Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata kofar rago suka ritsata a tsakiya turus tai ta tsaya tana huci yar sanda da aka zo da ita ce ta karasa tare da danko ta dayar tasa mata ankwa kokawa suka fara sai harbe harbe Ramatu take da 'kafa tana burgima da fisge fisge "ku sake ni azzalumai mugayen banza" make mata baki 'yar sandan tai wanda yasa Ramatu sakin kara tana cewa "wayyo Allah na zaluncin yan sanda Allah ya isa ban yafe ba tsinanniya kin make uwark............ Sake make mata baki tai saiga jini cikin tsawa tace "rufe mana wannan ru'babben bakin zaki bayani yau saikin gane Allah da girma yake wallahi bari mu karasa bayan kantar zaki yabawa aya za'kin ta" har lokacin bakin Ramatu bai mutu ba ta harari yar sandan tana cewa "babu abinda kika isa kimin harda bari muje bayan kanta idan kin cika yar halak idan an kulle ni ki dau dan mubud'in kije ki jefa shi a kogi mai ambaliya kaina fito har abada" "shikenan zaki gani zuwa jimawa saikin manta inda kike wahala sai tasa kinje suma kin dawo" yar sandan na fadin haka ta jawota zuwa inda motar su take guri ya cika dam sai nuna ta ake ana gulmar Mamman ne ya d'ebo mata 'yan sanda wulla ta sukai a mota suka tafi sai ihu da tsine tsine take wani d'an sanda yana shirin bugarta da kulke ogonsu ya hana shi cewa ya bari idan sunje can wuya zatasa tai shiru.

Duk abinda ake Ilyah na ji yai banza a cewarsa itace ta jawo rigima ba inda zaije belinta kud'in sa ko biyar bazai ciwon kaiba saidai a sayar da tumakinta a belota amma indai dan ta shine tai ta zaune a bayan kanta😲😦.

Aiko suna zuwa suka hau jibgarta ihu kamar zata fasa ofishin cikin tsawa suka ce "rufa mana baki tunda ke kin zama annoba zamuyi maganinki a garin nan ba me gari shugaban ku ba amma kin raina shi bakya ganin girmansa bari yazo zaki bayani ba ke tantiriya ba"? Ramatu na haki ga gumi jikin ta ya ji'ke tace "a'a wallahi yalla'bai ban raina mai gari ba dan Allah kuyi hakuri na tuba" cigaba suka da tambararta zuwan ogansu yasa suka dakata kallon ta yayi yana Jinjina kai kafin yace "ku 'kyale ta haka ku fito nayi magana da me garin yace gobe zasu zo da mutanen da suke 'kararta" fita sukai suna rufeta Ramatu dake kwance da'kyar ta tashi zaune tana cewa "Allah ya isa na mugaye ban yafe muku ba wallahi kuma halina na nan babu abinda za'a fasa rashin mutunci bakuga komai ba yanzu na fara" ta fad'a tare da gyara zama tana kalle kallen gurin babu komai sai 'kura da datti haushi ne ya kamata ta sake 'kudura a ranta bazata yarda ba saita rama duk shegen dayai silar zuwanta nan.

Washe gari mai gari da sauran wadanda sukai 'karar Ramatu sukaje ofishin fito da Ramatu akai duk ta jigata harda kumbura a fuskarta na dukan da sukai mata jiya kallon su take daya bayan daya kafin ta zauna tana cewa "munafikai matsiyatan banza me kuma ya kawo ku ai na dauka zakusa su kashe ni ne ashe iya duka ne" kallon ta da mamaki mai gari yayi yana cewa "amma wallahi ke dai Ramatu kin shiga uku ke wacce irin mace ce wato kawo kin ma da akai baki risina ba"? Wani irin kallo Ramatu ta wurga masa "au dama kun kawo ni a koya min ladabi to Babu abinda zai sauya ko yanzu na koma gida wani bankad'adden ya ta'bo ni sai naci 'kashin uban sa" kai me gari ya jinjina "bari ofisan yazo tunda kin zama shed'aniya" "eh fad'i ka 'kara idan kace shed'aniya ai ka 'bata daya kenan saidai kace shed'aniyas kaga da yawa kenan" "zan sanar masa duk abinda kike aikata mana a gari" "ka dade baka fada masa ba ofisan banza ofisan wofi yazo man tsoron sa nakeji nafi karfin wulakanci ni roba ce ina daidai da 'kugun kowanne shege....................

Jin tafiyar ofisa yasa sukai shiru zama yai ransa a had'e yace "ina jinka malam Rabi'u meya faru tsakaninka da wannan matar"?.

Gyara zama mai gari yayi yana cewa "ofisa kaga wannan matar da kake gani a rayuwar ta bata son zaman lafiya ta hana kowa yaji dad'in zaman garin ta addabe mu ranar kawai daga kawo min ita shari'a saida tai min zagin 'kare dangi sannan ta tozarta yan majalisa ta su Isubu tayi musu zagi na tsamar nama" mi'kewa Ramatu tai "to yau nake ganin sabon salon sharri me gari ni zakaiwa sharri amma Allah ya isa tsakani na dakai" tsawa officer ya daka mata yana cewa ta koma ta zauna zama tai jiki na 'bari.

Kallon sauran officer yai yana cewa "ku kuma meye tsakanin ku da ita"? Mamman ne ya soma magana "ranka ya dad'e ni kuma haka kawai wannan matar taje har gidana ta rufe yarana da duka babu dalili ta zagi mata ta" kallon d'ayan ofisa 'kai kuma meya faru"? "Ranka ya dad'e ni ma zuwa tayi har gida ta daki Balki yata ta 'kare min zagi tas" "ni kuma kud'i nake binta dubu goma sha biyar ta hana ni kusan wata shida" "nima yalla'bai kud'i nake binta ta hana ni" kowa da abinda yake cewa duk guri ya kaure d'aga musu hannu ofisa yayi yana cewa "ke kinji abinda suka ce haka ne"?.

Kai Ramatu ta girgiza "a'a ba haka bane ni babu wanda yake bina kud'i nuna mamamn tai "sannan shi wannan munafikin ba a banza na d'aki yarsa ba kullum 'ya'yansa sai sun tare 'yata Lami sunce mata jahila kuma saini dan na dake su aga zafi na saboda 'yata bata da gata su kuma 'ya'yan gwal ko"?.

"Kinga da Allah saurara bana son shashanci dama halin kine ba sau daya aka kawo ki ofishin nan ba kin zama kamar kwastoma dan haka duk abinda sukace zaki iya aikatawa dan haka bazaki koma garinku ba saikin biya kud'in da ake binki da kud'in belin da tarar dukan da kikaiwa 'ya'yan wannan mutumin".

Zaro ido Ramatu tai tana cewa "kan dambun uban nan wallahi ba wanda zan biya ko sisi ofisa baka da adalci ko kadan" mi'kewa ofisa yai yana cewa "zaku iya tafiya na gama magana idan an samu mai zuwa belinta saiku dawo" suma mi'kewa sukai yayin da aka tisa 'keyar Ramatu aka mayar da ita bayan kanta su me gari suka koma gida suna mamakin wato babu inda bakin Ramatu zai mutu ba.

Kwanan Ramatu shida a rufe babu wanda ya leka yaga kalau take balle ace za'a je belinta saida dan uwanta ya dawo daga neman kud'i yaji labarin tana can a tsare sannan yahau mashin yaje akai shari'a ya biya kud'in suka taho yana mata fadan ta girma amma har yanzu ace bata da hankali itakam jinsa take a banza idan maganar ta shiga ta kunnen dama saita fita ta kunnen hagu.

"Kina jina Ramatu kikai shiru ko"? Hashimu ya fad'a yana hararar ta ta'be baki Ramatu tai "to me kake so nace hashimu" "ban sani ba wai Ramatu yaushe zaki hankali d'abi'ar ki kamar ba ta mutane ba"? "Au kana nufin ni dabba ce"? "Ni bance miki dabba ba inda sharri kike neman yi min gaskiya ki canza halinki haba rahma da girman ki kina abin yara ko yara bazasu buwayi gari haka ba indai sun san me suke".

Murgud'a baki tai tana kawar da kai daidai sun iso dabar mutanen gari ta tsakiyar dandali ganin idon kowa a kanta yasa ta soma masifa "to mayu meye kuka zuro min ido kowanne tsinanne yana kallo na ina munafikan da sukai karata to gani na dawo ban tabbata acan ba kuma ko yau rigima ta sake hado mu babu fashi saina ci uwar mutum na jajjaga ubansa a turmi.............

Katse ta Hashimu yai "wai dan Allah me kike haka wannan fa zubda girma ne gaban yara da manya kina matar aure harda d'a saurayi kina irin wannan abun" itama caraf tace "kai ka 'kyale ni saina fad'i abinda ke raina ko zuciya ta tayi sanyi idan na bari ni abun zai dama, kuna jina ba'a haifi wani shege a garin nan wanda ya isa ya ta'bo ni na rabu dashi ba ni bala'i da yake bacci ma Saida na tashe shi ni mace ce mai had'ari ku kiyayeni" 'bacin rai ne sosai ya kama Hashimu cikin fad'a yace "amma dai Ramatu kinyi asara kinji kunya wallahi har bansan yadda zan kwatanta miki ba saidai kawai nace Allah ya shirye ki" ganin zata magana yasa yace "bansan jin komai muje" wucewa sukai Ramatu na dawo da hannunta baya ta ware su alamar duk wanda yai zancen ta uwarsa.

Suna zuwa gida Hashimu ya hauta da fada a gaban Baffah yana cewa "mai kake kallo har Ramatu ta zama irin haka? Wato bata jin maganar ka ta rainaka bata da mafad'i kinga Ramatu kibi duniya a sannu".

Shiru Baffah yai yana kallon Ramatu zuciyar sa na suya yana matukar nadamar aurenta a rayuwa saidai kaddara ta riga fata zuwa shikam yanzu Ramatu tafi karfin sa babu abinda zaice mata sai Allah ya shirye ta, tunanin sane ya dawo jin hararramin yayan Ramatu Hashimu yana kai mata bugu da gudu tayi d'aki tsaki yai yana cewa "kana jinmu da mara mutuncin nan ko Baffah"? Sauke ajiyar zuciya Baffah yai "to me zance Hashim bani da abin fad'a fatana Allah yasa ta gane da wuri ta gyara kafin lokaci ya 'kure mata" juyawa Hashimu yai yana shirin fita yace "to ai shikenan Allah ya sauwake mata idan masifa ce sai anjima" da kallo Baffah yabi bayansa kafin ya kalli kofar d'akin Ramatu yana girgiza kai ciki damuwa ya mike yana ficewa daga gidan itakam Salamatu har ta daina mamakin abinda Ramatu take yanzu tafi tunanin kila Ramatu ba ita kadai bace akwai mutanen 'boye a jikinta.

Tun daga ranar da Ilyah ya samu goyon bayan Ramatu cewa basai kara taimakawa Baffah da aikin gonna ba sai Ilyah ya kangare ya koma bin abokai 'batattu wanda iyayensu suka sangarta su har suka koya masa munanan d'abi'u ciki harda sata da shan taba sukan rufe fuska dan kar a gane su idan yara yan mata sun tafi gona su tare su wacce tsautsayi ya fad'a kanta suyi mata fayde anyi shari'a dasu yafi sau a kirge yan sanda har sun gaji da kawo case din su ba irin azabar da basuyi musu ba amma sunki dainawa kamar kara zugasu ake har zaman gidan maza sunyi.

Lokacin kaka ma haka abun ya faru daga Baffah sai Sabi'u da Habu sukai aikin komai Ilyah ko tsinke bai dauka ba amma adalci irin na baffa daya tashi musu dinki tare ya basu ladan gona baya bambanta musu gudun rabuwar kai sai wannan shekarar ne ya zarta akan Ilyah ko kunya haka Ramatu ta rufe ido ta ri'ka zazzagawa Baffah magana wai yaji tsoron Allah dan kawai bana daya Ilyah bai masa aiki ba shine yabi ya tsane shi Baffah ci kanki baice da ita ba data dame shi ma tashi yai ya barmata gidan.

Alhamdulillah Lami ta soma karatu cikin sa'a gata da kokari sosai kuma ko kadan bata tunanin gida balle ace ta damu kawai karatun ta take saida akai jarrabawa ta kar'bo result dinta sannan Musbahu yai tunanin kaita gida taga iyayenta da danginta yasan duk tsiya yanzu kam Ramatu ta hakura ta risina bazata hana ta karatu ba ganin yadda ta dawo tayi kyau da kiba ta koshi abinta.

Suna zaune a d'aki Lami da Naja'atu suna hira mama ta shigo tana cewa "ku kam bakwa gajiya da zaman d'aki kamar munanan amare" dariya sukai Naja'atu na cewa "mama labari take bani wai tayi saurayi d'an makarantar su sunan sa Alpha shine nace zamu sha biki" bud'e baki mama tayi ita kuma Lami ta rufe ido tana cewa "mama ba haka nace mata ba sharri zatai min ba cewa yai yana sona ba kawai mutunci muke" dariya mama tay "eh ai na sani basai kince komai ba babanku yace ki fara shiri nan da sati zamuje garin ku ki gano iyayen ki" 'yar fara'ar dake fuskarta ce ta 'bace tana kallon mama jiki a sanyaye tace "to Allah ya kai mu" haka nan taji lokaci guda hankalin ta ya tashi bata tunanin kowa sai Ramatu.

Ganin yanayin ta yasa mama cewa "Lami meke damunki naga kamar canjin yanayi"? Kaita girgiza "babu komai" "shikenan to zakuje da Naja'atu ayi miki lalle da kitso" "to mama" mama na fita naja tace "aiko sai anje dani saina gano garin ku" murmushin dole Lami tayi gabadaya ta kasa sukuni batasan meyasa amma haka nan taji bata son komawa.

Washe gari suka gama shiri tsaf suka dauki hanyar 'kauye har suka isa garin Lami bata Sani ba kanta na sunkuye tana faman tunani da sa'ka da warwara saida taji mota ta tsaya sannan ta d'ago gabanta ya fad'i ganin Ramatu ta fito amma abinda daya bata mamaki ko kallon inda motar take batayi ba tai gaba abin da gyalenta mai datti kafarta ko takalimi shi kansa Musbahu bai manta da Ramatu ba amma yayi mamakin ganin ta kallesu sau daya ta kawar dakai tai gaba abinta.

Fitowa sukai suna shiga gidan Baffah na kofar d'akin sa a zaune gurin sa suka nufa suna zama shi kansa yayi mamaki sosai da annuri a fuskarsa yace "Musbahu kaine? Banyi tunanin ganinku ba sannu kuna tafe kaida iyalin"? Murmushi Musbahu yai yana gaida Baffah matarsa ma ta gaida dashi tare da yaranta.

"Ke Salamatu kawowa ba'ki ruwa da abinci yanzu" fitowa Salamatu tayi tana d'ebo ruwa tayo wajensu tana ajewa da tabarma ta zauna suka gaisa tana ta kallon Lami ba Salamatu ba hatta Baffah yanayin yadda yaga Lami tayi girma da kiba ya bashi mamaki.

Suna haka Ramatu ta dawo bata kuma kallon inda suke ba ta shige d'aki harda wa'ka itakam mama da batasan dawar garin ba batai tunanin ma wata Ramatu bace uwar Lami ta dauka Salamatu ce saida zance yai nisa sannan ta fahimta anan Musbahu ke cewa Baffah su zasu tafi amma Lami ta zauna tunda yanzu ba makaranta idan an basu hutu sai yazo ya dauketa.

"Kai Baffah ya jinjina yana cewa "naji zancen ka Musbahu kuma nagode sosai Allah ya kara arziki Allah ya kiyaye hanya ya kaiku lafiya ka gaishe min da mahaifin naka" mi'kewa sukai Musbahu na cewa "to shikenan Baffah zamu tafi" mi'kewa shima Baffan yai zanyi musu rakiya shida Lami a hanya yana sake mishi godiya saida suka tafi ya dawo gida Lami zata zauna a gurin sa yace "a'a tashi maza ki shiga ku gaida da babar taki man ki bata hakuri kinji" kai Lami ta d'aga tana mi'kewa ta shiga d'akin Ramatu ganin ta tayi zaune har lokacin wa'ka take rerawa mamaki ne ya kama Lami yau Ramatu ke wa'ka kamar maro'kiya karasawa tayi tana cewa.

"Babah" d'agowa Ramatu tai tana kallon Lami zuwa wani lokaci tace "uban me ya kawo ki gurin na? Shiru Lami tayi Ramatu taci gaba "ai na dauka har abada a gunsa zaki tabbata tunda kin za'bi zama da wancan tambad'addan😲 saidai ki samu wata uwar daga yau amma badai niba".

Hawaye ne ya ciko idon Lami tana kallon Ramatu tace "dan Allah kiyi hakuri..................

Da yatsa Ramatu ta nunata "ke kada ki sake bani hakuri kinsan da hakurin kika za'bi zabin ubanki saboda kin maida ni sako tumaki 'ballo jakuna baki san wacece Ramatu amma yau zaki sani fita min a d'aki" kuka Lami keyi tace "dan Allah kiyi hakur.................

Bata karasa ba Ramatu ta bud'e kasan gado tana dauko sungumi ta mi'ke tsaye tare da cewa "dan ubanki kin dauke ni mutuniyar banza ce zaki fita ko saina rad'e ki" nufota tayi da gudu Lami ta fita a d'akin Ramatu ta rufa mata baya har gaban Baffah tana cewa "uban naki ma bai isa hani na karya miki 'kafa ba tunda kin za'bi kibi son ran ubanki na fad'a miki saidai ki nemi wata uwar" ta karasa maganar tana juyawa da sunguminta kuka sosai lami keyi ta durkusa a gaban Baffah tana cewa "dan Allah Baffah ka fahimtar da ita tayi min afuwa ita fa mahaifiya tace bazan iya jure fushinta a kaina ba hakan barazana ne ga zuciya ta da nasan abinda zai faru kenan bazan bishi ba zanyi ta hakuri ina zama cikin duhun jahilci naπŸ˜”.

Kallon ta Baffah keyi cikin tausayawa da rashin jin dad'in ganin yadda take kuka kamar ranta zai fita ya shiga jin wani irin d'aci na masa yawo a makoshi kirjinsa na zafi a fusace ya mi'ke yana zuwa kofar d'akin Ramatu yace "ke Ramatu kina ina? Caraf Ramatu ta bankado labule tana cewa "ga yar mutum biyu jikar mutum hud'u me ya faru ake nema na"? Ran Baffah a 'bace yace "kinsan Allah Ramatu ranki zaiyi mugun 'baci akan yarinyar nan sam babu d'igon imani a tare dake saikin kashe ta da 'kuncinki da kike sanya ta ciki to bari kiji yau kam kin kaini bango kibi a sannu zan iya yin komai".

Shewa Ramatu tai "ahayye nanaye yau ake yinta tofa ran maza ya 'baci lallai malam wato nan din me kake son nunawa zakasa nayi abinda banyi niyyar yiba Lami ce nace na sallama ta yadda ta za'bi tabi bare to yanzu ma haka ta dauka baren ya fini ta koma gunsu nace babu ni babu ita har raina haka abin yake babu kuma wani abu da zai canza".

"Haka kikace ko Ramatu"?.

Tana kad'a kai kamar zata hau bori tace "eh nace hakan malam, meye ko kana tunanin zanji tsoron kane? Nasan karshen abun bazai wuce kace zaka sake niba kuma ni yanzu dama haka nake so na samu 'yanci na nayi yawo a gari naci uban kowa na taka na murshe na wanke biyar na tsoma goma na fantama duk inda raina yake so" shiru Baffah yai na d'an wani lokaci kafin ya juya yana kallon Lami da har lokacin take kuka yace.

"Ramatu idan har baki yafewa Lami ba nima bazan ta'ba yafe miki abinda kikai min ba a rayuwa zaki ga karshen ki shiyasa nake miki kashedi tun wuri ki tuba ki canza kafin lokaci ya'kure miki".

Yana juyawa Ramatu taja tsaki tana cewa "wa'azi da zaka gane da ka dena dan wallahi babu abinda zaka fad'a min yai tasiri a raina ko yasa na sauko daga halina har abada muje zuwa koni ko kai".

Baffah babu yadda ya iya haka yayi ta lallahin Lami da fad'a mata magana me dad'i har yayi sa'a ta daina kukan ta saki ranta suka fara d'an zance yana matukar jin kaunar yarinyar da tausayin ta a ransa yana ganin bai kyauta mata ba daya auri Ramatu ta kasance uwa gare ta duk saiya tattara laifin ya dorawa kansa.

Satin d'aya da dawowar Lami aka daura auren Tanko tayi kuka ta kara harta gode Allah domin a dandali a gaban mutane yaci mata mutunci yace tabi son zuciya da kwadayi ta za'bi zaman wudil a kansa yanzu ya cireta a shafinsa lokacin da Ramatu taji harda dariya haka ta tusa Baffah a gaba da baka'ken maganganu wai ga abinda ya jawo nan batai karatun arziki ba ga wanda take so yayi aure yanzu a saiya ji'ka ta yasha.


Wudil zaune Naja'atu take tare da wani saurayi suna hira da murmushi a fuskarsa yace "wai nikam ba kuyi magana da Lami ba sai yaushe zata dawo nifa ina kewarta sosai duk na shiga damuwa" itama murmushin tayi tana cewa "hum Alpha kenan kaifa ina jin Lami bazata dawo ba domin dam bada amincewar mahaifiyar ta tazo ba inaga ta koma garin su da zama".

"Da gaske kike Najat"?

"Wallahi da gaske nake Alpha zanyi maka wasa da tunani ne".

"To amma wayar dana bata fa idan na kira bata shiga kullum a rufe me yasa"? "Oh ai dama bata tafi da ita ba tana gidan mu sai bayan tafiyar ta ina gyaran d'aki na ganta" dafe kansa yayi yana cewa " to yanzu idan zan ganta ya zanyi garin zaki raka ni ko kuwa? Gaskiya ina son ta da aure ba yaudara ba shin zaki iya taimaka min"?.

Murmushin jin dad'i naja'at tayi tana cewa "me zai hana ni kaina alpha ina son zaman Lami a kusa dani mun riga mun saba bana jin dad'i yanzu da bata nan".

"Ok shikenan karki damu zanyi magana da abbanku duk abinda yake akwai zaki ji" "to nagode sosai alpha" mi'kewa yayi yana mata sallama itama ta mi'ke suka fita tare kowa ya wuce gida.

MRS AL'AMEEN AHMAD CE 😘

Sai mun sake had'uwa a gaba masoya na masu yabo gareni godiya πŸ’–πŸ’•πŸ’š sosai sosai godiya.

Think before you do 🀨.

#Vote
#comments
#share
#fallow.

[email protected] MAMAN LITTLE ZARAN AUNTY πŸ’ƒπŸ‘ŒπŸ‘.

YUSRAHMS ABUBAKAR.

21~AL-BASIT
The extender
22~AL-KHAFID
The abaser

11~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Sajidinah.
🌹πŸ₯€πŸŒΉπŸ₯€πŸŒΉπŸ₯€πŸŒΉ

πŸŒ„DISCONTENTπŸŒ„
Episode 21 nd 22
Wata daya tsakani Musbahu da baban alpha suka zo nemawa masa auren Lami Baffah yayi farin ciki yayi godiya ga Allah ya kara yayi addu'a da fatan alkairi da sanyawar albarkarsa da samun zuriya ta gari sannan ya ro'ki Baffah akan zai tafi da Lami su Naja'atu sun damu ta koma tunda hutu ya rage saura sati daya a koma Baffah kuwa dad'i yaji a take yace ta dauko kayan ta su tafi itama Lamin taji dad'i sosai da sauri kuwa ta had'a komai bata ta shirya ta bisu suka tafi.

Bayan tafiyar su Ramatu ta dawo batasan me ake ba hakkinta na uwa itama dole ya fad'a mata tasan abinda ke faruwa bazai biye halinta ba zata wuce yace.

"RAMATU" da sauri ta waigo ganin kaya turus a gaban Baffah yasa ta washe baki tana cewa "na'am malam gani nazo ne"? "Eh magana zamuyi" kamar an jefota yaga taxo ta zauna tana le'ken babbar ledar dake gaban sa yace "to malam gani nazo in kaji kira an samu amma banda kiran dan sanda".

Shiru Baffah yai yana kallon ta ganin baice komai ba tace "malam ka kira ni kuma kayi shiru"?.

Sauke ajiyar zuciya yai yana cewa "ina fata yanzu kam zaki fahimce ni duk da nasa ke baud'addiyar mace ce wacce ba'a gane inda al'kibilar ki take amma ya zama dole na fad'a miki yau dazu bayan fitar ki Musbahu yazo tare da wani mutum wanda d'ansa yake son Lami sunzo nema masa aurenta kuma na basu duk da banyi shawara dake ba amma ya kika ce kema mahaifiyar tace kina da hakki a kanta ga dai kayan da suka kawo nan da kud'i".

Zaro ido Ramatu tai gani kud'i daure a kyaure dami guda baki washe tayi tana cewa "ayya malam ai bakai laifi ba meye a ciki basai kai shawara dani ba ai kaida kaya mallakar wuya ne" ta karasa maganar tana dauko 'kwallelan goro daga cikin ledar ta soma garza tana cewa "yaushe zasu sake dawowa ne nifa ban gane cewa mutumin nan yana son Lami ba saiyau kace gara daya dauke ta suka tafi gashi harda abin arziki ta samo saurayi d'an birni" kai Baffah ya jinjina lallai kam wato idan akace mutum nada son zuciya sai a hankali yayi mamakin ganin yadda Ramatu ta amince Shi dai farin cikin sa daya Lami zata bar kauyen nan taje ta zurfafa karatun ta tayi ilimi ta cika burinta.

"Malam me kake tunani"? Ramatu ta fad'a tana sake cewa "malam aban nawa kason zan rabawa dangi" .

Cikin mamaki Baffah yace "kason me"? Kud'in dake gefe ta nuna tana cewa "garin su Mariya zanje in an jima nasan kayan lambu sunyi na saro Lami ta fara min talle" "telle kuma"? Baffah ya fad'a yana kallon ta "eh talle saita tara kud'in da za'a saya mata yan kayan d'aki da kayan katako" "a'a indai dan wannan ne ki barshi ni zanyi mata komai".

Daina cin goron Ramatu tayi bakinta daya sauya kala zuwa ja ta bud'e shi tana cewa "amma dai malam zilama ce tasa kace haka"? Wani kallo Baffah ya mata tare da maimaita kalmar "zilama"? Ba kunya Ramatu tace "eh zilama nace kake dashi malam bada zilan zilan irin taka ba da had'ama taya zakace kaine zakai mata kayan d'aki dan karka bani ko sisi shine kace wani kaine zakai mata to wallahi bazan yarda ba domin nice nayi na'kuda na haifeta na fika iko da ita wato dan ka je ka sayi ru'babbun Kaya shine

Please Login or Register in order to submit comment