Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

karatu ya dan yi minti biyar a dakin snn ya koma dakinsa. Mami da kanta ta kawo wa Maryam drinks da snack ganin Afeefah bata da niyar kai mata, Maryam tayi mata godiya snn ta fita, hira ssae suka yi daga bisanni Maryam tace xata wuce ganin har biyar ya gota, Afeefah ta hade rae tace "to yaushe kika xo" dariya Maryam tayi tace "kar ki damu next tym xan kuma xuwa in dade amma sae kin xo namu gidan ke ma" Afeefah tayi murmushi tace "to ina nn xuwa idan Allah ya yarda" Dubu biyu Aliyu ya bata kudin mota, Mami kuma ta bata turare tayi masu gdya ssae snn Afeefah ta rakata har inda xata shiga mota, Maryam tace "amma de xa ki xo sch gobe ko Afeefah" Afeefah ta marairaice tace "Ehh kila in xo"

Washegari da safe ya Aliyu ya sa Afeefah gaba ta fara shirin sch, ko damuwa da kumbure kumburen da take bae yi ba, Karfe bakwae da rabi driver ya tafi da su da ita da su Jiddah, kmr munafuka ta nufi faculty dinsu ta samu karkashin wata bishiya ta xauna, takwas da minti sha biyar ta mike sanin suna da lecture Karfe takwas ta nufi lecture hall dinsu, gabanta yyi mugun ganin shima ga nufo hall din tasan lecture dinsa garesu ranan, har ya wuce ta bata ce komae ba tana shiga hall din ta nufi can back seat ta xauna, duk student suka soma nutsuwa ganinsa, sae da class rep ya mika masa marker snn ya daga kai yana kallon Afeefah yace "leave dat seat" kallonta duk yan aji suka fara yi ta ji kmr ta nutse kanta a kasa ta Mike tsaye, seat din dake gabansa ya nuna mata, a dan tsawace yace "come bck here" seat din ta nufa hawaye cike idonta ta xauna kmr munafuka gefen matan dake xaune gun tana goge hawayen da hijab dinta, bae damu da hka ba ya soma lecturing dinsa, kwata kwata hnklinta bae kan abinda yake koyarwa duk ta kagu ya gama ya tafi don duk a takure take, ita dae tasan ya fi awa daya yana lecturing ta ji yana buga desk da marker da sauri ta dawo daga duniyar da ta tafi ta ga kallonta yake "can yhu explain it to us plss" kwalalo ido tayi tace "explain wat?" Dariya duka class din suka kwashe da ta juya da sauri tana kallon kowa, sae hawaye, yarinyar gefenta ne tace "ga question din a board," Afeefah ta kalli board din da sauri, rungume hannayensa yyi yana kallonta, ta soma share hawayen da ya ki tsaya mata tace "Sir I didn't understand!" Wani kallo ya watsa mata yace "keep quiet nd stop lying, yhu weren't listen, leave my class!" Dago kai tayi tana kallonsa tana hawaye yace "i said leave my class" mikewa tayi ta fice daga class din da sauri tana kuka," karkashin bishiya ta samu ta dinga rusa kuka uwa an aikota, ta kusa minti sha biyar xaune gun taji an kirata, ta daga kai da sauri ta gansa tsaye bayanta, yace "am waitin for yhu at my office" bae jira cewarta ba ya bar wajen. Mikewa tayi bayan minti kusan biyar ta bi bayansa kmr munafuka, xaune ta samesa yana danna waya, ta sunkuyar da kanta a hnkli tace "am here sir" dago idanuwansa yyi yana kallonta ya nuna mata kujera yace "sit" ba musu ta xauna, ya ajiye wayar hannunsa yace "y were yhu absentminded in class today?" Sunkuyar da kanta tayi bata ce komae bae, kwankwasa kofa aka yi lkci daya aka bude aka shigo, ya daga kai yana kallon kofar, "ba ki iya sallama bne" tambayar da taji yyi ma wnda ya shigo knn, yarinyar ta karaso tace "srry nayi a xuciyata amma" kallonta kawae yake har yarinyar ta iso kusa da shi ta ajiye basket din hannunta da leda tace "yaya, Ummi tace kadda ka manta ka taho mata da drugs dinta later fah" yace "OK," yarinyar ta dafa goshinsa tace "kan ya daina maka ciwo yaya" yace "ya daina," tace "to ga abinci ka ci, ur favourite Ummi tayi maka," "ohh naji Teema, ba driver na jiran ki ba ne wae" ta juya da sauri tace "Bye yaya, sae ka dawo" tana kai wa nn ta fice daga office din. "Am tokin Zainab" Afeefah ta dago da sauri a hnkli tace "sbda bni da lfya" dan murmushi kawae yyi ya bude kulan abincin gabansa, shinkafa ce da lafiyayyen stew da nama, ya rufe ya dauki flask ya xuba ruwan xafi a mug snn ya shiga hada coffee, wani mug din ya kuma dauka ya xuba ruwan xafi snn ya hada wani coffeen ya xuba madara da sugar ya mika mata, dago kai Afeefah tayi tana kallonsa, yace "take" girgixa masa kai tayi da sauri tace "No thnk yhu" wani kallo ya watsa mata yace "ki karba my frnd" ba karamin tsoro ta ji ba ta karba hannunta na rawa yace "ke kar fa ki xubar min coffee kan table" sunkuyar da Kai tayi tana kallon coffeen hannunta gabanta na faduwa, ya dauki nasa ya soma sha.

Eeshatullah Goni 😘😘09077036932
[5/22, 07:56] Umar Dalha: πŸŒΈπŸ‘©πŸ»'Ya Mace Kyautar Allah πŸ‘©πŸ»πŸŒΈ


A true life love

By *Ashmaad*

18.....

A hnkli Afeefah ta dago kai tana kallonsa ta ga black coffee dinsa kawae yake sha, ta kuma sunkuyar da kai, bayan kusan minti uku ta kai mug din baki a hnkli ta kurbi coffee din ta ji yyi mata ddi ssae, hada ido suka yi tayi saurin ajiye cup din murya can tace "na koshi" wani kallo yyi mata yace "In xubar knn kike nufi?" Bata ce komae ba ta kuma daukar mug din, fiddo wani foil paper dake cikin basket din gabansa yyi ya bude ya ga cake ne ciki ya ajiye gefe snn ya dauki wani textbuk ya shiga dubawa, rabin mug Afeefah ta sha coffee din snn ta ajiye tace "thanks sir na koshi" ya kalli mug din yace "Its beta ki shanye don baxan xubar ba" kmr xata yi kuka tace "Sir ya isheni" kallon da yyi mata ya sa ta dauki mug din ta kuma kai wa bakinta bata kuma ajiyewa ba sae da ta shanye ta ajiye a kunyace tana goge bakinta, bayan kusan minti biyar ta Mike tsaye ganin hnklinsa na kan textbuk din gabansa murya can kasa tace "ngd sir" sae a snn ya dago Kai yana kallonta yace "Welcm" sunkuyar da kai tayi tace "can I go" yace "yes but dnt ever come to my class absentminded again" a hnkli tace "OK sir" snn ta juya xata fita yace "gashi ki tafi da wnn," juyawa tayi ta ga yana mika mata cake din dake cikin foil paper, xata yi magana ya daure fuska yace "take dis!" karasowa tayi ta dan risina ta karba tayi masa gdya snn ta nufi kofa ta fita daga office din. A bakin lecture hall dinsu ta hadu da Maryam da wasu yan matan class dinsu, Maryam tace "ina kika je ina ta nemanki Afeefah" Afeefah tace "Dr Sharif ne ya kira ni" Kallon juna duka yan matan suka yi amma bbu Wanda yace komae, Maryam tace "wae to tunanin me kike a class ana lecture" Afeefah tace "ni ba tunani nake ba" tana Kai wa nn ta shiga class abunta. Daga masallaci Maryam da Afeefah suka nufi cafeteria, xaunawa suka yi inda suka saba xama Maryam ta gaida matan da taga sun kafa masu ido da alama yan 300lvl ne, bbu yabo bbu fallasa suka amsa ta, Afeefah kam xama tayi abunta Maryam ma ta xauna tace "Me xa a kawo maki?" Girgixa mata kai Afeefah tayi tace "ni a koshe nake" Maryam tace "me kika ci?" Afeefah tace "Dr Sharif ya bani coffee a office dinsa, kuma kin ga cake din nn ma shi ya ban, kawae ki siya drink sae ki sha da cake din." Maryam ta saki baki tana kallon Afeefah tace "da gske?" Afeefah xa tayi magana ta ga yan matan da suka samu a cafeteria tsaye kansu, daya daga cikinsu tace "dama mun xo maku kashedi ne a kan ku fita hanyar Dr Aliyu Sharif, idan kuma ba hka ba duk me ya sameku ku kuka siyan ma kan ku wllh wllh" daga Afeefah har Maryam sake baki suka yi suna kallonsu, Maryam tace "ikon Allah, to a kan wani hujja ko dalilin xa mu fita harkansa yana lecturer dinmu ku ma hka" Daya daga cikin yan matan tace "to idan ku kun cika yan halak ku ci gaba da mu'amala da shi wllh sae kunyi da kun sanin xuwan ku makarantar nn" Maryam ta mike a fusace tace "sae de kuyi da kun sanin xuwan ku bayero ba dae mu ba, har mu ance maku muna da lkcn gantalallu irin ku, mu ba abinda ya kawo mu ba knn, kila ma wnda kuke dan shi bae san Allah yyi ruwan ku a bayero ba yan wahala" da mamaki suka ce "mu kike gaya ma hka?" Maryam tace "yes!" mikewa Afeefah tayi har hawaye ya cika idonta tana kallon yan matan tace "don Allah don Annabi kuyi hkuri...." Turata Maryam tayi tace "kada Allah yasa su yi din mana" xage xage suka soma yi har ana neman dambe, Afeefah tuni ta fashe da kuka tana rokon Maryam su wuce, Xuwa ynxu duk an taru ana kallonsu, masu cafeterian ne suka ce duk su fita su je waje suyi kadda su korar masu customer, Afeefah ta ja Maryam da kyar suka fita da cafeterian suka nufi faculty dinsu Maryam na huci tace "ke daga yau Afeefah ki daina sa baki idan ina abu bbu ruwan ki, idan kuma kina jin kuka to ki dinga fita ko kuma ki matsa daga inda nake ki je kiyi kukan ki," Afeefah dae bata ce komae ba sae share hawayenta take. Karfe uku saura ta ce ma Maryam da ta wani share ta a class tun bayan abinda ya faru a cafeteria xata wuce gida, Maryam ta ajiye littafin hannunta tace "baxa kiyi tutorial din bne?" Afeefah tace "um gida xan wuce" Maryam tace "ba tare ku ke tafiya da su Anty Jidda ba" Afeefah tace "na daina jiran su ynxu" Maryam tace "to shknn Allah kai mu gobe" Afeefah ta Mike ta dauki jakarta snn ta fita daga class din, a hanya ta hadu da Dr Sharif da alamar shi ma gidan xae wuce, ta kasa wuce sa bata gaishesa ba kmr munafuka kanta a kasa tace "ina yini" kallonta ya tsaya yi ta dago jin bae amsa ba kuma bae wuce ba, ya sauke idonsa kasa daga kallonta yace "y are yhu crying?" Wasu sabbin hawayen ne suka xubo mata lkci daya ta fashe da kuka, a dan tsawace yace "ba kya ji na ne?" Ganin student sun fara kallonsu yasa yace "follow me," snn ya bar wajen da sauri, ta shiga binsa tana hawaye har lkcn, motarsa ta ga ya nufa ya jingina jikin motar yana kallonta yace "answer my question" a hnkli tana wasa da fingers dinta muryarta na rawa tace "dama ni da Maryam ne mun je cafeteria sae wasu mata suka xo suka same mu wae daga yau kar mu sake kula ka, idan ba hka ba ni bn san me xa su mana ba, shine sae Maryam ta kula su suka fara fada shine..." Kasa karasawa tayi ta shiga rusa masa kuka kmr an aikota har da shessheka, kallonta kawae ya tsaya yi ta daga kai ita ma tana kallonsa tana ci gaba da kukanta, can ya dauke kai yace "kin san matan?" Girgixa masa kai tayi tana share hawayenta.

Eeshatullah Goni 😘😘
[5/22, 07:56] Umar Dalha: πŸŒΈπŸ‘©πŸ»'Ya Mace Kyautar Allah πŸ‘©πŸ»πŸŒΈ

A true life love story

By *Ashmaad*

19.....

Shiru Dr Sharif ya dan yi kmr me naxari snn daga kai yana kallonta yace "ina xa ki ynxu" A hnkli tace "gida" ya ce "yayyinki fa?" ta make kafada tace "ni baxan jira su ba" yace "OK cry no more, I will fish out those galz, su nawa ne?" Tana kallonsa tace "su biyu ne" yace "gud!" Yana kai wa nn ya xaga ya shiga motarsa ita kuma ta nufi main gate. Da daddare Afeefah na xaune falo da yayyinta da su Sumayya suna kallo Abba ya shigo Aliyu na biye da shi a baya, duk suka yi masa sannu da xuwa ya nufi sama, Aliyu ya dawo kusa da Afeefah bayan ya amsa gaisuwar kannin nasa yana kallon idonta yace "Me aka maki" bata fuska tayi tace "a sch ne mana" yace "hado min coffee ki kawo min" yana kai wa nn ya nufi stairs, ta Mike ta je tayi abinda ya sa ta snn ta haura sama don kai masa coffee din, yana xaune yana waya ta karaso ta ajiye masa ta xauna tana kallonsa, yana gamawa ya ajiye wayar yace "Mami ce ko" girgixa masa kai tayi tace "a sch ne mana, wasu mata...." Shiru tayi da sauri ya daga kai yana kallonta yace "wasu Mata me?" Kmr xata yi kuka tace "su ke son min dariya a sch" harara ya watsa mata yace "shine kike masu kuka wawiya kawae, ke baki da bakin masu dariyar ne" hawaye cike idonta tace "ina masu ni ma ae" tsaki yyi ya dauki coffee dinsa ya soma sha, ta wara manyan idonta da ke kyalli da hawayen ciki tace "yayanmu ashe dama coffee na da ddi?" Ba tare da ya kalleta ba yace "da baki sani ba" tace "wllh ban sani ba sae da na 'dan dana daxu kuma har da madara ya sa min, yyi ddi ssae" cire cup din yyi daga bakinsa lkci daya yana kallonta yace "wa ya bakii?" Xaro ido tayi kmr warce ta tuna abu tana kallonsa a dan tsorace ta fara inda inda, ya ajiye cup din hannunsa ya murtuke fuskarsa yace "nace wa ya baki coffee," kuka ta fara yi tace "yayanmu siya fa muka yi ni da Maryam" tsawa ya daka mata yace "yaushe kika fara karya Afeefah? OK gobe xa ki kai ni inda ku ka siya coffee din" ta xaro ido a tsorace tace "wayyo yayanmu kayi hkuri, wani lecturan mu ne ya bani..." Tsit tayi ganin irin kallon da yake mata, ya mike ya xabga mata mari mai lfya yace "ki ka ce wa ya baki" kuka ta fashe da ya daura hannu lebbansa alamar tayi shiru, lkci daya ta hadiye kukan, fuskarsa a daure yace "wani lecturer ne wnn?" Ta hadiye sauran kukanta tace "A makaranta" ya kai mata wani marin a fusace yace "fita ki ban waje, doluwa kawae, " mikewa tayi da sauri ta toshe bakinta da hannunta ta fice daga dakin da gudu ta afka dakinsu ta xube gabansu Jiddah ta dinga rusa masu kuka, harkan gabansu duk suka ci gaba da yyi bbu Wanda ya kalleta bare ya ji me ya sa ta kuka sanin irin halinta. Ta gaji da kukanta ta Mike ta nufi gado ta kwanta lkci daya bacci ya dauketa.

Washegari da safe Afeefah ta je gaida Abba bayan tayi shirin sch kmr ynda suke yi duk safiya, xaune ta tadda duk yan gidan a falon Abba bnda Mami da ya Aliyu, ta xauna gefen su bayan ta gaishesa ya amsa fuskarsa a daure, Mami ce ta shigo snn ya Aliyu, Afeefah ta ki bari su hada ido da ya Aliyu, sae wasa da fingers dinta take, sunanta taji Abba ya kira, ta dago kai da sauri yace "Wani lecturer ne a sch kike xuwa office dinsa yake baki abu ki ci?" Xaro ido tayi a tsorace tana kallonsa, Abba ya daka mata tsawa "ba magana nake maki ba kike kallona hka, meye tsakanin ku, kuma a ina kika san shi? Kin mance doka na ne" Kuka ta fashe da tana kallon Aliyu da ya wani hade rae, Abba ya mike a fusace yace "au kuka xa ki yi min don kaniyar ki don ban sa an xane min ke ba?" Sunkuyar da kai tayi ta hadiye kukan da sauri, Abba yace "today shud b d first nd last day da za ki sake kula lecturer a sch, na hane ki da sake kula ko wani namiji a makaranta, hka kika ga yayyinki suna yi, to na sake jin hka sae nayi mugun Saba maki wllh, tashi ki ban waje sha shasha kawae" mikewa Afeefah tayi da sauri ta fice daga falon da gudu. Abba ya juya kansu Jiddah yace "ku kuma ban ga amfanin ku ba a tare, ku tashi ku ban waje" sum sum suka fice daga falon su ma.

Eeshatullah Goni😘😘
[5/22, 07:56] Umar Dalha: πŸŒΈπŸ‘©πŸ»'Ya Mace Kyautar Allah πŸ‘©πŸ»πŸŒΈ

A true life love story

By *Ashmaad*

Dedicated to my kawalliya romon jaa6a(khaleesat haiydar) 😘😘

20....

Afeefah bata yi wani break din kirki ba tsabar kukan dake cin ta ga shi bbu daman yi, Mami da ya Aliyu na falo, bbu abinda take sae jujjuya Fork din hannunta, Da kyar ta iya yi ma Mami sallama don har wani rawa muryarta yake, ya Aliyu kam ko kallonsa bata yi ba, driver na barin gidan ta rushe masu da wani matsanancin kuka cikin mota, Driver yyi parkin da sauri yana kallonta da mmki yace "kai! me ya faru" tsaki su Jiddah suka yi suka ce "Da' alla baba mu je iskanci ne kawae" har suka isa makaranta bbu Wanda ya kalli inda take, Duk suka nufi faculty dinsu, ita ma ta nufi faculty dinta, Bakin lecture Hall ta ga Maryam tsaye suna magana da wasu yan ajinsu, Maryam ta saki baki tana kallonta har ta karaso snn tace "Ni kam kina bn mmki Afeefah, bbu ranan da xae wuce baxa ki yi kuka ba, kukan ma mara reason? Haba ki dinga maintain mana, ke fa ba yarinya bace don Allah ki bari, ni baxan boye maki ba gskya haushi kike ban, abu kadan kuka kmr wata yar shekara uku" tabe baki tayi ta ci gaba da xancenta da yan matan ajin, Afeefah tayi tsaki ta bar wajen ta koma karkashin bishiya tayi xamanta. Har lecturer su ta iso Afeefah bata shiga aji ba, yan ajinsu da dama sun yi mata mgna lecturer fa na class sae dae ta ce ta sani, Tun daga nesa ta hangosa yana tahowa, gabanta yyi mugun faduwa taji kmr ta tashi ta falla a guje amma ta kasa, wasa da hijab dinta ta shiga yi gabanta na faduwa, dago ido tayi suka yi ido hudu da shi, ta sunkuyar da kai da sauri, har ya wuceta bae ce komae ba ita ma bata gaishesa ba, mikewa tayi da sauri ta bar wajen kmr munafuka. Da yamma tana xaune cafeteria ita kadae amma ba wnda suka saba xuwa ba, kwata kwata ranan bata shiga lecture ba a cafeterian ta yini, ko Maryam bata san inda take ba, juyawa tayi jin student din cikin cafeterian na gaisuwa don ganin Wanda suke gaisar wa gabanta ne yyi mugun faduwa ganin sa da tayi ya shigo cafeteria, tayi saurin sunkuyar da kai ta jawo hijab dinta ta dan rufe fuskarta, kujerar dake kallon nata ta ga ya ja ya xauna, mikewa tayi da sauri xata bar wajen yace "if I shud slap yhu! Koma ki xauna" kallonsa ta tsaya yi ya watsa mata harara yace "sit" komawa tayi ta xauna ta sunkuyar da kanta, fuskarsa a daure yace "me ya hana ki shiga lectures yau?" Kin dago kai tayi bare ta basa amsa, waiter din dake cafeterian ne ya ajiye ma Dr Aliyu soft drink a table da pack din straw, ya xare straw daya snn ya bude chill coke din gabansa ya saka straw din yyi sip din kadan snn ya dago kai yana kallonta yace "Answer my question B4 i slap yhu" kin dago kanta tayi, a dan tsawace yace "Zainab!" Dago kanta tayi lkci daya hawayen da ke makale idonta ya gangaro, yyi mata mugun kallo yace "oh kuka kike min?" girgixa masa kai tayi ta share hawayen da sauri, ya hade rae yace "me ya hanaki shiga lecture yau" a hnkli kanta a kasa tace "an min fada a gida ne" jin yyi shiru bae ce komae ba yasa ta dago kai tana kallonsa, ta ga wani mugun kallo yake mata, ta dauke kai, a nutse yace "fadan me aka maki?" Shiru tayi bata ce komae ba, ta ji yace "Zainab!" Kallonsa tayi snn tace "Ni ma bn san me nayi ba" Maryam ce ta shigo cafeterian da alamar Afeefah take nema, hango hijab dinta tayi ta karasa table din da sauri tace "kin kyauta Afeefah daga na fadi maki gskya shine har da wani kin shiga lecture...." Harara Afeefah ta watsa mata tace "ehh ban shiga ba" tana kai wa nn ta mike ta fice daga cafeterian sae a snn Maryam ta lura da Dr Sharif da ya bi Afeefah da kallo, ta dan kirkiri murmushi tace "sir ashe kana nn, ina yini" yace "lfya lau" ta juya kmr munafuka ta fice daga cafeterian. Mikewa Dr Sharif yyi ya ciro kudi ya mika ma waiter din snn ya fita, parking space ya nufa ya shiga motarsa yyi reverse ya nufi main gate, tafiya kawae take tana share hawayen idonta taga mota ya tsaya daga kusa da ita, ya bude motar ya fito yana mata mugun kallo yace "yhu walked out of me ina maki magana koh?" Xaro ido tayi tace "Sir Maryam ce..." Dakatar da ita yyi yace "meet me at my office yanxun nn" yana kai wa nn ya bude motarsa ya shiga ya bar wajen.

Eeshatullah Goni πŸ˜˜πŸ˜˜πŸŒΈπŸ‘©πŸ»'Ya Mace Kyautar Allah πŸ‘©πŸ»πŸŒΈ

A true life love story

By Ashmaad

21....

A hnkli Afeefah ta tura kofa ta shigo bayan tayi sallama ta karasa kusa da table dinsa kanta a kasa tace "am here sir" jin bae ce komae ba yasa ta dago kai tana kallonsa, hararanta taga yana yi, yace "Sit" ba musu ta xauna tana kallonsa, yace "Me aka maki a gida?" A hnkli tace "yayanmu ne ya gaya ni da Abbanmu" kallonta yake yace "Me kika masa?" Girgixa masa kai tayi kmr xata yi kuka murya can kasa tace "wae don nace ka bani coffee" shiru yyi yana kallonta gnin hka yasa ta soma wasa da fingers dinta, "me yasa kika gaya masa na baki coffee?" Dago kai tayi ganin hawaye idonta yace "kar ki min kuka" gyada masa kai tayi ta mayar da hawayen snn tace "Dama yace in hado masa coffee ne da daddare shine da na kai masa daki nace masa ashe coffee yana da ddi ban sani ba sae yace eh mana, sae nace masa har da madara ka sa min....." Murmushin da taga yana yi yasa tayi shiru tana kallonsa, ya ce "ina jin ki" shiru tayi har lkcn, yace "go on!" Sunkuyar da kanta tayi tace "shine sae ya mareni, kuma ya gaya ni da Abbanmu ana ta min fada" muryarta na rawa ta kare maganan tana kallonsa, a hnkli ya daura fingers biyu kan lips dinsa yace "kar ki min kuka" ta gyada masa kai tare da hadiye kukan, murmushi ya kuma yi yace "meyasa kika gaya masa na baki coffee?" Girgixa masa kai tayi tace "ni ma ban sani ba" yace "beside gani nayi kina kallona ranan shi yasa na baki Zainab" xaro ido tayi tace "sir ni ban kalle ka ba wllh" murmushi kawae yake ya jawo foil papern dake desk a gabansa ya warware ya dauki table knife yyi slicin cake din ciki ya soma ci a hnkli yace "ya sunan yayan naki?" Sauke idonta tayi daga kallonsa tace "Ya Aliyu!" Ya dan wara ido yace "uhhn Namesake dina ne knn" Bata ce komae ba, bayan kusan minti uku ta dago kai tana kallonsa jin bae ce komae ba, suka hada ido don kallonta yake tayi saurin sunkuyar da kanta, cake din gabansa ya dauka ya mika mata yace "Take" ta girgixa kai da sauri tace "Thnk yhu sir" hararanta yyi yace "Shine kuma kike kallona?" Kmr xata yi kuka tace "ni ban

Please Login or Register in order to submit comment