Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne yasa ta daure fuska tace "me xa ki ci?" Afeefah ta girgixa kai tace "A'a na koshi ni" ko rufe baki bata yi ba Dr Sharif ya karaso cafeterian yan matan da tace yana ma mgna a lab daxun na biye da shi a baya, kujera ya ja ya xauna gefen Maryam yace "Ya exams Maryam?" Maryam ta kirkiri murmushi tace "Alhmdllh," yace "Ma'sha Allah, wishing u ol success, no carry over in'sha Allah" murmushi kawae Maryam tayi tace "Ameen" yan matan guda biyu dama duk sun xauna, ya juya yana kallon su yace "wani drink xa a kawo maku?" Duk suka ce fanta, Afeefah dae sae Satan kallonsu take tana yin kmr tana danna wayarta don yan matan ba karamin haduwa suka yi ba, fanta hudu yasa aka kawo na roba da snacks ya mika ma matan biyu ko wanne daddaya snn ya ba Maryam ma, Afeefah kuma ya ajiye mata gabanta, dauka tayi da sauri ta mayar masa ba tare da ta kallesa ba tace "Thanks bna jin yunwa" murmushi yyi ya bude shi ya fara sha, fira kawae yake da 'yan matan dake ta basa lbri, Afeefah ta Mike ta saka wayarta a jaka ta xuge snn ta gyara blck veil din kanta don har lkcn lab coat na jikinta tana kallon Maryam tace "sae mun yi waya" tana kai wa nn ta fice daga cafeterian yan matan suka bi ta da kallo, ta nufi inda ta saba xama ta jira su jiddah, bayan minti biyu da fitan ta Dr Sharif ya mike yana kallon yan matan da Maryam yace "excuse me, xan dan yi makin phone call" ya fice daga cafeterian ya nufi inda yasan xai ganta, xaune ya sameta tana danna wayarta kamshin turarensa kadae yyi announcin mata presence dinsa a gun, "Zainab!" Juyawa tayi tana kallonsa, ya xauna dan nesa da ita yace "me na maki kike fushi?" Hawaye ne ya taru idonta ta ki cewa komae sae jujjuya wayar hannunta take, yyi shiru yana kallonta, mota ne yyi parkin dan nesa da inda suke xaune, Afeefah ta kafa ma motar ido ganin kmr motar ya Aliyu, to amma ae bae dawo ba, wayarta ne ya fara ring a take, taga Aliyun ne ke kiranta, ta daga yace "Am in ur sch Zainab," wara ido tayi tace "Da gske yayanmu ka dawo ne" inda yyi parkin kawae ya gaya mata, ta juya tana kallon Dr Sharif tace "kaga motar yayanmu na Lagos ne can, he came to pick me," Dr Sharif yace "OK in je mu gaisa?" Shiru ta dan yi sae kuma tace "to" mikewa tayi ta nufi motar gabanta na faduwa Dr Sharif ya bi bayanta.

Eeshatullah Goni๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜

๐ŸŒธ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿป 'Ya mace kyautar Allah๐Ÿ‘ฉ๐Ÿป๐ŸŒธ

A true life love story

By Ashmaad

34.....
Karasowa cikin dakin Aliyu yyi yana kallonta, Afeefah tuni wayar hannunta ya sulale kan gado ta jawo pillow da sauri ta rufe ganin bae lura ba, tsaye yyi bakin gadon yana kallonta taki dago kanta, yace "Zainab!" Da kyar ta iya bude baki a hnkli ba tare da ta kallesa ba tace "Na'am" xaunawa yyi gefen gadon yace "Ki gaya min meyasa ke kadae ce baki jin mgna ta a gidan nn" Shiru tayi bata komae ba, a tsawace yace "Zainab!" Dago kanta tayi tana kallonsa da idonta da yyi ja, lkci daya hawaye ya cika idonta a hnkli tace "kayi hkuri yayanmu baxan kara ba" rungumeta yyi yace "Sau nawa kike making min wnn promise din kina break din sa Zainab?" Cikin muryar kuka tace "Na daina yayanmu" dago kanta yyi murya can kasa yace "promise?" Kai ta gyada masa tana hawaye, mikewa yyi ya kama hannunta suka fita daga dakin ya nufi nasa da ita. Kwata kwata Afeefah bata saki jiki da shi kmr ynda ta Saba ba ranan, duk sae ta ji ta a takure abinda bae taba faruwa da ita ba suna tare da Ya Aliyu, tsarabar da ya yo mata ma bata wani nuna farin ciki kmr ynda take yi da ba, kawae dae tana xaune dakin ne ta kafa ma plasman dake ta aiki ido, shi kuma yana danna laptop dinsa, gaba daya hnklinta na kan wayarta da ta baro a daki duk ta kagu ta fita, ta rasa dalilin da yasa ta damu da kiran Dr Sharif hka, Sumayya ce tayi sallama ta shigo dakin tana kallon ya Aliyu tace "yayanmu wae Mami tace in kira Afeefah" ba karamin farin ciki Afeefah tayi ba don sae da ta sauke ajiyar xuciya, Mikewa tayi tana kallon ya Aliyu tace "yayanmu na tafi Mami na kirana" kai kawae ya gyada mata ta dauki ledan tsarabar da ya bata ta fita ta nufi dakin Mami, kasan dakin ta xauna tana kallon Mamin tace "gani Mami" Mami tace "kin gama hada kayan naki?" Afeefah ta gyada Mata kai tace "na gama" Mami tace "je kiyi ma Abbanku sallama ynxu, gobe da sassafe Adnaan xae tafi kd sae ki bisa kawae" mikewa Afeefah tayi ta fita ta nufi dakin Abba, yana xaune falonsa yana kallon news, ta xauna kasa, yace "ya aka yi Zainab, yau ba ki yi bacci da wuri ba knn" tayi murmushi tace "eh bnyi ba Abba, dama Mami ce tace in xo in gaya maka gobe xan tafi kd" shiru Abba yyi yana kallonta can yace "toh shknn Allah kai mu, tafi ki kira min ita" mikewa Afeefah tayi ta fita daga falon ta koma dakin Mami tace "Mami Abba yace in kira ki" Mami tace "to jera min kayan nn kafin in dawo" Mami na Kai wa nn ta fita ta nufi dakin mai gidan nata, Kallonta kawae Abba yake har ta xauna snn yace "ynxu dae nuna min kike kin fini iko da Zainab a gidan nn koh Zuwaira?" Mami ta kallesa da mmki tace "kmr ya knn?" Abba yace "wato ke a ganin ki ke ya kamata ki dinga yanke wasu hukucin a kanta knn don Kinga ina maki shiru koh?" Mami tace "don nace xata kaduna shine nayi laifi Alhaji?" Abba yace "sae ana gobe xata tafi ya kamata a gaya min? kuma ma wae sae ki aiko min ita tsabar ki gwada min kin fi ni iko da ita ko me" Mami tace "Allah baka hkuri, kuma don naga Adnaan xae tafi kadunan ne gobe yasa nace kawae ya tafi da ita da su Jiddah, kuma kasan da sassafe yake tafiyarsa ba kmr Aliyu ba." Abba yace "to baxa su yi tafiyar sassafen da shi ba, ae Ali na nn da yamma sae ya Kai su" Mami bata ce komae ba, ya Mike ya shiga dakinsa ya dauko dubu 50 ya mika ma Mami yace "gashi kiyi Masu siyayyar da ya kamata" Mami ta sa hannu ta karba tace "Allah kara budi" snn ta mike ta fita daga dakin. Afeefah na gama gyara ma Mami kayan da ta sa ta ta tafi dakinsu, Jiddah kadae ce tayi bacci, Sadiya kuma na danna wayarta, kan gadonta ta nufa da sauri ta daga pillow ta dauki wayarta ta ga Dr sharif bae kuma kiranta ba, juyawa Afeefah tayi taga Sadiya ba kallonta take ba, kmr munafuka ta shige bayi da wayar, dailing number tayi, yana fara ringing ga katse ya kirata, "Baki yi bacci ba?" Kunya ne ya kamata don ko duba Karfe nawa bata yi ba, da sauri tace "ehh naga mis cal ne" Dr Sharif yace "na kira kin dauka kuma kika yi shiru" tace "uhm yayanmu ne ya kirani" Dr Sharif yace "OK, ya su mama?" A hnkli tace "suna lfya" yace "me kike yi har ynxu ba ki kwanta ba" tace "na hada kayana ne, gobe ya Adnaan xae tafi da ni Kaduna" yace "Really?" Kai ta gyada masa kmr yana ganinta, yace "Ashe xan yi missin crying student dina" murmushi Afeefah tayi murya can kasa tace "ae xan dawo kafin a kare hutu" a hnkli yace "Shknn, journey mercy Dear" shiru tayi jin abinda ya kirata da, "Are yhu there?" Ya tambayeta jin shirun, Da sauri tace "um na ngdd" yace "welcm, sleep sweet!" murmushi tayi ya katse wayar, ta fito daga bayin a sanyaye.

Washegari misalin Karfe goma Mami tasa Aliyu ya kai ta kasuwa don yi ma su Afeefah siyayyan tsaraban da xa su tafi da kaduna. Afeefah na xaune dinnin tana breakfast don tashinta knn tunda tasan tafiyar sae da yamma, Jiddah ta sakko ta mika mata wayarta tace "Ynxu dae tsakanin ki da Allah soyayya kuke da Dr Sharif din nn ko Afeefah" Afeefah ta hade rae ta karbi wayarta tace "Kinga Anty Jiddah bana so, kawae don ya kirani mu gaisa shine xa ki ce soyayya muke ni bna so" kmr xata yi kuka ta kare mgnr, dariya Jiddah take ta bar wajen da sauri kafin ta fara mata kuka, Afeefah ta daga kiran ta kara a kunne, muryarta na rawa ta gaishesa bayan tayi masa sallama, "Me aka maki?" Tambayar da yyi mata knn jin muryarta, a hnkli tace "Su anty jiddah ke neman tsokanata" yyi murmushi yace "to kiyi hkuri" shiru tayi bata ce komae ba, yace "kin fasa tafiyar yau ne" girgixa masa kai tayi tace "Abbanmu ne yace mu bari da yamma yayanmu ya Kai mu" yace "OK Allah kai mu" a hnkli tace "Ameen" yace "ltr" shiru tayi har ya katse wayar snn ta ajiye ta ci gaba da shan tean ta a hnkli. Da yamma misalin Karfe uku Afeefah ta gama shirinta da su Anty jiddah da Sadiya don tare xa su tafi amma su Washegari xa su dawo kano, Aliyu da kansa ya karbi jakar kayan Afeefah ya kai bayan mota, ita kuma ta haura sama da gudu ta shige dakinsu, Dr Sharif ta shiga kira tana kallon bakin kofar dakin a tsorace, yana fara ring ya katse ya kirata, kmr munafuka tace "sir dama em ina son in gaya maka ynxu xa mu tafi" murmushi yyi yace "ko in xo in raka ku?" Xaro ido tayi da sauri tace "A'a" yace "To Allah tsare hanya Zainab" a hnkli tace "Ameen ngd" Addu'o'in da xata karanta ya shiga tuna mata, ji tayi ya Aliyu na kiranta da sauri tace "toh toh ngdd sir, byee" da sauri ta katse wayar ta boye cikin hijab dinta jin har ya shigo dakin harara ya galla mata yace "ba ki ji ina kiran ki ne?" kmr xata yi kuka tace "yayanmu ina cikin bayi ne fa" ficewa yyi daga dakin ta bi bayansa, Mami taje tayi ma sallama snn ta fita don su Jiddah har sun shiga mota, gaba ta xauna as usual, Mami ta fito ta masu addu'ar Allah tsare hanya snn ya Aliyu ya ja motar suka bar gidan. Karfe Shidda da yan mintuna suka shigo kaduna, Afeefah ta juya ta kalli ya Aliyu jin wayarta na vibrate a hijab, ya lura da hkn yace "ya aka yi princess?" Murmushi ta kirkira tace "Um um ba komae" bakwae saura suka isa unguwar rimi tsabar traffic din kd, horn Aliyu yyi mai gadi ya bude gate, kusan a tare suka shiga makeken gidan da wata mota dake bayansu, ya Aliyu yyi parkin a parkin lot, Afeefah ce ta fara fitowa dae dae lkcn da mutumin cikin motar ya fito bayan shi ma ya gama parkin, wara ido tayi ta nufesa da gudu ta rungumesa tace "Ya Ma'aruf" rungumeta yyi shima yace "waow Zainab ku ne dama da magrib" Su Jiddah suka karaso suka gaishesa suna murmushi su ma, Aliyu kam kin fitowa daga motar yyi sae kallon Afeefah da har lkcn tana jikin Ma'aruf yake ta madubi fuskar nn tasa a daure. Ma'aruf yace "Driver ne ya kawo ku?" Afeefah tace "A'a yayanmu ne!" Sae a snn Aliyu ya fito yana kirkiran murmushi ya nufi inda suke ya basa hannu suka gaisa. Cikin gidan suka nufa gaba daya Afeefah na ta jero ma Ma'aruf tambayoyi, "to ya Ma'aruf ynxu xaka iya shiga da ni gurin da kuke xama idan kuna tuka jirgin in gani?" Dariya yyi ya lakaci hancinta yace "ke dae ba kya girma yarinyar nn koh?" Turo baki tayi xata yi mgna taga wani mummunan kallon da ya Aliyu ke mata, tuni ta hadiye abinda xata ce ta shiga wasa da yatsunta har suka shigo falon gidan. Hajiya Khadija mahaifiyar Ma'aruf ce ta sakko falon da mmki tana kallonsu tace "dama ku ne da magariban nn Aliyu" murmushi Aliyu yyi yace "wllh kuwa Ammi," mikewa Afeefah tayi da gudu ta rungumeta. Hajiya khadija tayi dariya tace "ke dae bakya girma ko Zainab, an xo hutu knn" murmushi Afeefah tayi ta rufe idonta, Hajiya khadija ta karaso cikin falon ta xauna da fara'arta ta amsa gaisuwar Su Jiddah, tana kallon Aliyu tace "barrister Ali knn, ina su Mami?" Yace "suna nn lfya Ammi," tace "kai baka xuwa sae ka kawo Zainab hutu koh?" Dariya yyi yana shafa kansa don ya ma rasa me xae ce ya kare kansa, mikewa Ma'aruf yyi yana kallon Afeefah yace "mu je ki ban lbrin Buk, ki kuma gaya min gskya samarin ki nawa?" Dariya tayi ta mike ta bi bayansa, Aliyu ya bi ta da kallo lkci daya murmushin da yake ma Ammi ya bace daga fuskarsa.

Eeshatullah Goni๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜

[5/22, 07:56] Umar Dalha: ๐ŸŒธ๐Ÿ‘ฉ๐Ÿป 'Ya mace kyautar Allah๐Ÿ‘ฉ๐Ÿป๐ŸŒธ

A true life love story

By Ashmaad

36__37
Afeefah na kwance daki tun fitowarta daga dakin Ma'aruf ita a dole tana fushi da Ya Aliyu sae kumbure kumbure take, tura kofar dakin aka yi Anty Jamila ta shigo tace "Zainab sakko ki ci abinci ana jiran ki" bata yi musu ba ta sauko daga kan gadon ta bi bayanta suka sauka kasa, ya Aliyu na xaune falo da Ammi da ya Saleem, Afeefah ta hade rae ta nufi dinnin, ta debi abincinta don su jiddah sun diba nasu, ilham tace "wnn dan abincin xae isheki Zainab?" Ba tare da Afeefah ta kalleta ba tace "ehh xae min" Anty jamila ta kalli Aneesah tace "ke kara mata me wnn dan abincin xae mata" da sauri Afeefah tace "wllh Anty ni ya isheni" kyaleta duk suka yi suka shiga cin abincinsu, da ke kadan ta xuba tuni ta cinye ta mike ta bar dinnin din, xata haura sama Ammi tace "har kin gama Zainab" tace "ehh na gama" dakin su Aneesah ta nufa ta shiga bayi don yin wanka, ko da ta fito kayan baccin ta ta fiddo a jaka tasa snn ta sa Hijab tayi kwanciyarta, balla sim dinta da ya Aliyu yyi ne ya fado mata nn da nn hawaye ya cika idonta taji wani mugun haushin sa kawae take ji ynxu, Ammi ce ta shigo dakin tace "ke baxa ki sauka falo kiyi kallo ba Afeefah," Afeefah ta ce "Ammi ni bna son kallon" Ammi tace "toh shknn, amma kar kiyi bacci sae kun gaisa da Baffan ki" Afeefah tace "toh" snn Ammi ta fita daga dakin, ko minti biyar Ammi bata yi da fita ba Ya Aliyu ya shigo dakin, rufe ido tayi da sauri kmr me bacci, ya karaso kan gadon ya xauna yana kallonta yace "Zainab!" Kin juyowa tayi bare ya sa ran idonta biyu, xagawa yyi ta daya side din yana kallon fuskarta ya kuma kiranta, nn ma taki amsawa, murmushi yyi don yasan idonta biyu sarae, ya mike ya fice daga dakin. Murguda baki tayi ta kuma tura kanta cikin pillow cike da jin haushin sa, Karfe tara da rabi Ilham da Jiddah suka shigo dakin suka ce Baffa na kiranta, mikewa tayi ta bi bayansu suka nufi falon baffa, murmushi yyi ganinta, ta xauna gefensa ita ma tana murmushin tace "Sannu da dawowa baffa" ya shafa kanta yace "yauwa mamata, ashe kun xo, ina su Abbanku da Mami," tace "duk suna lfya, sun ce in gaisheka" yace "Madalla, mun yi waya dasu daxu ma, ya makaranta ynxu kin xama 'yar jami'a koh" dariya tayi ta sunkuyar da kanta, baffa ya kalli Jiddah yace "ya baku xo min da Fadila ba Hauwa" jiddah tace "ba su yi hutu bne shi yasa" yace "Allah sarki, Adnaan na nn abunsa koh?" Jiddah tace "yana nn baffa" sun dde suna hira daga bisanni suka yi masa sae da safe dae dae lkcn da Ma'aruf ya shigo falon don yi ma Abban nasa sae da safe shi ma, Afeefah na shirin kwanciya Ma'aruf ya shigo ya xauna gefenta yace "gashi har xan tafi baki bni lbrin samarin ki ba koh?" Afeefah ta wara ido tace "ina xa ka Ya Ma'aruf?" Dariya su Ilham suka kyalkyale da suka ce "gidan sa mana" Afeefah tace "ohh na manta" dariya yyi yace "xa ki xo ki min sati koh?" Ta gyada masa kai tace "ehh xan xo yaya" yace "yawwa Kanwata" duk suka yi masa sae da safe snn ya fita daga dakin, Ammi ta shigo tace "Zainab taso ki kwanta bedroom dina" ba musu ta mike ta bi bayan Ammi.

Washegari da safe misalin Karfe goma su Jiddah suka fara shirin komawa kano, ya Aliyu ne ya shigo dakin da sallama, Afeefah da ke xaune gaban madubi tana shafe shafe ta hade rae tare da turo bakinta, gunta ya nufa yana kallonta yace "ina kwana Zainab?" Sunkuyar da kai tayi da sauri tace "yayanmu ni bn ganka ba, ina kwana," hancinta ya ja yace "dake ke makauniya ce ba" murmushin da bata yi niyya ba tayi, sae kuma a hnkli tace "ka yi hkuri" juyawa yyi yana kallonsu Jiddah yace "ina jiran ku a falo" har suka tashi tafiya Afeefah kin fita tayi har sae da Ammi tace "Zainab baxa ki je ku yi sallama da yayyin ki ba?" Mikewa tayi ba don ta so ba ta fita, kanta a kasa ta isa motar ya Aliyu ta daga ma su jiddah hannu snn ta nufi driver seat inda Aliyu yake ta dago kai a hnkli tace "Yayanmu Allah ya tsare hanya" ba tare da ya kalleta ba yace "Ameen" kmr xata yi kuka tace "yayanmu baka kalleni ba" fuskarsa a daure yace "in maki me?" Shiru tayi tana kallonsa lkci daya hawaye ya cika idonta ta juya xata bar wajen ya kamo hannunta, bbu yabo bbu fallasa yace "to me kike son in maki Zainab?" Girgixa masa kai tayi hawayen idonta ya gangaro, murmushi yyi yace "toh ngd Zainab, will miss yhu a lot" murmushi ita ma tayi, ya ciro handkerchief ya share mata hawayen fuskarta a hnkli tace "yayanmu kayi hkuri, daga yau xan fara jin mgnr ka" murmushi kawae yyi yace "Allah ya sa" har suka bar compound din bata daina daga masu hannu ba sae taji ba ddi kmr ta bi su, Aneesah ce ta ja ta tana dariya ta nufi cikin gida da ita ganin hawayen idonta. Da rana Afeefah na xaune falo suna kallo da su Anty jamila, Afeefah ta kalli ilham dake gefenta tace "Anty ilham dan ara min phone din ki don Allah, ilham tace yana sama a daki, mikewa Afeefah tayi ta nufi sama da sauri ta dauki wayar, ta fiddo nmbr Dr Sharif da ta ajiye a jakarta tayi dailin, bugu uku ya dauka tare da yin sallama, rasa abun cewa tayi kmr mara gskya tace " Sir ina yini" shiru taji yyi hkn yasa tayi saurin kallan wayar ta ga ko ya katse ne amma taga bae katse ba, sunanta ta ji ya kira ta amsa a dan kunyace, yace "me ya sami wayar ki?" Kmr xata yi kuka tace "yayanmu ne ya kwace" da dan mmki yace "sbda me?" Muryarta na rawa tace "wae don ina waya" Dr Sharif yace "uhm OK, wnn wayar waye" a hnkli tace "na sister na Ilham" yace "ok" shiru tayi bata kuma cewa komae ba, yace "ya mutan gidan" tace "duk suna lfya?" Yace "kinyi missin dina kuwa?" Shiru tayi ta kasa basa amsa, a hnkli ta ji ya kira sunanta, murya can kasa tace "Na'am" murmushi yyi ya kuma yi mata tambayar, cike da jin kunya tace "nayi!" Yace "karya kike" xaro ido tayi tace "wllh sir nayi missing dinka" yar dariya yyi yace "really kina son gani na knn!" Kunya ne ya kamata ssae, taki cewa komae, a hnkli yace "Zainab!" Tace "uhm" yace "baki son ganina knn" murya can ciki tace "ina so" yace "Toh in xo ki gan ni" rufe fuskarta tayi da pillow da sauri wae ita kunya a hnkli tace "Uhm" yace "I promise xan xo kd in gan ki dear" sallama yyi mata jin bata da niyyar cewa komae kuma, Afeefah ta ajiye wayar tana murmushi. Tun daga lkcn kullum sae sun yi waya da Dr Sharif da wayar Ilham, Aliyu kuma sau dayawa ta wayar Saleem yake kira yace ya bata, sae dae ynxu ta daina dokin kiran Aliyu kmr ynda take da, wani lkcn har pretend take tayi bacci idan aka kawo Mata wayar. Ranan da ta cika kwana uku Ya Ma'aruf ya xo da yamma, taji ddin ganinsa ssae, dakin Ammi ya nufa tana biye da shi a baya, bayan sun gaisa da Ammin tasa yace "Ammi na xo tafiya da Zainab ne tayi ma Amina kwana biyu," Ammi tace "To ae Abban ku bae sani ba" Ma'aruf yace "xan kirasa in gaya masa Ammi" Ammi tace "A'a da dae ka bari goben ka xo da safe ka samesa ka gaya masa sae ku tafi da ita" bata rae Afeefah tayi ta xamo daga kan gadon Ammi, Ammi tace "Au to Allah baki hkuri, ku tafi Ma'aruf idan ya dawo na gaya masa, amma kai ma ka kirasa," murmushi Afeefah tayi ta mike da sauri ta fice daga dakin don xuwa ta hada kayanta, jikinta ne yyi sanyi tunawa da tayi Dr Sharif yace mata gobe xae xo, can dae a xuciyarta tace to ba sae ya sameni can gidan ba, ilham ta samu da sauri dakin Anty jamila tace "Anty ilham idan Wnn da yake kirana ya kira kice bana nn amma xan kirasa" ilham tace "toh"

Karfe shidda na yamma Ma'aruf ya isa gidansa da Afeefah, bell ya danna bayan minti biyu wata kyakkyawa da baxata wuce 23 ba ta bude kofar rike da wani handsome boy a hannunta, rungumesu yyi gaba daya Afeefah ta kwalalo ido tare da dauke kanta da sauri, matar cikin sanyin murya tace "Sae ynxu Hubbi" yace "Ba nace maki xan tafi gida daga can ba, ba mu hanya bby" sae a snn Matar ta lura da Afeefah, ta bata hanya tana kallonta, Afeefah ta dukar da kai da sauri, kama taga matar take mata da warce ta sani amma ta rasa a ina, kmr munafuka tace "Ina yini Anty" "lfya lau, sannu da xuwa" matar ta amsa Mata a takaice. Har bedroom din da xata ajiye kayanta Ma'aruf ya kai ta, yace "feel at home dear" gyada masa kai kawae tayi ya fita. Tana xaune kan darduma ta idar da sllhn magrib Amina ta shigo dakin, bbu yabo bbu fallasa tace "ki sakko ki ci abinci" tana fadin hka ta juya ta fice, Afeefah tayi jigum tana da ta sanin biyo ya Ma'aruf, har ta yi sllhn isha matar bata kuma kiranta ta xo ta ci abinci ba, a xuciyarta tace to ko tana tunanin budurwarsa ce ni, Ma'aruf ne ya shigo dakin da mmki yace "Zainab ba Amina ta xo kiran ki ba, meyasa baki sakko ba" murmushi ta kirkira tace "um na koshi" ya galla mata harara yace "c'mon taso mu je ki ci abinci, ko sae na shigo na dago ki" mikewa tayi da sauri yyi dariya ya juya ta bi bayansa a sanyaye hka kawae taji ita tsoron matar ma take, da kyar take tura abincin gabanta a dinnin din tsabar irin kallon da Amina ke mata ga Ma'aruf ya isheta da surutu. Mikewa tayi daga karshe kmr xata yi kuka tace "yaya ni na koshi" yace "ba ki isa ba, Maza cinye shi" mikewa Amina tayi tana rike da yaronta ta bar dinning din ta haura sama, ya bi ta da kallo, can ya maido da dubansa ga Afeefah yace "sae fa kin cinye shi Zainab" komawa tayi a sanyaye ta xauna ta shiga tura sauran abincin, tana gama ci ya ki barinta ta haura sama, tayi da ta sanin

Please Login or Register in order to submit comment