Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kyau sukeyi yanda jean da rigan nan suka karbeshi zaka dauka wani American celebrity ne ko wani hip hop rapper hakanan, gashi da tsayi, ko kadan bai lurada itaba jidayayi ajikinshi ana kallonshi yasa yajuyo da kanshi, da sauri tadauke kanta kaman bashi take kallo ba, dan murmushi yayi sanan yacigaba da wayan dayake harta karaso inda yake, zare wayan yayi daga kunenshi yana kallonta, dan lunshe idanu tayi sabida wani irin classic kamshi dayakeyi ahankali tabude su, murya chan kasa tace “ina yini” dan murmushi yayi jin yanda tagaidashi bai amsa ba yabude gaban motan yaciro tsuntsayenta dakuma wani paper bag da popsicles ke ciki duka yasamata a hannu, kallon paper bag din tayi ganin sunanshi yasa takalleshi ahankali tace “thank u” murmushi yamata yamaida kofan motan yarufe sanan yace “direban ki yazo?” Gyadamai kai tayi hakan yasa ya karbe cage din yace “muje nakai miki” jerawa sukayi gabaki daya duka tsawonta a shoulder shi ta tsaya, har wajen motan yakaita gaidashi Adamu yayi ya amsa sanan yabude bayan motan ya ijiye case din sanan yakalleta yanda take tsaye gefenshi yace “get in” shiga tayi ahankali tazauna sanan yamaida kofan yarufe yamata waving hannunshi, murmushi tayi itama tai waving nashi back sanan Adamu yaja motan suka wuce, komawa motanshi yayi tashiga ciki yazauna kafin yaja motan shima hankalinshi ya na bala’in kwantawa.



Gidan Baffa suka wuce, parking Adamu yayi tafito rikeda case nata na tsuntsayen dakuma jakan popsicles dinta tai side din Mom, da sallama tashiga ganin Mom azaune tana koyama Zara’u homework yasa tai wajensu tace “Mom nayi tsuntsu” wani ihu Zara’u tayi tana murna tace “Ya Khairy kibani daya” makemata kafada Khairy tayi tace “zandai aramiki amman bani baki” ihu tayi cikeda murna Khairy tai murmushi wani kalan dadi Mom taji ganinta haka dayasa tama manta ta tambayeta waya bata, cikeda farinciki tace “Ya school din?” Ahankali tace “lpy lau Mom” Popsicles din taciro tabama Zara’u daya tace “ina Batool Zara’u” tana bacci, mikama Mom daya tayi, Mom tace “waaa rabani da kayan zakin nan naku Khairy” dariya tayi takai sauran fridge tarike daya tanasha dayan kuma na Batool tai sama Mom tabita da kallo cikeda mamaki dakuma farin ciki at the same time.

Duka ta dakama Batool dake bacci dasauri tabude ido tana turo baki ganin Khairy ne yasa tama manta dakomi ta rungume ta turata Khairy tayi tace “dalla gashi” dagudu ta karba suka shiga sha tare Batool namata hira, saida ta shanye sanan ta tashi tashiga bayi wanka tayi tafito daure da alwalan magrib salla tayi sanan itada Batool suka tafi dakin Mom.
Adakin Mom Baffa yazo yagansu dukansu sun taru suna koyama Zara’u homework, wani kalan dadi da Baffa yaji zaka dauka kyauta akamai fitowa Mom tayi tasameshi a falon sama wani kalan rungume Mom yayi ahankali yace “thank you for taking Khairy like your own wife” dan hararan Baffa tayi kafin ahankali tace “d’a nakowa ne, karka kara godemin Khairy y’ata ce, Ya Alhaji ya yarda yabika neman Auren kuwa”? Gyadamata kai yayi ahankali yace “amman da kyar, yanzu dai anyi magana nan da sati daya za’a daura auren, for now zan rike Khairy anan duk randa taji tanason zuwa gidan su she can go amman dai tana nan koya kika gani” gyadamai kai tayi tace “hakan yafi, kaga at least nan ga Batool ga Zara’u suna sata surutu, kaga takoma chan ita kadai ba kanne sai Yayyi kuma fita aiki suke abinsu” Gyadamata kai Baffa yayi cikeda gamsuwa da maganan ta yace “bari naje na kwanta nagaji” ahankali tace “mu kwana lpy” kashema ta idanu yayi yace “ashirya min da kyau gobe ina nan” dan dariya tayi tawuce ciki batare daya tankashi ba tunda yan tsokanan nashi ne suka tashi”.



Har wuraren 11 nadare takasa bacci tuni Batool tai bacci amman ita sai juye juye take tarike wayanta gam a hannunta babu abinda kemata dadi muryanshi kawai takeso taji ko zuciyanta zai mata dadi, tana haka wuraren 11:30 wayanta yahau vibrating, har wani dan gajeren ijiyan zuciya tasauke sanan tadauki wayan takai kunnenta dawata kalan murya da ita kanta batasan tanadashi ba tace “Ya Aliyu ina yini” wani dan kalan murmushi yayi da saida taji sautin murmushin tawaya dataji yasa hankalinta yawani kwanta, ahankali yace “how you?” Murya chan ciki ashagwabe tace “fine” dan shiru yayi sai chan yace “I am sorry nan kirada wuri ba, ina tareda Abba ne, most time around 11 yake barina, sorry for keeping waiting” gyadamai kai tayi ahankali tana turo baki. “Kinci abinci”? “Eh” ta amsashi kadan, “me kikaci” ahankali tace “tuwon shinkafa Mom tayi da miyan taushe” dan murmushi yayi yace “iyye kinci sosai” girgizamai kai tayi tace “oh’oh banci ba” murya chan kasa yace “why Pickle” ahankali tace “miyan was peprish, banson yaji yanasa cikina yay ciwo” cikeda kulawa yace “ohh no sorry about that mekika zo kikaci yanzu” dan murmushi tayi da saida yaji sautin murmushin tace “popsicles dina nakarasa shanye wa” dan zaro idanu yayi yace “duka kika shanye” dasauri ta girgizakai tace “naba Batool da Zara’u, nabawa Mom itama taki karba wai batacin zaki” ahankali yace “who is Batool and Zara’u” anatse tace “yaran Mom ne, Batool ne babba shes 22, itama tana 400level a baze sai Zara’u tana primary one, sai Ammi itakuma ta haifi su Ya Zayn shine Babba, sai Ya Hafiz, sai twin Ya Hassan da Hussain” ahankali yace “Uhm Masha Allah” dan shiru yayi hakan yasa ahankali tace “kaci abinci”? Dan shiru yayi saikuma yay murmushi dan ya bala’in jin dadin tambayan yace “yes, I just had tea yanzun nan tareda Abba, dazu da yamma naci tuwo awajen Gwaggo” wani dan murmushi tayi tace “Gwaggo, u have a grandmom”? Yanda tai tambayan he could feel excitement a voice nata that just tell him batada grandma nata are late.
Ahankali yace “Gwaggo is my grandma ta haifi yara goma amman Abba kadai ya rayu, she’s Fulani daga adamawa, she’s very old though sai masifa da kaima Abba gulma….” Dan dariya kadan dayaji tayi yasa yaji wani dadi hakan yasa tacigaba, yace “she’s very old bata iya tafiya dakanta yakai 10steps haka saida wheelchair nata, but dudda haka garin kaima Abba gulma ranan taje tafadi yanzu ko 5 step bata iyayi dakanta” wanan karan dariya tayi sosai bata taba sani Aliyu ya iya nada labari hakaba. Ahankali yace “why are you laughing I am being serious Gwaggo can gossip” wani irin rushewa da dariya tayi ashagwabe tace “stoppp Ya Aliyu u are so mean” dan murmushi yayi yace “are u supporting that old woman now”? Girgizamai kai tayi tana taushe bakinta, murya chan kasa yace “do you wanna meat her some day”? Gyadamai kai tayi ahankali tace “yes” anatse yace “ok u will meet her some day, zakiga abinda nake fadi, I have sisters also but duk ba anan naija suke aure ba, so they hardly visit sai salla salla, then my little sister Meenah, she’s your age mate kinaso kiganta?” Gyadamai kai tayi tace “eh” ahankali yace “you will I promise, do u have any lectures tomorrow”? Girgizakai tayi tace “a’a gobe Mom tace zanje saloon nai kitso” dan murmushi yayi yace “ayi mai kyau, idan kin tashi da asauba after observing subhi makesure to read Qur’an and ur books afterwards okay” murya chan kasa tace “okay” agogo ya kalla ganin 1 nadare yasa yace “u need to sleep okay” gyadamai kai tayi ahankali tace “saida safe” murya chan kasa dan daso samune suyita magana yace “Allah bamu alkhairi, I love you Ummulkhair!” Dip taji ya katse wayan, wayan tabi da kallo kafin tarungume wayan kam kam ahaka bacci yay awon gaba da ita.
[6/16, 7:57 PM] +234 701 275 3212: 3️⃣3️⃣

This book is 1k pay into 3107021073 aisha Muhammad first bank
Chat me up directly by clicking on this link
wa.me/+2347012181461


Yau bayan sun tashi sunyi salla tama Mama addu’a sosai hana Batool dake kokarin komawa bacci tayi taja hannunta suka shiga kitchen, lafiyayen Moi moi tayi dayaji kifi da kawai sanan tai kosai dakuma kunun gyada koda Baffa yashigo gidan yaganta a kitchen suna girki itada Batool baisan lokacin daya ciro waya yamata video batare datasani ba ya aikama Baba sanan yazauna kusada Mama a falon suna hira sanan suka fito dakomi Baffa saida yazauna yaci kosan da kunun dudda abincin shi is ready, suna zazzaune saiga su Manaf sunzo dubata as usual once in a while zokaga dadi bajewa akayi akai lafiyayyen breakfast afalon Mom saida aka gama tass sanan sukai clearing tazo itada Batool zasuje sama suyi bacci ganin Baffa namagana dasu Ya Manaf, kiranta Baffa yayi hakan yasa tadawo, zama tayi akasa dan gyaran murya Baffa yayi yace “Khairy kafin mahaifiyanki tarasu tanata fama da Baban ki ya kara aure sabida ku amman fir yaki” yadanyi shiru sanan yace “dazata rasu agaban kowa yayyinki nan duk suna wajen ta barmini wasiyya kan na aurar da Baban ki karna barshi baida mata” dan ijiyan zuciya yasauke yace “dalilin dayasa nakira su Manaf kenan su biyo tanan kafin su tafi aiki, inaso nagaya muku nasamoma mahaifiyar ku mata” yasake shiru yana kallonsu sanan yace “bayan long bincike akanta, yar limamin masallacin Utako ne, ba yarinya bace ta taba aure da yara biyu, amman mijinta yarasu, yaran na hannun Maman mijin, tayi karatu a FCE tana koyarwa Awani primary school dashi take taimakon kanta haka, tanada natsuwa ga kirki gakuma ilimin addini, na nemama Baba aurenta inaso nan da sati daya ayi Auren hope kun yarda Ummulkhairy” Baffa yakirata ahankali, murmushi tayi ahankali tace “Allah sanya alheri” cikeda jin dadi Baffa yace “Ameen tashi to kitafi” tashi tayi tawuce shikuma Baffa yacigaba da magana dasu Manaf.



Zasu koma bacci Mom tashigo tace su shirya suje saloon, shiryawa sukayi driver ya kaisu saloon tsife kan akayi aka wanke ana gyaran kafansu, kitso akamata mai kyau shiku daya fito da fuskanta, aka mata pedicure da manicure sanan suka biya kudi suka dawo gida, ganin yanda taketa duba wayanta yasa Batool tace “wa kike jira ne awayan nan” hararanta tayi batace komiba saikuma chan tace “Besty” hararanta Batool tayi tace “wlh karya kike” hararanta itama Khairy tayi tace “serious bata dawo school ba yakamata kuma tashigo Wanan dazamu fara exam next week” “laulayin ciki hala take” dasauri Khairy takalleta tace “ciki” Gyadamata kai Batool tayi tace “haka kawata Zara tana aure yanda kikasan da cikin tai tuntube abakin kofa sai ciki” dan murmushi tayi saikuma ta kalli flat cikinta tana picturing kanta da ciki, sosai Batool kemata surutu har suka kawo gida, duba kitson da akamusu Mom tayi kitson yay kyau sosai barinma na Khairy dan tanada wani irin gashi mai bala’in kyau, ga tsayi ga ciki gakuma santsi.
*****


Yau asabar tun ranan daya siyamata tsuntsu basu kara haduwa ba sabida yanason tai karatu saidai waya da night, baicika kiranta during day time ba sabida aiki, most time text yake mata just to check up on her, ko Allah yasan tanama Aliyu wani kalan so ne dan he’s super good to her, he’s caring ya iyasa taji all damuwanta are gone, bata taba sanin she can’t put mutuwan Mama behind her ba amman Aliyu helped her to, he’s just like her strength, yau sosai take murna sabida zata ganshi, yace he’s taking her out yatura mata sunan french restaurant din dazasu hadu.


Shiryawa tayi cikin wani dogon riga, silk ne milk color yadin is so lush rigan yazauna ajikinta dazaka dauka wata black American model ne, zama tayi tadaura wani black cotton dan kwali tai wani plain simple dauri tasaki jelan gyalen agefen shoulder nata, tadanja dan kwalin baya daya bayyana gaban kitson kanta dayay kyau, kwantaccen gashin gaban goshinta tadau karamin brush tai styling nasu da a bit gel daya bada wasu wavy corners subhanallah bakaramin kyau tayi ba, kallon fuskanta tayi a madubi ganin wuyanta empty yasa tadauki wani simple two step necklace dinta dakeda pendant na diamond tasaka awuyanta wuyanta yafara wani kyalli, sanan tadauki kananun dan kunnensu tasaka, mikewa tsaye tayi tanabin kanta da kallo ganin yanda kayan yabi jikinta yanda boobs dinta suka wanisa gaban rigan yay kyau yasa taji wani kalan kunya, wardrobe dinta tayi tadauko wani simple dark army green a bit transparent veil normally dark green goes with milk a whole lot yafashi tayi tagaban hakan yarufe kirjinta but still kana hango kyallin diamond necklace dinta ta gyalen, komawa tayi tazauna kan kujera sanan tadauki brush ta taje full black giranta sanan tadau man baki dake shining ta shafa kan lips dinta dayawani haskaka pink lips din, ganin idanunta sunyi bala’in haske dayawa yasa yadauki kwallin Batool ta zizara Omg, dan murmushi tayi dan ita kanta tama kanta kyau kaman taje studio tai hoto, tashi tayi ahankali yau batajin saka hill hakan yasa tasaka slippers na Hermes shima dark army green daya hadu yau complementing dressing nata gabaki daya, she look very simple but yet super super elegant, wani cute little handbag tadauka na Charles and Keith beige color dayasa tai kaman zata gasan kyau sanan tadauki turarukanta tafesa tanadan tunani mezata gayama Mom tabude kofa tafito, afalo tasami Mom zaune Batool batanan taje gidan kawarta amso note sabida fitanta da Aliyu yasa bata rakataba, ganinta yasa Mom tace “wanan gayu haka sai ina Khairiry”? Dan murmushi tayi ahankali tace “Mom zani wajen Besty dubata batada lpy” ahankali Mom tace “ayyah, laulayi Batool tagayamin dama, ki gaidamin da ita Allah sarki yarinya, haka tadinga sintirin zuwa dubaki, ki gaishemin da ita please” gyadama Mom kai tayi tawuce tafita Adamu na ganinta yatada mota shiga bayi tayi tazauna tagayamai inda zasu suka wuce.



Wani hadadden eatry sukaje, saida Adamu yay parking sanan taciro wayanta daga jaka kafin tai dialing number shi taga kiranshi ya shigo hakan yasa tadauka takai kunenta, murya chan kasa taji yace “come out of the car” sanan ya katse wayan, ahankali tafito daga motan tama Adamu bye yatada motan yawuce sanan tajuyo tana waige waige dan bata ganshi ba. “You look breathtakingly beautiful Miss” taji muryanshi ta gefenta, dawani irin sauri tajuyo da kanta ta kalleshi yana sanye dawani yadi mai laushi fari tass, yana wani irin kamshi mai dadi yasanya black glasses a idanunshi yana kallonta hannunshi rikeda flowers masu kyau combination na white and red yamika mata ahankali yace “flowers for Miss Khairy” fuskanshi takara kallo wani irin murmushi tasaki daya bayyana white teeth nata tasa hannu takarbi flowers din sanan ahankali takaisu saitin hancinta tai breathing in wani irin kamshi taji sunayi mai sanyaya rai kafin ta fuzar tasake dago kanta takalleshi cikin wani classic voice tace “I love flowers thank you Ya Aliyu, they’re beautiful” glasses na idanunshi yacire murmushi yamata yace “shall we” gyadamai kai tayi sanan suka wuce ciki tana rikeda flowers dinta kaman wasu english couples, akwai mutane amman badayawa ba table din daya musu reserving yakaita wajen sanan yajamata kujera zama tayi ahankali tace “thank you” sanan ta ijiye flowers nata agabanta tana kallonsu tana shafasu da hannunta, zama yayi kujeran dake facing nata yana kallonta baisan maisa ba but yau kyan datamai daban ne kodan yakwana biyu bai ganta ba, abincin daya musu placing order aka shiga kawomusu abinma mamaki yabata dan abincin sunyi yawa, this is a brunch date wow! Murya chan kasa yace “do you like it” gyadamai kai tayi ahankali tace “thank u” murmushi yasakeyi yace “zakici kosaina baki abaki” makemai kafada tayi akunyace sanan tadauki cutlery tashiga cin lasgana dashi yafi shiga idanunta tsayawa yayi yana kallonta Khairy nada wani irin natsuwa da inba kana tareda ita ba bazaka taba cewa tanadashi ba, she does everything a natse calmly batada rawan jikin nan, kaman taji ajikinta ana kallonta hakan yasa tadago kanta hada idanu sukai dashi akunyace ta sauke kanta tanajan gyalenta zata rufe fuskanta dasauri yace “nooo Pickle sorry bazan kara kallonki ba look nazama makaho” kallonshi tadanyi ganin yanda yay da idanu abin yabata dariya dan dariya tayi shima yayi sanan yafara ciCn nashi .

3️⃣4️⃣



Saida sukaci suka koshi sanan suka ture ga uban abinshi sun rage akwai wayanda bama sutaba ba ahankali yace “shall we?” Gyadamai kai tayi yatashi hakan yasa itama ta tashi suka fito maiikatan eatry namai godiya suka wuce motanshi yabude mata shiga tayi sanan yamaida kofan yarufe yadawo yazauna yatada motan suka bar wajen bini bini yake satan kallonshi ganin sunzo wonderland yasa tawani ware idanunta aljihun motanshi yasa hannu yaciro mata 2 ticket dinsu yamika mata Wanan Karan takasa boye excitement dinta tace “wowwwwww Ya Aliyu I am so sosoooooo happy thank uuu” u welcome baby yay maganan yana shiga ciki parking yayi a inda ake parking sanan yafito itama fitowa tayi she’s so happy datama kasa boyewa zagayowa yayi ta inda take yace “are u happy” gyadamai kai tayi tana dan tsalle tace “yes thank uuu” murmushi yamata yace “let’s go” ciki sukayi yariga yay recharging card nasu yace “me and u competition yau zamuyi kin yarda”? Gyadamai kai tayi tace “and I will win cus I am a born winner” murmushi yayi yace “let’s see then” da bumper cars suka fara suka shiga, both of them were literally screaming suna bubbuge juna da motan shi kanshi Aliyu baitaba sanin he could do this childish play ba sai yau, bugeshi tayi motanshi yakoma baya tahau ihu ta waigo tanamai gwalo kwafa yayi sanan yatashi yafita itama fitowa tayi tana tsalle sosai kaman Yar yarinya tace “I won yayy” hararanta yayi yay gaba dasauri tabishi sukaje next game dayakeso suyi shooting target, indai target ne babu wanda yakaishi but da gangan yabarta shima taci wayyo Ummulkhairy kaman zata zuba ruwa akasa tasha dan dadi, ice cream yasaya mata takarba tanasha saida yajiraa ta shanye sanan suka shiga wajen 3D zasu buga car race, nan ma ita taci, yanda takemai dariya ko shi kanshi baisan ta iya dariya hakaba she was really feeling herself, ta iya game sosai sabida su Maheer dan sunayi a gida, all games na wajen nan saida tayi har teddy bear saida taci katuwa tadauki abinta tana dariya, hararanta yayi yay gaba dasauri tabishi tace “Ya Aliyu wait, fushi kake sorry but I told you I am a winner” juyowa yayi yace “nine looser ko” hannu tadaura akan bakinta tana hadiye dariyan dake zuwa mata tace “uhm’uhm” hararanta yayi yace “let’s go waje kiga wanda zamuyi I promise u will be the one to loose” dasauri with confidence tace “eh muje” tabishi dasauri gaban rollercosta taga sunje koda tana yarinya bata yarda tai abin nan ba sabida tsoro hakan yasa ta ware idanu, magana taga Aliyu yayi da mutanen sanan yazo inda take tsaye yace “harkin fara tsoro ne” turamai baki tayi tace “never” dan bakinta data turamai yakalla saikuma ahankali yace “mutafi to aga who will lost, and yarinya kikamin kuka ko” dasauri tace “ni Bana kuka saikace wata baby” dariyanshi yahadiye dan he already saw d fears a eyes nata, yace “let’s go” tana bite dashi suka shiga wajen, ganin tsoro a fuskanta yasa bai bari ta shiga wajen one person ba, two sitter slot suka shiga na mutane biyu, zama yayi sanan itama tashigo tazauna kusadashi ahankali sakamusu abinda zai rike mutum yahanasu faduwa yayi sukadai akan makeken roller coaster dinan sanan Aliyu yakalleta yace “kin shirya” gyadamai kai tayi gabanta na faduwa tim tim, juyowa Aliyu yayi yakallesu yace “we ready” ajiyan zuciya tasauke hakan yasa yay dan dariya yaciro wayanshi yana bude camera yace “I need evidence” turo baki tayi tana hararanshi sanan aka kunna abun, rawa hannunta yafara tun kafin su fara moving, kawai jitayi sunyi sararin samaniyan Allah wani kalan ihuuu tayi. “Wayyoooo Ya Aliyu banyi banyi nafasa, huuuuu wlh nafasa kayakuri” tai maganan tana kankame idanunta jin kaman hanjin cikinta zai fito shiko dariya kaman zai mutu yana musu video, jin suncigaba da sama abin nawani chillarasu kaman zai kaisu lahira yasa kawai tawani kankameshi tana boye fuskanta akan kirjinshi. “Innalillahi, Ya Aliyu zanyi fitsari, wlh u won, Dan Allah kayakuri kace subari wayyooo Allah na na shiga uku, Ya Aliyu zan mutuuuu” alamu yamusu da hannu dasu kashe jin yanda heart nata ke beating, amman har suka dawo kasa bata saniba ta kankameshi gam gam tana cewa zatai fitasari, yadade yana zaune ahaka feeling her ajikinshi kafin ahankali yace “sokike kimin fitsarin ajiki cus we are down already” dago kanta tayi daga jikinshi ahankali kaman matsoraciya kallon idanunshi take dake cikeda dariya sanan takalli ko’ina ganin suna kasa, dan hararanta yayi yace “matsoraciya kawai harda kuka” dan turo baki tayi sanan akunyace tasake takoma gefenta, ciremusu abin rike mutum din yayi sanan yabude sit din yafita dagangan yashiga duba jikinshi yace “hope bakimin fitsarin ajikina ba” rufe fuskanta tayi da hannu tace “ni banyi ba” sanan ta sauko tagefenshi tabi da gudu tai restroom dan tagani wajen dasuke zuwa, shikuma yawuce dan sayomusu snacks yana kallon video daya musu awayanshi.


Popcorn yasai musu, unsweetened yasaima kanshi dan baicin sugar shi ko kadan itakuma yasaimata mai milk sanan yazauna yana jiranta.

Fitsari tayi sanan tafito tanadan murmushi ita kunya ma takeji, tana cikin tafiya taji an kwalamata kira Ummulkhairy dasauri tajuyo, ganin class governor dinsu yasa tadan tsaya tana murmushi shima yakaraso wajenta da sauri yana rikeda cotton candy guda biyu a hannunshi da alama bashi kadai bane, ganinta yasa yace “wow kema kinzo shakatawa” murmushi tayi tace “eh Governor ya aiki ya shirin exam” ahankali yace “Alhamdulilah” yana kallonta ganin yanda tai kyau yadade yanason Khairy amman yakasa gayamata dan yake yayi yace “u look good Khairy” murmushi tayi tace “thank you bari naje” tajuya zata wuce dasauri yabiyota gabanta yasha sanan yamika mata one cotton candy dake hannunshi yace “atleast take this” girgizamai kai tayi tace “no thank you Governor” dasauri yace “I insist Allah saikin amsa, nawane dana little sister na dama, nakoma nakara sayowa, idan baki amsa ba zanta binki ne wlh” badan taso ba bataso taga kaman wulakanci tamai wanan ma daya rantse saita amsa yasa gently tamika hannu takarbi wanda yake bata sanan tace “thank u” tawuce da sauri binta dawani irin mayen kallo yayi sanan yace “see you on Monday Khairy” ko tankashi batayiba dasauri take tafiya kanta akasa dan tabata lokaci tabar Ya Aliyu chan, jitayi ajikinta ana kallonta, ahankali tadaga kanta, Aliyu tagani tsaye rikeda pop corn guda biyu a hannu, fuskanshi kadai tagani ya tabbatar mata da yaganta tareda class governor dinsu, jitayi kawai jikinta yahau rawa sakin cotton candy don tayi akasa sanan ta taho da sauri kafin takaraso gabanshi gani tayi cikeda bacinrai yawani irin jefar da pop corns din akasa yajuya fuuu kaman zaki yawuce dasauri tabishi tana kiranshi. “Ya Aliyu Ya Aliyu” amman ko waigowa baiyiba har wajen dayay parking mota kafin ta isa wajen dan one step dinshi shine like 3 or 4 step nata harya shiga mota wani irin jan motanshi yayi Saura kiris yabuge wasu yarama ita kanta saida tai ihu Allah yakiyaye bai bugesu ba yafita daga wajen da balCa’in gudu.


3️⃣5️⃣



Jiyayi kafafunta sun mata sanyi wani dan dakali tasamu tazauna bata taba sanin cewa Aliyu nada fushi dakuma zuciya hakaba sai yau, sabida yaganta dawani saiya tafi yabarta anan, jiyayi duk wani iri zuciyanta badadi kaman ba ita bane tagama dariya yanzun nan ba, ahankali tabude jakanta taciro wayanta kiranshi tayi amman har kiran ya katse bai daukaba, hakan yasa takira Adamu tafadamai inda take, baa dauki cikakken 20min ba saiga Adamu yazo mota tashiga suka wuce gida.

Amota ma sake trying nashi tayi amman bai dauka ba, kaiwa gida sukayi hakan yasa tamaida wayan jaka ta fito tashiga ciki, Mom tagani afalo tareda Batool Mom tace “yamai jikin” murmushi tayi tace “yaji sauki Mom tace na gaidaku” “muna amsawa, jeki chanza kaya kiyi wanka ana ma kiran salla saiki salla ki sauko kici abinci” gyadama Mom kai tayi tawuce, daki tashiga wanka tayo tafito salla tayi sanan tazauna shiru jin Mom nakiranta yasa tafice taje abinci taci tadawo daki wasa wasa har 12 bai kirata ba kasa hakura tayi she called him twice bai dagaba kuma bai kirata ba da kyar bacci ya kwasheta ranan hakan yasa washe gari duktai wani kala data tashi takasa tabuka komi koyasan da hakan ne message dinshi taga ya shigo wayanta. “Go

Please Login or Register in order to submit comment