Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abinda yasa ta bukaci su taho kano, bata boye masa komae ba tun daga jiya da Afeefah ta dawo gida da abubuwan da ta gaya maya da kuma biyo ta da Aliyu yyi da yanda suka yi da shi, duk ta gaya masa, Abba yyi shiru yana kallonta da gani kasan shi ma ya dan girgixa da jin lamarin, Mami ta kara da cewa idan anyi breakfast duk xa a xauna kowa ya ji matsayin Zainab a gidan nn, bbu wani boye boye kuma, hawaye ne cike idonta ta karashe maganar tana kai wa nn kuma ta mike ta fice daga dakin da sauri, Abba ya bi ta da kallo daga karshe ya jinginar da kansa a hnkli jikin kujera ya lumshe ido don yasan shine sanadin faruwan komae, he never wished for a day like this a rayuwarsa.


Eeshatullah

πŸŒΈπŸ‘©πŸ» 'Ya Mace kyautar AllahπŸ‘©πŸ»πŸŒΈ

A true life love story

By Ashmaad

61....
Karfe sha daya saura duk yan gidan suka hallara a falon Abba, Aliyu kadae ne baya falon duk da kiran da Jiddah taje tayi masa, bayan kusan minti biyar kowa ya nutsu a falon, Mami ta kalli Adnaan tace "ina Ali?" Mikewa yyi ya fita, ba a dau lkci ba Adnaan ya dawo falon yace yana xuwa, da sallama can ciki Aliyu ya shigo falon yana sanye da jallabiya milk colour ya nemi gefen Safiya dake ta binsa da kallo ganin ynda yayan nata ya rame, ba ita ba duk kanninsa kallonsa suke hka ma Abba, Abba ya fara gaidawa snn Mami duk kansa a kasa don tunda garin Allah ya waye bae fito ba sae ynxu, Afeefah kam na xaune kasa daga gefen Mami, ita kadae Aliyu ya daga kai ya kalla suka hada ido, da sauri ta sunkuyar da kanta ta boye fuskarta jikin Mami, ya kuma sunkuyar da kansa kasa, Adnaan ne ya bude wajen da Addu'a bayan 'yan mintuna Mami ta fara magana kmr hka "Na so ace, ko kuma ince na sha fatan kadda Allah ya nuna min rana irin ta yau da ma abinda nake shirin fada ma kowa ynxu, sae dae am mistaken, ya xama dole in bude ma kowa wnn sirrin yau, Da farko dae ina san ku san na shigo gidan Mahaifin ku a shekara ta 1986, lkcn Aliyu na da shekaru uku a duniya, ran da na cika shekara daya a gidan aka haifi Adnaan kuma a ranan Allah yyi ma Mahaifiyar su Aliyu rasuwa, Wanda hkn yasa rikon marayun ya dawo hannu na, na kwashi shekaru fiye da uku ban haihu ba, daga karshe Allah ya bani 'ya ta ta fari Safiya, bayan shekara biyu na haifi Ummi, daga Ummi kuma na haifi Suhaila warce Allah yyi ma rasuwa ran da na haifi kanwarta Sadiya, to dama tun a haihuwar Suhaila na fara fuskantar matsala da mahaifin ku, inda yake nuna min shi fa yafi son 'ya ya maxa, ana dae xaune a hka har Allah ya kuma ban wata 'ya macen Wanda ba karamin canji naga daga gun Mahaifin ku ba, anyi suna da sati daya jaririyar Maryam ta koma ga Allah, bayan shekara daya da wani abu na haifi Jiddah," Shiru Mami tayi da dukkan alaman bata son ba yaran nata tarihin irin wahalar da tasha gun Mahaifinsu don tana haifan 'ya 'ya mata, hawaye ne kawae ke sakko mata, daga karshe ta ci gaba cikin sanyin murya tace "Jiddah na da wata Shidda Mahaifin ku ya kara aure, wato ya auro warce xata haifa masa 'ya 'ya maxa, bae san duk _YA MACE KYAUTAR ALLAH_ ce ba," hawaye ssae Mami take hka ma duk yaran nata mata dake kallonta a sanyaye, da kyar ta saita kanta ta ci gaba "Jiddah na da shekara daya cif a duniya na rabu da Mahaifin ku, wato ya sauwwake min, bae kuma yarda na tafi da ita ba bare yayyinta duk da naso yin hkan don nasan irin wahalan da xa su sha gun matar ubansu don bata da imani matar kuma ita ce sanadin rabuwa na da Mahaifin ku, amma bbu ynda na iya na tafi na bar ku" Kallonta kawae duk yaran nata mata suke suna hawaye, barin Zainab, Aliyu da Adnaan da Safiya sae ummi ne kaddae basu yi mamakin jin lamarin ba don da alamar sun san lbrin sae dae su ma duk jikinsu yyi sanyi, Mami ta ci gaba a sanyaye, "Ina fita idda da 'yan watanni Allah ya hada ni da Mahaifin Zainab" Mike Afeefah tayi da sauri hawaye na bin kuncinta xata bar falon Mami tayi hanxarin rikota ta mayar da ita ta xaunar tace "bbu inda xa ki Zainab" kuka ssae Afeefah take me ban tausayi, su Jiddah, Sadiya da Sumayya ma duk kukan suke, Abba dae har lkcn bae iya ya dago kansa ba, Mami tace "Ina auran Alhaji Umar da shekara daya da watanni biyu Allah ya bani Zainab, wata 'ya macen dae, tana kuma da shekara daya a duniya Allah yyi ma Mahaifinta rasuwa a hatsarin mota," Hade kai Afeefah tayi da gwiwa tana kuka kmr an aikota, Mami ma hawayen take har lkcn, don da kyar ta iya ci gaba tace "Ni baxan bada lbrin ynda rayuwar yayyinku ya kasance hannun matar uba ba kuma baxan ce nasan dalilin rabuwar ta da Mahaifin ku ba, sae dae nasan bayan rasuwan Mahaifin Zainab Mahaifin ku ya dawo yana min magiya yana ban hkuri in koma in rike 'ya ya na, dake Allah yyi xaman mu bae kare ba kuma akwae sauran rabo hka ba don na so ba na koma gidan Mahaifin ku, inda Allah ya kuma axurta ni da 'ya 'ya matan har biyu," Mami ta rungumo Afeefah jikinta ganin ynda take kuka, tana kallon duka yaran nata cikin sanyin murya tace "Kin ji matsayin ki a gidan nn Daughter, kuma Kaduna da kike xuwa sune dangin Mahaifin ki, Alhaji Mukhtar shine yayan Mahaifin ki uwa daya Uba daya" kin cewa komae Afeefah tayi sae boye fuskarta da tayi jikin Mahaifiyarta tana kuka ssae, bayan kusan minti uku Mami tace "Jiya Aliyu ya bullo min da wani lamari da ban taba xato daga gare shi ba, ban kuma taba kawo hkn a ka ba," Shiru tayi snn ta cigaba tana kallon yaran nata "wae 'yar uwarsa Zainab yake so da aure" kallon mmki Adnaan ya juya da sauri yana ma Aliyu da kansa ke kasa, hka ma su Safiya da Ummi, su jiddah kam kusan kallon tsoro suke masa, Mami tayi murmushin takaici tace "Ehh kwarae kuwa akwae aure tsakanin sa da Zainab na sani, amma get this Aliyu: Ni Zuwaira baxan taba baka auren 'ya ta ta xo tana haifa maka 'ya 'ya mata ka walakanta min ita ba, Neva!" kallon mmki Abba ya dago kai yake mata, hka ma Aliyu da ya dago da sauri yana kallonta da idonsa da ya kada ssae, su Safiya ma kallon mmkin suke mata, ita kam ko a jikinta ta ci gaba "gobe idan Allah ya kai mu xan tura Zainab gun dangin Mahaifinta su aura mata Wanda suka yi niyya tun farko, Wanda suka kuma ga ya dace da ita don nasan baxa su cuceta ba, amma da in baka auren Zainab Ali gwara ta xauna ba aure" Mami na kai wa nn ta mike ta daga Zainab suka fice daga falon.

Eeshatullah πŸ˜‚πŸ˜‚

Chaii Mami kin burge wllh.

[5/22, 07:57] Umar Dalha: πŸŒΈπŸ‘©πŸ» 'Ya mace kyautar AllahπŸ‘©πŸ»πŸŒΈ

A true life love story

By Ashmaad

62.....
Aliyu ne ya fara karfin halin mikewa ya bar falon bayan fitan Mami da Zainab, snn Adnaan, daki ya nufa ya dauki makullin motarsa ya fita daga gidan gaba daya. Bbu Wanda ya samu fuskar yi ma Mami magana yinin ranan, don a daki ta yini da Zainab, duk kayan da tasan Afeefah xa ta bukata ta hada mata a jaka don gobe da sassafe xata je ta sa ta a motar kaduna, da daddare misalin takwas da wani abu Jiddah ta shigo dakin Mami, tana kallonta tace "Mami wae Abba yace in kira Afeefah" Mami tace "Tana xuwa" juyawa jiddah tayi ta fita, Mami ta mike tana kallon Afeefah tace "tashi mu je" da kyar Afeefah ta mike ta bi bayan Mami suka nufi falon Abba, tsayawa kallon Mami Abba yyi da mmki, Mami ta nemi gu ta xauna tace "Ga ta" wani murmushin takaici yyi yana kallon Afeefah yace "Je ki Zainab" juyawa Afeefah tayi ta fita daga dakin a sanyaye, Abba yace "Wato kin ban mamaki ne Zuwaira, ko ance min xa ki iya yima ni, da 'ya yan ki cin fuskar da kika mana da safe baxan yrda ba, dama laifin wani yana shafan wani Zuwaira, naga ko Allah ka nemi gafara wajensa yana yafe maka, balle mutum, ynxu ki dubi tsabagen idona kice baxa ki ba Ali auren 'yar ki ba, kin kyauta min da 'ya yan ki knn" Mami tayi murmushi tace "Ban kyauta ba nasani, amma dats d last thing I will do on earth in ba Aliyu Zainab, Allah ya xaba masa warce ta fi ta don ita ma nasan karshenta 'ya 'ya matan xata je tayi ta haifo masa" tana kai wa nn ta mike ta fita. Xaune ta samu Safiya da Ummi a bedroom dinta, Mami ta xauna tana kallonsu tace "ya aka yi?" Duk da irin shakkarta dake bayyane a fuskokinsu hkn bae sa Safiya tayi kasa da gwiwa ba tace "Mami don Allah magana ta fahimta xa mu yi" Mami ta hade rae tace "wace maganar ce ta fahimta? Ina jin ku" Safiya ta sunkuyar da kai tace "Mami ki dubi girman Allah ki mance duk wani abinda ya faru a baya, Mami don mu 'ya yanki xa ki yi hkn, don Allah ki yi hkuri ki ajiye batun da kika yi daxu a falon Abba, kin fi kowa sanin halin Yayanmu tunda...." Dakatar da ita Mami tayi ta hanyar cewa "Ku bar min daki na" ganin basu da niyar tashi yasa ta daka masu tsawa, Mikewa suka yi kusan a tare jiki a sanyaye suka bar dakin, Mami ta ja tsaki ta shiga bayi.

Afeefah na kwance ita kadae dakin Mami misalin sha daya saura na dare tayi jigum kmr mara lfya, Mami kuma ta shiga yin wanka a bayi, bude kofar dakin da aka yi yasa ta saurin dago kanta don ganin Wanda xae shigo, Anty Safiya ce ta shigo dakin, ta karaso kan gadon ta xauna tana kallonta, Afeefah ta mike xaune ita ma tana kallonta lkci daya hawaye ya taru idonta, Anty Safiya ta jawo ta jikin ta cikin lallashi tace "Kar ki kuma xubda hawayen ki Zainab, ba a taba cire ki cikin mutan gidan nn ba kuma baxa a taba ba, ki kwantar da hnklin ki Kinji little sis, duk daya muke a gidan nn wllh, amma ina son in maki tambaya daya Zainab" dago kai Afeefah tayi tana kallonta, Anty Safiya tace "Ae kina son yayanmu ko Zainab?" A tsorace Afeefah ta dago kai tana kallonta, lkci daya ta fashe da matsanancin kuka ta boye fuskarta jikin Anty Safiya cikin rawar murya tace "Wllh Anty ni bana sonsa, ni yayana ne shi, wllh yayana ne, yayanmu ne fa Anty" Shiru Anty Safiya tayi jikinta yyi sanyi kalau, amma bata ce komae ba, bude kofar bayin Mami tayi ta fito, cikin fada ta fara magana "kin ga ku kiyaye ni Safiya, ku kuma kame kanku tun kan ran ku ya baci a gidan nn, maxa fita ki bar min dakina" Mikewa Anty Safiya tayi jiki a mace ta fita daga dakin. Washegari ko breakfast din kirki Afeefah bata yi ba Mami ta dauki jakarta bayan ta ja ta sun je sun ma Abba sallama, shi dae ko iya bude baki bae yi ba har suka fita daga dakin, duk yan matan gidan dake xaune jigum a falo suka bi uwar tasu da kallo har ta fita daga falon tana rike da Zainab, Adnaan dake xaune balcony bae ko kallesu ba har suka sauka balconyn, Mami kam ko a jikinta don ko gaisheta yau ma bae yi ba, Sae da Mami ta ga tashin motarsu Afeefah snn ta juyo gida. Karfe goma da rabi Zainab ta isa gidan kawunta a Kaduna, a gajiye ta shigo falon, dake Momy ta san da xuwanta don Mami ta kira ta shaida mata ta mike da sauri da fara'a ta karasa ta amshi jakarta tana mata sannu da xuwa, jin hka su Ilham suka sakko kasa su ma suna welcoming dinta cike da murnar xuwanta, murmushi kawae Afeefah ke kirkira har suka haura sama snn ta fada kan gado ta yi kwanciyarta. Kyaleta su ilham suka yi sanin ta gaji, suna fita daga dakin nn da nn bacci ya dauketa. Da matsanancin ciwon kai Afeefah ta farka da azahar, ta mike da kyar ta nufi bayi don yin alwala, ko da ta idar kasa mikewa tayi daga gun, lkci daya hawaye ya cika idonta tunawa da tayi wae fa ashe ita agola ce a gidansu na kano, kuka ssae ta fashe da tuno maganganun Mami na jiya da ta dinga yi, dama ya Aliyu ba Muharraminta bane, to don me ake ta boye mata matsayinta, Dr Sharif ne ya fado mata, hkn yasa tayi karfin halin mikewa da sauri ta nufi wayarta dake kashe cikin jaka ta fiddo ta kunna, ta jima tana kallon wayar daga bisanni tayi dailin nmbr Dr Sharif, bugu biyu ya daga, a sanyaye tayi masa sallama, shima cikin sanyin murya ya amsa yace "yhu left me vry worried about yhu Dear, me sa kike kashe wayar ki now a dayz pls" Sunkuyar da kanta tayi cikin sanyin murya tace "Kayi hkuri bbu charge ne" shiru yyi snn a hnkli yace "Are yhu still in Abj?" Girgixa kai tayi murya can kasa tace "No! Am in Kaduna ynxu" yace "Are yhu serious plss?" Dan murmushi tayi tace "Allah" yace "Waow m also in Kaduna ynxu, I just landed, jiya uncle din ki ya bukaci in xo if m less buzy, sauka na knn wllh, but let me ask yhu plss neman me yake min?" Xaro ido tayi tace "Nima daxu fa na xo sir, I don't knw" yace "Shknn, sae na shigo anjima da yamma, Allah sa kiran alkhairi ne Zainab" a sanyaye tace "Ameen" yace "Me kike son in taho maki da?" Murmushi tayi murya can kasa tace "Abu me ddi sir" murmushin shima yyi yace "Ok" sallama ya mata ya katse wayar, dai dai nn Anty Jamila ta shigo tana murmushi tace "Sarkin shagwaba sakko mu yi lunch, ina fatan kinyi sllh?" Afeefah tayi murmushi tace "Nayi Anty" snn ta mike ta bi bayanta. Ko da Afeefah ta koma sama bayan ta dan cakalkala abincin wanka tayi ta wanke bakinta ta fito snn ta dauki yar doguwar rigar ta shara shara mara nauyi ta sa, ta dauki net dinta ta saka a kanta, snn ta dauki wani nvl din Ilham dake dakin ta shiga karantawa absentmindedly, nvl din na hannunta har aka kira la'asar jin xa a tada sllh yasa ta Mike ta shiga bayi, ko da ta idar da sllh komawa tayi kan gado ta kwanta ta dalilin Sara mata da kanta yake ba kadan ba, har wani rufewa idonta yake tsabar ciwon da kanta ke mata, gashi taki nuna ma 'yan gidan bata jin ddi su kuma suka yi tunanin ko duk gajiya ne tunda mota ta biyo, hkn yasa Momy ta bata paracetamol ta kuma ki sha ta boye, wayarta dake ring ta jawo da kyar ta daga tare da karawa a kunnenta, muryan Wanda ta ji yasa xuciyarta ya kusa shigewa cikin ta don tsoro, cikin sanyin muryarsa me ddin sauraro ya kira sunanta a sanyaye, jikinta ne ya dau rawa lkci daya ta katse wayar snn ta kashe gaba daya ta jefar ta cusa kanta cikin pillow ta fashe da matsanancin kuka jikinta na rawa, ta jima tana kuka daga karshe bacci ya dauketa. Ko da Aneesah ta shigo dakin don yin alwala samunta tayi cikin bargo, ta yaye bargon tace "Lallai ma Zainab wae har ynxu gajiyan ne hka, baccin yamma ma da bae da kyau," shiru tayi jin jikinta ya dau xafi ba kadan ba, da mmki Aneesah tace "Baki da lfya ne Zainab," Afeefah ta bude idonta da ya sauya kala ta kasa ba Aneesah amsa sae hawaye da ta shiga yi, Aneesah ta juya da sauri ta fita, ba a dau lkci ba suka dawo da Momy da Anty jamila, Momy ta dago ta tace "Subhanallah baki da lfya ne dama Zainab?" Afeefah bata ce komae ba sae kuka da ta fara yi, hkn yasa hnklin Momy ya tashi ta juya tana kallon Jamila tace "Ke kira min saleem ya xo ya kai mu asibiti" Juyawa Jamila tayi da sauri ta fita, ba a dau lkci ba ta dawo tace "Mami baya dagawa ina jin yana masallaci" Da damuwa Mami tace "gashi ni bna driving da daddare ko xaki iya Jamila?" Jamila tace "Da sauki Momy, ki bari nasan ana idar da sllh ma xae shigo," Tare Dr Sharif ya shigo gidan da Saleem, Jamila dake falo tana jiran shigowar yayan nata tayi masu sannu da xuwa bayan ta gaida Dr Sharif da fara'arta snn tace "ya Saleem kae fa muke jira tun daxu, asibiti xa ka kai mu Zainab bata da lfya" kallonta Dr Sharif ya tsaya yi, Saleem yace "Kai Haba me ya sameta?" Da damuwa Jamila tace "ta ki fadi, sae kuka take" Saleem ya kalli Dr Sharif yace "Dr mu je" ba musu Dr Sharif ya bi bayansa, suna shiga dakin ya tsaya kallon Afeefah da ke rungume jikin momy idonta rufe, Momy na ganin Dr Sharif tace "A'a Aliyu ashe ka iso, sannu da xuwa" dan murmushi yyi ya gaida ta ya karaso bakin gadon yana kallon Afeefah da ta bude ido tana kallonsa lkci daya tayi saurin kulle idon, a dan sanyaye yace "Momy me ya sameta" Momy tace "Wllh bamu sani ba, tun da ta xo dama naga yanayinta, wae da asibiti xa mu ynxh" Durkusawa yyi bakin gadon yana kallon Afeefah cikin sanyin Murya yace "Zainab!" Bude ido tayi a hnkli tana kallonsa, jin ta ki cewa komae yasa Momy ta saketa tace "Bari in baku waje" tana fita Jamila ta bi bayanta snn Saleem, Dr Sharif ya mike da damuwa ya xauna gefenta yace "Tok to me plss Zainab ina ke maki ciwo," bargon jikinta ya cire ta koma baya ta dukunkune waje daya da sauri Sbda kayan dake jikinta, dauke kai yyi har ta rufe jikinta da bargo snn ya juya ganin ynda idonta yyi ja ssae yasa ya kai hannunsa goshinta jin xafi yasa yace " Subhanallah, Mu je asibiti?" Da sauri tace "A'a!" Yace "To gaya min inda ke maki ciwo" a hnki tace "Kai na ke ciwo"

Eeshatullah Goni

[5/22, 07:57] Umar Dalha: πŸŒΈπŸ‘©πŸ» 'Ya mace kyautar AllahπŸ‘©πŸ»πŸŒΈ

A true life love story

By Ashmaad

63.....
Da damuwa Dr Sharif yace "Tun yaushe kan ke maki ciwo?" Komawa tayi ta kwanta don wani sanyi take ji ba kadan ba, murya can kasa tace "Tun jiya" observing dinta kawae Dr Sharif ke yi bae ce komae ba har Saleem ya shigo dakin da sallama, yana kallonsu yace "Ta gaya maka Dr?" Dr Sharif ya mike yace "Ehh kanta wae ke ciwo, kuma na ga xaxxabi a jikinta" Saleem yace "To ya xa mu yi ynxu?" Dr Sharif yace "Mu tafi clinic, she need drip frm wat I've noticed" Mikewa Afeefah tayi xaune da sauri ta fashe da kuka tace "Sir ni wllh baxan je asibiti ba, kawae idan nasha magani xan samu lfya nasani" Saleem yace "C'mon wani maganin xaki sha bayan Wanda momy tace ta baki daxu, clinic xa mu tafi ynxu ki tashi ki shirya" ganin ynda Zainab ke kuka kmr an aikota yasa Dr Sharif yace "Olryt, tun da baki son asibiti bari in siyo in sa maki a gida, is dat OK?" Da sauri tace "Ehh!" Saleem yyi dariya yace "Ashe ma ciwon na gulma ne dae," Dr Sharif yyi murmushi suka fita dakin a tare. Afeefah ta fara bacci Anty Jamila ta tasheta, da kyar ta mike xaune ta jinginar da kanta jikin gado, da ganinta kasan tana jin jiki, ido hudu suka yi da Dr Sharif da ke tsaye gaban mirror yana hada drip yana kallonta ta mirror'n, murmushi ya sakar mata, ta turo baki ta dauke kai tana kallon Anty Jamila dake mika mata cup din tea, karba tayi ta shiga shan tean a hnkli, jin tashin da xuciyarta yake yasa ta ajiye tace ta koshi, Jamila ta fita daga dakin da cup din sauran tean, karasowa kusa da gadon Dr Sharif yyi yace "Har kin koshi" tace "Uhm" tana kallonsa har ya rataye ledan ruwan snn ya durkusa kusa da ita a hnkli yace "Ur hand" marairaicewa tayi tace "Sir baxae min xafi ba?" "Idan kika rufe ido" yyi assure dinta, a hnkli ta mika masa right hand dinta ya karba, a tare suka dago kai suna hada ido duk suka yi saurin sunkuyar da kai, ganin ya dauki dan alluran ta saka kuka tana yarfe dayan hannun, wani yar kara ta saki ta fixge hannunta jin shigar alluran vein dinta, lkci daya ta saki kuka ta sakko da kafafuwanta kasa daga kan gadon tace "Wllh sir akwae xafi ni dae" hade rae yyi yace "Yhu are joking" kamo hannunta ya kuma yace "Ki fa tsaya Zainab ko mu tafi asibiti, yhu see m almost missin jam'i" runtse ido tayi jin alluran har cikin ranta ta dafa sa ta saki kuka, da sauri yace "Take ur hands off me" ba shiri ta cire hannun, har ya gama sa mata drip din bata daina kukan da take ba, ya mike yana kallonta murmushi dauke fuskarsa yace "Yhu are vry funny" bata ce komae ba sae shirin kwanciya da ta shiga yi, yace "Wait saura allura" xaro ido tayi tace "Ba ga shi ka yi min ba a hannu" ya girgixa kai ya dauko alluran ya nuna mata, tuni ta kuma marairaicewa tace "Sir don Allah ka xuba cikin drip din ae ana yin hka" murmushi yyi yace "Wnn ba a xuba wa drip Zainab" hawaye ya xubo idonta tace "To a ina xaka min alluran," da sauri tace "A hannu?" Rasa me xae ce mata Dr Sharif yyi, ya ajiye alluran ya juya yace "Bari in tafi masallaci" Bin sa da kallo tayi har ya fita, snn ta bi drip din hannunta da kallo, yana fita Momy da Su ilham suka shigo dakin, Suna mata ya jiki, duk da ita bata ji ko wani sauki ba a hnkli tace "Da sauki" Anty Jamila ta shigo dakin da tsire a plate da hollandia drink ta ajiye mata tace "Tashi ki ci Zainab," To kawae Afeefah tace, Momy dake xaune gefenta tace "Wnn me xae mata, in xubo maki shinkafa Zainab?" Afeefah ta girgixa kai tace "Na sha tea fa Momy" suna xaxxaune dakin dad yyi Sallama ya shigo dakin Dr Sharif na biye da shi a baya da saleem, Momy ta mike su Aneesah ma hka suka fita daga dakin, Dad yace "Sannu Ummi, ya jikin" sunkuyar da kai Afeefah tai tace "Da sauki dady" gaishesa tayi snn tayi masa sannu da dawowa, ya tambayeta ya hanya da su Abbanta duk tace "Suna lfya Abba" Godiya dad yyi ma Dr Sharif snn ya fita daga dakin, Saleem ya kalli tulin tsiren dake gefenta yace "tab, duk ke xa ki cinye wnn Zainab" hararansa tayi tace "Toh xa ka ci ne?" Dariya yyi yace "A'a ni yau bnyi kuka da ihu nace kai na na ciwo ba, na masu yin hkn ne" xaro ido tai kmr xata yi kuka tana kallon Dr Sharif tace "Sir ka gansa ko?" Juyawa saleem yyi ya fita yana dariya, Murmushi Dr Sharif yyi yace "yi hkuri shima xae xo kansa wataran, ya ciwon kan?" Tace "Sir yana min fa har ynxu" ya kalli ruwan yace "To baki bari an maki allura ba" xaro ido tayi tace "Kai fa kace xaka tafi mosque" Karasowa kusa da ita yyi ya

Please Login or Register in order to submit comment