Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana kanne mata ido๐Ÿ˜œ.

Ta'be baki Maryam tai tana cewa "tab wallahi ba inda zanje saidai driver yakai".

"Umm kuma idan momy ce tace kije fa ya zakiyi"?.

"Insha Allahu ma bazatace ba ki daina min fata".

"To ai shikenan bari nikam naje gurin umma na nasan yanxu batai barci ba" tana fad'in haka ta fice mi'kewa Maryam tai bayan fitar Amatu ta shiga wanka Ikram dake zaune akan stool tana chat ta ta'be baki tare da kunna voice tana dannar ashar iri iri ta tura fitowar Maryam ta kalleta da mamaki tace.

"Haba Ikki dawa kike wannan zagin haka kamar ba musulma ba dan Allah ki rage zafin zuciyar nan karki manta kefa mace ce wata rana gidan wani zakije".

Tsuka Ikram taja tana cewa "rabu dani Maryam wannan akwai tsinanne baki san halinsa bane shiyasa kike ganin laifi na amma mugun tantiri ne dan raini hankali jiya kina gani lokacin da kukaje gidan nayi masa hidima na kashe kud'i amma yace bazai samu damar xuwa ba baya gari tafiyar ujila ce ta kamashi yau kuma wani wai ya kira ni d'azu muna modeling dan ban d'aga ba shine yake min masifa da 'korafi aikin banza".

"To ke Ikram dole ne soyayya da wannan yaren nifa gaskiya dama garinsu yayi nisa har Abia state gaskiya ki barshi zaki samu wanda ya fishi".

Kai Ikram ta girgiza tana cewa "bazan iya ba Maryam ina son sa shine mafarki na had'dd'an gayene na kwatance ga kud'i d'an gidan Minister gud'a ne fa taya zan 'kyale shi".

Kad'a kai Maryam tai tana sake kallon Ikram tace "um um Ikki kada fa, ki tsaya kiyi nazari karki bi son zuciya".

"Maryam aiba son zuciya bane waye zai samu dama ya sake gayen akwai sakin hannu yana zubar min da naira๐Ÿคจ shiyasa na narke ashi yanzu zamuyi fad'a naci 'kaniyarsa yanzu zamu shirya kin gani ko gashi harya turo min stikers da typing na bada ha'kuri ai nasan bazai ta'ba zuciya dani ba shiyasa nake masa abinda naga dama na zageshi naci mai mutunci duk ya had'iye".

"Hummmm" kawai shine abinda Maryam tace tana daukar kayan barci tasa tayi kwanciyar ta bata sake bi takan Ikram ba wacce take video call sai dariya take har barci ya fara d'aukarta taji Ikram tana she'ka dariya a firgice ta farka tana kallonta tace "dan Allah ikki badan niba kiyi shiru ko ki kasa da murya wallahi kin d'au alhaki na domin barci ya faramin dad'i kika katseni" tsaki Ikram tai tana juya mata baya tace "dama kuma ni na hanaki yin barci ne harda wani nayi kasa da murya bazan ba gara kiyi barcinki a haka ko ki ha'kura saina gama" Maryam bata sake kulata ba ta gyara kwanciyarta tana jan bargo.

๐ŸŒดCAMEROON๐ŸŒด
Su malam Habu sun sauka lafiya cikin garin Bamenda haka suka kwana a layi suka wuni cikin rashin sanin madafa basu samu masauki ba balle ayi zancen fara sana'a ganin idan suka tsaya kud'in guzurinsu zai 'kare kuma dama kawai basu San inda zasuje ba da ka suka taho sai kawai Sadi yace masa subar nan su koma Douala 'kila zasu dace.
Haka sukai a ranar suka tafi sun sauka lafiya saidai kud'in su ya tafe basu da ko biyar balle su sai abinci sakamakon da masu shagunan abinci a gurin yasa sukai musu magiya da Allah da annabi cewa su ba'ki ne sunzo neman kud'i ne yau daga Nigeria suke kuma kud'insu ya kare su basu bashi zuwa gobe amma ba wacce ta kulasu kusan guri biyar suka tambaya ba wanda ya basu sai wata mammah itace taji tausayinsu ta amince ta basu tare da d'aura alkawarin zasu biyata idan suka samu bayan sun kammala har zasu shiga gari Malam Habu yace su gwada tambayarta ko zasu samu wata sana'ar yi anan Sadi yace eh su gwada ko zasu dace.

Kallonta Malam Habu yai yana cewa "dan Allah hajiya ko kinsan wata sana'a da take kawo kud'i a garin nan"?.

Kaita d'aga "eh to banace babu ba zaku iyayin sana'ar gwangwan (baban bola๐Ÿ™…) idan kuna so domin yana kawo kud'i da wuri yanzu mutum zaiyi arziki".

"Eh zamuyi indai kud'i zai samu".

"Zaku samu amma fa kamar saida rayuwa ne domin yana da had'ari".

"Had'ari kamar na mefa hajiya"?.

Zama mammah tai bayan ta gama sakawa kwastomominta abinci ta fuskance su tana cewa "yanxu kamar a misali idan kuka fara zaku iya shiga 'kauyuka kuna samu matattun firiza da injina da video su gas da manyan 'karafina amma fa sai kuna hattara da takatsantsan domin da akwai 'barayin da zasu sato kaya masu tsada su kawo ku saya a rashin sani idan tsautsayi yasa aka kama mutum dashi ya sayi kayan sata tofa zaisha duka in kwanansa ya 'kare ma saidai a kashe shi".

Zaro ido sukai duk su biyu cikin tsoro Sadi yace "kisa kuma"?.

"Kwarai kisa ana kamaka ka saya a take za'a jefa maka taya da fetur asa maka ashana ka 'kone 'kayau".

Kai malam Habu ya jinjina yana cewa "wannan ba irin sana'ar da nake son yi bace ni nazo ne dan hankalina ya kwana na nemi kud'i cikin aminci naje na kyautatawa iyalaina bazan sa kaina cikin had'ari ba gaskiya gara nayi bara ko turin baro".

Sadi shima da jikinsa ya gama sanyi jin abinda mammah tace kallon Malam Habu yai yana cewa "gaskiya ne ni wallahi har naji tsoro ma ya kamani badan idan muka koma gida za'ai mana dariya ba musamman su Tanko da min tafi zama lafiya yafi zama d'an sarki".

Kai Malam Habu ya girgiza "a'a baza mu koma ba zamu samu abinyi Sadi tashi muje hajiya insha Allahu zamu kawo miki kud'in ki".

"To ba damuwa Allah yasa ku dace idan ma baku samu kud'in da zaku biyani ba na yafe muku".

"Insha Allahu zamu samu hajiya bari muje" .

Daga gurin hajiya mammah mai abinci gari suka sake shiga suna bi layi-layi kamar masu duban tsafta sun rasa inda zasu tsaya basu San kowa ba cikin sa'a suna shan wata kwana sukaga wani mu'ke'ken 'katon alhaji zaune a kofar gidansa ga mutane zagaye dashi sai raba musu kud'i ake fahimtar da sukai kamar sadaka yake yi yasa suka tsaya suna suna bin dogon layin da mutane sukai d'aya bayan d'aya ana basu har akazo kansu dubu goma goma godiya sosai da murna sukai masa cikin farin ciki suka koma gurin hajiya mammah mai abinci suka biyata sunai mata albishir d'in inda suka samu kai ta jinjina tana cewa.

"Oh nasan mutumin sunansa Alhaji Idrisu kuce 'kofar gidansa kukaje ai dama haka yake duk sati saiya rabawa mutane dubu goma-goman nan yana da kirki sosai kuma babban ma'aikacin gwamnati ne yana d'aukar mutane aiki ma idan kunyi sa'a kuka kai masa kukan ku zai kar'beku"

"Ok yanzu idan muka koma zai yarda ya d'auke mu"?.

Kaita d'aga "eh banace ba kasan ta yuwu yace basa d'auka yanzun tunda shima daga sama ake sashi duk wanda ya ra'bu inuwarsa zaisha sanyi dan mutum ne me sakin hannu ba laifi".

Jin bayanin da hajiya mammah tai musu yasa cikin zumud'i malam Habu yace "Aiko indai haka ne baza muyi kasa a gwiwa ba Sadi tashi mu koma ko zamu dace hajiya bari mu gwada zuwa a rashin tayi akan bar araha" to hajiya mammah tace musu yayin da suka mi'ke suna komawa amma cikin akasi domin bayanan motarsa ma bata nan ha'kura sukai suka bari sai dare sannan ya dawo gida suma sa dawo.

Da dare ma bayan sallar isha haka sukai ta zaman jira amma shiru har dare yai musu sosai babu shi babu alamarsa kawai suka 'kyalewa safiya.

Gari na wayewa asubar fari bayan sun fito daga masallaci basu zarce ko'ina ba sai kofar gidan haka suka samu guri suka zauna gurun suna zaman jira gaibu har rana ta fito ta fara zafi alhaji bai fito ba kamar yabar 'kasar tsaki Sadi yai yana kallon tabkeken gate d'in gidan yace.

"Wallahi masu kud'in nan sun fiya wulakanci kagani tun jiya kamar yasan muna nemansa ya wani shiga gida yai shiru kamar Wanda ya mutu"?.

Sauke numfashi Malam Habu yai yana cewa "ka zamo mai hakuri akan abu sai kaga ribar hakurinka a gaba bakasan abinda ya hanashi fitowa ba mara abu baya zuciya haka zamuci gaba da zama nan da fad'uwar rana baza muje ko'ina ba harsai ya fito mun had'u" dashi walakila jinkirin namu ya zama alkhairi kasan ance gaggawa aikin shed'an ce".

"Shikenan Habubakar Allah yasa muna da rabon zaman ne ya isheni kamar an dasa ni".

"To ka tashi kana d'an zagayawa man anan d'in saika mi'ke 'kafar taka".

"A'a idan su nan ba'a saba ba wani yaga ina haka sai ace turoni akai nayi si'aidin gidan ko kuma dai akwai abinda nake nema tunda kaji dai me mammah mai abinci tace su garin nan abun laifi bayai musu wuya saisu 'kone mutum kamar kara ko ice".

'Dan murmushi malam Habu yai yana cewa "kai kuma ga tsoro ba"?.

"Tsoro wajibi ne".

"Eh wajibi ne amma banda irin naka".

Malam Habu yana rufe baki Sadi zai magana sukaga motar alhajin tazo tayi parking a kofar 'katon gate din gidan kallon sa malam Habu yai yana cewa ashe ma ba'a gari ya kwana ba har kake cewa ya shiga gida yai zamansa an fad'a maka mutane masu harka da gwamnati suna samun zama ne? Tashi muje" mi'kewa Sadi yai amma kafin su farga d'uuu mutane nata zuwa har an cika guri basu san dawar gari ba abinka da bako (ra'ba๐Ÿ˜‚).

"Oh ji wata masifa wai da yaushe ma wad'annan mutanen suka zo har suka cika gurin haka"?.

Mi'kewa Malam Habu yai yana kallon sa yace "da baka farga ba kagani dai kamar wanda suke aiki da inji tashi muje" tashi Sadi yai yana kallon yadda ake turarreniya yace "wannan anya zamu samu ganinsa kuwa"?.

"Zamu samu idan mukai hakuri" tafiya gurin suke amma sai sukaga alhajin ya shige gida yabar wani a gurin yau shine mai rabon kud'in dafarko ya fara rabawa ya tsaya yana le'ka jakar yace "ba kud'i yau sosai saidai kuyi hakuri da dubu bibiyu" kallon kallo aka fara tsakanin sa da mutane domin sun san ha'incinsa shiyasa basa so alhaji ya bashi rabon kud'i bayai musu tsakani da Allah dannewa yake haka ya basu dubu biyu biyu sai tsine masa suke suka bar gurin.

Kallonsa Malam Habu yai tabbas wannan da ganinsa bazai kirki ba amma bari su gwada abun ba'a kama bane ya d'au jaka yana Shirin barin gurin sai waige-waige yake kar alhaji ya fito ya sameshi yasan zai shiga uku da sauri ya tari d'an mashin malam Habu daya karaso yace.

"Dan Allah Malam ina son na tambaye ka"?....

Wani kallo yai masa yana cewa "a'a ni ba'a tambayata baka da abinda zaka tambaye ni nima bani da abinda zance maka"?.

Kallon mamaki malam Habu yai masa yana cewa "taya ka sani ko akan wannan jakar hankalin ka ya'ki kwanciya muyi maganar? Shikenan dai kaje ka dawo ina son zanyi maka tambaya domin ina so ka had'ani da Alhaji".

Zaro ido mutumin yai yana kallon malam Habu cikin rashin gaskiya yace "uban waye zai had'aka da Alhaji Idrisu dama an fad'a maka kowanne kare da doki alhajin yake kulawa?.

A 'kule Malam Habu yace "kai banza ka iya bakin ka a kanmu".

A masife yace "bazanyi ba uban waye kai daga ina ka fito da ganinka koran yuwa ne kai ga alamar firgicin talauci ya gama katutu da samun gurin zama a wajenka kalli fa 'kasusuwa๐Ÿ™Š a jikinka๐Ÿ™„ mutsssssss kai mai mashin da Allah mu tafi rabu da wannan kila mahauci ne" yana rufe baki mai mashin ya zuga aguje yana basu iska.

Da kallo Sadi yabi mashin din yana cewa "kai jimin tsinannan mutum daga tambaya sai cibi ya zama 'kari had'uwa da irin wadannan sam ba alkairi bane dole mu sake taku tunda ba 'kasarmu bace bamusan komai ba".

Shidai malam Habu shiru yai bai sake magana ba kallonsa Sadi yai "mu tafi Allah yasa haka ne yafi mana d'an wannan koya saurare mu bazamu shirya dashi ba tunda baida mutunci muyi gaba Allah zai had'a mu da d'an arziki....................

Shiru Sadi yai jin 'karar bud'e 'kofa da rufewa yasa suka juya a tare alhajin ne ya fito yana shirin shiga mota aiko da sauri suka karasa gurinsa kamar zasu kifa suna masa sallama an bud'e masa mota harya shiga ya zauna kallonsu yai yana cewa.

"Ina fatan dai lafiya ba wani abu ne ya had'aku da yarona ba d'azu ina ta saman beni naga kamar kuna sa insa"?.

Kallon juna sukai da mamaki kai Malam Habu ya d'aga yana cewa "eh muna tambayarsa ne ya had'amu dakai ya'ki ba komai bane".

"Ok meya faru kuke nema na naga kamar ku ba 'yan 'kasar bane ko"?.

"Eh daga Nigeria muke munzo neman kud'i ne shine mugaka kana rabon kud'i ranar akace kai ma'aikacin gwamnati ne shine mukace zamu sameka ko Allah zaisa mu dace ka taimake mu".

'Dan shiru yai na wani lokaci kafin yace "wanne irin aiki kenan"?.

Da sauri Sadi yace "Alhaji ko d'eban bola ne zamuyi".

Murmushi yayi yana cewa "d'iban bola kuma? A'a zamusan yadda za'ai yanzu akwai gurin da zanje ku bari zuwa dare zan dawo gobe da safe babu inda zanje sai kuzo muyi maganar" cikin farin ciki sukai masa godiya yayin da ya rufe murfin motar yana barin gurin da kallo suka bi motar murna ta rufe su haka suka koma gurin mammah mai abinci suna fad'a mata yadda sukai dashi ta tayasu murna domin tasan idan sukai sa'a kwanan nan zasu zama masu kud'i dan mafi yawan wad'anda alhajin yake taimakawa wasu sun zama masu d'an abin hannu.

MRS AL-AMEEN AHMAD CE๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ.
Mai tambarin yma dutse Jigawa state new world new life and new style sabuwar duniya kuzo kuyi kallo dad'i yana Jigawa garin ilimi garin addini zaman lafiya Jigawa ๐Ÿƒ๐ŸŒฟ.

See you tomorrow morning๐Ÿ˜œ.

TYPING ๐Ÿ“ฒ Sun, Jul14 ME KAMAR SARKI ๐Ÿ’Ž.

A*W*A
ร€ร‘ร‘ร™RรŒ_WRรŒTร‰R'S_รƒSSร•ร‡รŒร…Tรร”ร‘๐Ÿ’ซ
_________________________________
HOME OF HOSPITALITY ๐Ÿค— AND HARMONY ๐Ÿ•Š๏ธ๐ŸŒด๐ŸŒฒ๐ŸŒณ gidan kar'bar mutane hannu biyu da zaman lafiya Annur haske ๐ŸŒƒ le'ka gidan kowa koda ma'kiya na kallon ka ramin kura sai 'ya'yanta.

A L ' A M
๐ŸŒน๐ŸŒน ๐ŸŒน ๐ŸŒน ๐ŸŒน๐ŸŒน ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน ๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒน๐ŸŒน ๐ŸŒน ๐ŸŒน๐ŸŒน ๐ŸŒน ๐ŸŒน ๐ŸŒน
๐ŸŒน๐ŸŒน ๐ŸŒน๐ŸŒน ๐ŸŒน๐ŸŒน ๐ŸŒน ๐ŸŒน
E E N
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน ๐ŸŒน๐ŸŒน ๐ŸŒน
๐ŸŒน๐ŸŒน ๐ŸŒน๐ŸŒน ๐ŸŒน ๐ŸŒน ๐ŸŒน
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน ๐ŸŒน ๐ŸŒน๐ŸŒน
๐Ÿ‘†๐Ÿ‘†๐Ÿ‘†๐Ÿ‘†
๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
A+L+A+M+E+E+N= AL'AMEEN๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜
You are my whole life๐Ÿ˜๐ŸŒน๐Ÿ’“.

๐Ÿ“šYUSRAH MUSA ABUBAKAR
โœ๏ธMRS AL-AMEEN AHMAD CE๐Ÿ’ƒ.

49~Al-Ba'ith
The Resurrecter
50~Ash-shahid
The Witness

24~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Mubashshirinah.

๐ŸŒ„PRIG ND MUTTERING๐ŸŒ„
Episode 49&50
India Chennai (mercy hospital๐Ÿฅ) zaune suke su Mami da Annur yayin da Ajeeb da Ameer suke gurin likita a ciki suma da'kyar likitan ya bari yace saidai mutum d'aya yazo gurin irin wanda ake so ya kasance silence please ne ba'a so ana yawan shige da fice saboda patient๐Ÿ˜ท d'in gurin na bukatar nutsuwa sosai doctor ya musu bayani da bayyana musu halin da Khimiyyah take har yanzu jiya iyau babu dad'i jikinta saidai zasuci gaba da dagewa iya iyawarsu sun shiga tashin hankali lokacin daya gama musu bayanin abinda ke 'boye shiyasa suna fitowa a hanya Ajeeb ya d'aga waya yana kiran Asad domin masa magana akan Khimiyyah dan likitoci sun tabbatar musu rayuwar ta tana cikin had'ari kusan kira uku yayi masa bai d'aga ba sai ana hud'u yana d'agawa Ajeeb ya soma balbaleshi da fad'a.

"Kai Asad yanzu tsakani da Allah abinda kake ka kyauta kenan wato ka daina kirana idan na kiraka saika ga dama ka d'auka saboda baka so na fad'a maka gaskiya ko Asad wai me kake son mayar da kanka ne? Kaji tsoron Allah Asad ka kiyayi duniya idan gigin samartaka ce take d'iban ka wata rana tsufa zai riskeka ko baka so nasan kasan me nake nufi da magana ta dan haka idan kayi ra'ayi kaga dama kazo muna Chennai mercy hospital ka same mu dukkan mu".

Shiru Asad yai yana sauraron sa saida yakai karshe sannan yace "ka gama"?.

A fusace Ajeeb yace "oho maka ban sani ba wato yau ma raina min hankalin zakai ko"?.

Bai bashi amsa ba cikin son 'kular dashi ya sake cewa "amma Ajeeb me kuka zo yi a India ko 'karin karatu๐Ÿ™Škai da waye"?.

A zabure Ajeeb ya kalli Ameer wanda shima ya kallesa mamaki ya gama cika shi katsesu Asad yai "Ina fata ba wani matsala bane I mean yawan ganin gari kuka zo"? .

"Uban ganin gari muka zo wallahi Asad kana da abin mamaki ni harna fara kokwanto ma anya da sauran imani a zuciyarka kuwa? Idan ba haka ba taya zaka kashe yarinyar nan sannan kayi burus da mutane zakajin kunya kodan son da mahaifin ta ke maka"?.

"Ajeeb a gidan ubanwa na kashe ta"?.

"Asad ka kasheta man meye marabarta da gawar tunda har yanzu batasan inda kanta yake ba"?.

"Oh wai da gaske? kenan akanta kuka zo Indian baku da aikin yine kuma da nasan haka zaku wahalar da kanku a kanta wallahi kaji na rantse? da bazata rayu ba tun ranar saina karasa murd'e mata wuya ta mutu a take domin batada wani amfani ita kamar package ne ka cire abin ciki".

"ร€SAD".

"Ya akai ne Ajeeb? Da alama sunana yanai maka dad'i ko exchange zamuyi๐Ÿ˜ƒ"?.

"Ban sani ba uban exchange zamuyi dama abinda nake son ji daga gareka kenan kazo ka dubata shine damuwata".

"Zaka dad'e damuwa tana damunka domin wallahi bazan zoba ko mutuwa tai".

"Asad kana da 1-hankali 2-imani 3-tausayi kuwa"?.

"kwarai fiye da yadda kake zato malam Ajeeb duk yadda kake jin tausayi a ranka nawa yafi naka duk yadda kake jin imani a zuciyarka na fika dan haka kada ka sake min magana akan wata Khimiyyah domin idona idonta matukar ka matsa nazo Chennai a yanzu saina karasa ta".

A she'ke Ajeeb yace masa "au haba to ko zaka gwada ne? dan Allah idan ka isa kazo ka kasheta".

"Ai kai Ajeeb a yanzu baka isa kasa nayi abinda banyi niyya ba baka da wannan zarrar".

"Haka ne bani da zarra a gunka tunda rana d'aya aka haifemu ban fika ba ka gama raina ni amma a tunani na Khimiyyah sistern kace komai tai maka zaka iya yafe mata ka ha'kura".

"Waye zai yafe mata? dama amfad'a maka ha'kura nai? tilas na rabu da ita saboda Mami kuma da kake magana a kanta ko yanxu na ganta saina kasheta wallahi๐Ÿ™Š".

"To Asad nace baka da imani kace a'a yanzu kuma a furicin ka uban me kake son nunawa kace ko yanzu kuka had'u saika kasheta that mean baka ha'kura ba kenan"?.

"Dama munyi ni dakai nace abinda tai min na ha'kura ne"?.

"To Asad saurara muyi magana ta hankali wai me Khimiyyah tai maka kad'au zafi har kayi mata irin wannan ba'kin dukan firgitarwa mai lahani gashi harnan Indian ma da mukazo abun sai a hankali please laifin me tai maka"?.

"Ban sani ba".

"Dan Allah Asad ka fad'a min abinda tai maka"?.

"Bazan fad'a ba".

"Na rokeka ka fad'a min babu wanda zan fad'awa".

"Ni zaka mayar me 'karamar 'kwa'kwalwata Ajeeb wayo ka fini ko me"?.

"A'a Asad ni bance na fika wayo ba maganar hankali muke a nutsuwa cikin lumana me tai maka"?.

"Nace ban sani ba Ajeeb don't disturbing me๐Ÿ™„ ya isa haka".

"Bai isa ba Asad ka fad'a min abinda ya had'aku dan Allah".

"Bazan fad'a ba Ajeeb".

"Asad baka san Allah ba"?.

"Kai daka sani sai ka sanar min tunda ina musulmi kafurta ni kake shirin yi akan gaskiya ta".

"Wacce irin gaskiya ce wannan Asad indai kasan ba laifin ka bane ka fad'a min"?.

"Ka daina 'bata bakinka Ajeeb bazan fad'a ba sannan wannan maganganun sun isheni haka idan akansu ka kirani sai anjima domin ni inada abin yi bani da lokacin shirme kamar ka" yana fad'in haka ya sauke waya.

Kai Ajeeb ya jinjina yana kallon Ameer yace "tabd'ijan tashin hankali wanda ba'a sa masa rana kaji abinda yake cewa ameer wai ko yanzu suka had'u saiya kasheta wai Asad wanne irin murd'add'an mutum ne"?.

Murmushi Ameer yai dan baisan meyasa ba amma ko kad'an baya ganin laifin Asad akan wannan al'amarin duk da baisan meya had'asu ba amma ya tabbata Asad bazai daketa kawai dan zalunci ba Khimiyyah bata da siffar masu gaskiya sau tari idan tayi abu zaka rantse ba ita bace aljanu ne".

"Ameer ina magana kayi shiru ko kaima abinda Asad d'in ya fad'a ya 'bata maka rai"?.

Kai Ameer ya girgiza "a'a Ajeeb bai 'bata min raiba kaima dan ka'ki tsayawa ka saurare shine nasan Asad da d'auke kai akan yaran nan bada banza ba ya daketa maganar anyi an kuma ka bari duk daren dad'ewa zai dawo gida ai gaskiya zatai halinta yanzu abinda ya kamata ayi shine mu mayar da hankalin mu akan Khimiyyah tukuna idan Allah yasa ta samu lafiya zan tayaka mu shawo kan Asad ya fad'a mana komai ta ruwan sanyi".

Cikin jin haushi Ajeeb yace "sai mun zauna ta warke sannan zai fad'a mana Ameer? waye yasan ranar farfad'owarta balle ayi abinda ake so"?.

"eh dole sai mun jira tashinta ayi komai a gaban kowa".

"Amma Ameer..................................

"A'a Ajeeb basai kace komai ba na fahimta yanzu muje gurin Mami daga baya ma karasa maganar".

"Ok shikenan amma wallahi yadda ya 'kona min rai shima saina hukuntashi ta inda baya zato".

Dariya Ameer yai yana cewa "tofa me zakai masa karfa ka jawo mana tashin hankali a gida idan kace dole yazo nasan zai iya yazo d'in kuma ya aikata abinda yace ya kasheta kasan Asad daya hauro zaku ri'ka uban dambe kamar wasu 'yan wrestling dan ma yanzu hankali yazo an girma an rage wasu abubuwan"?.

"Ba wani tashin hankali kawai kayi shiru kai kam Allah ya kaimu lokaci ya dawo wallahi saina bashi mamaki zan firgitashi idan yana jin kansa shi Aliyu Asad ne to zaisan nima Aliyu Ajeeb ba kanwar lasa bane๐Ÿ˜ก zan nuna masa isa da mallaka zai gane Allah da girma yake".

Murmushi Ameer yai yana girgiza kai yace "Uhm Ajeeb bansan meyasa ka zafafa al'amarin Khimiyyah ba bayan bakasan komai ba to kodai sonta kake"? Ameer ya karasa maganar yana kau dakai ya soma dariya.

'Dan bugarsa a baya Ajeeb yai yana cewa "so dai wanda na sani da zakacewa budurwa ina son ki shi kake nufi"?.

Kallonsa Ameer yai "eh shi nake nufi man".

Kai Ajeeb ya girgiza yana cewa "inaaa ko d'aya babu so tsakani na da ita saina 'yan uwankmtaka amma badai maganar aure ba kawai ina fad'a ne dason 'kwata mata hakkinta dan kaf cikinsu babu wacce tai min indai a matar aure ne bazanyi auren had'i ba".

"Humm mukwa kaga shi zamuyi".

Da mamaki Ajeeb ya kalleshi "da gaske kake amma wace a ciki"?.

"Kai wace kaga ta dace dani"?.

Shiru Ajeeb yai cikin tunani yace "a'a ai bansan abinda ke ranka ba kasan ra'ayi riga".

"Eh haka ne amma na baka za'bi banda Khimiyyah ka fitar min d'aya a cikinsu uku sai ayi tuwona maina ga abu a gida ai bazamu fita waje mu auro ba ko ya kace"?.

Kai Ajeeb ya jinjina "eh kun kyauta saidai gaskiya a cikin su kamar ina ganin Shaukiyyah tafi dacewa dakai".

Dakatawa Ameer yai yana cewa "da gaske tafi dacewa dani"?.

Kai Ajeeb ya d'aga "eh a nawa ganin ba".

"Ok Ajeeb dakata ka bud'e idonka ka kalleni dakyau ka za'ba min"?.

"Allah da gaske nake Shaukiyyah tafi saidai kai bansan wacce kake hari ba Makiyyah ce ko Khaldiyyah"?.

"A'a nima ta takan gaskiya dama tun tuni a raina Shaukiyyah na za'ba saidai na sake baka za'bi ne saboda ko zakaga wacce tafi dacewa dani sannan nifa ba sosai nake bambancewa tsakanin ta da Makiyyah ba tunda kaga kamar su d'aya".

"No akwai hanyar ganesu mana ai Makiyyah tafi Shaukiyyah fad'in fuska sannan ita kuma Shaukiyyah tafi Makiyyah haske da dogon hanci kai baka ta'ba lura ba"?.

Kai Ameer ya d'aga "eh gaskiya ban ta'ba ba saidai yanzu na tsaya na ganeta kar wata rana naji kunya garin kiran Shaukiyyah na kira Makiyyah".

Murmushi Ajeeb yai "idan ka kirata ba matsala ranar sai ayi hirar da ita a maimakon Shaukiyyan".

Kai Ameer ya jinjina yana cewa "to amma kai babu wacce tai maka a cikinsu ka za'bi Makiyyan shikenan tunda kaga ita Khaldiyyah Annur takewa naci dan ya'ki ne".

"Hum ai kasan Annur d'in sai a hankali muskili ne halinsu daya da Asad ko yana sonta bazai nuna ba saiya wahalar da ita Makiyyah kuma saidai ta auri wani a waje ita da

Please Login or Register in order to submit comment