Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsaya da wankin nan kici abinci kada olsa ta kama ki tun dazu na kawo miki na dauka ma kinci yanzu harya huce" numfashi mai zafi Indo ta fitar tana mi'kewa tsaye tare da rike bayan ta cikin yamutsa fuska alamar bayan ya rike ciwo yake mata ta fita cikin kayan wankin tana zama kan kujera ta bud'e kwanon ta fara cin abincin.


Fitowar Asabe kenan ganin abinda dake faruwa yasa ta karaso gurin da sauri tana zuwa tasa 'kafa tai bol da kwanon abincin ya tarwatse a kasa tabi da takalmi ta murmushe shi a kasa kafin ta juyo ta dauke Indo da mari wanda sai data kifa daga kan kujerar da take.
A masife ta soma magana "amma lallai Indo kin raina min hankali har nice zan kafa miki doka wannan bulkumar uwar taki mai kama da icen dogon yaro da ba'kin ido ta sa kika sabawa umarni na? Aiko yau sai kinci 'kashin ubarki" ta karasa maganar tana rufeta da doka ta ko'ina.

Wani irin d'aci ne yazo ya tokarewa Dalah a makoshi tana kallon yadda Asabe ke dukan Indo wanda ta rantse da Allah ko jaki baza a yiwa wannan dukan ba jin ihun da Indo take abin tausayi ga jini yana fita a hancin ta yasa zuciya tazowa Dalah wuya a fusace taje ta fincike Asabe a kan Indo tai wurgi da ita tana d'aga Indon dake kwance tana kiran wayyo ciki wayyo ciki.

Yunkurawa Asabe tai da'kyar ta mike domin ta bugu a kafa ta karaso tare da cukumar Dalah itama Dalah da ta riga ta hauro ranta a mugun 'bace ta sha'ki asaben wanda asabe taji shakar cikin bala'i ta soma magana "ki sake min wuya Dalah wallahi kin kira masifa da kanki zaki ga bala'in dayafi karfin tunanin ki saina sauya miki kamanni ki saki ni nace".

'Kara sha'ke ta Dalah tai tana cewa "ke din banza baki isa kimin komai ba bari kiji wata magana 'kyale kin da nake kike min cin mutunci kike yi duk abinda kikai niyya kinga na zuba miki ido ba yana nufin bazan iya daukar fansar abinda kike min bane amma yau kin gama yawo Asabe zaki yabawa aya za'kin ta".

Da gudu Bahijjah ta fito daga d'aki tana cewa "ai wallahi Dalah baki isa ba kika kashe min uwa kema saina kashe ki dallacan sake mata wuya" ta karasa maganar tana jan hannun Dalah wanda Dalah cikin kunar rai tasa d'ayan hannunta ta saukewa Bahijjah mari kara Bahijjah ta saki a gigice tai baya tana kuka kokawar kwacewa Asabe ta soma tana cewa "kinsan Allah Dalah kin shiga uku kin gama yawo kwanan ki ya 'kare kuma zaki gani" "naga alkairi baki isa kimin abinda Allah baiyi min ba" Dalah ta fad'a tana wujijjiga Asabe ta dokata da kasa tabi ta turmushe ta jin da Asabe tai Dalah na neman illata ta yasa ta soma kurma ihu tana kiran ma'kota suzo su ceceta kowa naji yai burus domin dama haushinta suke ji akan gallazawar da takewa Indo yau kuma take neman agaji wanda yazo ceton ta ma ya cika 'kasurgumin munafiki haka Dalah ta luguiguita Asabe Saida ta mata dukan data tabbata ya gama ratsa jikin ta sannan ta 'kyale tana rike hannun Indo suka bar taje ta bata wani abincin kafin ta fito ta d'ora mata ruwan zafin da zata dumama jikinta Asabe kam na kwance sai zafga ihu take ba ma'kwafcin daya leko balle ya tambayi me ake.

Da dare bayan sallar Isha Binta ta shigo d'akin su Amatu ganinta zaune sauran suna kwance yasa tace "mamar gida baki bacci ba zaman me kike"? Sauke ajiyar zuciya Amatu tai tana kallon Binta tace.

"Umma na gaza yin bacci ne ina ta tunani akan goben mu" kallon mamaki Binta tai mata jin abinda tace yasa ta ce "kamar ya"? Cizon yatsa Amatu tai cikin damuwa tace "umma na sani cewa muna cikin wahala da 'kuncin rayuwa kuma kowa ya sani musamman baba Ilyah yana da wadata amma ya taimaki babanmu ya'ki ga 'yan uwa na kowa ta damu taga tayi aure amma babu saurayin dake zuwa kofar gidan nan taulauci kamar a kan mu aka fara kullum wannan abun yakan hana ni bacci duk wanda ya d'ebo cin mutuncin sa sai yazo ya sauke mana kamar mune muka dorawa kanmu talaucin kinga jiya da bakya nan kinje anguwa Kande matar me gari har tsakar gidan nan tazo bakiji irin cin mutuncin da taiwa umma Saude ba akan Buba yazo hira gurin Asma'u harda gori iri iri kwata kwata jiya raina a 'bace na wuni".

Kallon ta sosai Binta keyi gaskiya akwai matsala a gidan nan wacce dole sai sun tashi tsaye sun had'a 'karfi da 'karfe sun magance ta sake kallon Amatu tai a karo na biyu tace.

"Amatullahi kiyi hakuri ki daina saka damuwa a ranki kada kina yarinya hawan jini ya kama ki insha Allahu komai zai daidaita kinji" kai Amatu ta d'aga batare datai magana ba Binta taci gaba "Amatu dama akwai abinda nake son fad'a miki gobe idan Allah ya tashe mu da rai ki shirya zamuje gurin 'kani na Bashari".

Zaro ido Amatu tai da mamaki tace "wai baba Bashir? kenan gobe zanga su Nabilah da Maryam kai amma naji dad'i umma Allah ya kaimu tun asuba zan fara shiri" murmushi Binta tai ganin ta kawar mata da wancan damuwar dake damunta tasan yau zata samu bacci cikin kwanciyar hankali mi'kewa tai tana cewa "eh ki shirya insha Allahu da wuri zamu tafi" "to umma saida safe" mi'kewa Binta tai ta fita yayin da Amatu ta cika da murna sosai domin ta dade bataje ba ganin bacci ya'ki daukarta yasa ta mike tayi alwala ta fuskanci gabas ta fara nafila tana jerowa mahaifin ta addu'o'i na samun wadatuwa da arziki mai dorewa".

Washe gari da wuri kamar yadda Binta tace mata suka shirya itakam Amatu tun asuba ma tai wanka suna karyawa ta shiga d'akin malam Habu yana kwance ya d'aga kansa sama ga kwanon d'umamensa da aka kawo masa bai tashi yaci ba durkusawa Amatu tai tana cewa "baba ina kwana"? Tashi zaune malam Habu yai yana murmushi yace "lafiya na tashin mamana har kun gama shiri kenan yau sai kwanan birni"? 'Dan sauke kai Amatu tai tana cewa "baba dan Allah na roke ka kadaina sa damuwa a ranka in Allah yaso wata rana sai labari komai yai farko zaiyi karshe duk nisan dare gari zai waye inda jirgin sama yaje kunkuru ma za'a ce masa barka da zuwa na sani kana cikin damuwa sosai baba amma ka roki Allah shine mai badawa idan kuma ya baka babu wanda zai hana ka" ta karasa maganar da shar'bar hawaye.

Har lokacin murmushi malam Habu keyi yana mai matukar farin ciki da godiya ga Allah da samun Amatu dayai matsayin 'ya a gareshi duk sanda ya shiga kunci ko damu ita ke fada masa kyawawan kalamai tayi amfani da sansanyan lafazi koda yaji bazai iya jurewa data fad'a masa zai ji ransa yayi sanyi kallon ta yana cewa "mamana kada ki damu share hawayen ki Allah ya miki albarka ya tsare min ke a duk inda kika tsinci kanki ya baki miji na gari wanda zai rike min ke da mutunci ya kyautata ki ya faranta miki kamar yadda kike faranta min" Amatu na shashshekar kuka tace "amin baba na gode da adduar ka gareni" "kada ki damu mamana Allah ya kiyaye hanya saikun dawo" mikewa tai ta fita yayin da malam Habu ya bita da kallo ji yake kamar da ransa zata tafi baya so tai nisa dashi ko kadan saidai ya danne bai nuna ba domin matukar Amatu ta sani baza taje ko'ina ba bude murfin kwanon yai ya soma cin tuwon a bisa jin yunwa badan yana so ba dawa tazo gida baida kudin dazai saya yaje wajen mutane da dama ya roke su ya basu gero su bashi dawa sun'ki.

Amatu na fitowa taga su Aisha sun dauki kaya zasuyi musu rakiya Binta kuma ta shiga d'akin malam Habu sallama taiwa su Saude kafin tai jin Bintan ta fito suka tafi saida suka hau mashin sannan su Aisha suka juya gida cikin rashin jin dad'in tafiyar Amatun.

'karfe daya na rana suka sauka a Dutse round na farko tare da 'yar jakar kayansu anan suka sake tarar d'an mashin sukai masa kwatancin anguwar da zai kaisu.

Bashir 'kanin Binta ne uwa daya uba daya shima dan asalin 'kauyen ne karatu ne ya fara kawo shi cikin dutse bayan ya kammala ya fita da kyakkyawan result wanda yai sa'ar wani mutum da suke hayar gida a gurin sa ya musu hanya su biyar aka dauke su aiki nan da nan ya samu abun hannu har yana iya taimakawa yan uwansa daga karshe ya sayi fili yai katon gida ya auri wata mace mai suna Safiyyah yar babban mutum ce kuma Allah ya azurta su da yara uku Ahmad shine babba sai Maryam da Nabilah suna zaune a mopal Base (mofalbes).

Mashin na sauke su Binta daidai an bud'e kofar gate din gidan mota ta fito biyan d'an mashin kudinsa tai Amatu ta dau jakar suka karasa sauke glass din motar akai matar Bashir ce da alama gurin aiki zataje fuskarta da mamaki ta dan zaro ido tana cewa "wata sabon gani anya ba 'batan kai kuka yi ba wa naka gani kamar aunty na ta kaina"?.

Murmushi Binta tai domin inda sabo ta saba da tsokanar Safiyyah indai tazo cikin wasa Binta tace "eh 'batan kai mukai shine muke tambayar gidan wani Bashir ko kin sanshi"? Dariya suka sa gabadaya banda Amatu dake murmushin jin dad'in ganin yadda safiyyah tai ba nuna wulakancin yan kauye sun zo.

Mayar motar da baya Safiyyah tai tana cewa "mai gadi amso kayan su ka kawo parlor" da gudu mai gadi yace "to hajiya" kallon su tai fuskarta fal da fara'a tace "mu karasa ciki" katseta Binta tai "ba wani gurin zakije ba kada ki makara mu yan gida ne har zaki dawo" kai Safiyyah ta girgiza "eh office zanje amma babu damuwa zan kira na sanar dasu yau bazan samu bulla ba ku shigo ina zanyi wannan manyan ba'kin na tafi wani gun ah ku shigo muje ku huta kun shawo rana" shiga katon falon gidan sukai babu kowa bayan sun zauna ta bud'e fridge tana dauko musu ruwa mai sanyi da drinks ta aje musu tana cewa" sannun ku da zuwa ya hanya da gajiya"? "Lafiya kalau ya muka sameku ina yaran ne banga ko daya ba"? "Sunje makaranta Najeeb kuma yana hospital wajen practical, bari nasa a kawo muku abinci" ta fad'a tana mikewa ta shiga wata kofa.

Sauke ajiyar zuciya Amatu tai tare dayin tsam tai shiru bata sha ko ruwa ba kallonta Binta tai tana cewa "Amatullahi meke damunki"? D'agowa Amatu tai idonta fal da hawaye tace "umma na tuna baba ne yanzu ko a wanne hali yake ya samu abinci yaci ko baici ba" kai Binta ta girgiza cikin kwantar mata da hankali tace "ki daina kuka yana halin lafiya cikin 'koshi domin dazu da zamu taho bayan na shiga d'akin na bashi dubu biyar nace ko d'an wani abu ya saya dan haka ki daina sa damuwa a ranki" sansanyan numfashi Amatu ta sauke kafin fuskarta da annuri ta dau ruwa tasha wanda Binta taji dad'in ganin sakin ran da Amatu tai.


Empire masarauta
Tun asuba su Ameer suka koma hospital domin sake jin me doctors zasu ce akan case din Khimiyyah a wanne hali take kuma jiya iyau babu wani labari mai dad'i.

Mami ta samu zazzabin ya sauka taji sauki saidai tayi kiran Asad bai d'aga ba tayi tunanin ko yayi fushi ne a zahirin gaskiya kuwa baya kusa da wayarsa mi'kewa tai tana fita ta shiga gurin me martaba tayi tare da neman izini ta zauna cikin nuna alamar damuwa tace.

"Ranka ya dade kayi hakuri abinda ya faru na sani babyn Mami yayi kuskure ina nema masa afuwarka".

Shiru taga mai martaba yayi bai d'ago ba bai kuma ce komai ba tasan lallai Asad ya fusata shi sosai kuma batasan da yadda zata bashi hakuri ba ko ta taushi Zuciyar sa a wannan lokacin, sake kallon sa tayi yana kallon kasa sauke numfashi tai tana nazarin sa cikin zurfafa tunani tace.

"Allah ya baka nasara magana nake".

'Dagowa yai yana kallonta ba tare da yace komai ba ha'ki'ka yana matukar kaunar Mami a rayuwar sa har baisan yadda zai kwatanta ba baya so yaga bata cikin walwala ko kadan a duk sanda ya kalleta yakan tuna lokacin suka had'u Mami balarabiya ce yar Bahrain ce sun had'u da mai martaba a Makkah wajen aikin hajji tun lokacin mahaifin me martaba nada rai sukai soyayya ta kwatance har sukai aure kuma rana daya ya aure su ita da sultana Fatima mahaifiyar su Ameer ita kuma 'yar Nigeria ce.

Ganin yayi shiru dama tasan bazai samu damar magana ba a irin wannan yanayin amma dai dole zata tsaya ta jajirce ta bashi hakuri tana shirin magana taji saukar muryarsa yace.

"Hauwa'u Asad ya fad'a miki me Khimiyyah tayi masa"? Cikin d'an jin sanyi a ranta sakamakon maganar dayai muryarsa ba a cikin fushi ba ta samu 'kwarin gwiwar cewa.

"A'a ur highness na Kira wayarsa bai d'aga ba nafi tunanin ko baya kusa" "amma me kike tunani ya had'a su"? "Gaskiya mai nasara ban sani ba nidai ana kamar gobe hakan zata faru ya shiga gurina da dare zaiyi min saida safe yake cewa yau kwana zaiyi yana aiki ya kusa gano abinda yake nema na masa fatan alkairi ya fita shikenan tsakani na dashi sai lokacin da Ajeeb yazo yana fad'a mana abinda yake faruwa na Khimiyyah da Asad din".

Kai mai martaba ya jinjina yana cewa "shikenan zanyi magana dashi karki damu ya jikin naki" "ranka ya dad'e yayi sauki" "Allah ya kara afuwa zuwa jimawa ki shirya idan mukaje duba jikin Khimiyyah sai kiga likita" "to ur highness godiya nake" bari naje na sake gwada kiransa ko zan dace ya dawo" "ok koda ma ace ya d'aga karki ce masa komai ki bari a hankali zan tambaye shi" Mami taji dad'in yadda mai martaba bai zafafa abinda Asad din yayi ba murmushi jin dad'i tayi tana cewa "to Allah ya baka nasara a huta lafiya" fita tai cikin murna sosai a farko tazo da fargabar meye zaice mata sai kuma taga canjin yanayi fiye da yadda take zato.

Till we meet ๐Ÿค—๐Ÿ’ƒ.

Mrs Al'ameen Ahmad ce mai tambarin YMA dutse Jigawa new world new life and new style ๐Ÿ‘Œ sabuwar duniya garin dad'i a kusa dutse birnin daraja daya batse ga haske ๐ŸŒƒ ga adon dutse ๐Ÿž๏ธ๐Ÿ”๏ธ.

Wannan page din naki ne keda mijinki fatan alkairi Allah ya sameku ya baku zaman lafiya ya sauke ki lafiya musha biki๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ‘Œ mu caskale.
BINTU MATAR SALISU
SALISU KOLI MIJIN BINTU MAI TAMBARIN NO GOING BACK๐Ÿ’ฃ๐Ÿ”ซ๐Ÿ—ก๏ธ๐Ÿ”ซ SOJA๐Ÿ‘ฎ MARMARI DAGA NESA ALLAH YA DAWO MANA DAKAI GIDA LFY ALLAH YA KARE KA DAGA SHARRIN MIYAGUN MAKIYA ALLAH DA SUKE CIKIN WANNAN DAJI NA SAMBISA๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜”๐Ÿ˜ฑ

Allah ya sauke ki lafiya ya kawo mana babyn mu a halin lafiya ya raya mana shi a tafarkin shiriya ta addinin musulunci Amin๐Ÿ‘.


Reader's yanzu lokacin azumi ne a sati zan ri'ka yi muku typing sau d'aya in Allah ya kaimu bayan sallah da rai da lafiya saimu ci gaba sosai to da fatan kun fahimce ni๐Ÿ˜œ๐Ÿคž๐Ÿคญ.

Sai mu sake hadewa satin sama idan mai duka ya bamu aron kwana rai da numfashi da lafiya zamu d'ora inda muka tsaya yan group din mu barkan ku da shan ruwa happy drinking water to all Muslims.
Annuri writer's association
Mr Hausa Ebook group 2/3 and 4
Vip women 24 tv novels and documents group
Hajara Abla's Glam group
Salmahrt md group
Ni'imatullah fan group
Da sauran group din da ban fad'e ku ba ina mi'ko muku d'unbin godiya ta da fatan alkairi a gareku.

{Mon Mar 11/24 9:04} TYPING ๐Ÿ“ฒ YUSRAHMS MAMAN LITTLE ZARAN AUNTY ๐Ÿ’ƒ.

๐Ÿ’ŽMe kamar sarki ๐Ÿ’Ž

๐Ÿ’ซ ANNURI WRITER'S ASS๐Ÿ’ซ


Malam always be watchful don't take risk don't try to get lost try to protect your life ๐ŸŒŒ always ๐ŸŒน๐Ÿฅ€๐ŸŒท be good be helpful people will like u to be a happy child like my daughter Fatima Ilham ๐Ÿ‘Œ then people will like u.

May Allah open the door of success for all of u may Allah accept our du'as may Allah bless us may Allah protect us and our family with all calamities amin amin.


Ga wata sanarwa ta musamman domin ban gane ba anyi gabas da kare gaskiya bazan dauka ba naga an fara amfani da wani bangare na littafi na kuma na gano wacce to ki bari dake nake mai kafafun agwagi idan kuma ba haka ba wallahi tallahi zaki yabawa aya za'kin ta don zaki ji kira sai dai mu had'e gaban hukuma ๐Ÿ˜ ๐Ÿ˜ก.

Yusrah Musa Abubakar ta kowa ce๐Ÿ˜œ.
[email protected]


Ya sahibul fairati d'an gidan batuli kai kanka amsa ne ga masu yin su'ali ganinka nasa a tuna da zulkamali barhama babban lamari nake nufata.

13~AL-MUSAUWIRU
The fashioner of forms
14~AL-GAFFAR
The Repeatedly forgiving.

7~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Abidina.

๐ŸŒ„ Session nd reaction๐ŸŒ„
Episode 13&14
#'KAUYE#
Majalisar manyan gari zaune suke fal sun cika guri ana ta hayaniya Tanko ya ta'bo Mudi yana nuna masa Malam Habu wai ya kalla anyi new dariya suka 'barke da ita Mudi yana cewa "malam Habubakar naga ka saro goro waye ya baka jari ko matarka ce Binta domin naji ance ka tura ta maula binni gurin 'kaninta" caraf Tanko yace "ai basai ka tambaye shiba kaga alama fad'a batawa lallai kace kwanan nan malam Habu za'a dawo attajirin da babu kamar sa a kauyen nan" hhhhhhhhhhh!!! Suka kuma fashewa da dariya suna cewa "Allah ya biya d'an uwan marigayi malam Sabi'u malam Habu katargar sugar kowa ya ra'bu dakai saiya lasa" suka 'kare maganar cikin sha'kiyanci.

Malam Habu na jin su ya dake bai nuna musu yaji haushin abinda suka ce masa ba ya kalli Sadi dake kusa dashi yana cewa "Malam Sadi na tambaye ka wani abu"? Da mamaki Sadi yace "tambaye ni mana Allah yasa na sani" kai malam Habu ya jinjina yana cigaba da cewa" a garin nan kowa ya sanni yasan halina ina kud'i ina da ma'ko a ciki na ma bana ci kullum ina yawo cikin datti hatta gidana ban iya rikewa ba gani da gonaki nayi shukar amfani iri daban daban amma na rufe shi a rumbu na'ki wadata iyali suci su 'koshi kullum suna gantali a gidajen mutane ana basu a hannu ana zund'ensu ana yamud'id'i ana zagina shin dan Allah banji kunya ba? Banyi asara ba? Ban fad'i ba girma ya zube cikin ahlin...............................

Dariyar da gurin ya kaure ne yasa malam Habu bai karasa maganar ba kuma ya dake ko d'igon murmushi baiyi ba balle ya taya su dariyar a fusace Tanko yace "Allah ya isa tsakani na dakai Malam Habu tunda har kasan wannan maganar ehh ban ciyar da ahlin nawa ba meya hana ka kawo musu naka kai da yake sarkin noma ne" hararar sa malam habu yai yana cewa "Tanko dan ka tsargu ne amma ni ba dakai nake ba labari fa na bayar kuma ba kai nake baiwa ba Sadi ka shigo cikin magana ta" "aiko wallahi malam Habu dani kake" "to ka dauka dakai nake Tanko idan kaga baka kyauta ba ka taimaka ka gyara halayyar ka ka saki hannu a gidan ka" "bazan sake ba babu ruwan ka da gida na kaima kai ta kanka ba hannunka ne ya cud'i bayanka ba mutum na fama da talauci yana tsirkun wasu" "aikai da kake da arzikin shiyasa naga baka damu da kowa ba har anyi new ake ce maka duk garin baka damu da kowa ba amma kowa ya damu dakai musamman mai ba'kin ido da jan baki da gajere mai tumbi mai hana zaman lafiya..............

"MALAM HABU!!! Tanko ya kira sunan da 'karfi yan cewa "ya isa haka kazo inda kaina bazai dauki maganganun da kake fad'a ba yanzu kam ya isa" ta'be baki malam Habu yai yana kallon Tanko yace "kwantar da hankali d'an uwa nima nasan ya isa domin naga haka kuma bana so ai magana a kaina domin nasan tsiyar da nake shukawa shiyasa nai shiru jikina yai sanyi dan kada nai magana a dawo kaina a tona min asiri" malam Habu na rufe baki Mudi yace "dawa kake"? "Da wani nake" "waye wanin"? "Wani ne" "to ka fad'i waye mana"? Kallon Mudi malam Habu yai yana cewa "to meye naka a ciki me ka damu saika sani ko labari kwarton da yaje 'kauyen madigai kake so na baka labari"? Zaro ido Mudi yai bakinsa na rawa zaiyi magana ya kasa.

"Fad'i man me kake son cewa"? Malam Habu ya sake tambayar sa cikin gulma Tanko yace "wanne kwarto aka kama"? Mikewa malam Habu yai yana daukar goronsa yace "nima bansan waye ba amma aminin naka Mudi ya sani ka tambaye shi zai fad'a maka domin yana garin lokacin da ake ihun cewa azo an kama kwarto shine yazo ya fesa anan cewa kwarton ma tsoho ne yaje gurin yarinyar da bata fi jikarsa ba ashe ya yaudare ta a kasuwa duk sati yakan sayi lemo da ayaba ya bata ita kuma yarinyar tallar dankali take shiga kasuwar duk sati ya dad'e yana bata kayan kasuwa sai ranar yace mata yana son zasuyi magana tace masa to suka fita daga kasuwa sai yace suyi nesa da mutane yake ta janta har suka wani sabon gida da ake gininsa ba'a karasa ba suka shiga nan ya bata kud'i mai yawa yake ta janta da hira idan tace zata tafi saiya hanata har akai kiran sallar magriba karshe dayaga ta damu ta tafi gida saiya nuna mata abinda yake so nan fa yarinya tai tsalle ta dire tace batasan da wannan maganar ba da yaga tana shirin gudu ya kamata da komawa yarinya d'anya shakaf taga za'ai mata zarrar data zarce ma tunanin ta ta fara zunduma masa ihu tana kururuwa nan mutane suka taro aka tara masa gayya 'kiii aka fito dashi sai kare fuskarsa yake matasa suka d'ebo makamai suna cewa a barsu su kashe shi da'kyar aka tattare su aka hana su aka jashi gaban mai gari nan akaita shari'a akaci tararsa kud'i haka ya tafi garin su jikinsa a sali'be yana d'ari d'arin shiga cikin mutane amma da yake yafi kowa idon akuya ganin anyi burus dashi ba'a nuna masa ansan komai ba saiya ware yaci gaba da fella tsiyar sa kunga wannan shi za'a Kira da yayi new ba malam Habu ba" yana kaiwa nan yai gaba.

Da ido suka bishi cikin mamakin dawa malam Habu yake wannan maganar kafin Tanko yace "kai Mudi kasan da wa Malam Habu yake wannan maganar"? A fusace Mudi yace "ban sani ba meyasa baka tambaye shi ba ka bari ya tafi sannan zaka zo ka dame ni' yana kaiwa nan ya kad'e rigarsa fuuuu yabar gurin da harara Tanko ya bishi yana cewa "jimin tsinanne wato harda ni zakai fushi? Aiko saina nuna maka na fika hauka" kowa na jinsu yai shiru domin sun fi kusa haka Tanko yai ta balbalin bala'i har ya gaji ya 'kyale.

Dutse mopal Base
Satin su Binta biyu take shirin komawa domin ta huta har tayi 'kiba ta murje suna zaune da 'kaninta Bashir ranar da zasu koma gida take ce masa.

"Bashir dan Allah ina da bukata a gurin ka" kai Bashir ya d'aga yana cewa "meya faru fad'a min Allah yasa ina da damar dazan magance miki matsalarki".

Bayani Binta ta fara yi masa "dama matsalar akan malam ne Bashir dan Allah ka taimaka masa da jari wallahi malam yana cikin damuwa da fuskantar 'kalubale a kauyen nan bai isa nuna wani abu da sunan nasa ba komai ya ta'ba a narke ya rasa inda zaisa kansa hatta yarinyar nan Amatullahi tana cikin damuwar mahaifin ta kullum tana cikin kuka da fad'a min cewa taya zata taimaki babanta wannan dalilin yasa nazo dan Allah Bashir ka taimakawa malam".

"Shikenan aunty kada ki damu insha Allahu za'a bashi jari malam Habu mutum ne na 'kwarai lokacin da kukazo banji dad'in yadda na ganku a rame ba saidai wannan bayanin da kikai min na gamsu dashi zan baki dubu d'ari ki tafi masa dashi a cikin kudin da zanyi zakka ba fitar ki

Please Login or Register in order to submit comment