Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

banza shashashan wofi da nace ka tsaya a kofar da baka bar gurin ba taya commissioner zai shigo ya kama ni da wannan yarinyar saboda cin mutumci maimakon ya rufa min asiri mu rufe maganar a office d'ina amma dan ya muzanta ni ya nuna ni 'kwarto ne a gaban yarana ya tozartani ya nuna ni ba mutumin arziki bane eh me zakace akan haka"?.

Shi dai Safyan shiru yai yana sauraron sa dama yasan irin wannan ranar zata zo kullum mutum ka girma amma kana da budurwar zuciya da son lalata yaran mutane kawai ka basu kud'i da motoci dan jin dad'i kamar kai baka haifa ba.

"Safyan tunanin uban me kake ne? Wato ina magana ka mayar dani majnun ko? Yanzun ina commissionern yake"?.

"Ai yalla'bai ba shine yazo ba wani drivern sa ya baiwa shine kawo kuma bai zauna ba tafiya yai".

Komawa yai da baya takwash ya zauna akan kujerar yana sake kallon takardar dasa hannun Governor shikenan ya shiga uku ya fito rana gashi wasu ma'kudan miliyoyin kud'ad'e da yake jiran shigowar su 'karshen wannan watan ne ga bala'in daya same shi tonan asiri biyu babu wanda yasan yayi danniyar kud'in na al-umma ne da gwamna ya bayar ayi musu aiki ya 'boye amma yasan dole yanzu kowa ya sani har gidajen TV za'a yad'ashi dafe kai yayi ransa na 'kuna kansa ya d'au zafi yace.

"Zaka iya tafiya".

"To yalla'bai a huta lafiya" Safyan ya fad'a yana fita "uban na huta ina cikin masifar taya zan samu lokacin hutu" ya karasa maganar yana huci shiru yai yana tunani zuwa wani lokaci ya rasa abinda yake masa dad'i jin ana kiransa a waya yasa ya d'auka jikinsa har rawa yake ya d'aga yana cewa.

"Hello haba commissioner ya zakai min haka wannan wanne irin cin mutumci ne da cin fuska ka nuna min"?.

Daga can 'bangaren commissioner yace "Prof ya kake"? Haushi maganar ta bashi kamar zaice ban sani ba sai kuma yace "ina lafiya amma yanzu abinda kai min ka kyauta kenan commissioner"? Cikin basarwa commissioner yace "oh sa'kon ya iso gareka kenan? Jin yai shiru yaci gaba "idan ka duba zakaga from Governor ne bani ba nima dan aike ne kawai aka bani kuma na isar dan haka yace a fad'a maka babu kai babu 'kara yin aikin gomnati har abada bayan haka yace sisi bazaka samu ba sannan wannan miliyoyin kud'ad'e da kace sunyi 'batan dabo watan daya wuce yanzu yace a fad'a maka ya samesu ta asusun jarinka da yake Australia na kamfanin ka ta hannun Mr wiliyam Emmanuel ka gane gobe zai aika ayi masa 'kwakkwaran bincike acan da abubuwanka saiya tabbatar wannan kamfanin iya kud'in kane Babu na gwamnati a ciki".


Innalillahi wa inna ilaihi raji'un shine abinda Prof Jibril yake maimaitawa bayan jin jawabin commissioner muryarsa na rawa yace "commissioner ka taimaka min dan Allah ka roki Governor ya rufa min asiri karya sanar da mutane komai karyaje Australia bincike wallahi zan kar'bo kud'ad'en da kaina zan na dawo dashi amma dan Allah karya fitar da wannan maganar tunda babu wanda ya sani" kai commissioner ya girgiza "a'a prof aikin gama ya gama bazan iya taimakon kaba maganar gaskiya laifin ka babbane ba kowa zai iya gyara maka ba saidai kayi hakuri ka d'auka cewa kamar da bakai aikin gwamnati ba kuma bawai dan mun kama ka da wannan yarinyar bane ko d'aya kar kayi tunanin haka dama gwamna ya gano cewa wadannan kud'ad'en ba 'bata sukai ba kaine ka dannesu ka gane"? Tsaki Prof yaja mai karfi wanda yasa commissioner cewa "oh tsaki ma kake min? To ai shikenan bari na barka da gwamnan sai naga yadda zaka 'kwaci kanka tunda kaiba mutumin arziki bane" jin abinda commissioner ke cewa yasa Prof yace "a'a dan Allah commissioner kayi hakuri kar muyi haka dai kai kasan duk lokacin da akace rai ya 'baci hankali ya 'bata to hankali ne ke nemoshi kaine ka fusata ni shiyasa kaja nai maka tsaki" kai commissioner ya jinjina yana cewa "hakan yayi kyau ai gara dana fusata ka tunda har ka gane idan hankali ya bata hankali ne ke nemoshi kaga da kanka kace hankalin ka ya 'bata kana lalata yaran mutane kamar ka manta kai baka haifa ba amma idan akaiwa naka baza kaji haushi ba haka ne"? Muryar Prof da tsawa yace "enough is enough malam commissioner karka nemi fad'a min magana dan kaga ina kas da kai ina neman taimako a gurinka baka isa ka wulakanta niba" shiru commissioner yai cikin mamaki jin Prof yace "hello kana jina"? Yasa yace "bana jinka amma tunda kai kana jina ka huta gajiya sai anjima" a gigice prof ke cewa "hello hello commissioner please karka kashe min waya ka tsaya ka saurare ni" jin d'if yasa ya kalli secreen din wayar wato ya katse wani wawan tsaki yaja yana buga wayar a jikin bango a fusace ya fice daga office d'in yai hanyar gurin parking din motoci a miliyon ya d'ebi motar da gudu sosai ko lura da yanayin hanya bayai haka ya isa office d'in commissioner ido rufe ba neman izini yaje fakam fakam zai shiga securities suka tare shi kokarin 'kwacewa yake wani gurmujejen 'kato ya kinkime shi yana fita dashi daga gurin saida ya kaishi har waje zai ja kofa ya rufe sannan ya kalleshi yana cewa "commissioner ne ya bada umarni duk wanda yazo karmu barshi ya shiga domin yana aiki ne" yana fadin haka yaja kofar ya rufe.

Kallon kofar ya tsaya yi kamar zai fasa ihu dan ba'kin ciki kafin a fusace ya shiga mota hankali tashe ya nufi gida horn d'in daya sakarwa mai gadi har Saida ya tsoratashi aguje ya tashi yana bud'ewa ko a tsiyace ya danno kan motar wanda a d'ari mai gadin yai gefe cike da mamakin meya samu mai gidan nasa yau ko parking bai gama daidaitawa ba ya bud'e murfin motar cikin azama ya fito yana yin hanyar shiga ciki dan sauri har takalmansa ya zubar da hular kansa duk ya had'a gumi yana karasawa cikin falon ya soma zunduma kira.

"HALIMA KE HALIMA KINA INA FITO YAU MASIFA TA SAMENI😣" da gudu ta fito ta ganshi sai kaiwa da komowa yake ya cire babbar rigarsa yayi jifa da ita gefe cike da mamaki tace "alhaji lafiya na ganka a haka"?.

"Hummm Halima ina fa lafiya yau na shiga uku na fito rana dama na mutu kafin naga irin wannan 'bacin ran daya sameni yau".

"Tofa subahanallahi alhaji wani abu ne ya faru"?.

"Meye ma bai faru ba nida wannan tsinannan commissionern ne yasa gwamna ya dakatar dani aiki har abada indai na gwamnati ne ya 'bata takarduna".

Zaro ido tai "to duk meya kawo haka kaidin meya had'aku dashi har abin yai zafi haka"?.

Shiru yai ya kasa bata amsa domin bazai iya ce mata kamashi commissioner yai tare da yarinya ba duk da dama tasan neman mata halinsa ne amma yana jin kunyar ce mata ga abinda ya faru................,...

"Alhaji magana nake menene ya had'a ku"?.

Zama yai cikin takaici yana kallon ta yace "akan baby ne".

Da mamaki Halima tace "baby kuma🙄😏😲? Humm tabdijam yau ake yinta wai tsakani da Allah dama alhaji baka daina mu'amala da yarinyar nan ba inace kayi alkawari ashe tuban ba'kin muzuru kai gaskiya ba ka kyautawa kaima ka haifa fa ya kamata ka daina abinda kakeyi ka roki ubangiji yafiya..........................

'Daga mata hannu yai "ya isa haka Halima ba wa'azi nace kimin ba I know abubuwan da nake aikatawa was improper saidai a halin yanzu ba wannan ne damuwata ba, ba wannan maganar nake bukatar jiba ki rufe min baki".

Dama tasan haka zai faru duk lokacin datai masa magana akan haka balbaleta yake da fad'an cewa babu ruwanta idone nata in duniya ce da more shagalin rayuwa yanzu ya fara".

Sauke ajiyar zuciya tai tana cewa "Allah ya baka hakuri" d'an tsaki yaja yana mi'kewa yace "yau zan tafi Australia zanje shima Mr Wiliyam d'in naci uban daya haifi ubansa mitsiyaci maci amana duk bashi kuka d'auka wallahil azim commissioner sai kunyi nadamar abinda kukai min bazan 'kyale kuba zaku sani".

Jin furucin da yake yasa Halima tace "a'a alhaji karkaje kayi abinda daga baya za'a zo ayi dana sani ka tsaya kayi nazari maybe kaine da laifi" tana rufe baki ya daka mata tsawa "Halima ya ishe ki kema tunda baki damu da damuwata ba kin goya musu baya to ki kyale ni nadau fansata" fuuuu ya wuce ta bishi da kallo tare da girgiza kai tace "tabdijan dama nasan koba dad'e koba jima sai wannan ranar tazo asirin ka zai tonu kullum ina tunatar maka amma ga irinta nan yanzu wa gari ya wayewa? Fatana Allah ya kyauta karka jawowa kanka wata masifar dan ko biyu bana rabawa idan kace zaka nunawa Wiliyam wani abu tofa za'ai babu kai mutumin da yake tsaface tsaface har kace zakaja dashi" mi'kewa tai tana bin bayansa da niyyar ta sake tausarsa ta hana shi zuwa Australia taga ko zata iya Allah yasa yaji maganar ta ya ha'kura.

Kusan karo sukai da shi zai fito da jaka a hannunsa tareshi tai da sauri tana ri'ke jakar tace "alhaji ina had'aka da girman Allah kar kaje ko'ina kana cikin fushi abin bazai maka dad'i ba" a fusace yace "sake min na tafi babu ruwanki" 'kara rikewa tai tana kallon yadda idonsa yai jajur tace "alhaji kayi hakuri amma kome zakai bazan sake maka jakar ba" 'karfin sa yasa ya fisge jakar zai wuce aguje ta sake shan gabansa tana cewa "please dan Allah kar kaje ka saurareni".

"Na saurare ki kike cewa bayan kinsan irin tashin hankalin dana shiga ko kin manta abinda ya sameni ne?.

Kai ta girgiza "a'a ban manta ba amma komai yana bukatar nutsuwa" wani kallo ya mata "nutsuwa? Nutsuwa kika ce? Nutsuwa fa? Wai da gaske kike? amma Halima baki da hankali" saroro tai tana kallon sa ganin yadda tayi yace "ke dalla matsa min gefe na wuce........,.............,...

Shiru yai jin ana ambatar sunan sa a TV yasa yaji jikinsa ya d'au rawa yawun bakin sa ya 'kafe idanuwansa kamar zasu fito waje ya zubawa gwamna dake jawabi ido ga Wiliyam zaune kusa dashi da d'ima d'imam jakakkuna sha'ke da kud'i dafe kai Prof yai yana jin wani ba'kin 'bacin rai da tu'ku'ki yana taso masa kansa na juyawa hajijiya na d'ibansa duhu ya fara gani yuuuuuu yai baya zai fad'i ta tareshi tana salati ri'ke 'kirjinshi yana sake kallon gwamna dajin abinda yake cewa runtse ido yai yana 'kakkamewa numfashinsa na fita da'kyar so yake yai magana ya kasa kai Halima ta girgiza.

"a'a alhaji kayi shiru numfashinka ya daidaita basai kace komai ba na fahimta......... shiru tai bata karasa ba tare da kallonsa ganin idonsa ya juye jikinsa na saki yasa ta fasa kara tana kiransa "Alhaji Alhaji!! Please ka bud'e idonka innalillahi wa inna ilaihi raji'un" da gudu ta bud'e fridge ta dauko ruwa tana shafa masa da'kyar taga numfashinsa yana d'an sauka kad'an kad'an kamar an taikare shi zunbur ya tashi zaune a gigice ya farfad'o kamar mahauci haka ya mi'ke yana cewa.

"Saina kashe shi Halima wallahi saina rama wulakancin da sukai min bazan 'kyale suba bazan 'kyale suba"...........................................

'Kwankwasa kofar parlon da akai ne yasa yai shiru yana kallon kofar cikin muzurai yace "uban waye anan"? Daga waje yaji ana cewe "kine Rabe wasu mutane ne sukace ayo musu sallama dakai suna wajen gate amma naga kamar harda motar yan sanda😲🚔" zaro ido Prof yai a rud'e yace " 'yan sanda kuma? Halima ya kalla yana cewa "To su waye ya turo su uban me zanyi musu"? Rabe dake tsaye bakin kofa yace "wallahi ban sani ba yalla'bai" a masife Prof yace "kuma dama dakai nake d'an munafika kada Allah yasa ka sani 'bace min da gani shashashan banza shashashan wofi ka wani zuro min ido ya na mufikin 'kwarto🙉😂 wallahi bazan je ofishin su ba babu inda zanje matsiyata kawai....................,........................


Shiru yai yana rarraba ido kamar wanda yaiwa sarki 'karya ganin 'yan sandan sun danno masa kai har cikin gidansa a fusace yace "malamai wannan wanne irin wulakanci ne zaku shigo min gida kai tsaye na baku izini ne"? Kallonsa officer yai yana kad'a ankwa da murmushi a fuskarsa ya d'aga masa ita yadda zai gani sosai yana cewa "professor Sir Alhaji Jibril your under arrest🤞" dafe 'kirji Prof idonsa kamar zai fito waje yace "ni kuma laifin me nayi waye ya turo ku kama ni"? Kafad'a officer ya d'aga yana kallon Prof dake faman rawar jiki yace "wannan kuma ba abinda ya shafe kaba ne idan munje zaka gani" jada baya Prof yai yana cewa "wallahi bazan jeba babu tsinannan da naiwa laifi dan haka bazanje nayi kwanan bayan kanta ba" kai officer ya jinjina "oh da gaske baza kaje ba? Amma kayi kokari Prof ya kamata a sara maka saidai inaso ka sani yau yanzu anan babu abinda zai hana mu tafi dakai sai mutuwa🤷" yana fad'in haka ya juya ya fice daga palon huci sosai Prof keyi ba'kin ciki ya gama cika shi ganin tozarci iri iri da gwamna ke masa yana tsaye yaga polisawa sun kuma danno kai sun shigo babu zato yaji sun cicci'beshi sunyi sama dashi suna fita Halima dake tsaye can gefe jin juwa na d'iban ta duhu ya baibayeta ganinta tana neman fad'uwa da sauri ta nemi kujera ta zauna tare da kife kanta tana sauraron yadda take wani yuyuyuyu kamar ana juyata hawayen takaici kuwa ya'ki tsayawa a fuskarta ta gaji da halin Prof ta kai bango tayi fad'an tayi nasihar amma ina yayi nisa bejin kira saidai bazata 'kosa ba kullum tana d'aga hannu tanai masa addu'a da neman shiriya da tuba kafin mutuwar sa ya gane gaskiya ya dawo kan hanya.


🤷AFTER TWENTY MOON'S🌚🤷
Komai ya lafa anyi masa hukunci yasha d'auri yayi zaman gidan yari daidai da laifinsa sannan dukkan kud'in daya zuba a ma'aikatar Australia Gwamna yasa anje an d'aga companyn an sayar anyiwa mutane tallafi da aiki da kud'in domin da aka tsananta bincike ko miliyon hamsim nasa na 'kashin kansa babu a ciki dukkan kud'ad'en bayin Allah talakawa ne da ake bashi yake dannewa ya fuskanci zunzurutun hukunci bayan gano gaskiya wanda hakan ya ba'kanta masa ya sake kaurara gabarsa da Gwamna ya shiga wani irin tafashasshan fushi da muradin ramuwar d'aukar fansa😠.

Zaune Prof yake yayi tagumi ya rasa abinda yake masa dad'i a duniya bayan tonan asiri da tozarci da gwamna yai masa ya tsiyata shi a TV da zahiri har baisan hawaye yana fita a idanunsa ba saida yaji salatin Halima tana cewa "na shiga uku Alhaji da girmanka kamar wani 'karamin yaro kukan me kake"? 'Dagowa yai a fusace yana kallon ta kamar ya tashi ya rufeta da duka haka yake ji jin tambayar datai masa yasa ya zafga mata wani irin kallo yana jan dogon tsaki jin zuciyarsa na turiri yasa ya mi'ke fuuuuuuu batare daya kulata ba yayi waje kaita girgiza tana maye inda ya tashi ta zauna tare da d'aukar remote tana canza tashar hijra tv.

Prof na fita ya d'au mota bai zame ko'ina ba sai gidan gonarsa inda yake shakatawa da 'yan mata masu 'kananan shekaru bai shiga cikin gidan ba direct bayan yayi parking ya fito garden ya wuce yana zama a karkashin bishiyar zaitun yana zama kamar daga sama yaga wani murd'ed'an ba'kin maciji ya taho da gudu wajensa gashi ya fasa kai🐍🐍🐍 tab a d'ari Prof ya mi'ke zai rufa a guje yaji wata murya tace "saurara ina zakaje"? Jikinsa na tsananin rawa ya had'a gumi shir'bim ya juyo yana kallon macijin da shine yai maganar kuma iya fuskarsa ta zama ta mutum mace saidai bata da kyan gani murmushi tai masa tana karasowa inda yake ya kasa gudu ta 'kafar dashi guri d'aya tana zuwa inda yake tai girgiza da wata haniniya sai gata ta zama mutum da kayan tsafi sanye a jikinta tsoro ne ya kama Prof dan duk zaton sa aljana ce ji yai muryarta na cewa.

"Professor Jibril kai tantiri ne irin yadda nake so an hukuntaka abisa shed'ancinka kasan kaine baka kyauta ba amma zuciyarka a cike take da fusataccen fushi da ba'kin muradin d'aukar fansa baka gane bane professor amma ka bini kabi umarni na kayi duk abinda nasaka zan ganar dakai ni nayi maka alkawarin taya ka rama wulakancin da sukai maka zasu sha'ki azabata zanyi musu u'kuba wanda sai sun 'kaunaci dama sun mutu kafin suzo wannan lokacin ka aminceeee dani na tafi dakai"?.

Kai Prof ya d'aga ransa na 'kuna yace "na yarda na amince zan biki zanyi duk abinda kika sani ko mayeshi idan har burina akan Gwamna da Commissioner zai cika wulakancin da sukai min na rama naga bayansu na zama abin tsoro mai bada tsoro wanda babu kamana sannan na zama sananne idan har zan samu wannan tofa babu abinda zakice na miki banyi shiba kome" ya karasa maganar da alamar tsantsan fushin dake cin zuciyarsa da bacin rai ga rashin tausayi.

Hhhhhhhhhhhhhh ta ri'ka mummunaar dariya har taso firgita Prof tsoro ya baibayeshi dakatawa tai tana kallon sa tace "ka samu kawai ka biyoni mujeeeeee zakai kallo zakaga muhallinmu inda zaka koma da rayuwar ka a sirrince" tana rufe baki Prof ya gansu a wannan 'bakin kumburarran mummunan hatsabibin dajin mai cike da kayan tsoro ga d'ima d'iman aljanu guda shida wanda suke rufawa bokanyar baya daga ita sai su a matsayi ji yayi tsoro ya sake rufeshi jikinsa na rawa kamar mai jin sanyi wani abun tsafi wanda zai 'batar da tunaninsa na d'an wani lokaci ta mi'ko masa yasha yana sha yaji jikinsa na canzawa kamar ana kara masa karfi yaji duk wani d'igon tausayi da imani ya fita a ransa babu shi a zuciyarsa a halin yanzu ko mutum d'anye tace ya cinye da rai tofa zai cinye😲😲 yana zaune akan dutsen tsafin tace.

"Daga yau ka shigo cikin mu kaine mutum na farko daya kar'bi tayi mu dan haka zamu baka 'karfi da matakan tsaro masu had'ari babu wani mutum daya isa ya gagareka amma kafin haka zaka bamu kyautar mutane biyu wanda kake matukar jin haushinsu😂😂😂.

TOFA DA SAU'KI TUNDA BA WANDA KAKE TSANANIN SO BANE🙉🙈🙉🙄🤩😘.

Tana rufe baki Prof yace "Commissioner da Gwamna" hhhhhh "sune ka bamu lallai ayau zamuyi aiki a kansu ka bamu jininsu kuma bawani me😠😡☠️☠️💀 dakatar damu zamu mayar dakai sannan dole ka sa mana mutum daya wanda kake so nan ma🤖👽👿 'kungiyar mu tana da 'karfi da tasiri wannan daji ne dana samar dashi na siddabaru da tsafi babu wanda zai ganshi sai idan a cikin mu kake na kirkire shi ne dan jin dad'i da cutar da mutane batare da sun min komai ba sannan dole suyi abinda nake so ko na hallaka su zaka iya tafiya kada kuskure ya sanya ka fad'awa matarka wani abu game damu zaka hallaka da u'kuba ta👹 rufe idonka" rufewa yai na tsawon mintuna baiji ance bud'e ba shikuma yana tsoron bud'ewa karyai kuskure jin muryar Halima yayi tana cewa.

"Ikon Allah alhaji wannan sabon salon fa kiran sallah da usur naga ka rufe ido ko gyangyad'i kake"?.

Kai ya girgiza "a'a ba gyangyad'i nake ba batace na bud'e ba"?.

Cike da mamaki Halimi ta sake kallon shi jin abinda yace kodai 'bacin ran da ya shiga ya ta'ba masa 'kwa'kwalwata ne sake duban sa tai sosai taga dai har lokacin idansa yana li'ke kamar tsohon makaho😂😁 tace "wacece batace ka bud'e ido ba wai alhaji kana lafiya kuwa"? Jin yana neman yin 'barna yasa da sauri ya bud'e ido a gigice yana kallon ta tuna cewa idan yai kuskure harda shi za'a 'batar jin ta sake jefo masa tambaya "Alhaji ina ta magana ka share ni wai ina kaje ne tun shekaran jiya baka dawo ba sai yau"

Cike da tsananin mamaki ya juya yanai mata kallon baki da hankali ne yace "shekaran jiya kuma? Wannan wanne irin hauka ne na fita d'azu kice wani kwana biyu bana gida saboda ga wanda baisan abinda yake ba ko sai nabar kwana a gida kawai tsabar kin mayar dani gaula"? Baki bud'e Halima take kallon sa anya bai fita hankalin sa ba da gaske take yau kwana biyu baya gida ganin ya mi'ke zaibar gurin tace.

"Amma alhaji da wasa kake ko"? Dakatawa yai "da wasa nake me"? "Da wasa kake dan kaji me zance ne shiyasa ko Australia d'in kaje...............

"HALIMA ya ishe ki bansan shirmen banza Italia naje ko California ba Australia ba zancen iska ke wai mahauci kika mayar dani ne inace d'azu na fita taya zanyi tafiya kwana biyu ban sanar miki ba"? Shiru tai kawai ta zuba masa ido ta kasa cewa komai yaci gaba "ko kina tunanin naje mun had'u da baby ne tunda naga yanzu zargi ya shiga tsakaninmu Halima ki shiga hankalin kifa kafin na saita miki shi............ shiru yayi yana kallon TV ganin ana haska gawar Gwamna da kuma Commissioner cewa sun rasu daren shekaran jiya zuwa safiyar yau zaro ido Halima tai tana kallon Prof wanda ya zubawa TV ido yana sakin murmushi d'ora hannu tai aka tana cewa.

"Nashiga uku Alhaji mezan gani haka badai kaine kayi wannan aikin ba karkace min da hannunka ko had'in bakin ka? Wata irin dariya ya saki wanda ta tsorata Halima yana cewa "eh mune muka kashe su nine na bayar da jininsu a 'kungiyarmu kuma ba kinji na fad'a miki ba duk wanda kika fad'awa wallahi zaki mutu ranar kwanan 'kabari zaki ni yanzu na zama had'ararran mutum ki bini a hankali Halima kinji dai na fad'a miki idan kunne👂 yaji"? Ya karasa maganar yana ri'ke kunnen sa Halima dai kasa magana tai duk jikinta rawa yake.

Yace "ina Hudayyah zan kaita wani wuri yanzu duk ma inda kika kaita kafin na shiga na fito ki dawo min da 'yata" muryar Halima na rawa tace "ina zaka kaita Alhaji na rokeka kada ka d'ora ta akan gur'batacciyar hanya kaima inai maka fatan shiriya please alhaji badan niba karka sanya yarinyar nan cikin wani mummunan bala'i dan naga ka matukar 'bata a halin yanzu ka fita haske ka shiga duhu kayi nisa Alhaji bakajin kira".

"HALIMA ki kiyaye nifa idan kika cika tambaya zaki hallaka saiki kame bakin ki" yana kaiwa nan yayi gaba d'ora hannu Halima tai aka tana binsa da kallo harya shiga part dinsa ya banko kofa toshe kunne tai tana sake kai dubanta kan TV jikinta na tsuma tabbas da gaske Gwamna ne da commissioner ana musu sutura hawaye ne taji ya cika mata ido yana zuba shar shar daidai ya sake fitowa Hudayyah na binsa a baya zasu fita Halima da kuka yaci 'karfin ta tace.

"Hudayyah karki je ko'ina idan na isa dake ki dawo idan kin d'auke ni mahaifiya wacce zan fad'a miki kiji".

Juyowa Hudayyah tai tana kallon ta tace "haba dan Allah mum yanzu fa zamu dawo Daddy yace zan raka shi sahat ne me zan taho miki dashi"?.

Halima data gama rudewa jin abinda Hudayyah tace yasa ta kalli Prof da alamar tambaya a fuskarta na mamakin 'karyar daya shimfid'a mata wato 'yarsa ma saiya yaudare ta jin bud'e 'kofa yasa ta kallon kofar harsun fita da gudu ta bisu compound d'in gidan ya bud'e mata mota ta shiga Halima fuskarta fal da tsananin fushi tace.

"Hudayyah nace karki je ki fito a motar nan"?.

Tsaki Prof yaja yana ri'ke da murfin motar ya zafgawa Halima wata ba'kar harara yana cewa "ta fito taje miki gidan uban wa? Halima kibar sakun ido yanzu idan ba haka ba zamu kwashi damben tsiya dake wallahi kinji na rantse".

Takaici ne ya rufe Halima tana kallon sa ta jinjina kai tana cewa "shikenan Alhaji kayi komai lokacin kane akwai ranar dana sani tana nan zuwa abinda ka shuka shi zaka girba ba'a shuka gyad'a dawa ta fito kabi a sannu kabi a sannu Alhaji ina gargad'in ka cewa ka dawo hanya ka tuba tun kana da sauran lokaci kafin duniya ta juya maka baya" banza yai mata yana had'e rai maida hankalin ta tai kan Hudayyah data sa earpiece a kunne sai kad'a kai take tace.

"Ke kuma tunda kin za'bi kibi makauniyar hanya babu ruwa na idan kikaje ban yafe miki ba".

"Sai mai dan baki yafe mata ba dama albarkar ki wata tsiyar zata amfana mata kije ki

Please Login or Register in order to submit comment