Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace "No! I wil b OK idan na maida drip din, kar ki tashe su" ta juyo tana kallonsa, wani lallausan murmushin da ya kwantar mata da hnkli ya sakar mata yana kallon kwayar idonta, a sanyaye ta mayar masa snn ta dawo ta durkushe gabansa tana kallonsa cikin sanyin murya tace "Toh ka tashi ka mayar da drip din sir," sunkuyar da kai yyi don wasu sabbin hawayen ya ji na shirin xubo masa, lkci daya ya mike ya koma kan gadon, ita ma ta mike ta xauna daga gefensa, a hnkli tace "In je in hado maka tea sir?" Girgixa mata kai kawae yyi cikin dakiya yace "Bacci nake ji" gyara masa pillon kan gadon tayi tana kallonsa ya kwanta a hnkli tare da lumshe idonsa, ta matso dab da shi cikin sanyin murya tace "Sir baka sa drip din ba kuma" ba tare da ya bude ido ba yace "Anjima xan sa, ki tafi kiyi kwanciyar ki" ta dan bata fuska tace "Sir ni nn xan tsaya in dinga duba ka plss, baxan iya tafiya in bar ka ba" kmr xata yi kuka ta kare maganar, ya girgixa mata kai cikin sanyin murya yace "Addinin mu bae yarje mana kwana waje daya ba Zainab, ni ba muharramin ki bne ki tafi kiyi kwanciyar ki I will b alryt in'sha Allah" hawaye ya cika rinannun idonta muryarta na rawa tace "Amma sir ae Allah ma ya san lalura ne, its nt intentional don Allah ka bar ni in tsaya da kai plss sir" hawaye na bin kuncinta ta karashe tana kallonsa, bude ido yyi a hnkli yana kallonta lkci daya ya mayar ya lumshe don wani tukuki xuciyarsa ke masa ba kadan ba, tagumi tayi gefensa idonta a kansa, sun kusa minti talatin a hka idonsa a rufe, a tunaninta bacci yyi, shi kam bbu abinda yake sae kukan xuci wanda ya gwammace da ma na idon yyi ko xae ji saukin abinda xuciyarsa ke masa, bae taba sanin hka ake ji a other side of love ba, so da yawa a kan kawo masu cases irin hka a clinic bae kuma taba ba irin cases din muhimmanci ba hasali ma haushin victims din yake ji sae ga shi shima yau yyi falling victims of such circumstance, yyi daya sanin sanin Zainab, yayi da ya sanin fara sonta without notice, bae taba soyayya ba sae a kanta, nd he can sew they are much prepared to break his heart, a hnkli ya ji ta daura kanta gefen pillon da yake kwance duk da hijab din da ke jikinta hkn bae hanasa jin 'dad'da'dan kamshin da gashinta ke yi ba, bayan yan mintoci ya ji saukar numfashinta a hnkli alamar ta yi bacci, cikin dubara ya xame kansa daga kan pillon ya mike xaune snn ya sauko kasa ynda baxae tada ta ba, ji yyi jiri na neman kada sa da ya mike tsaye, yyi saurin dafa bango yana kallon agogon dakin, Karfe uku ya dan gota, button din shirt din jikinsa da ke bude ya shiga buttoning cikin rashin kuzari, yana gama wa ya kwashi wayoyinsa da Atm ya nufi kofa yana hada hanya ya bude a hnkli snn ya fice daga dakin ya sauka falo, ba karamin daurewa ya dinga yi ba don jiri yake gani ssae har ya fito compound ya nufi gate ya bude ya fice daga gidan, yana gnin dishi dishi ya isa bakin titi, da ka gansa kasan kiris ya rage yyi collapse, ya dan jima tsaye bakin titi yana layi kmr wani mashayi kafin ya samu dan sahu, ya shiga ya rike kansa da ke neman rabewa, jin tambayar da dan sahun ke masa yasa ya dago da kyar yace "Airport xaka kai ni"

Karfe uku da minti kusan ashirin Dr Faisal ya shiga bedroom din da sallama don cire ma Dr Sharif drip yaga Afeefah kadae ce takure daga gefen gadon tana bacci har lkcn kanta na kan pillow, a xatonsa yana bayi kuma sanin likita ne shi ma ya sa ya juya ya fita duk da yyi mamakin me yasa ya cire drip din bae bari ya kare ba, hudu saura Afeefah ta farka ta mike xaune tana mitsika ido, gnin bata gansa kwance kan gadon ba yasa tayi tunanin ko yana bayi, tana nn xaune har aka kira sllh amma bata ga ya fito ba, Faisal ne ya shigo dakin da Saleem, Saleem ya sakar mata murmushi yace "Mai jinya har kin tashi, ya jikin patient din na ki? Ae Faisal ya ban lbrin baccin ki kika sha" Murmushi kawae tayi a hnkli tace "Ni bn yi bacci ba" Dr Faisal yace "yana bayi ne?" Kai ta gyada masa, saleem yace "to mu je mu yi alwala kan ya fito" har suka dawo dakin xa su masallaci ita bata ga Dr Sharif ya fito ba, Saleem yace "Wae bae fito ba har ynxu" kai ta gyada masa a hnkli, Saleem xae yi magana ya lura bbu wayoyinsa da Atm dake bedside drawer, bayin ya nufa da sauri ya tura ya ga wayam, still yyi a wajen, dae dae nn Dad ya shigo dakin, Saleem ya juya da damuwa fuskarsa yana kallon dad din yace "Dad, Aliyu yyi tafiyarsa fa" mikewa da sauri Afeefah tayi, dad ya kasa daina kallon 'dan nasa fuskarsa dauke da yanayi Mae wuyar fassara, Faisal ma baki ya bude da mmki yace "A condition din nn nasa ya tafi, he can collapse anywhere, shi sae kace ba likita ba hw will he do such, gashi bae bar drip din yyi ko rabi ba" Kuka Afeefah ta shiga yi a rikice, Dad da ya kasa cewa komae ya juya jiki a sanyaye ya bar dakin, Saleem ya bi bayansa hka ma Faisal. Layyukan Dr Sharif dad ya shiga kira ya ji su duk a kashe, hnklinsa ya tashi ssae, gnin xa a tada sllh yasa suka nufi masallaci da su saleem, Da kyar momy ta lallaba Afeefah ta tashi tayi alwala don kuka kawae take, dad na dawowa daga masallaci ya kira Ma'aruf, bae amsa gaisuwar da 'dan nasa ke masa ba yace "Aliyu na gidan ka ne?" Ma'aruf yace "Wani Aliyun dad?" Dad yace "Dr Aliyu" Ma'aruf ya girgixa kai yace "A'a dad rabona da shi tun jiya da yace xae taho gida" katse wayar dad yyi ya dafe kansa ya ma rasa tunanin da xae yi, to ina Aliyu ya tafi cikin daren, kiran Ma'aruf ne ya shigo wayarsa ya dauka Ma'aruf yace "Wani abu ya faru ne dad?" Dad ya sauke ajiyar xuciya yace "Ka taho gida ynxu Ma'aruf" yana fadin hka ya katse wayar ya ajiye, Momy ce ta shigo dakin damuwa dauke fuskarta ta xauna gefen mai gidan nata tace "Ynxu ya xa ayi wnn abun Alhaji?" Dad ya sauke ajiyar xuciya yace "Kai na ya kulle Khadija, Kinga shi ma halin da yake ciki ynxu"

Karfe takwas jirgi yyi set down a Aminu kano, da kyar Dr Sharif mike da taimakon mutumin gefensa suka fito daga jirgin, ba kadan ba mutumin ya tausaya masa ganin condition dinsa, yyi niyan su tafi asibiti daga airport din amma Dr Sharif ya ki, hkn yasa kawae ya sa shi taxi bayan ya gaya masa inda xa shi, dake gidansu sananne ne a Nasarawa me taxin bae tsaya sae an kuma maimata masa ba bayan gaya masa da aka yi a airport, yana isa kantamemen gate din gidan yyi parkin ya juya yana kallon Dr Sharif da idonsa ke lumshe yace "Mun isa yallabae" Dr Sharif ya bude ido a hnkli snn ya bude kofar motar ya fita don an riga an ba drivern kudi tun a airport, Drivern ya rakasa da "Allah ya sauwake" bae iya amsa wa ba ya nufi gate yana hada hanya ya shiga compound dinsu, gida ne me girman gske da ya kayatu da shuke shuke masu ban sha'awa ga parkin lot har biyu side by side, da ka ga gidan kasan naira sun xauna, ikon Allah kadae ya isa da shi babban falonsu, dai dai lkcn da wata kyakkyawar matashiyar mata da baxa ta wuce 48 ba ta shigo falon daga kitchen, da sauri ta karasa tsakiyar falon da mamaki ganinsa tace "Yaushe ka shigo Haiydar, amma..." Makalewa sauran maganganun nata suka yi gnin yanayin 'dan nata, a kidime tace "Meye hka Abba, me ya faru?" Rikesa tayi da sauri tana kallon fuskarsa gnin faduwa yake neman yi ta maxa ta xaunar da shi, duk ta rikice tana tambayarsa daga ina yake me ya faru, barin da taji xafin jikinsa, fadawa kanta yyi ya shige jikinta hawaye na sakko masa ssae yace "Wllh Ummi ina sonta, ina son Zainab, baxan iya rayuwa ba ita ba, kar ku bari a rabani da ita plss" sakin baki tayi tana kallonsa don its vry unusual of him ya bude baki yace yana son mace, rungumesa tayi ssae tace "Wae Zainab kke nufi Abba, wa yace xae raba ka da ita" k'asa bata amsa yyi sae hawaye, hnklinta ya tashi ssae don tasan daga kd yake.

Eeshatullah
[6/29, 06:19] Umar Dalha: 🌸👩🏻 'Ya mace Kyautar Allah👩🏻🌸

By Ashmaad

71__72
Teemah ce ta sakko falon xata shiga kitchen, kallo daya tayi masu ta nufi kitchen don idan da sabo ta saba ganinsu hka kai kace shi ne auta a gidan tsabar ynda yake ma Umminsa shagwaba, idan ya fita kuwa baxa ka ce xae yi hkn ba, don he is over gentle, tana isa kofar kitchen tace "saukan yaushe yayana" Ummi tace "Fatima xo kira Dadynku bae da lfya ne, kiyi maxa su taho tare da likita" da sauri ta dawo falon tana kallonsa ya runtse ido jikin Ummin sa har wani rawan sanyi yake, da damuwa tace "Me ya same shi Ummi," bata jira amsa ba ta nufi sama da sauri don dauko wayarta.

Ma'aruf ya rike kanshi bayan dad ya sanar da shi abun da ke faruwa, da kyar ya dago yace "Nasan da kmr wuya dad, yana sonta ssae," Dad ya sauke ajiyar xuciya yace "Ni ynxu nauyin kiran Alhaji Shariff nake, gashi wayoyinsa duk bae xuwa ina kke tunanin xae tafi" Ma'aruf yace "Kano xae koma, amma ka kira don a tabbatar dad" Dad yace "Ni ban iya kira ne, amma bari in sa Hajiyarku ta kira mahaifiyarsa koh?" Ma'aruf yace "Toh shknn" dad yace "Amma ya kke ga xa ayi Ma'aruf? Wae ina ma Aliyu?" Ma'aruf ba tare da ya kallesa ba yace "Ban sani ba dad" wayarsa ya dauka ya kira Saleem yace ya samesa falo, ba a dau lkci ba Saleem ya shigo, dad yace "Aliyu fa, kace xae xo da safe kuma shiru" Saleem yace "Wllh kuwa hka muka yi da shi, gashi ina ta kiran nmbobinsa basa shiga, na kira abokin nasa yace Bae kwana gidansa ba" Dad bae kuma cewa komae ba, Ma'aruf ya mike ya fita daga dakin, Saleem ya bi bayansa. Mikewa dad yyi cikin rashin kuzari ya nufi dakin mum, tana xaune ta sa Afeefah gaba ta ci abinci don kun cin komae tayi, tsaye yyi bakin kofa yana kallonsu, can ya juya ya fita, mikewa tayi ta bi bayansa don tasan magana xae mata, yana kallonta yace "Hajiya Hajarah xa ki kira ki ji ko Aliyu gida ya koma, snn sae ki kira Hajiya Zuwaira ki ji shi ma Aliyun ko gida ya wuce" Mum tace "toh bari in kira" yace "Ita kuma Zainab ta shirya, Ma'aruf ya kai ta airport ta koma gida xae fi," yana kai wa nn ya juya ya nufi falonsa. Ba a dau lkci ba ta shigo falonsa da damuwa tace "Ehh wae gida ya koma Alhaji sae dae ynxu hka wae suna asibiti" shiru kawae dad yyi yana kallonta, ta ci gaba tace "Shima Aliyun gida ya wuce a daren jiya, su ma kuma suna asibiti jikinsa ya tashi" Dad ya daga kai yana kallonta, ta girgixa kai tace "Da xa ka ji ta nawa Alhaji da kawae Zainab ta ci gaba da karatun ta har Allah ya fito mata da nagari, Amma kada ka ba ko wanne cikinsu" kasa cewa komae yyi ta mike tayi ficewarta, ba a dau lkci ba Ma'aruf ya shigo falon yace "Ynxu xan kai ta airport din dad ko sae anjima?" Dad yace "ka bari Gobe da safe ka kai ta, bata da nutsuwa ynxu" shiru yyi na dan lkci snn ya daga kai yana kallon dad dinsa yace "Dad a gani na da kawae kar ka ba kowa Zainab cikinsu don akwae matsala, kawae Allah ya fito mata da wani mijin nagari hkn xae fi" jin dad bae ce komae ba yasa ya mike ya fita.

Washegari Afeefah ta ji duk damuwarta ya dauke ganinta a kano, taxi ta samu ya kai ta har gida ta basa kudinsa snn ta fito tayi cikin gidansu da sauri bayan ta gaida mai gadinsu, Anty Safiya da Anty baby ta samu falo ko wannensu bbu wani annuri a fuska, Jiddah na kitchen tana wanke wanke, da gudu ta fada kan yayyin nata a dan sanyaye ta gaishesu, suka amsa suna tambayarta hanya da murmushin su, tace "Lfya lau, ina Mami fa?" Anty baby tace "Mami na sama, ya su dad da mum na Kaduna" tace "Suna lfya, wae in gaisheku" Jiddah ce ta fito daga kitchen tana kallonta, karasawa kusa da ita Afeefah tayi tana kallon idonta ganin ynda yyi ja alamar tayi kuka, da damuwa tace "Me ya faru Anty jiddah" Jiddah ta girgixa mata kai tace "Bbu komae, ya hanya" a sanyaye Afeefah tace lfya, snn ta nufi sama, dakin Mami ta shiga ta samu bata nn, ta fito ta shiga nasu dakin, Sadiya ce xaune da ganinta kasan tana cikin damuwa, Sadiya ta dan kirkiri murmushi tace "Zainab" Afeefah ta karaso da sauri da damuwa fuskarta tace "Anty sadiya me ya faru?" Sadiya tace "Bbu komae, yaushe kika iso" bata 6ata amsa ba tace "Mami fa" Sadiya tace "bata dakinta?" Mikewa Afeefah tayi da sauri ta fita, Adnaan ne ya fito daga dakin Aliyu, kallo daya yyi mata ya kara gaba abun sa, jikinta yyi sanyi ssae, dakin Aliyun ta nufa ta tura a hnkli, kwance ta gansa cikin bargo ya rufe har kansa, Mami na edge din bed din xaune rike da cup din tea alamar fiffitawa take, Mami ta dan mata murmushi tace "Har kin iso, ya hanya" murmushin ta mayar mata amma a sanyaye snn ta karaso cikin dakin ta gaisheta tana kallon Aliyu tace "Mami ashe yayanmu ya dawo, bacci yake ne?" Mami bata 6ata amsa ba, ta hau kan gadon ta xauna kusa da shi ta yaye bargon jikinsa tana kallonsa, ba karamin tashi hnklinta yyi ba jin temperature dinsa, da damuwa tace "Mami bashi da lfya ne kuma?" Ba tare da Mami ta kalleta ba tace "Ehh, kar ki tashe sa" hawaye ne ya cika idonta ta daura hannunta a goshinsa a hnkli tana kallon kyakkyawan fuskarsa da yyi haske ba kadan ba lebbansa yyi ja ssae, lkci daya ya bude rinannun idanunsa jin hannu a goshinsa ya daura kan nata, ganinta yasa ya mike xaune da sauri yace "Zainab" shigewa jikinsa tayi hawayen idonta ya gangaro a hnkli tace "Har ynxu baka da lfya ne yayanmu?" Girgixa mata kai yyi ya rungumeta ssae, ya runtse ido cikin sanyin murya yace "Na fara jin sauki little sis, flight kika bi?" muryarta na rawa tace "To ni na ji jikin ka da xafi ssae ae" a hnkli yace "Na sha magani ne" bata kuma cewa komae ba tayi lamo jikinsa tana jin irin ynda xuciyarsa ke bugawa kmr xae fito, duk wnn abinda suke Mami bata kalli inda suke ba sae fiffita tean hannunta take a hnkli, can ta ajiye cup din tea'n ta mike ta fita daga dakin. Daga kai Afeefah tayi tana kallonsa ta ga idonsa a lumshe, lkci daya ya budesu yana kallonta shi ma ya sakar mata murmushi, da damuwa tace "Yayanmu ina ke maka ciwo?" Kirjinsa ya nuna mata kawae, ta xame jikinta daga nasa ta sakko daga kan gadon ta dauki cup din tean da Mami ta ajiye ta dawo gabansa tace "Ga shi yayanmu ka sha, sae Ka kara shan magani koh" ba musu ya karba ya kai baki ya shiga sha a hnkli, tayi tagumi gefensa tana kallonsa har ya sha fiye da rabi snn ta karbi cup din tace "Ka koshi yayanmu" kai ya gyada mata yana goge bakinsa, ta shanye sauran snn ta ajiye cup din tace "Kayi wanka yayanmu?" Girgixa mata kai yyi, ta mike tace "Bari in hada ma ruwa" bin ta yyi da kallo har ta shige bathroom, bayan 'yan mintuna ta dawo tace "Na hada maka ruwan yayanmu" mikewa yyi ya sakko daga kan gadon a hnkli snn ya cire rigan sanyin jikinsa tana kallonsa ta ga ya rame ba kadan ba, milk jallabiyan jikinsa ya cire ya rage masa singlet da 3 qtre ya nufi bathroom kmr me counting steps dinsa don tun jiya bae iya tashi, sae gashi ynxu ko jirin bae gani ba, cups da plates din dake dakin sae cans din malt da robobin drip duk ta kwashe ta fita daga dakin ta sauka kasa, har lkcn yayyinta na xaune falo, duk suka bi ta da kallo ta shiga kitchen ta ajiye cups da plates, cans din malt kuma ta xubar cikin shara snn ta dawo falo, Anty Safiya ta kalleta tace "Ya tashi ne?" Afeefah tace "Ehh ya tashi" Anty baby tace "Ke kika shanye tea'n cup din" girgixa Kai tayi tace "A'a shi ya sha ya rage kadan" shiru suka yi duk suna kallonta, ta juya ta koma sama, bedroom din ta shiga gyarawa ta canxa bedsheet snn ta sauka kasa ta dauki sweeper ta koma ta share dakin tayi tidyn din shi duk da fez dakin yake, tana kkrin kunna burner ne Mami ta shigo dakin, gadon ta kalla kafin tace "Ina Aliyun?" Afeefah tace "Wanka yake yi" shiru Mami tayi ta kasa cewa komae, can tace "Tea'n fa?" Afeefah ta ce "Ya sha na kai cup din kitchen" da mmki Mami tace "Ya sha da gske?" Afeefah ta gyada kai, Mami bata kuma cewa komae ba ta juya a sanyaye ta bar dakin, Anty baby da Safiya ne suka shigo dakin su ma, Anty baby ta kalli kan gadon tace "A'ah Ina yayan namu" Afeefah tace "wanka yake yi" Anty baby tace "Da gske?" Kai kawae Afeefah ta gyada mata, Anty Safiya tayi murmushi ta juya ta bar dakin, hka ma Anty baby, kananan kaya Afeefah ta fito masa da ta ajiye gefen gado, dai dai nn ya fito ta juya tana kallonsa tace "Yayanmu kayan nn yyi maka" Shiru yyi ya kasa bata amsa tuna da da yyi, kusan kullum ita ke fito masa da kayan da xae sa tun tana k'an k'anuwarta, Karasowa gabansa tayi tana kallonsa a hnkli tace "Yayanmu!" Firgit ya dawo da sauri yace "Yyi mana little sis" tace "To ka sa kayan bari in wanke bathroom" bin ta da kallo yyi har ta shiga bathroom din duk da ita ma jikinta yyi sanyi, Aliyu ya isa bakin gado da kyar ya xauna ya rike kai sae ga hawaye, me yyi ma Mami xata yanke masa danyen hukuncin nn hka, don me baxata yi la'akari da ynda ya rainan mata Zainab ba har ta kai matsayin da take ynxu, tun Zainab na cikin tsumma yake wahala da ita har goyonta ya sha yi, ta kuma yi bacci a bayansa, tun tana karamarta bbu wanda take yrda da a gidan bayan Mamin sae shi, komae shi ke mata, ya kuma fi fiffita ta kan wa enda suke uba daya, kwata kwata bae san laifinta a gidan har yau har gobe, me yyi ma Mami da xata yi masa hka, tamkar uwar da ta haifesa a cikinta ya dauketa, hawaye ssae yake, gnin numfashinsa na yin sama kmr jiya yasa ya saita kansa, ya kusa minti goma kafin ya dan dawo nml ya tashi da kyar ya saka kayansa snn yyi kwanciyarsa kan gado ya lumshe ido.

Afeefah na gama wanke bayin ta fito tana kallonsa, gnin idonsa a lumshe tayi tunanin ko bacci yake ta fita daga dakin, dakinsu ta nufa lkci daya Dr Sharif ya fado mata, duk sae taji damuwar ta ya dawo, tana jan kafa ta shiga dakinsu, ta samu Jiddah da Sadiya xaune dakin, gefen gado ta xauna tace "Su fadila fa?" Jiddah tace "Sun tafi sch" Afeefah tace "Abbana fa?" Sadiya tace "Daxu ya tafi abuja" kwanciya tayi ta juya masu baya, Sadiya ta dawo kusa da ita tana kallonta a hnkli tace "Afeefah" mikewa Afeefah tayi tana kallonta, Sadiya ta kwantar da murya tace "sbda me kika ce baki son yayanmu" kallonsu Afeefah ta tsaya yi lkci daya mood dinta ya canxa, a sanyaye Jiddah tace "Baki masa hallaci ba Afeefah, duk irin son da yake maki ki rufe ido kice baki son sa" mikewa tayi hawaye cike idonta tana kallonsu tace "Kmr ynda bbu xancen aure tsakanin ku da shi, to nima bbu, don a matsayin Yayan da muka fito ciki daya na daukesa, don hka ku kyaleni" tana kai wa nn ta fice daga dakin hawaye na bin kuncinta, dakin Mami ta shiga ta sameta xaune tana waya, ta fada kan gadonta ta shiga rera kuka a hnkli, Mami ta kammala wayar ta juya tana kallonta da mmki tace "Me ya faru?" Cikin kuka tace "Ko ba su Anty jiddah bne suke min magana wae me yasa nace bna son yayanmu, ni kice masu su daina min irin maganan nn bna so, don matsayin yayana na daukesa kuma ni ba aure tsakaninmu" Mami bata ce komae ba sae danna wayarta kawae take amma da ganinta kasan jikinta yyi sanyi, mikewa tayi ba tare da ta tanka ta ba ta fita daga dakin, Afeefah ta ci kukanta daga karshe bacci ya dauketa.

Karfe biyar saura na yamma Afeefah na daki kwance ta tsura ma Tv ido, tun bayan maganar da su jiddah suka mata daxu taki komawa dakin ya Aliyu, har abinci bbu ynda Mami bata yi da ita ta kai masa ba tace ita kanta na ciwo, duk da ma bacci yake tayi bayan fitarta don sae lkcn ya samu bacci. Fadila ce ta shigo dakin tace "Ya Ma'aruf ya xo" da sauri Afeefah ta mike tace "Da gske," bata rufe baki ba ya shigo dakin, murmushi tayi tace "lah Ya Ma'aruf" ya mayar mata murmushin yace "Kina ta bacci ko kasa" murmushi ta kuma yi tace "wllh ba bacci nake ba kallo nake, ya su Fadil" yace "su Fadil na gida, ya jikin yayanku" ta sunkuyar da kai tace "Da sauki," yace "na shiga yana ta bacci, bari in je in dawo" tace "Ina xa ka ya Ma'aruf?" Yace "Gidansu Dr Aliyu xan tafi, bashi da lfya" mikewa tayi sa sauri tace "Don Allah ya Ma'aruf mu je tare" kmr xata yi kuka ta kare maganan, yace "Ae Mami baxa ta yrda ba," hawaye cike idonta tace "Ka tambayar min ita plss yaya" ya dan yi shiru snn yace "To ina xuwa" ya fita daga dakin, Hijab dinta ta dauko da sauri tana Addu'ar Allah yasa Mami ta yrda, ba a dau lkci ba ya dawo yana kallonta yace "Mami bata yrda ba, idan naje I wil extend ur greetings kin ji" bata sauraresa ba ta fice daga dakin xata dakin Mami har hawaye ya cika idonta, yyi dariya yace "Ke wasa nake maki, ki je ki sallameta ina jiran ki a waje" dan murmushi tayi ta sa hijab dinta snn ta nufi dakin Mami, ta sameta ita kadae, ta durkusa gefenta tace "Mami xan raka ya Ma'aruf" Mami tace "Ya gaya min amma kada ku dde Zainab, ku yi masa sannu, Allah kara lfya" mikewa tayi tace "To Mami" snn ta fita daga dakin, Su Anty Safiya dake girki a kitchen tayi ma sallama, suka ce "Ina xa ki?" Tace "Ni da ya Ma'aruf xamu fita xan rakasa ya duba..." Hararan da suka watsa mata yasa ta yin shiru, Anty baby tace "Maxa ki je

Please Login or Register in order to submit comment