Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewa "wayyo na shiga uku ina da test yau" wanke baki tayi tayi wanka ta fito da sauri, takwas saura kwata ta gani, tana hawayenta na gado tayi sauri ta shirya snn ta figi jakarta bayan ta sa hijab ta fice daga dakin, bbu abinda Jiddah da Sadiya suke bnda dariya, Mami da fitowarta daga kitchen knn tace "ke ina xa ki kinyi break ne?" Kuka ta fashe da tace "Kinga Mami yau ina sa test Karfe takwas shine bbu wanda ya tasheni gashi na makara ynxu" Mami ta watsa mata harara tace "Akwae wnda kika ajiye sa xae dinga tashin ki ne, da'alla wuce kiyi breakfast" Afeefah ta kuma fashewa da kuka tace "ni baxan yi ba nayi latti" Adnaan dake xaune falo yana sa safar kafa yace "Ke da'alla wuce ki ci abinci," tana hawaye tace "ni baxan ci ba Dubi fa Karfe nawa" mikewa yyi, yyi kanta da gudu ta nufi dinnin tana rusa kuka, sae a snn Mami ta haura sama, hka Adnaan ya tsare ta har sae da ta hada tea ta sha da bread, wajajen Karfe takwas da minti sha biyar ta fita daga gidan tana kuka. Ba ita isa faculty dinsu ba sae kusan takwas da rabi, tsaye tayi bakin lecture Hall din tana hawaye ganin har an fara test din ga student dayawa sun xo, kallonta kawae yake, taki dago kai, karasa wa yyi bakin kofa ya tsaya yana ci gaba da kallonta yace "Gud mrnin Ma'am Can we help yhu" juyawa tayi da sauri ta bar wajen tana ci gaba da kukanta. Ana idar da sllh Afeefah ta dawo class duk da basu da lecture da gninta ranan kasan ba karamin kuka ta ci ba, ko kadan bata damu da dariyar da yan ajin ke mata ba don ixuwa ynxu tasan kukanta ke basu dariya, wani handout take dubawa ita kaddae a xaune don yau din ma Maryam bata xo ba, Class rep ne ya shigo class din ya nufi seat din da take yace "Malama Zainab, Dr Aliyu yace ki je office dinsa," xaro ido tayi lkci daya gabanta ya fadi tace "Ni?" Yace "ehh mana" kai kawae ta iya gyada masa ya wuce, ta fi minti goma a xaune snn ta Mike kmr mara laka ta fita daga class din, office dinsa ta nufa, a hnkli ta kwankwasa masa kofa, ya amsa da "come in" tura kofar tayi shima a hnkli ta shiga office din da sallama can ciki, suna hada ido ta sunkuyar da kai da sauri tace "Ga ni Sir" jin bae ce komae ba yasa ta dago kai a hnkli tana kallonsa, kallonta taga yana yi lkci daya ya sauke idonsa kasa yace "sit" ba musu ta karaso ta xauna kan kujerar dake facing din nasa, ya ajiye pen din hannunsa yace "y were yhu late today" hawaye ne ya cika idonta muryarta na rawa tace "bbu Wanda ya tashe ni yau har sae da nayi latti, kuma Mami tace sae nayi breakfast bayan nayi latti" cikin muryan kuka ta kare maganan, jin be ce komai ba yasa ta dago kai tana hawaye tana kallonsa, murmushi ta ga yana yi, ta yi saurin sunkuyar da kanta tana share hawayen, "Are yhu now ready for d test?" Gyada masa kai tayi da sauri ba tare da ta kallesa ba, fullscap ya 6alla ya mika mata da pen ta karba, yace "am dictating d questions for yhu" ta gyada masa kai snn ya shiga dictating mata questions din, yana gamawa yace "answer 3 out of d five, am giving yhu 20 min" a hnkli tace "OK sir" wani kujera daban ya nuna mata ta koma ta xauna tana kallon questions din hannunta kmr me shirin kuka ganin ko question daya bata gane ba, dago kai tayi a hnkli don kallonsa, suka hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta, ta fi minti goma ta kasa amsa ko daya, sae take ga kmr bae taba koya masu topics din da take gani yyi question a kai ba, mikewa taga yyi ya dauki books ya fita daga office din, hawayen dake makale idonta ya gangaro mata, bayan fitansa da minti biyar Abdul ya shigo yana ganinta yace "lah ashe baki samu test daxu da safe ba" kai kawae ta gyada masa ya ajiye abinda xae ajiye xae fita tace "don Allah Abdul mun yi topics din nn" dawowa yyi yana kallon questions din yace "kai ai shine farko ma a semestern nn, amma ni kaina na manta, komawa yyi kan table din office din yace " lah ga text book xo ki bude ki duba da sauri kafin ya shigo" xaro ido tayi a tsorace tace "Textbook?? Ni tsoro nake ji kar ya shigo" Abdul yace "tab ae kuwa xa ki fadi, can cafeteria fa naga ya nufa ba ynxu xae dawo ba" kmr xata yi kuka tace "to ae ban san page din ba" Abdul ya shiga nema mata page din da sauri, yana gani yace "xo kiyi sauri ki kwafa ga shi nn" da sauri Afeefah ta karasa kusa da table din hannunta na rawa ta soma copy din answer din, Abdul yace "kiyi sauri kafin ya shigo kuma ba dukka xa ki kwafa ba" juyawa yyi xae fita Afeefah ta xaro ido a tsorace tace "tafiya xa kayi" yace "Kinga sauri nake, ke dae kiyi maxa kafin ya shigo," yana kai wa nn ya fice daga office din, har wani xufan tsoro Afeefah ta shiga yi ga wani rawa da jikinta yake, ji tayi an bude kofar office din, suka yi ido hudu da shi, mikewa tsaye tayi a rikice ta saki pen din hannunta lkci daya ta fashe da kuka tana kallonsa, karaso wa table din yyi yana kallon textbuk din gabanta, durkushewa kasa tayi cikin kuka tana yarfe hannu tace "Don Allah don Annabi, kayi hkuri sir, ban iya bne" daukan papern test din nata yyi yana kallon abinda ta rubuta, wani mugun kallo da ya kada mata hanjin cikinta ya daka mata yace "Stand up" jikinta na rawa ta mike, yace "come here" karasawa tayi kusa da shi tana hawaye har lkcn jikinta na bari.

Kuyi hkr kamar yadda na fadi maku banjin dadi neh, yau kun samu... Godiya dubu😍😍

Eeshatullah 😘😘
😘
[5/22, 07:56] Umar Dalha: πŸŒΈπŸ‘©πŸ»'Ya Mace Kyautar Allah πŸ‘©πŸ»πŸŒΈ

A true life love story

By *Ashmaad*

15......



Kallonta ya tsaya yi fuskarsa daure bayan ta karaso gabansa yace "Leave My office!" Kin fita Afeefah tayi tana kuka ssae ta koma baya tace "Sir wllh am nt the one dat opened the textbook, don Allah kayi...." Wani tsawan ya kuma daka mata yace "Get out," Afeefah ta bar wajen da sauri ta koma can jikin bangon office din ta dinga rusa kuka har da buga kafa a kasa tana cewa "Don Allah sir kayi hkuri wllh I'm nt d one dat open d textbook bani bace ba wllh" Ajiye textbuk din hannunsa yyi yace "fita nace" nn ma taki fita sae rusa kuka take, xagawa yyi ya xauna kan kujerarsa ya ci gaba da aikinsa, har aka kira la'asar Afeefah bata fita daga office din ba kuma bata bar kukan da take ba, Mikewa yyi ba tare da ya bi da kanta ba ya fita daga office din don xuwa masallaci, har ya dawo bayan minti kusan ashirin Afeefah na durkushe inda ya bar ta, sae a snn ta mike ta dauki jakarta ta nufi kofa a sanyaye ta fita, bin ta yyi da kallo har ta rufo masa kofar. Main Gate Afeefah ta nufa don bata jin xata iya jiran yayyinta, ta tsaida adai daita ta gaya masa inda xata. Tana isa gida ta ba sa kudinsa ta nufi cikin gidan, Zaune ta samu Mami da su Sumayya a falo, ta xube kasa ta fashe masu da kuka, Mami ta Mike a rude hka ma su sumayya duk aka shiga tambayarta me ya faru ina su Sadiya, cikin kuka tace "Suna sch" Mami tace "to me ya dawo da ke ynxu, me faru" cikin kuka tace "ni kaina ke man ciwo" tsayawa kallonta Mami tayi, can ta haureta tana huci ta wanka mata mari tace "wllh baxa ki fasa min xuciya ko ki daura min hawan jini ba Zainab, don uwar ki don kan ki na ciwo sae ki shigo ki ruda mutane??" Da gudu Afeefah ta mike tun kan ta kuma kai mata wani marin ta nufi sama tana ci gaba da rusa kuka. Har su Jiddah suka dawo bbu wnda ya bi ta kan Afeefah da ke daki har lkcn, sadiya tace "Afeefah ta dawo" Su Sumayya suka ce eh, Jidda tayi tsaki tace "Gskya Mami ki gaya ma Afeefah ta daina daga ma mutane hnkli, idan xata tafi gida ba sae ta xo ta ce mana ta wuce ba hka kawae xata ba mutane wahala ayi ta neman ta" Mami tace "duk ran da baku ganta ba kuyi tahowar ku kawae,"
Da daddare duk yan gidan na xaune falo suna kallo Adnaan dake danna laptop yace "wae ina Afeefah ne?" Rahma tace "tana daki tun daxu" Mami tace "Kai ma ka kula bata falon, ae na kusa fara dukan Afeefah a gidan nn, ko kanninta basa min iskan cin da take min," sae da Abba ya shigo shi ma ya tambayi Afeefah snn Adnaan ya mike ya nufi sama ya bude dakin da yasan xae sameta ya shiga, kwance ya ganta cikin bargo ya karaso kan gadon ya yaye bargon yana kallonta, mikewa tayi xaune tana mitsika ido, ya galla mata harara yace "me aka maki?" Kanta ta nuna masa a hnkli tace "kai na ke man ciwo" dafa goshinta yyi ya ji xafi, yace "tun yaushe?" Kmr xata yi kuka tace "tun da rana" juyawa yyi ya fita daga dakin ba a jima ba Jiddah ta shigo dakin da abinci ta ajiye mata tace "ya Adnaan yace ki tashi ki ci" bnxa Afeefah tayi mata Jiddah ta juya ta fice, bayan kusan minti ashirin Adnaan ya dawo dakin rike da ledan magani, ya wani hade rae yana kallonta yace "baki tashi kin ci abincin ba yar rainin wayo" Afeefah ta sakko daga kan gadon hawaye cike idonta, hka ya tsareta har ta ci abincin snn ya bata magani ta amsa ta sha ya juya ya fice. Hka Afeefah ta kwana da xaxxabi daren ranan, bbu Wanda ya lura da hkn har suka sauka kasa yin break, ganin irin hararan da Mami ke watso mata yasa Afeefah ta shiga hada tea kmr ynda yayyinta suka yi, kmr kar ta kai cup din tean baki ta mike da gudu jin amai ya taso mata ta bar dinnin din kan ta karasa bayi hat ta soma kwarara amai, Jiddah ta mike tabi bayanta da sauri hka ma Mami, Amae ta dinga yi kmr xata amaye hanjin cikinta, Adnaan ya sakko hka ma Abba duk suna tambayar me ya sameta, Mami dae na tsaye bata ce komae ba, Jiddah ta taimaka mata ta shiga bayi don gyara jikinta, Abba na kallon Mami yace "me ya sameta?" Mami tace "Nima bn sani ba wllh" Abba ya dubi Adnaan yace "Dauko makulli a tafi asibiti" bbu bata lkci Adnaan ya dauko makullin motarsa ya nufi asibiti da Afeefah, kuka ta dinga rusa masa a mota wae kanta na ciwo har suka isa bbu bata lkci suka ga likita da yake da safe ne, bayan ya gama mata tambayoyi da rubuce rubucensa yace "kina sa damuwa ne a ran ki da yawa, kuma naga alamomin malaria a tare da ke xa mu yi maki karin ruwa"

Yau kwanan Afeefah uku rabonta da sch kuma ko kadan bata damu ba ita a dole ba lfya, hka kawae taji bata ma son xuwa sch din kwata kwata, da an mata maganar makaranta sae ta kuma langwabewa tace kai ko ciki, bata da aiki sae na danne dannen waya da kallo, yau kam tun safe take fara'a tunda ya Aliyu na hanya, Mami ta shigo dakin ta sameta kwance sae game take, tana ganinta tayi lamo kan pillow, Mami ta tabe baki tace "in Kinga kin xauna min gida gobe to shure shuren mutuwa kike," Afeefah ta turo baki kmr xata yi kuka Mami ta ajiye abinda xata ajiye ta fice daga dakin, Karfe sha daya da kusan rabi ta ji mai gadi ya bude gate, ta mike har tana tuntube ta nufi window din ganin Wanda ya shigo, Motar ya Aliyu ta gani, ta yi karan murna ta nufi kofa da gudu ta sauka downstairs bata bi ta kan Mami dake cewa ina xata da dangalallen rigan jikinta ba ta fice abunta, ya bude mota knn ya fito ta nufesa a guje ta rungumesa tace "oyoyo yayanmu" Murmushi ya sakar mata yana shafa kanta yace "baki je sch bane" ta turo baki tace "ba bani da lfya ba ka manta ne" ya xaro ido yace "har ynxu?" Langwabar da kanta tayi murya can ciki tace "ehh mana" ya kulle motarsa yace "Amma Adnaan yace min kin warke ae" bata fuska tayi tace "ko daxu fa sae da nayi amai, kuma har ynxu bna cin abinci, shi bae san komae ba" kama hannunta yyi ya nufi cikin gida da ita yace "idan na huta sae mu koma asibiti" kan rug Aliyu ya xauna ya gaida Mami dake falon a xaune, ta amsa tana murmushi tace "ya hanya Aliyu amma gudu kayi koh" ya shafa kai yace "A'a Mami ni bnyi gudu ba" tace "toh sannu, kaje ka huta bari in hado maka break" mikewa yyi Afeefah ma ta mike ta kama hannunsa suka nufi sama, ita ta hada masa ruwan wanka a bathroom dinsa ta fito ta samesa har ya soma bacci, ta hade rae ta shiga tashin sa tace "yayanmu na fa hada maka ruwan wanka" mikewa yyi ya xauna yace "na gaji da yawa ne" tace "to kayi wanka sae ka kwanta" ya gyada mata kai snn ya mike tsaye ya nufi bathroom.

Maryam ce xaune karkashin bishiya da wata kawarta sun fito daga lecture Karfe sha biyu, kawar me suna Fatima tace "wae har ynxu Afeefah bata ji sauki bne?" Maryam tace "ko daxu na kirata wllh, wae har ynxu jikin ne, tun da gobe da wuri xamu gama lecture xan kokarta in je in dubota" Fatima tace "Allah sarki Allah ya sauwake mata," Maryam tace "Ameen, ko xa ki rakani" Fatima tace "wllh Kinga akwae inda xa ni gobe da Mama da na raka ki wllh" Taku suka ji duk suka juyawa a tunaninsu wata course mate dinsu da suke jira ce, Fatima tace "Dr Shariff, ni dae mutumin nn na burge ni bbu ruwansa wllh" Maryam tace "ae kam bbu ruwansa duk cikin lecturers dinmu ya fi burgeni" shiru suka yi ganin ya karaso, duk suka gaishesa da ladabi ya amsa da dan murmushi a fuskarsa, har ya wuce ya dawo yana kallon Maryam yace "Maryam ryt?" Ta gyada masa kai tana murmushi, yace "ina kawarki Zainab?" Maryam tace "Wllh bata da lfya yau kwana uku," shiru ya danyi sae kuma yace "Me ya sameta?" Maryam tace "nima dae bn sani ba amma har anyi admitting dinta a asibiti, gobe ma xan je dubata" ya kusa second ashirin bae ce komae ba sae kuma ya juya ya bar wajen kawae.

Eeshatullah Goni 😘😘
[5/22, 07:56] Umar Dalha: πŸŒΈπŸ‘©πŸ»'Ya Mace Kyautar Allah πŸ‘©πŸ»πŸŒΈ

A true life love story

By *Ashmaad*

16......

Washegari kowa na ta shirin sch bnda Afeefah da tayi lamo kan gado, Jiddah dake xaune gaban madubi tana shafa mai tace "Wae Afeefah baki kallon agogo ne?" Afeefah ta galla mata harara tace "Bni da lfyan xan je sch?" Dariya Jiddah da Sadiya suka fashe da basu dae ce komae ba kowa ya ci gaba da harkan gabansa, Mami ce ta shigo dakin don ganin me suke har lkcn ba su sakko yin break ba, baki bude take kallon Afeefah tace "me kike har ynxu a kwance?" Afeefah ta mike xaune kmr xata yi kuka tace "Mami ni kmr amai nake ji" Karasowa Mami tayi cikin dakin ta nufi gun wayar rechargeable din dake gaban madubi, Afeefah na ganin hka ta mike da gudu ta fice daga dakin a tsorace, dakin Aliyu ta shige yana kwance yana bacci ta fasa masa kuka ya farka a rikice yana kallonta yace "Me ya faru," bae rufe baki ba Mami ta shigo dakin, Afeefah ta kuma fashewa da kuka ta nufi bayansa ta rikesa cikin kuka tana cewa "Don Allah yayanmu ka taimake ni Mami xata dokeni" Da sauri Aliyu ya rike wayar hannun Mami ganin tana neman shauda mata yace "don Allah Mami kiyi hkuri me tayi" tsawa ta masa tace "ka fita idona Aliyu, ka matsa ka ban waje" kin sake wayar Aliyu yyi yace "A'a don Allah kar ki doketa Mami, ki gaya min ne tayi" Afeefah ta kankamesa tana rusa kuka tana cewa "Wayyo yayanmu ka taimake ni" Fixgota Mami ta shiga yi Aliyu ya mike da sauri ya tare ta har lkcn yana rike da wayar hannunta yace "don Allah fa nace Mami" Afeefah na ganin hka ta nufi bathroom da gudu ta sa key, Mami ta fara ma Aliyu masifa kmr xata maresa shi dae bae ce komae ba ta juya ta fice daga dakin. Kulle kofar dakin yyi ya dawo ya nufi kofar bathroom yace "ae sae ki bude kofar" bude kofar tayi ta fito tana kuka har lkcn, ya galla mata harara yace "me kika yi" cikin kuka tace "yayanmu ban fa gama samun sauki har ynxu ba, wani lkcn sae in dinga jin amai, shine wae sae na je sch" wani mugun kallo yake mata lkci daya ya daka mata tsawa yace "a hkn ne baki samu sauki ba" wani sabon kukan ta fashe da ta durkushe nn tsakiyar dakin, yyi tsaki ya nufi bathroom. Har goma na safe Afeefah bata fito daga dakin Aliyu ba, wanka ma a bayinsa tayi, ya faki idon Mami ya tafi can dakinsu ya dauko mata kayanta, break ma a boye ya kai mata, ta ci ta sha hnklinta kwance tana kallo, yana danna laptop tana xaune gefensa tana kallo yace "gobe fa ko suma kike kisan sae kinje sch, gashi ynxu Kinsa Mami na jin haushi na" turo baki tayi tace "ae na sani"

Karfe hudu da minti goma Maryam ta fito daga faculty dinsu tafiya take tana kkrin kiran Afeefah da wayar hannunta don tayi mata kwatancen gidansu, shawara ta yanke kawae ta je ta samu su Jiddah su mata kwatancen gida, cikin rashin sa'a ta samu suna lecture, juyawa tayi kawae ta kama hanyar gate, Dr Aliyu ta gani ya fito daga office dinsa ya kulle ganin sun hada ido yasa ta tsaya don gaishesa, ya amsa da murmushi yace "ya lecture?" Tace "Alhmdllh" tafiya suka shiga yi don hanyar daya ne, ba tare da ya kalleta ba yace "ba tutorial ake maku a class ba Mae yasa baki tsaya ba" tace "Gidansu Afeefah nake son xuwa ne idan banje yau ba bani da tym kuma" yace "OK" parkin space suka isa ya nufi gun motarsa hkn yasa tace "Sae gobe sir" kai ya gyada mata yace "Allah ya kai mu" tada motarsa yyi, yyi reverse sae da ya iso inda take ya dan tsaya yace "idan ba damuwa shigo in rage maki hanya, if its OK by yhu" kasa cewa komae tayi gashi bata iya kallon fuskarsa tsabar kwarjinin da yake mata, xagayowa tayi kmr me tausayin kasa ta bude front seat din ta shiga da sallama wani dad'da'dan kamshi ya bugi hancinta , ba tare da ta kallesa ba kanta a kasa tayi murmuring din "Thnk yhu sir" "Welcm" kadae yace mata ya ja motar suka nufi gate. Sae da suka hau kan titi snn yace "jan bulo koh?" Da mmki ta daga kai tana kallonsa, to wa ya gaya masa, juyawa yyi ya kalleta lkci daya ya maida dubansa kan titi, Maryam tace "ehh can gidansu yake, amma ban san anguwar ba sae na kirata" bae ce mata komae ba ta shiga kiran Afeefah, Afeefah dake dakin ya Aliyu har lkcn ta dauki wayarta dake gefensa don ganin me kiranta, wara ido tayi tace "kawata ke kirana yayanmu, yarinyar tana da kirki ina sonta" bata jira cewarsa ba ta daga wayar, Maryam tace "Afeefah ki ban Address din gidanku ina hanya" Afeefah ta mike xaune da sauri tace "da gske?" Maryam tace "da gske mana," karan jin ddi ta saki tace "bari in maki text din sa ynxu" Maryam tace "kai Afeefah a hkn ne baki da lfya" tuni Afeefah ta kashe wayar ta shiga tura mata text din Address cike da jin ddi, Mika ma Dr Shariff tayi ya karba yana duba address din da suka xo traffic, yace "OK," snn ya mika mata wayarta, tace "ka gane wajen sir?" Yace "yea, ina da frnd a layin" Maryam bata kuma cewa komae ba har suka shigo layin, yyi parkin dae dae nmbr din Address din da ya gani, ya juya yana kallon Maryam yace "I think nn ne, ki kirata" Maryam ta shiga kiranta tace "ki fito ga ni a kofar gida" Afeefah ta doka tsalle tana kallon ya Aliyu da ke ta bin ta da kallo tace "ta xo yayana" hijab dinta ta figa ta daura kan 3 qtr gown din dake jikinta ba tare da ta bi ta kansa ba ta fice da gudu, kitchen ta nufa da sauri ta samu Mami tana girki ta marairaice tace "Mami kawata a sch ta xo gaishe ni bani da lfya tana gate wae" harara Mami ta watsa mata ta ci gaba da abinda take, kmr xata yi kuka ta fita tana isa balcony ba tare da ta bi ta kan takalmi ba ta nufi gate da gudu, leka waje tayi ta ga mota a Parke dae dae nn Maryam ta fito daga motar tana murmushi, Afeefah ta doka tsalle ta nufi gun motar ta rungumeta cike da jin ddin ganinta, Maryam tace "kai Afeefah Ca nake xan xo in ga baki da lfya ssae" Afeefah ta bata fuska ta taba wuyarta tace "taba wuya na ki ji toh" dariya kawae Maryam ke yi tana kallonta, duk wnn abinda suke Dr Aliyu Sharif na kallonsu, Maryam tace "xo ku gaisa da Wanda ya kawo ni" Afeefah tace "yayanki ne? Nima yayanmu jiya ya dawo" motar Afeefah ta nufa ganinsa a bude ta isa maxaunin Driver tace "ina yini ya....." Makalewa sauran gaisuwar suka yi a throat dinta, Maryam ta kauda kai tana yar dariya, kallonta kawae yake daga sama xuwa kasa barin foots dinta da ba takalmi, ta sunkuyar da kai kmr munafuka tana wasa da hijab.

Eeshatullah Goni😘😘
[5/22, 07:56] Umar Dalha: πŸŒΈπŸ‘©πŸ»'Ya Mace Kyautar Allah πŸ‘©πŸ»πŸŒΈ

A true life love story

By *Ashmaad*

17....

Dauke kai daga kallonta yyi yace "Allah ya sauwake Miss Zainab" ta sunkuyar da kai murya can ciki tace "Ameen ngd" tada motarsa yyi yana kallon Maryam yace "I will b on my way" Maryam tace "OK am grateful Sir, Allah kiyaye hanya" yace "Ameen" snn yyi reverse ya bar anguwar, sae a snn Afeefah ta galla ma Maryam harara tace "Wa yace ki xo da wnn mutumin Maryam" Maryam tayi dariya ssae tace "Ke rage min hanya yyi ba cewa nayi ya xo ba" Afeefah ta tabe baki don bata ma son tuna abinda ya faru ranan, ta kama hannun kawartata suka nufi cikin gida, Har kasa Maryam ta duka ta gaida mami da fitowarta daga kitchen knn, Mami ta amsa da fara'arta tana mata sannu da xuwa, Afeefah ta kuma janta suka nufi sama ta kai ta bedroom dinsu, dakin ya Aliyu ta koma da sauri baki har kunne tace "Yayanmu xo ka ga kawar tawa Maryam, tana dakinmu xo ka ganta" Aliyu da hnklinsa na kan laptop yace "kai Haba har kawar ta mu ta iso, to sannun ta da xuwa, maxa je ki gani nn xuwa" ta bata rae sanin idan ta tafi ba fitowa xae yi ba tace "ni yayanmu ka taso mu je mana" mikewa yyi sanin idan yana son kwanciyar hnkli to ya bi ta kawae, da fara'a ya gaisa da Maryam yana tambayarta ya

Please Login or Register in order to submit comment