Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inna ilaihi raji'un tun ba'aje ko'ina ba Balarabe ya fara canzawa ina ga yayi auren kenan.

Tafiyar su habu da kwana biyu Rakiya ta haihu gashi ba waya a tsakani balle ta fad'a sai wata tsohuwa ce daga ma'koftansu take kula da ita da jaririn mutane nata zuwa barka ranar suna itace ta za'ba masa tunda Sabi'un bayanan cikin dabbobin da yake kiwo aka yanka mata raguna biyu Binta ma tazo bikin sunan saboda tayi wata biyu jira take Habu ya dawo daga tafiya ta dawo d'akin ta gashi dama Bashir ya bar gida ya tafi dutse karatu sai lokaci lokaci yake d'an zuwa gida su gaisa yana can yayi gidansa da matarsa harda d'an sa Ahmad.

Suna zaune anata hira irin wacce akeyi idan an had"u a gidan biki Dalah da shigo da atamfar biki a hannunta suna gaisawa ta shiga d'akin Rakiya domin 'kawarta ce sosai tun suna yara sakamakon zafi yasa Dalah ta fito waje tana zama cikin mutane a 'kar'kashin bishiyar badalar dake tsakiyar gidan yafendo ce ta kalleta tana cewa "sannu 'yarnan kinji Allah ya miki tsari da sharrin wannan muguwar mace Asabe da mijinki yake kokarin aura" zaro ido waje Hajjah tai "ke wacce Asaben amma dai ba Asabe ta bayan layin muba matar da tai zaman logus ko lagwas (Lagos) yake na manta sunan garin ai itace zai aura"? Kai yafendo ta d'aga "eh itafa" har 'kwaruwa Hajjah take waje tafa hannu da cewa "Innalillahi amma gaskiya Balarabe baiyi zabin mace ta gari ba na taya ki ba'kin ciki Dalah Allah ya tsare ki daga sharrin ta dan wannan matar kwalba ma haka ta ganta" "aike dai kawai bari dan ko wancan mijin nata ma ba mutuwar Allah yai ba kashe shi tai haka mutane suke cewa dama saboda dukiyar sa ta aure shi* "oh ni kinji irin abun ko? Kuna zamanku lafiya zai yayo muku bala'i ke dashi" ita dai shiru tai kawai tana sauraron su yayin da suke tsinka mata zuciya da maganganunsu amma ya zatai bayan ha'kuri da addu'ar Allah ya tsare ta da tarkon Asaben.

Batun su habu kam sunje gurin me magani mutumin ya matukar 'kwarewa a iya cire aljanu komai taurinsu amma me abun ya bashi mamaki babu aljanu jikin Salamatu kuma ba mayu bane yayi iya bakin kokarin sa amma baiga komai ba dan haka shawara ya basu cewa kawai saidai ai mata sauka ko Allah zaisa a dace damuwa da tashin hankali baisa sun iya ce masa 'kala ba sai shine ya fahimci suna wani hali na d'imuwa ya taimaka musu amma dai labarin yana nan yadda yake babu sauki ko sasssuci a jikin Salamatu sunfi wata yana abu d'aya karshe yace sunyi hakuri su koma gida su sake jarrabawa zuwa gurin wani malamin ko zasu dace shikam ya gaza haka suka tattaro suka dawo gida jiki a sanyaye mutane sai zuwa dubota ake harda masu kuka ganin yadda ta koma kamar ba mutum ba ta wani rame halittarta ta canza.

Wata biyar tsakani Salamatu tabar duniya😥 wanda kowa yana mata fatan mutuwa ta zama hutu gareta madadin wuyar da take sha lokacin da Ramatu taji mutuwar cewa tai "uhm kace yau Salamatu da shan duka a kabari🙊" to waiwaye ance adon tafiya ne amma fa ta tuna me wadannan halittun suka ce mata koba dad'e koba jima abinda tai zai dawo kanta nanfa tashin hankali ya same ta ta ri'ka gurza kuka a gidan mutuwar nan kowa yayi zaton akan Salamatun ne ashe ita abinda ke damunta dabam ko gida data koma 'kin cin abinci tai har dare saida Ilyah ya shigo Bara'atu take fad'a masa ya shiga d'aki ya ganta zaune tayi tagumi mamaki ne ya kama shi yaushe rabo yaga Ramatu a haka ai harya manta zama yai yana sake kallon ta da karantar meke damun ta yace.

"Babah lafiya me akai miki"? Jin tashin murya yasa a gigice Ramatu ta tashi a guje tana fad'awa saman katifa tare da jan bargo ta lullu'ba muryarta na rawa tace "na shiga uku na lalace wayyo Allah na dan Allah kuyi hakuri wallahi ba a son raina bane dama fa nace muku na ha'kura kune kuka 'ki wallahi ba ruwana nidai ku 'kyaleni".

Tsananin mamaki ne ya kama Ilyah wannan kuma lafiya maganganun me take haka kamar ta samu ta'bi yaye mayafin data lullu'ba yayi yana cewa "babah nine fa me kikeyi ne haka"? Jin tashin muryar Ilyah yasa ta bud'e ido tana kallon sa tare da sauke ajiyar zuciya tace "Ilyah kaine aina dauka wadannan tsinannun ne" da alamar tambaya yace "su waye tsinannu"? Dan shi ya dauka da Bara'atu da Maimuna take sai kuma yaji tace "wasu tambad'add"un halittu ne saida nace musu bana so na ha'kura amma suka 'ki" Ilyah jiyai hankalin sa ya sake tashi gashi ta kuma lumar dashi ya kasa gane inda ta dosa........................


Tunanin sane ya katse jin ta fasa ihu tana cewa "gasu nan sun shigo ka gansu nan da yawa idanuwan su yayi ja kallona suke wayyo Allah zasu kama ni zasu tafi dani" habawa a guje Ilyah yai tsalle ya shige bayan murfin kofar d'akin cike da tsoro daidai su Bara'atu sunzo ganin yadda Ramatu take 'barin kwanuka duk ta hargitsa d'akin yasa mamaki suma ya kamasu saidai da yake sun san rigimammiya ce zata aikata fiye da haka ma yasa suka tsaya kawai suna kallon ta sai susa take tana yagar gashin kanta ganin takalmin Ilyah a kofar d'aki yasa Bara'atu cewa.

"Kana ciki ne"?.

Jin anyi magana yasa Ilyah kallon Ramatu idanuwan ta sun sauya kala a tsorace ya sand'a zai fice yuuuu tayo kansa tana cewa "ina kuma zaka je bazaka tsaya muyi wasa ba zonan taho muyi rawa" ganin ta kawo masa rifka yasa yai wani irin ihu tare da dira tsalle sai gashi a waje da mugun 'karfi ya zuba a guje ya fad'a d'aki yana banko kofa kaiii suma aguje suka shige d'ayan d'akin yayin da Ramatu ta d'auki ta'barya tana dukan kofar kamar me karfin doki "dan uwarku bazaku bud'e min kofa ba matsiya wato dodo kuka mayar dani tsinannu wallahi gobe sai Ilyah ya sake ku sai kun bar gidan bankad'add'u 'ya'yan talakawa" dukan kofar take da karfi suna jinta kowa jiki na 'bari haka ta kwana tana abu daya har asuba sannan ta koma d'akinta ta sheme ta kama barci babu wanda ya iya fitowa a cikin su duk da sunji shiru an rasa me wannan jarumtar saida suka ji shirun har yayi yawa sannan suka bud'e kofa suna le'ke ganin dai bata nan yasa suka fito suna 'kwan'kwasawa Ilyah shiru yai yana jinsu yay kamar ya mutu🤣 saida sukai magana ya tabbatar sune sannan ya bud'e shima ya fito yana zazzara ido ya had'a gumi shir'bim sauke ajiyar zuciya yai yana kallon kofar d'akin ta yayi 'kasa da murya yana cewa "ina take"? suma kallon kofar d'akin sukai Maimuna tace "kila tana ciki" tura ta Ilyah yai "jeki gano😂" tirjewa Maimuna tai tana had'e rai tace "ba kaine namiji ba kaine ya kamata ka gano" shiru yai alamar bazai iya ba sai kuma ya kalli Bara'atu "ko ke zaki gano mana"🤣? Itama baya taja tana cewa "a'a wallahi bazan iya ba ni dama jinin mu bai had'u ba bari ma kagani sallah zanje nayi gashi har rana ta fito muna kulle kamar wanda mukai lefi" tana barin gurin itama Maimuna tabi bayanta dole tasa Ilyah tafiya a hankali yana d'auke sau yaje ta window ya le'ka ta tana kwance tana sharara bacci dur'kusawa yai ya dauki takalmi shima ya tafi sallah daga nan ya zarce gidan malam Zayyanu ya masa bayani tunda dama shine wakilin Baffah".

Balarabe ya auri Asabe ta tare abinta cike da murna dan tana sonshi sai zuba masa soyayya take irin ta 'yan bariki Dalah kam ta zama abar tausayawa gashi yanzu hatta Indo bai damu da ita sosai ba ada baya so yaji tayi kuka ko yaga hawayen ta amma yanzu ko zatai kukan jini yana ji bazai kula ba a yadda ake ciki ko mutuwa Indo zatai a yanzu kila bazai nuna damuwa ba yafi son agolarsa bahijjah yar gidan Asabe akan Indo yakan sayo mata komai jiki na rawa ya bata ya dauketa suje yawo amma banda Indo saidai tace ya mata haka a da😢.

Hummm duk nisan jifa zai dawo kasa inda jirgin sama yaje wata rana za'a cewa kunkuru barka da zuwa kuma duk nisan turin da za'ai wa lilo zaije ya dawo inda yake👌 Ramatu dai an haukace gara Salamatu dan ita yanzu inta faki ido ta fito sai bola kuma bakinta baya shiru tana fad'a-fad'e da zage zaga dama hali a jikin rai maganganu iri iri wanda ba'a san dasu ba sai fad'a take haka duk sunan mutumin daya zo bakinta a 'kauyen inta fara ambatonsa tana tsine masa tana 'kwal'kwale masa albarka saita wuni batai shiru ba kullum idan an rasa ta dama ansan inda za'a sameta saidai a tsinto ta kan bola tana ta tsintar ledodi tana daurewa a jikinta tana surutai kala kala wanda babu wanda yasan me take cewa wanne irin yare ne sudai yan 'kauyen basu ta'ba ji ba saifa a bakinta gajiya Ilyah yai ga kud'i yanzu yana ta bun'kasa amma jinya sai cinyewa take dan haka ya yanke shawara ya dauko wani malami cewa yazo ya ganta yana zuwa da fara aiki Ramatu tahau ihu iri iri da kururuwa yana yayyafa mata ruwan addu'a sai burgima take tana tsalle ta tumu a kasa timm ta tashi ta daki bango tai girgiza har katanga saida ta ture ta zube mutane kwa sun cika gidan kamar anyi busa sai gulma ake babu wanda ya ankara har malam kawai sai gani akai ta zuba da gudu tana yage yage a guje Ilyah da malam suka bi bayanta yan gari ma d'uuuu suka bisu aguje dan ganin 'kwa'kwaf daji Ramatu ta ri'ka linkuwa suna bita ga wata ba'kar iska me duhu data taso ta lullu'besu da guguwa a cikinta da 'kura duk 'kasa ta cika musu ido amma basu daina binta ba kwatsam sukaga kogi a gaban su ruwan har kumfa yake yana murd'ewa da ambaliya amma Ramatu takai take gudu kamar tana bin normal hanya tsayawa sukai suna haki ganin zata bace musu malam yace "ba ruwa bane sharrin miyagun makiya shed'anu ne muje cikin azama suka fara bi ta kan ruwa aiko sai sukaji kasa kawai suke takawa ashe rufa ido ne suna shiga wani ba'kin daji sukaga abu jimmmn ya fad'o gaban su wani shirgegen dodo jikinsa duk gashi ga jan ido turus mutane sukai wasu suka yanke jiki a gurin suka fad'i a sume wasu suka juya da aguje dariya dodan yai wanda tasa bishiyoyi ganyensu ya fara kad'ewa ya zuba muryarsa kamar saukar tsawa yace.

"Me kuke nema anan waccan tamu ce ku juya inda kuna son ranka Wanda kuma yake son muyi fate fatansa to yazo" malam na haki cike da gajiya yace "waye kai" hhhhhhhhhhh!!! Dariya ta hauka da tashin hankali dodon keyi yace "baka sanni ba kawai kalleni a haka saidai zaku wahalar da kanku domin ta zama tamu aiki tasa mukaiwa kishiyar ta har muka zu'ke mata jini ta mutu kuma dama mun fad'a mata aikin zai dawo kanta ta duk daran dad'ewa ta amince dan haka yanzu ido ne naku babu abinda ya isa ya 'kwaceta a wurin mu tayi bankwana kenan bazan hana ku binta ba ga hanya nan saidai zaku mutu hhhhhhhhhhh ku taho👻👹" yana fad'in haka ya 'bace addu'a malam yaci gaba tayi ba fashi da gudu suka sake yin dajin can suka hango Ramatu a wani wuri tana lilo abinda ya basu mamaki babu alamar igiya amma bala'in hillon da take ya 'baci addu'a malamin keyi yana nifar inda take yaje gaf da ita yaga wani ba'kin abu yazo ya shiga jikinta bai fasa ba ya sake matsawa wani irin tattarashi yeji anyi kafin ya ankara an li'kashi da kasa da sauri ya mike bai fasa addu'ar ba gashi gurin sai canza kala yake yana duhu kamar yanayin almuru Ramatu kuwa kamar wacce ake 'kara hilla ta can ta tsaya sai kuma ta dirgo ta sauka ta soma wata kalar tafiya kamar yar maye tana rangaji tayi gaba tayi baya ihuuuu ta zunduma tana rike kanta wanda malam yai amfani da wannan damar zai ri'ko ta aka daukeshi fiiiii kiffff aka watsa shi gefe har rawaninsa Saida ya fad'i yana yai yunkurin tashi da sauri yana sake nufota kafin ya karaso inda take sai gani sukai ta zama ba'ki 'kirim kamar ta 'kone bata da kyan gani daga haka ta zama 'bakin murtukekken haya'ki ta 'bace 'bat🙊😣 shikenan.

Haki malam keyi sosai yana innalillahi wa inna ilaihi raji'un mutane na amsa masa kowa jiki na bari malam yace "ya kamata mu barnan yanzu yanzu" aguje kowa ya ruga sai gware suke wadanda suka fad'i ana take su a haka suka samu da'kyar suka fita dajin suka koma gida da labarin abinda suka gani gari sai gulmar ake ana Allah wadai da halinta dama itace taiwa Salamatu asiri ya dawo kanta kowa da abinda zaice shikenan fa'kat masifa ta mutu Bara'atu ta huta ba wanda zai fadi abun alkairi a kanta sai na tsiya ga Ilyah bai nuna alamar zaiyi wani zaman makoki ba ko kadan kawai yadan zauna wunin ranar amma shikenan ya basar sai ranar sadakar uku.

Dalah na zaune tana sa'ka mifici na saidawa da take Indo tana kefenta sai bori take mata ta'ki cin abinci wai saita bata kud'i ta sayo irin alewar bahijjah itakuma sisi bata dashi sauri take ta karasa maficin ta bata takai shagon tunda dama mai shagon yana Sara saiya saya ya bata alawar shigowar Balarabe kenan jin yadda take kuka harda shid'ewa ya daka mata tsawa "uban me akai miki zaki damu mutane da koke koke kamar gidan mutuwa"? Yaro ba hankali kuma ka saba mahaifin ka na sake maka da sauri ta tashi tayi gurin sa bataji wannan tsawar dayai mata ba da gudu taje zatai masa oyoyo tana rike shi ya tureta yana wuce ciki kifawa Indo tai tana kuka da sauri Dalah ta mi'ke tana d'ago ta tare da kad'e mata kasar jikinta ta rike mata hannu suka koma bata karasa maficin ba tsabar takaici haka ta bata cike da damuwa tace "kar'bi kije gurin Bintan gidan Habu ai kinsan gidan ko"? Kai Indo ta d'aga tana goge hawayen fuskarta tace "eh na sani" cigaba Dalah tai "maza ki bata kice wai ta baki kud'in zaki sai alewa inji ni sauri" kar'ba Indo tai zata fita Asabe data fito daga d'aki ta riski karshen zancen Dalah bata ankara ba sai jitai an rafka salati a bayanta Asabe na cewa "to sabon salo gemu a kafad'a malam fito kaji wata magana ga Dalah nan ta aiki Indo maula dan a zageka a gari ace 'ya daya ka kasa mata abinda uba yakewa 'yarsa" kamar an hankad'o Balarabe ya fito yana cewa "meya faru" nuna Indo Asabe keyi "kalli man wai mafici ta bata ta wai waye a cikin matan Habubakar tace wai ta bata abinci yanwa take ji mu bamu girka ba tun jiya kaji fa bayan d'azu ta sauke abincin dan kawai tasa a gari a zageka" kumbura sosai Balarabe yai yana huci kamar zai rufe dala da duka "oh yanzu kuma sharrin da zaki min kenan daga kin bar wannan saiki koma wannan kinje gari kin yad'a wai banai miki sutura duk kayan da kike sawa kece kike dinka abinki na shareki ban nuna miki fushina ba shine kuma yanzu zaki fara tura ta maular abinci bayan ban rageku da komai ba ke wallahi Dalah kina da ba'kin hali indai baki canza ba zan dauki mataki a kanki" juyawa kan Indo yai yana fisge maficin "kema dan ubanki bani nan shekiya munafika tun baki girma ba uwarki zata koya miki halin tsiya halin karya gwafar ubanki zakici wallahi" ya karasa maganar yana ralla mata maficin aka sannan ya jefashi a wuta ya kone dur'kusawa Indo tai a gun tana kukan azaba Dan yajin dukan har 'kwa'kwalwata nuna Dalah yai da yatsa wacce take tsaye hawaye fal idonta yace "ke kuma daga yau sai yau kinyi na farko kinyi na 'karshe kada tsautsayi yasa na kara jin kin tura gidan uban kowa maula biyar bana tauye muku hakkinku wallahi tallahi idan kika sake makamancin haka saimu kwashi dambun tsiya dake sakarya bagidajiyar mata kawai" yana fadin haka yai waje yana maganganu dariya Asabe tai tana kallon yadda Indo keta mulmula gurin daya rad'a mata maficin tace.

"Hummm ubanku zakuci daga ke har tsogalgalar uwar taki zakusan wace Asabe dan wallahi sunana kawai kuke ji wannan somin ta'bi ne ban nuna muku komai ba yanzu aka fara wasan za'a kwashi yan kallo nan gaba kuma ki jira ki gani" d'aki itama ta shige tabar Dalah tsaye kamar bishiya dukawa tai tana d'ago Indo suka koma kan tabarma ta goge mata hawaye cikin danne damuwar ta dason farantawa Indon tace "kinga kiyi shiru ki daina kuka indai akan alewa ne zan sayo miki" cike da yarinta Indo tace "baba ne zai taho min da ita"? Kallon ta Dalah tai da sauri jin furucin datai Allah sarki cikin tausayawa wato dai babu abinda ya canza harta manta da abinda yai mata yanzu amma saboda ta kwantar mata da hankali tace "eh shine zai taho miki da ita kinga d'auki abincin kici zai kawo miki" da murna fal ranta ta dauka ta fara ci Dalah ta zuba mata ido kawai ta fad'a kogin tunani.

A ta'kaice bayan wani d'an dogon matsakaicin lokaci Bara'atu ta haihu yan biyu maza Hassan da Hussain haihuwar su day wata sha biyar ta sake haihuwar mace aka saka mata Nafisa Maimuna itama ta haihu mace sunan yarinyar salmah ta sake mace da namiji amma akwai gaf sosai tsakanin su da shekaru.

Haka a bangaren Habu ma A'i ta haihu mace sunan yarinyar Jamila tsakani shekara biyu da Binta itama ta haihu mace Habu yasa sunan mahaifiyarsa Hauwa (Amatullah) watan Amatu goma sha daya Saude ma ta sake haihuwar mace Aisha daga nan nefa rayuwa ta soma bun'kasa ahli yayi yawa saidai babu wani kyakkyawan zumunci tsakanin su da Ilyah baya sauraron su ko kadan kamar baisan da zaman suba abun ya damu Habu dan haka ya samu Sabi'u sukaje gurin malam Zayyanu aminin Baffah tare da zayyane masa komai akan ya kira Ilyah ya masa nasiha amma da Ilyah yazo bayan ya gama sauraron dalilin kiran bud'ar bakinsa cewa yai shifa kar a takura masa baida wasu yan uwa bayan matansa da 'ya'yansa da kuma dukiyar sa wannan abinda ya fad'a ya matukar 'kona musu rai babu irin shan kan da wa'azi wanda malam Zayyanu baiyi masa ba amma karshe mikewa yai ba magana ya karkad'e musu 'kura yai gaba duk binsa sukai da kallo ransu a 'bace musamman habu da yake jin kamar ya she'ka aguje ya sha'ke masa wuya hakuri da magana mai dad'i malam Zayyanu ya ri'ka musu da nuna musu cewa zai dawo kan hanya zai shiryu kuma suma suna yi masa fatan hakan kafin lokaci ya'kure masa.


Bayan d'agowar yaransu sun kasance babu makaranta ta zamani basu santa ba basayi saida aka zowa mai gari da takarda daga 'karamar hukumar da take mulkarsu dan haka tun jami'an basu tafi ba mai gari yasa aka tara magidanta na garin suyi musu bayani yadda zasu gane karshe bayan su tafi mai gari yasa akai shela nan fa gari ya dauka harda masu zagi wai za'a toshe musu hanyar samun kud'i haka kawai za'a 'kir'kiro makaranta wai ita boko wasu suna ce wallahi yaransu bazasuyi ba kaf 'kauyen baifi mutum biyar ne suka yarda da abinda ba'kin suka zo dashi ba ba'a garin 'karamar hukumar tai makarantar ba a wani babban kauye ne kusa dasu saidai garin nada girma sosai amma dai 'kauye ne bayan an kammala a gari tsirarun mutane ne suka shigar da yaransu wannan makaranta wadanda basu amince ba sunfi yawa suna yi musu kallon wawaye ganin babu yara sosai a makarantar ga malamai 'kwararru yasa suka kai kukan su cewa babu d'alibai wakili ya sake turowa aka sake yin shela ana bi gida gida ana daukar sunan yara da basu uniform da littafai da jaka da sandals kyauta ga motar yan makaranta school bus 🚌 wacce zata ri'ka fitowa dasu tana kawo su idan an tashi driver ya mayar dasu amma duk da haka a banza wannan baiyi aiki ba dan wasu iyayen har 'boye 'ya'yansu suke dan a 'bangaren Ilyah ma cewa yai Allah ya sauwake makarantar 'karyace da yaudara kila nan gaba su sace yara su gudu babu wanda zaiyi a yayansa kadan ne a garin ke zuwa amma habu dai babu wanda aka bari cikin yaransa kowa na zuwa shi baya jiran motar daukar d'aliban ma a tasa yake d'iban su yakai yawan zuwa da yake har tasa malaman sukai sabo dashi suka sanshi sosai sune silar da aka dawo kiransa da malam Habu yan gari na masa isgili wai kodai yana cusa kaine dan su d'auke shi koyarwa.

A wannan garin kuma da akwai wani mahauci ana kiransa 'kwalisa yara suka samasa sunan sakamakon idan yaje rafi yayi wanka duk sai jikinsa yai farin ta'bo da farar kasa kuma idan ya dawo gari saiya ri'ka tafiya irin ta yan gayu yana doro yara suna tsokanarsa kullum idan d'aliban sun tashi shi kuma nan ne gurin zaman sa wata ranar har kwana yake kuma gashi a lokacin sanyi ne yana kwance da dare sanyi ya dameshi ya kasa barci sai juyi yake yana ma'kyar'kyata tashi yai akwai wani guri ta bayan makarantar da aka jibge kara da yawa kawai yaje abinka da mahaukaci ba hankali ya dauko ashana a aljihunshi ya kunnawa karan wuta dan ya samu yaji d'umi tun wutar tana ci kad'an kadan hartai karfi yadda shima ta dameshi gashi dare yayi babu mutane jin zafi a jikinsa yasa shi matsawa daga gurin yana dariya yace "ina yara kuzo muyi 'kwalisa na kunna haske kun ganshi yana yawa kuzo muyi 'kwalisa na iya had'a haske" ya karasa maganar yana rawa da tafi shi kadai sai shirmensa yake yayin da wuta taci gaba da tsiri har farfatsi take haka ta fara kama makarantar nan ga gidajen garin kusan duk dangan kara yafi yawa ga iska da ake mai karfi watsuwar da wutar take yasa ta fara kama ko'ina gidanjen kusa da gurin farkawar wani mutum ganin hasken daya sa'ba hankali yasa ya fito da sauri daga d'aki zaro ido yai yana raraka wani uban ihu.

"Subahanallahi innalillahi wayyo Allah jama'a ku tashi wuta ta kama shikenan tamu ta 'kare" da gudu yayo waje yana kara zunduma wani ihun "ihuuuuh jama'a ku tashi gobara ta kama kara dan Allah ku farka" nan da nan mutane suka fara tittid'owa suna fitowa gari ya rud'e da salati kowa ya rasa inda zaisa kansa sai ruwa suke de'bowa suna watsawa amma kamar basa zubawa sai kara tsiri take kamar zata ta'bo sama ruwan gidaje ruwan rafi ruwan rijiyoyi haka suka ri'ka kwararawa da'kyar suka samu wutar ta mutu bayan tayi musu mummunan ta'adi duk ta kone gidajen dake makotaka da gurin babu abinda ya tsira sai mutanen gidan da yan kayan da suka samu nasarar fitowa dashi.

Washe gari haka gurin ya zama ba'ki'kirim bayan makarantar ma da rufin ta duk ya 'kone jama'a ta taru an cika guri sai kallo ake babu wanda yasan ya akai wutar ta tashi dole suna bukatar taimako amma basa da wani tsayayye a garin me shige musu gaba haka suka dauki tsawon lokaci suna fama shan wahala musamman wadanda gidajen su ya'kone makaranta ma haka suka cigaba da karatun ba'a gyara ba yau da gobe tafi karfi wasa ganin zasu shiga tsaka mai wuya domin akwai kayan amfanin gonakin su da suka 'boye a cikin karan gashi ya kone sun dawo fama da 'karancin abinci yasa liman din garin sukai hadu sukai shawara aka za'bi manya a garin suka kai kokensu karamar hukuma cewa ga abinda ya same su suna neman tallafi daga can aka d'ebo wakilai domin suzo su gani harda 'yan jarida aka zo suka danyi

Please Login or Register in order to submit comment