Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

and study for exam naki u have paper tommorow”
Dudda message din baiyi acknowledge na calls nata but tadanji nauyi yasauka daga mind dinta, kasa hakura tayi tamai reply.
“Ya Aliyu I am sorry, please kayakuri” jin shiru baimata reply ba yasa tasake turamai wani sakon.
“I know him, class governor namu ne saisa nama amsa maganan shi, but I will not do it again I promise”

Almost 5min but bataga reply ba, sosai taji ta bala’in damu sake turamai wani sakon tayi.
“Ya Aliyu I am sorry”
Tana turawa yamata reply.
“I said kije kiyi karatu” gyadamai kai tayi kawai ta ijiye wayan book dinta tadauka ta tashi taje tazauna kan dadduma dudda karatun rabi tunanin shine but hakanan ta tursasa kanta tayi.

Yau rabonta dajin muryan Aliyu sati daya chur kenan dan gashi nan wata asabar din ta zagayo, exam ma adaddafe take tabashi hakuri harta gaji yaki hakura dudda kullum saiya mata text yasata tayi karatu but other than that shiru kakeji, har dan ramewa tayi dayake ansan exam take babu wanda yabama abin attention, yau tunda gari yawaye Mom tasata ta shirya taje tagaida matan Baba da tuni akai biki harta tare, bataso taje amman bazata iya cewa no ba hakan yasa ta shirya dan yau at the same time zaa raba gadon Mama abinda yasama bataso taje kenan.


Parking direba yayi acikin gidansu gani tayi gidansu ya chanza an sake penti, Baba tagani akujera a tsakar gidan da alamu shan iska yake yasa farin jallabiya ga flask don shayi agabanshi dawasu papers yarame sosai ganinta yawani fadada murmushin fuskanta yabude mata hannu dawani irin gudu tazo batai wata wata ba tawani rungume shi she miss baba so much, sun dade ahaka sanan tasakeshi yazauna kan kujeran dake kusada shi tace “Baba ina yini” murmushi yamata yana tana kumatunta yace “Khairy na ya jarabawa next week zaki gama ko” gyadamai kai tayi yace “yaushe zaki dawo gida” gidan tabi da kallo sanan ahankali tace “bayan jarabawa Baba” Gyadamata kai yayi sanan yadauki papers dake gabanshi yabata yace “ga gadon Maman ki nan dakika samu na filaye biyu dakuma gidan kifinta guda daya, sai kayayyakin ta, duk wani abu na Maman ki daidai da cokali an raba, duk suna store, su Manaf duk sunkai nasu gidan marayu sunyi sadaka dasu naki kome kikace ayi dasu haka zaayi” ahankali tace “Baba akai gidan marayu, kayanta na sawa zan cire wanda nakeso sauran sai akai” Gyadamata mata kai yayi sanan ahankali yakama hannunta yace “I am here for you Khairy okay, hope bakida any damuwa” dan murmushi tayi tace “Baba I am fine Allah kuwan, ina su Ya Manaf” “sun tafi office” gyadamai kai tayi ahankali tace “ina new Mom”? Yadade yana kallonta sabida yanda tafadi sunan kafin ahankali yace “tana ciki” tashi tayi tace “bari naje nagaidata” tawuce ciki Baba yabita da kallo, ahankali tabude kofar falonsu wani sanyi yamata sallama tadade tsaye kafin ta shiga cikin falon daidai da foot mat nabakin kofa an chanza har tv bango an chanza komi tatas kaman ba gidansu ba kaman ba falon Mama ba, abin was so strange, mutuwa mutuwa wlh karshe ne! yanzu shikenan this falo is not for Mama again na wata ne, Anya zata iya cigaba da zama agidan nan kuwa Anya bazata koma da zama gidan Baffa gabaki dayaba Dan what she is feeling right now jitayi kaman ta kurma ihu hatta labule duka bana Mama bane jin kuka yazo mata sosai dawani irin sauri tajuya zata fita taji ankirata. “Ummulkhairy” chak ta tsaya, sanan takai hannuwanta ta goge hawayen dasuka zubomata daga idanunta tass kafin ahankali tajuyo, sabuwar matan Baba tagani batada wani makusa Babba ce itama amman daga gani Mama ta girmeta sosai, doguwa da ita kana ganinta kaga natsassiyar mace, murmushin dole Khairy ta kakalo ahankali tace “ina yini uhnnn” tama rasa sunan dazata kirata dashi murmushi matan tayi daidai takaraso gabanta hannunta tasa ahankali takama hannun Khairy tace “sunana Mariya, maisa kika tsaya anan bakin kofa keda falonku shigo mu gaisa” taja Khairy cikin falon danne kukanta Khairy tayi sosai sanan ta zauna akan kujeran da Mariya ta zaunar da ita sanan tace “ina zuwa” dasaurinta ta wuce kitchen tafito da drinks a tray takawoma Khairy ta ijiye sanan tasake zama kusada Khairy data kasa kallonta dan wani iri takeji, ahankali takai hannunta tadaura kan cinyan Khairy cikeda tausayawa tace “ina tunamiki da mahaifiyanki ko” dauke kai Khairy tayi da sauri tana kokarin danne hawayen dake gab da zubowa tace “uhn uhn” ahankali Mariya tace “Khairy I am so sorry about your mother’s death, Allah ubangiji ya haskaka makwancinta, Allah yasaka mata da gidan aljanna” ahankali Khairy tace “Ameen” murya chan kasa tace “Khairy mijina na farko nima yarasu so I understand pains dinki sabida yarana suma sunma mahaifinsu kuka, at first da akazo nemama babanki aurena nariga nai alkawari bazan kara aure ba but danaji matarshi tarasu tabar yara abinda yasa na aure mahaifinki kenan sabida inaso nazama uwa ga yaranshi dan ni bansami chance dinan nama yarana hakaba” dasauri Khairy takalleta tana share hawayen daya zubomata, Gyadamata kai tayi tace “bayan rasuwanshi iyayenshi suka karbe yaran, kafin naga yarana yanzu sai Hutu Hutu akawosu sumin kwana biyu, tuntuni naso nazo dakaina ma har gidan Baffan naku ko Baban ki ko yayyinki sukawoni nadawo dake gidan mahaifinki, Khairy just know this, nasan ba lallai ki daukeni ko ki kalleni a matsayin mahaifiyanki yanzu ba saidai a matsayin kishiyaneuwa, I want to assure u ke y’ata ce Khairy, u can come to me for everything and anything, zan rikeki da yayyinki amana kaman yaran da na haifa, bazan taba cutar daku ba kinji” Gyadamata kai Khairy tayi sanan ahankali tace “thank u” hannu Mariya tasa tashare mata hawayen sanan tace tashi muje sama binta Khairy yayi Baba dake kofa yaji komi baitaba jin sonta aranshiba sai yau, tunda akai auren basuma taba kwana daki daya ba dan gani yake kaman yacuci Mama amman yau yakudiri aniya komi zai chanza zai saki ranshi da ita.


Khairy bata bar gidan ba sai bayan sallan magrib shima saida matan Baba tasa tamata alkawari dazaran tagama jarabawa zata daCwo gida.


3️⃣6️⃣



Yauma hartai bacci Aliyu bai kirata ba ita at this junction tama fara tsoro haka Aliyu keda fushi, abinma haduwa yayi yataru yamata yawa hakan yasa ta tashi da zazzabi jikinta zafi gashi hancinta yatoshe mura, wuraren 7:30 tafito kasa, ganinta wani iri yasa Mom tace “meke damunki idanunki sundan kumbura da hancinki” ahankali tace “mura ne” jin yanda take magana da hanci yasa Mom tace “Ayyah sannu zoki breakfast bari nakowa miki maganin mura” kunu tadeba tafara sha bata wani dade ba Mom tasauko rikeda maganin mura karba tayi tasha sanan takarasa shanye kunun ta tashi tama Mom sallama ta tafi.

Tun kafin sukarasa wajen parking space din ta hango Aliyu tsaye yay wani irin bala’in kyau yakara haske kaman wani balarabe, yana sanye da uniform din yan sanda jingine da motanshi yay folding hannunshi a kirji yana kallon motansu tunda ta doso, idanunshi sun fada ciki kadan kana ganinshi kasan shima yawahala yan kwanakin nan kaman yanda itama ta wahala.


Jitayi wani abu yazomata wuya amman ta danne, parking Adamu yayi hakan yasa tafito daga motan ahankali kallonshi tayi kaman yanda yake kallonta, hawayen dataji yazo mata yasa takauda kanta gefe dasauri taredakai bayan hannunta tashare sanan ahankali tadaga kafanta tafara tafiya wuceshi tayi ahankali kaman bata ganshi ba dawani irin sauri yasha gabanta hakan yasa chak ta tsaya batare data dagokai ta kalleshi ba dan dazaran ta kalleshi zata iya kuka kuma bataso tayi, ahankali tace “excuse me please I have exam by 9” dan ijiyan zuciya yasauke tareda lumshe idanunshi jin muryanta sanan ahankali yabude su yadaura akanta, murya chan kasa yace “Ummulkhair!” Wani abune yataso mata tundaga cikinta harzuwa wuyanta dataji inbata amayar dashiba zata iya mutuwa dago idanunta dasukai jaa tayi sun cikada kwala tace “don’t call my name again Ya Aliyu, nadauka ai kadena daukan wayana, kadaina kirana, kadaina texting dina? Why are you here then? Mekazo nema wajena”? Kallonta yake idanunshi sundanyi ja, jiyayi zuciyanshi na tafarfasa, ko kadan baiso yanunama Khairy fushin shi that’s the reason why he avoided her yamaki wayada ita, wani irin zuciya yakawomai wuya ciki wani irin harsh tone that’s not loud yace “kinmin laifi and kina fushi dani? Why would you talk to anyman har kina karban abinshi why?!” Yamata wani kalan ihu da saida tadan firgita tadan koma baya tana kalle kalle tagodema Allah dababu kowa awajen, zuciyanshi yanuna mata yace “kinsan what you did to me? To my heart haaa? Why will you talk to anyman why?? Akanme zaki tsaya kinama wani namiji magana bayan kinsan I love you! My heart beats for you! You are my life! U are my happiness! You are my everything Khairy haaa” yanda idanunshi taga sunyi jajir saida abin yabata tsoro kaman zai daketa, jijiyoyin kanshi sun fito, bayan hannunta tasa tagoge hawayen daya zubomata kafin ahankali tace “Ya Hydar akanme zakai tunanin wani abu bayan nacemaka class governor dinmu ne, is it my fault we bumped into each other that day? Ya Aliyu akanme zakai tunanin wani nakeso bayan nariga nama zuciyata alkawari cewa ita taka ce, zuciyata, gangan jikina, ruhina duka nakane Ya Aliyu Wanan shine ALKAWARIN ZUCIYA na, akan me zakai tunanin bana sonka uhmm”? Hawayen daya zubomata ta share, kawai tawuce fuuuu hannu yamika zai kirata amman yakasa cikin wani irin fushi yadaki motanshi da kafa shikanshi baisan mesa yake da mugun kishi nan ba.


Adaddafe tai exam din ranan, inda ace batai karatu ba dababu abinda zata iya rubutawa sabida yanda babu abinda kemata dadin nan, bata taba sanin haka akeji idan akai fada da masoyi ba sai yau, she miss Aliyu badly, she just miss him.
Tana gama paper tafito bata tsaya jiran su Besty da Amal ba sabida yanda batajin dadin komi ga jikinta yakara zafi, fitowa tayi yanda takeji batajin zama ta iya jiran Adamu yazo daukanta ba hakan yasa tafara tafiya tai hanyar gate, wani irin shan gabanta da mota Aliyu yayi tana ganin motan tajuya zata chanza hanya da sauri yafito baima tsaya mata magana ba hannunta yaja ganin mutane yasa tabishi dan ayanda yake zai iya cewa daukanta zaiyi gaban mutane idan bata bishi ba, bude mata yayi tashiga batare data kalleshi ba sanan yamaida kofan yarufe yazagaya yashiga mazaunin direba yaja motan, batare data kalleshi ba tace “kana fita daga gate kasauke ni natare cab natafi gida” kallonta yayi da jajayen idanunshi cikin husky voice dinshi yace “idan naki fa” hannunta tadaura akan fuska tafashe da kuka sosai cikin kuka tace “I said I am sorry, I don’t have anything to do with class governor munhadu ne by accident, he said yazo wajen da sister shine, and he insisted saina karbi candy hannunshi, I don’t wanna be rude koyaga namai wulakanci saisa na amsa, nabaka hakuri kaki hakura what do you want from me, what do you want from me?” Wani irin fizgota taji anyi da bala’in karfi, dawani irin sauri tabude idanunta jikinta na rawa, tuki Aliyu yake da hannu daya akan titi amman ya fizgota da karfi tana jikin kafadanshi yakai hannunshi ta waist nata yariketa gam ajikinshi takasa kwace kanta yana kallon hanya, dasauri takalli hanyan jikinta narawa tace “Ya Aliyu dan Allah zamuyi accident kayi parking” gangarawa gefen hanya yayi yawani kalan taka burki kaman motan zai kife kankameshi tayi tareda runtse ido gam gam jikinta narawa still, habanta dataji ankama yasa tabude idanunta ahankali, hada idanu sukai da Aliyu da idanunshi sukai ja faduwa taji gabanta nayi, cikin wani irin murya yace “you ask wat do I want from you” gyadamai kai tayi tana wani irin shakkan shi, wani kallon fuskanta yake ahankali yace “I want you Ummulkhair! I want you so bad saisa my heart can not stand yaga kinama any namiji magana, zuciyana yakusan bugawa ranan I had an accident” dan zaro idanu tayi cikeda mamaki, lumshe idanu yayi sanan ahankali yakai fuskanshi dab da nata yana kallonta dawani irin sauri ta lumshe idanunta gabanta nafaduwa dasauri dasauri yadade yana kallon fuskanta ahaka kafin ahankali yadaura goshinshi kan nata yanajin saukan numfashinta akan fuskanshi, cikin wani whispering voice dake nuna so yace “I am sorry for hurting you, I couldn’t help it, Ummulkhair ina sonki da yawa and Aliyu is a very very jealous man bayin kaina bane, can you put up with me? I can’t help it bazan iya magance kishina akanki ba, zaki iya rayuwa dani eh Ummulkhair?” Jitayi zuciyan ta gabaki daya yasaki gyadamai kai tayi ahankali tace “but don’t ever hurt me the way you did by not answering and responding to my calls, Ya Aliyu I….Love yhuu” this is the first time tafadimai kalman daya dade yakeso yaji daga bakinta, ahankali yace “you are the PROMISE OF MY HEART Khairy” ahankali tace “Ya Aliyu nima kaine ALKAWARIN ZUCIYA ta” ahankali yamata peck a forehead sanan yakai hannunshi yashare mata fuska tass sanan gently yasake ta yamaidata kujeran datake kafin ahankali yatada motan zuwa pharmacy, magunguna yasayo mata da ruwa da kanshi yabata sai kallonta yake sanan yadawo motan yatada har anguwan su Baffa yakawota nesa da gida yay parking sanan yakalleta, kallonshi tayi sanan ahankali tabude motan tasauka tawuce saida yaga shi ganta gida sanan yatada motan yabar anguwCan.


[6/20, 7:15 AM] +234 904 375 3898: 3️⃣7️⃣

Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.

wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp

This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461
Thank u❤️


Wuraren 10 yau taga kiranshi wayan na gabda katsewa tadauka ahankali tace “Ya Aliyu” ahankali shima yace “Ya muran? Jikinki yadena zafi” gyadamai kai tayi tace “eh yadena naji sauki” dan ijiyan zuciya yasauke kafin ahankali yace “I am sorry for hurting you Pickle, will you forgive me” gyadamai kai tayi tace “bakomi yawuce” dan ijiyan zuciya yakara saukewa ahankali yace “kinada paper ranan Monday” gyadamai kai tayi tace “yes but in the morning” ahankali yace “good, I want to invite you to my promotion stuff zakizo” wani irin murmushi tayi tace “za’ayi promoting naka awajen aiki”? Dan yatsine fuska yayi yace “kind of and I want you to be there for me, ina stage ina ganinki ina murmushi” dan murmushi tayi sosai tace “to baranzo ba” Dasauri kaman dan yaro yace “pleaseeee Khairirin Baba” dan dariya tayi ganin yanda yake tsokanta ahankali tace “okay shikenan zanzo but kaizaka daukamin jakana” dasauri yace “zanma goyaki like my baby idan kinas..…..” katse wayan yayi dasauri jin alamun mutum tsaye adakinshi, dago kanshi yayi ganin Abba tsaye yana sanye da jallabiya ya rungume hannunshi yana murmushi yasa yaji wani kalan kunya, daman abinda yasa baije wajen Abba ba sabida yay wasu manyan baki ne, patient dinshi saisa baije ba.

Ahankali Aliyu yatashi zaune daga gadon kasa kallon Abba yayi dan murmushin da Abba keyi kadai ya tabbatarmai da yaji all maganan dayake da Ummulkhair, akunyace yace “Abba bakin sun tafi” dan murmushi Abba yayi yamaida kofan yarufe sanan yashigo dakin har zuwa inda Aliyu yake zaunen sanan yazauna agefenshi, ahankali yace “Aliyu so kanada yarinyar dakakeso haka baka sanar dani ba” kunya yasakeji ganin yakasa magana yasa cikeda kulawa Abba yace “what’s her name”? Ahankali murya chan kasa Aliyu yace “Ummulkhair” dan murmushi Abba yayi yadade yanaso yaga Aliyu yayi aure amman ko budurwa Aliyu baidashi, daurewa yayi yay hiding farin cikin shi karya nunamai yace “yaushe zamuje mu nemamaka aurenta”? Dan murmushi yayi dashi kanshi Abba saida yaga murmushi hakan yakara tabbatarmai da yanda Aliyu ke sonta sanan yace “inaso dama takarasa gama school ne Abba” ahankali Abba yace “nan da kaman yaushe kenan” ”sauran mata just one semester, Accounting takeyi” gyadamai kai Abba yayi saikuma yatashi tsaye yana kallonshi ganin yanda har yanzu yakasa hada idanu dashi, cikeda tsokana yace “bari natafi nabarku kucigaba da soyayyan ku, anyway greet my daughter in law for me” dan dariya yayi Abba yawuce yafita ranshi fess. Kiran Khairy yakarayi sai after 1 sanan sukai sallama.



Yau Monday wuraren 12 tadawo gida dan 11 tagama paper ta na yau, tanacin abinci tai bacci dan 4 zata wajen ceremony na karin girman Aliyu.


4 ta tashi agurguje tashiga bayi wanka tayo tana fitowa tai salla sanan tashiga shiryawa cikin wani embroidery exclusive atampa, gold and red, an mata dinkin doguwan riga A-shape dayay mata kyau, dan kwalinshi ta daura dayay kyau akanta sanan tadauki wani simple red veil tasa kafin tadauki wani warwaron zinare ta tasaka da dankunnen zinare mai kyau sanan takalli kanta a madubi kwalli tadauka tasaka ma manyan idanunta kafin tashafa man baki, wani takalmi mai tudu tasaka red, sanan tadauki gold jaka tahada sake kallon kanta tayi amadubi tai wani irin kyau kaman amarya, dan murmushi tayi sanan tafito tana kallon agogo 4:40, sallama tama Mom da sunan zata gidansu sanan tawuce Adamu yadauketa she wants to get a gift for him is his promotion and banda hakama bata taba bashi anything ba, hakan yasa tacema Adamu yakaita wani Men’s boutique.

Shigatayi ciki tana kalle kalle kayan maza ne awajen babu abinda babu gaban wani Jaguar special edition watch tana kallo, yanda take kallonshi yasa mai shagon yadauko yabata murmushi tayi tace “how much is it”? 359k, gyadamai kai tayi sanan tazabi wani bakin sunglasses dayamata kyau shima designers product na police shikuma 156k sanan taciro ATM card dinta tabiya, indai kudi ne tanada shi, every month tun suna yara Baba nabasu monthly allowance, yayyinta nabata kudi just like that, Mama ma nabata kudi, Baffa shima every month saiya bata kudin break dan haka yake kiran kudin, banda random kudin datake samu every now and then bata kashe kudi tanada komi, wrapping everything aka mata sanan tasa aka rubutamata congratulations a paper tag aka makala jikin cute bag din sanan tafito tashiga mota suka tafi wuraren 5:15 sukakai wajen, tana rikeda abin tashiga wajen bayan tanuna IV dinta daya turamata awaya, wajen yacika makil baya tasamu tazauna tana kallon stage lokacin ana decorating Aliyu ana karamai stars a uniform nashi murmushi tayi tahau tafi, yayi wani irin kyau kaman bashiba, bata wani dade da zama ba aka gama abin Dj yasa waka, gani tayi Aliyu ya sauko daga stage din yafara tafiya dudda ana tareshi ana gaisawa dashi but idanunshi nakanta chass, ita bama tasan yaganta ba sai yanzu dataga yana kallonta dauke kai tayi daga kallonshi ganin yanda mutane ke kallon inda yake kallo tahau wasa da yatsunta chan kuma taciro wayan ta daga jaka tana daddannawa. “U look beautiful Pickle Anya zan iya jira kigama school kuwa”? Taji muryanshi akanta, dan turobaki kadan tayi sanan takalleshi ganin yanda yake kallonta yasa akunyace tadau bag dinshi tamikamai murya chan kasa tace “congratulations” wani irin kallon cute bag din yayi sanan yay murmushi yasa hannu yakarba yace “Pickle got me gift, I promise dazaran nakoma gida shi zan fara budewa thank yo….” Bai karasa maganan ba jin wayanshi na ringing zaro wayan daga aljihu yayi yakalli screen din sanan yamaida kafin yakalleta yace “come muje lemme introduce u to some people” makemai kafada tayi ahankali tace “ni kunya nakeji kabari natafi” dan hararanta yayi yace “kokizo muje Kona daukeki wlh” dasauri ta tashi daga kan kujeran tana turomai baki, murmushi yayi yace “muje gimbiyar Aliyu” jerawa sukayi atare yana kallonta ganin yanda take bin wajen da kallo tayi kyau ba kadan ba kaman amarya, wajen dasu Gwaggo ke zaune yakaita, Gwaggo da Mami sai Meena da Khadija da Amal ke zaune Abba ne kadai bashi awajen shima bai dade da tafiya ba sabida emergency da aka kirashi for a hospital, ita binshi kawai take har gabansu Gwaggo dabatasan suwaye ba, dukansu kallonsu suke sanan yadan juyo yakalleta ahankali yace “meet my family Pickle” Innalillahi! Tafadi dasauri jitayi zata nitse akasa dawani irin sauri tajuya zata gudu dan bama tasan mema zatayi ba, hannunta ya chapke yanadan dariya cikeda wani irin mugun sonta yace “come back here” wani rin boyewa abayanshi tayi tana jan gyalenta trying to cover her face, sanan Aliyun yakalle su Gwaggo kafin ma yay magana Meena tace “Ya Hydar Anty Khairy ce”?Gyadamata kai yayi sanan yakalli Gwaggo hararanta yayi yace “ga Ummulkhairy nakawo miki kiganta” wani irin washe baki Gwaggo tayi itakuma Meena tashi tayi tazo har bayan Aliyu tawani irin rungume Khairy tace “Anty Khairy oyoyooo please kibari inga fuskanki dan Allah” kafinma Khairy tai magana tashi Gwaggo tayi ta dakama Meena duka abaya tace “ke dalla tashi kibama mutane waje da rawan kai zakija yarinya tafadi bakiga kunya takeji ba, angayamiki irinku ce ita fitsararru muna kallonku kuna kallonmu kuri, Khairiya ta yaki kinji” Gwaggo tai maganan tana kamo hannun Khairy, sakin hannunta Aliyu yayi yana binta da kallo ahankali Khairy tabita still tana rikeda hannun Aliyu dake murmushi dudda shi yasaketa, sosai Mami tabi tundaga hannun nata data rike Aliyu dashi da kallo harzuwa fuskan Aliyu dazata iya cewa bata taba sanin yanama murmushi hakaba sai yau, wani irin kallon yarinyar yakema yarinyar kaman zai hadiyeta, zama Gwaggo tayi akan kujera Khairy kuma tadan tsugunna agabanta sanan ahankali taja gyalen Khairy baya sunnar da kai Khairy tayi kasa murya chan kasa tace “ina yini Gwaggo” wani irin washe baki Gwaggo tayi tace “Allah nagode maka Aliyu wayyo Allah na, yarinya ga ladabi ga biyayya gakuma kunya kagama biyana Hydar, Allah ya tabbatar da Alkhairi, inane gidanku gobe zanzo na nemama jikana aurenki” dagota Aliyu yayi dasauri yana hararan Gwaggo yace “ni bazakije neman mini aure ba hakanan kisa ahanani” Mami yadan kalla sanan yadauke kai yace “ga Mami Pickle” ahankali batare data dagakai takalli Mami ba tace “ina yini Mami” kan Mami nakan waya batare data kalleta ba tace “lpy sannu” Khadija da Amal ne duk suka gaidata suna murmushi sanan yakalli Gwaggo yace “bari narakata sai indawo mutafi” dasauri Gwaggo takara tashi tana warware kullin zaninta tace “bari nabata kudin mota” dariya Aliyu yayi yace “direbanta na waje Gwaggo” “kai wlh makirin yaro ne Aliyu bakin ciki kake zan bata kudi kai bani baka, katon banza kawai andaiji kunya” dariya Khairy tayi kanta akasa, sanan Gwaggo takawo dubu daya tasamata a hannu tace “gashi asaiwa kanne tsaraba ki gaidamin da mamanki kinji” Gyadamata kai Khairy tayi tace “nagode Gwaggo” Aliyu ya harareta irin hararan makwaduwa dinan yace “muje” Meena tace “bye Anty Khairy” bye tamata sanan suka wuce Mami tabi Khairy da kallo tundaga kasa har sama daya tabbatar mata da Yar masu kudi ce, ga zinare a hannunta da kunne atampan jikinta kadai is worth 260k gashi kuma taji Aliyu nacewa direban ta na jiranta awaje, a ina Aliyu yasamo Yar masu kudi haka, iska tadan fuzar ahankali takara kallonsu yanda Aliyu ke kappa kappa da ita kaman Yar Kwai, jitayi zuciyanta namata zafi, “kinga Zainabu kiramin mijinki awayanki bani da kati atawa in gayamai danshi yasami mata ohhh ashedai zanga Auren Aliyu kafin na mutu iyye, kai Allah nagode maka Allah, kiramin imaza” akufule tace “nima banda katin” dasauri Meena tazo wajen tace “Gwaggo inada shi bari nakira” wai Gwaggo kaman zata zare, sabida murDna.
[6/20, 7:15 AM] +234 904 375 3898: 3️⃣8️⃣

Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.

wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp

This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp number na 07012181461
Thank u❤️


Saida sukakai waje kaman zatamai kuka tace “Ya Aliyu maisa baka fadamin u are taking me to your family ba” yana kallon fuskanta yace “sabida nasan bazakije ba idan nagayamiki” kaman zata fashemai da kuka tace “kasa inatajin kunya” dan dariya kadan yayi cikeda tsokana yace “kinata rirrike musu d’a agabansu kina wani boyewa abayana kaman zaki cinyeni” dan dariya tayi akunyace tace “Allah bakada kirki” ”ahaka kike sona” yay maganan yana dagamata gira daya, turomai baki tayi tace “nadena daga yanzu” bakinta yakafe da idanu ganin kallon dayakema bakinta yasa taji wani irin kunya dasauri tajuya tai hanyar motansu bamata tsaya jiranshi ba tabude motan ta shiga, biyota yayi har wajen hakan yasa tasaukar da glass

Please Login or Register in order to submit comment