Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suna haka Asma'u Aisha da Jamila da suke dur'kushe kowa ta tashi tana shiga d'akin su kamar sakan biyu suka fito suna sake dur'kusawa a gabansa kowa da kud'i a hannunta kallonsu yai da mamaki cikin sanyi Asma'u tace.

"Baba ga wannan kud'in ka kar'ba na tabbata zai isheka kud'in mota basai kaje gurin baba Ilyah ba dan Allah".

Hannu biyu Malam Habu yasa yana kar'bar kud'in cikin mamaki yace "a Ina kuka samu kud'i Asma'u"? Asma'u kanta na sunkuye ji take kamar ta fara zubar da hawaye tsananin tausayin babanta ya kamata muryarta tana rawa alamar ta fara kuka tace "baba jiya ne muka sayar da hulunan mu da muka gama d'inkawa gashi munsa wasu kayi kud'in mota da wannan d'in".

'kirgawa malam Habu yai na Asma'u duhu hud'u na Aisha uku na Jamila dubu biyar da yake ta fisu iya d'inki tata har dubu biyar da d'ari biyar ko shida da biyar tana yi haka malam Habu ya had'a kud'i dubu goma sha uku daidai yasan duk da haka bazai isa ba amma ya 'kyale ya ha'kura da zuwa gurin Ilyah tambayar ya taimaka masa kamar yadda 'ya'yansa suka bukata albarka da addu'a mai kyau ya musu kafin suka tashi suna komawa can gaban d'akin su sukaci gaba da d'inka sabin da suka saka dama Amatu da yawa tayo musu yankin da zaren ta bayar akai fulo kawai saidai subi su tisa zubi da ciko A'i dai ta cika tayi fam saboda tun jiya take lallamin Jamila ta bata kud'in ta kara akan jarinta ta'ki ashe rabon malam Habu ne dukkan 'yar 'kwafa tai tana kallon Jamila ji take kamar ta tashi taje ta rufeta da duka kota huce haka ta tashi kamar mara lafiya ta shige d'aki harda hawayen ba'kin ciki tai ta kasa zama tayi nan tayi can sai hasko sanda Jamila ta mi'kawa Malam Habu kud'in take.


Tabdijan A'I kina da abun fad'a bawan Allah yana kokarin yaga ya faranta muku๐Ÿคจ ke kina wani tunani daban akan dubu biyar mstttt๐Ÿ™„ aikin kawai ki turo account number d'inki zansa FANS d'ina kowa ta tura miki 10k๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚ ina shikenan? an wuce gurin FANS kada ku bani kunya ๐Ÿ—ฃ๏ธ๐Ÿ—ฃ๏ธ๐Ÿ—ฃ๏ธina sis Zarah Musa d'an Adam๐Ÿคฃ maza fito ko takan ๐Ÿ—ฃhajia ๏ธNajat Musa Abubakar maman baby nasan akwai money๐Ÿ’ฐ๐Ÿ’ฐ๐Ÿ’ฐ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ yana nan a 'boye a banki๐Ÿฆ dila-dila๐Ÿ™…๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚ wallahi karma kice min baki da kud'i ehe๐Ÿ™„ matar nan kwanan nan kika sake sabuwar mota๐Ÿš˜๐Ÿคธ๐Ÿคธ fil a leda kin barmu da kwanan gida wunin gareji๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜๐Ÿ˜€๐Ÿ˜†๐Ÿคฉ๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜๐Ÿ˜›๐Ÿค“๐Ÿคญ๐Ÿคซ๐Ÿ˜‡๐Ÿ˜น๐Ÿ˜ป๐Ÿ˜บ๐Ÿ™ˆ๐Ÿคธ

Tofa reader's ayi hakuri typing ๐Ÿ“ฒ din yau ba yawa ba kamar na kullum ba na gaji ne ku lalla'ba zuwa gobe idan Allah ya bamu aron rai da lafiya saimu karasa.

MRS รƒL'ร…Mร‰ร‰ร‘ รHMรƒD CรŠ๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜.

MAI TAMBARIN YMA DUTSE๐Ÿž๏ธ ๐Ÿ†•WORLD๐ŸŒ ๐Ÿ†•LIFE๐ŸŒŒ ๐Ÿ†•STYLEโ›ฒ๐ŸŽก๐Ÿš„๐ŸŽข.

JIGAWA DUTSE Sร€BUWAR DUNIYA KUZO KUYI KALLO DA'DI YANA JIGAWA GARIN ILIMI GARIN ADDINI ZAMAN LAFIYA JIGAWA ๐Ÿ‡๐Ÿ‰๐ŸŽ๐ŸŒน๐Ÿฅ€๐Ÿต๏ธ.


๐Ÿ’‹YUSRAH MUSA ABUBAKAR๐Ÿ’‹

We will meet again๐Ÿค— na gode๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™ much appreciated ๐Ÿ‘Œ yabonku gareni ni๐ŸคŸ๐Ÿค.


TYPING ๐Ÿ“ฒ FRI, JUL 12/24 7:13PM YUSRAHMS ABUBAKAR๐Ÿค™๐Ÿค™๐Ÿค™๐Ÿค™.


๐Ÿ’ŽME KAMAR SARKI ๐Ÿ’Ž

AWA
๐Ÿ’ซANNURI WRITER'S ASSOCIATION ๐Ÿ’ซ HOME OF HOSPITALITY ๐Ÿค— AND HARMONY๐Ÿ•Š๏ธ๐ŸŒด๐ŸŒฒ.

WANNAN PAGE DIN NA SADAUKAR DASHI GA DUKKANNIN ๐Ÿ‘‰๐Ÿ‘‰MASOYAN ANNABIN MU MASOYIN MU SAHIBIN MU ABIN ALFAHARIN MU MANZON MU SHINE RAYUWAR MU SHINE MUTUWAR MU SHINE GATAN MU SAYYIDINA MUHAMMADIN RASULULLAH๐Ÿ‘ˆ๐Ÿ‘ˆ ๐Ÿ’• MUNA SONKA FIYE DA RAI๐Ÿ‘Œ DA IYAYE๐Ÿ˜˜ DA DUKIYA๐Ÿ’ฐ MUNA SONKA FIYE DA DUKKA MURADI NA ZUCIYA ANNABI MU MUGANKA SHINE BURI NA ZUCIYA LAMUNCE MU GANKA YA MAI SALSABIL DA KHAUSARA.

BANDA KAMAR KA YA RASULULLAH A DUNIYA BANDA KAMAR KA YA RASULULLAH A LAHIRA.
๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ
๐Ÿคฒ๐Ÿคฒ๐Ÿคฒ๐Ÿคฒ๐Ÿ“ฟ๐Ÿ“ฟ๐Ÿ“ฟ๐Ÿ“ฟ
Hฤ€PPY JรšMรƒ'ร‚T MรœBร…Rร„K
๐Ÿ‡๐ŸŽ๐Ÿ‰๐ŸŒ๐Ÿ๐Ÿฅฅ๐Ÿฅ•๐Ÿ’๐Ÿฅ๐Ÿ“๐Ÿ๐Ÿฅ‘๐Ÿ†๐Ÿ
=_==_==_==_==_==_==_==_==_==_=

KUNA INA FANS KU FITO YAU RANAR MUCE MASOYAN MANZON ALLAH SAW.
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒน ๐ŸŒน ๐ŸŒน ๐ŸŒน
๐ŸŒน ๐ŸŒน ๐ŸŒน
๐ŸŒน ๐ŸŒน
๐ŸŒน ๐Ÿ’“ANNABI๐Ÿ’“ ๐ŸŒน
๐ŸŒน S*A*W ๐ŸŒน
๐ŸŒน ๐ŸŒน
๐ŸŒน ๐ŸŒน
๐ŸŒน ๐ŸŒน
๐ŸŒน ๐ŸŒน
๐ŸŒน
KUCE MINI SAI MANZON ALLAH๐Ÿค—
KUCE MINI SAI MANZON ALLAH๐Ÿค—
HABIBI HABIBI HABIBINA HABIBI MA'AIKI RASULULLAH๐Ÿ’•๐Ÿ’žโœŠ.

ANNABI NAKE 'KAUNA ABADAN BAZAN MAI KISHIYA BA ALLAH KA YARDA NAI YABO GURIN MAHMUDU SHA YABO WANNAN DAKE RABON RABO KYAUTA BA'AI YASHI BA.

YA MUSTAPHA ANNABI HASKEN IDANU NA YA MUNTAKA YARDA DANI YA MASOYI NA๐ŸŒน๐Ÿ’“๐Ÿ’—๐Ÿ’–.


๐Ÿ’žMANZON ALLAH S*A*W๐Ÿ’ž
You are the

YUSRAH MUSA ABUBAKAR INA YI MUKU BARKA DA JUMA'A FATAN DUK ALKHAIRIN DA YAKE A CIKIN WANNAN RANA ALLAH YA SADA MU DASHI DOMIN HASKEN MASOYIN MU๐Ÿ™ ALLAH YA GAFARTAWA MAHAIFAN MU๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ MUSULMAI MAZA DA MATA WANDA SUKA RASU ALLAH YA MUSU RAHMA YA LULLU'BE ZUNUBAN SU๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™.

๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
It's Friday don't forget to recite suratul Al-khaf may Allah bless you and your household may Allah open the door of success 4u all Muslims.
Juma'at Mubarak by Yusrah Musa Abubakar maman little Zaran aunty ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ.

47~AL-WADUD
The Loving
48~AL-MAJID
The Glorious

23~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Munzirinah.

๐ŸŒ„ LEAVE TAKING ND WED๐ŸŒ„
Episode 47_48
_____Kwana biyu tsakani kamar yadda Sadi ya fad'awa Malam Habu haka ne ya faru sun tafi Cameron cikin 'kwarin gwiwa da zummar neman kud'i ta hanyar halal basu sare ba musamman Malam Habu tsabar farin ciki kasa ko shan ruwa yai har suka tafi nan labari ya karkad'e gari malam Habu da Sadi sun tafi neman kud'i Cameron kowa da abinda zai tofa wasu na fatan alkhairi wasu na fatan tsiya harda masu cewa kowa yai ta kansa kwanan nan malam Habu arzikin sa zai dawo ya manta da rayuwar 'kunci.

๐Ÿ™๏ธDUTSE MOPAL-BASE๐Ÿ™๏ธ
Cikin shiri Amatu da Maryam harda Nabilah suka fito harabar gida Maryam na d'auko musu mota zasuje Miyetti kar'bo d'inkin ashobi d'insu idan sun dawo zasuje benin galadima a musu saloon sunsha gyara kamar sune amaren Maryam ce ke driving lokaci zuwa lokaci tana kallon Amatu dake ta faman murmushi cikin mamaki tace.

"Amatullahi na tambaye ki"?.

Juyowa Amatu tai tana kallon ta har lokacin da murmushin ta akan fuskarta tace "eh meya faru"?.

Daidai Maryam zata sha kwanar asibitin police clinic ta shiga takur site zuwa gidan 'kanwar ummansu tace "nifa na kasa ganewa tun d'azu muna breakfast naga sai murmushi kike akwai abinda ya saki farin ciki ne"?.

"Kai Amatu ta d'aga tana cewa "eh akwai kawai na matsu sosai gobe tayi ne".

'Dan zaro ido Maryam tai har tana hadawa da dariya tace "saboda kece Aunty Lailah amarya"?.

Kai Amatu ta girgiza "a'a kawai na tuna gobe umma zata zo zan ganta ta ganni kuma na tabbata babanmu zaizo d'aurin aure Allah yasa domin ambatonsa danai har yasa naji ina kewarsa ke kuma har kikai min wata fassara daban wai amarya rufa min asiri ina zaune lafya amarya a gidan wa".

Le'kowa Nabilah dake baya tai tana cewa "amarya a gidan mijinki koba haka ba"?.

"Eh ba haka ba waye miji na"?.

"Mai sonki mana".

"Waye mai Sona"?.

"Hhhhh ji Amatu da wata tambaya dan Allah taya zan sani abu a duhu kodan banace ba ko wannan zuwa gidan da kikai wani yace yana sonki".

"Oh Nabilah zaki fara ko? Please kiyi shiru".

"Shikenan nayi shiru๐Ÿคญ Nabilah ta karasa maganar tana rufe bakinta parking Maryam tayi da mota suna fitowa suka shiga gidan da ya kasance gate ne amma ba mai gadi kuma ba laifi gidan Masha Allah ya matukar had'uwa matar gidan tana zaune a parlor tana kallo suka shiga da sallama ganinsu yasa ta d'au remote tana rage 'karar vidion tace.

"Tofa Antin gida (Maryam haka take kiranta saboda sunan yayar mijinta ce) yau kune a cikin namu sannunku da zuwa bismilllah ku shigo man kuke ra'bewa kamar wasu ba'ki" zama sukai suna gaishe da ita ta amsa da fara'a taba kallon Amatu tace "wannan yarinyar ce 'yar gidan Binta yayar Bashir ko"? Kai Maryam ta d'aga "eh itace Aunty Umma munzo kar'bar ankon mu a gurin telan momy shine nace bari mu karaso mu gaisa ke"

"Aiko kun kyauta Maryam nagode muku kunfi Ahmad zumunci gashi a kwanakin nan kusan zuwanku hudu amma yaron nan shiru kamar baya gari rabo dana ganshi harna manta sai yanzu da bikinsa ya tashi zanje mu had'u ai sai naci 'kaniyarsa".

'Yar dariya Maryam tana mi'kewa tace "ina Ikram ko bata nan banji motsinta ba"?.

"Oh Ikram tana kitchen wai saurayinta nefa zai zo daga nan-nan Yadi shine take masa iyayi tun d'azu a kitchen ko uwar me take girka masa oho shima da bajajjan hancinsa a gurin".

Murmushi Maryam tai tana cewa "bari na gano abinda take yi ku jira ni" Maryam na rufe Nabilah tace "ai gara kizo mu tafi dan Allah wallhi yanzu idan kika shiga gurin Aunty Ikram sai mun 'bata lokaci muzo munata jiranki baki fito bakuma kin manta zamuje saloon"?.

Wucewa Maryam tai tana cewa "a'a ban manta ba ku jirani minti daya shigewa hanyar da zata kitchen tai tun kafin ta karasa taji Ikram na sakin ashar loya-loya a waya da sauri ta karasa tana cewa.

"Iki miya faru kike zagi"?.

Da sauri Ikram ta rungume Maryam cikin murna tace "ke sis yaushe kika zo kullum ina kiran wayar ki amma ta'ki shiga"?.

Had'e rai Maryam tai "humm ban yarda ba Ikram ganin idona yasa kika ce haka"?.

"Ke wallahi da gaske bata shiga but idan kin koma ki tambayi ya Ahmad zai fad'a miki ai shi muna waya dashi".

"Na'ki na tambaye shi idan da gaske ne ki bari saina koma zan tambaye shi domin daga nan Miyetti muka nufa bari na tafi dama Nabilah tana can a falon Aunty umma tana min 'korafi".

"Oh harda Nabilah kika taho"? Ikram tai maganar tana d'auko abinda data dafa masa da wanda ta soya dukka ta d'ebo musu shi zuwa falor amma Maryam tace bazasu zauna ba kar lokaci ya kure a yau zasuje saloon da lalle gashi yaune farin biki yace sai anyi 'kauyawa party suna shirin tafiya Ikram tace.

"Ku jirani kawai bari na dauko kayana mu tafi nima tunda nasan umma zuwa jimawa zaki le'ka kema ko"?.

Kaita d'aga mata "eh zanje mana zamuje mu gano 'kauyawa party dole" wucewa Ikram tai tana d'auko kayanta a jaka zasu tafi sukaiwa Aunty umma sallama .

Saida suka gama safgoginsu sannan suka kar'bi ashobin suna komawa gida ko zama basuyi ba iya kayan suka aje cikin sauri ganin lokacin yana neman fita musu suka tafi saloon basu suka dawo ba sai la'asar sosai a harabar gida suka ga Ahmad da wasu abokansa suna magana ganinsu yasa yace.

"Amatu dama ke nake nema dan Allah ki fad'a min ya shigar 'kauyawa take mun rasa yadda zamuyi"?.

'Dan harararsa Amatu tai tana had'e rai tace "ai nima ban sani ba saidai kayi sacin a gogul zaka gani" dariya Ahmad yai "haba ke kuwa sorry gani nayi ke kin sani shiyasa Allah kuwa serious nake tambayarki ki fad'a min yadda zanyi"? "Shikenan zan fad'a maka sai zuwa jimawa dan wallhi yanzu a gajiye nake" .

"ok ba damuwa ki huta zamuyi magana an jima kafin lokacin shiri yayi" to kawai Amatu tace masa tana wucewa ciki domin ita yau bata jin dad'i sosai zazza'bi ne yake neman rufeta tana shiga bedroom kwanciya tai taja bargo dan har taji sanyi ya mata kad'ata kallonta Maryam tai "Amatu yada kwanciya"? Kaita d'aga "eh bana jin dad'i ne".

"Ok Allah ya sauwake amma da kin tashi kinga la'asar fa tayi idan an Kira sallah saiki kwanta" "eh zam tashi wanda nake son maybe hakan zaisa naji d'an dama dama zazza'bi keson kamani".

"Subahanallahi Amatu zazza'bi kuma Bari naiwa ya Ahmad magana yazo ya duba ki".

"A'a karki kira shi ban tabbatar ba tukuna sanyin da nakeji ne ga jikina yai zafi" tun kafin Maryam tayi maja Ikram taja tsaki tana jan hannun Maryam tace.

"Ke dan Allah zo mu tafi yar rainin hankali wai tazo birni ta waye sai wani wahalar dake take wai ita ga maamaa kema kina biye mata muje share ta" murmushi Maryam tai tana dafa goshin Amatu da gaske jikinta d'au yake da zafi kamar wuta kai ta jinjina tana cewa.

"Amatu zazza'bi man kike bari na kirashi" fita sukai Ikram sai harararta take tabe baki Amatu tai tana gyara kwanciyar ta tace "wannan budurwar akwai yar jin kai amma babu komai ina daidai da zamaninki wallhi ba kyaleki zanyi naga take-takenki nima zan fito miki cikin kalata idan ba haka nayi miki baza mu zauna lafiya ba baki isa raina niba dan daga 'kauye nazo".

Bayan sallar magriba suka fara taruwa a harabar gidan inda zasuyi 'kauyawa kowa yayi shiga kayayyaki komai daban-dabam harda amarya Lailah tasha had'in gambiza da tawagarta daga gida dubu ba shigar wanda tafi hargitsa ba'a ci dariya an more har ciki yai ciwo ba saida ango yazo da abokansa riga daban wando daban takalmin 'kafarsa d'aya fari d'aya ba'ki silifas da combus๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚ ga d'aurin kara a wuya๐Ÿคฃ๐Ÿคฃinnalillahi wai maimakon a d'aure a d'auko aka shine suka d'add'auro shi a wuya sun datsa shi 'kanana yadda zai dadi daurewa ansha dariya fuskar amarya Lailah tasha kwalliya da bakin kwalli idan ka ganka birad'al kamar ka gudu ga takalma an zurasu a jikin gyale kowa ta d'aure a kugu ga kuma sandunan rake ana sha 'kawayen amarya kuma sunyi d'an malele yasha manja da yajin maggi๐Ÿ˜‹๐Ÿ˜ƒ sun yanka albarka da cocumber abun dai sai wanda ya gani 'kauyawa party yayi kyau ansha dije sosai an girgije dama Ahmad yace kunyarsa galan d'aya ce kuma ranar aurensa zai tintsirar dashi haka ne kuwa ya faru ya gyagiye ba laifi kalangu ya daku a gurin makad'i sai kusan karfe goma ta dare suka koma gida sannan Amatu ta dad'e dayin barci domin bataje ba zazza'bi ya hanata zuwa.

Washe gari tun wuri gida ya sake cika Binta ma tazo tare dasu Aisha harda Saude da A'i Amatu tayi farin ciki ta 'kara ganin ahlinta anan Binta take fad'a mata malam Habu ya tashi sun tafi neman kud'i tare da Sadi tuni murna ta sake lullu'be ta harda hawayenta ta d'aga hannu tana rokar nasa samun abinda yaje nema duk sai taji zazza'bin nata ya warke da Binta ta mata wannan albishir mai dad'i.

'Karfe hudu aka d'aura auren Ahmad da Lailah a babban masallacin sallar idi da yake wajen gida dubu bakin Ahmad kamar zai yage๐Ÿ˜‚ tsabar murna bayan an gama daurin abokan sa sai taya farin ciki suke suna bashi hannu haka da suka shiga gaisuwar iyaye Ahmad ba kunya harda 'kara jawo Lailah jikinsa a gaban mutane sukai photuna kafin zuwa yace ta sanar da 'kawayen ta dinner nan da 'karfe biyar a moderling event center๐ŸŒ†.

Biki yayi biki haske ya gama haskawa a wajen kid'ane mai mugun 'karfi yatshi kamar kunnen mutum zai fice tsabar 'karar tai yawa Amatu da su Maryam suna gurin harda su Aisha Asma'u da Jamila sun zo balle iyaye 'kirjin biki su Safiyah da Aunty umma su maman Asraf sune akan gaba suna rawa 'ya'yansu sunai๐Ÿคญ Binta dai dasu A'i suna gefe suna kallon abinda yafi karfinsu suna mamaki su abun saiya zama sabo a gurin su anyi bajinta an raba kyautuka na fad'a a gurin humm Safiyah tayi kokari.

Har dare yai sosai ba'a basu ankara motoci da yawa sun tafi wasu ma babu mutane ga guri ya d'au duhu hankali tashe Amatu tace.

"Maryam wai me muka tsaya yine kalli fa babu kowa daga mu sai masu dije kuma suma tafiya zasuyi dan Allah ki Kira ys Ahmad idan bazai samu damar zuwa ya d'auke muba ya turo mana mota".

Shiru Maryam tai cikin tunani da rashin madafa tana kallon su tace "kuzo muje" ta juya zata fara tafiya Amatu ta dakatar da it's "muje ina Maryam date nefa"? Amsa Maryam ta bata suna kokarin fita tace "eh aina sani zan Kira ya Ahmad amma gara mubar wajajen nan haka baki gani ba masu dijen kamar marasa gaskiya sai kallonmu su d'ayan harda murmushi suna fitowa ta dialing numbar wayar Ahmad tana kiransa yana d'agawa tace.

"Ya Ahmad an baro mu acan fa babu mota ka turo a d'auke mu".

Daga can 'bangaren cikin fad'a Ahmad yace "azo a d'auke ku duk da uban me kuka tsaya yi har aka watse"?.

Kallon Amatu Maryam tai kamar zatai kuka "tace dan Allah yanxu ba lokacin tambaya bane la rufa mana asiri kazo ka d'auke mu daga baya saikayi mana fad'an" tana rufe baki d'ittt taji ya kashe kiran kallon su tai jiki a sanyaye tace.

"Bazai zoba gara mu tafi da wannan tsaiwar tamu anan bamu sani ba ko wani ya fake yana kallon su da asara gara gidadanci da zaman banza gara aikin kishiya ko zata zagi uwarka๐Ÿคช๐Ÿ˜  ku muje mubar wannan" aiko tana rufe baki suka d'eba a guje suka bar gurin tun suna tafiya da sauri har suka gaji suka dawo tafiya a hankali da azaba tai azaba duk cire takalman kafarsu masu tsini๐Ÿ‘  sukai suna rikeshi a hannu sunaci gaba da tafiya gashin sun fahimci kamar binsu ake motar bayansu kamar daga gurin event din domin mai motar yaiwa Amatu magana bata kulashi yaiwa Ikram ita kuwa harda ashar ta sakar masa dama saida ya jinjina kai kafin yabar gurin da suke a modeling din daga haka basu sake ganin wulginsa ba Nabilah tsabar wuya tayi wuya har kuka take dayake dama ita raguwa ce ga shagwa'ba bata juri wuya ba.

"Haba ke kuwa Nabilah wannan kukan ba magani zai miki ba abinda yafi sau'ki kiyi shiru insha Allahu babu abinda zai samemu har muje gida" Amatu tai maganar tana ri'ko hannunta tare da kar'bar takalman data ri'ke da jaka duk dan ta rage mata kaya ko tayi shiru hatta gyalenta da d'an kwalin kanta suna hannu duk tabi ta burkice ganin motar tayi kusa dasu yasa ta kara fashewa da kuka tana cewa.

"Wayyo Abbana ka taimake mu zai kashe mu".

A fusace Maryam ta juyo tana cewa "wai ke Nabilah kinyi hauka ne ubanwa kike fad'awa anan d'in kin wangame baki sai kuka kike 'yar tselan uwa kawai wallahi idan baki rufa min baki ba saina fasa shi".

Cikin jin haushi da gajiya Ikram tace "Maryam 'kyale 'yar bura uba ta zauna anan d'in Abban yazo ya ceceta kinga nan da kwana uku sai muci waina aikin banza kawai mstttt haba dan masifa kin dame mu da kuka keba jaririya ba waye bai gaji ba ya danne saike ce fallalliya harda kiran Abba ai mu kuma daga sama muka fad'o bamu da uba shiyasa bamu kirashi yazo ya cecemu ba saike ko na sake jin bakin nan".

"Haba dan Allah kuwa wannan tai mata wannan tai mata dame zataji da gajiya koda jarabarku"?.

Harara Ikram ta sakarwa Amatu tana cewa "to uwar iyayi ban sako dake ba bana son shishshigi ga da wacce nake idan kuma bazata iya yin shiru ba saidai mu raba tafiya tunda duk wani harkar 'kauyanci ta iya".

"Baza'a raba tafiya ba amma dai ku 'kyale ta gaskiya takurar taku tai yawa irin haka da a gida d'aya kuke wannan ai saiku sa ta rame keda Maryam hum'um".

"Ke rufe min baki ina ruwanki ne a tunani da Nabilah nake magana ta bada ke ba dan haka karki sake shiga ciki" Ikram na rufe baki Amatu tace "idan kinyi da ita kamar kinyi dani ne domin yar uwata ce kuma jini na ke bari fa kiji baki isa kice zaki fad'a min magana na 'kyale kiba never in history kin gane"? Cikin 'bacin rai Ikram ta kalli Amatu tana shirin magana sukaga hasken motar ya haske musu idanu tuni suka manta da abinda suke kowa ta rud'e ciki ya d'uri ruwa ri'ke hannun Nabilah Amatu tai cikin jarumta tace "kada kiji babu abinda zai same mu insha Allahu zamu koma gida lafiya" janta tai suka cigaba da tafiya yayin da Maryam da kuma Ikram suka tsaya guri d'aya sun kasa gaba ganin har Amatu tai nisa yasa Maryam d'aga murya tace.

"A'a Amatu kada kibi tanan bakisan waye ba kizo mu canza hanya".

Amatu bata tsaya da tafiyar da take ba kuma bata juyo ba tace "wallahi Maryam bazan canza hanya ba tanan zanbi babu wani mutum da yake da ikon da zai cutar da d'an uwansa sai Allah yaso idan kuna iyawa ku taho mu tafi idan bakwa iyawa ku tsaya anan d'in ko ku canza hanyar mukam mun wuce".

A rikice Maryam tace "a'a Amatu kada kije kizo mubi tanan".

Ko juyowa Amatu batai ba suka yi gaba sunje daidai motar suka tsaya su Maryam na tsaye daga nesa jiki na'bari suna kallonsu suga abinda zai faru a mamakin su gani sukai sun shiga motar tabar gurin ihu Maryam tayi tana cewa "na shiga uku na lalace idan na koma gida ba tare dasu ba me zance waye wannan ya d'auke su kar suje a kashesu" ta'be baki Ikram tai tana cewa "a kashe sun mana uban waye ya kaisu ba kinyi musu magana ba sukai kunnen uwar shegu dake Allah yasa kidnapping d'insu akai naga ta tsiya" harara Maryam ta zafga mata "ba amain ba mai bakin tsiya insha Allahu babu abinda zai samesu" tsaki Ikram taja daidai wani mai keke napep yazo wucewa suka tsayar dashi suna ce masa Mopal-Base sannan suka shiga babu kud'i a hannunsu saida suka sauka Maryam ta kar'bo ta kawo masa a gajiye suka shiga bedroom turus suka tsaya suna 'kare musu kallon mamaki dama gida suka zo d'agowa Nabilah tai tana kallon su ganin yadda sukai yasa ta kwashe da dariya tana cewa.

"Sai yanzu kuka 'karaso? sannunku da hanya".

A fusace Ikram tace "ke dawa kike uban wa kikewa sannu"?.

Shiru Nabilah tai bata, bata amsa ba sai mi'kewa datai tabar d'akin tsaki Ikram taja tana cewa "zanci ubanki ne Nabilah kafin nabar gidan nan maza cigaba da shiga safgata jikin kine zaiyi tsami" kallon ta Amatu tai baki bud'e dariya na kamata tasan duk cikin jin haushin su taho sun barsu ne ga gajiya maida hankalin ta tai kan Maryam data cire kayan tana sauke numfashi tace.

"Sannunku da zuwa abinda bakwa so d'in dai zan fada sai yanzun kuka karaso"?.

A masife Ikram tace "oho miki kema ba'a sani ba".

"Kada Allah yasa ki sani idan ke nake tambaya" mutsssssss Amatu taja tsaki tana kallon Maryam tace "amma a abin hawa kuka zo dan naga da 'yar tafiya kuma kunyi saurin zuwa"? Kai Maryam ta d'aga "eh d'an napep muka tara badon haka ba ai da yanzu muna can a hanya to amma ke Amatu waye mai motar daya kawo ku"? Dariya Amatu tai cikin tsokana tace "wannan saurayin ne dayai min magana ban kula Shiba ya koma kan Nabilah itama ta share shi to shine ya d'auko mu" zaro ido Maryam tai "haba dai dan Allah da gaske bakuji tsoron ya sace kuba"?.

Kai Amatu ta d'aga "eh man ba wani sace mu dazaiyi bayan tare suke da ya Ahmad".

Da mamaki Maryam tace "kai dan Allah harda ya Ahmad amma baki mana magana kawai kuka shiga kuka tahowarku"?.

"Eh shine yace na 'kyaleku ku taho da sayyadarku ('kafa)".

"Humm ai shikenan ya Ahmad ya kyauta kuma wallahi tunda haka ne gobe bazanje G9 (jinayin) gidansa ba na kara shan wahala balle yana zumud'in amarya ko ta kanmu bazai bi ba".

Dariya Amatu tai "kai Maryam kema dai wallahi aiko zuwa gidan sa ya zama dole gobe 'karfe hud'u da rabi na asuba zaki tashi ki musu breakfast kuma kikai idan da dama sai kinyi seving d'insu kin jira sunci sannan ki wanke kayan ki mata shara sai ki dawo๐Ÿ˜‚" ta karasa maganar

Please Login or Register in order to submit comment