Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

batasan halacci ba daga yau tayi kai bazan sake baki kayana ba".

"To kuma ni sai akace miki zan sake kar'ba saboda ga wacce kare ya lashewa zuciya tirrr da kayanki dama can 'kaddara ce tasa na d'auki bashin a gurin ki ga mutane nan da yawa masu daukowa saina canza she'ka".

"Ki canza man bai dameni ba nidai kawai kud'ina nake bu'kata kiban zan wuce kina 'bata min lokaci".

"Au ina 'bata miki lokaci danai me? Dama na ri'ke kine kalli ki gani ba tike nai a gun na d'aure kiba zaki iya tafiya".

"Wallahi tallahi kinji rantsuwa ko A'i bazan bar gidan nanba saikin bani cikon kudina ko kiga tsiya".

Ja A'i tai ta ture tana gyara daurin zani tace "wallahi bazan biya ba sai ranar dana samu a shirye nake mu dambu mu juya mu fidda raini dama na dad'e banyi fad'a ba jini na a daskare yake yau saiya tsinka shi".

"Kika ce bazaki biya ba"?.

"Eh bazan biya ba haka nace ko akwai wani abu da kika isayi"?.

"Niko nake da abunyi tunda ni 'yar kasuwa ce bana rasa abinyi" tana rufe baki ta fad'a d'akin A'i tana d'auko sabuwar tunkuya lamba sha biyar data sayo ta dafa abincin saidawarta tayo waje da ita zata fita a guje A'i taje tana kamata da kokawa ganin zata tafi mata da kayan kud'i tace.

"Gidan uban wa zaki kaimin tunkuya ajiye tunda ba tsofinki ne suka saimun ba" A'i na rufe baki taji saukar mari tasss a fuskarta 'kara ta saki dan batai zato ba kawai zafin marin taji kokawa suka fara sosai suna dambe-dambe da dake-dake baji ba gani da sauri Saude ta Binta suka zo suna rabasu sai fisge-fisge A'i tana da kururuwa "ku barni in rama akan me zata mareni na 'kyale ta wallahi saina fasa mata baki" huci Dijeh keyi tana kallon ta tace "dan Allah ku saketa naga da yadda zata fasa min bakin wallahi yau da saina targad'aki saidai ki kwana a asibiti".

"Saidai ki targad'a uwarki wallahi saidai ki targad'a uwarki kisa tai kwanan asibiti amma badai niba inke mayyace nafi karfinki kurwata kurrr nama na yai miki d'aci" A'i tana rufe baki Dijeh ta sake kawo mata raruma da sauri Binta shiga tsakanin su tana girgiza kai tace.

"Kinga dan Allah Dijeh kiyi hakuri jeki tafi fad'a ba girmanku bane babu dad'i irin haka mu kanmu bama jin dad'in balle kuma kalli yaran nan suna kallonku dan Allah kije ki tafiyarki zata biyaki kud'inki".

Hayayya'kowa A'i tai tana cewa "wallahi bazan biya ba ta mari kud'inta".

Kallonta Dijeh tai zatai magana Binta tace "a'a basai kince komai ba kiyi hakuri dan Allah kije" hararar A'i tai ji take kamar ta sake sha'kota ta turmushe ta a 'kasa ta daki kud'inta "taya zan tafi kina jinta fa abinda take cewa danta raina min wayo" kai Binta ta d'aga "eh naji Dijeh amma nace dan Allah kiyi hakuri ki tafi zata biyaki kud'inki" "shikenan zan mata lamuni kamar yaushe zan dawo"? Tun kafin Binta tayi magana A'i tace "kefe ko uban lamani zaki wallahi tallahi bazan biya ba" kai Dijeh ta jinjina tana yin sama da tukunyar ta d'ora aka tana cewa "shikenan zan tafi da tukunya zuwa nan da ranar litinin idan baki aika min da cikon kudina ba zan sayar na d'auka na kawo miki sauran".

"Aiko wallahi kika kuskura kika sayar min da tukunya hukuma ce zata raba mu dan saina d'ebo miki 'yan sanda".

Hanyar fita a gidan Dijeh tai da tukunya aka tana cewa "yan kul'ke ko 'yan kokara zaki d'ebo min ba yan sanda ba kin dad'e baki d'ebo suba zanga tsinannan dazai tsaya miki banga shegen daya isa hana na sayar da tukunyar nan ba dama wanda nakejin kunya malam Habu ne dalilin sa nake d'aga miki 'kafa yanzu tunda baya nan humm mu zuba nidake d'an halak ka fasa" tana kaiwa nan tayi tafiyar yayin data bar A'i sai masifa take duk ta cika gida da hayaniya sai tsine tsine take ta kasa zama ta shiga d'aki ta fito tayi nan tayi can kamar wacce ta zare takaici ya gama cikata sukam babu wanda ya bata baki ko yace tayi shiru domin gamuwa tai da gamonta.

Aliyah na zaune da Dauda tana masa tsari Dalah tai sallama tana karasowa ta nemi gurin zama ta zauna da 'yar fara'a a fuskarta ta 'karfin hali tace "a'a Dauda yaushe a gari dama ka dawo ne"?.

Kan Dauda na sunkuye bai d'ago ba sakamakon a fusace yake da'kyar ya tattara nutsuwar shi cikin had'a ba'ki yace.

"Jiya na shigo da dare ina kwana"?.

"Lafiya kalau Dauda ayya kace jiya ka dawo cikin dare to sannu da dawowa 'yan Osun kuna can abinku kuna shan dad'i kin barmu a 'kauye 'boye cikin lungu mun zama kifin rijiyoyi".

Ganin wasan da take masa bai d'ago ba kuma a iya saninta da dane sosai zai biye mata suyi tayi yasa ta d'an kalli Aliyah tana cewa.

"Lafiya kuwa naga yayi shiru haka ban saba ganin irin wannan yanayin a tare dashi ba fatan ba wani abu bane"?.

Murmushi Aliyah tai daidai Dauda ya mike tace "Dauda karkaje gidan nan nasanka da zuciya yanxu sai kaje ka faffake shi dan haka ban amince kaje ba".

Dakatawa Dauda yai muryarsa a fusace yace "ba gurin sa zance ba" kafin Aliyah ta kara magana harya fice da sauri kai ta girgiza tana cewa "oh Allah kafi 'karfin abinda yafi 'karfinmu nikam wannan zuciya taka Dauda Allah yasa kar ku had'u da malam Balarabe nasan baza'ai ta dad'i ba".

Da mamaki Dalah tace "Balarabe dai? Amma ba wanda na sani ba"?.

"Shi dai Dalah".

"To meya had'asu daga dawowar sa jiya"?.

"Nice na fad'a masa cewa ga abinda Balarabe yake shirin yiwa Indo yana tallar sadakarta alhali baisan yaron ba kawai dan duk shekara yana zuwa shine zai mata auren dole dashi".

'Dan shiru Dalah tai ranta babu dad'i ta kalli yayar tata tana cewa "to ya zamuyi da 'kaddara yaya Aliyah a jiya da abun nan ya faru yaje gida ya sameni da maganar wallahi yaya Aliy da'kyar nai bacci".

"Zaki kasa bacci man Dalah abun kam da ciwo muma yake damun mu balle ke mahaifiyarta ni yanzu so nakeyi asan yadda za'ai Indo tazo gidan amma nasan tsinanniyar Asaben nan bazata barta ba matukar Balarabe yana gidan a ba'kin halinta ma kila ta jawo ya mata duka".

"Daya zata barta yaya Aliyah ba'kar wahala ce nasan tana can tana shanta tunda uban ta an gama dashi Allah masanin irin lalacewar datai yanzu ina gidan ma meye balle ba idona".

Kai Aliyah ta girgiza tana cewa "kada ki damu in Allah ya yarda bazata auri wancan yaron ba na gama magana da Dauda cewa shizai aureta domin bazan bari kawai ba'asan yaro ba a d'auki Indo a bashi yanzu taya zan samu Indo tazo nan gidan inason magana da ita".

Shiru Dalah tai cikin tunanin ta yadda za'ai tazo d'in zuwa wani lokaci ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Aliyah tace "gaskiya da kamar wuya Balarabe baya barinta taje ko'ina bawai dan kare mutuncinta ba yake haka a'a kawai dan Asabe ta mayar da ita baiwa a gidan shara girki wanke wanke dafa mata abincin sayarwa d'ebo ruwa kai abun ba'kin cikin na harda wankau d'in mutane yanzu naji Sahurah makofciyarsu ta fad'a min wai suna kaiwa wankin kud'i gidan kuma Indo ce takeyi".

Cizon yatsa Aliyah tai tana cewa "tabd'ijam amma Asabe kwai tsinanniyar mace insha Allahu 'karshenta bazai kyau ba saita girbi abinda ta shuka karki damu Dalah zansa malam yaje yai magana da Balarabe cewa ya soke maganar wancan yaron Iluh tunda iyayensa ba'a gari suke ba kuma dama ba wani saninsa akai ba za'a dauki yarinya kawai dan zalunci a bashi saboda rashin galihu to tana da mai tsaya mata Dauda zai aureta zata fita daga 'kunci da wahala".

Cikin jin dad'i da nuna farin ciki Dalah tace "na gode sosai yaya Aliyah Allah ya bar zumunci wallahi harnaji dad'i da kikace Dauda zai aureta jiya da'kyar nayi bacci shima ban samu nayi ba sai jikin asuba".

"Humm ke dai kawai bari komai yazo karshe Allah ya rufa asiri".

"Amin Dalah tace fuskarta wasai ji take kamar wani 'katon nauyi aka sauke mata akanta tsabar murna tasan indai aka ce Dauda ne ya aureta wahalarta ta kare itama yanxu zatai rayuwa irin ta kowa ta huta 'kuncin gidan uba.

MRS ÃL'ÅMÉÉÑ ÁHMÃD CÊ😘.

Masha Allah alhamdulillah na gode sosai fans d'ina a gaskiya ina yinku sau ba adadi kaunarku gareni tamkar garkuwace ina son ku da dukkan zuciya ta💞🤙.

Sai Allah ya kaimu gobe darai da nisan kwana zamu tashi inda muka tsaya🙅.

✍️ YUSRAH MUSA ABUBAKAR💋🤟.
Banda kamarka ya rasulullah 🥀 a duniya banda kamar ka ya rasulullah a lahira 😢 ya sarkin dayaiyi sammai kassai gabadaya babu abinda babu ikonka jikinsa kulliya inkaso na raira wa'kar kobabu kafiya ga Manzon da kayyiwa wahayi ya hijrah.

TYPING 📲
LITTLE ZARAN AUNTY 💃💃💃

🤙Me kamar sarki🤙

Dedicated to my mum may Allah bless you may Allah accept your du'as may Allah open the door of success 4u mama may Allah protect u from all calamities🤲🤲📿🙏👏Amin.


ÀÑÑÙRÌ WRITER'S ASSOCIATION 💫 Home of hospitality and harmony🤙.

53~AL-QAWWIYU
The strong
54~AL-MATIN
The firm

26~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Nabi'ina.

🌄WITCHERY ND DISCONTENT🌄
Episode 53&54
Tanko da Mudi ne zaune a cikin daji gaban wani shirgegen mummunan ba'kin boka ya shafe fuskarsa da jan colour duk jikinsa layune da guraye kansa a d'age sai dariya yake 'kya'kyatawa yana shure Shure da surkulle surkulle saida ya gama sannan ya dawo da kansa daidai yana fuskantarsu ga 'katuwar 'kwaryar tsafi a gabansa sai ci take da wuta amma bata 'kone ba kallonsu yai cikin kakkaurar muryarsa mai amo abin tsoro yace.

"Inaaaa jinnnku yaaa akaiii neeeee"?.

Gyara zama Tanko yai yana cewa "ran boka Hambuwa ya dad'e yauma mun sake dawowa gareka da babbar bukata ne, wato boka wannan mutumin dakai mana aiki a kansa ya talauce shekarun baya shine yanzu ya sake d'agowa ya tafi wata 'kasa neman kud'i wai saiya dawo da arzikin sa daya rasa saiyafi da kud'i ma mu kuma boka hakan ne bamaso duk yadda za'ai duk rintsi karya samu abin kansa sannan a cusa masa son gida yaji ya tsani zaman can boka ka tura aljani ya hanashi sukuni ya hanashi walwala da aiki mai kyau yaji garin ya masa zafi ya tattaro ya dawo gida kuma karya zo da ko naira biyar ce a aljihunsa inso samu nema boka ya dawo butu-butu da yagaggun kaya a jikinsa yanayin mahauci🙊 ka gane dai boka to abinda muke so kenan".

Tanko na rufe baki boka Hambuwa ya kwarara wani irin ihu yana dukan 'kwaryar dake gabansa wacce take ci da wuta tuni wutar ta mutu muss sai haya'ki dake fitowa wani ruwan tsafi ya zuba a ciki tare da garin magani yana 'kwalla kiran sunan Malam Habu da 'karfin gaske kamar zai fasa jejin su kansu sai toshe kunnuwa sukai.

Bayan ya gama yace "ku kalli nan me kuka gani"?.

Duk hankalin su suka kai kan 'kwaryar ga mamakin su ganin Malam Habu sukai shida Sadi zaune suna 'kirga kud'ad'e💰💰 dami-dami💵 masu tarin yawa kamar yayi ga manyan jakankuna sunata jerawa a ciki sai hira suke da Alhajin suna dariya zabura Tanko yai yana girgiza kai yace.

"Ya haka boka ko har yayi kud'in wannan bazai ta'ba yuwuwa ba hakan kuskure ne bazan bari Malam Habu yai arziki ba boka ka taimaka hakan bazata yuwu taya za'ace daga zuwa har ya samu guri kamar haka zanso ace wannan ba gaskiya bane ace yanzu a tagayyare na gansa zaune cikin bola yana tsince-tsince da surutai ko na ganshi yana bara amma sai naga sa'banin yadda nake fata"?.

Kai Mudi ya jinjina yana cewa "eh gaskiya boka Hambuwa kayi mana maganin sa kalli fa ka gani wai kud'i ne malam Habu yake 'kirgasu haka harda dangwalar yawu💵 ko kuma takardune"?.

Mangare shi Tanko yai yana cewa"Humm bud'e idonka dakyau kayi kallo kud'i gasu nan inda ba'asan ciwon suba kai dai bari kawai Mudi ai duk laifin wannan tsinannan Sadin ne shine ya gayyaceshi dan haka boka harda shi zaka had'a".

"Aaann gamaaa ku jiraniiiii" boka yana rufe baki ya soma juya 'kwala-'kwalan idanuwansa kamar yadda yake juya idonsa👀 haka 'kwaryar gabansa ma take juyi yana yi yana yayyafa wani abu ciki yana kiran sunan Malam Habu da Sadi zuwan can sai gani sukai faaaaa💥💥wuta ta kama a cikin 'kwaryar hhhhh hahaha hihihihih hhhhhhhhhhh haka boka ya cika musu kunne da 'kara zuwa wani lokaci yai shiru yana kallon su yace.

"Shikenannnn aikinnku yaaa kammalaaa saura biyaannn bukataaa kamarr yaddaa wannan 'kwarya ta 'kone hakaa arzikinn suu zaii 'konee ammaa badaa wutaa baa zann turaa aljanii Shahirgiii ya d'ebee kud'inn suu tashii basuu daa koo siisii dagaa suu saii kayann jikinsuu hakan yayi muku"?.

Kallon juna Tanko da Mudi sukai suna fashewa da dariyar mugunta Tanko daya kasa tsayawa yace "kwarai boka tabbas haka yayi wannan zai faranta min raina shakka babu boka na yarda da tsarin aikinka mai kyau ne shikenan zamu tafi boka saimun sake dawowa da babbar kyauta idan muka ga malam Habu ya dawo a firgice kuma a talauce kamar yadda ya tafi jiya iyau".

"Hhhh karrku damuuu kunn samuuu mazaaa a fitaaa daga nan da sauriii ku d'age 'kafa d'aya da tsalle babu waiwayeee idan kuka juyo abinda zai sameshi zai dawoo kankuu kujeee naceeeeeee🙊".

Ba arziki da sauri suka tashi jiki na rawa kowa ya d'age 'kafa d'aya suka bar gurin suna tafe suna tsalle kamar kwad'i sun ji'ke da gumi shir'bim sai sauke numfashi suke da'kyar suka karaso bakin wata 'yar siririyar hanya dake dajin sai a gurin dole suka zauna idan sun dawo daidai numfashin su ya tsirga sa tashi su tafi kallon gabas yamma kudu da arewa Tanko yai yana cewa.

"Kaii ah kaii sai yanzu naji dad'i d'an bala'i haba malam idan nabar malam Habu ya dawo da arzikin sa irin nada ai bazan iya rayuwa ba tsabar ba'kin ciki takaici ne zai kasheni saidai a wayi gari nayi bunga😂 wallahi"

Dariya Mudi yai yana cewa "balle kuma ni inaga nafi jin haushin sa akanka"?.

Zaro ido Tanko yai "inji ubanwa kafini tabbbbb kasan yadda nake son ganin karshen Malam Habu kuwa hummm abun bazai dad'i ba idan na tsaya yi maka bayani zai kaimu tsawon shekara guda ban gama fad'a maka ba so nake kafin ya mutu ya dandani azababbiyar azaba ya tagayyara ya zama abin tausayi da abin kwatance idan ya mutu babu wanda zaije kan gawarsa balle a samu wanda zaice aimai wanka har akaishi kabari inaaa wallahi bazan bari ba malam Habu! Malam Habu!! Hummm zaka ga tashin hankali da damuwa a gabanka talauci zaita bibiyar jininka har abada kuma nayi alkawari bazan ta'ba bari ko d'aya cikin 'ya'yanka tayi aure ba musamman ma wannan yarinyar" tsayawa yai yana kallon mudi yace "meye ma sunanta Mudi"?.

Dariya Mudi yai yana cewa "sunan gyatumarsa yasa Hauwa'u suke ce mata Amatullahi shi kuma yana ce mata mamarsa".

Tsaki Tanko yai "to ko uban mamarsa ce tunda yafi sonta itama saitaga bala'i iri iri sai na hanasu zaman lafiya" ya karasa maganar yana kallon Mudi wanda ya zuba masa ido kafin yace.

"Meye"?.

Kai Mudi ya kad'a yana cewa "babu komai tashi mu tafi na gaji mubar dajin nan" mi'kewa Tanko yai yana cewa "muje to ai yanzu hankalina ya kwanta bani da matsala sai jiran yadda zanga Malam Habu ya dawo garin nan a gigice kamar an koro shi ranar zanyi dariya a majalisarmu na buga 'kafa nayi shewa inta kama na mi'ke na taka rawa kaidai humm a rufe da buzu wai matar Malam tayi cikin shege bari kawai muje dai" Mudi dai bai sake magana ba suka cigaba da tafiya iya muryar Tanko ce ke tashi a dajin wanda ya kasance shiru babu motsin komai koda ganyen bishiya.

CAMEROON
Cameroon Douala zaune su Malam Habu suke a kofar gate d'in kofar gidan Alhaji Idrisu suna zance dama kuma baya gari kamar daga sama suka ga motarsa ta nufi kofar gidan da sauri malam Habu ya tashi yana bud'e masa gate d'in yana karasowa ya tsaya yana kashe motar ya sauke glass d'an le'kowa yai da fara'a a fuskarsa yace.

"Sannunku da kokari yaya kuke"?.

Suma fuskarsu da annuri suka gaida shi kallonsu ya sakeyi yana cewa "ok Malam Habubakar fatan ba wata matsala"?.

Kai Malam Habu ya d'aga cikin yabawa da halayyar Alhaji Idrisu na kula da wanda yake karkashin sa yace "eh Alhaji babu wani abu muna lafiya" saidai mutane da dama sunzo nemanka d'azun ma wani mutum yabar nan".

"Ok bai fad'a muku sunansa ba"?.

"Eh bai fad'a ba kawai dai ya d'an dad'e sannan ya mi'ke ya tafi amma yace zuwa dare zai sake dawowa".

"Ok shikenan zan shiga gida idan ya dawo ka min magana".

"To Alhaji insha Allahu a fito lafiya".

Tada motar yai yana karasa wucewa ciki kafin Malam Habu yaja gate ya rufe yana zama tsaye simm yaga anzo anyi a kansa yana d'agowa yaga yaron Alhaji Idrisu ne malam komai da ruwanka da mamaki yace.

"Yadai bismillah zauna mana".

"Dama zama ya kawo ni"? Ya fad'a yana fiddowa Malam Habu girman idonsa waje.

Cikin son 'kular dashi Malam Habu yace "oh haka akai yi ha'kuri ba zama ya kawo kaba tsaiwa ce ashe ka hangoni a mota na dawo kanata sauri kazo mu gaisa ni kuma na shiga gida saboda yau bazan bari kayi ha'inci ba da kaina zan fito na raba kud'i wa al-umma na gaji da ragal din da ake min".

Zaro ido waje malam kamai da ruwanka yai yana cewa "kuturun ubancan ni kake fad'awa magana a kaikaice"?.

Wani kallo Malam Habu yai masa yace "a'a kaina nake fad'awa magana ba dakai nake ba kasanni akwai saurin tsarguwa musamman yanzu dana fahimci bani kad'ai ne yaron Alhaji ba akwai wasu idan banyi hattara ba asirina gaf yake da tonuwa ka gane dan haka kaja baki kai shiru"🤫.

A masife Malam komai da ruwanka yace "bazan ja bakin nai shirun ba wato saboda kaga gurin kwanana shine kake neman d'ora min hau🙆 ko? Na rantse da Allah kayi da d'an halak kuma zaga gani" yana gama fad'in haka yabar gurin a fusace da kallo suka bishi Sadi da baya son hayaniya yace.

"Amma daka 'kyale shi nifa inaga kamar mutumin nan yana da ta'bin 'kwa'kwalwata wasu lokatan yana abu babu kan gado kaga fa yadda yaxo yaima wani tserere aka kamar bishiya haba wannan abun ba tsari".

Ta'be baki malam Habu yai yana gyara zama yace "kai da Allah manta dashi wannan mutumin baisan me yake ba nafi yarda da abinda ka fad'a kila ya samu ta'bin 'kwa'kwalwar haka nake zato saidai duk wani gigi da hauka da yakeji dashi na damashi na shanye baisan waye ni ba ba'ai min hauka badan ruwa ya daki babban zakara🐓 ba ake masa kallon d'an tsako🐤 humm manta kawai Allah ya rufa asiri amma inaga kafin mubar garin nan saina saita masa zama".

Shidai Sadi shiru yai bai sake magana ba amma a ransa yana fargaba domin yaga take taken Malam komai da ruwanka ba mutumin arziki bane saidai Allah ya kiyaye karya 'kulla musu 'kulallaya suda ba kowa suka sani a garin ba fatan sa Allah ya rabasu lafiya.

'KAUYE🏕️
Kwana biyar tsakani Balarabe yana zaune a kofar d'aki sai gyangyad'i yake har kamar zai kifa sannan ya d'ago fitowar Asabe ta kalleshi tana cewa "inye duniya taka 'kwarai ma Balarabe wato saboda sangarta tai maka yawa shine kazo ka zauna anan harda samun damar barci ko akan na d'auke nayin gidan to daga yau na sauke gara ka tashi ka nema dama wanki ne tsinanniyar 'yar taka takeyi dashi nake cefane kaga yanxu tunda bata nan kaine zaka dawo dan wankau shara girki wanke wanke da dafa min kayan sayarwata duk ranta ta dawo ka huta".

Kallonta Balarabe yai yana cewa "nifa bada yawu na tabar gidan nan ba kinsani bansan ta fice ba laifin Dalah ne".

Katse shi Asabe tai "kai dalla gafara can dama tsari nace kamin ko kaji nace laifinka ne damuwata ka tashi yanzun nan ka fara min aiki ".

Su'kuri Balarabe yai yana kallon ta wata uwar ba'kar harara ta sakar masa tana cewa "oh ka tsaya kallo na bazaka tashi ba kenan"? Da sauri Balarabe ya mi'ke yana kad'e jiki ya nufi gurin wanke wanke tsaki taja tana cije yatsa tace.

"Bahijjah kina ina"?.

Daga d'aki Bahijjah tace "gani a kwance bacci zanyi yane😳"? .

"Au ni kike cewa yane dan ubanki"?.

Ta'be baki Bahijjah tai tana cewa "eh man dole nace yane me zan miki"?.

Asabe bata damu da tambayar rainin da bahijjah tai mata na cewa yane gani take hakan duk cikin fashion🤪 ne tace.

"Ba komai fito da kayanki wadanda sukai datti ki watsowa Balarabe zai wanke".

Daga d'aki Bahijjah tace "ni wallahi na riga na kwanta bazan tashi ba in kin matsu ya wanke min kizo ki d'ebe gasu nan a tsakar d'aki".

Cikin haushi Asabe tace "dan ubanki ni kike fad'awa haka Bahijjah"?.

A hantare Bahijjah tace "Toya kike so nayi nace na riga na kwanta bazan iya tashi ba dole ne wannan wacce irin jaraba ce? Haba da Allah mutsss aikin kawai dun abi a dameka da magana" ta karasa maganar tana gyara kwanciyar ta daidai Asabe ta shigo d'akin ganin zatai magana kawai ta juya mata baya tana jan bargo Asabe batai magana sai kayan data tattara tana fitowa waje dasu ta watsawa Balarabe aka tana cewa.

"Kayi sauri gashi nan yana jiranka bana son asaranci ace har yanzu baka wanke kwano yai goma ba duk da uban me kake kallo? Kaga Balarabe ka kiyaye ni ka fara isata a gidan nan fa zan 'bab'bama maka ransa" shidai Balarabe shiru yai yana sauraron jikinsa sai kikir kirir yake a gaban kwanuka tunda ba sabawa yaiba ba iyawa yaiba duk ya jike jikinsa da ruwa ga kayan wanki data tulo masa tayi zamanta a gefe tana kallonsa a rana sai gumi yake yana sharcewa harda dariyar mugunta take ita kad'ai ganin yadda yai faca-faca.

Humm duniya mai juyi juyi kwad'o a ruwan zafi Allah ya sauwake 😘MIJI😘 wanda kake sa ran da albarkacinsa🤨 zaka shiga ALJANNAH🌲 amma kuma shi ka mayar bawanka😳🙆 wannan ta'bewar har inaaaaa??? hummm gaba gaba dai Asabe🤫.

KANO🏙️
_____Yau ranar asabar week end ne babu aiki Nurain yana gida shi kad'ai a parlor yana waya da Nafisa Auta da Amnah sun tafi gidansu gaida momynsa Zainab na bedroom tana barci dan haka ya sake ya bararraje suke zuba hira ta soyayya😝 shida Nafisa a waya sai dariya yake bai lura da Zainab dake tsaye tun d'azu ta zuba masa ido jikinta na rawa idonta fal da hawayen tsananin kishi ba jin maganganun da suke fitowa daga bakinsa wanda hankalin ta bazai d'auka ba a guje tazo tana fisge wayar tana jifa da ita tare da fashewa da kuka tana kallonsa tace.

"My choice me nake ji haka kalaman soyayya a bakinka kana furtawa wata? Wacce tsinanniyar ce 'yar uban waye? waye ubanta me take ta'kama dashi dahar zata shigo cikin rayuwarka wallahi tallahi my choice bazan d'auka ba bazan yarda ka fad'a min wace ita" ta karasa maganar tana rikeshi tare da jijjigashi da karfi wanda da alama batasan tana yin hakan ba.

'Bam'bare hannuwanta Nurain yai a jikinsa yana fuskantar ta yace "kinga Zainab bana son shirme ki nutsu muyi magana".

A burkice Zainab tace "nutsuwa my choice taya zan nutsu bayan wannan mummunan tashin hankalin daya sameni wai me kake 'boye min ka fad'a gaskiya idan har ba cin amana ta kake ba"?.

Kai Nurain ya girgiza yana ri'kota dan yasan yanxun nan saitai hanyar kitchen tace zata kashe kanta ba hankali gareta ba idan kishinta ya tashi yace "ni ban ta'ba cin amanarki ba ban kasance mai zaluntarki ba saboda ina son ki".

Fusge jikinta Zainab tai tana cewa "idan har kasan baka cin amanata kana da gaskiya ka fad'a min wacece wannan yarinyar sannan meye ala'kar ka da ita"?.

'Dan shiru yai yana kallon ta kamar bazai magana ba sai kuma ya sauke numfashi yana cewa "kinsan 'kauyen da Dad yake tura ni 'karbo kayayyakin da ake kaiwa gidan marayu a gurin wani mai kud'i a 'kauyen"?.

Tsayawa Zainab tai da kukan tana kallon sa tace "shine ya baka 'yarsa"?.

Kai ya girgiza mata "no ba shine ya bani ba nine naganta naji ina son ta".

Zaro ido waje tai tana dafe kirji zatai magana ta 'kwaru ta soma tari da ruwa a kusa

Please Login or Register in order to submit comment