Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haushi ba"?.

Kallon sa zainab tai cike da zarguwa tace "ni kawai ka fad'a min bana son kwane-kwane".

"Zan fad'a miki shiyasa na tambaye ki baza kiji haushi ko ki tada hankali ba"?.

Jitayi zuciyarta na harbawa amma ta dake tace "eh ka fad'a kawai zan tafi office I don't want to be late".

Kai ya jinjina yana kunna wayarsa ya nuna mata photon yana cewa "nasan baki ta'ba ganin ta ba ko kalleta dakyau" karewa photon kallo Zainab keyi na wani lokaci kafin taja dogon tsaki tana d'auko karamin towel cikin handbag👜 d'inta ta tsartar da yawu tana cewa "wannan me kamar aman fa daga ina ka samu photon da gani 'yar asalin tantagaryar 'kauye ce bata san komai ba" 'yar dariya Nurain yai yana kallon Zainab bai bata amsa yace.

"Kije ki tafi office karki makara maybe patient😷🛌 d'inki suna can suna jiranki".

Mi'kewa tai tana kallon sa tace "kaifa bakaje office ba ko yau hutu ka d'auka d'azu Daddy ya kirani yace ya kira wayarka a rufe sai kuma yanzu na ganka anan"?.

Shima mi'kewar yai suna fita harabar gidan tare yace "eh jiya na rufe ta da wuri kuma yau ban bud'e ba sai yanzu zanje na sameshi" "ok shikenan ni na wuce ka kula" tana fad'in haka ta shiga mota shima tasa ya shiga yana kallo ta fita $annan yabi bayanta yana tunanin tashin hankalin dake gaba daga ranar da Zainab ta fahimci son auren Nafisa yake akwai damuwa dazai iya ha'kura to daya ha'kura din saidai maganar gaskiya bazai iya ba turbar lafiya a bita da shekara a zahirance bason Nafisa yake ba kawai yana jin sha'awar tane yana son kasancewa da itane idan harba haka yai ba kuma yaci gaba da zuwa 'kauyen yana ganinta komai zai iya faruwa za'ai abun kunya wanda shi hakan ne baya so duk rintsi gara ya aureta zaifi da ace yadda mahaifin sa sukeyi da mahaifin ta abin kunya kamar haka ya faru yasan Daddy bazai ta'ba yafe masa ba zai lalla'ba Zainab kota halin 'ka'ka tayi hakuri ta bari ya aureta yasan ba'kin kishinta a kansa kuma shima yana matukar 'kaunar matarsa saidai dole a wannan karon bazai kawaici ba zai fara samun Daddynsa da maganar idan ya amince saiya sanar da ita idan yace a'a saiya ha'kura amma bazai sake zuwa 'kauyen ba saboda idan yana ganinta akwai murgujejan kuskure komai zai iya faruwa🤫.

MRS AL-AMEEN AHMAD CE😘

Na gode FANS tnks for ur support I really appreciate it🌹💓💯 ina godiya's🙏 da kulawa🤝🤗 Allah ya barmu tare nagode👍.

Insha Allahu gobe zan huta😉 fans d'ina bazan yi muku typing ba sai zuwa jibi idan muna darai.

💋YUSRAH MUSA ABUBAKAR💋

Ya mustapha ANNABI {saw) hasken idanu na ya muntaka yarda dani ya masoyi na💓.
Dole hankali nafa ya tashi😧🙆 wanga al'amari😔 ba abinda nai gashi kwa lokaci yana sauri😣😞 naga mutuwa ta d'au babba harda jariri😭😭😭 nasan tana tafe lamarinta zaya zo kaina😭😓😢.

BINTU MUSA ABUBAKAR MUHAMMAD CE.

See👀 you theday😉 after tomorrow🤣.

TYPING 📲 YUSRAH MUSA ABUBAKAR MRS AL-AMEEN AHMAD CE 😘.


👑ME KAMAR SARKI 👑


WhatsApp no:234 905 527 3614.


💫A*W*A💫
ANNURI WRITER'S ASS💫
__________________
________________________
_____________________________ HOME OF HOSPITALITY 🤗 AND HARMONY GIDAN KAR'BAR MUTANE HANNU BIYU DA ZAMAN LAFIYA ANNURI HASKE LEKA GIDAN KOWA KODA MA'KIYA NA KALLON KA RAMIN KURA SAI YAYANTA TAKEN MU KENAN💫💓🌲.

STORY AND WRITTEN
📚✍️Mrs Al'ameen Ahmad ce😘


HHHHH!!!😂😂 Gaskiya wallahi FANS d'ina ina yinku sau💯 comments d'inku da kuma yabonku gareni yana sa naji kamar na taka rawa💃💃💃 Allah ya 'kara barin mu tare sakallahu kairan na gode da nuna 'kauna godiya💞 sosai sosai godiya💓🤙👍.

45~Al-Wasi'u
The vast
46~Al-Hakimu
The wise

22~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Akraminah.

🌄WREAK ND OPTIMISM🌄
Episode 45-46
Bikin Ahmad d'an gidan Bashir ya kusa an gama komai kwanaki ya rage sunata shirye-shirye da yake Binta take gano Amatu anan Safiyah take fad'a mata batai 'kasa a gwiwa ba tana dawowa ta sanarwa 'yan gidan ga mai son zuwa tana gayyatar kowa da kowa su Aisha ma sai murna suke zasu zo biki Dutse suga yadda birnin daraja yake🤗 wanda ya cika ya batse da al-umma ga haske🌃 ga adon dutse🗻🏞️😎😊 (FANS karfa kuce dan gari na ne shiyasa nake kod'ashi😜 Abinda na fad'a gaskiya ne sabuwar duniya kuzo kuyi kallo dad'i yana Jigawa 💃🙅😃).

Dan haka Amatu data samu lokaci taxo gida ba wani dogon hutu tazo yiba satin ta biyu ta koma Dutse taci gaba da karatunta Bashir ya sai mata laptop saboda wani aikin dole sai a ciki Ahmad da Maryam suna kokarin su kwarai wajen koya mata yadda ake amfani da laptop d'in da yake tana da saurin fahimta tuni ta koya ita kad'ai zata zauna a bedroom tasa ta gaba tayi ta bincike iri iri ta shiga nan ta fita nan ta 'kware sosai tasan komai kuma alhamdulillah karatunta yayi nisa komai dai yana zuwa mata da sauki musamman a ma'koftansu akwai wata budurwa itama karatun sojan takeyi suna abota da Amatu a makaranta suka had'u babanta mai kud'i ne sosai dan haka kusan komai yana yiwa Amatu ya hutar da Bashir saboda ya yaba da hankalin ta har wasu ma'kudan kud'i ya biya musu suka je American 'karin wani aiki a bangaren abinda ya shafi soja kusa watansu takwas acan sannan suka dawo.

Prof na zaune a parlor yana waya da Mr Famous sai dariya yake kwararawa dariyar hauka da mugunta kiran Mr Danual Chai ya shigo bai katse ba saiyai holding dinsa sukaci gaba da waya su uku kowa sai mummunar dariya yake kwararawa mai busar da imanin zuciya gefen sa 'yarsa Hudayyah ce da wani abun tsafi a hannunta tana kallo fuskarta fal da murmushin mugunta tace "dawo masa da hankalin sa" tab abin tsafin na kalla wasu murd'a murd'an aljanu ne sun d'aure wani kyakkyawan saurayi suna azabtar dashi sun canza masa kamanni d'aya a cikin su ya ri'ko gashin kansa yana d'ago fuskarsa idonsa a rufe subahanallahi ai Muheed ne abokin Asad (Jay).

Bud'e idonsa dayai jaa sosai yayi yana kallon su cikin tsawa wani yace "kaii bamu zaka kalla ba kalli gabanka" da'kyar ya d'ago kai yana duban Hudayyah ta cikin wangamemen abin tsafin dake manne a jikin wani 'katon dutse cikin ba'kin kogon da suka d'aure shi kogo ne na tsantsan tsafi mai duhu da had'ari dariya Hudayyah tai tana cewa "kalleni dakayu meye jarumi na sunanka"? Muryar Muheed na fita da'kyar cikin jarumta da karfin hali irin na soja yace "ban sani ba" wata dariyar ta kuma she'kawa da ita tana sake shafa abin tsafin ji yai tana ta'ba fuskarsa da fushi yace "ki daina ta'ba ni tunda ke ba maharramata bace baki dawani iko a kaina sai yadda ubangiji na yayi dani baku isa kumin komai ba".

'Dan zaro ido Hudayyah tai irin surprise d'in nan tace "really? har yanzu kana da 'kwarin gwiwa jarumtakarka tana burgeni kana da taurin kai shiyasa nasa a killace min kai kaine irin mijin da nake son aure nake mafarkin samu bazan ta'ba barinka ba bazan kyale kaba harsai ka amince min zaka aure ni! kayi magana ina sauraron ka.

"Baki da wani abu da zaki bani wanda zaisa naji sonki a zuciyata Allah ya sauke min auren mace irinki wacce batasan ciwon kanta ba irinki".

Cikin lallahi Hudayyah tace "idan ka amince min zan fitar dakai daga nan sannan zan aure ka na nuna maka gata na sanya ka a cikin 'kungiyar mu ka gane zaka samu komai kake so kud'i dukiya duniya duk zaka samu ina tare dakai fatan ka gane"?.

A fusace yace "ban gane ba kinga bar ganin kin samu damata babu wani abu da kika isa yimin Allah ya tsare ni da kaucewa hanyarsa ina neman shiriyarsa".

Kai Hudayyah ta jinjina tana kallon shi tace "shikenan sai mun sake had'uwa kuci gaba da ganar dashi wacece Hudayyah yar gidan Prof shugaba jagaba a cikin wannan babbar 'kasurgumar 'kungiyar mai d'unbin had'ari kada kuji tausayinsa kada ku sassauta masa sawata ce ku azabtar dashi harsai kun ya bud'e baki yace yana sona ya amince min" tana rufe baki ta d'aga abin tsafin a fusace ta doka ya tarwatse tana kallon Prof daya sauke waya shima yana kallon ta kawai ta saka mai kukan shagwa'ba tana cewa.

"Wallahi Daddy bazan yarda ba ina son sa bazan 'kyale shiba harsai ya amince zai aureni"

Ri'ko hannun ta Prof yai cikin lallahi yace "oh my daughter can you be quiet🤫 ki daina 'bata hawayen ki shidin banza ya isa jadamu bayan yana d'aure a gurin mu a 'kar'kashin ikon mu sai abinda mukaga dama muyi dashi karki manta badan kina kaunar saba kinsan bazan barshi darai ba da yanzu ya hallaka dan haka ki bar min komai a hannu na zanyi maganin abin".

Goge hawaye tai tana cewa "to shikenan Daddy kuma wallahi bai isa ba saiya aureni"

Kai Prof ya jinjina "Kibar 'bata bakin ki na fad'a miki ki daina cewa saiya aureki kawai kice ya aureki ko kuwa" Prof ya karasa maganar yana d'age mata gira🙊 dariya tai tana rungumeshi tace "I love you Dad shiyasa nake son ka baka son ganin kuka na ba kamar Mom ba nagode much appreciated💋💞" ta fad'a tana sakar masa kiss kafin ta mi'ke da jaka a hannunta tana yin hanyar fita tace "Daddy na tafi can zanje na dakatar dasu daga azabatar shin da nasa sukeyi karsu kashe shi nima mutuwa zanyi in babu shi I swear bazan iya rayuwa ba sannan ina son zuwa gurin Khimiyyah ma Dad saboda nayi kiran wayarta bata d'auka kuma duk iya sihirin dazanyi dan naga meke tafiya nayi banga komai ba shiga wannan tsararriyar masarautar tasu zatai min wuyar shiga tunda ba ita amma zansan yadda zanyi na tafi" "ok daughter safe journey saikin dawo" kai Hudayyah ta d'aga tana fita a parlon tare da d'auko phone d'inta tana sake jarraba kiran numbar wayar Khimiyyah tayi sa'a kuwa ta shiga amma ba'a d'aga ba harta katse tsaki taja tana cewa "itakuma wannan gidan uban wa takai phone din nata oho" kara danna Kira tai a karo na biyu.

Khaldiyyah na kwance taji waya tana ta ringtone ta hana ta barci da kira ya katse za'ai wani haushi ne ya kamata ta mi'ke tana sauka a gadon ta soma birkice dan bata ga wayarba can ta bud'e drawer ta ganta but kiran ya katse daukowa tai tana kallon number da akai kiran ba suna sai wani emojis 👹👿💀 mai siffar abin tsoro aka sa ga photo nan akan numbar mace ce jikinta dajan kayan ta ya'be fuskarta da wani ba'kin abu da mamaki take sake kallon numbar tana shirin Kira aka sake shigo da wani Kiran da sauri jikinta na rawa ta d'aga tana cewa "hello waye"? Jitai wata murya tace "barka dai kyakkyawa kena kina sha'awar yin shigar kaya irin kalar na wacce take a wannan photon ne"? lokacijikinta yayi sanyi kafafunta suna rawa zurrrr zurrrr taji kamar zu'kar jininta ake ihu ta saki tana jefar da wayar cike da tsoro ta fita da gudu daga d'akin har fad'uwa tai a hanya da'kyar ta karasa parlor kusan karo sukai dasu Shaukiyyah wanda already sun jiwo ihunta suka taho 'kan'kame Shaukiyyah tai tana cewa "wayyo Allah ku taimake ni wallahi wani abu na gani acan".

A rud'e Shaukiyyah tace "acan kamar ya me kika gani"?.

Idon Khaldiyyah a rufe jikinta yana rawa bata iya bata amsa sai sakinta datai tayi baya luuuu zata fad'i da sauri suka tare ta suna kiran sunanta cikin tashin hankali wanda Makiyyah da gudu ta fita zuwa part din mahaifansu domin ta sanar dasu ga wata masifa ta shigo musu gida.

Da sauri suka shigo ganin yadda Khaldiyyah take mimmi'kewa yasa Sultana Hadizah d'ora hannu aka tana fashewa da kuka tace "idan nace kaf masarautar nan ni aka tsana ace nayi rashin arziki idan Khimiyyah dukanta akai ta suma to itakuma Khaldiyyah meya sameta take irin wannan abun wallahi bazan ta'ba yarda a kashe min 'ya'ya ba tabbas akwai mayu a cikin ku"😱😳.

Ta karasa maganar tana nuna Mami da Sultana Fatima da kuma Sultana Shafi'ah ba wanda ya ankara sai jin 'karar mari sukai mai girma Alhussain ne ya karaso a fusace ya wanka mata marin data gigice tayi baya talau talau zata kifa da sauri Mami ta tare ta amma tana dawowa cikin nutsuwar ta ganin wacce ta taimake ta yasa ta 'kwace tana cewa.

"Matsa min anan babu abinda zaki ce min Sultana Hauwa'u kece komai.............…......……..

"HADIZAH" Mai girma Alhussain ya fad'a zai dad'a marinta mai martaba ya hanashi huci yake cikin tsananin 'bacin rai yake kallon ta yau badan mai martaba Alhassan ba wallahi ya rantse da Allah idan ya ri'ke Sultana Hadizah baza kwana a gida ba saidai tai kwanan hospital. .

Batare da nuna wata damuwa akan abinda Sultana Hadizah ta aikata ba mai martaba yace "meye abinda ya sameta"?.

Kai Shaukiyyah ta girgiza "Allah Abba bamu sani ba tana bedroom muna falo sai ihunta mukaji tana cewa wayyo Allah ku taimake ni wallahi wani abu na gani acan daga haka muna tambayarta meta gani batai magana ba ta suma".

"Ok shikenan bari muga" Ajeeb mai martaba ya kalla yana cewa "ka duba mana ko a kaita hospital".

Mi'kewa Ajeeb yai yana fita ya koma part d'in su d'auko kayan aiki Sultana Hadizah kuwa dama ta fice tana kuka Makiyyah ce da Shaukiyyah suka kinkime ta suna kwantar da ita akan kujera Ajeeb ya duba ta ba wata matsala suma kawai tai ruwa yasa aka miko masa ya shafa mata sukai dace numfashin ta ya dawo amma tana bud'e ido ta sake rufewa har tana d'ora hannunwanta akan fuskarta tace.

"Wayyo Allah wallahi wani abu ne karya kamani".

Taruwa sukai a kanta cikin nutsuwa mai martaba yace "Khaldiyyah bud'e idonki babu komai anan mune" kaita girgiza "Allah Abba na ganta a cikin wayar Khimiyyah" da alamun tambaya yace "wa kika gani"? Da hannu Khaldiyyah tace "itace ita na gani".

"Ita wa kika gani Khimiyyan kika gani a wayar"?.

"A'a ba ita bace wata da jan kayan a jikinta kuma tasa manya ha'kora za'ko-za'ko idanuwan ta sunyi ja ta 'bata fuskarta da ba'ki sannan da wanin abu a hannunta kuma magana take".

Kasa gane inda Khaldiyyah ta dosa sukai d'agowa mai martaba yai yana kallon Annur yace "duba min wayar Khimiyyah a bedroom d'insu" to Annur yace yana shiga amma babu wayar ba alamarta yà duba ko'ina bai ganta ba juyawa yai zai fita yaji saukar abu tass ya fad'o da sauri ya juyo yana kallon abun ga mamakinsa wayar ce subahanallahi meye haka kodai da gaske Khaldiyyah take ba kowa a d'akin ubanwa ya jefo wayar?🤔 share batun yai batare da wani tsoro ba ya d'auki wayar yana fita ya baiwa mai martaba batare da yace komai ba amma me da aka kunna wayar sai fari alamar taci secreen ganin ta lalace sai kawai mai martaba ya mi'ke yana kallon su yace.

"Ku fito daga part tunda ta riga ta tsorata baza iya ci gaba da zama ba ta dawo gurin su Shaukiyyah duk mi'kewa sukai suna fita anan yake tambayar su ya sukai da doctor Amar akan jikin Khimiyyah Ameer yace.

"Wallahi Abba babu wani sau'ki tana nan a yadda take gara mu fita da ita India muje akwai wani babban asibiti a Chennai mercy hospital ina ganin haka zaifi akan zaman nan ba cigaba, amma me kace Abba"? Kai mai martaba ya d'aga cike da gamsuwa yace "shikenan ranar monday saiku tafi kaida Ajeeb da Annur tare da Hauwa'u Allah yasa a dace kaje a yau zan had'a ka da wani mutum kuyi maganar shi masanin India ne sosai yayi zama acan shekaru da yawa yasan ko'ina zan baku numbarsa zuwa an jima kuyi abinda ya kamata" to Abba Allah yasa idan muka je Khimiyyah ta samu lafiya koda yaya ne amma Abba zan Kira Asad na fad'a masa ya same mu acan saidai kasa baki idan ba haka ba nace nine zan fad'a masa bazai zoba" kai mai martaba ya girgiza "a'a Ajeeb babu ruwan ka dashi kuyi abinda ya kamata kawai" to Abba insha Allahu.

Bayan kwana biyu kamar yadda mai martaba Alhassan yace haka ne ya faru sun shirya tsaf zuwa India amma fa Sultana Hadizah ta dage ta rufe ido tai ruwa tai tsaki akan wallahi bazata yarda a tafi da Sultana Hauwa ba idan kuma ya zama dole tafiya da ita to saidai su tafi tare haka kawai za'a tafi mata da 'ya kuma a rasa dawa za'a had'a su tafiyar ma saida ma'kiyanta taje su 'karasa kasheta acan su dawo mata da gawa saita bisu, shima mai girma Alhussain yace wallahi ya rantse da wanda ya halicce shi bazataje ba idan kuma ta nace saitaje a bakin auren ta Sultana Hadizah ta shiga tashin hankali tayi kuka tayi ihu da kururuwa lokacin da zasu tafi amma haka tana kallo jirgi ya tashi🛫 ba ita koda suka dawo gida ita kad'ai a d'aki sai yage yage take duk ta birkita d'akin harda gwara kanta a bango tana tsinewa Mami uwa da uba🤪.


🗣️Hummm duniya mai cike da abinda mamaki😯 Sultana Hadizah babu wanda yasan inda rana zata fad'i😠😬 mental ur self☹️😖🙄 if u go to the river🌊🌊 don't swim🏊 it can carry u away🏃🏄

🏕️'KAUYE🏕️
Malam Habu yana zaune akan tabarma a kofar d'akinsa yaro ya shigo da sallama yana cewa "wai malam Habu yazo inji Malam Sadi yana waje" malam Habu yana shirin magana A'i tace "tofa Malam nesa tazo kusa inkaji Kira an samu amma banda kiran d'an sanda Malam kayi sauri karya wuce ka Allah yasa zakkar shinkafa ko dawa ya kawo maka muma mu samu canjin d'an wani lokaci mu huta da wannan ba'kin cikin cin gero da muke fama dashi kullum mu ba kaji ba koda yaushe mu tabbata a tsatstsagar tsaba" wani kallo Malam Habu ya mata zaiyi magana Saude tace "Malam dan girman Allah karka kulata batasan me take ba ka mata uzuri" kai kawai ya girgiza bai ce mata 'kala ba kamar yadda Sauden ta ro'keshi yasa takalmansa ya fita mi'kewa Saude tai bayan ta gama wanke shinkafar saidawa zata zuba a wuta tace.

"Gaskiya A'i ki gyara halinki wannan d'abi'ar da kika d'auka bazata amfanar dake da komai ba kar ki zama butulu man mai manta kyautar jiya meye baki samu ba meye Malam bai bamu ba lokacin da yake da wadata har iyayen mu da dangin mu sun moreshi shin ke bakya jin kunya idan kina fad'a masa magana? ki canza kullum dai ina fad'a miki".

Wata uwar harara A'i ta sakar mata tana cewa "ah sannu da 'ko'kari Saude wato nan d'in wa'azi kike min kome"? Kai Saude ta girgiza "a'a ni bance miki haka ba amma dai ina gargad'in ki ki gyara" a masife A'i tace "bazan gyara ba na fad'a ai da ta wuce gaba ake hange kowa yana jin dad'i a 'kauyen nan amma banda mu ko gidan biki muka shiga zakaga ana kallon mu kamar wanda mukai abun kunya saboda mun fita dabam matan fa'kiri😳 kowa da sutura mai kyau banda mu sai kod'dd'un kaya da matattun gyale da hijabai kowa da 'kibarsa mu kuwa a 'kai'kashe kamar 'kanzo hum wannan ce rayuwa kuma a hakan har zakice min bulutu? Na butulce d'in kiyi abinda zaki aikin banza kawai" ta karasa maganar tana jan tsaki babu wanda ya sake mata magana daga Saude har Binta sai takaici daya rufe su Asma'u da suke gefe suna d'inkin hula domin tunda Amatu taje Mopal-Base ta koya da zata zo gida ta sayo musu yanki da zararrika tana zuwa ta ri'ka koya musu yanzu da wannan hular sukan taimaki iyayen su harma su d'anyi abin kansu.

Suna nan zaune Malam Habu ya shigo da fara'arsa yana cewa "ina kuke Saude Binta A'i kuzo nan yanzu ina son magana daku ga dama ta samu" A'i ce akan gaba da kujera a hannunta da gudu tazo ta zauna tana cewa "nesa tazo kusa meye yazo kusa Malam irin wannan fara'a kodai kasar zaku bari"? Ta karasa maganar cikin sha'kiyanci kai ya d'aga mata daidai sauran su zauna yace "eh 'kasar zamu bari idan Allah ya kaimu jibi da rai nida mutumina Sadi" har had'a baki sukai wajen cewa "kasar waje dai Malam amma wacce kasar waye ya biya muku kud'in jirgi"? Murmushi malam Habu yai yana kallon su dad'i ya gama cika shi yana hasko yadda rayuwar su zata canza kwana kusa su dawo jin dad'i kamar da yace "ba'a jirgi zamu ba a mota ne" da mamaki Binta tace "amma Malam wacce kasar ce a mota daga nan ko Niger"? Kaiya girgiza "a'a Binta ba Niger zamuje ba Camaron ne".

"Amma Malam sana'ar me zakuyi"? "Nima ban sani ba yace dai ana samowa kud'i sosai acan saimun je komeye zamuyi fatana Allah yasa muje a sa'a na samu kud'i kona rufin asiri ne saboda ku kunyi ha'kuri ni nasan da haka amma kusa ranku a inuwa ku taya ni da addu'a Allah ya kaini a sa'a idan naje ko nima na samu d'an wani abu nawa harna manta rabo da naga biyar a hannu na wai da sunan tawa humm" ya fad'a abun na masa ciwo arai kafin ya sake d'agowa yana kallon su yace "amma shikenan nan babu komai kowanne irin aiki na samu duk wahalar sa zanyi saboda ku addu'ar ku nake nema kuyita min Allah ya dafa min ya zama shine jina da ganina da kafafuna sannan ya zama hannuna dazan ta'ba abu dashi zanyi kokari zan jajirce nasan ba'a maraya😣 sai rago".

Had'a baki sukai suna masa addu'a harda su Aisha dake gefe tuni suka aje d'inkin hula suna sauraren su farin ciki ya gama cika su ji suke dama Amatu tana nan da zatafi kowa nuna murnarta sun tabbata sai tayi kuka.

Cigaba malam Habu yai da cewa "to sai maganar kud'in mota kunsan dole zaiyi tsada ni kuma dai biyar ban ajiye ba a cikin ku akwai wacce take da kud'i ko dubu biyar ne ta ara min kafin na dawo inyaso ko gurin yaya Ilyah sai naje na ro'keshi da Allah ko zanji tausayi na ya bani 'yar dubu goma shima na rage".

Zaro ido Binta tai tana kallon malam Habu tace "amma Malam kana da tabbacin zai baka"?.

Kai ya girgiza "a'a nima ban sani ba sai naje bana ji a jikina zai bani amma ya zanyi marar abu baya zuciya😔 da inada gurin wanda zanje na kar'bo wallhi ko kallon yaya Ilyah bazanyi ba to amma yanzu idan nace bazanje gurin sa ba gurin wa zanje duk garin nan bani da kowa sai shi sai 'ya'yan yaya Sabi'u su kuma suna marayu abin kunya ne ina 'kanin ubansu ban basu ba nake nema a gurin nasan ba iya garin nan ba har 'kauyukan dake kusa damu sai sun taru sun tsine min".

"Ayya malam ka daina cewa haka insha Allahu yaya Ilyah zai taimaka maka".

Sauke ajiyar zuciya malam Habu yai yana cewa "umh Allah yasa amma banga alama ba, yanzu anan zan samu a gurin ku ne"?.

Da sauri A'i tace "a'a nikam gaskiya malam ta yara ina olo (tsoro) kar nace na tafe d'an kud'in da nake juyawa kazo tafiya batai kyau mu shiga uku mu sake dulmiya cikin wata azabar talaucin kuma nidai kud'i na baifi dubu sha biyar ba kuma wani duk yana gurin 'yan bashi baza ka samu guna ba" ta karasa maganar tana soke d'aurin kwali.

Kai malam Habu ya jinjina yana cewa "ai dama bake na tambaya ba" shiru A'i tai tana murgina kai Saude tace "wallhi malam kud'in gurina yanzu baifi dubu biyu ba jiya yaya Saleh ya turo matar Ladiyo da dare yace na ara masa dubu ashirin na d'auka na bata gashi yau kana so rashin sani yafi dare duhu"

"A'a karki damu babu komai Saude Allah ya miki albarka magana mai dad'i ma sadaka ce".

"To malam me kake nufi ni kuma Allah ya tsine min kome"?.

"Ni bance miki haka ba, ke dama Binta nasan baza'a samu a gunki ba tunda ba komai kike ba shikenan dai bari zuwa goben muga abinda zai faru Allah yasa na samu ina son barin garin nan kodan ku naje nayi aiki tu'kuru na samu kud'i na faranta muku ranku".

Kallonsa suke cikin girmamawa domin gaskiya Malam Habu mutum ne na 'kwarai baya so yaga wanda yake 'kar'kashin sa cikin 'kunci

Please Login or Register in order to submit comment