Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kalle ka ba wllh" a dan tsawace yace "C'mom take this" har wani rawa hannunta yake ta karbi cake din da yake mika mata, yace "Eat" tace "Sir...." Kallon da ta ga yana mata yasa ta kai cake din bakin ta shiga ci a hnkli yana kallonta, rabi ta ci tace "Sir na koshi wllh" ba tare da ya kalleta ba yace "In xubar kike nufi, yhu had beta finish it right away," kmr xata yi kuka ta karasa cin cake din ya mika mata table watern da ya fara sha, ta karba a hnkli ta bude ta sha snn ta ajiye sauran, wayar ta dake jaka ne ya soma vibrate ta bude jakar yana kallonta ta fiddo wayar, xaro ido tayi sae kuma ta mayar da wayar da sauri yace "feel free, pick yhur cal" girgixa masa kai tayi da ganinta kasa a tsorace take, a nutse yace "wa ke kira?" Da kyar ta iya cewa "Yayanmu" yace "To dauka mana" bude jakar ta ta dauko wayar da ya katse a lkcn, kuma kira aka yi, ta daga kai tana kallon Dr Aliyu kmr xata yi kuka, yyi murmushi yace "pick" daga kiran tayi ta kara a kunne tayi shiru, ya Aliyu yace "Baki gama fushin ba Afeefah" turo baki tayi tace "Eh" yar dariya yyi yace "Srry Angel, nayi laifi baxan sake ba...." Make kafada tayi ta fashe da kukan karya tace "bana so, kuma ni bbu ruwana da kai kar ka sake min magana bbu ruwana da kai" Kallonta kawae Dr Shariff yake, ya Aliyu yace "ohh Haba yar Kanwata, I said am srry, yhu caused everything" ta kuma saka kukan karya tace "ni ka kyaleni joor" lallashinta kawae ya Aliyu ke yi yana mata promises kala kala, lkci daya ta fashe da dariya tace "yhu Promised fa yayanmu" yace "Allah Kanwata I mean it" dariya take sosae tace "ohk byee na hkura" katse wayar tayi ta mayar cikin jakarta ta dago kai tana kallon Dr Aliyu da ya kafa mata ido, wani kunya ya rufeta ta rufe fuskarta da tafin hannunta da sauri tana yar dariya tace "Sirrr" murmushi yyi yana kallonta har lkcn, hkn yasa ta cusa kanta cikin Hijab dinta tana dariyar jin kunya.

Eeshatullah Goni😘😘
πŸŒΈπŸ‘©πŸ»'Ya Mace Kyautar Allah πŸ‘©πŸ»πŸŒΈ

A true life love story

By Ashmaad

Dedicated to all my fans.... Luv u all❀❀


22......

Gajiya tayi da boye fuskarta ganin bae ce mata komae ba ta bude fuskar a hnkli ta mike ba tare da ta kallesa ba tace "Sir am goin home" Yace "ashe bayan kuka ma har da dariya kika iya hka?" Boye fuskarta ta kuma yi da sauri ta fara wani sabon dariyar kmr an aikota, murmushi yyi yana kallonta, can ya mike ya dauki makullansa ya fice daga office din ta bi bayansa. Ba tare da ta kallesa ba yana kulle office dinsa tace "Sae gobe sir" yace "OK Allah ya kai mu" Main gate ta nufa ta samu adai daita da xae kai ta har gida. A falo ta samu ya Aliyu da Mami ta gaida Mami shi kuma ta 6alla masa harara xata haura sama Mami tace "ina su Jiddah" Tace "Mami sae shidda fa xa su gama lecture ni kuma tun uku na gama" Mami bata ce komae ba Afeefah ta haura sama, Aliyu ya dan saci kallon Mami snn ya Mike ya bi ta. Bedroom dinsu ya sameta ta bata fuska tace "ni ka tafi" Dariya yyi yace "ba kin ce kin hkura ba Kanwata" juya masa baya tayi yace "To ki shiriya mu fita yawo da daddare," tsalle ta doka ta rungumesa tace "Yeehhh thanks yayanmu, wllh na hkura" dariya yyi yace "toh ina jiran ki downstairs ki xo mu yi kallo," juyawa yyi ya fice daga dakin, ta shiga cire kayan jikinta snn ta fada bathroom don yin wanka. Da daddare Ya Aliyu ya fita da ita kmr ynda yyi mata alkawari, yawo suka yi ssae snn ya biya da ita shoprite don siya mata ice-cream da kuma shopping da ta ce xata yi, Shopping ta fara yi duk abinda tasan tana bukata ta dinga diba yana tura mata trolleyn, bangaren Ice-cream suka nufa daga karshe bayan ta gama siyayyanta tace "yayanmu mu dan siya ma su Anty Jiddah da Sumayya kar su ji haushi na koh? Ka ga suna ta fushi da xa mu fita" Yace "to xa mu siya masu" ice-cream robobi Shiddah suka siya snn ta kuma sa shi ya siya mata Wanda xata sha a hanya aka sa mata scoop biyu na vanilla da chocolate, juyawa tayi da sauri ba tare da thinking twice ko akwae mutum a bayanta ba taji ta fada jikin mutum kusan rabin ice-cream din hannunta ya xube jikinsa, da sauri ta koma baya, ta xaro ido ganin duk ta juye masa ice-cream din ta daga kai tana kallonsa feelin guilty, sae kuma hkurin da take shirin fara basa ya makale ta kafa masa ido, murya can kasa tace "Sir!" Kallonta shi ma yake, ta cire dankwalin kanta da sauri ta shiga goge masa ice-cream din chest dinsa bayan ta dafa shoulder dinsa duk da ynda ya fi ta tsayi tana cewa "Am srry sir bn san.... Kayi hkuri plss sir" kallonta kawae Dr Shariff yake, kanwarsa ce ta bullo da trolley tana ganin abinda ke faruwa ta karaso da sauri tace "ya aka yi yaya, bata gani ne," Afeefah dake goge masa jikinsa har lkcn da dankwalinta tace "Mistake ne bn sani ba" kmr xata yi kuka ta kare maganar tana kallon yarinyar, Dai dai nn ya Aliyu ya karaso gun da trolley ya tsaya kallon Afeefah da mamaki yace "meye hka wat happened?" Kmr xata yi kuka tace "ban sani ba na buge sa yayanmu shine sae ice-cream ya xube jikinsa" Karasowa Aliyu yyi ya fixge dankwalin hannunta yana mata mugun kallo, snn ya karasa goge ma Dr Sharif jikinsa ya danka masa dankwalin ba tare da ya lura da na Afeefah bne fuskarsa a daure yace "srry" snn ya ja ta suka bar wajen, waigawa take tayi tana kallon Dr Sharif da ya bi su da kallo kafin su sha kwana ta daga masa hannu alamar _bye bye_ tare da yi masa murmushi, shi ma ya mayar mata, biyan kudin kayansu yyi yana janta har lkcn fuskarsa a daure suka fita ya tura ta cikin mota cikin tsawa yace "don kin xuba masa ice-cream shine xa ki kama gardi kina goge masa jiki? Kina da hnkli kuwa?" Girgixa masa kai kawae tayi, yyi tsaki ya xaga driver seat ya ja motar a fusace ya bar wajen. Sae da suka isa gida yyi parkin snn ya kamo hannunta a hnkli yace "am srry sweet sis, me yasa kike taba namiji" sunkuyar da kanta tayi bata ce komae ba, hkuri ya shiga bata don yyi mamakin rashin kukan da bata yi ba, daga karshe ta dan yi murmushi alamar ta hkura, shima murmushin ya sakar mata ya ja kumatunta yace "ko kefa yar Kanwata," a hnkli tace "dankwali na yayanmu" yace "yana ina?" Ta dan yi shiru snn tace "ka bar masa" wara manyan idonsa yyi yace "meyasa baki ce min naki bane? Ohh yi hkuri xan siya maki wani atamfar me kyau kin ji" murmushi tayi da ya bayyana beauty point dinta da ke gefen kumatunta na dama tace "thnk yayanmu" ya bude motar ya fita ya fiffito mata da kayanta ya kira su Jiddah su xo su kwashe.

Eeshatullah GoniπŸ˜˜πŸ˜˜πŸŒΈπŸ‘©πŸ» 'Ya mace Kyautar Allah πŸ‘©πŸ»πŸŒΈ

A true life love story

By Ashmaad

23/24....
Da sallama Afeefah ta shigo office din ita kadae rike da coke din da straw ta karasa table dinsa ta ajiye tace "Sir ga shi" ba tare da ya kalleta ba yana ci gaba da danna wayarsa yace "Thnk yhu" ajiye masa change dinsa tayi ta nufi jakarta ta dauka xata fita ya dago da sauri yace "Ina maryam din?" Juyawa tayi tana kallonsa tace "tana waje tana jira na" yace "OK, ku baxa ku sha coke din ba" ta girgixa masa kai tace "Aa mun sha daxu" yace "OK" har ta isa kofa yace "Zainab!" Juyawa tayi tana kallonsa yace "Waye ku ka je shop rite da shi jiya?" Ta wara ido tace "Shine yayanmu ae" gyada mata kai yyi yana kallonta yace "Cousin brother koh" ta girgixa kai da sauri tana dariya tace "lah Abbanmu daya wllh fa Sir" shiru yyi yana kallonta snn ya gyada mata kai, ta juya ta fice daga office din.

Ana gobe xa su tafi mid semester break Afeefah ce xaune da su Maryam da Rukayya inda suka saba xama bayan sun fito daga lecture tana masu explaining wani topic a course dinsu BiOC 312 da suka ce ba su gane ba, Maryam sae kallonta take don bata taba tunanin Afeefah na da maida hnkli hka ba ka rantse kace lecturer ce ynda ta xage take fahimtar da su da turanci, duk ajin anyi xaton kuka ne kadae abinda ta fi iyawa, Muryar lecturen Course din suka ji a bayansu da alamar ya gama lecture da yan 200lvl yace "Ashe bayan kuka ma kina da kkri wajen karatu Zainabu" Afeefah ta rufe fuskarta da sauri da littafin hannunta tana dariya da yake sun dan saba da lecturan tana yawan ganinsa office din Dr Sharif ko a department wani lkcn, su Maryam suka fara dariya suna kallonta, shima yyi dariyan ya wuce. Da yamma suna dawowa daga mosque Afeefah ta nufi cafeteria da Maryam suna tafe suna hira Maryam tace "kin ga yan matan nn basu sake xuwa gun mu ba" Afeefah tace "Allah ya taimake mu don ni tsoronsu ma nake, kila sun...." Maryam ta xabga mata harara tace "Da'alla, matsoraciya kawae to me suka isa su mana, ae Dr Sharif ya kirani a ranan ban san wnda ya gaya masa ba, muka je har department dinsu da shi na nuna su" Afeefah ta xaro ido tace "ba ki ji tsoro ba Maryam? To me ya ce masu" Maryam ta tabe baki tace "oho, kawae yace in tafi, nayi wucewa ta" drinks Maryam tayi masu orderin bayan sun xauna. Biyar saura suka fito daga cafeterian Afeefah tace "ni gida xan tafi Maryam, sae mun hadu next wkk, xan sha bacci wnn break din da muka samu" Maryam tace "wae meyasa kika daina jiransu Anty jidda, kuma fa Abdul na tutorial a class tun daxu kuma course din Dr sharif" Afeefah tace "sbda wani lkcin ina riga su gama lecture sae in ta jiransu har in gaji" Maryam tace "to mu shiga tutorial din" Afeefah tace "A'a ni baxan shiga ba xan yi karatuna a gida, byee" tana kai wa nn bata jira cewar Maryam ba ta kama hanyar main gate, Maryam ta tabe baki ta nufi Department don shiga tutorial, tafiya kawae Afeefah take ko rabin main gate din bata yi ba ta hango yan matan da suka samesu da Maryam a cafeteria ranan da kawayensu su kusan uku suna tafe suna hira da shewa. ta xaro ido a tsorace ganin tahowa suke ta inda take tafiya, rawa jikinta ya dau yi ta fara kalle kallen inda xata buya kan su iso inda take, wani cafe dake wajajen ta shige da gudu ta labe kmr munafuka xuciyarta na bugawa, bayan kusan minti Uku taji muryar matan a cafe din sun shigo da alamar xa suyi photocopy, saura kiris ta fashe da kukan tsoro ganin basu lura da ita ba yasa ta fice da gudu ta kama hanyar gate, mota taga ya ja burki gefenta, har xata falla a guje ta ga Dr Sharif ne, tsayawa tayi tana share hawayen fuskarta da sauri tana kalle kalle kmr munafuka don bata yi wani nisa da cafen ba, yana fitowa daga motar ya hade rae yana kallonta yace "Meyasa baki shiga tutorial ba?" Girgixa masa kai tayi muryarta na rawa tace "gida xan tafi" ya galla mata harara yace "kukan me kike?" Ganin xata fashe masa da kuka yasa ya daka mata tsawa ba shiri ta hadiye kukan har lkcn bata bar waige waigen da take ba ta ga ko yan matan sun fito, ya juya yana kallon inda take kallo, dae dae lkcn da yan matan suka fito daga cafen, bayansa ta nufa da sauri muryarta na rawa tace "Sirrr," kallon yan matan kawae yake su ma kallonsa suke lkci daya kuma duk suka dauke kai suka fara tafiya suna isa dai dai inda yake tsaye Afeefah na bayansa kmr munafuka suka gaishesa, bbu yabo bbu fallasa ya amsa suka ci gaba da tafiyarsu kmr sun hada baki suka juyo gaba daya suna kallon Afeefah sae kuma suka kwashe da dariya suka yi gaba da sauri, Afeefah ta fito daga bayansa tana share hawaye ya daka mata wani mugun tsawar da ya raxanata yace "kuka kike min?" ba shiri ta hadiye kukan tana girgixa masa Kai, ya bude mata front seat bata jira yace ta shiga ba ta shige da sauri, ya rufe motar ya xaga ya shiga maxaunin driver snn ya tada motar ya nufi main gate, hanyar jan bulo taga ya nufa da ita, ita dae sae wasa da fingers dinta take, "kina jina?" Dago kai tayi tana kallonsa ta mayar da kanta kasa da sauri ganin ynda ya hade rae, "Seriously daga yau, i mean daga yau na kuma ganin kina kuka a sch xaki sha mamaki na, yhu re not a kid I c no reason xa ki dinga yi ma mutane kuka unnecessarily, kar in kuma ganin hawayen ki a sch" a dan tsawace ya kare maganan, ta gyada masa kai a hnkli, yace "kin ji ni da kyau kuwa?" Kai ta gyada masa nn ma, yace "to me nace?" a hnkli tace "kace kar in kuma kuka a sch" yace "good! Repeat after me" dago kai tayi tana kallonsa yace "ki ce, ke Zainab," murya can kasa tace "Ni Zainab," yace "kinyi alkawarin" nn ma a hnkli tace "nayi alkawarin," yace "baxa ki sake kuka a sch ba da ma ko ina!" Sunkuyar da kanta tayi ta maimaita abinda yace a hnkli, yace "yhu promised fa kika ce?" Kai ta gyada masa tace "yes sir" ya galla mata harara yace "da wani katon idonta a gurin" boye fuskarta tayi da tafin hannunta ta fara dariya a hnkli, dan murmushi yyi ya mayar da hnklinsa gaba daya kan tukin da yake, a hnkli dan kanta ta xame hannunta daga fuskarta. Nesa da gidansu ssae yyi parkin ya juya yana kallonta, ta dan wara ido tace "Sir dama kasan gidanmu?" Da sauri ta ba kanta answer tace "ohh Maryam ta taba xuwa da kai na manta" murmushi kawae yyi, tace "na gode sir" snn ta bude motar ta fice, "Zainab!" Taji ya kirata a nutse, ta juya da sauri tana kallonsa, a hnkli yace "Read ur books, dnt sleep too much during d break, ur exam is around the corner, nd I will b conducting my last test on Tuesday" Kai ta gyada masa tace "OK sir xan yi karatu," kai ya gyada mata ta kulle masa motarsa ta nufi gate dinsu shi kuma yyi reverse ya bar anguwar, tsaye ta ga Ya Aliyu a gate da alamar shigowarta yake jira, xuciyarta ya kusa shigewa cikinta, cikin rawar Murya tace "yayanmu"

Eeshatullah GoniπŸ˜˜πŸ˜˜πŸŒΈπŸ‘©πŸ» 'Ya mace Kyautar AllahπŸ‘©πŸ»πŸŒΈ

A true life love story

By Ashmaad

26.....
"Zainab wa ya ajiye ki a mota?" Afeefah da jikinta ke bari ganin yanayin yayan nata, cikin rawan murya tace "Wayyo yayanmu ni ban shiga mota....." Mari ya kai mata yana huci yace "Ni xa ki ma karya? I will so beat the hell out of yhu ynxun nn idan baki gaya min gskya ba, wa ya ajiye ki a mota nace?" A tsawace ya kare mgnr, Afeefah da har hawaye ya soma taruwa idonta ta tuno promise din da tayi ma Dr Sharif da sauri ta hadiye kukan, tana girgixa masa kai a hnkli tace "yayan Maryam ne ya xo daukar ta shine suka rage min hanya" bata san lkcn da karyar nn yyi formulatin kansa a bakinta ba, Aliyu da idonsa suka sauya launi ya fixgo hannunta ya nufi cikin gida da ita yana huci, dakin Mami ya nufa da ita, lkci daya duk ya xayyane ma Mami abinda ya gani da kuma abinda ta ce masa, Mami ta saki baki tana kallonta tace "wato ke kin xama me kunnan Kashi ko Zainab, bbu Wanda ya isa da ke knn a gidan nn, to wae ni hka kika ga yayyin ki na yi ne, wllh ka tafi da ita ka xaneta Aliyu, gobe idan ance ta shiga motar mutane gudu xata yi ta bar wajen" Afeefah dae kanta na kasa, Mami tayi mmki wae yau Afeefah aka sa gaba ana yi ma fada bbu ko digon hawaye abinda bata taba gani ba tunda ta haifeta, shi kansa Ya Aliyu ba karamin mmki yyi ba har ya mareta bata yi kuka ba, kofa ya nuna mata alamar ta fita, ta nufi kofan a sanyaye ta fita ta jira sa a corridor, dakinsa ya nufa da ita ya xaunar da ita gefen gadon yana kallonta fuskarsa a daure yace "me yasa baki jin magana Afeefah, baki da kudin mota ne xa ki shiga motar mutane?" Girgixa masa kai kawae tayi, ya ji tausayin ta ya dawo gefenta ya xauna yace "Haba yar Kanwata, ynxu kin daina jin maganata ko?" A hnkli tace "ina ji yayanmu" yace "to meyasa kike disobeying dina idan na hanaki abu" kanta a kasa tace "na daina" ya dan yi murmushinsa me kyau ya dago kanta yana kallon cikin idonta yace "yauwa princess dina" dan murmushi ita ma tayi tana kallonsa, ssae ya Aliyu yyi mmkin kukan da Afeefah bata yi ba yana mata fada, ya mike yace "go nd bath ki sauko ki ci abinci kinji" mikewa tayi ta gyada masa kai ta fita daga dakin ta tafi nasu. Da misalin karfe goma na dare Afeefah ta fito daga wanka knn tana shirin kwanciya, su Jiddah gaba daya suna falo suna kallo, wayarta dake ajiye gefen gado yyi haske alamar ana kiranta don alwayz a cylnt wayar yake, karasawa tayi ta dauki wayar ta kafa ma new numbern dake kira ido tana tunanin waye, har sae da ya kusa katsewa snn ta daga a hnkli ta kara kunnenta, shiru taji na kusan second sha biyar har tana shirin katsewa taji anyi sallama, mamaki ne dauke fuskarta jin muryar namiji, da kyar ta iya gather din courage tace "Waye?" Yace "Baki amsa sallama ne?" Ta dan yi jim snn tayi saurin cewa "Srry, wrong number malam" tana kai wa nn ta fara kkrin katse wayar, "Wait Zainab!" still tayi jin ya kira sunanta, da kyar ta ce "A ina kasan ni?" A hnkli taji yace "Allah ne ya hada ni da ke" kuma kallon nmbr tayi da sauri snn ta mayar kunnenta tace "don Allah kayi hkuri wrong number ne ka kira" murmushi taji yyi yace "Wrong number kuma? Ba da Zainab Mahmoud Umar nake magana ba?" Xaro ido tayi jin ya kira full name dinta tace "Dan Allah ka rufa min asiri a ina ka samu nmbr na?" Yace "Allah ne ya bani" a tsorace tace "toh ni ba ni bace" bata jira cewarsa ba ta katse wayar snn ta kashe wayar gaba daya, jikinta na rawa ta kwanta ta shige bargo don ita dae tasan bata taba ba namiji lambarta. Da Asuba ringing din wayarta ne ya tasheta daga bacci ta mike a firgice tana kallon wayar, wani kara ta saki da ya farkar da su Jiddah gaba daya snn ta fice daga dakin da gudu ta afka dakin ya Aliyu tana ihun sunansa, shi ma a firgice ya farka yana kallonta yace "me ya faru?" Bayansa ta labe tana kuka tace "yayanmu na kashe wayata kafin in kwanta wani aljani ya kunna min wlh" sake baki yyi yana kallonta aka bude kofar dakin ta fasa ihu, shi kansa sae da ya ji tsoron bude kofar, Mami ce ta shigo dakin a tsorace ita ma, sae ga Adnaan ma ya shigo da sauri, su Jiddah ma a rude suka shigo dakin, duk suka tsaya kallonta, Abba dake tsaye bakin kofar duk suka ba hanya ya shigo dakin yana Kallon Afeefah da mamaki yace "me ya faru Zainab?" Kuka ta fashe da ta fito daga bayan ya Aliyu da sauri ta nufi gun Abba tace "Abba ka ga na kashe wayata jiya da daddare kafin in kwanta kawae ina jin aljani ne ya kunna min ya fara ringing ina bacci, wllh Na kashe kafin in kwanta" cikin matsanancin kuka ta kare maganan, su Jiddah suka kwashe da dariya har da kyakyatawa, Abba ya daka masu tsawa, Sadiya tace "Abba ni ce fa na kunna xanyi browsing jiya da daddare bn da data" dariya ssae su Jiddah suke suna kallon Afeefah, Ya Aliyu ya daka masu tsawa yace "don me xa ku kunna mata waya, wawayen yara kawae" juyawa Abba yyi tsaki Adnaan yyi yana hararan Afeefah ya fice daga dakin ransa a bace, Mami ta yi kwafa ita ma ranta a bace tace "nasan maganin ki, ba dae ke yarinya bace xa ki tada mutanen gida da ihu, xa ki sha mamaki na" tana kai wa nn ta juya ta fice daga dakin ita ma, su Jiddah suka kuma kwashe wa da dariya, ya Aliyu ya dauki filo ya jefa masu a fusace snn ya Mike da sauri, da gudu suka fice daga dakin, ya juya yana kallon Afeefah ya galla mata harara yace "fita ki ban waje da'alla" mikewa tayi ta fice daga dakin a sanyaye.

Ees
hatullah Goni😘😘


[5/22, 07:56] Umar Dalha: Ya mace kyautar Allah
A true life love story

By Ashmaad

27__28
Afeefah ne xaune daki ita da Sadiya, ita tana karanta handouts dinta sadiya kuma na kwance tana danna wayarta, Mami ta shigo dakin tace "wae me ku ke yi ne? Ina Jiddah? Ku fito ku daura girkin rana don bbu yar da xan ma girki yau ta ci ku fito ku shiga kitchen" tana kai wa nn ta juya ta fita daga dakin, Afeefah ta ajiye handout din hannunta da sauri ta kwanta tare da lumshe ido kmr me bacci, Sadiya tace "ehh kya ma bude idon ne yarinya, sannun ki da wayo" tana kai wa nn ta fice, Afeefah ta kuma gyara kwanciya kmr me bacci, Jiddah ce ta shigo dakin bayan kusan minti biyar tace "ke Afeefah baxa ki fito mu shiga kitchen bne" Shiru Afeefah tayi kmr me baccin gske, Jiddah ta juya ta fice, Mami ce ta shigo dakin a tsawace tace "Zainab!" Mikewa xaune tayi da sauri tana murxa ido kmr xata yi kuka tace "Mami ni bacci..." Bayi ta shige da gudu ta kulle tun kan Mami ta karaso ganin ta yo kanta, Muryar Adnaan taji a dakin alamar Mami taje ta kirasa yana cewa "baxa ki fito ba sae na bude kofar nn, wa kika ajiye xae maki girki a gidan nn, ke baki da aiki sae dae a baki ki ci ki addabi mutane da kukan bnxa koh" murguda baki tayi kmr yana ganinta taki bude kofar, gate taji an bude downstairs ta washe hakora sanin ya Aliyu ne ya shigo, lkci daya ta saki kukan karya, Adnaan ya bude baki yana kallon kofar hka ma su Jiddah dake bakin kofar dakin a tsaye suna jiran fitowarta, muryar Aliyu su ka ji a corridor din rooms din yace "me ya faru?" Jiddah ta tabe baki tace "kaga yayanmu Mami ce fa tace mu je muyi girki shine ta shige bayi ta kulle" daga cikin bayin Afeefah tace "yayanmu ka ga fa karatu nake xa muyi test Monday" kmr xata yi kuka ta kare maganar, Aliyu ya watsa masu harara yace "mutane nawa xa suyi girkin? Ina su Sumayya?" Sadiya ta bata fuska tace "ba suna sch ba su" ya kuma watsa masu harara yace "ku biyu baxa ku iya girkin ba sae kace masu girkin gidan bikin, common get lost my frnd" Muryar Mami suka ji tana cewa

Please Login or Register in order to submit comment