Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'aya tsakani da mutuwar Yusairat Asad yaje gida a lokacin khimiyyah tayi nisa sosai ta samu yanki babba cikin wannan mummunar 'kungiyar kwatsam ta fahimci asirin su yana gaf da tonuwa a daren ta cikin mirron tsafi ta kira Hudayyah ta sanar da ita abinda yake faruwa ita kuma a take tace tazo su had'u a samo mafita taje suka had'a meeting da shugabannin cewa su bazasu shigo masarautar ba akwai tsaro za'a iya samun matsala amma ita tunda anan take itace zatai musu aikin lallai ta dakatar dashi kar asirin su ya tonu tunda ta dawo ta kasa zaune ta kasa tsaye tayi la"be tayi le'ke a ranar Asad yayi waya da Isham cewa gobe zai taso sannan ya kusa gano abinda yake nema da shirinsa cikin kayan sojoji hula ce kad'ai da takalmansu bai saba kwana yai curr yana aiki sai asuba ya fita sallah masallaci tayi amfani da wannan damar ta shiga masa d'akin sirrin sa tayi masa 'barna dalilin samunta dayai a d'akin shine hujjar dayai mata dukan hallaka sannan ya shirya batare da sanin kowa ba yabar masarautar a ranar ya koma Marshall islands.


๐Ÿ’‹MRS AL-AMEEN AHMAD CE๐Ÿ˜˜.

See you next time, tanks for ur support I really appreciate it ๐ŸŒน๐Ÿ’“๐Ÿ’ฏ nagode 'kwarai da gaske masoya ha'ki'ka kuna raina har bansan yadda zan kwatanta a gane ba baki bazai iya fad'a ba kalmomi bazasu tsaru ba kawai abinda zan iya cewa saidai nace ina son ku da dukkan zuciya ta ๐Ÿ’‹๐ŸคŸ๐Ÿ’”๐Ÿ’—.


YรšSRรƒH Mร›Sรƒ ร€BรšBร…Kร‚R
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ

5608ร‘G๐Ÿ“ฒ F4D, J7ร‘/ร€ร‘/Bร–BD 67แบž4ร€H M7แบžร€ ร€B7BรƒKฤ€4๐Ÿ’ป๐ŸŽค ku fito nazo๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿค—.


๐Ÿ’Ž Mร‰ KรƒMรƒR SรRKร ๐Ÿ’Ž


WhatsApp no:234 905 527 3614
๐Ÿค™โœ๏ธ YUSRAH MUSA ABUBAKAR ๐ŸŒน.
Ba maraya๐Ÿ˜ฃ___sai rago๐Ÿ˜ช
Ba nakasashe๐Ÿคจ___sai kasashshe๐Ÿ˜ž
Ba mai raina kad'an๐Ÿ™„___sai 'barawo
Ba makaho๐Ÿšถ____sai ma'ki gaskiya๐Ÿคฅ
Ba munafiki๐Ÿ˜ณ____sai wanda ya'ki gaskiya, idan kaga abinda ba daidai ana aikatawa please yan uwa mu gyara shi๐Ÿ‘ whoever sees a wrong thing should correct it๐Ÿ™.NONE OF YOU WILL HAVE FAITH UNTIL HE WISHES FOR HIS BROTHER WHAT HE LIKE FOR HIM SELF. Removing harmful object from the road is charity.

ร€ร‘ร‘ร™RรŒ WRรŒTร‰R'S รƒSSร•ร‡รŒร…Tรร”ร‘๐Ÿ’ซ
๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ๐ŸŒผ
_________________
______________________________
__________________

๐Ÿ’ซA*W*A๐Ÿ’ซ
MRS รƒL'ร…Mร‰ร‰ร‘ รHMรƒD ร‡ร‹๐Ÿ˜˜
_________________________

Mai tambarin yma dutse Jigawa state new world ๐ŸŒน new life and new style sabuwar duniya kuzo kuyi kallo dad'i yana Jigawa garin ilimi garin addini zaman lafiya Jigawa.

๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ
May Allah bless u may Allah protect you and your household frm all calamities ๐Ÿคฒ๐Ÿ‘๐Ÿ™.
HรƒPPY JรšMรƒ'ร‚T MรœBร…Rร„K
๐Ÿ‡๐Ÿ‰๐ŸŽ๐Ÿฅฅ๐Ÿ“๐ŸŒ๐ŸŠ๐Ÿ’๐Ÿ๐Ÿฅ๐Ÿฅ•๐Ÿ.


๐ŸŽˆY๐ŸŽ‰U๐ŸŽˆS๐ŸŽ‰R๐ŸŽˆA๐ŸŽ‰H๐ŸŽˆ๐ŸŽ‰๐ŸŽˆ๐ŸŽ‰
โœจ๐ŸŽ€Mโœจ๐ŸŽ€Uโœจ๐ŸŽ€Sโœจ๐ŸŽ€A
๐ŸŽŠA๐ŸŽB๐ŸŽŠU๐ŸŽB๐ŸŽŠA๐ŸŽ
๐ŸŽ†K๐ŸŽ‘A๐ŸŽ‡R๐ŸŽ‘
๐ŸŽ„Y๐ŸŽ‹M๐ŸŽ„
๐ŸŽˆA๐ŸŽ‰
๐ŸŽˆ

LITTLE ZARAN AUNTY ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ
๐Ÿ’ฎ๐ŸŒธ๐ŸŒผ๐Ÿต๏ธ๐Ÿ’ฎ๐ŸŒธ๐ŸŒผ๐Ÿต๏ธ๐Ÿ’ฎ๐ŸŒธ๐ŸŒผ๐Ÿต๏ธ

41~AL-JALIL
The majestic
42~AL-KARIM
The bountiful

20~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Akilinah.

๐ŸŒ„AVENGE ND REASSURE๐ŸŒ„
Episode 41&42
Asabe bata gida kwananta biyar kuma koda wasa bata fad'awa Balarabe inda taje ba amma sakamakon ta gama dashi ta shanye shi yasa baya da kata'bus bazai iya cewa ina taje ba, tana can ta sake sabo shiri ta d'ingumo masa wani asirin na cin mutumci gabadaya a duniya ya rasa dawa yake son kasancewa sai 'yarsa Indo kullum yana ha'kon ta yana neman d'an dalilin da zai fitar da Dalah anguwa ya samu abinda yake so Asabe bata auri Balarabe dan ta samu wani abu daga bangaren dukiya ba kawai wannan d'auke mata kan da yayi lokacin da taiwa Indo kyautar 'kosai da sanda ta shigo gidansa ya wulakanta ta wannan hujjar yasa ta aure shi da niyyar tarwatsa masa iyalinsa da hana shi farin ciki daga burinta ya gama cika koya saketa ko karya saketa zata tattare kayanta ta 'kara gaba ta koma Lagos tare da 'yarta Bahijjah.

Kamar yadda Balarabe yai fata hakan ne ya faru Asabe bata dawo ba Dalah ta tafi gidansu yana shigowa tana zaune tana wanke-wanke d'an gyara murya yai a firgice ta waigo domin yanzu masifar tsoron sa take ji murya na rawa tace.

"sannu baba" ta karasa maganar a d'ari-d'ari a mamakin sai taga ba kamar kullum ba ya saki fuska harda murmushi yace "yauwa me kike anan"? 'kara d'agowa tai tana kallon sa jin me yake cewa anya babanta ne mutumin da baya kulata ya tsaneta rabon da tai masa magana ya amsa mata a sake harta manta jin ya sake cewa "Indo ba dake nake ba nace meye kikeyi anan"?.

A zabure tace "ina wanke kwanuka ne" kallon kofar d'akin Dalah yai ganin ba takalminta yace "ina Dalah"? Cikin sanyi Indo tace "taje gidan babah Aliyah tace zata biyo ta gida su gaisa da Innah" kai ya jinjina "to to shikenan zonan yanzu" yana fad'in haka wuff ya fad'a d'aki mi'kewa Indo tai jikinta na rawa ta bishi d'aki tana shiga ya banko kofa๐Ÿ™Š.

Shigowar Dalah ganin ba Indo a gurin wanke wanken kuma ga takalmanta dana Balarabe a kofar d'akinsa yasa da sauri taje tura kofar tayi sa'a baisa sakata ba abinda ta gani ne yasa hankalin ta yai mugun tashi zuciyarta na bugawa ta rafka wani uban salati dafe 'kirji tace "na shiga uku na lalace malam mezan gani haka? Wacce irin ba'kar rana ce wannan"? Jin maganar Dalah yasa a firgice Balarabe ya saki Indo dake kuka tana ta kokawar 'kwacewa daga jikinsa jin ya saketa da sauri ta mi'ke da gudu ta fita daga d'akin tana kuka dan ma Allah ya rufa asiri babu abinda yai mata binta Dalah itama tayi da sauri dan batasan inda zata nufa ba shima Balaraben biyo bayansu yayi sai muzurai yake cikin takaici Dalah tace "Malam wacce masifa ce ta sameka ace 'yar daka haifa kake kokarin lalata da ita meya sameka haka ya akai ka canza rayuwa"? Daidai Asabe zata shigo taji abinda Dalah ke cewa dan haka a hankali cikin sand'a ta koma da baya ta la'be tana murmushi wato ha'konta ya cimma ruwa.

Tsawa Balarabe ya daka mata cikin borin kunya yace "ke dalla gafara matsa min anan danai me mekike nufi dan kawai nace ta shiga d'akina tamin shara shine ke kuma saboda gidahuma ce har kika fassara hakan da wata tsiyar" kai jimin mutum kallon sa Dalah tai hawaye na taruwa mata a ido ta ce " yanzu tsakanin ka da Allah Malam ko kunya bakaji ba kake kokarin lalata mata rayuwa gaskiya nagaji bazan iya ba wallahi kawai ka canza hali" a masife yace "bazan canza d'in ba da nace bazan canza d'in ba kinga Dalah ki kiyaye zanci mutunci fa mekike nufi da zan lalata mata rayuwa iye? Saboda ga 'kwarto jikan 'kwarata ko? To nayi maza kisa lasafika garin nan da kewayensa kowa ya sani na nemi Indo wallahi duk ranar da tsautsayi yasa kika tona min asiri naji wannan labarin ya fita waje sai kinga yadda zanyi dake shashashar banza mahaukaciyar wofi" yana kaiwa nan yayi waje yana surutai iri iri na borin kunya da gudu Asabe ta fice a gidan dan karya ganta sauri take kamar zata tashi sama daidai anyi kiran sallar magriba suka had'u da 'kawarta Markah da sauri ta tareta.

"Ke Markah ina zuwa haka? gurin ki fa na taho".

"Tofa 'kawar arziki ince dai lafiya ko asirin ne ya karye muku fito rana bankad'a ta same mu"?.

Kai Asabe ta girgiza "ke a'a waya fad'a miki ai kinsan nace miki na tafi gurin boka ko? To zuwa nai aka sake bani sabon sihiri nasa boka ya cusawa Balarabe son kasancewa da Indo aiko sai gashi d'azu gida ba kowa sai ita kad'ai Dalah bata nan ya lallameta yasata a d'akinsa humm naso yayi 'barna ya aikata abun kunyar dazai bar abin fad'a har jikokinsa amma shegiyar Dalah ta dawo ta katse min hanzari yauwa kuma sannan ya gargad'eta kada ta kuskura wannan labarin wani ya sani basu san ina ra'be ina jiba shiyasa na garzayo na fad'a miki dan kema in kinyi gaba ki yad'a so nake zancen ya bazu ko'ina".

Dariya Markah tai "kai amma wallahi 'kawata baki da mutunci kin iya tsiya ya kamata ki barshi haka ai kin rama yanzu saiki 'kyale shi ki fita rayuwar sa ki barshi ya huta".

"Ta'be baki Asabe tai "humm naki wasa ne tabd'ijan waya fad'a miki na gama ramawa ina dai kan hanya har yanzu nasan komai ya lafa bari na koma gidan naje nayi 'kirmishishi kamar bansan komai ba sai anjima kawata" "to shikenan 'kawar dama gulma ce ta kawo ki kuma kin fad'a min hankalinki ya kwanta nima bari na koma gidana, toni dama ina zanje ne mema na fito yi a waje? Dan tsaki taja tuna had'uwar da sukai da Asaben yasa ta manta kawai ta juya gida, duk abinda suke tattaunawa Malam Habu yana zaune 'kar'kashin wata bishiya yana jinsu ya danji mamakin Balarabe daya nemi 'yarsa Indo subahanallahi kai jama'a Allah ya kiyaye 'bacin rana.

Tafiya sannu sannu kwana nesa lokaci ya mi'ka shekarun da aka d'ebawa Tanko na zaman gidan yari sun cika ya dawo gida Hummm!!!๐Ÿคช Me kuke tunani Tanko ya dawo bayan wadannan shekaru da wani irin turnu'kakken ba'kin dafin d'acin 'bacin rai na daukar fansa da mugun nufi musamman daya tarar babu iyayen sa ko daya sun rasu ga cewa da mahaifin sa yai bai yafe masa ba ya cuceshi Allah ya isa ce tsakanin su nan ba'kin ciki 'kiyayya ta kara d'amfara a zuciyarsa ga rad'ad'i da hassada ganin yadda su Habu suka zama masu arziki matuka wanda kaf garin babu kamarsu musamman Habu shi yafi Sabi'u da Ilyah kud'in ma kamar yayi ga rabon kayan arziki da suke a gari duk an daukake su ganin haka baiyi wata ba wata ba ya samu Mudi suka had'a hannu domin d'aukar fansa gari gari suka rika yawo domin cimma 'kudurinsu a karshe suka sami wani boka sunansa Hambuwa๐Ÿ˜ก๐Ÿ˜ฑ yayi musu aiki, aikima kuwa mummuna maici tun daga wannan lokacin Malam Habu ya fara ganin canji a kasuwancinsa da al'amuransa haka ake tafiya har lokacin damuna kamar yadda suka saba ana raba musu kayayyakin amfanin gona kamar su buhunhunan taki dasu shinkafa da Abubuwan feshi daga baya idan kaka tayi sai su biya Malam Habu yana d'aya daga cikin wadanda ake kawowa mota mota saidai a wannan shekarar sakamakon hannu da aka saka masa sai kaf gonakinsa suka 'ki yin abun arziki gonar kowa 'kalau amma tasa hayam yaga tashin hankali ya shiga damuwa a haka dole ya samu ya sassayar da wasu filayensa da gonaki ya biya amma me Tanko bai barshi ba ya sake komawa cewa a rufa masa ba'kin 'kyalle ya zama kasuwancinsa ya dod'e samunsa ya tsaya cak ya ri'ka baya ya talauce ya lalace haka Malam Habu lokaci d'aya abu ya juye ya'ki masa dad'i aka wayi gari bashi da biyar tasa dazai d'aga yayi ikirari da mallakin sace babu abinda ya rage masa daga gona guda d'aya sai gidan da yake ciki Sabi'u ne ya d'auke dukkan d'awainiyarsa da iyalansa komai shine yake masa suna cikin haka me rabawa tazo ta raba ciwon cikin rana d'aya Malam Sabi'u yabar duniya๐Ÿ˜ญ Malam Habu ya shiga tsananin tashin hankali da rud'u yayi kuka yayi ba'kin ciki da rashin d'an uwansa saidai duk da haka matar Malam Sabi'u Rakiya tana kokari wajen d'an taimaka musu iya iyawarta.

(*(*()*)*) (*(*()*)*) (*(*()*)*) (*(*()*)*)
๐Ÿ˜ฃ๐Ÿ‘‰Wannan shine asalin labarinsu da abinda ya faru a baya๐Ÿ‘ˆ๐Ÿ˜”.
(*(*()*)*) (*(*()*)*) (*(*()*)*) (*(*()*)*)

๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’MUN DAWO CIKIN LABARI๐Ÿ’๐Ÿ’ƒ
Hassan da Hussaini 'ya'yan Ilyah sun dawo daga neman kud'in da suka tafi Cameron bayan shekaru biyar Ilyah yayi farin ciki ya 'kara ji yake kamar ya goyasu a bayansa tsabar so da gata gasu da girman kai na bugawa a jarida Amatu ma tad'an samu hutu tazo ganin gida ta tarar da wadannan samarin sun addabi gari suna fariya sunce babu yarinyar data isa su sota 'yan matan 'kauyen kucakai ne sunyi musu 'kazanta kullum saidai su ci wanka da kwalliya su fantama a gari babu ruwan su suyi shiga kowacce iri ce maimakon Ilyah ko Bara'atu suyi musu fad'a sai hakan ya zama abun burgewa har fasa kai suke yanzu 'ya'yansu ne suke lokaci a garin babu kamarsu hatta Nafisa haka tad'au huma da 'kafafa wai yayyinta sun dawo daga wata 'kasa sun zama 'yan gayu ga yanzu Nurain dinta ya bud'e wuta da kashe mata kud'i ya sai mata waya babba a sati sau biyu yake zuwa ya ganta ya koma su Ilyah anyi hototo ana han'kara ha'kora a gari 'ya zatai aure a binni zata fita zakka a 'kauyen, yana cikin wannan murna ne sabon al'amari ya sameshi wato dai Hassan da Hussaini sun zo masa da zancen sun samu matan aure yayi murna ya hura hanci jin shima lokaci yazo kansa zai d'au surukai๐Ÿคฃ๐Ÿคฉ suna zaune bakinsa ya'ki rufuwa kamar gonar audiga yake kallon su da annuwa yace.

"Ah masha Allah Hassan haka nake son ji ko kufa amma da kun tafiyar ku daga neman kud'i kune har shekaru biyar baku dawo ba 'yar gidan wa kake so a ina take fad'a min ko waye ubanta matukar a 'kauyen nan yake dole ya amince ya baka ita kodan kud'i na tunda a yanzu babu kamata".

Hassan yana zaune akan kujerar roba a gefe ya mi'ke yana gyara fosing cap d'in dake kanshi kafin ya kalli Ilyah dayai sa'kwa'kwa yana kallon shi alamar jiran amsa yace "ai baba ada nace nafi 'karfin aure a garin nan amma fa yanzu rana d'aya nayi karo da Amatullahi 'yar gidan kawu Habubakar kaga tuwo na mai na kawai sai kaje gurin sa kuyi magana abinda kuka yanke a shirye nake nan da wata daya ayi mana aure idan na tashi komawa Cameron mu tafi tare da aba ta kome kace"?.

Wata iriyar 'kamewa Ilyah yai yana kallon Hassan jin abinda yake cewa yasa yaji cikin sa yana hautsinawa tari ya d'anyi jin zai 'kwaru kafin ya sake d'agowa yana cewa "mema kace Hassan banjika sosai ba kunne na ya fara samun matsala d'an maimaita kace me"?.

'Kara d'aure fuska Hassan yai domin tunda suka dawo ya samu labarin Ilyah ba ruwansa da Malam Habu kuma wannan tambayar dayai masa yaga take takensa na 'kin amincewa auren abinda bazai yuwu ba kenan me hana shi auren Amatu a yanzu sai mutuwa๐Ÿคท.

"Hassan nace me kace"? Ilyah ya sake jefa masa tambaya yana karkata kunne yaji me Hassan d'in zaice kauda kai yace "cewa nayi ina son Amatullahi 'yar gidan kawu Habubakar kuma so na aure aurenta zanyi shiyasa nazo na sanar dakai".

Kai Ilyah ya jinjina cikin takaici yace "Au haba auren ta zakai? shiyasa kazo ka kayi min 'kerere akai kana kallona kamar zaka rufeni da duka ka aureta dai? Shiru Hassan yai yana murgina kai Ilyah yaci gaba "lallai Hassan yau na yarda ka fara haukacewa to bari kaji wallahii wallahi tallahi wallahi tallahi kaji rantsuwa uku ko? To wallahi bazaka aure taba ba Amatu ba ko Binta ce uwar data haifeta saika rabu da ita kaji dakyau na fad'a maka shashashan banza sakaran asara wacce Amatun ka rasa inda zakaje kaso 'ya duk girman 'kauyen nan sai yar Habubakar matsiyaci fatararre wanda talauci yaiwa katutu Allah bazaka aureta ba wallahi kaji na fad'a maka".

Ilyah na rufe baki a zabure Hassan yace "wallahi tallahi wallahi tallahi wallahi tallahi na rantse da Allah kaji rantsuwa uku ko? Kallon sa Ilyah ya tsaya yi cike da mamakin abinda yake shirin yi Hassan yaci gaba "wallahi bazan rabu da ita ba saina aureta ko zakai bunga๐Ÿ™Š๐Ÿ™Š๐Ÿ˜‚" zaro ido Ilyah yai yana sake duban Hassan takaici ya gama cika shi yace.

"Hassan Hassan tabd'ijan amma wallahi baka da hankali kayi hauka ne ni kake fad'awa haka"?.

Ran Hassan a had'e zaiyi magana Hussaini dake gefe yana cin abinci yace "ai bakai ba Hassan koni akwai wacce na hasko a cikinsu Aisha 'yar gidan Saude kuma babu wani so'ko'kon dazai hana na aure ta ban ganshi ba๐Ÿ˜ฒ๐Ÿ˜๐Ÿ˜ณ" ๐Ÿ˜‚tabd'i tashin hankali wanda ba'a sa masa rana Ilyah kallon su yake a fusace ji yake kamar yayi hauka tsabar ba'kin cikin da suke cusa masa yama kasa magana sai sunkuyar dakai yayi yana shiru kallon juna sukai suna dariya Hassan yace.

"Baba karfa ka zauna 'bata lokacin ka wajen tunani da nazarin ya zaka 'bullowa al'amarin bari na baka shawara wallahi gara ka koma gefe ka zuba mana ido dan aure kamar munyi inace 'karfin zumunci zamu ninka ka manta me yanke zumunci babu shi ba rahmar Allah kai kuma kake kokarin rabawa tab kaji fa Hussaini meye makomar baba"?.

Batare da Hussaini ya d'ago yace "makomar sa suya da babbaka wuta ce idan aka wullashi saiya 'kone ya toye ya dangwalo 'kasan bakwai๐Ÿ˜ฒ" had'a ido sukai suna fashewa da dariya Ilyah tsabar takaicin da suka 'kunsa masa ji yake kamar ya zubar da hawaye Bara'atu ce ta karaso gurin ranta a 'bace saboda tana jin komai dukkan su biyun ta kalla tana cewa "wai shin kun gamu da ciwon hauka ne a garin da kukaje kome? Uban daya haife ku kukewa dariya๐Ÿ˜ก gaskiya tunda har yanzu bakuyi hankali ba bansan yaushe zakuyi ba gani kuke riba zakuci ku tsaya ku gyara halinku wannan d'abi'ar da kuka d'auka bazai kai kuba".


"Yo umma ai kina jin fa abinda yake cewa miye a ciki๐Ÿคท dan kawai muce yan matan kawu Habubakar muke so ba abin farin ciki bane yana matsayin yayan sa amma harda wani wallahi tallahi wallahi tallahi wallahi tallahi kaji rantsuwa uku ko ๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚ baza ku aure suba mu kuma wallahi tallahi saimun auresu ko mutum zaiyi bunga๐Ÿ™Š๐Ÿคฉ๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿคฃ Hassan ya karasa maganar yana tsayar da idonsa tarr cikin na Bara'atu.

Kae Bara'atu ta jinjina tana cewa "tabdijam babbar magana kenan d'an sanda yaga gawar soja Hassan Hussaini yaushe kuka zama haka har ana fad'a muku magana kuna mayarwa dan raini to bari kuji maganar gaskiya koni ban amince muku ku auresu ba kun dai ji dakyau na fad'a muku inba shashancin kuba ai da gaske yake fatararran ne uwar me yake dashi yanzu wanda lomar abinci take masa wuya kowa yana gudun auren 'ya'yansa saboda kar talauci ya shafe shi ku kuma tsabar 'batan basira kuna cusa kai zakuje ku yayo mana masifa ku kawo mana gida lokacin da suke matasa kamar ku wanne irin wulakancin ne Habubakar baiwa ubanku ba har sha'ke masa wuya ya ta'ba yi ya hankad'a shi gaban Baffah duk wannan cin mutumcin dayai masa amma tsabar sakarci harku so 'ya'yansa uwar me zakuyi dasu meye abin so a jikinsu gayyar talauci da 'kas'kanci yanzu kaf garin nan ba wanda yakai gidan Habubakar fatara da shan wuyar rayuwa to wallahi baku isa ba kuji dakyau na fad'a muku".

Ta'be baki Hussaini yai yana kallon Bara'atu yace "wallahi umma saimun aure su ko mutum zaiyi bunga๐Ÿ˜ฌ garama kiyi shiru ki daina 'bata bakinki akan mu ba wani so'ko'kon dazai rabani da Aisha saiya shirya duk wanda yai yunkurin shiga tsakanin mu saina jajjaga shi nayi 'kuli 'kulin kubura dashi๐Ÿ˜ฒ๐Ÿ˜‚".

Mi'kewa Hassan yai yana cewa "kaima kenan Hussaini balle ni akan Amatu ai inaga saidai na markad'a mutum nayi farfesu dashi๐Ÿคฃ๐Ÿ˜„ nikam nayi gidan kawuna Habubakar yau acan zanci abincin dare๐Ÿ™Š" yana rufe baki Hussaini ya ture kwanon abincin dake gabansa shima yana mi'kewa ya kalli Bara'atu data bisu da ido yace "umma munyi gidan kawun mu Habubakar acan zamuci abincin dare karki d'ora damu idan kuma umma Maimuh ce itama ki fad'a mata karta dafa damu yau ko 'kasa aka dafa a gidansa shi zamuci๐Ÿ™‰" suna kallo basu da damar hanawa haka suka fice numfashin daya tokarewa Ilyah a 'kirji da'kyar ya fisgoshi yana sake kallon hanyar fita yace.

"Na shiga uku Bara'atu kiji wata masifa da yaran nan suke neman d'ora min kawai ina zamana da arziki na zasu auro masu 'kashin tsiya su sa na talauce to wallahi bada yawu na ba lallai zasuga fushi na akan wannan al'amarin idan basu rabu dasu ba".

Bara'atu dake tsaye guri daya ta kasa gaba ta kasa baya sai maimaita maganar su take na cewa wallahi tallahi saimun auresu ko mutum zaiyi bunga akwai matsala gagaruma ko itama bata kaunar wannan auren dole ne ta dakatar dasu da 'karfin tsiya.

"Wallahi baku isa ba inna yarda kun auresu ni ba 'yar halak bace shegun yara dan kunga kun zama samari karfin ku ya kawo shikenan kuke ganin kamar kunfi 'karfin kowa zanga ta yadda zakuyi auren ba tare da yardar muba harda ba wani so'ko'kon dazai hana tabd'i gaskiya yaran nan sunyi nisa".

Cikin takaici Ilyah yace "dani suke so'ko'kon wai ko zanyi bunga?๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ akan iyalan gidan Habubakar suke fad'a min haka amma shikenan nima take d'in zanga uban dazai amince ya d'aura musu auren a 'kauyen nan ban ganshi ba dan ko mai gari ne wallahi bai isa ba yasan sauran ai tunda yana amfana ta kud'i da kayan abinci yai min gardama yaga yadda ake wasan tsutsa๐Ÿ› a rana๐ŸŒ… su kuma zasu dawo gidan su sameni dan ubansu tunda dawowa sukai domin su d'ora min hawan jini su kashe ni saidai su koma inda suka fito akan su auri 'ya'yan Habubakar gara idan sun tafi karsu dawo garin nan har abada zaifi min kwanciyar hankali da abinda suke 'ko'karin jawo min".

Maimuna na d'aki tana sauraron su bata fito ba dan kar ace tayi gulma tunda ba abinda ya shafeta bane kuma Ilyah dan bazai gane bane rashin biyayyar dayai wa Baffah ne alhaki ya fara bibiyarsa kuma zaici gaba da bibiyarsa har karshen rayuwar sa tunda bai nemi yafiyar Baffah ba baiyi zaman d'a na gari dashi ba taya zaice dole 'ya'yansa sai sun bishi bayan shima bai kasance mai biba dukkannin halin Ramatu na mayar da martani da rashin 'kyaliya su Hassan shi suka d'ebo dan haka zaisha kwasar ba'kin ciki damuwa yanzu ya fara gani kiran ya shiga uku ya jira dai lokaci ne gaggawar me yake tafiya dai wata rana saiya kasa furta wata kalma balle ya samu bakin magana ko kad'an bata jin haushin duk wani abu da zasuyi masa domin taga kalar wulakancin da sukewa Malam Habubakar shida Bara'atu talauci aiba hauka bane tana jin tsoron gaba Ilyah zai iya taka matakin da malam Habubakar yake ciki yanzu daga baya Malam Habun kuma Allah ya d'aga shi ya zama wani abu amma duk rashin kunyar Ilyah a wannan lokacin tasan bazai iya fuskantar shi da sunan ya yafe masa ko ya taimaka masa ba domin Allah yana taimakon bawansa matukar bawansa yana taimakon d'an uwansa musulmi sauke ajiyar zuciya tai tana sake gyara kwanciyarta domin ba itace da aikin gida ba gara tai bacci datayi ta sauraron zancen su tunda taga Bara'atu ma layinsu d'aya da Ilyah zuciyarsu bamai son ganin d'an uwa cikin farin ciki bane amma Bara'atu da bazata manta ba itama fa haka iyayenta suke a fatare a talauce auren Ilyah datai ne ta samu guri take d'an aika musu da kayayyakin abinci ai Ramatu batai 'karya ba da tace tazo a 'kar'kashe ta samu guri ta zama 'bukekiya kamar alade๐Ÿ– hummm rayuwa ce ba wanda yasan gobe๐Ÿคจ subi a hankali su taka a sannu akwai ranar nadama ranar da zasuyi kuka da idonsu.

TO YAU KAM NA GAMA TYPING SAI ALLAH YA KAIMU GOBE DA RAI DA NISAN KWANA INSHA ALLAHU ZAMU D'ORA LITTAFIN ME KAMAR SARKI ๐Ÿ‘‘ A INDA MUKA TSAYA๐Ÿ™….

Kudai ku kasance da๐Ÿ‘‡
MRS AL-AMEEN AHMAD CE ๐Ÿ˜˜.


TYPING ๐Ÿ“ฒ ME KAMAR SARKI ๐Ÿ’Ž๐Ÿ‘‘๐ŸŽง ๐Ÿ’‹YUSRAH MUSA ABUBAKAR๐Ÿ’‹ ๐ŸŒน๐Ÿค™.


๐Ÿ‘‘ME KAMAR SARKI๐Ÿ‘‘


๐Ÿ‘Œ SABUWAR DUNIYA KUZO KUYI KALLO DADI YANA JIGAWA GARIN ILIMI GARIN ADDINI ZAMAN LAFIYA JIGAWA ๐Ÿ‡๏ธ๐Ÿ—ป๐Ÿž๏ธ๐ŸŒƒ.

AYI HAKURI IDAN AN SAMU TYPING ๐Ÿ“ฒ ERROR ๐Ÿ”ด๐Ÿ›‘ MATSALAR KEYBOARD NE๐Ÿคซ.

โœ๏ธMrs Al'ameen Ahmad ce ๐Ÿ˜˜.
Inai muku barka da wannan lokaci fatan kuna cikin kyakkyawan yanayi๐ŸŒ„ Allah yasa haka Amin ๐Ÿคฒ๐Ÿ‘๐Ÿ™.

DON'T HARM ANYONE๐Ÿคซ DON'T ALLOW ANYONE TO HARM YOU ๐Ÿ˜ก๐Ÿ˜ 
_____________________

43~AR-RAQIB
The watchful
44~AL-MUJIB
The Responsive

21~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Muhsininah.

๐ŸŒ„ PALACE ND DISPLEASE๐ŸŒ„
Episode 43&44
Masarauta gabadaya yau ahlin gidan suna tare guri daya suna wani babban d'akin shan iska 'kawatacce mai girma sosai mai martaba Alhassan yana waje daya da matansa shima mai girma Alhussain yana gefe da nasa sai sauran samarin da 'yan matan suma can suna ta hayaniya kowa fira yake cikin jin dad'i saidai amma a 'bangaren mai girma Alhussain idan ka duba zakaga akwai matsala domin sultana Hadizah ta cika tayi famm kamar zata fashe sai huci take tana kumbure kumbure shi kuma yana mata magana.

"Hadizah wai me kikeyi haka kinsan abinda kike fad'a kuwa d'an gidan nawa (Asad) zance na yanke ala'ka tsakani na dashi tsabar rashin hankali dan kawai ya daki Khimiyyah? ta farfad'o ne kin tambaye ta laifin me tayi masa ni bana abu

Please Login or Register in order to submit comment