Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maka inace duka na kazo yi dan irin wannan 'kerere da kayi a kaina duka kawai nake jira".

'Kara hade rai yai jin abinda tace shifa uwarsa ce amma harga Allah ta fara isar sa lamarin ta ya gama cika masa ciki...............

"Dan ubanka me kake kallo tunanin wa kake amma dai ba wannan tsinanniyar 'kai'kasashshiyar matar taka ba?.

"Wai dan Allah baba me kike yi haka ne"? Ilyah yai maganar ransa a mugun 'bace cikin fad'a Ramatu tace "dambun ubanka nake yi haka, wato dama akan shegiya matarka bankad'add'iya zaka gaya min magana? A lallai Ilyasu wuyanka ya isa yanka".

Takaici ne ya cika Ilyah shi ya rasa gane kan Ramatu kodai ta fara samu zarewa ne bai sani ba dan yaga abun nata yana neman wuce gona da iri amma bari ya bita a sannu tsuntsu me wayo ta wuya ake kamashi zama yai yana cewa "kiyi hakuri nifa dama ba akan wani abu na tambaye kiba mubar maganar d'azu bayan na fita alhaji Munniru yai Kira na akan zai sayar da wata gonar sa kozan saya saidai kafin mu gama ciniki kawai shegen nan Habubakar yaxo ya sayeta da filin kusa da gidan Buba haka mafa kwanan baya gidan me doki wanda ya rasu 'ya'yansa da suka d'aga zasu sayar shine ya saye ga gonar wajen gabar inda yake noman shinkafa kiga girman ta duk shekara saiya d'inke kusan buhu d'ari a bai samu da yawa ba ya samu buhu saba'in ko tanin komai aka d'aga a garin nan za'a sayar shi zai saya na rasa a ina yake samun kud'in sai kace me kud'in ganye ko matsafi kuma fa akwai haihuwa a gabansa amma tsabar had'ama alhaji Munniru ya kara masa kud'i shima da yake mitsiyaci ne ya sayar masa".

Zaro ido Ramatu tai tana cewa "kace da haihuwa a gabansa waye me ciki Saude ko Binta"?.

"Eh Binta ce harya tsufa kuma kwanan nan zai sake auren A'in gidan su me guga har ankai ro'kon arziki".

Dafe 'kirji Ramatu tai "au kuma shine tsabar hassada Salamatu bata zo ta gayyace niba aiko wallahi zan rama har ayi bikinka da Maimuna bazasu sani ba mitsiyatan mutane kawai duk sun asirceka ka'ki abun arziki amma na samo hanyar tarwatsa su kada ka damu Ilyah Bara'atu tayi gida nice na saketa domin bata haihuwa gara ka kara aure".

Kai ya d'aga cikin so kwantar mata da hankali yace "shikenan zan kara amma dan Allah ki bari na dawo da ita nifa ina son mata ta".

Shiru Ramatu tai tana kallon sa kamar me tunani zuwa wani lokaci tace "to shikenan ka dawo da ita amma ba yauba ba gobeba ba jibi ba sai an gama komai na maganar aurenka da Maimuna an tsayar da rana tukuna idan ma zan yarda ka dawo da itan kenan".

"A'a zaki yarda man na fad'a miki nifa ina son mata ta" hararar sa tai "sannu d'an masoya na gama magana matukar kana son sake bud'e ido kaga barakatu ko Bara'atu sunan nata? Indai kana son sake ganin ta matsayin matarka tofa saika kara aure".

Mi'kewa yai yana cewa "to shikenan zan 'kara saida safe" Ramatu data bishi da kallo tace "kowa ya kwana lafiya shi yaso๐Ÿ˜" a'a kai jama'a wannan wacce irin uwace shidai tari da bai kama shiba bai sake yi ya shige d'aki.

Zunbur Ramatu ta mike tare da dauko maganin data kar'bo d'azu ta dauki bokiti da ruwa da sand'a tai waje tana yin hanyar daji ga ihun karnuka ya cika gari domin dare ya yi sosai yadda aka bata umarni haka ta aikata haka ta fara zuba magani cikin ruwan bokitin tayi wanka dashi kafin ta dauki gatarin da aka bata ta soma sara tana kiran Salamatu bayan ta tona tasa maganin ta rufe sannan ta dawo gida a bayan d'akinta nan ma tayi kamar yadda tai a dajin sai waige waige take kada Ilyah ya fito ta shiga uku tana gama tai wuf a guje ta fad'a d'aki tana gumi tare dayin dariya tace "haba malam sai yanzu naji daidai hankali na ya kwanta da wani ya kamani bansan me zai faru ba bari na kwanta mu jira wayewar gari muji me zai samu Salamatu"โ˜น๏ธ๐Ÿ˜ง ta karasa maganar tana kwanciya akan katifarta da Ilyah ya sayo mata.

MRS AL'AMEEN AHMAD CE ๐Ÿ˜˜

Maman little Zaran aunty sai Allah ya kaimu gobe da nisan kwana๐Ÿ˜ฃ da rahmarsa garemu ina yiwa kowa da kowa fatan alkairi.


Yau typing d'in ba yawa sai hakuri.

๐Ÿšจ GARGA'DI DA TUNATARWA๐Ÿšจ
Ban yarda a juyi ko kwafin wani bangare daga cikin wannan littafin nawa ba domin hakki na ne mallaka ta da gumi na basira ta na 'kir'kira na rubuta kada mutum ya min satar koda kalma daya ce idan kuma ba haka ba mutum zaiga sakamako kada ace na yanke hukunci ba sanarwa shiyasa na fad'a sai a kiyaye idan kunne ๐Ÿ‘‚๐Ÿ‘‚ yaji?.....................๐Ÿ˜ ๐Ÿ˜ก.


๐Ÿ™ˆ'YAR MUSA JIKAR ABUBAKAR MUHAMMAD TA KOWA CE๐Ÿ‘Œ.

Nayi kewar ku kwana biyu yan uwa fatan kuna lafiya ku fito mu warwasa zamu shiga duniyar nishad'i๐Ÿคฃ๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜….

Bani da haushin kowa nifa i haven't girman kai if you are fushi dani to wallahi you are just 'batawa kan k lokaci ๐Ÿ™ƒ๐Ÿค‘.

TYPING ๐Ÿ“ฒ {WEND 13/24 8:10AM}๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’

๐Ÿ’ŽMe kamar sarki ๐Ÿ’Ž

๐Ÿ’ซAnnuri writer's association ๐Ÿ’ซ home of hospitality and harmony gidan karba hannu biyu da zaman lafiya.

Yusrah Musa Abubakar maman little Zaran aunty mai tambarin YMA dutse Jigawa new world new life and new style ๐Ÿ‘Œ. sabuwar duniya kuzo ku kallo dad'i yana Jigawa ๐Ÿ˜œ ga garin ilmi garin addini zaman lafiya Jigawa.

29~AL-ADAL
The utterly just
30~AL-LATIF
The Gentle

15~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Mustagfirina.


๐Ÿฆ๐Ÿ•Š๏ธYUSRAHMS ABUBAKAR
๐Ÿฆ‹[email protected].

๐ŸŒ„ UNCARING ND TRAGEDY๐ŸŒ„
Episode 29_30
Juyi Salamatu tayi cikin barci taji murya ana kiranta a firgice ta bud'e idonta ganin wani 'katon ba'kin abu tai a samanta yana yawo gashi bata ga alamar d'akin da take ciki a kwance ba "innalillahi wa inna ilaihi raji'un" shine abinda take maimaitawa 'kara matsowa abun yake taga yayi wani juyi wurrr ya rufo kanta da sauri ta tashi a guje ya sauka akan gadon sai kuma ya 'bace jitai kanta yana juyawa lokaci guda taji hajijiya na dibanta ko ganin gabanta batai ta kama hanyar fita daga gidan babu ko d'an kwali akanta.

Daidai Rakiya matar Sabi'u ta fito da buta a hannunta ganin inuwar mutum yana tafiya yasa a tsorace taja da baya tana cewa "a'uzubillahi minal shaidanur rajim" jikinta na 'bari ta haska da fitila cikin salati ganin wacce take shirin fita yasa tace "Babah ina zakije a wannan tsohon dare kanki fa ko d'an kwali babu"?.

Ganin tayi banza da ita yasa da sauri ta koma d'aki tana taso Sabi'u a gigice ya fito bai tsaya sa takalmi ba aguje ya fita waje can ya hango tayi nisa sai tafiya take ga karnuka na mata haushi cikin azama yaje yasha gabanta yana haki yace "Babah ina zakije"? Bata bashi amsa ba kuma bata kalleshi ba ganin haka yasa ya sake cewa "meya sameki ne ko baki da lafiya"?.

Namma shiru tayi masa kanta kuma yana kallon 'kasa ta'ki d'agowa mamaki ne ya kama shi sosai har ya kasa ce mata wani abu sai hannunta daya ri'ke yana janta don ya mayarta gida amma sai yaji ta tirje kamar yaja irin kafaffiyar bishiyar nan juyowa yai yana kallon ta tare da zaro ido waje jin 'karfi a jikinta kamar doki zaiyi magana kawai yaji ta kwashe da wata iriyar dariya da sauri ya saketa yana ja da baya dariya take sosai kamar zararriya d'ifff kuma yaji tayi shiru tare da dafe kanta ta kurma ihu tana yanke jiki ta fad'i 'kasa, da gudu Sabi'u yazo yana durkusawa a gabanta girgiza ta ya soma yi amma shiru mi'kewa yai cikin jarumta ya d'agata yana sa'bata a kafad'a yai gida da ita saida ya kaita har daki ya kwantar kafin ya fito yana mamakin ina Rakiya tayi ne nasu d'akin ya shiga can ya hangota saman gado ta lullu'ba sai kakkarwa take karasawa yai yana janye bargon yace.

"Rakiya meya sameki, baki da lafiya ne"?.

Jin muryar sa yasa ta bud'e ido tana cewa "a'a ina lafiya ihu naji da dariya daidai nasa hijab na fita zanbi bayanka shine tsoro ya kama ni na dawo gida ina Baban take ka ganta"?.

"Eh tana d'aki jira nake gari ya waye muje asibiti ni abun ne da tsoro kamar ciwon hauka ne ya kamata saboda ganin abunda takeyi itace fa me wannan ihun da dariyar kamar zata fasa gari" zaro ido Rakiya tai "itace kuma innalillahi wayyo Allah na meya samu Babah ne ban ta'ba ganin irin haka ba".

Zama yai yana sauke ajiyar zuciya yace "ni kaina Rakiya ban ta'ba gani ba sai yau Allah yasa dai ba aljanu ta had'u dasu ba" Amin Rakiya tace tana tashi zaune daga tashi tai tana le'ko kofar d'akin da Salamatu take ciki tana cewa "nifa ina jin tsoron karta 'kara fitowa bamu sani ba tayi waje ka taso muje gurin ta gara mu tsaya zuwa wayewar gari a gurin ta" mi'kewa yai yana cewa "shikenan muje" fita sukai suna shiga d'akinta a 'kan'kame suka sameta ta 'ka'k'kafe idanuwanta sun juye babu ko d'igon ba'ki sai fari tana wata irin jijjiga abin tsoro.

Rakiya dake kan gaba da sauri ta koma baya tana salati jikinta na rawa ganin abinda yafi 'karfin ta kuka ta kama cikin tashin hankali tana cewa "ta ya zamu bari sai gobe baban hajiya gaskiya musan yadda zamuyi a daren nan kalli fa abinda takeyi sai nad'ewa guri d'aya take kamar taya dan Allah kayi wani abu".

"To mezanyi wanda ya wuce addu'a ina zamuje dare ya riga ya raba mu ba asibiti ne damu a gari ba saidai muyi hakuri mu jira wayewar gari".

Goge hawaye Rakiya tai tana cewa "shikenan Allah ya kaimu Allah ya bata lafiya" amin yace tare da fara karanta mata addu'a haka suka kwana cur basuyi barci ba saida akai sallar asuba sannan ya samu wani d'an ma'koftansu mai mashin ya nemi alfarmar yakai su asibiti amma dayaje gida ba damar da zata iya hawa mashin dan tana nan a san'kare guri d'aya hatta yatsarta baya tan'kwasuwa balle ga'bo'bin jikinta rasa mafita Sabi'u yai dole karshe sai mashin d'in ya kar'bi aro yana fita wajen garinsu ya samo motar haya da'kyar suka fito da ita kamar itace haka suka sata a mota suka nufi asibiti.

Habu bai sani ba sakamakon baya gari ya tafi cikin Kano sarin kaya sai bayan ya dawo yaji labari ko hutawa baiyi ba ya tafi asibitin a zaune ya samu Sabi'u da Rakiya sunyi shiru cikin damuwa yace.

"Yaya Sabi'u dama Babah bata da lafiya? Wallahi ban sani ba dawowa ta kenan yanzu Binta take fad'a min ya jikin nata fatan da sauki"?.

Numfashi Sabi'u ya sauke tare da girgiza kai yace "Habubakar ban sani ba abun da tsoro tun safe muka zo amma har yanzu babu likitan daya fito balle muji wani labari da zaisa muji d'an dama dama".

"To meya sameta ne"?.

"Humm habu Habubakar to me zance na kasa ganewa 'kwa'kwalwata bazata dauka ba irin abubuwan da take da dare ya bani tsoro baka gani ba yadda take sandarewa kamar busashshen ice harda ihu".


Zaro ido Habu yai "innalillahi meya faru haka ko aljanu ne"?.

"Ban sani ba Habubakar Allah yasa dai ba wani mummunan abu ne ya sameta ba" Amin Habu yace yana samun guri ya zauna suna jiran tsamani kafin likitan daya kar'bi Salamatun ya fito.

GIDAN BALARABE
Dalah na zaune a kofar d'aki tana tajewa Indo gashi taji an rafka sallama tana d'aga kai taga mace ta shigo mamaki ne ya kama ta ganin Asabe a ranta tace ita kuma wannan lafiya ba dangin iya ba na baba katse mata tunani tai da cewa.

"Ke haka ake kar'bar ba'kuwa kin barni a tsaye kamar bishiya"?.

Da sabon mamaki Dalah ta kuma kallonta tana cewa "sannu da zuwa 'karaso bismilllah ga kujera ki zauna".

Zama Asabe tai tana 'karewa gidan kallo kamar wacce tazo duban tsafta zuwa wani lokaci tace humm tare da ta'be baki tana yiwa Dalah kallon uku saura sisi takaici ne ya gama cika Dalah ganin mace tazo mata har gida zata raina mata wayo tace.

"Wai meya faru ne kinzo bakice komai ba lafiya"?.

Gyara daurin kwalin kanta Asabe tai tana soke shi a gaban goshi tareda dauko cingum daga cikin Jakarta tasa a baki tana taunawa sannan ta soma magana "humm Hajiya Dalansi dama nasan zaki mamakin zuwa na saidai da baki wahalar da kanki ba domin ba wani abu ya kawo niba kawai nazo ne mu gaisa naji ya d'iya ta take".

Baki bud'e Dalah take duban Asabe jin abinda take cewa tace "kinzo ne mu gaisa kiji yadda lafiyar d'iyarki take"?.

Gira Asabe ta d'age "eh haka nace ranar baki ga tazo miki da 'kosai ba? Ai nice na bata har nake cewa idan tazo tace ina gaida ke ko bata fad'a miki ba"?.


"Eh bata fad'a min ba mun gode".

Karya kai Asabe tai cikin yanga zatai magana taji gyaran muryar Balarabe alamar ya shigo gidan cikin tane taji yana hautsinawa na shakku da tsoro tuna abinda 'kawarta Meroh tace mata akan Balaraben mi'kewa tai tana susa kamar me ciwon 'kazuwa tana rarraba ido tare da satar kallon Balarabe da yake tsaye ganin ta a gidansa muryarta na d'an rawa tace.

"Barka da gida ina yini"?.

Wani kallo ya mata yana d'auke kai bai amsa ba sai tambaya daya jefo mata "meya kawo ki gidana me kikazo yi shin kinyi ajiya ne"?.

Kallonsa Asabe keyi ganin yadda yai mugun had'e rai yasa jiki a sanyaye tace "kayi hakuri dan Allah yanzu zan tafi dama nazo ne mu gaisa".

Da yake mutum ne mai fad'a a hasale yai kanta yana cewa "da uban wa zaku gaisa dama kina zuwa min gida ne? Karki sake na sake ganin ki a gidannan idan ba haka ba zaki bayani saikin yabawa aya za'kin ta fita min a gida nacee" ya karasa maganar cikin tsawa yana nuna mata hanyar 'kofar fita jiki na 'bari Asabe tai waje kamar zata kifa tsabar sauri tana haki.

Juyawa yai cikin fad'a yana kallon Dalah yace "kece kika bud'e mata kofa kika bata lasisin shigowa gidana ko kuwa duniyanci ne ya kawo ta fad'a min naji"? Cikin shakku Dalah tace "kayi hakuri wallahi bansan komai ba kawai ganinta nai ta shigo wai tazo mu gaisa taga d'iyarta".

"Taga d'iyarta? A gidan uwar wa Indo na ta zama d'iyar yar duniya irinta kuma bari kiji daga yau na kafa doka kada ki kuskura na sake ganin wannan matar a gidan nan kin jini"? Kai Dalah ta d'aga "eh insha Allahu zan kiyaye kayi hakuri" tsaki yai yana yin hanyar ficewa daga gidan sai balbali yake d'an d'aga murya Dalah tai tana cewa "ga abincin ka" a fad'ace yace "bazan ci ba bana so" rike baki Dalah tai "oh ni Aminatu yau naga ta kaina Allah ka tsare ni da sharrin matar nan kada tai silar mutuwar aure na" ta karasa maganar tana kallon Indo tace "dauko min hijabi na a d'aki muje na kara ki gidan kitson nan Allah yasa Suwaiban bata aiki yanzun nan tayo miki na dawo gida na d'ora abinci kar dare yayi maza tashi ki dauko min" mi'kewa Indo tai tana daukowa rufe d'akunan Dalah tai tana sa hijab din suka fita.

Asabe na fita daga gidan Balarabe tayi anguwar babbar 'kawarta Markah hankalin ta a tashe tana zuwa ta yada gyale da jaka ta soma zaga tsakar gida tana jan tsaki da maganganu ita kad'ai Markah na gefe tana yanka loma ganin yadda Asaben ke zarya tace "a'a 'kawar arziki na ta'ba ki da alkairi wannan abinda kike nasan bakya cikin nutsuwar ki akwai wani wanda ya 'bata miki rai wa kike zagi"?.

Zama Asabe tai tana sake jan dogon tsaki cikin takaici kamar zata fashe da kukan ba'kin ciki idonta fal da ruwa tace "wannan mara mutuncin ne ya tozarta ni dan kawai naje gidansa harda cewa uban me ya kawo ni".

Cikin alamar tambaya tace "wa kenan akan me kike magana ne"?.

Cizon yatsa Asabe tai tana zama tace "waye kuwa Markah bayan masifaffan nan Balarabe kalar jaraba wai kawai dan naje gidan sa bakiji wulakanci ba kamar wacce naje maula".

Dariya Markah tai tana cewa "kema dai Asabe kina da shishshigi kinsan waye Balarabe meyasa zakije masa gida"? "Humm Markah kenan sonshi fa nake da gaske so nake na aureshi banajin dad'i idan ban ganshi ba" baki Markah ta ta'be "tab aiko kin hada kanki da wahala Asabe maganar gaskiya Balarabe bazai ta'ba sonki ba balle ya aureki gara ki ha'kura" zaro ido Asabe tai "kinsan me kike cewa kuwa na ha'kura fa kikace Markah"? Kai Markah ta d'aga "eh shine mafita kema kya hutar da zuciyarki daga 'kuncin da kika jefata" mi'kewa Asabe tai tana daukar gyale tace "inaa bazai yuwu ba Markah ya yau d'in nan zanje gurin boka na" zaro ido Markah tai "haba Asabe a yau kuma"? Kaita d'aga "eh yanzu ma kuwa kinga tashi ki raka ni" kallonta Markah tai kafin ta she'ke da dariya harda tafa hannu da sakin gud'a cikin zolaya da sha'kiyanci tace "sai kinyi hajiya Asabansi amarya a gidan malam Balarabensi mai kayan gwanjo in Allah ya yarda" hade rai Asabe tai tana cewa "kinga idan zaki rakani kawai ki taso muje wallahi indai kika taimake ni na cika burina zan baki kud'i naira dubu hamsin kyauta kiyi jari ki bud'e kasuwanci a gidanki" dafa 'kirji Markah tai "da gaske kike 'kawar arziki? Aiko yanzun nan makuwa zamuje tab irin wannan samun gara'basa da ganima haka ahh muje akwai gurin wani ri'kekken boka a cikin wani ba'kin daji sunansa 'kadaga aikinsa me kyau ne yanka daya ne saidai akwai kashe kud'i da tsada" jin haka yasa cikin azama Asabe tace "indai aikina akan Balarabe zaici ko maye zan bayar ko meye zan 'batar dashi naga na samu kansa ya soni ya aureni" "shikenan 'kawar muje" Markah ta fad'a tana dauko gyale suka fita tana sake fad'awa Asabe shaharar bokan da irin aikin da yake farin ciki kuwa tuni ya cika Asabe hango Balarabe kawai take a tafin hannunta tana jujjuya shi kamar yadda ranta yake so.


๐Ÿค—AYI HAKURI YAU TYPING ๐Ÿ“ฒ DIN BABU YAWA KUMA BANI DA CHAJI๐Ÿ“ฑ GASHI SABODA INA MATUKAR 'KAUNARKU A GIDAN BIKI NAYI MUKU TYPING๐Ÿ‡๐Ÿ˜˜๐Ÿคฃ.


MRS AL'AMEEN AHMAD CE ๐Ÿ˜˜
Yusrah Musa Abubakar maman little Zaran aunty ๐Ÿ˜‚๐Ÿคฃ๐Ÿค—๐ŸŒนโœŒ๏ธ.


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒDuniyar da za'a barta
Me ya kawo had'ama?๐Ÿคจ
๐Ÿ™๏ธRayuwar da zata 'kare
Ina wani farin ciki?๐Ÿ˜ง
Ana sauraron mutuwa๐Ÿ˜ข
Ina wata walwala?
Jikin da zai zama gawa ๐Ÿ˜”
Me zaisa alfahari?
'Karshen da makomar sa kabari ๐Ÿ˜ญ
Me zai jawo girman kai?
Duk wanda ya manta da wannan ๐Ÿ˜Ÿ
To ina yabar hankalin sa?๐Ÿค”.


๐ŸŒน๐Ÿ’žMU'KAMIN KA DA GIRMA YAKE ME KA'ABU DA ZAHIDU KA TAKA DAI DAI UBAN GIDANA YA RASULULLAH๐Ÿ’–๐Ÿ’.
A baitin farko sunanka ne ya Al Aliyu ina tawassuli ga annabin nan almakiyu sirrin wadatuwa wanda ya zamma madaniyu albarkacinsa nazo kai mini ya 'kawiyyu ka 'kara bani dama in wa'ke nuru zatullah.๐Ÿ’ž๐Ÿ’˜
Summas salatullahi alam daharujjanani mai kausara da zam zam ya sahibul bayani mai kyau da kyan gani ya sirrin samun sukuni wadatuwar wadata kaine ayyunul ya'kini lale wa marhaba bika ya kairu kal'ki indallah.โค๏ธ๐Ÿ’
Ranar kowa yana kasa kai kuwa kana buraka mala'ku rundunar Allah na bayanka suna ta gaisuwa da sallamar su a gareka ranar dukkan annabawa ne fadawan ka ashe kwa zamu sha kallo matsayin rasulullah,๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿฅ€
Niko nace ka taka daidai abban kasim ina isar waninka a yau ya jikan hahim aljannah taka ce makiya ba uhm ba um um ashe kwa zasu sha narko tunda sun 'ki sallallah๐Ÿ’•๐Ÿ’š.

TYPING ๐Ÿ“ฒ {Sat 20Apr 24 02:18PM}%๐ŸŒน๐Ÿ‘‰ YUSRAH MUSA ABUBAKAR.


๐Ÿ‘‘ME KAMAR SARKI ๐Ÿ‘‘

WHATSAPP NO:234 905 527 3614.

Story and written
โœ๏ธMrs Al'ameen Ahmad ce maman little Zaran aunty ๐Ÿ’….

Wannan page din naka ne d'an uwa rabin jiki ha'ki'ka kai jarumi ne a cikin jarumai jarumtacce a cikin jarumtattu u're the champion ๐Ÿ‹๏ธ๐Ÿ’ช best hero in the world ๐ŸŒน d'an uwa na Allah ya tsare mana kai ya tsare ka daga sharrin miyagun makiya annabi na wannan daji Sambisa๐Ÿ˜ฃ๐Ÿ˜ฅ Allah ya dawo mana dakai gida lafiya cikin aminci alfarmar Manzon Allah saw Amin ๐Ÿคฒ๐Ÿ‘.
CPT. SALISU ABDULLAHI (*()*) KOLI๐ŸŸ ME TAMBARIN NO GOING BACK๐Ÿ‘ฎ๐Ÿ’ช๐Ÿ”ซ๐Ÿ”ซ๐Ÿค›๐Ÿ‘Š๐Ÿ’ฃ.


YUSRAH MUSA ABUBAKAR MRS AL'AMEEN AHMAD CE MAMAN LITTLE ZARAN AUNTY ๐Ÿ’ƒ.

[email protected] INA MASOYA 'YAN UWANA MA MAKARANTA (READER'S)๐Ÿ“š INA MATUKAR FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA GA WATA BABBAR DAMA TA SAMU YAR UWA KO DAN UWA MAKARANCI KANA NEMAN LITTAFI SABABBI KO TSOFAFFI NA TARIHI KO NA YA'KE YA'KE WANNE A CIKI KAKE DA BUKATA? HUMM MAZA KA MATSO KUSA GA BABBAR DAMA TA SAMU TASKAR HAUSA EBOOKS TA SAMAR MUKU SABUWAR DUNIYA WATO SHAFIN SU NA MR HAUSA EBOOKS KUMA KODA LITTAFI KA RUBUTA KANA SON YA'DAWA ZASU DORA MAKA SHI SHAFIN SU NA GOOGLE TWITTER FACEBOOK DA TELEGRAM KAI HARDA INSTAGRAM KAWAI YAN UWA KU DANNA WANNAN LINK 'DIN.
Taskar Mr Hausa Ebooks
http://tnovels.com.ng/novels/ sai kuyi serch kuna kasa sunan littafin da kake so kai tsaye zaka shiga shafin sai kayi downloading duk littafin da kake so๐Ÿค—.


#VOTE
#SHARE
#COMMENTS
#FALLOW

31~AL-KHABIR
The all Aware
33~AL-HALIM
The Forbearing.

16~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Nadiminah.

Bintu Musa jikar Abubakar Muhammad.

๐ŸŒ„ INFANT ND PRETENDING ๐ŸŒ„
Episode 31&32
Har dare ya fara nisa wajen karfe sha daya babu likitan daya fito balle su samu wani d'an labari dazai sanyaya musu rai a gajiye Sabi'u ya kalli Habu dayai tagumi yana cewa "Habubakar ya Kamata kaje gida dare kada yai nisa ga Rakiya ku tafi tare" kallonsa Habu yai tare da girgiza kai yace "yaya Sabi'u bazan iya tafiya na barka ba cikin kad'aitaka ga damuwa bayan babu likitan daya fito balle muji abinda ya sameta bazan iya zuwa ko'ina ba anan zan kwana" dafa shi Sabi'u yai yana cewa "a'a Habubakar na sani kayi matukar damuwa da hakan amma zan baka hakurin dan Allah ka tafi gida ka dawo da safe kaji"? Shiru Habu yai tare da sunkuyar da kansa kamar me tunani zuwa wani ya d'ago zaiyi magana Sabi'u ya dakatar dashi "a'a dan Allah kar kace komai ka tashi ku tafi" mikewa habu yai batare daya sake cewa 'kala daidai Rakiya ma ta tashi tana d'iban kwanuka Sabi'u ya d'ora da cewa "yauwa habu gobe da safe kaje gidan malam Zayyanu kace wannan kud'in dana bashi ya baka na fasa sayan gonar baba ce bata da lafiya zan biya kud'ad'en asibiti" kai Habu ya d'aga "to zan fad'a masa saida safe" Allah ya tashe mu lafiya" har wajen asibitin ya rakosu yana sake jaddadawa Rakiya tazo da wuri.

Ramatu na zaune da safe a kofar d'aki Ilyah ya shigo da sauri sai ganinsa tai a kanta kamar an jefoshi har haki yake binsa tai da kallon mamaki tana cewa "kai makau lafiya meye hakan zaka shigo min a wani hargitse kamar sabon kamu meya faru"? Kasa zama Ilyah yai sai kaiwa da komowa yake harda gumi yace "yanzu naji labari wai babah Salamatu bata da lafiya an kai ta asibiti" tsaki Ramatu tai tana zafga masa harara tace "au Salamatu bata da lafiya shine na wannan shigowar a gigice kana dawurwuri kamar me neman wani abu saime dan tana jinya asirin tane ya fara tonuwa irin 'kulle 'kulle da makirce makircen da take ne ya fara dawowa kanta kaga yanzu kowa zaisan ita ba mutuniyar arziki bace sungungumar asarace" "kai dan Allah wai me kikeyi haka"? Gyara zama Ramatu tai "ubanka nakeyi haka asararran banza asararran wofi wanda ya rako maza meye hadinka da Salamatu ne dan malafar ubanka fad'a min naji idan ta fini martaba sai nasan matsayin daka ajiye ni tunda dama ka fara nuna matarka ta fini mu'kami inaga nan gaba zakace banice na haifeka ba" jin abinda Ramatu tace Ilyah yasan fitina kawai take nema saboda kwana biyu babu Bara'atu da take saukewa damin bala'i shiyasa zata koma kansa amma bari ya bita a sannu zama yai kusa da ita yana cewa "kiyi hakuri nifa ba haka nake nufi ba gani nai ya cancanta a dubata tund.. .......,........

Katse shi Ramatu tai da cewa "a gurin kaba sakarai ni a gurina bai cancanta ba bani da had'i da ita" mikewa Ilyah yai takaici ya gama cika shi domin ta gama 'kureshi amma bai nuna mata ba yace "Ki tashi muje dan Allah ki dubota" wani kallo Ramatu tayi masa tana cewa "uban waye zaije dubo Salamatun amma dai bani Ramatun ba wai Ilyah meke damunka ne ka fara haukacewa kome ka

Please Login or Register in order to submit comment