Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace “Mama Mama, world best tashi kiji, Mama ai bacci kikeyi ko” tasake shiru, ganin ko motsi Mama batayi yasa tai tagumi tana kallonMama tace “zan jira harsai kin tashi kinmin magana” ahankali Baba yataho yazauna kusada ita dasauri tajuyo takalleshi kaman mai karantan wani abu akan fuskanshi, kafadan Khairy yakamo sanan ahankali yace “Ummulkhairy mamanki has been bathling with cancer for so long, blood cancer bataso kisani cus tasan abinda zakiyi kenan idan kikaji she has few days left, u will not take it likely, saisa taboyemiki all this while mamanki has been sick, seriously sick amman taki yarda kisani duk ciwon da mamanki keyi taganki she will pretend she is fine” hawaye masu bala’in dumi ne suka zubo mata dasauri tasa hannu tashare, ahankali Baba yace “karki sakawa Maman ki hakan nan Khairy inhar she’s your world best, kimata addu’a tasan tabar ya tagari aduniyan nan muje mukaita makwancinta, your mum is tired she need rest, go and pray for your mum” ahankali Khairy tasake matsawa kusada Mama she can’t believe Mama ne nan kasa addu’an tayi sai kuka ahankali tace “Mama dan Allah dagaske wai kin rasu?”, zuwa yayyinta sukayi kawai rungumeta ahankali Manaf yace “Mama tarasu Khairy pray for her” Ahankali tace “Mama Allah yajikanki Allah ya gafarta miki, Mama why did u leave me, shikenan bazan kara ganin ki ba, Mama maisa baki bari na rokeki kiyafemin ba, kullum ina cikin batamiki rai inta rashin ji, Mama Tayaya zan cigaba da rayuwa baki aciki Mama Innalillahi wa Innailaihi raji’un” tashi Baba yayi ahankali hakama Baffa dasu Ya Hassan da Hafiz dakuma Zayn zasu dauki Mama dan kaita waje salla, wani Zabura tayi zata tashi dasauri Manaf yariketa, Mom yabama ita tana wani kalan nishi hannu Mom tasa takarbi inhaler ta tace “Khairy Khairy” kaman zata haukace haka takeji da kyar ta iya kallon Mom tace “Mom na shiga uku, Mom Mama tarasu Innalillahi wa innailaihi raji’un, Mom wlh wlh ko….” kawai maganan yakakare takara suma, ruwa Mom tashafa mata a fuska tanamata addu’a, tafarfado ta sume tai having Asma attack haka tadingayi ahaka har akama Mama salla aka tafi da ita, Khairy bamatasan inda kanta yakeba tana jikin Mom, jikinta yay wani mahaukacin zafi dayasa Mom takalli Ammi dake zaune tanajan charbi tace “Hajiya kira Alhaji Dr yazo jikinta yay zafi dayawa, kuma suman nan datakeyi yay yawa” dan jim Ammi tayi sanan tadauki wayanta takira Baffa ta sanar dashi.


Bayan magrib Baba yashigo gidan tareda Baffa gaisawa yayi da matan dake falo dakemai gaisuwa sanan suka taho sama tundaga stairs yake kallon Khairy dake kwance akasa gatanan gatanan ne kawai baa cewa komi, tsugunnawa Baba yayi agabanta ahankali yadagota sharaf ta taso Mom yakalla yace “tayi salla kuwa”? Girgizamai kai Mom tayi, Baba zaiyi magana kawai tasaki wani sabon kuka mai bala’in tabarai dayasa kowa na dakin yazuba mata idanu tana taba zuciyanta kaman ta mutu takeji, kaman tai hauka takeji, kaman tadawo da hannun agogo baya takeji tama Mama duk abinda takeso batare datasa Mama fushi ba, duk su Baba magana suke mata amman harga Allah bata gane komi kunenta ma yadode, duk suna zaune ahaka tai kuka ta sume tadawo Dr yashigo gidan, allura kawai yamata aka samu tai bacci, Baba zai dagata Dr yace “ku kawo bargo kurufa mata, let her sleep anan” Baffa da kanshi yashiga dakinta pink bargonta da filonta yadauko yakawo Baba yakarba yasamata akarkashin kai sanan yarufa mata bargon yana kallonta yana kafin yasa hannunshi yacire rolling gyalen dake kanta ya ijiye gyalen agefe long kalaban ta suka bayyana duk akai shiru.


Hayowa saman sukayi duka yaran Hafiz na rike da jakanta daya dauko daga motanshi Dan dazu amotar tabari dakinta yabude ya shiga ya ijiye sanan yafito yasamu gefe daya yazauna afalon, suma su Hassan da Manaf suka zazzauna, ahankali Zayn ke hayowa stairs din da duk yay wani irin tsayawama waje yayi yin wata waya saisa bai shigo tareda kannen nashi ba,hayowa yayi kallo daya yama Khairy dake bacci akasa da aka lullube da pink bargo yadauke kai sanan yawuce gefen Ammin shi yazauna akasa tareda daura kanshi kan cinyanta hakan yasa tadaura hannunta ahankali tana shafa kanshi, kallon yaran Baffa yayi yace “kutashi kutafi gida mu muna nan” cikinsu duka babu wanda yay motsi, ahankali Ammi dake shafa kan Zayn tace “Son tashi katafi gida kahuta yau ka dawo daga tafiya” girgiza mata kai yayi ahankali yace “I don’t wanna go Ammi” kallon Hafiz Baba yayi yace “wuce katafi gidan ka Hafiz” girgiza kai yayi shima yace “Baba ai basu kadai bane kanwarta damai mata wanka duk suna nan” addu’a Baffa yayi dukansu sanan aka shafa, aka zauna turus duk wanda yaga su Baba da yaranshi saiya tausaya musu abinda kuma yahana yaran Baffa tafiya kenan Dan idan suka tafi gidan zai musu wani iri kai mutuwa batada dadi! Baba da Baffa sauka falon kasa sukayi sukuma yaran duk suna wajen kusan ahaka bacci ya kwashe kowa daga Ammi da Mom da duk suke kan kujera zuwa su Manaf dake bacci rabi rabi falon yarage only Zayn ne baiyi bacci ba dayake tattaba wayanshi maganan da Baffa da Baba keyi akasa yanaji.


Motsin da Khairy tayi cikin bacci yasa yajanye kanshi daga waya yazuba mata idanunshi kusan sai yanzu nema yake mata a very good kallo tunda yazo, hawaye yaga suna gangarowa daga gefen idanunta pink lips dinta na motsi sosai cikin bacci ta kankame pink bargon da aka lullubeta dashi tana maganganu da kana gani kasan mafarki take. “Mama Mama wai kin mutu? Ai baki mutu ba ko, bansan menama su Baffa dasukemin karya ba, Mama zansha madara, in dauka, Mama Mama Maaaaa….” Wani dogon ijiyan zuciya tasauke na kuka kalabanta daya na saukowa kan fuskanta, dauke kai yayi daga kallonta shi dabama danta ba mutuwan yajishi balle yaran data haifa, he can’t even imagine loosing Ammi God no please, Allah ya sassauta musu koma mesukeji a zukatan su.


Wuraren 4 daidai tabude idanunta daga kwance datake tana kallon saman dakin da kallo, the first thing daya fado brain nata is mutuwan Mama, ajiyan zuciya tasauke tana assuring kanta cewa mafarki ne tayi, juyoda kanta tayi tabi kowa na dakin da kallo, Hafiz nakan kujera yatakure yana bacci, Ya Manaf na zaune shima kan kujera yana bacci, Ya Mu’az ma haka Maheer ne kadai akasa yana bacci, sai Zayn da kanshi kekan kafan Ammi yana bacci shima kaman wani auta, Mom dake saitin inda take akan kujera tana bacci itama ta kalla ajiyan zuciya ta sauke zuciyanta na tsinkewa but she’s still in disbelief, bargon jikinta ya yaye ahankali sanan tamike tsaye da kyar cikinta namata wani irin ciwo na yunwa dan jiya all through babu abinda tasa abaka, tadade tsaye tana rikeda cikinta kafin ahankali tafara tafiya jelan kalaban kanta na lilo abayanta tai hanyar dakin Mama, ahankali tasa hannunta tabude kofan kaman a kunnen Zayn danshi baida nauyin bacci hakanan any movement kodan kara daza’ayi yana tashinshi da sauri yajuyo da kanshi yakalli kofan tana tsaye bakin kofa tarike handle na kofan da hannu tana kallon cikin dakin gashinta na lilo.


Ko’ina na dakin takebi da kallo idanunta namata gizo daga taga Mama tafito daga bayi tana mata murmushi saita ganta kan dadduma tana mata murmushi, saita ganta kan kujera tana zaune rikeda littafin zikirin ta saikuma chan taganta kan gado kwance tana mata murmushi, hannayenta duka biyun tadaga takai kan idanunta ta murza idanun da kyau sanan taciresu tasake kallon dakin amman babu kowa ciki dawani irin sauri ta shiga dakin tai bayi budewa tayi dasauri tace “Mama kina ina” ganin babu kowa abayin yasa tadawo dakin tana juye juye kalle kalle bakinta na rawa tace “Mama kina ina”? Gadon tayi ta yaye bargon kan gadon, jini jini datagani a zanin gadon wanda na aman jinin da Mama tadingayi ne yasa taji kafafunta sun kara sanyi kawai tayi kneeling awajen takifa kanta akan gado sai kuka kaman ta kwakulo zuciyanta tayar takeji kukanta sa duk wani wanda zaiji tanayi kuka yake, kowa na falon tunda tafara kiran Mama suka farka amman babu wanda ya iya shigowa yacemata wani abu abar Khairy tai kuka dan ita akama Wanan mutuwan.

Da kyar Manaf ya iya tashi yashigo dakin gaban gadon yazo kusada ita yadaura hannunshi akan bayanta murya chan kasa yace “Khairy stop crying and pray for Mama, kinga tun jiya baki magrib ba balle isha’i, muje dakinki kicire rigan nan shower kiyi salla and pray for Mama, Mama tariga tarasu……” wani kalan ihu tayi da saida gidan gabadaya ya amsa. “Mama bata rasu ba, Mama batada lafiya babu wanda yafadamin, mena muku? Ni yarinya ce dazaa boyemin uwata batada lafiya, nama Mama laifi dayawa bansami dama na roketa gafara ba, nabar Mama agida natafi school nadawo kucemin Mama tarasu, babu wanda yagayamin Mama batada lpy saidai kugayamin tarasu, Mama b…….a…” maganan yasoma gagaranta sabida mugun attack na Asma daya taso daukanta chak Manaf yayi yafito da ita daga dakin yana karban inhaler da Maheer kebashi, Mom tace “please ku kulle dakin nan tadena zuwa ciki” kwantar da ita kan gadonta yayi yasa mata inhaler cus nishi take kaman zata mutu da kyar ta shaka, Mom tashigo dakin takalli Manaf dake kanta tace “tafi Manaf” fita yawuce yayi daga dakin.
[6/16, 7:56 PM] +234 701 275 3212: 2️⃣7️⃣

Free page

Da taimakon Mom tai wanka ta chanza mata kaya zuwa wani simple atampa doguwan Riga sanan tasata tai salla itadai tasan tai salla amman bamatasan metakeyi cikin sallan ba kotana karatu dakyau kobatayi jikinta yay munannan zafi, kwanciya tayi kan dadduman Mom tazo dagata tayi tacire mata hijabi tace “kwanciya akasan ya isa haka nan kar sanyi ya shigeki zoki kwanta akan gado” Mom ta kwantar da ita kan gado ta kwanta lamo kan gado hawaye nabin idanunta suna sauka kan katifan, hannu Mom takai tana sharemata hawayen ahankali tace “Khairy nasan mekikeji aranki yanzu haka amman kisani kome yan uwanki sukayi da mahaifinki sabida mamanki sukai hakan, shi mara lafiya ana so ana cikamai wishes nashi, barinma mara lafiya kaman na mamanki, Mamanki ita ta haifeku duka idan she choose ke kadai zata boyemawa rashin lafiyanta believe me tanada reason nata maybe taga Kece mai weak zuciya u can not take it, and believe me yanzu idan nagayamiki Wanan abin dakike yi yanzu is not what she wants Khairy, be strong dan yanzu Kece maman su yayyinki, kinyi tunani what Baban ki is going through yanzu haka, matarshi dasuka tsufa tare bata kuma dawanne zaiji dake koko da rasuwan da akamai? Khairy ki kwantar da hankalinki kinji, bari na sauka kasa na hadomiki ko shayi ne kisha” Mom tashafa kanta kafin ta tashi daga kan gadon tawuce tafita daga dakin su Manaf zasu shiga tahanasu.


Ranan haka aka wuni Khairy gatanan gatanan ne, takasa cin komi kotaci amai straight, rasuwan Maman ta yabi gari bama asan ya kawayenta sukaji ba before you know it kawayenta suka cika gidan harda Besty duka dakinta aka kawosu kallonsu kawai take kaman ta haukace, babu wanda take amsa gaisuwan shi, duk wanda yazo gaisuwan bazaiyi kuka ba amman dazaran kaga Khairy saikai kuka kawayenta sunyi kuka sunyi kuka harsun gaji, Besty tunda tazo take rungume da Khairy da jikinta kaman wuta tana kuka da kyar ta iya tauna kosai guda da Besty tabata abaki ahaka dare nayi suka tafi.




Hakanan yaji ya bala’in damu cus yakira Khairy yanaganin miss calls din daya sunkai 20 maybe but all ba amsa same with text messages nashi ba reply, he don’t know why but kasa jurewa yayi tashi yayi daga office din nashi yadauki car keys dinshi yafito wajen police station din, motarshi yashiga yajata yafice daga police station din, he don’t even know why he’s driving to layinsu Khairy but yasan zuciyanshi keeps pulling him to go there dudda bawai shiga gidansu zaiyiba, ahaka har yazo layin, kofar gidansu yagani tsaitsaye da maza sanan gashi an bude gate an saka canopy a compound din ga tabarmai maza sun zazzauna, hakanan yaji kirjinshi yabuga dum! Waje yasamo yay parking motarshi yadade zaune sanan ahankali yafito ya tsaya jikin motanshi yana kallon jama’a dake shiga da fita gidan yakasa zuwa, yana tsaye awajen Ya Mu’az yafito tareda wasu friends nashi dasuka zomai gaisuwa, shiga motansu sukayi suka wuce daidai zai juya yakoma ciki idanunshi suka sauka kan Aliyu dake tsaye jikin motanshi yay folding hannunshi yana kallonshi tunani yafara inda yasanshi kafin daga baya kanshi yagayamai police man din ranan nan takowa yayi zuwa inda Aliyu yake tsaye yamikamai hannu dasauri Aliyu yabashi hannu yace “meke faruwane wucewa zanyi naga mutane gate abude shine nai parking, what happen?” Aliyu yasake tambayan Ya Mu’az heart nashi nabugawa, ahankali Ya Mu’az yace “Maman mu ce ta rasu, muje nakaika ciki kaman Baba gaisuwa” Ya Mu’az yay maganan yana gaba binshi abaya Aliyu yayi har zuwa cikin gidan har inda Baba yake kan tabarma tareda Baffa dawasu abokanen arziki Mu’az yakai Hydar, Baba nada gane mutane kallo daya yana Hydar yace “Aliyu” hannu yamikama Baba anatse yace “Baba yahakuri, Allah yajikanta Allah yamata rahama” ahankali Baba yace “Ameen Ameen Allah yayimaka Albarka” sanan yakalli Baffa yace “Wanan ne officer dana gayamaka ranan da Khairy tai shirmen nan yadawo da ita gida” dasauri Baffa yace “Allah sarki, yaro mai hankali angode Malam Aliyu, gashi Ummulkhair ba lafiya da an kirata kamata gaisuwa nasan zataji dadin hakan” gyadama Baffa kai yayi yakasa magana kirjinshi na bugawa dum dum, kafin da kyar ya iya tashi yamika musu hannu yace “bari nakoma wajen aiki” addu’a su Baffa sukamai sosai sanan yajuyo Ya Mu’az biyeda shi har waje zuwa wajen motanshi sanan Ya Mu’az yace “mungode Allah bada lada” murmushi yamai tareda gyadakai har Ya Mu’az yajuya zai wuce yaji yakasa hakura ahankali yace “Ya Ummulkhair take”? Juyowa Ya Mu’az yayi yakalleshi cikeda damuwa yace “not good at all” yay shiru yana kallon Hydar din dayaga ya tsaya yaki tafiya yana kallonshi kaman yana jiran yace wani abu ahankali Ya Mu’az yace “Mama had cancer all this while Khairy bata sani ba cus Mama tahana afadi mata, as it is now kaga yau uku this is the third day da abinci bai shiga bakin Khairy ba, she’s not handling the whole thing very well, she’s not doing okay, kuka suma asma attack duka yahadu mata kaman zatai hauka takeji, kasan she’s very very close to Mama, naji Baffan mu yana cewa yau zasu wuce da ita gidansu Dan gidan nan is not helping her at”. Gyadamai kai Aliyu yayi idanunshi sunyi ja yakasa magana juyawa Ya Mu’az yayi yCawuce ciki.
[6/16, 7:56 PM] +234 701 275 3212: 2️⃣8️⃣


Free page
Shiga motan Aliyu yayi dasauri sanan yatada motan wani irin jan motan yayi da bala’in gudu yayi tafiya mai bala’in tsayi sanan ya gangara gefen hanya ya kashe motan kafin yawani irin daki siterin motan yace “noooooo” he just wish zai iya shiga cikin gidan yaganta, wayanshi yaciro dasauri idanunshi sunyi ja baimasan mezaiyi ba text yashiga turamata.
“Rashin uwa is not something I wish for even my enemy, but muna plan dinmu ne Allah is the master of all planners. Ummulkhair nasan mekikeji, I know abinda zuciyanki kije because I was once there, just know this wherever Mama is she’s resting, tana cikin jannatul Firdaus, I want you to calm down, pray for Mama, cry but just little sabida nasan it hurts alot, babu wanda zai gane how it hurts sai ke, so cry little and pray lot, be strong for me Khairy, and kisani cewa I am here for you koda bana wajen presently but my love and my heart is there with you, I love you to the moon and back Ummulkhair, Allah ya yassaremiki wanan nauyin dakikeji aranki”
Turamata text din yayi yadade ahaka sanan yafuzar da iskan yatada motanshi yawuce.


Bayan sallan magrib Mom da kanta tashigo dakin, Khairy na kwance kan gado tadagota tana kallonta tawani irin rame tace “muje gidan mu, bayan kwana biyu saiki dawo nan bari nakawo miki hijabin ki” bin Mom kawai take da idanu tadauko mata hijabin tazo har gaban gadon tasake dagota danta kara kwanciya tasaka mata hijabin dagota tayi tasauko kasa baya tayi kaman zata fadi dasauri Mom tariketa tana kallon fuskanta idanun idanunta sukai suntum har lokacin jikinta da zafi ahankali tace “kiyakuri Khairy, kiyakuri” fita da ita Mom tayi tana binta luuu kaman wacce tasoma zarewa duk su Baba da kowa na tsakar gida wajajen mota Mom tafito da ita binta da kallo sukayi, dafa Baba Baffa yayi dayaga yana kallonta cikeda tausayi yace “don’t worry she will be fine” karasowa wajen Mom tayi tasata acikin mota bata musu duk yanda akai da ita, kowa shishiga mota yayi Baffa yana su Baba sallama sanan suka tafi da ita.


Suna kaiwa gidan parking suka yi, Zayn yafara saukowa daga motan Ammi side dinshi yawuce dan yagaji he needs rest, Mom kuma tafito da Khairy dahar lokacin take yanda take, Ahankali Baffa dake kallonsu yace “kitafi da ita side dinki tunda akwai Batool” gyadamai kai Mom tayi tawuce da ita itakuma Ammi tadaure fuska tawuce abinta Baffa yabi bayanta yana amsa wayan daya shigo phone nashi.


Kafin suma iso Batool tabude musu kofa tana kallon Khairy dan ita all this while bataje gidan rasuwan ba tana gida tana kulada kannensu, zata fashe da kuka ganin Khairy Mom ta ballamata harara hakan yasa tahadiye kukan taya Mom riketa sukayi sukai sama da ita zuwa dakinsu zaunar da ita kan gado sukayi kwanciya tayi sharaf Batool zatai magana Mom tace “ki barta jekimin tea yanzu zanzo nabata tasha yauma bataci komiba” Gyadamata kai Batool tayi tafito daga dakin tsayawa tayi nan bakin kofa tana kuka ahankali, bude kofa Mom tayi tafito ganinta yasa Mom taidan jim sanan tace “kinsan wahalan da akasha kafin Khairy tadaina kuka? Tana ganinki kina kuka yanzu zata fara” Mom tai maganan tana janta daga wajen kofa sukai stairs, cikeda da bala’in tausayi Batool tace “Mom kaman na Khairy mai surutu ba Mom kaman tazare Innalillahi, duniyan nan babu komi cikinta Mom, look at Khairy damuka sunan Ya Hafiz da ita muna wasa muna rawa, Mom I can’t stand seeing her this way” ahankali Mom tace “then u should support her as ur sister, show her love abinda take bukata kenan yanzu, sanan mudena nuna mata muna tausayinta, kijata ajiki u will help her tadawo daidai” gyadama Mom kai tayi, Mom tace “good yanzu jekiyo mata tea kizo kibata tasha, lemme go and shower” wucewa tayi zuwa kitchen da sauri.

Tea Batool tahado mata tadaura cup din a tray tadawo dakin nasu tana kwance sharaf agadon yanda suka barta, ijiye tea tayi tahayo gadon tadagota ta tashi zaune ahankalli murya chan kasa tace “Khairy zoki sha tea bakici komi ba” tsare Batool tayi da idanu da dazaran kaga yanda take kallon Batool kasan bata hayyacinta don ahankali tace “ina Mama”? Danne kukan datakeji tayi zatai mata magana taji kukan yatokare mata wuya hawaye yazubamata dasauri tashare daidai Mom tashigo hararanta Mom tayi tadauki tea tace “tashi kibani waje” da kyar Mom tasamu ta kurbi tea sau biyu sanan takara kwanciya dagata Mom tayi takaita bayi alwala tamata tasata a dadduma salla tajirata tayi Allah dai ya karba sanan tadagata, wani sabon kayan bacci na Batool Mom ta dauka tasamata bayan tacire mata atampan jikinta spaghetti hand ne dan kaman shimi yake iya guwiwanta ya tsaya mata pink color dan itama Batool nasan komi pink, dawowa tayi kaman wata Yar baby roba akayan looking damn cute, kaita Gado Mom tayi ta kwantar da ita tarufa mata bargo itama kaman abinda takeso kenan rufe idanu tayi dasauri, Mom tazauna abakin gadon tana tofamata addu’a bude kofa akayi Baffa ne yashigo yana sanye da jallabiya ganin Mom namata addu’a yasa ya tsaya yana kallonsu saida tagama sanan yace “tai salla”? “Eh tayi” “what about abinci” Baffa yatambaya anatse, ahankali Mom tace “tasha tea kadan ba laifi, shine na chanza mata kaya nakwantar da ita, karka damu she will be fine nan bada jimawa ba” murmushi Baffa yayi yana kallon Mom ahankali yace “thank you mace tagari” yakalli Batool dake bayanshi tai zuru zuru yace “dama kuka zaki dingayi kika dameni nadawo da ita nan kisami Yar uwa” dasauri ta girgiza kai tace “Bazan karaba Abba” murmushi yayi yashafa kanta yace “jeki kwanta” sanan yakalli Mom yace “jeki kwanta kihuta wife muje narakaki” murmushi tayi ta tashi, itakuma Batool taje gefen Khairy ta kwanta itama tashiga bargon Baffa yakashe musu wuta tareda jawo musu kofa sanan yaraka Mom zuwa dakinta kafin yafito yasauka kasa yakashe wutan falo sanan yaja kofan yawuce side din Ammi.




Wuraren karfe biyun dare tabude idanunta tass jin muryan Mama nakiran sunanta. “Ummulkhairy!” Hakan yasa tabi dakin da kallo ganin Mama tsaye jikin kofa tana sanye da Atampa mai kyau tai lullubi yasa ta yaye bargon data rufa dashi tawani tashi tsaye tai wajen kofan bakinta na motsi, gani tayi Mama tabi ta kofan tafice bude kofan tayi dasauri tafita ko’ina duhu but she could see Mama natafiya akan stairs dan fararen kayane ajikinta, hanyar stairs din tayi itama dasauri ganin Mama tai kofa tafice yasa itama tai kofan, hannu tasa tabude kofan tafice batare data rufe kofan ba, tsakar gidansu kaman rana sabida ko’ina hasken lantarki tashiga sauka daga stairs din gaban kofan tana mika hannu ganin Mama tamata nisa tai hanyar gate murya chan dake cikeda nuna alamun bacci tace “Mama jirani!”



Zaune yake kan daya daga cikin wasu hadadun kujerun dayake nan barandan flat dinshi, irin hadadun kujerun basket dinan da ake sawa a garden, dagashi sai wani gajeren wando dayakaimai guiwa da farin singlet tass yadaura kafafunshi kan class table din wajen yana shan shishi, tunda yadawo naija saiyau yasamu yakeshan shisha, yama fito waje ne yanasha sabida kar dakinshi yakama kamshin gashi Abba nashigowa dakin dakannenshi duka, jin karan kofa an bude flat din Mom dan daga flat din Mom sainashi at this hour of night yasa yasaki pipe din shishan kasa dasauri yana mika hannu yana sauke shisha pot din daga kan table din at the same time yana kallon kofan yaga wanda zai fito daga dakin.
[6/16, 7:56 PM] +234 701 275 3212: 2️⃣9️⃣




Free page
Ganin yarinyar nan da Mamanta tarasu dayaga antaho da ita gidansu dazu dazasu dawo dan he can’t even remember her name yasa yadan ware idanu yana binta da kallo yanda take sauka daga kan staircase din gaban flat din Mom, babu takalmi akafanta babu dan kwali akanta kalaban kanta na lilo atsakiyan bayanta, daga ita saidan rigan bacci pink mai hannun taliya daya tsaya a guiwanta, ganin yanda take tafiya one one as if she’s trying to hold something yasa yadanja karamin tsaki yace “God am I a baby sitter now” jin tace Mama kijirani tai hanyar gate yasa yadanja tsaki yatashi dasauri ganin tai hanyar gate, dawani irin sauri yasha gabanta batare dayace kalaba yay folding hannunshi a chest dan ihu yaso yamata but to his biggest suprise gani yayi gabaki daya idanunta are close is she sleeping walking or what? Yatambayi kanshi daidai ta iso gabanshi babu any tazara tsakanin shi da ita tsayawa yayi yana kallonta just to feed his curiosity yaga mezatayi, wani kalan heart melting murmushi tasaki daya bala’in lobar da dimples dinta all the 2 yabayyana set na white teeth dinta, pink lips dinta nawani kalan shinning kafin ahankali takai duka hannayenta biyun tadaura kan hannunshi daya rungume a kirji takama cikin muryanta kaman na baby tace “Mama kinjirani, Mama I miss u, karki kara tafiya ki barni kinji Mama” tai maganan tana warware hannunshi daya rungume a kirji tasaukar da hannun kasa sanan gently takara tako one more step ta shige cikin jikinshi tai wrapping two hands nata around his back tawani kalan kankameshi tana sauke ijiyan zuciya dahar cikin brain dinshi saida yaji ahankali tace “Mama bacci” tunda yake in his life what he just felt now baitaba jinshi ba, sandarewa yayi hannunshi sauke akasan batare daya iya komiba yanajin saukan ijiyan zuciyanta akirjinshi yana kallon tsakiyan kanta da yanda gashinta ke lilo sabida iskan dake kadawa da yanda heart dinta ke biting each beat yana jinshi anashi heart din, yakai kusan 2min ahaka

Please Login or Register in order to submit comment