Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

manta ita muguntar da tai maka kazo saika wuni a rana tun daga safe zuwa dare biyar bata bata shigo maka ba wallahi Babu inda zanje na dubata Allah yasa ma ta mutu"😲 shiru Ilyah yai yana kallon ta ya kasa magana tsaki tayi "meye ne ka wani tsaye tserere a akai na kamar bishiya ko bakiji yaren da nai maka magana dashi bane? nace bazanje asibitin ba kuma kaima in kaje ban yafe maka ba" zaro ido yai cikin mamaki yana kallon ta zaiyi magana sukaji sallama duk kallon gurin sukai Habu ne ya shigo yana durkusawa a gaban Ramatu yace "babah ina kwana"? Baki da ido Ramatu ta bud'e tana kallon sa tace "tofa jama'a yau za'ai ruwa da 'kan'kara a garin nan Habubakar yaushe rabon duniya da ayyaraye kaine a gaba na kake gaida ni ko kuma mafarki nake"?.

'Dagowa Habu yai cike da mamaki yana kallon ta abinda kullum sai yazo ya gaida ita wata rana harda aje mata kud'in goro yake amma zata ce yaushe rabon duniya da ayyaraye tab lallai Ramatu ta fara gigin tsufa kawai yabar abun a matsayin haka katse masa tunani tai "Habubakar dakai fa nake ko kaima kazo ne ka fad'a min Salamatu na asibiti" kai ya girgiza yana cewa "a'a nazo ne na fad'a miki an samu 'karuwa a gidana yau da asuba Allah ya sauki Binta lafiya mun samu namiji kuma ranar sunan za'a d'aura min aure da A'i" zaro ido Ramatu tai har batasan lokacin da tace "Binta ta haihu namiji na shiga uku na lalace wannan wanne irin bala'i ne da masifa kaji fa Ilyah sai haihuwa suke tayi amma kai ka ma'kalewa waccan mayyar tsinanniyar bunjinjimar matar taka wacce batasan komai ba saici kamar jaka tazo a 'kai'kashe ta samu arziki ta bararraje yanzu gashi ta zama kamar alade ko'ina bulbul ba rama ai wallahi tallahi Ilyah a satin nan saika auri Maimuna na gaji ace har yanzu baka da d'a ko daya Sabi'u 'ya'yansa uku ga Habun ma daka girmeshi gashi shima yayi biyu ehe uban me ka tsaya kallo" ran Ilyah a 'bace yace "to haihuwa ai ba ita bace kuma ba'a girma ko 'kan'kanta bane ina ga makocinmu nan malam na gabas ya tsufa tukuf amma baida d'a ko daya kuma ga d'an uwanki Hashimu inace shima bai ta'ba haihuwa ba saini zaki takurawa".

A masife Ramatu tace "dan gwafar ubanka ni kake cewa ina takura maka saboda bankad'a ta same ka"? Shiru yai yana kallon wani gun daban ganin bai tanka ba tacigaba "kasan Allah wallahi a satin nan saika auri Maimuna babu fashi kaji dai ko na fad'a maka garama ka sani" Ilyah bai sake magana ba yasa kai ya fita a gidan tsaki Ramatu tai tana bin kofar da harara mi'kewa Habu yai ransa babu dad'i da yasan abinda zaizo ya tarar kenan ba baizo ba kallon Ramatu yai yana cewa "shikenan zan tafi sai anjima ni zan koma" binsa da kallo Ramatu tai tana cewa "to ka gaida mejegon Allah ya raya" Amin Habu yace yana fita cizon yatsa Ramatu tai tana mi'kewa ta dauko gyalenta tana yin hanyar fita sai magana take ita kad'ai "wallahi Ilyah baka isa ba hauka ma kenan haka kawai kana zaune kara zube ba tsuntsu ba tarko aradu a kwana bakwai dinan saika yi aure kaga hauka.


Bara'atu na kwance a kofar d'akinsu kandiya tana gefenta ta ji'ka magani sai yi take da bakin ta akan ta tashi tasha ta'ki saboda batasan magani kallonta ta kumayi "wai bara meke damunki ne? dama kina da ciki baki fad'a ba amma meyasa kikai shiru Ilyan ya sani ne? Kai Bara'atu ta girgiza "a'a bai sani nima kaina bansan dashi ba badan kin fad'a ba" zaro ido kandiya tai tana cewa "ah lallai kam sannunki da rashin hankali wato cikin na jikin ki kice bakisan dashi ba nifa abin fitina ne banaso Dan ina tsoron jarabar Ramatu kar tace bata yarda ba bazasu kar'ba ba ya kamata kisan yadda zaku had'u dashi ki fad'a masa gara yasan kina da ciki kinji ko".

Kai ta d'aga "to zan fad'a masa saiyazo" zaro ido kandiya tai "sai yazo kuma? Anya bara kinsan me kike cewa kuwa yanzu zuba ido zaki sai ranar da Ramatu ta barshi yazo inda kike, tabdijan to bari kiji sanki 'kanin kafarki idan kina neman zaman lafiya ki tashi kije ki nemeshi ki fad'a masa inta kama kije har gidan" tashi zaune Bara'atu tai tana kallon kandiya tace "zanje amma yanzu bana jin dad'i saina ji sauki" dauko maganin kandiya tai"shikenan kar'ba kisha" kar'ba tai tasha sannan ta aje kofin tare da komawa ta kwanta.


Kwana biyu likitoci suna aiki akan Salamatu amma shiru sai uban ma'kudan kud'i ta ake ci daga ase wannan sai ase wancan gabadaya Sabi'u da habu sun gigice ciwon nata ba sauki sai gaba yake yau idan anyi gwaji ance ciwo kaza ne gobe wani dabam za'a gani hatta likitocin mamaki suke ba'a ta'ba kawo musu patient irin wannan ba.

Asabe na zaune ta zuba tagumi tai shiru sallama Markah tai amma shiru bata amsa ba mamaki ya kama Markah saida tazo saitin kunnenta ta sake rafka mata sallama a firgice Asabe ta d'ago ganin Markah yasa ta sauke ajiyar zuciya batare da tace komai ba sai kallon bahon dake gaban ta tai waken 'kosai ne data sayo ta zuba masa ruwa harya kumbura ya tsotse tana tunani bata sani ba tsaki tai tana sa 'kafa ta ture bahon tana huci zama Markah tai tana sake karantar yanayin Asaben tace "ya akai ne kawata naga kin zauna shiru ko har yanzu maganin bai ciba Balaraben baizo ba ne"?.

Kai Asabe ta d'aga tana cewa "ina yazo kuwa dama yanzu gurin ki nake shirin zuwa Markah na gaji har yau ba wani labari gaskiya muje ki kara rakani gurin bokan nan kila ma baiyi aikin ba kawai kud'i na ya cimin wallahi bazan ta'ba yarda ba saiya biyani tashi muje" katseta Markah tai "a'a Asabe dan Allah ki saurara kiji na tabbata bazai cinye miki kud'i ba 'kadaga aikinsa mai kyau ne" mikewa Asabe tai "a'a nifa banason dad'in baki kawai in zakije ki tashi muje" markah zatai magana yaro yai sallama yana cewa "wai inji wani mutumi wai yana sallama da Asabe" da sauri asabe tace "wani kuma ya sunansa"? "Nima ban sani ba amma yace Balah" da mamaki Asabe tace "Balah kuma wanne balan kenan? Shikenan dai jeka kace ina zuwa" fita yaron yai daidai Asabe ta dauki gyale tace "ni waye Balah a garin nan Markah"? Kai Markah ta girgiza "nima ban sani ba Balah dai daya ne baban Tanko kuma ya mutu saboda ba'kin cikin abin da d'an sa ya aikata bayansa bansan wani ba amma kije ki gano ko Balarabe ne" zaro ido Asabe tai "Balarabe kuma anya? Gaskiya da kamar wuya" "to kije ki gano man ina jiran ki" shikenan bari na dawo Asabe ta fad'a tana fita kamar a mafarki ta ganshi tsaye a jikin bishiyar kofar gidan tabbas Balarabe ne amma anya ita yake nema amma bari ta jarraba 'karasawa tai tana masa sallama ga mamakin ta sai taga ya washe baki yana amsawa "am kaine kake nema na"? "Eh nine fa Asabe kinji mamaki ko kiyi hakuri dan Allah abinda ya faru ranar da kikaje gidana nazo ne muyi magana" numfashi Asabe ta sauke tare da sakin murmushi abun yazo kwarai aiki yaci kallon tai tana cewa "to ina jinka Allah yasa lafiya ina d'iyata Indo"? Da sauri ya amsa "d'iyar ki tana gida lafiya da'kyar ma ta barni na fito sai rigima take wai sai ta biyoni" kai Asabe ta jinjina a ranta tace "humm da dukkan alamu akwai sha'kuwa da so mai karfi tsakanin ka da 'yarka kuma saina rabata.

Abu fa yayi nisa tun Markah tana zaune har ta gaji ta fara gyangyad'i a kan kujera karshe ta kwanta ta kama barci ta dauka abun na wasane taga har ta tashi a barci Asabe shiru to kodai tayi wani wurin ta barta ne tashi tai tana le'ka kofar gida hangosu tai suna tsaye suna hira 'kara murtsuke ido tai ganin da gaske Balarabe ne yasa ta koma tana dariya tace "kai Masha Allah kawar burin ki ya cika saura nawa azo aban alkawarin dubu hamsin cascas nima naje na shana wallahi yau kaza ce abincin darena" tana rufe baki Asabe ta shigo bakinta kamar zai 'bare tana jefar da gyale ya yarfa gud'a tare da tafi tai tsalle ta dire tana rawa tace "ke Markah albishirinki wallahi da gaske Balarabe ne yazo kinsan abun mamaki yadda ya sake yana zuba min zance harda ban hakurin wulakancin da yai min a gidan sa kinsan yana jana da zance karshe sai cewa yai yana sona dan Allah na amince ya aureni kinji wani irin sanyi da naji yana ratsani kai gaskiya na gode Markah aikin bokan nan me kyau ne"

Dariya Markah "aha kin gani ko? Ai dama na fad'a miki karki gaggawa kice aiki baiyi kyau nasan waye bokana shiyasa na kaiki gurin sa dan nasan bazai saki 'kasa a gwiwa ba wannan somin ta'bi ne kika gani Asabe wallahi nan gaba idan kika aje kara Balarabe bai isa ya tsallaka ba muna nan dake zakice na fad'a miki" sauke ajiyar zuciya Asabe tai farin ciki ya gama cikata jiki na 'bari ta shiga d'aki sai gata da dubu hamsin kamar yadda taiwa Markah alkawari ta bata tana cewa "to ko yanzu nasan burina zai cika naga alama ga alkawarin danai miki nan" bakin Markah 'kin rufuwa yai godiya kuwa kamar wanda tayi mata kyautar miliyon ranar wuni tai a gidan sai bayan sallar magriba Asabe tayi mata Rakiya ta tafi gida.

Dalah na zaune Balarabe ya shigo yana zama d'an kallonsa tai tana cewa "daga ina haka na ganka afujajan tun d'azu da kace bari ka dawo sai naji shiru ko nisa kayi ne"? Shiru Balarabe yai yana sake kishingid'a kamar bazai magana sai kuma yace "daga anguwa nake" da sabon mamaki Dalah tace "anguwar gabas ko yamma wacce kaje" da yanayin fad'a yace "anguwar kudu da ta arewa naje ina ruwan ki da samun ido ko da haka kike idan na fita na dawo idan kuma yau zaki fara ki sanar dani" kasa rufe baki Dalah tai sai ido da take binsa dashi jin abinda bata saba jiba to kodai wani ne ya 'bata masa rai a waje sake kallonsa tai tana cewa "kayi hakuri bari a kawo maka abinci" zata mike yace "na 'koshi karki zuba" komawa tai ta zauna bata sake magana ba shima haka kamar kuma an taikare shi zunbur ya tashi zaune yana cewa "Dalah nifa aure zan 'kara" jiki a sanyaye Dalah tace "Allah ya sanya alkairi wacece"? "Kinsan Asabe"? Kaita girgiza "a'a ban santa ba" "to amma ai kinsan wacce ta baiwa Indo kosai kwanakin baya to itace" a d'an zabure Dalah tace "wai matar da tazo gidan nan kwanan baya" "eh ita" da mamaki Dalah ta kalleshi "amma kasan bazawararka ce harda kama ta da balbalin fad'a a gabana"? "Eh ai sannan banji ina son ta ba" sauke ajiyar zuciya Dalah tai "ai shikenan Allah yasa haka ne yafi alkairi idan kuma ba alkairi bace a tare dakai Allah ya baka wacce ta fita" caraf Balarabe yace "ai itace ma ki daina yimin fatan tsiya kodan kina ba'kin ciki zan karo miki kishiya ne" kai Dalah ta girgiza bata sake magana ba sai tsananin mamaki daya gama cika ranta mutumin daya hau fad'a ranar da tazo kamar zai daketa shine kuma yau me cewa yana sonta anya kalau ta barshi abun nan da dubawa.

Lokacin rabon da habu yake yi yayi ya sayo atamfofi da yadika kamar yadda ya saba gida gida da majalinsa haka yake rabon kaya da kud'i sosai yake shan addu'a shiyasa koda yaushe samunsa yake bun'kasa ga bikin suna ya gabato Habu yayi shirin sunan yarosa ya sayo komai da manyan raguna guda biyu ba'kin 'yan uwa kuwa har sunzo ana gobe suna jaririn ya rasu😣 innalillahi kamar babban mutum ne ya rasu haka gidan ya cika da jama'a kofar gidan ma haka sosai Habu mutuwar ta ratsa masa jiki ba shiba hatta sauran jama'a sun jajanta masa washe gari kowa cewa yake saidai a hakura da daurin auren Habu yace a'a kawai a d'aura haka akai daurin auren babu wani armashi ranar da yaron ya cika kwana bakwai da rasuwa ranar aka rako A'i.

Tashin hankali da bala'i iri iri Ramatu ta ri'ka saukewa Ilyah ta hana shi zaman lafiya har saida taga ya auri Maimuna sannan bakinta yai shiru ta 'kyale shi ya huta bayan sallar isha kad'an sai ganin tawaga Ramatu tai tana shigowa duk zaton ta masu rako Maimuna ne amma sai taga sunyi hanyar d'akin Bara'atu da gudu taje ta sha gaban su tare da cewa.

"Kai kai kai ya haka ku tsaya meye wannan daga ina zuwa ina?".

Da mamaki wata 'kanwar kandiya tace ", a'a kamar ya daga ina zuwa ina wanne wacce irin tambaya ce Bara'atu mana muku rako ta dawo d'akin mijinta" wani kallo Ramatu ta watsa mata tana cewa "ke kuma me kamar 'kanzo ki rufa min baki ban sauko dake ba da wannan asararriyar nake wato tsabar rashin zuciya ba'a je bikonki ba shine kika d'ebo wadannan murd'a murd'ar 'kafafun naki masu zubin doyar kudu kika dawo ko to wallahi bazaki shiga d'akin nan ba sai an kawo Maimuna kinji na fad'a miki dai ko"?.

Ri'ke baki Kulu tai tana kallon Ramatu tace "to ikon Allah wannan wulakancin har ina wai madai tsaya ma dai tukuna wace wannan me maganar uwarsa ce ko 'yar gayyar sod'i ce? Dan duk wacce tasan me take bazata tozarta mu haka ba"

Wata uwar harara Ramatu ta sakar mata tana sake tare kofar d'akin tace "au sannu isashshiya to uwar sace idan bakisan Ramatu ba ko kinajin labari na yau kin ganni" kai Kulu ta jinjina "tabd'ijan Allah ya sauwake wannan rashin arzikin naki har yai yawa ai da Kandiya zataji shawara ta Bara'atu bata samu gurin zama ba hartai shanya ba" kanta Ramatu tai "au jimin makirar mace dama ina ta isa samun gurin zama a gidan nan can da tsiyarta Ilyah yafi karfin aurenta dan haka zaku iya tattarawa ku juya inda kuke fito harda yin 'karyar tana da ciki wata shida ai zamu gani idan wata taran tayi kuma wallahi ba kinji nace haka ba nan gaba kikace ya 'bare sai kin ci gwafar ubanki" duk zaro ido sukai Dijalle zatai magana sukaji ana sakin gud'a alamar an kawo Maimuna matsawa Ramatu tai tana musu kallo she'ke'ke tace "to yanzu kam zaku iya shiga mayu kawai" tana fad'in haka tai gaba.

Da kallo suka bita cikin takaici Kulu tace "ke Barah baki zauna a gidan nan ba komawa zamuyi ke dama ba sonki take ba amma saboda tsabar rashin sanin ciwon kai kika yarda ki sake zama dashi" tsaki Dijalle tai tana cewa "to gashi kinga alama kuwa a gaban mu ma tana wulakanta ta balle kuma taci gaba da zama da d'anta yadda bata da mutuncin nan har dukan suruka zata iya" 'kanwar kandiya dake kallon yadda jikin Bara'atu yai sanyi tace "to yanzu me kuke so ayi zamu juya da itane"? Caraf Dijalle tace "me zai hana Ilyan wa? zata samu wanda ya fishi amma wallahi yadda uwarsa nan bata da mutunci tasa ya kara aure idan Barah tace zata zauna ma ba'kin ciki ne zai karta kuzo kawai mu tafi" juyawa sukai zasu fita Ramatu dake kallon su tace "as as as a gaida na gaba mayu kawai masu ba'kin ido" babu wanda ya kula ta a cikin su suna fita kofar gidan suka hadu da Ilyah yana shirin shiga da mamaki yace "ya na ganku haka akwai abinda ya faru"? Yai tambayar dan shi ko kad'an bai kula da Bara'atu ba ya dauka tana ciki ko Ramatu tai musu wani abu dan yasan sai ita gani ba 'kyalewa.

Kulu ce tace "to me zamuce Ilyah mahaifiyar kace ta wulakanta mu shiyasa mu kuma zamu juya da Bara'atu dan bazata zauna hawan jini ya kama ta ba tunda har mahaifiyar ka tana maganar cikin 'karya gareta".

"Subahanallahi yaushe wai duk yanzun hakan ta faru? Ai ban sani ba dan Allah kuyi hakuri abinda tai muku muje ciki" Karima 'kanwar kandiya tace "a'a Ilyasu babu cikin da zamu koma gaskiya gida zamu mayarta ba abinda Bara'atu zata d'auka a gidan ka sai wahala da damuwa dan haka kayi hakuri kuzo mu tafi" ganin da gaske tafiya zasuyi yasa a rikice Ilyah yace "dan girman Allah kuyi hakuri kuzo muje ku mayar da ita nayi muku alkawari babu abinda zai sameta bazan bari ba" shiru kowa yai Kulu tace "shikenan amma gaskiya ka kula sosai da gidan ka domin akwai matsala" zan kula karku damu ina son Bara'atu bazan bari a wulakanta taba" sun d'an ji dad'i ganin ya damu da ita ko tanan zataji sauki dan haka suka amince ya musu jagora suka mayar da ita har d'akinta tare da mata fad'a cewa duk wani abu zaisa ta tashin hankali da uwar mijin ta koda kishiyar ta ta kiyaye ta ri'ka kawar dakai akan abinda bai shafe taba tunda tasan Ramatu ba mutunci gareta ba karta shiga harkarta karta bari wani abu ya shiga tsakanin su.

Amma asubar fari gari da duhu ko assalatu ba'ai ba Ramatu ta fito daga d'akin ta tana zuwa kofar d'akin Bara'atu ta soma bukawa da karfi tana cewa "ke tsinanniya bunjinjimar asara fito ai ba barci kika dawo yiba zaki bud'e ko saina karya murfin kofar na shigo da kaina na fito dake na miki dukan tsiya yar fatararru" cikin takaici Bara'atu ta bud'e kofa tana kallon Ramatu dake tsaye zatai magana Ilyah ya fito daga d'akin maimuna cikin rashin jin dad'i yace.

"Wai dan Allah babah me yasa kike haka ne da asubar farin nan me zatai miki kika zo kina buga mata kofa duk makota na jinki".

Kansa ta koma "dambun ubanka zatai min asararre waini Ilyah kodai bankad'add'iyar matar nan asiri tai maka ban sani ba babu dama nayi magana saika mayar min bakaso a fad'i laifinta nuna Bara'atu tai da yatsa amma Allah ya tsinewa uwarki kandiya dan komai silarta ne itace ma'kasudin komai bari gari ya gama wayewa wallahi ko bari su karya cikin dad'in rai bazan ba sainaje na 'kaddamar musu bala'i iri iri dama ai tasan hadina da ita ta iya d'ebo ba'kin ido tazo a gantsara mata abinci taci zakuci gwafar ubanku ne daga ke har tsigalgalar uwar taki".

"Dan Allah babah kiyi shiru wannan fa zubar da girma ne" Ilyah yai maganar ransa a 'bace.

"Kai zanci malafar ubanka idan bakai min shiru ba so'ko'kon banza sakalin asara wanda kare ya lashewa zuciya kayi asara tunda harka za'bi matarka akan ni da nake uwarka".

Had'e rai Ilyah yai "ni bance miki na zabeta akanki ba fad'ar kice kawai daga naga kinyi ba daidai ba nayi magana gaskiya abinda kike bakya kyautawa wannan fa ba neman girma bane".

Caraf Ramatu tace "dama nace maka ina neman girma ne? Karta girmama nin mana taga yadda zanci 'kashin ubanta tasan karon mu da ita ai abin baya mata dad'i" Ilyah bai sake magana ba ya kalli Bara'atu yana cewa "koma d'aki ki kwanta" da sauri Bara'atu ta shige cike da tsoro ta rufo kofa hararar sa Ramatu tai "humm Ilyasu kayi asara wallahi kaji jiki da ina da wani d'an bazan zauna a gidanka ba saidai ka nemi wata uwar badai niba" shikam tari da bai kama shiba bai sake ce mata uffan ba ya juya shima yana komawa d'akin amaryarsa yayin da Ramatu taci gaba da balbali a tsakar gida ita kadai taja kujera ta zauna sai zazzaga fad'a take bakinta har kumba yake ta'ki yin shiru duk ta dami jama'ar anguwa sai Allah wadai suke har akai assalatu aka shiga masallaci bata tashi ba balle tai alwala da sallah saida gari yai haske sannan tayi niyyar yi.

Habu ne zaune yayi tagumi gaban Salamatu dake kwance sharkaf kamar gawa Sabi'u na gefensa sunyi shiru babu mai cewa uffan shigowa d'akin Rakiya tai da sallama cikin sanyin jiki tace "ya jikin nata"? Kai Sabi'u ya d'aga "da sauki Rakiya" zama tai ta wajen 'kafafun Salamatun tana cewa "amma me gida tunda likitoci sunce ba ciwon asibiti bane mezai hana muyi na gargajiya kaga ciwon gaba yake 'kara yi kuma kalli wani abun tsoro yadda jikinta yake 'kai'kashewa kalli yadda fuskarta ta koma kallonta kamar bana mutane ba" ta karasa maganar tana fashewa da kuka.

Kallon Sabi'u Habu yai cike da damuwa yace "yaya Sabi'u gaskiya wannan ciwon na babah ba 'kalau ba abun da tsoro tunda kaji likita yace a dawo gida ayi na gargajiya lallai akwai abun dubawa ga kuma kullum sai anyi mata 'karin ruwa amma yan awanni ace sun tsotse wanne irin abu ne wannan kodai mayu ne"? Numfashi Sabi'u ya sauke tare da girgiza kai ganin yadda bakinta ke kakkarwa ya kalli Habu yana cewa "nima tunanin dake raina kenan saidai bamu tabbatar ba na samu malam Zayyanu jiya akan batun yace yasan wani mutum mai maganin hausa duk abinda ya shige duhu indai anje wurinsa insha Allahu ana samun waraka dama jira nake alhaji Hamidu ya dawo daga saudiyya kud'ina da yake gurinsa ya bani sai mu tafi" gyara zama Habu yai yana cewa "ba matsala yaya Sabi'u indai maganar kud'i ba damuwa mudai lafiyar ta muke bukata bari naje gida na dawo saimu tafi tunda kaga yanzu na iya motar dana sayo ba haya nake bada itaba sai muje" mikewa Sabi'u yai shima yana cewa "to bari naje gurin malam Zayyanun yamin kwatancen garin kafin ka dawo" Rakiya ya kalla "ki jirani a gurinta ina zuwa" to tace yayin da suka fito tare Sabi'u yai gurin da zai sami malam Zayyanu Habu kuma yai gida.

Zaune ya sami Saude da amayarsa A'i dan Binta kam tana gida wanka ganinsa da damuwa yasa Saude cewa "lafiya meya faru naganka haka"? 'Dan tsayawa yai yana kallon Asma'u dake zaune gaban A'i tana mata kitso yace "eh lafiya babah zamu kai gurin magani wani gari yanzu" "subahanallahi sake tashi jikin yai"? Wucewa habu yai zuwa d'akinsa yana cewa "ai dama baya sauka kullum a tashe yake" shiru sukai cike da jimami harya fito Saude tace "bari muje mu gano ta A'i bar kitson nan sai mun dawo" mikewa suka kowa na dauko hijab suka fita motar na waje yace su shiga tunda shine zai jasu shiga sukai duk inda ya gifta da ido ake bin motar masu hassada nayi masu tayashi murna nayi saidai yan ba'kin ciki sunfi yawa a sanda sukaje al'ajabine ya kamasu ganin yadda kumfa ke fita a bakinta sai mummurd'ewa take tana surutai duk zaro ido sukai jiki na rawa musamman A'i da sauri tai baya Dan akwaita da tsoro cicci'bota habu da Sabi'u sukai suna fita da ita wajen motar da'kyar suka tan'kwasata suka sata a cikin kafin suka shiga habu na baarwa Saude sakon yadda zasuyi amfani da kayan abinci kafin suka dau hanya.

Dalah na zaune Balarabe ya shigo da kaya cikin leda a hannunsa ya aje mata ba magana d'agowa tayi a damuwance tana kallon sa kamar hawaye zai zubo mata dan tasan ba kalau ba yanzu gabadaya ya canza ya zama wani iri tace "wannan meye a ciki"? Bai kalleta ba yace ki bud'e ki gani mana ba kina da ido ba"? Bud'ewa Dalah tai ganin kayane yasa tace "na maye"? Kai tsaye Balarabe yace "na fad'ar kishiya ne kin gane aure zanyi Asabe zan aura dan haka duk wani shirginki da kika san yana wancan d'akin ki tattare zan gyara" sauke zazzafan numfashi Dalah tai tana cewa "shikenan Allah yasa haka ne mafificin alkairi" Amin inda gaske kike" ya fad'a yana Mi'kewa zai fita sai kuma ya tsaya tare da cewa "nayi gidan Asabe kada ki dafa abinci dani" kafin Dalah tai magana Indo tace "baba ka taho min da biskin" "da uban biskin zan taho miki dashi tsohuwarki ta baki kud'i kije shagon Habu ki sayo ni bani da kud'i" yana fad'in haka yai waje yabar Dalah tana sharar 'kwalla Innalillahi wa

Please Login or Register in order to submit comment