. Wnn ciwo kan da Fannah take bata sonsa.. Dibar Abincin tayi ta kai mata sama.. Duk yanda tayi da ita taci kinci tayi.. Har seda ta kira mata mummy.. Mummy nazuwa ta fashe mata da kuka.. Mummy ta rungume ta tana bubbuga bayan ta.. Tasan abinda ke damun diyar tata.. Is not easy ace mutumin da kk so kk mutuwar gani ace bazaka aure sa ba.. Mummy bata hanata ba har seda tayi kukan me isarta snn mummy ta fara bata abincin da kanta.. Bayan ta koshi ta bata magani daga nan bacci ne ya dauke ta... Shima baccin duk ba wani me dadi ba duk nasu Amoon ne da sauran family din....
Ko washe gari kin zuwa sch tayi sbd ciwon kan .. Maryam ce kade taje.. Wanka kawai fannah tayi ta kwanta , dan kallon break dinta da aka aje mata tayi ta dauke kai.. Ta juya tare da janyo jacket din Amoon ta rugume tanajin kamshin sa me dadi.. Ta lumshe ido a haka bacci ya dauke ta.... Har maryam ta dawo bata tashi ba motsin maryam ne ya tashe ta.. Maryam ta dubi break din ta kalle ta.. "Don't tell me tunda na tafi bacci kike".. Fannah tace "wai har kin dawo"... Maryam ta zauna gefen gado "oh ni wnn soyayyar taku harni wahala nake sha wlh".. Dariya Fannah tayi tace "se akace maki sbd shine bnd lpy"... Maryam ta nuna mata jacket din "ga sheda nan abun yakai ma baki iya bacci seda shi a kusa dake".. Fannah ta watsa mata harara.. "Bnsan saka ido".. Maryam ta tabe baki "anyway yana parlor".. Babu shiri fannah ta zauna tana zare idanu "what wa? you mean yana parlor me yazo yi"... Maryam na kunshe dariyar ta tace "see you dalilai dayawa.. Shima fa gidan su ne snn ga kuma matar sa a ciki"..... Wata harara Fannah ta zabga mata. Ganin yanda take kunshe dariya.. Aikam ta fashe da dariya... Fannah ta hade rai... Seda maryam tayi me isarta snn tace, wajen ki fa yazo ki shirya ynx ze shigo nan din"... Fannah ta marairaice ce "na shiga uku" Mikewa Maryam tayi tabar fannah da zare idanu ...janyo hula tayi tasaka se Kuma ta ja blanket ta rufa tanata zare idanu ....tun kafin ya shigo ma kamshin sa ya mata sallama ..runtse idanu tayi kamar me bacci ..bayan ta tabbatar ta kauda jacket dinsa dake gefen ta .. Da sallama ya shigo.. Zuciyar Fannah se bugawa take.. Idon sa na kanta ya karasa kujerar dake gaban mirror ya ja zuwa gefen bed din ta ya ya zauna.. Ya zuba mata idanu.. Duk da yasan ba bacci take ba se bece da ita komai ba kuma idon sa ta kanta ta.... Fannah tana jin yanda ya tsare ta da idanu gaba daya seta tsargu.. Can de ta kasa jurewa ta bude idanun suka hada idon tura baki tayi "kallon fa".. Ya ware idanu... "To ina ruwanki keda kike bacci"... Ta hararesa, "taya zanyi bacci bayan kazo kamun tsaye".... Ya gyara zama yace "ai naga kamar idan ina kusa se baccin yafi maki dadi".. Tace "tayaya".... Jacket dinsa ya nuna mata dake gefenta.. "Gashi nan".. Kallon jacket din tayi se kuma ta hade rai.. "To me ne hadin ta da bacci na"... Ta gyara zama "it suppose to be in the press not on the bed".... Tace "toni nasan meya kawoshi nan ne".. Ta basa dariya amma beyi ba yace "how are you feeling".. Tace "Alhmdllh".. "What's wrong with you".. Kanta ta nuna masa.. Turo kofar maryam tayi ta shigo duk suka bita da kallo tana rike da tray.. Ta mikawa Amoon "yaya Aliyu pls help us ka bata wlh bataci komai ba".. Karba yayi snn ta juya ta fita.. Ajewa gefe yayi ya ciro wani abu kamar touch cikin pocket dinsa.. Yace "muga idon ki".. Dan matsawa kusa da ita yana dan haska idanun ta for some seconds.. Snn ya kashe yace "kina sakawa kanki damuwa ko".. Shiru tayi batace ce komai ba.. Yace "srry inshaallahu everything will be ohk".. Dan gyada masa kai tayi.. Yace "srry for yesterday am srry love.. I caused us all this" yanda yayi din duk se taji ya bata tausayi itama setaga duk ya rame tasan shi kansa yana cikin damuwa sosai dauriya ce kawai irin tasa.. A hankali tace "duk ka rame kayi rashin lpy ne".. Ya kalleta se kuma ya girgiza kai.. Yace "just pray for us pls pray for us".... Idanun ta ya cika da kwalla.. Wayar ta ne yy ringing duk suka kalla sultan ne... Amoon ya ringa kallon wayar zuciyar sa na tafarfasa yanada wani mugun kishi inde akan Fannah ne... Lura da hakan da Fannah tayi ne yasa ta dauki wayar ta kashe gaba daya.. Dan sauke ajiyar zuciya yy se kuma ya kalle ta.. Ta langwabar da kai "srry..". Yy murmushi tare ta kamo hannun ta a hankali yace "I love you".. Ta dan lumshe idanu a hankali se kuma ta bude kamar zatayi kuka tace "am afraid".. Shafa gefen fuskar ta yayi a hankali yace "do you love me?". Gyada kai tayi tana hawaye.. Kafin a hankali tace "yes I love you.. I love you Aliyu.. I don't knw how to say it but you're the only person I love"... Se kuma ta fashe da kuka...rungume ta yayi cike da farin ciki "I love you too, I love you more and more dear".... Ya fada cike da tsananin sonta.. Da bayajin akwai wani mahaluki dayake mata kalarsa kuma bayaji ze iya bari wani ya mallaketa ba shi ba sede idan babu ransa sede idan mutuwa zeyi".. Fannah tanajin yanda zuciyarsa ke bugawa.. Gashi sosai ya rugumeta ... A hankali ya dago ta yana share mata hawayen.. Ta danyi murmushi tare da janyo jacket dinsa ta rungume tace "I love this jacket".. Yace "really zan kawo maki irinta".. Ta girgiza kai.. "No wnn nake so.sbd taka ce", yayi murmushin dake Kara masa kyau yace "abuna naki ne".. tace "thank you".. "Ba thank you ba abinci zaki zo ki ci and ni zan baki da kaina".. Fannah ta noke kafada.. Dauka yayi aje mata a cinya "I'll watch you eaten.. One day I will feed you my self".. Fannah tayi masa gwalo.. Murmushi kawai yayi yana kallon ta happily... Ita kanta Fannah duk setaji ciwon kan ya tafi rabon data samu tym dashi irin haka har ta manta...... Koda ze tafi ji tayi kamar karya tafi.... Yana tafiya maryam ta shigo tana kallon ta Fannah tace "yade kallon fa".. "Dole na kalleki ai har kinji sauki sbd maganin ki yazo".. Murmushi kawai tayi "kinga laifi na?"..
Ranar Fannah ta ware.. Ita kanta mummy tasan dalilin ware war tata kuma taji dadi kullum Addua take ma diyar tata Akan Amoon ita kanta tayaba da hankalinsa dakuma irin kaunar da yake wa Fannah. Tana kuma adduar Allah yasa rabon ta ne"..... Koda dare ranar bnd chart da Amoon babu Abinda take.. Ko a rayuwar su tada bata taba sakewa dashi ba irin yau..". Ita kanta bata taba sanin haka yake ba seyau data sake dashi.. Da kyar ya bari tayi bacci... Suna tashi daga lectures ya tura mata message wai ta jira inda suka saba haduwa.. Duk yanda tayi da maryam ta bita kin zuwa tayi.. Hakanan ta wuce.. Tana zuwa seta gansa a zaune.. Ta karasa tace "ashe kana nan shine kace na jiraka..". Ya aje wayar sa yana kallon yanda tayi kyau.. Yace "wancan karon

Please Login or Register in order to submit comment