Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tambayoyi daya wutar ta tashi sannan sukai wa gurin video da makarantar sannan bayan su koma suka fad'i dukkan abinda suka gani lallai mutanen garin na bukatar taimako ba karamin 'barna wutar tayi musu ba, dole aka dakata dayin makaranta harsai an gyara kafin aci gaba domin gyaran zaici kud'i sosai ga 'konewa gidajen mutane.

Kamar yadda 'yan jaridar nan suka dauki video suna zuwa suka yad'a shi a gidajen television da radio mai martaba yana zaune yana ganin labaran hankalin sa ya tashi wannan abun ya faru amma bai sani ba taya zai zauna lafiya indai irin wannan abubuwan suna faruwa ransa ya 'baci sosai don gani yake maybe sakacin Governor ne domin ai duk tsiya yasan da garin tunda a campaign yaje ya musu za'kin baki gari ko gida daya ne indai lokacin campaign ne ana zuwa dan haka yasan da garin amma ace harsu shafe tsahon watanni takwas da gobarar babu wanda ya tallafa musu abar ta batun makaranta amma magidanta fa wadanda gidajen su ya 'kone a ina suke kwana? A layi ko kwa a ina? 'Daga waya yai fuskarsa babu alamar walwala ko wasa yana bada umarnin lallai yau d'in nan yana son ya gana da gwamna, yadda ya bada umarni haka ne ta faru da dare misalin goma suka samu ganawa mai martaba da Governor ya nuna 'bacin ransa sosai yayi fad'a gwamna ya nuna masa cewa ba laifin sa bane shima bai sani ba wakilan 'kananan hukumomi ne basa aikinsu yadda ya kamata dan haka mai martaba yace lallai gobe ko shi bazai samu damar zuwa ba ya tura wakili zaisa 'kaninsa Alhussain su tafi tare a kai musu tallafi na kud'i sutura da kayan abinci amsa masa gwamna yai sukai sallama tare da alkawarin zai tura wakilin sa gobe suje garin tare.

MRS AL-AMEEN AHMAD CE๐Ÿ˜˜.

See u next time, nagode masoya we will meet again ๐Ÿค—๐Ÿค—.

Sai Allah ubangiji mai duka mai yau da gobe jallo mafi girma ya kaimu gobe da rai da nisan kwana ๐Ÿ˜Ÿinai wa dukkan masoyana barka da wuni da fatan alkairi ๐Ÿ’“๐Ÿ’•๐Ÿ’ž.

YUSRAH MUSA ABUBAKAR ๐ŸŒน๐Ÿค™๐Ÿ‘Œ MAI TAMBARIN YMA DUTSE NEW WORLD ๐ŸŒ NEW LIFE ๐ŸŒŒ ANDA NEW STYLE ๐Ÿ‘Œ SABUWAR DUNIYA KUZO KUYI KALLO DAD'I YANA JIGAWA GARIN ILIMI GARIN ADDINI ZAMAN LAFIYA JIGAWA๐Ÿž๏ธ๐Ÿž๏ธ๐Ÿ—ป.

See๐Ÿ‘€ u next morning ๐Ÿค™.

Mrs Al'ameen Ahmad ce ๐Ÿ˜˜
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

TYPING ๐Ÿ“ฒ Thus, Jun5/6/24 YUSRAH MUSA ABUBAKAR ๐ŸŒน๐Ÿค™.


๐Ÿ’ŽMe kamar sarki ๐Ÿ’Ž



WhatsApp no:234 905 527 3614.
Yusrah Musa Abubakar maman little Zaran aunty ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ.

๐Ÿ—ฃ๏ธ๐Ÿ—ฃ๏ธ๐Ÿ—ฃ๏ธ๐Ÿ—ฃ๏ธ๐Ÿ—ฃ๏ธIna kake d'an uwa rabin jiki ha'ki'ka ka cancanti jinjina ๐ŸŽ‡๐ŸŽ‰ ina maka barka da wannan lokaci fatan alkairin Allah yakai maka duk inda kake Amin ๐Ÿ‘๐Ÿ‘.
๐Ÿ’•SALEEM MUSA ABUBAKAR ๐ŸŒนโœŒ๏ธ.

Sulaiman Ibrahim Usman
Usman Ibrahim Usman
Abubakar Musa Abubakar
Ibrahim Musa Abubakar
Fatima Musa Abubakar
Husnah Ibrahim Usman.

KU TAHO MASOYAN 'KWARAI๐Ÿคฃ๐Ÿคฉ๐Ÿ˜œ.

MARUBUCIYA๐Ÿ“š๐Ÿ’ถ๐Ÿ‘‡
โœ๏ธ Yarima Abdul-maleek
โœ๏ธ Rayuwa biyu
โœ๏ธ Safreeyyah
โœ๏ธ'Dan millionaire
โœ๏ธMinah-Umer
โœ๏ธDama kece
โœ๏ธ Royalty
โœ๏ธ Husnah ko Badiyat
โœ๏ธ Zuciyar Aliyu
โœ๏ธ Haskena Sauban
โœ๏ธA gidan talaka
โœ๏ธKowacce 'kwarya
โœ๏ธMe kamar sarki.

35~As-shakur๐Ÿ’•
The grateful
36~Al-Aliyu
The Sublime ๐Ÿ’•

17~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Shakirnah .

๐ŸŒ„ULCERATION ND ASTONISHED๐ŸŒ„
Episode 35&36
Washe gari Aisha da Jamila ba lafiya anyi cinye cinyen kayan mai'ko bayamma ta tashi Asma'u kuma bata nan sunyi tafiya ita da Saude sai sati mai zuwa zasu dawo iya Amatu yanzu malam Habu yake kaiwa makaranta dan haka baya kaita a mota saboda ita kad'ai ce mashin d'in haya yake hawa ya rakata kullum yauma kamar yadda ya saba yana zaune a kofar d'akinsa yana jiran ta ganin shiru bata fito ga lokaci yana dad'a 'kurewa kuma dama yau sun makara rana ta d'ago sosai kila ma period d'aya ta wuce d'an 'kwalla mata kira yai.

"Binta wai ina maman nawa ne bata fito ba? lokaci fa yana kara ja karta makara a dake mun ita bazan ji dad'i ba".

Fitowa Binta tai da cooler 'karamar irin ta basket d'in yan makaranta bayanta Amatu sanye da uniform lokacin shekararta shida d'an zuba mata ido malam Habu yai kafin ya sauke numfashi yana cewa "ubangiji Allah ya d'aukaki rayuwar ki mamana ina fatan ki zama wani abu nan gaba wanda bani ko Binta ba al-umma da yawa su 'karu dake" murmushi Binta tai cikin jin dad'i tace "insha Allahu addu'ar ka zata kar'bu amma irin wannan kallon haka da kake mata kamar akwai abinda kake tunani domin na riski lokuta da dama idan kuna tare da ita sai naga ka zuba mata ido meyasa"? Rike hannun Amatu yai yana kar'bar cooler breakfast d'inta ya mi'ke zasu tafi yana cewa "eh dalili shine idan ina kallonta zuciya ta tana samun nutsuwa da kwanciyar hankali shiyasa koda yaushe nake addu'ar Allah ya bata nisan kwana lallai soyayyar wannan yarinyar a cikin rai da jini na take yawo Binta ina son yarana kuma dukkan su daya suke a gurina amma fa maganar gaskiya nafi sonta" ya karasa maganar yana sake rike hannun nata dakyau yana sake jin sanyi yana ratsa shi 'yar dariya Binta tai cikin tsokana tace "soyayya tasa ka manta da fitar lokaci kar abinda kake gudu ya faru ta makara a mata bulala a gabanka" dafe kirjinshi yai yana mata hararar wasa yace "Aiko yau damun kwashi damben tsiya da malaman nan dan wallahi nad'e hannun riga da 'kafar wando zanyi mu daku dasu sai inda karfi na ya 'kare" dariya sosai Binta keyi tace "kai da anyi abun kunya kun saba dasu fa" jan Amatu malam Habu yai suka fara tafiya yana cewa "sabo da kaza๐Ÿ”baya hana a yanka ta ayi farfesun ta dan kawai mun saba saina zuba musu ido su dake ta wallahi ko an shiga aji haka zasuyi hakuri su barta dan yau d'aya dai, mu mun wuce" to Allah ya tsare" Binta ta fad'a tana shiga d'aki domin duba jikin su Aisha dan itama A'i bata gidan ta tafi dubiyar wani d'an uwan su da mota ta bugeshi ya fad'i a mashi yaji ciwuka.

Lokacin da malam Habu ya fito ba kowa shiru garin da yake dama tun wuri masu mashinan suke ficewa wajen 'kauyen dan sufi samun kud'i duba gabas da yamma yai nan dai ba kowa ga tsewa bazata kaisu ba indai ba hakura zatai da zuwa makarantar ba yau daukarta yai ya fara tafiya da ita dan yafi sauri da nufin idan ya samu me mashin a hanya sai su hau idan kuma bai samu ba nan da awa yaje bai bar anguwar tasu bama ya hango Dauda zai fita d'aga masa hannu yai amma bai gano shiba d'an tsaki yai yana cigaba da tafiya ya fito bayan gari ya sake had'uwa da Daudan ya shawo kwana da alama akwai abinda yake nema dan a hankali yake tafiya yana kallon kasa dakatar dashi malam Habu yai.

"Dauda lafiya ina zakaje haka ina d'ago ma hannu baka ganni ba"?.

Kashe mashin d'in Dauda yai yana sauka yace "wallahi kud'i na zubar dubu biyar kuma ba nawa bane kud'in babah ne ta bani na saro mata goriba a kasuwa bari nabi hanya a kafa ko zan samu" to malam Habu yace yana d'ora Amatu akan mashin d'in dake tsaye da kamar minti goma ya dawo da ganin fuskarsa bai samu kud'in ba kallonsa malam Habu yai "ka samu ne"? Kai ya girgiza "a'a wallahi ban ganshi kuma yanzu fitowa ta a gida kenan gari shiru ban ci karo da kowa ba balle na tambaya shikenan ya zama asara muje na kaiku" hawa suka ya tada mashin sukai gaba zuwa makaranta dama kuma yaune kasuwar garin shiyasa 'kauyen su malam Habu yai shiru kowa ya taho cin kasuwa sauke su yai a bakin shiga makarantar hannu malam Habu yasa a aljihu yana dauko kud'i ya bashi dubu biyar d'in yana cewa "ri'ke Dauda kaje ka sai mata goribar ka kai mata karka nuna kud'in ya fad'i sannan ga wannan kud'in aca'barka" ya d'ora masa d'ari biyu akai baki bud'e Dauda ke kallon sa da mamaki saidai ba abin mamaki bane tunda dama ya saba kyauta halin malam Habu ne ko ma'kiyi zai bada sheda saidai in baya tsoron Allah godiya sosai Dauda yai wa malam Habu kamar bazai daina ba murmushi malam Habu yai "karka damu kaji jeka abinka ai yiwa kaine" wucewa Dauda yai yana sake gode masa yayin da malam Habu ya ri'ke hannun Amatu suka fara tafiya zasu shiga makarantar.

Jin jiniya yasa mamaki ya kama malam Habu to yau kuma me akeyi a cikin makarantar bai gama tunani ba yaga motoci tsala tsala masu kyau da tsada sai she'ki suke suna ta fitowa a jere har daukar ido suke komawa gefe malam Habu yai yana sake ri'ke hannun Amatu dakyau kafin motocin su wuce wata farar mota data fito mai ba'kin glass 'katuwa tsadadda ce ta taka burki a daidai saitin su motar dake bayan farar aka bude murfin ta wani bafade ya fito da gudu yana bud'e murfin farar motar tare da durkusawa cikin girmamawa yace.

"Allah ya taimake ka akwai matsala ne"?.

Kai ya girgiza yana kallon fuskar kyakkyawan matashin saurayin dake hakimce zaune a gefensa ya d'ora 'kafa d'aya kan daya yana sanye da tsadaddun kaya ganin yadda ya had'e girar sama da kasa kamar ba shine ya bukaci su tsaya ba yasa Alhussain yai murmushin rigima irin tasa yana cewa "eh Harun akwai matsala" sake kallon fuskar saurayin yai bazai wuce shekara sha takwas ba amma fa kyakkyawa ne na kwatance kyau kuma irin na larabawa idan ba magana yai ba zaka rantse da Allah baisan meye wani yaren hausa ba.

Mamaki ne ya kama 'kanin mahaifin nasa har yana dafa shi cike da kulawa yace "Asad kana lafiya meke damun ka meyasa kace a tsaya kuma ka "ki magana"? Cikin aji da sarauta ya d'ago yana kallon sa na wani lokaci har Alhussain ya fidda rai bazai ce komai ba sai kuma yaji zazza'kar tsadaddiyar muryarsa mai sauka cikin tsari da dad'in sauraro a hankali yace.

"Ina son magana da wannan".

Inda yake kallo shima Alhussain nan ya kalla su malam Habu ya gani tsaye da mamaki ya kuma kallon Asad domin shi idan ba yanzu ba bai kula dasu ba da har zaice masa me zai masa sai kuma ya ce bari ya 'kyale yaga abinda Asad din zaiyi kallon sauran fadawan dake dur'kushe Alhussain yai yana cewa "ok Harun bud'e masa ya fita" da sauri cikin gaggawa Harun ya mi'ke da gudu ya zagaya 'bangaren ya bud'e masa tabd'i yafi minti goma bai fito ba kafin ya ziro 'kafa a hankali ya fito kai Masha Allah kamar babban saurayi akwai 'kira a tsaye yake zarrr jarumtacce sadauki 'kakkafa yana da manyan ido ga dogon hanci fari irin na larabawa ga pink lips kaiii ya gama had'uwa cikin taku ya fara tafiya cike da nutsuwa zuwa inda malam Habu ke tsaye wanda Alhussain jin hankalin sa bai kwanta ba shima ya fito yana bin bayansa ganin Alhussain ya karaso yasa malam Habu ya saki hannun Amatu yana dur'kusawa cike da girmamawa yace.

"Gaisuwa nake ranka ya dad'e Allah ya baka nasara".

Fadawan dake bayansa ne suka amsa masa "an gaisheka kaima mai nasara ya amsa gaisuwarka" kallon Asad Alhussain yai ganin ya zubawa Amatu ido kuma baiyi magana yasa ya mayar da hankalin sa kan malam Habu yana cewa "tashi" mi'kewa malam yai tsananin mamaki ya kamashi da yake ba iya bambance su ake ba baiyo tunanin ba mai martaba bane 'kaninsa ne lallai ya jinjinawa rashin girman kansu.

Shirun ne yai yawa gajiya Alhussain yai don yaga alama indai ba cewa yai su tafi ba Asad baida niyyar cewa 'kala kuma baida niyyar tafiya yace "Asad kazo mu tafi ko"? 'Dagowa idanonsa yai yana kallon Alhussain kafin ya mayar da hankalin sa kan malam Habu yana cewa "wannan 'yarka ce"? Kai malam Habu ya d'aga "eh 'yata ce" sake jefa masa tambaya yai "mene sunan ta"? "Sunanta Hauwa" d'an rufe ido Asad yai jin sunan mahaifiyarsa kai Alhussain ya jinjina yana cewa "shikenan fad'uwa tazo daidai da zama sunan maminsa ne" fuskar malam Habu da mamaki yace "masha Allah".

Bud'e ido Asad yai yana kallon malam Habu yace "zaka bani ita"? A tare Alhussain da malam Habu suka zaro ido Alhussain na cewa "to fa Asad kamarya zai baka ita matsayin 'kanwa ๐Ÿ‘ซ ko mata ๐Ÿง•"? Kai Asad ya girgiza yana cewa "mata" a d'ari Alhussain ya sake zaro ido da 'yar dariya yace "to mata kuma Asad? A lallai mun kusa daukar suruka kwana kusa muna komawa zani yiwa yaya albishir" kallon malam Habu Asad yai "zaka bani ita"? Fuskar malam Habu da murmushi yace "eh zan baka ita indai kana son ta"? A hankali Asad ya d'aga kai "eh ina son ta" "to shikenan na baka ita".

"Asad shirmen ya isa haka kazo mu tafi" Alhussain yai maganar kawai da murmushi fal fuskarsa juyawa Asad yai yana kallon sa kafin yace "ina son zamuyi photo" ya fad'a yana mi'ka masa wayar hannunsa "kayi mana" kai Alhussain ya girgiza yana amsar wayar matsawa Asad yai yana sa hannu ya d'aga Amatu sama yasata a kafad'arsa dariya Amatu tayi cike da yarinta daidai za'a d'au photon shi kuma yai murmushi daukarsu yai yana cewa "kunyi kyau kar lokacin shiga ajinta ya wuce ka ajeta mu tafi" ajeta Asad yai yana shirin bin bayan Alhussain wanda sukai sallama da malam Habu sai kuma ya tsaya yana cewa "shekararki nawa"? Cikin za'ki Amatu tace "talatiin da goma da d'ari ๐Ÿ˜‚".

*KAI ๐Ÿ™† AMATU SHEKARA 'DARI DA ARBA'IN ๐Ÿคญ๐Ÿ˜ฒTAB AIKO BAFFAH BAIKAI HAKA BA๐Ÿคฉ๐Ÿ˜‹*.

Dariyar da ba shiri malam Habu yai yana cewa "shekararta shida" "shekararki shida ni kuma sha takwas idan kika hada da nawa kina da shekara ashirin da hudu kenan" ya karasa maganar yana cire kyakkyawar rigar sanyin dake jikinsa da photon zaki kwance a jiki a 'kasan zakin an rubuta ALIYU ASAD da manyan ba'ki bata yai batare da ya sake magana ba ya juya ya soma tafiya da kallo suka bishi har ya shiga mota aka rufe suka bar gurin tun suna iya hangosu har suka 'bacewa ganinsu.

Sauke ajiyar zuciya malam Habu yai yana kallon rigar dake ri'ke a hannun Amatu sai tashin 'kamshi take yace "Mamana muje ko? Lokaci ma ya matukar 'kurewa da yake yau Juma'a gashi yara har sun fito inaga baifi nan da awa a tashi ba kawai ki barshi mu koma gida yau din kya zo ranar litinin muje a kasuwa na sai kayan miya mu tafi gida" kar'bar rigar yai ya zuge jakar goyon dake bayanta yasaka a ciki ya zuge kafin ya kama hannunta suka wuce.

Kamar yadda malam Habu ya baiwa Dauda kud'in gudun karya sake zubarwa sai kawai ya sayi goribar ya koma kai mata daga baya ya dawo yai hayar da mamaki babarsa ke kallon shi tace "sannu sarki shiririta na baka kud'in goriba saika tafi ka barshi anan ina shara na ganshi a inda ka zauna kuma da ya ka sayo goribar bayan kace baka da kud'i ko bashi ya baka"? Kai Dauda ya girgiza yana zama yace "aini babah na dauka a hanya a jefar kud'in ashe tun a gida ne kuma wallahi kinga muka had'u da malam Habu zai kai 'yarsa makaranta shine ya bani kud'in yace na sai miki" d'an zaro ido tai tana ri'ke baki tace "oh Allah mai baiwa kai malam Habubakar baya gajiya da alkairi Allah ka bud'a arzikin sa ka tsole idon ma'kiya gaskiya Habubakar mutum ne na 'kwarai Allah ya biyashi da mafificin alkairi" Amin Dauda yace harya mike zai tafi yace "am babah tunda an samu kud'in inaga ki bayar a mayar masa abinsa ko" kallon sa tai tana cewa "eh kayi gaskiya kar'bi wannan din kace masa a gida a manta" kar'ba Dauda yai yana fita ya hau mashin d'in ya hango malam Habu ya sauka da jibgin kaya yasa da sauri ya karasa yana cewa "ashe kaga kud'in a gida na barshi ban sani ba na jefarshi" kallon sa malam Habu yai "haba Dauda kuma dan ka gani saika dawo min da kud'ina mayar mata dan Allah ta 'kara jari" cike da jin dad'i Dauda yace "to an gode Allah ya kara arziki" "Amin kai kam karka damu mayar mata" malam Habu ya karasa maganar yana fara d'iban kaya yana shiga gida dasu Saida gama sannan ya zauna kan tabarma a kofar mashigar d'akinsa cikin gajiya ya ce "Binta Kai min ruwa nai wanka a d'an fad'a yau garin da sanyi" to Binta tace tana mi'kewa cikin mamakin labarin abinda ya fad'a mata na had'uwar da sukai da mai girma Alhussain ya nuna mata rigar da Asad d'in ya baiwa Amatu saida ta gama komai ta dawo daidai zai tafi wanka tace.

"Malam amma dagaske ka bashi ita da aure kuma idan ya dawo fa yace yazo kar'bar ta"? Murmushi malam Habu ya "idan ya dawo yace yazo ne dan cika alkawarin sa wallahi Binta zan bashi" 'yar dariya Binta tai tana cewa "tab saidai a mafarki mezai dawo yayi yanzun ma sila ta kawoshi balle ya auri d'iyar talaka" "oh kina mamaki ne"? Kai Binta ta d'aga "eh 'kwarai ina mamaki sosai ma abin da kamar wuya" juyawa yai yana tafiya tare da cewa "ki daina jin mamaki babu abinda gagari mahalicci" da kallo Binta ta bishi harya 'kule sannan ta sauke ajiyar zuciya tana sake zubawa Amatu ido wacce gabadaya ta tattare hankalin ta ga wasan da take da 'kyar karamar Teddyn ta.

Mai nasara Alhussain sun koma gida lafiya saidai bai samu shiga gurin mai martaba ba sai bayan sallar isha yana part dinsa ciki ni'imtaccen 'kayataccen tsararran kyakkyawan falonsa wanda yaji kayan more rayuwa daga shi sai matansa biyu amma daya balarabiya ce da alama itace mahaifiyar Asad dan yana kama da ita zama Alhussain yai suna niyyar tashi domin basu guri su tattauna ya dakatar dasu "a'a kuyi zaman ku ba wani abun bane" komawa sukai suna zama shikuma ya fara bayyanawa mai martaba halin dayaje ya tsinci mutanen wannan kauyen amma yanzu alhamdulillah komai yazo karshe an taimake su da sutura kayan abinci da kuma kud'i su gyara gidajen su" fuskar mai martaba fal da annuri yace "masha Allah sai yanzu naji nutsuwa ta zo min hakan yayi kyau sannu da 'ko'kari d'an uwana Allah ya kiyaye gaba" Amin yace yana mayar da hankalin sa kan Mami yace "baki tambayi babyn kiba Asad gidan rigima" murmushi Mami tai "ai bansan kun dawo ba sai yanzu dana ganka ya hanya" "humm hanya lafiya amma suna bukatar gyaran ta nayi magana da wakilin da Governor ya tura cewa ayi musu titi suna shan wahalar abin hawa a hanyar rairayi yayi yawa" kai mai martaba ya d'aga"eh kayi gaskiya Allah ya taimaka" Amin yace da murmushi akan fuskarsa yace "babyn ki fa yayi budurwa kwanan nan zamusha biki" zaro ido Mami tai "to ikon Allah a ina ya ganta ko a garin take"? tabd'i shifa Alhussain sai yanzu ma ta tuna masa basu tambayi malam Habu sunansa ba balle ya fad'a musu wani abu game dashi yace "tanan munyi kuskure ni ko sunan uban yarinyar ban sani ba" dariya sultana Fatima tai "to harda gurin uban 'ya kukaje ko ro'kon arziki kuka kai daga can ๐Ÿ˜œ" ta karasa maganar da rasha kowa darawa yai Alhussain yace "a'a ba ro'kon arziki mukaje ba ya taho ne fa zai rakota makaranta ya hango su shine yasa aka tsayar da mota yaje gurin su yarinyar shekararta shida๐Ÿ˜‚" dariya Mami tai "tofa shekara shida kace ma karamar yarinya ce" kai Alhussain ya d'aga "eh yarinya ce sosai sunan ta Hauwa"..,...............,.....,.,...

Duk abinda ya faru a gurin ya fad'a musu har kyautar riga da yai mata mamaki ne ya kama Mami tace "to abin nasa babba ne kam gaskiya zamusha biki amma inba shirmensa ba taya zaice a take zaku taho tare" "eh kinga laifinsa ne sone ya kawo haka ni nayi mamaki ma Asad da magana bata dameshi ba amma a gurin bakiji tambaya ba salo salo kamar wani d'an jarida".

Murmushi mai martaba yayi "nidai nafi tunanin ganinta da uniform dayai ne yasa yace ku tsaya nasan waye Asad akwai d'auke kai" yar karamar dariya Alhussain yai yana cewa "ai yaya Asad nada hankali yanzu shekara sha takwas baza ace yarinta ce tasa kawai uniform dinta ya burgeshi ba da gaske na hangi son yarinyar a idanunshi" kai mai martaba ya jinjina "shikenan bamu da ja koma wacece ita muna maraba ta shigo familin mu matsayin 'ya kuma suruka garemu zanso naga yarinyar data sace min zuciyar jarumtaccen jarumin sadaukin yarona miskili kyakkyawan gaske".

Hhhhhh tab dariya su Mami suka fara dan indai aka zo bangaren Asad mai martaba da kansa yake kurara abinsa yayi masa kirari ya kambama shi yaace Asad sawun giwa ne 'badda na ra'kumi saraki sadauki mai gyararran gashi, Mami na murmushi tace "uhm idan da sabo mun saba babyn Mami ya d'aukaka da yawa" kai mai martaba ya jinjina "eh toda ya kikace kina da jane" ri'ke baki Mami tai "a'a masu yaro mukam yan kallo ne" "eh na yarda ku zama yan kallon yayin dazan baku mamaki akan Asad d'ina tun daga yanzu ya fita zakka a cikin su rana daya aka haife su amma fa ya girme musu yanzu domin yahau turbar da babu wanda ya hau".

"Eh wannan gaskiya ne yaya kaima Kazo da magana domin nine shaida bari na tafi dare yayi sha daya ta kusa saida safenku" to Allah ya tashemu lafiya ka huta gajiya" fita Alhussain yai ya barsu suna ci gaba da tattaunawa.

Asad na zaune a bedroom misalin karfe sha daya na dare Ajeeb na kusa dashi sai sharar barci yake shikam yana tsaye jikin window ya d'aga labule yana kallon waje gabadaya tunanin ya hana shi sakat ya kasa nutsuwa balle ya samu runtsawa waya ce kawai a hannunshi ya zubawa photon da sukai d'azu ido yana kallon fuskarta da dariyar datai juyowa yai ganin Ajeeb yai juyi yana magana da alama mafarki yake yasa yaja tsuka yana fita daga bedroom din ya fice a part din nasu ma gabadaya ya kama hanyar shiga garden babu kowa gidan yai shi ji yai wata murya tace.

"ALIYU ASADULLAH๐Ÿฆ".

Dakatawa yai cike da mamakin waye yai masa magana amma ba kowa ya sake duba gabansa da baya babu ko 'kwaro bai fasa ba ya tunkari bud'e kofar shiga garden ya shiga jiyai an sake cewa " 'Dana Asad" da sauri yakai kallonsa 'karkashin wata bishiyar tsohuwa ya gani zaune akan wani farin abu mai walwali tasha kwalliya da murmushi a fuskarta gabanta babban littafi mai girma da tudu" mamaki ne ya kama shi ya tsaya cak yana kallon ta bawai dan ya razana ba sai tunanin wace wannan tsohuwar bai ta'ba ganin taba me takeyi anan? Tambayar dake ransa kenan yaji ta sake kiran sunansa a karo na uku tana masa alamar yaje gareta babu fargaba ko wani tsoro a tattare dashi ya soma takawa zuwa inda take.

"Bismilllah zauna"? Tana rufe baki yaga kujera mai kyau a gefensa zama yai batare da jin ko d'ar ba yana kallon ta ta soma magana "sunana Innah Habibati na sani kai yaro ne mai hankali kuma da akwai tambayoyi a ranka game dani wace ni ya akai nazo nan ni mutum ce ko a'a? To maganar gaskiya ni aljana ce a Duniyar aljanu ni sarauniya ce ina da 'ya'ya guda d'ari shida da hamsim sannan mijina ma yana nan muna rayuwa a cikin daula kamar ku kuma har gobe kasan wani abu? 'Dazu lokacin da kai rakiya wa 'kanin mahaifin ka kun tsaya inda kaje gurin mutumin da yake ri'ke da yarsa kunyi zance a fadata kuma na yaba da hankalin ka shiyasa naji bazan iya barinka ba dan akwai 'kalubale a gaban ka saidai nayi maka alkawari zan zame maka garkuwa bazan bari a cutar dakai ba, d'an shiru tai tana kallon sa sai kuma tace "kalli nan" kallon littafin yai saiya gansu lokacin da suke tsaye a gurin inda yake tambayar Amatu shekarun ta nawa tace talatiin da goma da d'ari" d'an murmushi ya sake wanda baisan yayi hakan ba tare da d'agowa ya kalli fuskar tsohuwar exactly women sak babu wani abu dazai nuna maka cewa aljana ce ta fito a kyakkyawar sura zaiyi magana ta katseshi "a'a basai kace komai ba na sani kaidai karka damu kuma kada ka fad'awa kowa yanzu zan tafi amma zan dawo gareka kwana kusa idan na samu

Please Login or Register in order to submit comment